Chapter 14: Chapter 14
“sauran ki tsaya siyan banza da hofi” murmushi ta yi ta ce“ba zan siya ba, kawai dai chocolate zan ɗauka” ta ƙare maganar tana langwaɓar da kai, taɓe baki Amma ta yi ta ce“shige kuma kar ku daɗe” to kawai ta ce sannan ta waje da sauri.
Tana sauka daga balcony ta hango Maimoon tana tawowa, sanye take da Abaya Egyptian ruwan ƙasa, ta yi rolling mayafin akanta, ta ƙaraso gabanta tana murmushi wanda ke ƙara mata kyau,
“ai na ɗauka sai na yi jiranki”
Ta yi maganar tana kallon Nana, harararta Nana ta yi ta ce“a’a abin da ya fi jirana zaki yi, ni muje” murmushi kawai Maimoon ta yi sannan suka riƙe hannun juna gwanin sha’awa suka nufi parking lot ɗin gidan. Sun yi nisa Maimoon ta ɗan kalleta cike da zolaya ta ce“wai ina sir Junaid kuwa?” taɓe baki Nana tayi ta ce“ni na daina kula shi, kina ganin saboda shi rannan uncle ya dakeni” tuntsirewa da dariya Maimoon ta yi dai dai sanda motar ta yi kwana ta ce“au wai daman wajensa ki ka je?” kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“ba fa wajensa naje ba, bashi da lafiya ne sai abokinsa ya kirani ya faɗa min shi ne naje duba shi” Maimoon ta gyaɗa kanta kafin ta ce“kuma shi ne ki ka kai dare?” ɗan siririn tsaki ta yi ta ce“ke baccine ya kwashe ni, daren ranar ne ban yi bacci ba, kuma da wuri na tashi na fita shi ne da naje bacci ya ɗaukeni” Maimoon ta dinga dariya sai kuma ta ce“eh lallai Ashababba a asibitin ki ka hau bacci?” gyaɗa mata kai Nana ta yi, ta ci gaba da dariyarta, haɗe rai ta yi ta ce“ni ki daina min dariya ke kuma” kallonta ta yi sai kuma ta rufe bakinta da hannunta saboda wata dariyar da ta tawo mata. Nana ta harareta ta ce“banza kawai” ta ƙare maganar tana kallon titi. Har suka ƙarasa supermarket ɗin babu wanda ya sake cewa komai, bayan driver ya yi parking suka fito suka nufi cikin mall ɗin. Banda turaruka da maya-mayai babu wani abu mai amfani da suka siya, sai tarkacen kayan zaki chocolate da biscuits, sai ƙarfe 6:00 sannan suka fito daga cikin mall ɗin, kai tsaye kuma in da drivern su yake suka nufa, suna cikin tafiya kamar daga sama suka ji ya kira sunanta,
Cak Nana ta tsaya amma bata juyo ba, ya ƙaraso gabanta hannayensa zube cikin aljihu, kallonsu ya dinga yi duka kafin ya yi murmushi yana kallon maimoon ya ce“hii Moon” ɗan durƙusawa ta yi ta ce”afternoon sir” ya jinjina kansa sannan ya mai da kallonsa ga Nana wadda ta yi shiru ya ce“Nana me nayi miki da zafi haka ki ka daina ɗaga kirana? Uhm, meyasa? Ko na yi wani laifi ne” ya ƙare maganar yana murmushi. Wata uwar harara ta watsa masa sannan ta ce“saboda banida buƙatar kiran naka, bana son kana kirana, dan Allah kar ka sake ƙoƙarin neman yin magana dani, ka barni na yiwa iyayena biyayya” ta ƙare maganar tana haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo, da wani irin mamaki Junaid ya dinga kallonta, duk zatonsa wasa take dan haka yayi murmushi ya ce“haba Nanata, duk cikin fushin nan? Rannan Abba ya bugeki ne? Ki yi hakuri kin ji” wani irin kallo ta dinga masa sai kuma ta yi tsaki ta kama hannun Maimoon dake tsaye kamar an dasata ta ce“muje dan Allah” daga haka suka yi gaba, da sauri shima ya sake biyo su ya sha gabansu yana kallonta ya ce “wait Nana me ki ke nufi ne? Ban gane inda ki ka dosa ba? Wane ya sauya miki ra’ayi?” sakin hannun Maimoon ta yi a fusace ta ce“baka gane me nake nufi ba? Hala baka ji abin da na ce ba, to bari na maimaita maka, ni Nana na rabu da kai rabuwa ta har abada, ba dan na daina sonka ba sai dan ba zan iya bijirewa iyayena saboda kai ba! Dan haka kaje na nemi wata nima zan zauna da wanda Allah ya zaɓa min, Allah ya baka wadda ta fini”
Tamkar zararre haka Junaid ya dinga kallonta, nan da nan kammaninsa ya sauya, idanunsa suka circiko da hawaye ya shiga girgiza kansa yana faɗin“a’a Nana, wallahi ba ke ba ce, ba zaki taɓa yanke wannan hukuncin ba, ni na san ba haka bane, ƙarya ki ke Nana! Ƙarya ki ke ki ce zaki iya rabuwa dani! Wallahi ba zai taɓa yiwuwa ba!” shiru ya yi yana kallonta ganin yanda ta haɗe rai, ya mai da idanunsa kan Maimoon muryarsa na rawa ya ce“yauwa Maimuna ki faɗa mata ta daina cewa haka dan Allah, ki faɗa min wane ya sauyata? Me ya sa zata min haka?” kallonsa ta dinga yi cike da tausayawa, Nana ta ja tsaki sai kuma ta yi gaba fuuu ta bar wajen, da idanu ya bita sai kuma ya kalli Maimoon kafin ya yi magana ta ce“ka yi hakuri dan Allah, ka bar ta haka, tun da har ta haƙura mu ma haka muke fata, dan Allah kada ka sake nemanta koda a waya ne, ka manta da Naana!” ta ƙare maganar a sanyaye sai kuma ta ratsa ta gefensa ta yi gaba itama. Junaid ya juya yana kallonsu har suka shige mota suka bar wajen, ya durƙushe a wajen yana rike saitin zuciyarsa saboda wani irin bugawa da ta yi.
Basu daɗe da hawa babban titi ba Maimoon ta ɗan kalleta ganin yanda take sharar hawaye tun ɗazu ta ce“amma Nana me ya sa ki ka yi haka? Da gaske kin haƙura dashi? Ko kuma haushi ya baki?” kallonta ta yi sai kuma ta ɗauke kanta cikin shassheƙar kuka ta ce“wallahi na haƙura dashi, na haƙura da sir Junaid, zan zauna da Yaya Safwan koda hakan na nufin mutuwata, ba zan bawa Abba da Amma kunya ba, ba zan bari su yi dana sanin haihuwata ba, ba zan bar su ba!” ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka, matsawa kusa da ita Maimoon ta yi ta dafata kamar jira take ta faɗa jikinta tana ci gaba da kuka, shafa bayanta ta dinga yi a hankali tana sauke numfashi.
Driver na ƙarasa parking suka buɗe motar suka fito, Maimoon ce ta ɗebo kayan nasu duka tana kallon Nana da ke goge hawayenta ta ce“kar ki bari a gane kin yi kuka dan Allah” gyaɗa mata kai ta yi har sannan bata bar sauke ajiyar zuciya ba, suka jera suka fara tafiya babu wanda ya ce komai. Siyama ta dinga kallonsu har suka matso dab da ita, Nana ta ɗan kalleta sai kuma ta ɗauke idanu dan ta ganeta, murmushi ta sakar musu bayan ta tsaya wanda suma ya sanya dole suka tsaya ta ce“sannunku” Maimoon ce kawai ta amsa dan ita Nana ko kallonta bata yi ba, bata damu da rashin amsawar ta ta ba ta ce“yauwa daman na zo wajen Aunty Zahra ne to amma ban ganta ba, shi ne nake tambaya ko kun san inda take” girgiza kai Maimoon ta yi ta ce“ayyah wallahi bamu sani ba, mu ma kin ga dawowar mu kenan” jinjina kai Siyama ta yi, suna shirin tafiya ta sake cewa“au afuwan dan Allah D
Safwan fa?”
Ganin irin kallon da suke mata ba tare da sun bata amsa ba ya sanya ta ɗan yi murmushi tana basarwa ta ce“daman zan ɗan amshi saƙo ne a hannunsa” jinjina kai Maimoon ta yi kafin ta ce“eh Yaya Safwan yanzu ya dawo daga office na san, maybe yana apartment ɗin Hajiya Babba, tun da ba’a fara kiran sallah ba, yana ma can” ta ƙare maganar tana bata tabbacin inda yake, faɗaɗa murmushinta ta yi ta ce“okay na gode sosai bari naje can ɗin” to kawai Maimoon ta ce sannan ta bi bayan Nana wadda ta yi gaba abin ta, Siyama ta juya ta sake bin su da kallo sai kuma ta yi murmushi a fili ta ce“nan gaba kaɗan zaku fara girmamani” ta ɗan yi dariya sai kuma ta bar wajen, Maimoon ta dinga kallon Nana sanda ta tsaya a balcony nasu kafin ta ce“wai me ya sa baki bata amsa ba?” taɓe baki ta yi ta ce“ke ni bata min ba wallahi, rannan na gansu a Apartment ɗin Aunty Zahra, kawai na tsaneta” murmushi Maimoon ta yi tana miƙa mata tata ledar ta ce“ji min baƙin hali kawai sai ki tsaneta, to Allah ya kyauta miki” karɓa Nana ta yi ta ce“ki gaida gida” okay kawai ta ce sannan ta nufi nasu gidan, ita kuma ta juya ta murɗa handle ɗin ƙofarsu.
****
Zaune suke cikin ɗaya daga cikin sorayen gidan guda biyar, wanda kuma shi ne ya kasance na huɗu a lissafi, gabansu wani mutum ne ya durƙusar da kansa yana dube-dube, wuyansa rataye da ƙaton carbi irin mai dubun nan, Mutumin ya yi gyaran murya ya ɗago mummunar fuskarsa irin ta gardawan tsangaya ya kallesu, Kaddu dake zaune kusa da Auntt Khadijah ta ce“Malam ya ake ciki?” atishawa ya yi kafin ya ce“wannan aikin naku zai yiwu, amma domin samun biyan buƙata dole ana da buƙatar juyar da tunaninta” Kaddu ta ce“wace Malam?” sai da ya sake wata atishawar sannan ya ce“ita yarinyar, dole ne a juyar da tunaninta ta dawo ɓangaren ku, dole ne ta sanya baki cikin maganar auren, domin ta haka ne za’a iya jawo hankalin sa har ya fara sonta” Aunty Khadijah dake saurarensa tun ɗazu ta ɗan zaro idanu kafin ta ce“wai kana nufin Zahra za’a juyarwa da tunani?” gyaɗa mata kai ya yi, ta ɗan girgiza kanta ta ce“a’a Malam idan kuma ba’a yi nasara ba fa?” tuntsirewa ya yi da dariya sai kuma ya ce“da baki yarda da aikin namu bane? To idan har ki ka ga an samu matsala sai dai inda ba yanda na ce ku yi ba ku ka yi, dole ne a sauya tunaninta, ta dawo bayanku ta shiga cikin maganar auren, daga nan sai ta jawo hankalin yaron ta hanyar abubuwan da zamu dinga yi, shi kuma a gefe ɗaya zamu yi aiki a kansa, daga nan komai zai zo da sauki zai auri yar ki ya dawo yi miki biyayya kamar ke ce uwar da ki ka haifesa!”.
Aunty Khadijah ta dinga murmushi ba tare da ta ce komai, Kaddu ce ta kalleshi ta ce“tom malam yanzu nawa za’a bada?” girgiza kansa ya yi sai kuma ya ce“a’a ba zan karɓi komai daga hannunku ba, amma nima ina da abin da za’a yi min kamar yanda ki ka sani” Kaddu ta jinjina kanta dan daman ta san da hakan, lokaci ɗaya ta juya tana kallon Aunty Khadijah da ke kallonsu a hankali ta ce“muje ki ji” okay kawai Aunty Khadijah ta ce sannan suka miƙe a tare suka nufi ɗaya soron.
Wani irin kallo ta dinga yi mata kafin a ɗan fusace ta ce“Haba Kaddu ya ma za’a yi na yarda da wannan ƙazamin mutumin? Ta ina? Gaskiya ba zan iya ba, idan yana son kuɗi kawai a bashi” tsaki Kaddu ta yi tana jan hannunta ta ce“ashe ba biyan buƙatar ki ke so ba, to mene a ciki dan dai sau ɗaya, daga wannan fa shikenan ba sake neman wani zai yi ba” shiru ta yi tana tunani, Kaddu ta ɗan yi murmushi ta ce“muje dan Allah” girgiza kai Aunty Khadijah tayi ta ce“kai Kaddu! Kai! Gaskiya bana jin zan iya wata mu’amala da wannan mutumin, to wait idan ma na yarda dashi aka zo aikin bai yi ba shikenan ya cuceni kenan?” harararta ta yi ta ce“kin ga ni ba zaki ɓata min rai a banza ba wallahi tallahi, ya ina ƙoƙari akan ki kuma bakya gani, kin san aikin nasa ne? Wane ya ce miki idan aka yi za’a iya rashin nasara? To ki zauna, idan bakya so kawai mu shige mu tafi daga nan” furzar da iska ta yi daga bakinta tana tunanin abin da ya kamata ta yi, ta yarda dashi ta bashi kanta domin biyan buƙatarta? Ko kuwa ta yi tafiyarta ta nemi wani?.
****
Sati ɗaya a tsakani lokacin shirye-shiryen biki ya kankama, ranar wata Litinin ta kama ita ce ranar da aka kai wa kowace yarinya kayan aurenta, dan haka estate ɗin a cike take da yan uwa da abokan arziki. Zahra ce ta buɗe ɗakin tana kallonta ta ce“Nana har yanzu baki tashi ba?” tana kwance kan gadon ta juya mata ba, ta sanya hannunta ta share hawayenta sannan ta ce“na tashi Aunty”
“to ki fito ki yi breakfast kin ji” toh kawai ta ce, Zahra ta juya ta fita, sai a sannan ta tashi zaune tana sake fashewa da wani sabon kukan, she just can’t believe ace aurenta nan da one week, auren ma kuma bada Junaid ba, da Yaya Safwan wanda ko a mafarki bata taɓa tunanin irin haka zata kasance a tsakaninsu ba, ta goge hawayenta sannan ta janye duvet ɗin data rufa dashi ta sakko daga kan gadon, gaban dresser ɗin ɗakin ta tsaya ta dinga ƙarema kanta kallo a jikin ƙaton madubin, ta rame sosai, idanunta sun firfito har ɗan duhu ta yi wanda yake nuni da rashin kwanciyar hankalin da take ciki. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta bar wajen ta shige toilet, after 20mins ta fito ɗaure da towel, ta ƙarasa press ɗin Aunty Zahra ta buɗe, wata simple gown ta ɗauka mara nauyi ta saka, ta shafa mai a jikinta sannan ta ɗaure kanta da mayafin rigar ta nufi hanyar fita daga ɗakin.
Hayaniyar data dinga ji a parlon shi ne ya hanata ƙarasowa, ta maƙale jikin benan tana kallon su ɗaya bayan ɗaya, Aunty Khadijah ce sai Siyama da Safeena sai kuma wata wadda bata taɓa ganinta ba amma bata fi girman su Safeenan ba.
“Laa Nana ki ƙaraso mana”
Safeena ta yi maganar sanda ta lura da ita, gaba ɗaya suka kalli wajen da taken, ta ɗan sunkuyar da kanta sannan ta ƙaraso a hankali ta ɗan durƙusa tana kallon Aunty Khadijah ta ce
“ina yini?”
Babu yabo babu fallasa ta ce“lafiya sannu” daga haka ta ɗauke kanta, ita ma Nanan bata damu ba ta mai da Idanunta kan Safeena ta ce“sannu sister ya ki ke?” washe baki Safeena ta yi ta ce“Alhamdulillah kefa Nana? Ya shirye-shirye?”
“Suna nan muna fama” Nana ta yi maganar a sanyaye, sai kuma ta kalli Zahra ta ce“aunty bari naje” harararta Zahra ta yi ta ce“ki je ina Nana? Shiga kitchen ki ɗauka breakfast ɗin ki har kusan 1pm baki karya ba” langwaɓar da kai ta yi ta ce“a’a ai zan karya a wajen Amma” girgiza kai ta yi ta ce“ban yarda ba ɗauki ki koma sama ki ci idan ma zaman nan ne baki so” babu yanda ta iya dan bata san musu da Zahra yasa ta tashi ta nufi kitchen ɗin, ba’a jima ba ta fito hannunta riƙe da plate ɗayan kuma ta riƙe mug ta nufi sama da sauri, da idanu suka bita har ta ɓacewa ganinsu sannan Siyama ta taɓe baki ta ce“wai ita wannan yarinyar wace ce a gidan nan? Naga ta fiye girman kai, can you imagine rannan nazo ina musu magana ko kallona bata yi ba” ɗan murmushi Zahra ta yi ta ce“ayyah ai daman Nana bata da magana sosai, in dai bata sanka ba, ba zata taɓa sakin jiki da kai ba, yar ƙanin babansu doctor ce” Aunty Khadijah ce ta ce“har da ita a waɗanda za’a aurar ɗin ne naji Safeena na cewa ya shirye-shirye?” gyaɗa mata kai Zahra ta yi kafin ta ce“eh mana, ai ita ce zata auri Safwan!”
Da wani irin mamaki suka dinga kallonta duka, barin ma Aunty Khadijah da hankalinta ya tashi matuƙa, ta buɗe baki a hankali ta ce“kenan dai ita ce zata fasa aurensa Siyama ta aureshi” Zahra ta kalleta amma bata ce komai, Ɗayar wadda tun zuwansu bata yi magana ba ce ta ce“to ba dolenta ba, ai wallahi sai Siyama ta yi aure s cikin gidan nan!”
Safeena ce ta kalleta sai kuma ta ce“ke Amal me ke damunki ne? Wai mene haka?” harararta ta yi ta ce“bansani ba, wallahi ke duk abin ki sai ta aure shi, to mene amfanin arzikin idan ba’a ci ba, yanzu duk inda ta aureshi mun zama muna da mutum biyu namu a family ɗin nan, nan da wani ɗan lokaci sai ki ga mun mamaye dangin”
Aunty Khadijah ce ta ce“yauwa Amal daɗina da ke hankali, su ai basu gane hakan ba, idan yanzu Siyama ta auri ɗan dangin nan ai kin ga mun ƙara yawa, sunanmu zai daukaka mu ma” murmushi Amal ta yi ta ce“wallahi fa Aunty, ai ki saka ran ki a inuwa da tuggu da makirci sai ya aureta wallahi sai dai idan bai shigo hannunmu ba” tsaki Safeena ta yi ta ce“to sai naga a lokacin da har zai shigo hannun naku bare kuma ya yarda ya auretan, yanzu haka nan da wani satin ma shi ya yi aurensa” wata dariyar mugunta Siyama ta yi sai kuma ta ce“to ai shi tuni yana hannu bari ki ji ba’a shiga dawa dan ƙarya, ko yanzu na kira shi a waya nace masa gani a gidansu ya zo wallahi sai ya zo” ba Safeena kaɗai ba har Zahra sai da ta yi mamaki, ta kalleta a sanyaye ta ce“Siyama me ya sa? Akan me ki ke son dole sai kin shiga tsakanin zumucin su? Mene haka dan Allah?” yanda ta yi maganar cikin sanyin murya ya sanya Aunty Khadijah yin tsaki kafin ta ce“ni ba wannan ba yanzu za ki taimaka ayi maganar nan ko ba zaki yi ba?”
Zahra ta girgiza kanta ta ce“a’a gaskiya ni ba zan jawo abin da zai dameni ba, kudai ku ke ku yi ta yi”
Shiru Aunty Khadijah ta yi tana tunanin yanda zata yi, ashe daman mutumin ƙarya yake mata? Ya ce idan ta tambayi Zahra ba zata bijire ba, sai ma ta fi kowa ɗaukan abun da gaske, but why?.
“Danƙari!”
Ta ce a ranta, amma sam bata yi tunanin duk sun ji maganar ba, Zahra ce ta sake cewa“ni dai dan Allah dan Annabi ku bar wannan maganar, ni wallahi dana san irin abun da zai faru kenan da ban zo ƙasar nan ba, wannan wace irin masifa ce?!”
Taɓe baki Amal ta yi sai kuma ta ce“haba Yaya Zahra ke baki son ci gaban gidanku sai na wani gidan?”
Miƙewa tsaye Zahra ta yi a fusace ta ce“ke kar ki ɓata min rai Amal! Ni idan wannan abun ne ya kawo ku to gaskiya nagode da ziyara ku tashi ku tafi!”
A fusace ita ma Aunty Khadijah ta ce“iyee wato korarmu ki ke daga gidan ki ko Zahra? Korarmu ki ke” ɗauke kai Zahra ta yi ta harɗe hannayenta a ƙirji ta ce“ni in dai irin wannan maganar ce ta kawo ku to wallahi gara ku tafi, dan banga amfanin zuwan naku ba!” ta ƙare maganar tana wara hannayenta. Jin jina kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“eh lallai kin isa! To bari ki ji zamu tafi amma wallahi tallahi sai Siyama ta auri Safwan koda hakan na nufin ke zaki bar gidan!”
Da wani irin expression Zahra ke kallonta sai kuma ta yi murmushi yaƙe ta ce“to Allah ya baki sa’a Aunty, Allah kuma ya tabbatar?” daga haka ta yi hanyar sama fuu ta bar su tsaye.
Tashi itama Safeena ta yi tana kallonsu rai ɓace ta ce“gaskiya wannan ba adalci bane, akan me za’a lalata auren wadda take ciki saboda na wadda ba’a yi ba? Wannan gaskiya ba adalci bane! Kuma Allah ba zai bar ku ba wallahi” daga haka ta ɗauki gyalenta ta yi sama da sauri itama.
Zaman daɓaro Aunty Khadijah ta yi akan kujera tana tunanin mafita, yanzu ya zata yi da Zahra? Ita ce makamin da zata riƙe domin ganin auren nan ya yiwu amma gashi sam taƙi bada haɗin kai, wayarta ta zaro ta shiga danna kira sannan ta kai wayar kunne, ringing ɗaya ta ɗauka kafin ta yi magana Aunty Khadijah ta yi saurin katseta ta hanyar faɗin
“Kaddu ni wannan mutumin zai cuta? Ni zai yaudara? To wallahi ƙarya yake” Kaddu dake kwance kan gadon hotel ɗin ta tashi zaune tana faɗin “mene ne ya faru? Ki min bayani yanda zan gane”
“Kaddu Zahra taƙi aminta da buƙata ta, tama ƙi saurarena ke ƙarshe ma dai korata take daga gidanta”
Girgiza kai Kaddu ta yi ta ce“haba da sake wallahi, ita ta isa, na rantse miki ko kaffara ba zan yi ba akan dole ta yi biyayya, sai dai idan ba wajensa muka je ba, ki jira kawai ki ga da kanta zata dawo tana baki haƙuri wallahi yanda zata yi a maganar auren nan ke ba zaki iya yi ba, kawai ki zuba mata idanu”
Numfasawa Aunty Khadijah ta yi kafin ta ce“amma hankalina ya ƙi kwanciya Kaddu, na kasa samun sukuni sauran sati ɗaya fa bikin”
Tsaki tayi ta ce“ko ranar ɗaurin auren ne sai ya auri Siyama, kuma ki jira ki gani” Okay kawai ta ce sannan ta kashe kiran, ta dago kanta ta kalli su Siyama da ke tsaye cirko-cirko ta ce“ku tashi mu tafi” okay kawai suka ce sannan ta tashi itama suka fice daga parlon.
Acan sama kuwa Zahra ce zaune gefen gado tana hawaye, Safeena dake kusa da ita ta dafata a sanyaye ta ce“dan Allah dan Annabi Aunty ki yi haƙuri, Allah yana tare da ke babu abin da suka isa su yi” cikin shessheƙar kuka Zahra ta ce“tsoro nake ji Safeena, babu abin da Aunty Khadijah ba zata iya ba domin biyan buƙatarta, tana iya kashe min aure indai Siyama zata auri Safwan, ni ba wannan ne ma abin da ya dameni ba, yanda take ƙoƙarin sakani ciki shi ne abin da yafi daga min hankali. Ya zan yi Safeena? Ta ina zan fara ƙoƙarin haɗa Safwan da Siyama? Bayan kuma Nana zai aura, Nana fa, ba zan taɓa iya ruguzawa Nana aurenta ba wallahi, ba zan iya ba, Nana bata cancanci haka daga gareni ba, ita ɗin tamkar ƙanwa take a wajena, idan har zan iya hanaki aure na tozarta ki to tabbas zan iya yiwa Nana haka, kinga ko ba zan taba iyawa ba!”
Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka, Girgiza kai Safeena ta yi itama tana kukan ta ce“nasani Aunty, na san baki da zuciyar mugunta, dan haka kawai ki riƙe addu’a, nima zan tayaki sannan zan faɗawa Umma” da sauri Zahra ta kalleta sai kuma ta girgiza kanta ta ce“a’a kar ki faɗa mata, domin zata ci gaba da ganin baƙin Aunty Khadijah ne, ni kuma ba zan zo haka ba, kawai ki bari Allah ya san yanda zan yi dasu” jinjina kai Safeena ta yi sai kuma ta ce“to Aunty”..



