⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 21: Chapter 21

“Idan kuma shi ya sauya lamba ya kira ki fa?”

Ta sauke numfashi sai kuma ta ɗaga kiran bakinta na rawa ta ce

“Salamu alaikum”

Daga ɗaya ɓangaren aka ce

“Ina magana da Nana ne?”

Nana ta yi shiru tana tunanin inda ta san muryar, ganin ta kasa tunawa yasa ta ce

“Eh ni ce.”

Siyama ta gyara zamanta kan sofa sannan ta ce

“kece wadda ki ke shirin auren Safwan ko? To ki sani tun wuri gara ki rabu dashi. Domin Safwan ba mijinki bane, ni zai aura. Ki fita a sabgarsa tun kafin ran ki ya ɓaci wallahi, dan zan iya komai akan sa, ke zan iya kasheki akansa”

Nana ta yi shiru sai kuma ta ce

“tam na gode.”

Daga haka ta kashe wayarta ta yi jifa da ita, sai kawai ta sake fashewa da wani irin kuka. Nan da nan tari ya fara turnuƙeta, sai kuma ta fara aman jini har da guda-guda dai dai nan Amma ta buɗe ɗakin ta shigo hannunta riƙe da mug. Sai dai halin da taga Nana ya sanya ta saki mug ɗin a ƙasa ta ƙarasa gabanta cikin tashin hankali ta ɗagota tana faɗin

“Nana! Nana! Ke Nana”

Ko kaɗan Nana bata jin abin da take faɗa, dan babu alamar tana tare da ita. Dan haka ta tashi da gudu ta fice daga ɗakin, Abba na tsaye a balcony shi da Sultan ta ƙarasa cikin tashin hankali take faɗin

“Yallabai Nana! Nana”

Abba ya kalleta ganin yanda take kuka yasa ya ce“lafiya me ya samu Nanan?”

Bata iya bashi amsa ba sai girgiza kanta kawai take, Sultan kuwa bai jira sun gama maganar ba ya nufi cikin gidan da sauri. Ganin haka yasa Amma da Abban suka bi bayansa.

Sultan ya dinga kallonta ganin halin da take ciki yasa ya sunkuya ya ɗauketa kamar ƙaramar yarinyar suka fito daga ɗakin, Abba ya biyo bayansa. Aunty Ramlah kuma ta rike Amma ganin babu ko mayafi a jikinta, cikin kuka take ƙoƙarin janye hannunta tana faɗin

“Ramlah ki cikani dan Allah, ki bar ni na bisu”

“To Yaya amma ki fara saka mayafi”

Aunty Ramlah ta ƙare maganar cike da damuwa.

****
Around 3pm Sultan ya fito daga ward ɗin hannunsa riƙe da wata takarda, Abba da Amma da ke zaune suka mike a tare suna kallonsa. Ganin bai ce komai ba yasa Abba ya ce

“Ya jikin nata?”

Miƙewa Abba takardar hannunsa ya yi cike da damuwa ya ce

“Ban san mene ya dameta haka ba da har ya haifar mata da wannan ciwon, but koma mene ne ya kamata a ɗau mataki akansa”

Abba ya warware takardar ya shiga karantawa. Bayan ya gama ya ɗago kansa yana kallon Sultan cike da mamaki da kuma tashin hankali ya ce

“Nana ce ke fama da ciwon zuciya?”

Sultan ya gyaɗa masa kai jiki a sanyaye. Amma ta riƙe Abba cikin tashin hankali ta ce“ciwon zuciya kuma? Nanan tawa?” Abba ya riƙe hannunta ba tare da ya ce komai ba. Fashewa ta yi da kuka tana kallon Sultan ta ce“ina take? Ina son na ganta” da hannu ya nuna mata ɗakin da aka kwantar da Nanan. Ta yi gaba da sauri ba tare da ta sake cewa komai ba, Abba ya numfasa sai kuma ya naɗe takardar yana kallon Sultan ya ce“ya jikin nata?”

“Da sauƙi sosai ta farfaɗo ma. Muje ka ganta”

Okay kawai Abba ya ce sannan yabi bayan Sultan jiki a sanyaye.

Zaune suka tarar da Amma gefen gadon ta riƙe hannun Nana sai kuka take, Abba ya tsaya jikin ƙarfen gadon yana kallon Nana wadda idanunta ke rufe tana sauke numfashi a hankali. Sultan ne ya yi ƙarfin halin cewa

“Dan Allah Amma ki yi haƙuri”

Tashi ta yi daga wajen ta juyo tana kallon Abba ta ce“Idan har kana son Nana. Idan har baka shirya rasata ba dan Allah dan Annabi ka bar maganar auren nan. Wallahi shi ne abin da ya haifar mata da wannan mugun ciwon, ka taimaka ka bar maganar auren nan. Kada ka yi abin da zamu rasa yar mu da kanmu”

Abba bai ce komai ba, sai numfasawa da ya yi. Sultan ya kalli Amma da mamaki ya ce”Nana bata son auren nan?”

Cikin kuka Amma ta ce“Bata so Sultan, tun ranar da aka fara maganar ta ce bata so. Amma na hanata faɗa, na gargaɗeta akan ta yi shiru. Ban yi tunanin abun zai kai haka ba, ban yi tunanin Nana zata damu kanta irin haka ba, tun daga sanda aka fara maganar auren nan ban sake ganin walwalarta ba. Yarinya ce ƙarama, aure ba dole bane akanta, dan Allah ka fahimtar dashi”

Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka.

Shiru Sultan ya yi, lokaci ɗaya ya ji jikinsa ya yi wani irin sanyi. Ya kalli Amma wadda ke faman kuka sai kuma ya mai da idanunsa kan Abba wanda tun ɗazu bai ce komai ba, Ya taka har gabansa cikin sanyin murya ya ce

“Abba dan Allah…”

Ɗaga masa hannu Abba ya yi, Sultan ya yi shiru yana kallonsa. Amma ta juyo tana kallon Abba da mamaki jin bai ce komai ba. Ya numfasa sannan ya taka har gaban gadon ya dafa goshin Nana jin babu zafi yasa ya sauke numfashi. Amma ta dawo gurin tana kallonsa ba tare da ta ce komai ba.

Abba ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonsu duka ya ce“Babu yanda za’a yi na janye maganar auren nan, dole sai Nana ta auri Safwan. Wannan shi ne matsayata!”

Kallonsa suka dinga yi da mamaki, Sultan ya yi shiru ba tare da ya ce komai ba, amma gaba ɗaya ransa babu daɗi, bai so a ce haka Abba ya ce ba. Amma dake tsaye gefen Nana ta ƙaraso gabansa dan sam ta kasa jurewa cikin tsananin ɓacin rai ta ce

“Me ka ce Yallaɓai? Ba za’a fasa auren nan ba? Kenan ka shirya ta mutu ta bar duniya?”

Abba ya ɗan kalleta sai kuma ya mayar da idanunsa kan Nana da ke sauke numfashi ɗaya bayan ɗaya ya ce“Eh. Ba za’a fasa auren nan ba, sai Nana ta auri Safwan, idan ki ka ga an fasa auren nan sai dai idan Safwan ne da kansa ya zo ya ce min baya son Nana, ke to ko haka ne bai isa ba, dole sai ya aureta. Babu yanda za’a yi yara su zo daga baya sannan su nemi ruguza mana dangi, ba zai taɓa yiwuwa ba”

“Kenan gara ka aurar da ita ta mutu ko? Haba dan Allah Nana ce fa, ur one and only daughter, bayan ita fa baka da wata. Ita kaɗai ce amma har ka yi tunanin gara ta mutu akan ƙima?”

Amma ta ƙare maganar a mugun fusace. Abba ya gyaɗa kansa jin tana neman ɓata masa rai ya ce“haka na faɗa Rabi’ah, kuma babu wanda ya isa ya sauya wannan hukuncin dana yanke! Idan har ni Ahmad ni ne na yi cikin Nana kuma ki ke haifeta to wallahi ba zan janye maganar auren nan ba, idan ta so ta mutu.”

Abba ya juya ya fice daga ɗakin rai ɓace. Amma ta bishi da kallo sai kuma ta mai da Idanunta kan tilon ƴar tata da ke kwance tana bacci, ta durƙushe a wajen tana fashewa da kuka. Sultan ya dinga kallonta cike da tausayinta, lokaci ɗaya kuma ya juya ya fice daga ɗakin.

Tsaye ya samu Abba a kofar dakin ya harɗe hannayensa a ƙirji, gumi sai tsatsafo masa yake, ko ba’a faɗa ba kasan ransa a ɓace yake, haka kuma hankalinsa a tashe yake. Sultan yaja ya tsaya yana kallonsa cike da damuwa. Above 5mins kafin ya sauke numfashi ya gyara tsaiwarsa cikin tattausan harshe ya ce

“Abba dan Allah ka yi haƙuri”

Ɗan murmushin yaƙe Abba ya yi yana girgiza kansa ya ce“Babu komai Sultan. Zuwa yaushe za’a iya discharging nata?” Sultan ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce“ai jikin nata da sauki ma, ko zuwa magrib za’a iya sallamarta. Kawai dai abin dubawar shi ne halin da take ciki”

Toh kawai Abba ya ce sai kuma ya juya ya koma ɗakin ba tare da ya sake cewa komai ba, Sultan ya sauke numfashi yana cin ransa babu daɗi. Dan ya san halin Abba, muddin ya kafe akan magana to babu wanda yake sauya shi.

Ko da ya koma zaune ya samu Amma gefen gadon sai kuka take a hankali. Hannunta ɗaya akan goshin Nana tana shafawa, ɗayan kuma riƙe da nata hannun. Kallonsu kawai ya dinga yi ba tare da ya ce komai ba. Shi kansa baya jin daɗin halin da Nanar ke ciki, amma hakan ba zai taɓa sakawa ya bari a zubar da mutuncin gidansu ba, dama ace wata ce ba ƴarsa ba, da zai iya yin shiru idan har iyayenta sun aminta. amma hakan ba zai taɓa faruwa da yar sa ba

“Never!”

Maganar ta suɓuce masa ba tare da ya yi aune ba. Amma ta juyo tana kallonsa sai kuma ta ɗauke kanta ba tare da ta ce masa komai ba, shima bai damu da shirun nata ba dan daman bai saka ran zata masa magana ba.

****
Siyama ta dinga kallon Aunty Khadijah sai kuma ta kalli Kaddu, lokaci ɗaya ta zumɓura baki tana hararar malamin ta ce

“wallahi ba zai yiwu ba, tabɗijan, ni ba zan iya ba!”

Ta ƙare maganar tana mai da kanta ga kallon waje. Aunty Khadijah ce ta matse hannunta murya can ƙasa ta ce“ke wace irin shashasha ce?”

Juyowa ta yi tana kallonta kamar zata yi kuka ta ce“Mom kin ji fa abin da ya ce, ya ma za’a yi na yarda da wannan mutumin ya wani taɓani. Ni gaskiya a’a!”

Ta sake ɗauke kanta. Shiru Aunty Khadijah ta yi sai kuma ta mai da Idanunta kan malamin wanda yake kallonsu tun ɗazu ba tare da ya ce komai ba, ta ɗan kirkiri murmushi kana ta ce“Malam babu wata hanyar ne? Ko ni na fansheta, ka ga budurwa ce wallahi bata taɓa sanin namiji ba”

Haɗe rai ya yi muryarsa babu wasa ya ce“to idan kin fansheta kece zaki aureshi? Kada ku manta gobe ne ɗaurin aure nan, dan haka ni babu ruwana zaɓi ya rage naku”

Aunty Khadijah ta yi shiru dan jikinta ya yi sanyi, ta kalli Kaddu wadda ita ma su ɗin take kallo sai kuma ta mayar da idanunta kan Siyama ganin yanda ta juyar da kai yasa ta ce“zo ki ji” daga haka ta miƙe tana riƙe hannunta. Soro na biyu ta jata tana mata wani irin kallo ta ce“kina son ki lalata mana aiki ne? Kin san wahalar da muka sha har muka kawo i yanzu?”

Siyama ta tura baki tana leƙan ciki ta ce“to wai Mom baki ji me ya ce ba, wai na bashi jikina zai min wani aiki. Ni wallahi ba zan iya ba”

Tsaki Aunty Khadijah ta yi ta ce“to mene ne a ciki? Duk ba ke ake nemawa farin ciki ba? Shi ne zaki watsa mana ƙasa a ido”

Siyama ta yi rau-rau da idanu ta ce“kenan na yarda na bashi kaina? To shi kuma Safwan ɗin fa? Idan aka yi auren ya gane ni ba budurwa ba ce”

Tsaki Aunty Khadijah ta yi ta ce“to taya za’a bar shi ya gane? Ko ma ya gane me zai iya bayan kin riga da kin mallakeshi. Ai babu yanda zai yi da ke, kuma wannan aikin da za’a yi shi ne zai saka ya bijirewa gidan ya ce shi ke yake son aura ba wacce yarinyar ba. Kin ga idan har baki yarda ba shikenan mun ɓata lokacinmu a banza, kuma burinmu ba zai taɓa cika ba”

Siyama ta yi shiru tana kallonta ba tare da ta ce komai ba, tunaninta ya kasu gida biyu, ta yarda da abin da ake faɗa mata ko kuma ta ƙi yarda. Jin bata ce komai ba yasa Aunty Khadijah faɗin

“Mu je ko”

Kasa yi mata musu ta yi, ta samu kanta da bin bayan mahaifiyar tata wanda ke nuni da cewa ta amince da duk abin da ta ce.

****
Around 6:00 na yamma motarsu ta yi parking a compound ɗin gidan, kasancewar ranar ake yinin yan mata yasa ko ina yake a cike. Jama’a an taru sai shige da fice ake. Amma ce ta fara fitowa daga motar sannan Nana ta fito, Amma ta riƙeta tana sake mata sannu, Abba ya kalli Sultan wanda ke tsaye ya ce

“Kaje ka huta Sultan ka sha wahala”

Girgiza kai ya yi ya ce“ba komai Abba. Bari naje na faɗawa Hajiya Babba”

Abba ya ce“a’a kada ka sanar da ita yanzu, a bari ko zuwa gobe idan Allah ya kaimu. Ka ga yanzu jama’a sun taru” Sultan ya jinjina kansa kafin ya ce“,haka ne kuma, to bari naje ciki” okay kawai Abba ya ce sannan ya amshi ledojin drugs ɗin da ke hannunsa. Yabi bayan su Amma dan tun fitowarsu ta shige ciki ita da Nana. Ta ƙofar baya ta shiga gudun kada mutane su damesu, ta kai Nana bedroom ɗinta ta zauna sannan ta ce

“Sannu bari na kawo miki abinci”

Riƙe hannun Amma ta yi tana girgiza kanta ta ce“na ƙoshi Amma” Amma ta zauna gefenta ta jawota jikinta ta rungumeta muryarta na rawa ta ce

“Nana dan Allah ki kwantar da hankalinki, kada ki yi abin da zai sa mu rasaki. Ba zamu jure ba, dan Allah dan Annabi ki yi hakuri ki bar maganar nan kin ji” Amma ta ƙare maganar tana ɗago kanta. Murmushi mai haɗe da hawaye Nana ta yi kafin ta ce“na bari Amma, wallahi na bari. Ba zan sake maganar ba, koda auren Yaya Safwan na nufin rasa rayuwata zan aureshi, ba zan bari Abba ya yi baƙin ciki dani ba”

Amma ta sauke ajiyar zuciya tana jin shessheƙar kukanta. A hankali ta dinga shafa bayanta tana sake bata haƙuri. Ana haka Aunty Ramlah ta buɗe ɗakin ta shigo tana kallonsu ta ce“Yaya ya jikin Nanar?”

Ganin yanda duk suke kuka ya sanya jikinta ya yi sanyi fiye da misali, ta zaune gefen gadon murya a sanyaye ta ce

“Lafiya dai Yaya?”

Amma ta ɗago kanta tana janye Nana daga jikinta ta ce“da sauƙi Alhamdulillah” daga haka ta tashi ta fice daga ɗakin. Da idanu Aunty Ramlah ta bita sai kuma ta kalli Nana wadda ta kwanta kamar gawa ta ce

“Nana ya jikin?”

“Da sauƙi”

Ta ce a sanyaye tana rufe idanunta. Aunty Ramlah ta ɗan yi jim sai kuma ta tashi ta fice daga ɗakin.

Bayan sallar magriba Zahra ta shigo parlon Amma tana neman Nana, Amma ta sanar da ita tana cikin daƙinta dan haka ta nufi ɗakin kai tsaye. Bata samu kowa a ciki ba sai Nanar dake kwance tsakiyar gado idanunta a lumshe sai dai ba bacci take ba, ta tsaya a gefen gadon tana ƙare mata kallo sai kuma ta ce

“Nana”

Kamar a mafarki haka Nana taji saukar maganarta, dan haka ta buɗe idanunta a hankali tana kallonta. Lokaci ɗaya kuma ta tashi zaune tana girgiza kanta cikin kuka ta ce

“Dan Allah dan Annabi Aunty Zahra ki barni haka, ki rabu da rayuwata haka. Na fadawa Abba bana son auren amma yaƙi saurarata, dan Allah dan Annabi ki bar ni haka, ki rufa min asiri”

Zahra ta yi wani irin kyakkyawan murmushi sai kuma ta kai hannunta ta dafata. Nana ta dinga kallonta ganin bata ce komai ba, after 2mins ta sauke numfashi ta ce“Nana ni ba wai ina son cutar da ke bane, Ni bana nufinki da sharri. Yanzu ma naji an ce baki da lafiya ne nace bari na zo na duba ki, dan haka ki kwantar da hankalinki”

Nana ta yi shiru tana kallon Zahra da mamaki, Zahra ta sanya hannunta ɗayan ta goge mata hawaye da ke zubowa kan fuskarta ta ce“let bygone be bygone, ki bar damun kanki kada wani ciwon ya sameki” ban da gyaɗa kai babu abin da Nana ke yi dan duk zatonta Zahra ta zubar da makaman yaƙinta ne. Dan haka taji damuwarta ta ɗan ragu da kashi 40, suna nan zaune kowa ya yi shiru aka buɗe ƙofar ɗakin, Maimoon ce ta shigo tana sanye da doguwar rigar lace ɗin da aka musu, fuskarta ta sha makeup wadda ta ƙara mata kyau. Ta dinga kallon Zahra fuska a haɗe sai kuma ta ƙaraso wajen ta zauna gefen Nana na dama ta riƙe hannunta ta ce

“Nana ya jikin naki?”

A sanyaye ta ce“Da sauƙi”

“ɗazu make up artist ta zo za’a mana make up aka zo kiranki aka ce wai kuna asibiti, Nana ki daina damun kan ki kinji”

Gyaɗa mata kai kawai Nana ta yi, dan da gaske magana wahala take mata. Zahra ta dinga kallon Maimoon ganin bata kulata ba, Maimoon kuwa ɗauke kanta ta yi dan ba zaka taɓa cewa taga Zahra a wajen ba, cikin son cusa mata takaici ta ce

“Yanzu uncle zasu shigo ma, dashi da Haule amaryarsa. Nana kin ganta kuwa? Kyakkyawa da ita”

Nana ta ɗan kalleta sai kuma ta ce“ni na warke fa”

Maimoon ta harareta tana sake riƙe hannunta ta ce“to dan kin warke ba za’a zo a dubaki ba? Harda angonki ma Yaya Safwan zasu zo”

Nana ta yi shiru tana jin ƙirjinta na tsananta bugu, haka kawai idan taji an yi maganar Safwan sai taji ƙirjinta na bugu da sauri. Ta lumshe idanunta wanda ya bawa hawayen dake cikin kurmin damar gangarowa kan fuskarta. Zahra na ƙoƙarin tashi aka sake buɗe kofar ɗakin, dan haka ta tsaya tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya har suka gama shigowa. Sultan ne sai Safwan, Aliyu, Hamid, Abdusammad, Hamida, Amrah, da kuma Haule.

Zahra ta koma ta zauna ba tare da ta ce komai ba, sannu suka dinga yiwa Nana kowa na jinjina al’amarin barin ganin yanda ta rame ta ƙarmashe kamar ka hureta ta faɗi. Maimoon da ke son baƙanta ran Zahra ta kalli Safwan ta ce

“Yaya baka ga matarka ba? Abar tausayi”

Murmushi kawai ya yi idanunsa zube kan Nana wadda yake ganin ta ƙara wani irin kyau duk da ramar da ta yi, Ganin haka yasa Maimoon ta ce“gobe i yanzu dai ai tana gidanka sai dai idan ɗan baƙin ciki ya mutu!” ta ƙare maganar tana hararar iska. Babu wanda ya fahimci abin da take nufi a wajen sai Abdusammad duk da shima bai gane da wata take ba.

Hamida ta girgiza kanta tana sake kallon Nana ta ce“Allah sarki Nana kamar ba ke ba duk kin rame, ki daina saka komai a ranki kin ji”

“To me zata saka a ranta daman? Bayan tana cikin rufin asirin dangi da yan uwa, ji fa kowa anan nata ne. Duk nan danginta ne, ai yan uwa sun fi komai daɗi”

Maimoon ta sake maganar tana satar kallon Zahra, kamar yadda ta yi tunani haka ce ta faru kuwa dan iya ɓaci ran Zahra ya ɓaci amma gudun kada a gane ya sanya ta danne bata ce komai ba. Haka suka dinga hira ana zolayar juna wanda ya sanya Nana ta saki jikinta har da dariya wadda rabonta da dariya har ta manta. Aliyu ya dinga kwasar Abdusammad da maganar Haule wadda ta yi shiru ta sunkuyar da kai saboda kunya irinta Fulani, hakan kuma ya sake tunzura Zahra ba kaɗan ba. Daga ƙarshe ta tashi tana kallon Nana ta ce

“Nana Allah ya ƙara sauƙi bari naje” toh kawai Nana ta ce ta juya ta fice daga ɗakin ba tare da ta cewa kowa komai ba, suma hakan bai damesu ba dan ba da ita suke hirar su ba. Suna nan har kusan ƙarfe 10:00 na dare sannan Abdusammad ya ce kowa ya tafi. Nan da nan kuwa kowa ya watse ya yi apartment ɗinsu aka bar wa gobe sauran.

Zahra na zaune gefen gadon bayan sun gama waya da Aunty Khadijah idanunta ya yi luhu-luhu da alama ba ƙaramin kuka ta ci ba, ta dinga jujjuya envelope ɗin hotunan dake gabanta. Ganin lokaci na tafiya ya sanya ta mike ta zura hijabi sannan ta fice daga ɗakin.

Around 11:00 na dare Amma ta buɗe dakin ta shigo, kwance ta samu Nana ta juya baya ta zauna gefen gadon sannan ta taɓa ta a hankali ta ce

“Nana!”

Buɗe idanunta ta yi dan daman ba bacci take ba, ta tashi zaune tana jingina da jikin gadon. Amma ta dinga kallonta sai kuma ta ce“ya jikin naki?”

“Da sauƙi Amma”

Ta ce a sanyaye. Jinjina kai Amma ta yi sai kuma kowa ya yi shiru, can kuma Amma ta ce“ko zaki dada abincin?”

Girgiza kai ta yi kafin ta ce“a’a Amma na ƙoshi ma”

Amma ta jinjina kanta sai kuma ta mike ta ce“to ki kwanta ki yi bacci sai da safe”

To kawai Nana ta ce sannan ta zame jikinta ta kwanta. Amma ta rage mata gudun ac sannan ta kashe hasken ɗakin ta juya ta fita.

Nana na ganin ta fita ta tashi zaune sannan ta jawo wayarta, ta buɗe password ta koma WhatsApp cikin sa’a ta samu Khadijah na online, dan haka ta tura mata message tana tambayar meya hanata zuwa. Khadijah da ba zata iya tsayawa bata amsa ba ta kirata ta WhatsApp bayan ta ɗaga ta ce

“kin san me ya hanani zuwa Nana?”

Shiru Nana ta yi dan ba ƙaramin haushinta taji ba, Khadijah ta yi murmushi dan tasan halinta ta ce

“to Daddy ne bai dawo ba. Kin da daman nace miki sai ya dawo zan zo”

Nan ma Nana ta yi shiru tana kwanciya a kan gadon, Khadijah ta yi tsaki ta ce

“Ina miki magana kina jina banza”

Sai a sannan ta sauke wani wahalallen numfashi cikin sanyin murya ta ce

“Yaushe zaki zo?”

Ta yi maganar a takaice. Khadijah ta taɓe baki ta ce

“wai dan zaki yi aure shi ne ki ka wani fara magana da isa? To gobe”

Nana ta ce“alright zan jira ki. Ki gaida Mami”

“Zata ji, ta ce da bata da patient ai har Yola zata zo”

Ɗan murmushi Nana ta yi dan ta san Mami farin sani ta ce“Allah sarki. Ki ce ina gaisheta”
Okay kawai Khadijah ta ce sannan suka katse wayar. Nana ta ajiye wayar a gefe tana lumshe idanunta, gaba ɗaya ji take kamar ba ita ba. Tunanin abin da zai faru gobe idan har Junaid ya ji an ɗaura aurenta shi ne ya fado mata, dan haka ta gaza samun sukuni balle ta samu nutsuwar bacci.

****
Safwan ya dinga kallon wayarsa kafin ya ƙarasa da mamaki ya ɗauketa yana tsane ruwan kansa dan fitowarsa kenan daga wanka, ya ɗaga wayar ya kai kunne kafin ta yi magana ya ce

“Aunty Zahra lafiya?”

Murya can ƙasa Zahra ta ce“lafiya kalau Safwan kana gida ne?” gyaɗa mata kai ya yi kamar yana gabanta sai kuma ya ce“Eh ina ciki”

“To ko zaka ɗan fito dan Allah ina compound ɗin” toh kawai ya ce sannan ya kashe wayar har sannan bai daina mamaki ba. Ya ɗauko jallabiya a press ɗinsa ya zura sannan ya saka slippers ya fito daga ɗakin. Babu kowa a parlon dan har an kashe haske, ya buɗe ƙofar ya fito. Tsaye ya hangeta ita ɗaya ya ƙarasa a sanyaye yana kallonta ya ce

“Aunty Zahra lafiya dai?”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *