Chapter 2: Chapter 2
“Su Maimoon?”
Nana ta tambaya tana miƙewa tsaye, jinjina mata kai Hajiya Babba ta yi ta ce”eh su mana, kitchen suka shiga” bata sake cewa komai ba ta nufi hanyar kitchen ɗin da sauri. Tsaye ta samesu suna magana ƙasa-ƙasa, ta dinga kallonsu sai kuma ta ce”ashe kuna nan” Amrah ce ta ce”da mun yi niyyar mu zo apartment ɗinku idan muka bar nan ashe zaki zo kema” ɗan taɓe baki Nana ta yi kafin ta ce”to hirar me kuke?” Maimoon ce ta ƙarasa ta jawota murya can ƙasa ta ce”hirar Yaya Sultan muke, Hameeda ce tace wai tana mugun son shi, shi ne muke addu’a Allah yasa Hajiya Babba ta ce ya aureta, tun da daman duk ta girmemu kuma ta fimu hankali” Nana ta dinga kallonsu amma bata ce komai ba, Hameeda da ke tsaye tun ɗazu bata ce komai ba ta ƙaraso gabanta, hannunta ta kama cikin sanyin murya ta ce”Nana ina son Yaya Sultan tun ba yau ba, duk da naga shi bai fuskanci hakan ba, amma wallahi duk sanda na ganshi ji nake zuciya kamar zata fito. Ina son shi, shi nake burin na aura” ita dai Nana kallonta kawai take tana ayyana wawta irin tata, Ganin bata ce komai ba ya sanya Hameeda ta sauke ajiyar zuciya ta ce”ba zaki taimakeni bane Nana?” Numfasawa Nana ta yi still looking at her ta ce”amma kin yi ganganci Hameeda, akan me zaki fara jin kina sonsa bayan kina da tabbacin ba lallai bane ki same shi? Kin san a gidan nan babu ruwansu da wanda ki ke so, wanda ya dace dake kawai za’a baki. Akan me ki ka fara son yaya Sultan?”
Hameeda ta dinga kallonta sai kuma ta juya ta fara tafiya toward direction ɗin window muryarta na rawa ta fara faɗin”kaddara! Kaddara ce Nana, ita soyyaya babu ruwanta da wanda ya dace, ina son yaya Sultan tun bansan kaina ba, wallahi ina jin idan bashi na aura ba bazan taɓa iya biyayyar aure ba. Nana inason Yaya Sultan fiye da yanda ki ke son Sir Junaid!”
With so much surprised Nana ke kallonta, Ba ita kaɗai ba har da sauran dake tsaye. Ji tayi ƙafafunta suna neman gagara ɗaukanta, ta dinga kallon bayan Hameeda zuciyarta na ɗagawa. Bata ce komai ba ta juya ta fice daga kitchen ɗin gaba ɗaya.
A parlon ta samu Hajiya Babba tana ganinta ta ce”Allah dai yasa ba ɓarna ku kemin a kitchen ba” ko amsa Nana bata samu damar bata ba ta fice daga parlon da sauri kamar zata tashi sama, Hajiya ta dinga bin ta da kallo sai kuma ta taɓe baki sanin halinta ta ce”abun ne ya motsa kenan”.
Bayan fitar ta Maimoon ta ƙarasa gaban Hameeda ta dafata cike da damuwa ta ce”meyasa zaki ce mata haka? kin san batasan ana dawo da maganar sir Junaid ko?” Juyowa ta yi tana goge hawayen fuskarta ta ce”shine zata gane halin da nake ciki, kamar yanda Nana ke son Junaid kuma take da yaƙinin ba zata sameshi ba haka nima nakeson yayanki Maimoon, Dan Allah idan har kina da dama ki taimakeni na aureshi” ta ƙare maganar kuka na kwace mata. Rungumeta Maimoon ta yi cikin shessheƙar kuka itama ta ce”zan so ace ina da wannan damar wallahi da tuni na saka kin aureshi, amma ban isa nace ga abin da zai faru ba, Allah ne kawai yasan ƙaddarar kowane ɗayanmu, kuma ba zamu iya guje mata ba, kawai ki yi addu’a” Hameeda ta dinga gyaɗa mata kai ba dan ta gamsu da maganganun nata ba.
****Koda ta shiga parlon bata samu kowa ba dan haka kawai ta wuce ɗakinta da sauri ta rufe ƙofar, jingina ta yi da jikin ƙofar ta shiga sauke numfashi da sauri da sauri, kafin daga bisani ta fashe da wani irin kuka ta sulale ƙasa kan tiles ta shiga rera kukanta. She wish zata iya ci gaba da zuwa AUN, she wish a ce ita bata kasance ƴa a cikin dangin M-Shuwa ba, da tabbata Sir Junaid shi ne wanda zai zamo miji a gareta, mutumin daya nuna mata ƙauna tun bata san kanta ba, mutumin daya sota saboda Allah ba dan wani abu ko halitta nata ba. Mutumin da take jin bazata iya haƙura da soyyayarsa ba, sai dai ƙaddara ba zata bata ikon rayuwa dashi ba, bata isa ta ce ga wanda take so a cikin gidansu ba, ba za’a taɓa yarda ba! Ba zasu yarda ba!. Nana ta sauke dogon numfashi sannan ta miƙe daya inda take ta koma kan gadonta ta kwanta a hankali kamar me tsoron wani abu, haka ta dinga tunawa da masoyinta Junaid gami da kewarsa, ta dinga jin kamar ta tashi ta koma AUN suyi rayuwarsu cikin farin ciki. Tana nan kwance tana yan matan hawayenta har bacci ɓarawo ya saceta.
Ƙarfe 7:20pm ya shigo cikin gidan, kai tsaye kuma apartment ɗin Hajiya Babba ya nufa, zaune take kan sallaya tana jan cazbahar hannunta, ya ƙarasa ya zauna bayan ya yi sallama ya yi shiru yana jiranta. Sai da ta kammala laziminta sannan ta juyo tana kallonsa ta ce”Aliyu sai yanzu?” jinjina mata kai ya ce fuskarsa ɗauke da fara’a ya ce”wallahi Hajiya, na ɗan tsaya ne da wani former friend ɗina” Hajiya Babba ta ce”to bari a kawo maka abinci” girgiza kansa ya yi ya ce”a’a yanzu na dawo sai nayi wanka na shirya nagaji sosai” Hajiya Babba ta gyaɗa kanta kana ta ce”to shikenan nima isha’i zan yi na kwanta yau yaran nan duk sun gaji dani”
“Su Juwaira sun shigo miki ne?”
“Ai yau ba yaran bane yan matan gidan ne suka dawo daga makaranta”
Aliyu ya ce”to ai ni shaf na manta wallahi su Nana danger an dawo gida kenan” Hajiya ta yi murmushi ta ce”ai har ma ta fara halin nata, daga zuwa ɗazu ta yi baƙar zuciya. Ai jira nake gobe ta yi idan Allah ya ara mana rai na kira su Kabiru azo a yi maganar aurensu kowa ya huta!”
Aliyu ya ɗan yi murmushi ya ce”Daga dawowarsu Hajiya da an bari sun ɗan huta ai” Wani kallon sheƙeke ta masa kafin ta ce”hutun me zasu yi Allah na tuba? Kowacce ta huta a gidan mijinta aurar dasu zan yi!”
Shiru ya yi yana kallonta ba tare da ya ce komai ba, Hajiya ta ci gaba da fad’in “In sha Allah zuwa gobe zan yiwa su Kabiru magana, azo a san yanda za’a yi, dan bana son akai watan gobe ba’a san matsayar aurensu ba” Aliyu ya jinjina kansa ya ce”To Hajiya Allah ya kaimu” Ta amsa da Amin sannan ta ci gaba da laziminta. Tashi ya yi bai ce mata komai ba ya nufi sama, ta bishi da kallo sai kuma ta taɓe baki.
Ƙarfe 8:20 na dare Amma ta dinga knocking ƙofar, ganin har sannan bata buɗe ba ya sanya taja tsaki da ɗan ƙarfi ta ce”Nana! Nana!”
Sai da ta goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta saita nutsuwarta a sanyaye ta ce”na’am Amma”
“Ki fito ina jiranki”
To kawai ta ce sannan ta tashi jiki a sanyaye ta zare hijabin jikinta. Sai da ta ƙarasa gaban mirror ta kalli fuskarta ta tabbatar babu alamun kuka, duk da idanunta sun ɗan kumbura. Ta gyara ɗaurin kanta sannan ta nufi ƙofa ta fita.
Turus ta yi tana kallonsa, zaune yake kan sofa idanunsa zube akan tv, daga bayansa zaka gane babban mutum ne mai ƙiba, da sauri ta ƙarasa gabansa, ta zauna kusa da shi ta ɗora kanta a gefen kafaɗarsa. Ɗago kansa ya yi ya kalleta yana murmushi, Kyakkyawan bafulatani ne mai matuƙar kama da ita, ya shafa kanta cike da nutsuwa ya ce “Khadijatou” madadin ta amsa masa kawai sai ta fashe da kuka tana sake rikeshi, Ya girgiza kansa fuskarsa a sake ya ce”rigimar na mene ne kuma?” kasa magana ta yi sai shessheƙar kuka take, Amma dake zaune kujerar dake facing tasu ta dinga kallonta sai kuma ta taɓe baki. Ganin bai ce komai ba ya sanya ta kalleta a ɗan tsawace ta ce”Idan baki da abin faɗa tashi ki bar nan!” Ƙin juyowa ta yi amma tafara rage kukan nata, Alhaji Ahmad ya yi murmushi ya ce”ki yi shiru ki faɗa min me aka yi miki?” Sauke ajiyar zuciya ta dinga yi kafin ta ɗago daga jikinsa tana kallonsa ta ce”Abba kawai nayi missing ɗinka ne fa” girgiza kansa ya yi dan daman ya san kwanan zancen, ya ce”to ba gashi kin dawo ba Nana? Uhm, yanzu kukan na mene ne?” Tura baki ta yi ta ce”Abba shikenan yanzu na bar Aun? Duk friends ɗina mun rabu” Abba ya ce”Ai daman haka yake Nana, komai akai kira zai zo ya shige” ta gyaɗa kanta ta ce”Eh haka Mommy ta ce mana, ta ce daman haka rayuwa take” Abba ya jinjina kansa ba tare da ya sake cewa komai ba. Shiru parlon ya ɗauka kafin ta sake gyara zama ta ce”Abba ina alƙawarina?” Tashi ya yi yana gyara zaman hular kansa ya ce”baki manta ba kenan?”
“I’ll not”
Ta faɗa tana washe baki.
Hannunsa ya miƙo mata ta ɗora nata a kai ta miƙe tsaye, waje suka nufa Amma ta bisu da kallo kafin ta ce”a haka zata fita?” Sake kallonta ya yi sai kuma ya ce”and what’s wrong with her dress?” Amma ta girgiza kanta ba tare da ta sake cewa komai ba, ya juya suka fice daga parlon.
Tafiya suka dinga yi suna hira kamar abokai, yana ɗaya daga abin da ya sanya take son dawowa gida saboda Abbanta. Yanda suke hira dashi koda Amma bata yi, dan ita Amma tana da ɗan zafi wani lokacin, saɓanin Abba da kome take so shi yake yi. Ganin sun nufi gidan kawu ya sanya ta ce”Abba wajen Uncle zamu je?” Eh ya ce mata yana gyara zaman glasses ɗinsa.
****
Bakinsu ɗauke da sallama suka shiga, Ummi dake zaune kan kujera ta tashi tana murmushi ta ce”wa’alaikummusalam, Sannu da zuwa Alhaji” Abba ya jinjina kansa ya ce”Yawwa sannu Maryam, Yaya yana ciki ne?” Ummi ta ce”Eh yana nan, bismillah” Abba ya saki hannun Nana sannan ya nufi hanyar apartment ɗin Alhaji Kabir ɗin. Ummi ta kalli Nana ganin yanda ta tsaya ta ce”Mai sunan Hajiya Babba zo ki zauna mana” To kawai ta ce sannan ta nemi gefen kujera ta zauna, Ummi ta ce”Nayi tunanin ai ba zaki shigo ba, kin dawo babu ko ziyara” ɗan murmushi ta yi ta ce”to ai daman jira nake Abba ya dawo sai na biyoshi” Ummi ta harareta ta ce”da yake bakisan hanyar nan ɗin ba ko” tuntsirewa ta yi dan dariya ganin irin kallon da Ummin ke mata kafin ta ce”Ai Amma ce ta hanani fitowa, cewa ta yi na zauna na huta” ta taɓe baki ta ce”ita Rabi’an?” Ta gyaɗa mata kai, Sallamar da aka yi ya sanya ta ɗaga idanunta ta kalleshi.
Ya ƙaraso parlon ya zauna akan kujera ya ɗan yi baya yana jingina da kujerar ya ce”subhanallah!” Ummi ta kalleshi ta ce”har ka dawo?” Ya gyaɗa mata kai ba tare da ya yi magana ba. Ummi ta mayar da idanunta kan Nana wadda ta haɗe rai kamar ba ita ba, ta ce”zo muje kitchen na baki abu ki kai wa su Papa” kamar jira take ta miƙe tsaye tana cewa”to Ummi” daga haka ta nufi kitchen ɗin ba tare da ta yarda ta kalli inda Sultan yake ba. Sai da yaga duk sun shige kitchen sannan ya ɗago kansa ya kalli hanyar, ya miƙe ya nufi upstairs da sauri. Drinks ta zuba mata akan wani ɗan madaidaicin tray ta miƙa mata tana cewa”kai sai ki dawo ki kai musu abinci” to kawai Nana ta ce ta karɓa sannan ta fita daga kitchen ɗin. Da idanu tabi inda ya zauna da kallo ganin bayanan ya sanya ta taɓe baki, tana gama hawa saman ta kalli hanyar ɗakinsa sai kuma ta shige da sauri.
Zaune ta samesu suna tattaunawa, Ta ajiye tray ɗin a ƙasa sannan ta durƙusa cike da ladabi ta ce”Papa ina yini?” Alhaji Kabeer dake zaune kusada Abba ya yi murmushi ya ce”lafiya kalao Nana, an dawo lafiya?”
“Alhamdulillah”
Ta bashi amsa tana wasa da fingers ɗinta, jinjina kansa ya yi ba tare da ya sake magana ba, ganin haka ya sanya ta tashi ta fice daga ɗakin. Ta dinga kallon ƙofar ɗakin kamar ta shige sai kuma ta ƙarasa, a hankali ta murɗa handle ɗin tana ɗan runtse idonta. Ta ɗan sauke ajiyar zuciya jin ƙofar a buɗe, tura ƙofar ta yi ta shiga, tayi saurin jan numfashi saboda wani irin ƙamshi daya daki hancinta, ga wani irin sanyin ac mai shiga jiki. Ta maida ƙofar ta rufe a hankali a ranta ta ce”ko meyasa yake son sanyi oh!” Ta dinga kallon tsaftace ɗakin wanda yaji luxury furnitures, komai na ɗakin white colour ne, dan ita ce favorite colour nasa, ba zaka taɓa cewa ɗakin namiji bane saboda yanda yake neat dashi, komai a muhallinsa. Ganin baya cikin ɗakin ya sanya ta nufi inda press ɗin kayansa take tana tafiya kamar mara gaskiya, buɗewa ta yi without making any sound, kayan ciki a linke suke kuma a tsaftace, komai an jera shi a inda yake, ta taɓe baki sannan ta fara dube-dube. Above 2mins amma bata samu abin da take nema ba, dan haka kawai ta miƙe ta rufe press ɗin. Drawer dake dressing mirror ta kalla sai kuma ta ƙarasa wajen da sauri ta buɗeta, murmushi ta yi ganin abin da take neman. Ta sanya hannu ta ɗauko empty bottle ɗin ta buɗe, gaba ɗaya ƙamshi ya gauraye ɗakin, ta kai bottle ɗin hancinta ta shanshana sai kuma ta yi murmushi a fili ta ce”A siyan turare kuɗinsa ke ƙarewa” daga haka ta mayar da drawer ta rufe sannan ta janyo babbar kwalbar turaren dake gaban mirror ɗin, buɗewa ta yi ta tsiyaya dayawa a ciki sannan ta mayar ta rufe ta ajiye. Ta ɗauki wanda ta ɗiba ɗin ta rufe shima sannan ta juyo, Tsabar yanda ta tsorata ya sanya ta jefar da kwalbar ta faɗi ƙasa ji ka ke “tass!” Ta tawarwatse a wajen.
Nana ta dinga kallonsa tana haɗiyar miyau dakyar, tsaye yake gabanta daga shi sai ɗan boxer jikinsa sai ɗigar ruwa yake da alama daga wanka ya fito. Ta ƙurawa faffaɗan ƙirjinsa wanda gashi ya rufe shi idanu lokaci ɗaya kuma ta saki ƙara tana rufe fuskarta da hannayenta.
Saurin rufe mata baki ya yi yana mata wani irin kallo, ta dinga zare idanu hawaye na biyo gefen fuskarta, jawota ya yi daga inda take tsayen suka yi very close dashi har suna jin hucin numfashin juna. Ya janye hannunsa daga kan bakinta still looking at her eyes, Sauke numfashi ta dinga yi tana riƙe da ƙirjinta. Cikin kakkausar murya taji ya ce
“Me ki ke yi a ɗakina?”
Yanayin yanda ya yi maganar in a serious tone ya sanya ta yi shiru bakinta na rawa, a tsawace ya ce”I said who brought you here!?”
A mugun rikice ta dinga kallonsa tana girgiza kanta, magana takeson tayi masa amma tsoro ya hanata, ya yi kwafa sannan ya ce”Saboda bakida kunya ko? Haka ki ke shiga ɗakin maza without knocking ko?” Ta sake girgiza kanta. Sake tamke fuska ya yi ya ce”Ba zaki daina gyaɗa min kai kamar kadangaruwa ba” Gyaɗa masa kan ta sake yi ba tare da ta san tayi hakan ba. Wata muguwar tsawa daya daka mata ya sanya ta fadi ƙasa tana fashewa da kuka, ta riƙe ƙafafunsa cikin kuka ta ce”A… Dan…dan Allah Yaya Sultan ka yi haƙuri, daman turare fa zan ɗiba”
Hannu ɗaya ya sanya ya ɗagota yana kallonta ya ce”wa ki ka tambaya da zaki ɗebi turaren?” Ta girgiza kanta sai kuma ta ce”babu kowa” ya ce”oh sata zaki fara kenan?” Muryarta na rawa ta ce”A’a dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba”
Kallonta ya dinga yi ba tare da ya ce komai ba, ta sunkuyar da kanta har sannan tana ɗan shessheƙar kuka. An ɗauki aƙalla mintuna biyar kafin ya janye idanunsa daga kanta, ya bar wajen yana faɗin”bar ɗakin nan” kallonsa ta yi sai kuma ta nufi ƙofa da gudu ya juyo yana kallonta har ta fice, ya girgiza kansa yana wani irin murmushi ya ce”my mumu girl”.
****Kallonta Maimoon ta dinga yi ganin yanda take haki, ta ce”Lafiyarki dai?” Kasa magana Nana ta yi sai hanyar ɗakin Sultan data nuna mata, Maimoon ta tuntsire da dariya sai kuma ta ce”ke mene ne ya kai ki ɗakinsa?” Sai da ta saci kallon Ummi da hankalinta ke kan tv sannan ta kalleta murya can ƙasa ta ce”turare naje ɗauka shine ya kamani” Rufe bakinta ta yi da hannunta ta ce”me ya ce miki?” Nana ta ɗan haɗe rai tana kallon gefe ta ce”tsawa ya yimin har sai da na faɗi ƙasa” Maimoon ta dinga dariya kamar zararriya, ganin haka yasa ta sake haɗe rai ta ce”dan baki ga yanda ya yimin bane da sai kin tausaya min” ta ƙare maganar kamar ta yi kuka.
“Nana ɗauka abincin ki kai musu mana”
Maganar Ummi ta katse su, toh kawai ta ce sannan ta nufi kitchen. Maimoon ta bita da idanu, sai da ta ɗebo warmers ɗin da plates sannan ta kalli Maimoon ta ce”help me mana” daga haka ta miƙa mata plates ɗin, amsa ta yi sannan suka nufi saman a tare, Ummi ta bisu da idanu.
Ko minti biyu basu yi a ɗakin Papa ba suka fito, Maimoon ta tsaya tana kallonta ta ce”wai wane turaren ki ka je ɗiba?” ɗaga kafada ta yi ta ce”ni ina ma na sani, kawai naji yana da ƙamshi, sai na ɗiba”
“To ina yake?”
A sanyaye ta ce”ya fadi ya fashe” taɓe baki Maimoon ta yi ta ce”asara”. Nana ta ce”wai kuma a haka Hameeda take cewa tana sonsa? Wannan ai sai ya kasheta da masifa barin ita da bata iya ramawa ba” harararta Maimoon ta yi ta ce”ki bari aji wannan maganar a bakin ki wallahi babu ruwana yawwa” tura baki ta yi tana yin gaba da ƙarfi ta ce”to aji ɗin mana, sai me?” Daga haka ta sauka daga stairs ɗin, Maimoon ta girgiza kai sannan tabi bayanta.
****
Mama ta dinga kallonta da mamaki kafin ta ce”mene ne haka Hameeda? Meke damunki?” sunkuyar da kanta ta yi a sanyaye ta ce”babu komai Mama” rai ɓace Mama ta ce”ni ki ke cewa babu komai ko? Ni zaki kalla ki cewa babu komai!”
Sallamar da aka yi ya sanya ta yi shiru, ya dinga kallonsu kafin ya ƙarasa gabanta. Ya kalli Hameeda dake zaune kan kujera kanta a ƙasa sai kuma ya kalli Mama dake tsaye ya ce”lafiya dai Mama?”
“Ina fa lafiya Safwan, wai ni Hameeda ke kalla ta cewa lafiyarta kalao bayan tun da rana nagane akwai abin da ke damunta, amma ta faɗa min taƙi”
Safwan ya kalleta a sanyaye ya ce”Hameeda ke dawa?” Tashi tsaye ta yi muryarta na rawa ta ce”babu komai fa Yaya, kawai ina missing Aun ne shiyasa” daga haka tabi ta gefensu ta nufi ɗakinta. Da mamaki duk suka bita da kallo, ya sauke numfashi ya ce”Allah ya kyauta” Amin kawai Mama ta ce, ya miƙa mata ledojin hannunsa ya ce”Abbansu Hamid ya ce na kawo miki” okay kawai ta ce sannan ya juya ya fita. Koda ta shiga ɗaki kwanciya ta yi ta ci gaba da rera kukanta kamar wadda aka yiwa albishir da mutuwa, ita kanta bata san dalilin kukan nata ba, a haka har bacci ɓarawo ya saceta.
2weeks later.
7:30 na safe
Amma ta turo ƙofar ɗakin ta shigo hannunta riƙe da mug, kwance ta sami Nana kamar yanda ta barta. Ta ƙarasa ta ajiye mug ɗin akan drawer sannan ta hau gadon, yaye duvet ɗin data lulluɓa ta yi, idanunta a rufe yake sai rawar sanyi take ga kuma gumi daya cika fuskarta. Amma ta riƙe hannunta ta ce”tashi ki ɗan sha tea ɗin kafin Abbanki ya fito ya kai ki asibiti” dakyar Amma ta taimaka mata ta tashi zaune ta jingina da jikin gadon tana hawaye, sauka tayi ta ɗauko mug ɗin ta dawo ta miƙa mata. Hannunta na rawa ta karɓa ta kai baki, ko kwata bata sha ba ta miƙawa Amma tana girgiza kai.
“Kin shanye zai taimaka miki”
Muryarta na fita da kyar ta ce”Amma ba zan iya ba” daga haka ta sake komawa ta kwanta ta ci gaba da birgima akan gadon. Kallonta kawai Amma ta dinga yi cike da tausayawa dan tasan azabar irin wannan ciwon, ta tashi ta fice daga ɗakin da sauri. Tana ƙoƙarin shiga ɗakin ya fito, sanye yake da wata shadda sky blue, daka gansa kasan kuɗi ya zauna.
“Daman kiran ka zan yi”
Amma ta yi maganar da damuwa a fuskarta. Abba ya ce”ya jikin nata?” Girgiza kanta ta yi ta ce”da sauƙi za’a ce, kaje ka kaita asibitin dan Allah” okay kawai ya ce sannan ya nufi ɗakin nata da kansa. A durƙushe ya sameta ya ƙarasa ya tsaya yana kallonta ya ce”Daughterna” ɗago kanta ta yi ta kalleshi kawai sai ta fashe da kuka, da kansa ya kamo hannunta ya sakko da ita, ya taɓa jikinta. Zafi sosai yaji ya janye hannunsa ya jingina da jikinsa yana cewa”Ya jikin naki?” kasa magana ta yi sai kuka da take faman yi, girgiza kansa ya yi daidai lokacin da Amma ta shigo ya kalleta ya ce”ɗauko mata riga” okay kawai ta ce sannan ta ƙarasa press ɗinta. Abaya ta ɗauko da veil ta miƙo masa, da kansa ya sanya mata sannan yaja hannunta suka fita daga cikin ɗakin.
Suna fitowa daga gidan motarsa na yin parking a compound ɗin, Abba ya dinga kallon motar har ya fito daga ciki, sanye yake da ƙananun kaya daga ganinsa kasan shirin fita ya yi. Ya dinga kallonsu har ya ƙaraso wajen ya ɗan risina ya ce”Good morning Abba” fuska a sake Abba ya ce”Morning Sultan, ka tashi lpy?”
“Alhamdulillah”
Ganin irin yanda take kwance a jikinsa ya sanya ya ce”Abba lafiya dai?” Girgiza kai Abba ya yi ya ce”wallahi Sultan wai bata da lafiya, cramps ke damunta tun cikin dare, kuma kasan yanda take yi, so shine zan kai ta asibiti” Sultan ya ɗan girgiza kansa ya ce”Ayyah subhanallahi, to ko zan tafi da ita asibitin ne Abba? Kai sai ka huta kaga” Abba ya yi murmushi sannan ya ce”Da naji daɗi wallahi dan daman ina da appointment da Ig kawai dai zan kai ta ne” Sultan ya ce”kawai ka je Abba, bari mu tafi tare” okay ya ce sannan ya ɗagota daga jikinsa. Kuka ta saka muryarta bata fita ta ce”a’a Abba ni ba zan bi Yaya ba” cikin rarrashi ya ce”sorry daughter ki bishi kin ji, idan nagama da wuri zan zo” kuka ta dinga yi ba tare da ta yi magana ba. Shi dai Sultan ya tsaya yana kallonta.



