Chapter 18: Chapter 18
Har bayan mintuna talatin da fara tafiyarsu babu wanda ya ce wa wani komai, Nana ta mai da kanta gefen titi tana kalle-kalle wanda take jin yana ɗan ɗebe mata kewa, she wish ace ba yau zasu koma gida ba, dan daga jiya zuwa yau ta ji wani abu yana ɗan ragar mata daga cikin damuwarta. Saɓanin kwanakin baya da kullum take yini babu walwala. Ringing ɗin wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar data tafi, ta kalli wayar dake kan cinyarta sai kuma ta ɗauka, ganin wanda yake kiran ya ta matse gefen wayar ta mayar ta ajiye sannan ta ci gaba da kallon da take. Ko sakan biyu ba’a ayi ba aka sake kira, ta ɗan saci kallon Safwan dake tuƙinsa ba tare da yana lura da ita ba. Ta sake katse kiran tana tura baki a hankali, ko ajiye wayar bata yi ba ƙarar faɗowar saƙo ya shigo, ta buɗe wayar ganin a WhatsApp ne ya sanya ta shiga, numbern Junaid ta gani dan ta yi unblocking ɗinsa tun bayan daya nemi hakan, a hankali ta buɗe saƙon ganin kamar hotuna aka turo ya sanya ta danna downloading tana jin bugun zuciyarta na tsananta, kamar kiftawar idanu haka hotunan duka suka buɗe, ta yi saurin kifa wayarta bayan ta ga abin da ya turo. Dakyar ta iya mai da kanta gefen titi hawayen dake cikin kurmin idonta ya samu damar gangarowa kan fuskarta, ta ɗan ja numfashi ba tare da sauti ba tana kallon hotunan a cikin idanunta. Sabon sakon daya shigo ya sanya ta sake firgita, ta kasa ɗago wayar saboda fargabar abin da zata gani, sai dai sanin bata da wata mafita data shige ta buɗe saƙon ya sanya ta ɗago wayar, sakone ya rubutu kamar haka
_Ina sake tuna miki ne, idan har ki ka ɗauki maganata wasa to tabbas ranar Lahadi za’a wayi gari da maganar waɗanda hotunan naki a kowace kafa ta sada zumunta, sannan bugu da ƙari Abba zai yi farin cikin da bai taɓa yi ranar ba, domin ranar ta kasance daya daga cikin ranaku mafiya tsada a cikin rayuwarsa. Wato ranar auren yar sa! na san ba zaki so ya rasa wannan farin cikin ba, ko nace baƙin ciki mara misaaltuwa ya maye gurbinsa. Dan haka ki san duk yanda zaki yi a fasa daura miki aure da wannan mutumin, shawara nake baki._
Nana ta dinga kallon screen ɗin wayar tana jin wani irin abu nayi mata yawo tun daga tsakar kanta har zuwa ƙafafunta, gaba ɗaya jikinta ya yi wani irin saki, dakyar ta iya danne hoton da maganar ta yi deleting ɗin su daga kan wayarta. Kafin ta kashe wayar gaba ɗaya tana lumshe idanunta, hawaye suka dinga zuba daga cikinsu kamar an buɗe famfo.
Safwan dake lura da ita tun ɗazu ya ɗan taɓe baki dan duk tunaninsa maganar auren ce har yanzu bata haƙura ba. Ganin sun fara shigowa cikin gari ya sa ya yi gyaran murya ba tare da ya kalleta ba ya ce
“Ina son maganar da muka yi dake jiya ta zama sirri tsakanina da ke, koda wasa banson na ji ta a wani wajen, ka da ki kuskura ki faɗawa wani koda kuwa a cikin labari ne”
Ya ƙare maganar yana kallonta, Bata amsa mata ba, dan babu alamar ma tana sauraren abin da yake cewa, she’s just busy crying. Dan haka a ɗan tsawace ya ce
“Ke Nana!”
Wannan karon ta ji shi sai dai nauyin da idanunsa suka mata shi ne ya hanata buɗe su, muryarta cikin wani irin sanyin da ya shige misali ta ce
“na’am”
“kin ji abin da na ce ko?”
Gyaɗa masa kai ta yi duk da bata jin ba, kuma bata da burin jin koma mene ya ce mata ɗin. Ya jinjina kansa ya ce“good” sannan ya ci gaba da tuƙinsa ba tare da ya sake cewa komai ba.
Har suka ƙaraso gida bata daina kuka ba, kuma ko sau ɗaya bai yi tunanin rarrashinta ba, a ranta ta dinga tunanin Yaya Sultan wanda ta tabbata da ace shi ne yaji tana kuka ba zai taɓa barinta ba, koda ace ya san dalilin kukan nata to sai ya tsaya ya sake jin ba’asi sannan kuma ya yi iya yin sa wajen ganin ya sanya ta yi shiru.
Har ya yi parking a compound ɗin Hajiya Babba bata sani ba, sai da ya ga da gaske bata san zo ɗin a sannan ya kai hannunsa na dama ya taba ta. Ta buɗe idanunta da kyar tana kallonsa, sosai ta bashi mamaki da bai yi tunanin kukan da take har ya kai yawan wannan ba, Babu yabo babu fallasa ya ce
“it will be better for you if you stop this nonsense, ki sauka ki tafi gida”
Bata ce komai ba ta ɗauki wayarta da ke kan cinyarta sannan ta sauka daga motar, kowa apartment ɗin Hajiya Babba ya nufa amma ita juyawa ta yi ta nufi nasu sashin dan bata jin zata iya magana da kowa. Babu kowa a parlonsu sai tv dake aiki ita ɗaya, ta ɗan kalli hanyar kitchen jin ƙamshi na tashi yasa ta tabbatar da Amma na kitchen dan haka kai tsaye daƙinta ta nufa, koda ta shiga zame doguwar rigar jikinta ta yi ta faɗa kan gado ta rufe jikinta gaba ɗaya sannan ta sake fashewa da wani irin kuka tana jan numfashi da kyar..
****
Around 9:30pm Zahra ke zaune gefen gadon tana shafa bayanta a hankali, sai da ta tabbatar da baccinta ya yi nisa sannan ta tashi ta rage gudun ac ta rufeta ruf da duvet sannan ta sauya mata hasken zuwa blue ta fice daga ɗakin. Sai da ta koma daƙinta ta fashe jikinta da turare sannan ta nufi ɗakinsa tana gyara zaman doguwar sleeping dress ɗin dake jikinta. A hankali ta tura ƙofar ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, A zuciya ya amsa idanunsa maƙale da farin glasses wanda ya ƙara masa kyau, yana danna system da hannunsa na dama ɗayan hannun kuma ya riƙe mug ɗin coffee sai tiriri yake, yana sipping a hankali. Gefen gadon ta zauna tana kallonsa ba tare da ta ce komai ba, Jin har bayan mintuna biyar bata yi magana ba ya sanya ya ɗago kansa yana kallonta fuskarsa a sake ya ce“Da matsala dai?” girgiza kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta, ya ɗan yi jim kafin ya ce“to mene ne?” ɗan kallonsa ta yi ganin ya kafeta da manyan idanunsa yasa ta sake ƙasa da nata a sanyaye ta ce“daman ina son magana da kai ne” rufe system ɗin gabansa ya yi yana gyara zamansa ya ce“okay go ahead”
Zahra ta ɗan yi shiru tana tunanin ta in da zata fara can kuma ta ɗan numfasa cikin sassanyar murya mai cike da ladabi ta ce
“Dan Allah dan Annabi dan girman Allah Doctor kada ka auri Nana, ka da ka yarda da maganar Atta. Wallahi zan iya mutuwa idan ka aureta, ba zan jure ganin ku tare ba, Dan Allah kada ka bari maganganunta su yi tasiri akan ka. Ka rufa min asiri dan Allah…” ta ƙare maganar cike da damuwa mai tarin yawa.
Abdusammad ya dinga kallonta ba tare da ya ce komai ba, fuskarsa kuma sam babu alamun damuwa ko kuma mamaki. Jin shirun nasa ya yi yawa ya sa ta ɗago jajayen idanunta ta kalleshi sai kuma ta sake faɗin
“na sani ka aureni ne ba da soyyayar danginka ba, na sani daman dole wata rana zasu iya cewa ka ƙara aure, kuma wallahi ba zan taɓa ja da wannan ba, ba zan yi yunkurin hanaka ba. Amma dan Allah dan Annabi ka auri wata ba Nana ba! Ka samo mata wadda ban sani ba, dan girman Allah kada watarana ka ce zaka haɗani kishi da Nana, zan mutu ne Doctor.. wallahi mutuwa zan yi…”
Ta kasa ƙarasa maganar saboda wani irin kuka daya kwace mata. Furzar da iska kawai ya yi daga bakinsa still looking at her, Lokaci ɗaya ya saki wani yalwattacen murmushi yana ɗan ɗauke kansa zuwa gefe guda kafin ya yi gyaran murya cikin nutsuwar data gama ratsa shi ya ce
“Fateemarh kenan. Kina tunanin zan iya auren Nana? Ko da ace ya zama dole na ƙara aure. Kina tunanin zan iya zama da yarinyar da nake ma kallon ƴata? Yarinyar da ya ci ace na haifi kamarta, how?”
Ya dakata da maganar yana furzar da iska daga bakinsa. Gyara zamansa ya yi yana riƙo hannayenta duk biyun cikin nasa ya ci gaba da faɗin “Ba zan taɓa auren Nana ba, koda ace zan ƙara aure to ba zan aureta ba. Ballantana ma kawai kina son ɗaga hankalin ki ne akan abin da ki ke da tabbacin ba zai yiwu ba, ko kin manta nan da wani satin i yanzu Nana matar aure ce?”
Ya ƙare maganar yana kafeta da idanu, Zahra ta sunkuyar da kanta tana sauke ajiyar zuciya murya a sanyaye ta ce“ban manta ba, kawai dai na tsorata ne da kalaman Atta. Kai da kan ka kace ba’a tsallake umarninta idan har ta ce ayi abu to dole sai an yi shi, to kuma kana gani da kanta abin da ta ce. Wallahi ba zan taɓa hanaka ƙara aure ba, saboda na san ka yi min, ka aureni duk da kasan hakan ba abu ne wanda aka yarda dashi ba cikin danginka. Sannan kana shige min faɗa idan har wani ya yi yunkurin takani ko kuma aibatani. Kuma ka bani damar haifa maka ƴa wadda na san ba dan ka yarda dani ba, ba zaka taɓa yin hakan ba. Kaga kuwa dan yanzu ka ƙara aure ba zan ja da kai ba!” Ta ƙarasa maganar hawaye na zubowa kan fuskarta.
Murmushi kawai ya yi dan ya san ta dai faɗa ne amma ba har ranta ba. Ya ɗago fuskarta da hannunsa ɗaya yana ƙare mata kallo ya ce“Zahra kenan, ki daina damun kan ki kinji. Ni Abdusammad Muhammad Shuwa banida niyyar ƙarin aure, ban da niyyar yi miki kishiya. A tsarin rayuwata mace ɗaya kaɗai ta wadaceni, muddin na samu mai kyakkyawan hali kamar dai ke ɗin nan” ya ƙare maganar yana jan kumatunta cike da zolaya. Bata san sanda dariya ta kufce mata ba, ta kifa kanta akan cinyarsa tana yi a hankali. Shima murmushi kawai yake dan yaji daɗin ganinta cikin farin ciki.
****
Bayan sallar magriba babu daɗewa ta fito parlon tana sanye da wasu English wears riga da wando wanda basu kamata ba, gashin kanta a gyare kamar koda yaushe ta tufke da riboom ya sauka har gadon bayanta. Ta ƙaraso parlon jiki a sanyaye tana kallon Amma da ke zaune a kusa da Abba tana nuna masa abu a waya, Amma na ganinta ta mike tana faɗin “gata nan ma” da idanu Abba ya kalli Nana sai kuma ya ce“yauwa daughter zo nan” babu musu ta ƙarasa ta zauna in da Amma ta tashi tana kallonsa. Abba ya dinga kallonta ganin yanda ta rame kamar ba ita ba ya ce“Nana lafiyar ki? Akwai abin da ke damunki?”
Ƙirƙiro murmushi ta yi ta ce“Babu komai Abba, kawai nagaji ne” shiru ya yi yana nazarin maganarta can kuma ya ce“anyway tashi muje ki rakani” to kawai ta ce sannan ta mike ta koma daƙinta. Wayarta da ke gefen drawer ta dauka dan yanzu sam bata yarda ta yi nesa da ita, ta buɗe press ta ɗauki wata Dubai chiffon Abaya mara nauyi ta ɗora kan kayanta sannan ta fito parlon. Tsaye ta same shi hannunsa riƙe da car key da alama ita yake jira, tana fitowa ya kama hannunta suka fice daga parlon.
A cikin wata Lexus jeep black colour suka fita daga gidan, Abba da kansa ke driving dan baya buƙatar wani a tafiyar tasu. Nana ta dinga kallon titi ba tare da ta tambayeshi inda zasu je ba, saɓanin da, da idan zai fita da ita ta dinga tambayarsa kenan har sai ya gaji. Abba ya ɗan yi mamaki rashin tambayar tata dan haka ya gyara zamansa yana murza steering motar a nutse ya ce
“Nana”
Ɗago idanunta ta yi ta kalleshi a sanyaye ta ce“na’am Abba”
Yana ƙoƙarin shan kwanar round about ɗin ya ce“tell me me ki ke so? Like abubuwan da ki ke so irin na amare” Nana ta ɗan yi shiru can kuma ta ce“a’a Abba bana son komai” sai da ya juyo da fuskarsa ya kalleta dan ba ƙaramin mamaki hakan ya basa ba. Ya mai da idanunsa kan titi yana faɗin “Na riga da na gama shirya komai, akwai waleema da za’a yi bayan ɗaurin aure wanda duk abokaina zasu halarta, and I want to you to be there saboda akwai waɗanda muka haɗu dasu a makkah time ɗin da muka ce Hajj dake last two years sun ce suna son su ganki, basu san kin girma haka ba” ya ƙare maganar yana murmushi. Nana da ke saurarensa ta jinjina kanta ba tare da ta ce komai ba, Abba bai damu da rashin maganar ta ta ba ya ci gaba da faɗin
“And ina son ki kula sosai Nana, aure ba ƙaramin abu bane, ki yi kokarin zama yarinyar kirki a gidan mijinki, idan ki ka yi haka zan yi alfahari dake. Kin san ke kaɗai ce yata, ke kaɗai Allah ya bani a matsayin kyauta, so duk wani abu da iyaye ke yiwa ya’ya ko kuma suke so daga gare su ni akan ki nake da wannan burin. U’re my last hope Nana, Dan Allah kada ki bawa Abbanki kunya, na sani kina da sauƙin hali amma bakya ji Nana, bakya son zaman lafiya. Dan Allah dan Annabi ki bar wadannan ɗabi’un a matsayin yarinta, ki sani idan ki ka yi aure kin riga da kin girma. Ke ba yarinya ba ce kamar da. Zaki zama uwa ne, dan haka dole ki sauya kin ji ƴar albarka, kada ki bari nayi kuka da ke Nana. Idan har ban samu kwanciyar hankali daga gareki ba ki sani babu wani wajen da zan samu kuma, daga gani har mahaifiyarki ba zamu so koda dana rana ɗaya a kawo mana ƙararki ba. Hakan zai sosa ran mu and na san ba zaki so ran mu ya ɓaci ba ko?”
Abba ya ƙare maganar yana kallonta dan tabbatar da abin da yake son sanin, Allah sarki Nana ban da kuka babu abin da take, dan ba ƙaramin tausayi Abba ya bata ba. Me ta aikata ne? Taya zata iya kaucewa abin da yake gabanta domin ta faranta ran iyayenta? Ya zata yi da Junaid da Aunty Zahra? Wadannan tunanin su ne suke hanata bacci duk dare. Waɗannan tunanin su ne abin da ke neman haifar mata da ciwon zuciya, Ta kifa kanta a tsakanin cinyoyinta tana sake rushewa da wani irin kuka.
Abba da mamaki ya cika shi ya gangara gefen titi ya yi parking ya juyo gaba ɗaya yana kallonta fuskarsa cike da damuwa ya ce
“Nana why? Mene ne? Maganar dana faɗa ce ta saka ki kuka?”
Abba ya jera mata tambayoyin yana ƙoƙarin ɗagota.
Madadin ta bashi amsa sai kawai ta rungumeshi tana sake fashewa da sabon kukan, Abba ya dinga shafa kanta yana cewa ta yi shiru amma sam bata saurarensa. Sai da ta yi mai isarta sannan ta fara sauke ajiyar zuciya tana shessheƙar kuka, Ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce“mene ne?”
Cikin shassheƙar kuka ta ce“Abba tsoro nake ji, wallahi tsoro nake ji Abba” ta ƙare maganar wani kukan na tawo mata, Murmushi irin na manya Abba ya yi sannan ya ce“ki yi haƙuri kin ji, ki daina jin tsoro ina nan babu abin da zai sameki” Abba ya yi magana cikin sigar rarrashi. Da kyar ta daina kukan amma bata bar jikinsa ba shima bai takura mata ba ya yi wa motar key suka ci gaba da tafiya. Har suka je wajen babu wanda ya sake cewa komai, Abba ya yi parking yana kallonta ya ce“Nana taso” a sanyaye ta ɗago kanta wanda take jin yana wani irin sara mata saboda tsabar kukan da take. Ya sauka daga motar sannan ita ma ta sauko tana ƙarewa wajen kallo, Babban shagon furnitures wanda yana ɗaya daga cikin manyan shagunan furnitures a cikin garin Yola. Abba ya riƙe hannunta cikin nasa sannan suka nufi cikin store ɗin.
Kai tsaye second floor suka nufa, Nana ta dinga bin ko ina da kallo dan bata taɓa zuwa irin wajen sai da kayan furnitures ba, duk da yanda take jin babu daɗi hakan bai hanata sakin jikinta tana kallon komai ba, a wani waje mai kama da reception suka zauna Abba ya ɗauko wayarsa ya danna wata lamba sannan ya kau kunne, ita dai Nana ta dinga kallonsa ba tare da ta ce komai ba, after 2mins ya sauke wayar ya sakar mata murmushi ganin yanda take kallonsa. Dakyar ta iya mayar masa da murmushin sai kuma ta sauke kanta ƙasa tana jin wani irin abu ya tsaye mata a ƙirji. Suna nan zaune har bayan mintuna biyar sannan mutumin ya sakko daga sama ya ƙaraso wajen yana kallon Abba cike da girmamawa ya gaishe shi, Abba ya amsa sannan ya tashi yana rike da hannun Nana suka bi bayan mutumin. Can hawa na uku suka hau, wanda komai na wajen yafi kyau da tsada, Nana ta dinga kallon kayan furnitures ɗin masu matuƙar kyau. Ko ba’a faɗa maka ba ka san kuɗi ke magana a wannan wajen, Abba ya yi murmushi yana sakin hannunta ya ce“yanzu ki zaɓa wanda ki ke so anan”
Da sauri ta kalleshi. Ya gyaɗa mata kai, sai kawai ta shige jikinsa tana sakin marayan kuka, girgiza kai Abba ya yi ya ɗago kanta yana murmushi ya ce“ke ba zaki daina rigima ba ko?” hannunta ta sanya ta rufe fuskarta tana ɗan dariya ƙasa-ƙasa. Ya ɗan kalli wajen sai kuma ya ja hannunta ya ce“c’mon muje na tayaki zaɓa” jiki a sanyaye Nana ta bi bayansa, suka dinga kallon kayan tare yana nuna mata wanda suka yi kyau. Abba ya taɓota sanda idanunsa suka sauka kan wasu Fendi casa Italian furniture ta dinga kallonsu ba tare da ta ce komai ba, Abba ya ja kumatunta yana fadin“ko basu miki kyau ba mu sauya?” girgiza masa kai ta yi dan itama kayan sun burgeta. Ya kalli mutumin dake tsaye bayansu ya nuna masa kayan ya ce“wannan muke so” okay kawai ya ce sannan ya nuna musu inda zasu biya, Abba ya yi gaba tana biye dashi. Cashier ɗin ya kalli kayan da suka nuna sannan ya ɗan duba system kafin ya ce
“10.5m”
Okay kawai Abba ya ce sannan ya miƙa masa atm card ɗinsa, Nana ta dinga kallonsa baki buɗe dan gaba ɗaya ta rasa abin cewa. Sai da aka cire kuɗin sannan aka basu receipt sannan ya juyo ya kalleta ya ce“muje” muryarta a ƙarye ta ce
“Abbaaa.”
Yanda ta yi maganar a sanyaye kamar wani abin na damunta ya sa ya ce“mene ne?” kamar zata yi kuka ta ce“sun yi tsada fa” taɓe baki Abba ya yi sannan ya ce“Ko?” ya yi maganar yana yin gaba ba tare da ya jira amsarta ba. Da idanu kawai Nana ta bi shi sai kuma tabi bayansa ganin yana shirin tafiya ya barta. Har suka koma mota babu wanda ya ce wani abu, ita gaba ɗaya zuciyarta a dagule take, ta rasa wani irin abu ya kamata ta yi, farin ciki ko kuma baƙin ciki. Taya ya zata iya bijirewa umarnin Abba? Ta ya zata iya cewa ba zata auri Safwan ba? To amma idan ta yarda da auren Safwan mene ne makomarta a wajen Junaid da Zahra? Zasu fitar da hotunanta domin su shiga tsakaninta da iyayenta da kuma danginta ko kuwa zasu haƙura ne su daina mata barazanar?.
“Ki zauna anan zan amso invitation cards ɗin ku”
Maganar Abba ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi, a hankali ta gyaɗa masa kai tana ɗan kallon in da suka tsaya ɗin dan sam bata lura ma da sun daina tafiya ba. Sai da Abba ya fita daga motar sannan ta samu damar sakin wani irin kuka mai ban tausayi, a fili ta dinga faɗin
“wayyo Allahna, na shiga ukuna. Allah ka gani, kaga abin da ke damuna,Allah ka yi min maganinsa, idan ba zan iya da wannan masifar ba Allah ka ɗauki raina na huta, Allah kada ka bari na tozarta iyayena a idanun jama’a. Allah ka dubeni, Allah ka shiga lamarin nan…”
Ta kasa ƙarasawa saboda kukan daya kwace mata, haka ta dinga rerashi har sai da jijiyoyin kanta suka fara tashi, kanta ya yi mata wani irin nauyi, idanunta suka ƙara kumbura. Ganin Abba yana tawowa ya sanya ya tayi saurin goge idanun tana jan numfashi a hankali. Koda ya shigo bai kalleta ba ya yi wa mota key suka bar wajen.
****
Safeena ta dinga kallonta amma bata ce komai ba, Zahra da ke Ƙoƙarin haɗa miya ta sake cewa“kina ji na kin yimin banza, ban son iskanci fa”
Ajiye wuƙar hannunta ta yi tana jingina da jikin cabinet ta ce“ni ban san abin da zance mikin bane Aunty,saboda ban san yaushe ki ka sauya har ki ka fara goyon bayan su Aunty Khadijah ba. Bayan kina da tabbacin abin da suke shirin yi ba dai-dai bane. Ta ya za’a ce sauran sati ɗaya bikinta ku yi yunkurin hanata aurensa? Ba ma wannan ba yanzu ke da kanki ki ka ce kun je ƙauyensu an nuna miki ba’a son ki, sannan kuma har matar tayi iƙirarin sai ya ƙara aure, kuma fa ki ka ce Nana aka ce ya aura.”
Safeena ta yi maganar tana kallonta. Jinjina kai Zahra ta yi jiki a sanyaye ta ce“eh haka ne, amma kuma ai doctor ya faɗa min ba zai aureta ba, kuma na san tun da ya ce haka ba zai taɓa aurenta ba. Sannan kuma ya ce min nan da next week ai ta zama matar aure…” Zahra ta yi shiru tana nazarin abin da tace. Jinjina kai Safeena ta yi kafin ta ce
“you see, kin ji abin da ki ka ce da kan ki, idan har an yi auren nan next week shi ne ki ke da tabbacin ba zata auri Daddyn Noor ba. Amma idan har ki ka dage sai kin hana auren to ki sani kamar kina kirawowa kan ki kishiya ne da kanki, domin wallahi ba zasu fasa aura masa ita ba. Muddin ba’a yi aurenta da waninsa ba!”
Shiru Zahra ta yi tana kallon Safeena fuskarta cike da damuwa, kenan idan har ta matsawa Nana akan kada ta auri Safwan zata dawo ta auri mijinta?
“Impossible! Ba zan taɓa bari ba wallahi, Nana ba zata taɓa auren doctor ba”
Zahra ta ce tana girgiza kanta, Safeena ta dafata cikin sanyin murya ta ce“mu ma ba zamu miki wannan fatan ba Aunty. Amma ki sani domin ki tabbatar da Nana ba ta auri Daddyn Noor ba dole sai kin bari ta auri Safwan, ki janye jikinki daga gurinsu Aunty Khadijah, wallahi! Wallahi Aunty zasu kai ki ne su baro!”
Zahra ta dinga kallon Safeena ba tare da ta ce komai ba, gaba ɗaya tunaninta ya tsaya cak, ba zata iya barin Nana ta auri Safwan ba muddin Siyama na son aurensa. Haka kuma ba zata bari Nana ta auri Doctor ba dan ba zata jure zama da ita a matsayin kishiya ba, to idan haka ne mene ne abun yi?
“A lalata rayuwarta, a raba ta da kowa nata, ta yanda zata gudu tabar gidan da kanta. Ta yanda zata zama abar kyama a wajen kowa, walau iyayenta ko kuma dangin gaba ɗaya!”



