Chapter 19: Chapter 19
Kamar daga sama haka suka ji maganar dan haka suka juya a tare suna kallonta. Aunty Khadijah ce tsaye jikin ƙofa ta harɗe hannayenta a ƙirji, Safeena ta sauke numfashi tana kallon Zahra wadda ita ma take kallonta. A hankali ta shiga takowa har gaban Zahra ta dafata cikin kakkausar murya ta ce
“Idan har ki na gudun kada daga baya ta zo ta auri mijinki to kawai a rabata da gidan, kin ga hakan zai fi mana sauki gaba ɗaya. Siyama ta auri Safwan ba tare da tashin hankali ba.”
Ta ƙare maganar tana ɗan murmushi, Zahra ta dinga kallonta da mamaki can kuma ta janye hannunta daga kafaɗarta tana faɗin “A’a aunty wannan ba shawara ba ce, kuma ni gaskiya ba zan iya saka hannu cikin lalacewar rayuwar Nana ba. Saboda babu abin da ta yi mana, kuma ni ba tsanarta nayi ba, kawai dai zan yi abin da zai sa Siyama ta auri Safwan amma ban da lalata rayuwarta gaskiya.”
Aunty Khadijah ta yi murmushi tana gyara tsaiwarta ta ce“To kenan kin shirya zama da ita a matsayin kishiya?”
Rai a haɗe Zahra ta ce“akan me zata zama kishiyata?”
“Akan zata fasa auren Safwan mana, ko kina tunanin zasu fasa haɗata da mijinki ne?”
Aunty Khadijah ta yi maganar tana kallonta. Shiru Zahra ta yi tana tunani can kuma ta girgiza kanta ta ce“Ni na san doctor ba zai taɓa auren Nana ba, kuma shi ba’a masa dole ma, dan haka kawai zan yi abin da zata rabu da Safwan. Amma fa ki sani Aunty idan har rabuwarta da Safwan na nufin zata auri mijina wallahi sai dai Siyama ta haƙura, ta auri wani a gidan, tun da akwai sauran samari wanda basu aurar ba.”
Safeena dake gefe tun ɗazu ta yi murmushi sai kuma ta ce“Nima dai abin da nagani kenan Aunty, gara Siyama ta haƙura dashi idan yaso ta auri wani”
Wani mugun kallo Aunty Khadijah ta watsa mata wanda ya sanya ta sunkuyar da kanta, Ta mai da idanunta kan Zahra fuska a haɗe ta ce
“Yanzu ke me ki ke nufi?”
Zahra ta kalleta sai kuma ta ɗauke kai tana kallon gefe ta ce“ni kawai ina nufin ba zan yi abin da zai zo ya dameni ba, ba kuma zan gyara auren wata na lalata nawa ba!”
Murmushin yaƙe Aunty Khadijah ta yi babu yabo babu fallasa ta ce“Alright kin yi ƙokari, abin da baki ƙarasa ba ni zan ƙarasa shi da kaina”
Daga haka ta juya ta fice daga ɗakin kamar zata tashi sama. Safeena ta ƙaraso gaban Zahra tana murmushi ta ce“Yauwa Aunty, kin yi dai dai. Ki bar su suje can su ƙarata”
Shiru Zahra ta yi bata ce komai ba, dan gaba ɗaya zuciyarta ba tai mata daɗi ba yanda suka yi da Aunty Khadijah. Sam bata son tana ɓata mata rai, Safeena ta dinga kallonta jin bata ce komai ba yasa ta ce
“Aunty lafiya?”
Sauke numfashi ta yi sannan ta ce“babu komai Safeena, bari na zo na tafi gida kada dare ya yi min” to kawai Safeena ta ce sai kuma ta koma ta ci gaba da abin da take.
Koda Zahra ta fito zaune ta samu Umma da Amal suna magana, kai tsaye sama ta shige ta dauƙo mayafinta da kuma jakarta sannan ta dawo ƙasan. Umma ta dinga kallonta kafin ta ce“tafiya za ki yi?” tana yafa mayafin akanta ta ce“eh Umma dare ya fara yi” Umma ta jinjina kanta ta ce“haka ne, ki gaida mutan gidan”
“Zasu ji in sha Allah Umma”
Ta ce tana ɗaukan wayarta da ke kan kujera. Amal ta kalleta babu yabo babu fallasa ta ce“ki gaida gida”
“Zai ji”
Zahra ta amsa tana yin waje cikin hanzari.
****
Kaddu ta dinga kallon Aunty Khadijah sai kuma ta ce“to yanzu mene ne abun yi?” tsaki Aunty Khadijah ta yi rai ɓace ta ce“to nima ina na sani, kawai ya cuceni a banza gashi gaba ɗaya asirin nema yake ya saketa” girgiza kai Kaddu ta yi ta tashi daga zaunen da take ta shige bedroom ɗinta. After 5mins ta fito hannunta riƙe da mayafi tana ƙoƙarin yafawa ta ce“tashi mu je kiga”
“Ina zamu je?”
Aunty Khadijah ta tambaya tana kallonta.
“wajensa mana, komawa zamu yi ya faɗa mana yanda ya kamata a yi”
Okay kawai ta ce sannan ta dauki wayarta da jakarta suka fita.
****
Tun da ta shigo gidan take kallon motocin da suka yawaita fiyeda da, ta dinga mamaki wadanda suka zo da yawa har haka. A compound ɗin apartment ɗin su ta yi parking sannan ta sakko ta nufi cikin gidanta kai tsaye. Bata samu kowa a ciki ba dan haka ta haye sama ta shige daƙinta ta zauna tana sauke gajiya.
A can Apartment ɗin Hajiya Babba, Atta ce zaune ta hakimce kan sofa two seater tana sauraren maganar da Abba ke faɗa mata, Har ya kai ƙarshen maganar babu wanda ya ce komai ba, sai jinjina kai take kamar gaske. Sai da taji ya yi shiru sannan ta ce
“To yanzu me ku ke nufi?”
Abba ya ɗan yi murmushi ganin yanda ta haɗe rai ya ce“Ai kin ga Atta kamar a bar wannan maganar ko? Tun da an riga da an gama komai na aure bai kamata a sauya ba”
Taɓe baki ta yi kafin ta ce“wato dai nufi ake ba zai aureta ba?”
Abba ya girgiza kansa ya ce“ba haka ake nufi ba Atta. Da ace ba’a fara maganar aurensu da Safwan ba sai a bari ya aureta, amma tun da har an fara magana kuma yau sauran kwanaki 4 a ɗaura auren kin ga kamar zai zama fitina abun” Atta ta yi shiru ba ta ce komai ba dan tana matuƙar ganin girman Abba, ko Papa da yake gaba dashi bata fiye yarda da zancensa ba kamar na Abba. Jin bata ce komai ba ya sanya Abba ya sauke ajiyar zuciya dan ya san ta haƙura, Above 2mins kafin ta ce
“To idan bai auri Nana ba ni zan saka a kawo masa mata daga gidana, Akwai yarinyar wajen Kaltume Haule sai ya aureta dan wallahi sai ya ƙara aure” ta ƙare maganar tana gyaɗa kai. Abdusammad da ke zaune kusa da Papa ya kalleta sai kuma ya ɗauke kansa, Abba ya yi shiru can kuma ya ce“Amma Atta…”
Katse shi ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu. Cike da masifa ta ce
“Wallahi ba za’a fasa maganar auren nan nasa ba, dole ne sai ya yi aure dan ba zai ci gaba da zama da wadda ba danginsa ba, tana haifa masa ya’ya muna haɗa zuri’a da wasu can bare”
“Atta kina da gaskiya, Nima ina goyan bayan ya ƙara aure. Dan daman nayi shiru ne kawai dan na ya ba da hankalin yarinyar, amma tun da har akwai wadda za’a iya haɗa sun kawai a haɗa su, son samu ma a haɗe da auren duka a yi ranar Juma’an”
Da sauri Abdusammad ya kalli Hajiya Babba wadda ta yi maganar a nutse, Lokaci ɗaya ya ji jkinsa ya yi wani irin sanyi. Dan ya san ko da wasa ba zai taɓa tsallake umarninta ba. Dan haka ya sauke kansa a hankali. Abba daya lura da yanayinsa ya ɗan yi jim can kuma ya kalli Papa da har yanzu bai ce komai ba ya ce
“Yaya kana ji fa”
Jinjina kai Papa ya yi ya ce“Ai duk abin da suka yanke dai dai nan Ahmad. Daman bai yi shawara da kowa ba sanda zai aurota, bai kallemu matsayin iyaye ba yaje ya yi son ransa. Dan haka yanzu dan an aura masa ƴar dangi ai bana jin zai ƙi amincewa.”
Shiru Abba ya yi dan tun da yaji duk sun ce haka to babu makawa sai sun saka ya sake auren, Abdusammad ya tashi ba tare da ya ce komai ba ya fice daga parlon. Da harara Atta ta bi shi sai kuma ta ce“Ka daɗe baka yi zuciya ba. Wallahi tallahi sai ka yi auren nan, idan ma wani surkullen aka yi maka sai mun warware shi”
Murmushi irin na manya Papa ya yi kafin ya ce“Atta kenan”
“To ai naga kamar ba kansa ɗaya ba, ji ana maganarsa ya tashi ya mai da mu gantallalu” Abba bai sake cewa komai ba ya mike ya musu sallama ya bar parlon shima. Atta ta buɗe baki sai kuma ta yi kwafa ta ce“Ɗan uwan ɗayan, wato dan ya tashi shi ne shima ya tashi to ku je da baƙin halinku”
Murmushi Hajiya Babba ta yi ta ce“Atta ki shiga ciki ki huta kin deɓo gajiyar hanya”
Girgiza kanta ta yi ta ce“A’a kafin na shiga cikin a kira min Sulaimanu ya je ya ɗauko Haule a gida” Toh kawai Hajiya Babba ta ce dan ta san halinta da kafiya, tun da ta ce hakan ba zata tashi ba har sai ta gama abin da ta yi niyya.
****
Aunty Khadijah da ke zaune gefen Kaddu ta girgiza kanta idanunta cikin na malamin ta ce“to yanzu mene ne abun yi? Gaba ɗaya Zahra ta fara bijirewa maganata, sam bata ɗaukan abin da nake faɗa mata. Ni kawai gara da kan ka ka yi min maganin waccan yarinyar, ko a yi mata kurciya ta bar gidan kawai. Ko kuma ta shiga duniya”
Malamin ya yi shiru kamar me tunani, can kuma ya fashe da dariya ya ce“babu wata duniya da zata shiga. Sannan babu ruwanmu da yarinyar a cikin aikin da zamu yi yanzu” Aunty Khadijah ta kalli Kaddu sai kuma ta kalli malamin da mamaki ta ce“Ta yaya haka zai yiwu?” Ɗan murmushi ya yi sannan ya ce“wannan ba damuwar ki ba ce, ni na san yanda zan saka ta yiwun. Ke dai abin da nake buƙata daga gareki shi ne ki bada haɗin kai”
“Ni wannan ba damuwata ba ce, muddin zan samu biyan buƙata to koma mene ne zan yi shi. Kawai ka tabbatar da cewa Siyama ta shiga cikin wannan gidan a matsayin suruka. Ko suna so ko basa so”
Aunty Khadijah ta yi maganar a ɗan fusace. Jinjina kai Malamin ya yi ya ce“Ki ɗauka an gama wannan maganar!”
****
Washegari ta kama ranar Laraba, wanda a ranar ne zasu yi henna’s party a cikin estate ɗin. Ƙarfe 8:00 na safe Maimoon ta shigo apartment ɗin, Amma na ƙoƙarin shiga kitchen dan fitowar kenan ta ganta. Gaisheta ta yi ta amsa sannan ta ce“Nana tana ciki?” gyaɗa mata kai Amma ta yi kafin ta ce“eh tana ciki” okay kawai ta ce sannan ta nufi bedroom ɗin Nana.
Tura ƙofar ta yi ta hangeta zaune ƙasan gado ta jingina da jikin gadon fuskarta a rufe, mayar da ƙofar ta yi ta rufe sannan ta ƙaraso ciki tana kallonta a sanyaye ta ce
“Nana!”
Shiru taji ta yi mata, dan haka ta durƙusa tana ƙoƙarin janye hijabin jikinta ta ce“Nana mene ne…”
Cak maganar ta maƙale a maƙoshinta saboda jinin data ga yana zuba daga bakinta, ta ɗagota a ruɗe tana faɗin
“ke Nana, mene ne ya same ki? Mene ne?”
Kasa bata amsa Nana ta yi sai hannunta data riƙe gam tana sauke wani irin numfashi.
Maimoon ta mike da niyyar barin wajen ta sake riƙeta tana girgiza mata kai. Dawowa ta yi ta tsuguna tana riƙe da hannunta ta ce“Bari naje na faɗawa Amma” girgiza kanta ta dinga yi hawaye na zubowa kan fuskarta. Maimoon ta rasa abinda zata yi sai kawai ita ma ta fara kukan, Haka suka dinga rera kukansu ba tare da wani ya jiyo su ba. Sai da suka yi mai isarsu sannan suka bawa kan su haƙuri, Maimoon ta ɗago fuskarta wadda ta yi caɓa caɓa da hawaye tana kallon Nana ta ce“tashi ki wanke jikinki” gyada mata kai kawai ta yi sannan ta mike a hankali ta nufi toilet. Ita kuma ta naɗe laddumar ta ajiye kan drawer tana ƙoƙarin juyawa wayarta da ke gefen drawer ta fara ringing, dan haka ta kai hannu ta dauki wayar tana ƙarewa sunan da ta gani akan screen ɗin da kallo.
“Junaid?”
Ta ce a fili da mamaki. Ganin wayar ta katse yasa ta mayar zata ajiye sai ga text message ya shigo, kamar bata duba ba sai kuma ta kai hannu ta buɗe wayar gaba ɗaya dan ta riga da ta san password ɗinta. Text message ne da bai shige layi biyu zuwa uku ba an rubuta
_Kina ɗaukan maganganuna wasa ko? To idan Allah ya kai mu an jima lalatattun hotunanki zasu isa ga mahaifinki, dan yanzu ma haka na samu numbern wayarsa. Idan kina son ki tabbatar ki hau WhatsApp na tura miki._
Maimoon ta dinga karanta saƙon ba tare da ta fahimci inda ya dosa ba, lalatattun hotuna? Mahaifinta? Sai kawai ta shiga WhatsApp dan already wifi ɗin ta a kunne yake.
Babu inda bata duba ba amma sam bata ga lambar Junaid ba, ballantana taga saƙon da yake magana akai, kaf unreads ɗin dake wayar Nana da basu shige ashirin ba babu wanda bata duba ba, ganin wadda ta yi magana da ita last Khadijah ce ƙawarta ta Aun yasa ta shiga tana duba chats ɗin su. Ganin bata samu komai ba ya sa ta fita tana sake duddubawa. Can ta hango lock chats ta yi ƙoƙarin buɗewa ta ga ya nuna mata sai ta saka Face id, Ta yi tsaki har sannan tana rike da wayar. Nana ta fito daga toilet ɗin tana goge fuskarta wadda take a jiƙe. Ganin Maimoon tsaye da wayarta a hannunta yasa taji gabanta ya yi wani irin faɗuwa, nan da nan tari ya turnuƙeta, da gudu ta karasa gabanta ganin tana shirin faɗuwa ta riƙeta tana mata sannu. Har gaban gado ta kawota sannan ta zaunar da ita ta fice daga ɗakin. Kai tsaye kitchen ta shiga ganin Amma bata ciki yasa ta ƙarasa wajen freezer ta buɗe ta dauki ruwan gora da cup ta fito da sauri. Ɗakin ta koma ta samu Nana in da ta bar ta sai sauke numfashi take dakyar, ta zauna gefenta sannan ta ɓalle murfin robar ta tsiyaya mata ruwan ta miƙa mata. Amsa ta yi ta shanye tas sannan ta bata cup ɗin tana sauke numfashi.
“Ko na ƙara miki?”
Girgiza kanta ta yi tana lumshe idanu. Maimoon ta ajiye robar a ƙasa tana kallonta, After 5mins ganin kamar ta dawo nutsuwarta yasa ta ce
“Nana”
A sanyaye Nana ta juyo ta kalleta sai kuma ta ce“na’am”
Yanda ta yi maganar kamar ba ita ba yasa Maimoon ta dinga kallonta. Sai a sannan ta lura da ramar da ta yi, gaba ɗaya ta sauya kamar ba ita ba. Wuyanta duk ƙasusuwa sun fito duk da daman bata da wata ƙibar arziki, amma ramar tata tafi ƙarfin ta fargabar aure. Idanunta kuwa sun ƙara firfitowa waje kamar zasu faɗo. Maimoon ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce
“Wane hotuna Junaid yake magana akai Nana? Yaushe ki ka ci gaba da kulashi? Wasu lalatattun hotunanki ne a hannunsa? Kuma ya akai ya same su.? Me ya sa yake cewa zai faɗawa Abba?”
Maimoon ta jera mata tambayoyin tana kallonta. Da sauri Nana ta kalleta Lokaci ɗaya hawaye ya cika kurmin idanunta, ta kalli wayarta dake hannun Maimoon sai kuma ta kai hannu da sauri zata karɓa, Maimoon ta janye hannunta ta ce
“Sai kin fara faɗa min mene ne abin da ya haɗa ki da Junaid?”
Cikin kuka Nana ta ce“Dan Allah Maimoon ki bani wayata, dan Allah ki bani”
Tashi tsaye Maimoon ta yi tana mata wani irin kallo ta ce“Wallahi ba zan baki ba har sai kin faɗa min abin da ya haɗaki dashi. Ki faɗa min wasu hotunanki ne a hannunsa, Idan ba haka ba na rantse sai naje na faɗawa Amma yanzun nan, idan yaso ita ta saka ki faɗa!”
Shiru Nana ta yi tana kallonta idanunta cike taɓ da hawaye. Ganin bata ce komai ba ya sanya Maimoon gyaɗa kanta ta ce“Alright tun da ba zaki yi magana ba bari na kira Amma sai ita ki faɗa mata” daga haka ta juya tana shirin ficewa daga ɗakin. Tashi Nana ta yi ta riƙota da sauri a lokacin hawayen dake cikin idanunta suka samu damar zubowa kan kuncinta, ta riƙe gefen hijabin Maimoon tana hawaye a hankali. Haɗe rai Maimoon ta yi tana ƙoƙarin janye hannunta daga jikinta ta ce“Ni sakeni. Wallahi idan har baki faɗa min ba ba zan fasa kiranta ba”
Sauke numfashi Nana ta yi cikin kuka ta ce“shikenan zan faɗa miki ki dawo ki zauna dan Allah” yanda ta yi maganar a mugun sanyaye shi ne ya sake bawa Maimoon mamaki, dan sam ba haka Nana take ba. Ta ɗan kalleta sai kuma ta nufi ciki ta zauna gefen gadon tana kallonta ta ce“Ina jin ki”
Nana ta sanya gefen hannunta ta share hawayen dake zubowa kan fuskarta sannan ta fara bata labarin duk abin da ya faru, tun daga sanda suka rabu dashi a supermarket da kuma sanda ya zo gida ya kawo mata wannan hotunan. Da kuma yanda suka yi da Zahra. Nana ta sauke ajiyar zuciya cikin shessheƙar kuka ta ce
“Ban san ya zan yi ba Maimoon. Bana son Junaid ko kuma Aunty Zahra su fitar da hotuna na, idan Abba ya gani ban san wane hali zai shiga ba, sannan kuma bana son na ce ba zan auri Yaya Safwan ba. Maimoon ji nake dama na mutu, daman ban zo duniyar ba, zuciyata zafi take min wallahi”
Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Maimoon da ke zaune tana kallonta fuskarta ta yi caɓa caɓa da hawaye ta taso jiki a sanyaye ta rike Nana cikin kuka ta ce“Nana shi ne baki faɗawa kowa ba? Shi ne ki ka bar abin a ranki?” girgiza kanta ta yi ta ce“wa zan faɗawa Maimoon? Kowa tunani yake saboda bana son auren nan yasa nake damuwa. Babu wanda ya zauna dani ya tambayeni abin da ya dameni, To taya zan iya fadawa wani?”
Maimoon ta sanya hannunta dake rawa ta share mata hawayenta sannan ta ce“shikenan ki daina kuka, ki zauna mu ga ta inda zamu ɓullowa al’amarin”
Jinjina mata kai kawai Nana ta yi, Ta kama hannunta suka ƙarasa gaban gadon suka zauna sannan ta ce“Yanzu ina ga abin da yafi shi ne a sanarwa da manya. Maganar Aunty Zahra ina ganin uncle ya kamata mu faɗawa, shi ya san yanda zai yi da ita”
Zaro idanu Nana ta yi sai kuma ta shiga girgiza kanta murya a sanyaye ta ce“a’a bana son kowa ya sani, bana son su sani dan Allah”
Maimoon ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce“to Nana idan bashi ba wane ki ke ganin zai fahimceki? Wane ki ke ganin faɗa masa zai kawo sauƙi a lamarin?”
Ta yi maganar cike da damuwa. Cikin kuka Nana ta ce“nima ban sani ba, kuma bana tunanin faɗawa kowa. Amma ya zan yi? Junaid ya ce muddin nayi auren nan sai ya fitar da hotunan, sannan ita Aunty Zahra ta ce in dai na auri Yaya Safwan sai ta fitar dasu. Kenan duk basu son na aure shi ne. Dan haka mafita ɗaya kawai nake nema”
Maimoon ta dinga kallonta can kuma ta ce“wace mafita kenan Nana? Idan baki auri Yaya Safwan ba to hakan na nufin zaki bijirewa maganar gidan nan, kuma hakan na nufin lalata al’amarin”
Nana ta rasa abin cewa sai kawai ta fashe da kuka ta ɗora kanta a cinyar Maimoon. Ita kanta Maimoon kasa daina hawaye ta yi, dan ta san dole sai wani abu mara daɗi ya faru. Ƙaddara ta riga da ta faɗawa Nana, mai fitar da ita sai dai Allah. Bayan mintuna biyar ta ɗago kanta tana kallon Maimoon ta ce
“Maimoon na tambayeki”
“Ina ji”
Ta ce tana gyara zamanta. Nana ta ɗan numfasa sai kuma ta ce“ashe daman ana barazana a soyyaya? Ashe daman mai sonka zai iya abin da zai cutar da kai? Da gaske sir Junaid yana sona kamar yanda nake son shi?”
Ba ƙaramin tausayi ta bawa Maimoon ba, amma ta dake ta girgiza kanta a sanyaye ta ce“a’a Nana, babu yanda za’a yi wanda yake sonki ya yi ƙoƙarin yi miki barazana. Mai son ki tsakani da Allah ba zai taɓa tunanin samunki ta kowace irin hanya ba. Ba zai tunanin cutar da ke ba, Nana na faɗa miki wani abu.?”
Gyaɗa mata kai Nana ta yi, ta numfasa ta ce“Wallahi sir Junaid ba sonki yake ba! Ke ce ki ke son shi fiye da yadda ya dace, amma shi akwai wani abu a ransa”
Nana ta yi shiru tana kallonta, can cikin zuciyarta kuma tana tunanin irin dadewar da suka yi da Junaid. Yanda ya dinga kulawa da ita, ya bata duk taimakon da take buƙata, ya sota ya ƙaunaceta, to ya za’a yi ace ba sonta yake ba? To idan ba sonta yake ba me yake?.
Maimoon ta dinga kallonta ganin ta yi shiru yasa ta ce“ki bar wannan tunanin mu tashi mu yi abin da yake gabanmu”
Girgiza kanta ta yi ta ce“ni ƙirjina ciwo yake ba zan iya yawo ba” Maimoon ta mike tana cewa“a’a ki taso mu je, Atta tun ɗazu ta ce ina ki ke”
Kamar zata yi kuka ta ce“to ni sai an jima zan fita” tana gama faɗin haka ta koma ta kwanta tana juya mata baya. Maimoon bata sake bi ta kanta ba ta tashi ta fice daga ɗakin dan ta san tunda tace hakan ba tashin zata yi ba..
Amma na tsaye jikin drawer tan haɗe wasu takardu na Abba da ya zube, yayinda shi kuma yake zaune gefen gado idanunsa maƙale da glasses yana duba system a hankali. Sai da ta haɗe takardun ta zuba a envelope sannan ta ajiye su gefe guda, ta ɗaga car key ɗinsa zata ɗauke taga wata takarda kamar receipt. Ɗauka ta yi a hankali ta ware ta, ta dinga kallon takardar sai kuma ta kalleshi daga inda take tsayen. Numfasawa ta yi a hankali ta ce
“Yallabai”
“Uhm”
Ya ce ba tare da ya ɗago kansa ba. Amma na sake karanta rubutun takardar karo na uku ta ce“amma sai naga kamar wannan kuɗin is too much” sai a sannan ya ɗago kansa ya kalleta sai kuma ya kalli takardar hannunta. In a very calm voice ya ce“too much for what?”
“Sun yi yawa kuɗin, 10.5m kawai na furniture?”
Kafeta Abba ya yi da idanu sai kuma ya ce“hala akwai wata yar da zan aurar bayan Nana right?”
Amma ta ɗan kalleshi sai kuma ta girgiza kanta ta ce“a’a ba wai haka ba, amma koma ita kaɗai ce ai wannan kayan sun yi tsada” taɓe baki ya yi kafin ya ce“to ni basu min tsada ba. Kuma da a ce ta zaɓi wanda suka fi haka kuɗi ni mai siya mata ne. Sanin kan ki ne bayan Nana bani da wata yar ko ɗan da zan aurar har na masa hidima, ita kaɗai Allah ya min kyautarta. Dan haka idan ba zaki tayani ba, ki yi shiru da bakin ki”
Amma ta yi shiru sanin halinsa yasa yasa ta mayar da receipt ɗin ta ajiye sannan ta ce“to Allah ya ƙara arziki da wadata”
“Amin. Idan kuma kin shirya haihuwar wata yar ne sai ki faɗa min na rage”
Murmushi ne ya kubuce mata, ta kalle shi ta ce“a’a to ni na hana kai na haihuwa ne?” ta ƙare maganar tana zama kusa da shi. Rufe system ɗin gabansa ya yi ya juyo yana kallonta ya ce“to laifin wane? Ni dai kin san jarumi ne ba?” Amma ta ɗauke kanta tana murmushi, Ya tashi yana zare glasses ɗin idanunsa ya ce“bari na zo zan nuna miki” tashi itama ta yi ta ce“Allah ya huci zuciyarka. Ni breakfast ma na ɗora” daga haka ta nufi hanyar fita daga ɗakin da sauri. Da idanu kawai ya bita sai kuma ya yi murmushi ya juya ya shige toilet.



