Chapter 22: Chapter 22
Zahra ta juyo tana kallonsa sai kuma ta yi murmushi ta ce“lafiya kalau Safwan kawai ina son magana da kai ne”
Safwan ya ɗan yi jim sai kuma ya ce“to ina ji”
Zahra ta ɗan kalli both hand side ɗinta sannan ta sauke numfashi ta zaro envelope ɗin daga cikin hijabi ta miƙa masa. Safwan ya dinga kallon envelope ɗin ba tare da ya karɓa ba, ganin irin kallon da yake mata na neman karin bayani yasa ta sauke hannunta sannan ta ce
“na san kasan Siyama yar Yayata ce ko? Kuma ka san nasan kana sonta, kana da burin aurenta sai dai ka rasa ta inda zaka ce baka son Nana. Ko kuma ka ce ka fasa aurenta”
Safwan ya yi shiru yana kallonta, ta ɗan murmusa sannan ta ci gaba da faɗin
“zan so ace ka auri Siyama ko dan na samu yar uwa a gidan nan. Haka kuma zan so ace ka aureta kodan farin cikinka saboda haka na zo maka da abin da zai iya sakawa a fasa aurenka da Nana koda a filin ɗaurin auren ne!”
Da wani irin mamaki Safwan ke kallonta, Zahra ta sake mika masa envelope ɗin, wannan karan samun kansa ya yi da amsar envelope ɗin, ya dinga kallonta ba tare da ya yi yunkurin buɗewa ba. Ta numfasa sannan ta ci gaba da fad’in
“Idan har ka yi amfani da abin da ke cikin envelope ɗin nan to zaka samu Siyama cikin sauƙi, koda a gobe ka ke so za’a ɗaura maka aure da ita”
Safwan ya girgiza kansa cikin rashin fahimta ya ce
“Nifa ban gane abin da ki ke faɗa ba Zahra, ban fuskanci in da ki ka dosa ba”
“Ba dai kana son Siyama ba? Kuma ita ka ke son aura ba Nana ba?”
Safwan ya jinjina kansa ya ce“Haka ne. Ina son Siyama, so irin wanda ban taba yiwa wata ƴa mace shi ba. Ina jin idan ban sameta ba kamar ba zan iya ci gaba da rayuwa ba”
Zahra ta yi murmushi dan ta tabbata ta samu abin da take so ta ce
“To idan har kana son Siyama ka yi amfani da abin da na baka, ka ce ka fasa auren Nana. Kana iya kafa hujja dashi”
“Hujja!?”
Safwan ya ce da matuƙar mamaki, gaba ɗaya kansa ya ɗaure. Zahra ta gyada kanta ta ce“Eh hujja, gobe ka gabatar dashi a gaban kowa sannan ka ce ka fasa aurenta saboda abin da kagani. Daga nan ka ce Siyama zaka aura a maimakonta”
Ji ya yi kawai ya gyaɗa mata kai ba tare da ya san ya yi hakan ba. Ta sake murmushi ta ce“ka koma sai da safe”
Daga haka ta juya ta bar wajen, Yafi mintina goma tsaye a wajen baki a sake, kafin yaja jikinsa ya koma ciki dakyar. A kan gado ya ajiye envelope ɗin sannan ya zare rigar jikinsa ya shafa mai ya dauko pyjames ɗinsa ya saka, gaba ɗaya tunani ya hana shi sakat, maganganun Zahra sai kai komo suke masa cikin ransa, yana gamawa ya koma ya zauna yana ƙarewa envelope ɗin kallo.
“Hujja?”
Ya sake furtawa da mamaki, sai kuma ya ɗauki envelope ɗin ya ɓare dan ganin abin da ke ciki, a hankali ya zaro hotunan da suke ciki, lokaci ɗaya ya mike tsaye zumbur yana ƙare musu kallo, so yake ya ƙaryata abin da yake gani amma sam ya kasa, ya sake ƙara light ɗin ɗakin ko idanunsa ke masa gizo, amma ga mamakinsa sai ya ci gaba da ganin abin da ya gani ɗazun. Cikin wani irin tashin hankali da faduwar gaba ya dinga kallon hotunan ɗaya bayan ɗaya, hannunsa sai rawa yake yana girgiza kansa da sauri, gaba ɗaya kusan rasa nutsuwarsa ya yi. Ya yi zaman yan bori a ƙasa kawai sai yaji wasu zafafan hawaye na zubowa daga cikin Idanunsa, bakinsa na rawa ya shiga furta
“Innalil lahi wa ina ilayhi raji’un!”
Ya dinga maimaitawa ko zai samu sauƙin abin da yake ji cikin ransa. Yana nan zaune har bayan mintuna talatin sannan ya miƙe jiki a sanyaye ya kwashe hotunan ya haɗe su waje ɗaya ya mayar inda suke sannan ya zura cikin drawer. Dakyar ya ja jikinsa ya koma gefen gado ya zauna ƙwaƙwalwarsa cike da tunani kala-kala. A ina aka sami wannan hotunan? Da gaske kuma Nanar daya sani ce? How? Su ne tambayoyin da suka fi tsaya masa arai. Ya ji kamar ya tashi ya koma ya tambayi Zahra sai dai bashi da halin yin hakan, dan lokacin 12 na dare ta kawo kai. Dan haka ya dinga saƙa da warwara shi kaɗai yana tunanin abin da zai wakana gobe.
A ɓangaren Zahra kuwa tana koma gida kitchen ta shige, ta zaro wayarta dake cikin hijabi ta yi dialing numbern Aunty Khadijah. Kasancewar ta san da kiran yasa ringing ɗaya ta ɗauka daga ɗaya ɓangaren Aunty Khadijah ta ce
“Zahra ya dai.”
Sai da ta kalli ƙofar kitchen ɗin dan tabbatar da babu kowa a wajen sannan ƙasa-ƙasa ta ce
“Nagama komai fa, na bashi hotunan”
Aunty Khadijah ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi ta ce“yauwa Zahra aikinki ya yi kyau. Yanzu sauran ya rage namu, daman gobe da wuri zamu zo gidan”
Jinjina kai Zahra ta yi sannan ta kashe wayar, ta jingina da jikin cabinet tana tunanin abin da ta aikata, dai dai tayi? Ko kuma ba dai dai ba. Sanin babu wanda zai faɗa masa gaskiya a sannan ya sanya taja jikinta ta fice daga kitchen ɗin.
Koda ta shiga daƙinta kwanciyarta ta yi dan ko Abdusammad bata nema ba, shima kuma bai nemetan ba saboda ayyuka da suke neman shan kansa.
A ɓangaren Nana kuwa kasa bacci ta yi, haka kawai taji zuciyarta na karyewa, taji kamar wani mummunan abu na shirik faruwa da ita. Dan haka ta tashi ta shige toilet ɗin Amma ta ɗauro alwala sannan ta fito ta sanya hijabi ta fara gabatar da sallolin nafila. Bayan ta idar ta zauna ta dinga addu’o’i kala da kala har kusan 3 na dare. A ɗakin Abba kuwa Amma ce zaune ƙasan gado hannunta riƙe da cazbaha tana ja dan sam ta kasa bacci, idan ta tuna gobe za’a ɗaura auren Nana ta yi nesa da ita sai taji duk jikinta ya sake sanyi, kamar yau ta haifeta aka dinga zuwa kallonta amma ace har ta yi girman da za’a aurar da ita, itama ta zama matar gida. Wannan tunanin shi ne abin da ya hanata bacci, ga kuma tausayin Nana sanin ba son auren take ba, babu yanda bata yi da Abba ba amma sam yaƙi fahimta, ya kuma kafe akan dole sai Nana ta auri Safwan. Dan haka ta rabu dashi bata sake cewa komai ba, shi ma bai sake yi mata magana ba sai sabgoginsa yake a ɗakin, ya dinga waya da mutanensa na ƙasar waje wadanda zasu halarci ɗaurin auren da za’a yi gobe, a zahiri idan ka ganshi zaka iya rantsewa akan babu abin da ke damunsa, amma cikin zuciyarsa fal take da ƙunci da kuma damuwa. Ji yake kamar kada gobe ta yi domin bai shiryawa jin kukan tilon ƴar tasa ba, duk da bai san dalilinta na ƙin auren ba, amma yaji shima baya son auren. Sai dai ba zai taɓa iya yarda ya ce haka ba saboda gudun lalacewar zumunci. Dan haka ya dinga ƙoƙarin riƙe kansa da kawar da komai daga ransa, wanda haka yasa Amma ta dinga tunanin ko dai bai damu da Nanar bane.
Kiran Sallar asubahin farko mutane suka fara tashi, masu ɗora tuwon ɗaurin aure suka fara aikinsu haka ma masu yin sauran girke-girke. Wajejen ƙarfe 6 na safe kuwa sai mutum ya ɗauka 12 ce ta yi saboda yanda ake shige da fice a cikin estate ɗin, dangi da abokan arziki sai kai kawo suke. Burin kowa ya gama abin da yake gabansa domin ɗaurin auren karfe 10:30 na safe ne.
Ƙarfe 7 saura Hamida ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Nana na zaune gefen gado ta zuba uban tagumi dan bata san ma ta shigo ɗin ba, Hamida ta girgiza kanta tana mamakin yanda Nana ta fi kowa damuwa akan auren, a hankali ta taɓata ta ce
“Nana”
A ɗan firgice Nana ta kalleta sai kuma ta sauke numfashi ta ce“na’am”
“ki zo in ji Mama”
To kawai Nana ta ce sannan ta fara ƙoƙarin miƙewa, ta zura hijabin da ta yi sallah sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin Hamida na biye da ita. Gaisar da mutanen dake parlon suka yi sannan suka fice, Hamida sai hira take mata ita kuwa ta kasa cewa komai sai uhm da uhm’uhm, a haka har suka ƙarasa apartment ɗin su Hamidan.
Koda suka shiga ciki Nana turus ta yi ganin su Amrah, Maimoon da kuma Haule. Kowannensu zaune sun yi shiru suna jiran su ji abin da Mama zata ce, zama Nana ta yi gefen Maimoon sannan ta gaida Mama, Mama ta amsa fuska a sake sannan ta gyara zamanta tana kallonsu duka ta ce
“Nasan kun san abin da ake nufi da aure, ba sai na yi wani dogon jawabi ba. Kawai dai zan ɗan tunasar daku ne na kuma ƙara muku haske akan wasu abubuwan wanda na san ba lallai bane kun san su” shiru duka suka yi suna saurarenta. Mama ta sauke numfashi sannan ta fara masu nasiha cikin salo na yanda zasu gane me take nufi, duk wani abu mai muhimmanci sai da ta tabbata ta sanar dasu, sannan ta sanya suka yi addu’a a tare kafin ta sallami kowa ya tafi don shiryawa lokacin wajejen ƙarfe 8:00 na safe.
Koda suka fito Maimoon ce ta ja Nana gefe tana kallonta ta ce“ya ake ciki?” Nana ta sauke numfashi kafin a sanyaye ta ce“nima ban sani ba Maimoon. Abba ba zai taɓa bari a fasa auren nan ba, kawai yanzu ina tsoron abin da sir Junaid zai yi ne, domin jiya Aunty Zahra ta ce min komai ya shige ita”
“komai ya shige ta ce?”
Nana ta gyaɗa kanta. Shiru Maimoon ta yi tana mamaki can kuma ta ce“to ta baki hotunan?” girgiza kai Nana ta yi ta ce“a’a suna hannunta, so nake idan komai ya lafa sai naje na amsa na hada dana wajena na ƙona”
Maimoon ta buɗe baki zata yi magana kenan ta hangi su Aunty Khadijah suna tawowa, Siyama ce ke biye da ita sai Safeena da Amal, kowaccen su ta ci uwar kwalliya kamar bikin gidansu ake. Ta gaban su Nana suka zo suka shige, Maimoon ta taɓe baki sannan ta ce
“gayyar tsiya”
Ɗan murmushi Nana ta yi ta ce“ke ina ruwanki dasu?”
“to banda neman magana uban me ya kawosu gidan mu? Har su ci wata kwalliya”
Nana ta girgiza kanta tana kawar da zancen ta ce“ke ni ƙirjina ciwo yake bari na tafi na kwanta kafin karfe 9 ta yi, Khadijah ta ce min da wuri zata tawo”
“Zuwa zata yi?”
Gyaɗa mata kai Nana ta yi, Maimoon ta ce“Khadijah bala’i ta zo mu sha dariya”
Nana ta ɗan yi shiru tana ƙarewa compound ɗin gidan kallo can kuma ta ce“sai an jima”
“ok. Duk yanda ake ciki ki faɗa min ko a waya ne”
Toh kawai Nana ta ce sannan ta saketa ta nufi hanyar apartment ɗinsu, Itama Maimoon juyawa ta yi ta nufi nasu apartment ɗin. Safwan ya sauke wani zazzafan numfashi sannan ya juya ya bar wajen bayan ya gama kallonsu. Koda ya shiga gida sama ya shige ya zauna a gefen gadonsa yana tunanin mafita. Tabbas idan ya ce ya fasa auren Nana a yau to komai zai zo masa da sauki, kuma zai samu damar auren Siyama. to amma ta ina zai fara fitar da wadannan hotunan nata? Ya girgiza kansa a fili ya ce
“No i can’t! Ba zan iya ba wallahi”
Ya ƙare maganar yana kawar da tunanin daga ransa.
****
Around 9am Zahra ta shiga sakkowa daga saman hannunta riƙe da Noor wadda aka mata kwalliya da wata doguwar riga ta atampa Holland ɗinkin t-boubou wanda yasha aiki, ɗinkin ya mugun yi maga mata kyau kamar ba ƙaramar yarinya ba. Zahra kuwa sanye take da wani ubansu lace ash colour ɗinkin doguwar riga yaji stones sai kyalli yake, ta yi yar simple make-up a fuskarta wadda ta ƙara mata kyau. Safeena na murmushi ta ce“woww Aunty wallahi kin yi kyau kamar kece amaryar”
Murmushi kawai Zahra ta yi sannan ta zauna kan sofa tana cewa“ban san sharri Safeena”
“Ai ba sharri ta miki ba wallahi kin yi kyau”
Amal ta yi maganar itama tana murmushi, kallonsu Zahra ta yi sai kuma ta gyaɗa kanta irin ta jin nan ta ce“tofa ai shikenan” daga haka ta kalli Aunty Khadijah ta ce“har na fara tunanin kiran ki” Aunty Khadijah na taunar cew gum wanda ya zame mata dabi’a ta ce
“wallahi mun biya ta wajen Kaddu ne na amshi saƙo shiyasa ki ka ga mun daɗe. Hope dai komai na tafiya dai dai?” jinjina kai Zahra ta yi tana kallon Noor ta ce“eh in sha Allah komai zai tafi kamar yanda muka tsara”
“Ummi zan tafi wajen Hajiya”
Noor ta yi maganar tana wasa da ɗankwalin dake hannunta, Zahra taja hancinta ta ce“ba zaki jira mu tafi tare ba?” maƙale kafaɗa ta yi, ta ce“to je ki Allah ya tsare” tsalle Noor ta yi sannan ta fice daga parlon da gudu.
Miƙewa Siyama ta yi tana danna wayar hannunta ta ce“ina zuwa”
“Ina zaki je Siyama?”
Aunty Khadijah ta tambayeta. Juyowa ta yi tana kallonta ta ce“Safwan ke kirana yana waje”
Jawo hannunta Aunty Khadijah ta yi ta zaunar da ita sannan ta buɗe jakar hannunta tana ƙoƙarin zaro abu ta ce
“ke wace irin banza ce ne? Ba sai ki faɗa min ba, ko kin manta?”
Ta ƙare maganar tana fito da kwallin ta miƙo mata, amsa Siyama ta yi sannan ta buɗe tana ƙoƙarin sakawa ta ce“to bana manta ba, kin san…” maganar ta maƙale saboda waya irin azaba da taji ta ziyarci ƙwaƙwalwarta, ta saki kwallin sannan ta miƙe tsaye tana fashewa da ihu ta ce
“wayoooo Allah na na shiga ukuna Mommy, idona na shiga uku” tashi Aunty Khadijah ta yi ta riƙeta tana faɗin “meya samu idanun”
“barkono, wallahi barkono ne a ciki wayyo idona, na shiga uku na makance Mom”
Ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani kukan, sai murza idanun take da duka hannayenta biyu. Gaba ɗaya rikicewa suka yi, suka dinga yi mata sannu ana zuba mata ruwa, Safeena ce kawai zaune tana dariya ƙasa-ƙasa dan ita daɗi taji da hakan ta kasance. Kusan mintuna 15 kafin ta iya buɗe idanun, amma sun kumbura sun ji jajur dasu. Ta miƙe kamar me cutar makanta tana dafa gefen kujera ta ce“wallahi Mom bana gani”
Ta ƙare maganar tana sake gwale idanun nata, Zahra ce ta riƙe hannunta ta ce“wai duk bakya ganinmu?” sai dai ta gwalalo idanun sannan ta ce“ina ganinki kaɗan-kaɗan” dariya ce ta kusa kama Zahra amma ta dake ta ce“to za ki iya zuwa wajen Safwan ɗin?” kamar ƙaramar yarinya ta gyaɗa kanta ta ce“eh zan iya, Mom ara min glasses ɗin ki” tsaki Aunty Khadijah ta yi tana nuna ta da hannu ta ce
“Ji banza, to uban me zai gani idan idanun na cikin glasses?”
Siyama ta yi shiru sai kuma ta juya ta nufi hanyar waje jin wayar na ringing.
A can wani garden na bayan estate ɗin ta samu Safwan tsaye yana jiranta, sanye yake da jallabiya baka a jikinsa, ya dinga kallonta har ta ƙaraso wajen. Murmushi Siyama ta sakar masa sannan ta ce
“Ina kwana?”
Kasa dauke idanunsa ya yi daga cikin nata sai murmushi da ya yi ya ce“lafiya kalau my love kin zo ashe?”
Tana wasa da fingers ɗinta ta ce“Eh ba dole na zo aurenka ba”
Haɗe rai Safwan ya yi ya ce“aurena kuma?”
Siyama ta sake fari da idanunta sannan ta ce“eh aurenka mana, ba yau za’a ɗaura maka aure da Nana ba?” tsaki ya yi yana kallon gefe ya ce“sai aka ce miki ita zan aura?”
Ganin kamar ransa ya fara ɓaci yasa Siyama ta langwaɓar da kanta ta ce“a’a ai haka naji ne”
“To ba ita zan aura ba. Ki je ki jirani kinji”
Siyama ta saki murmushin jin daɗi ta ce“tom shikenan sai ka zo” daga haka ta juya ta bar wajen tana tafe cike da kwarkwasa. Safwan ya haɗiye wani yawu sannan ya juya ya bar wajen.
Ƙarfe 10:00 na safe Abba ya shigo ɗakin yana sanye da wata dakkakiyar madam gezner fara ƙal ɗinkin jamfa da babbar riga, ya sanya hular zanna akansa sai zuba ƙamshi yake. Ko ba’a faɗa maka ka san ba ƙaramin kuɗi aka kashe a gurin ba, Ya tura kofar dakin Amma bakinsa ɗauke da sallama. Zaune ya sameta tana sanye da wani lace mai azabar kyau da tsada itama, sai dai sam fuskarta babu annuri, musamman yanda taga Nana ta yi shiru tun ɗazu bata ce komai ba.
Abba ya dinga kallon su sai kuma ya ce“Nana ki je apartment ɗin Hajiya Babba”
Sai a sannan Nana ta ɗago kanta ta kalleshi da idanunta wanda suka sake kumbura da alama ba ƙaramin kuka tasha ba. Sanye take da wani ubansu lace blue colour mai adon pink a jiki, an yi musu ɗinkin straight gown wadda ta ɗan kama jikinta amma ba sosai ba, ɗankwalin lace ɗin na ajiye gefen gadon kanta wanda yasha gyara sai sheƙi yake. Murya a sanyaye ta ce
“to Abba”
Ya jinjina kansa sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Amma ta sauke numfashi ta kalleta ta ce“zo na ɗaura miki ɗankwalin” babu musu Nana ta tsaya ta daura mata duk da ba wani ɗaurin me kyau bane amma sai ya saka ta ƙara kyau, ta miƙa mata pink ɗin mayafinta wanda ya kasance big size ta ce“saka ki tafi” a gefe ɗaya Nana ta yafa sannan ta tashi tsaye tana gyara zaman rigar jikinta. Amma ta ce“bari naje wajensu Ramlah” to kawai Nana ta ce Amma ta fice daga ɗakin. Komawa ta yi ta zauna tana fashewa da wani sabon kukan, ta kalli wayarta sai kuma ta sake rufe fuskarta da hannayenta cikin kuka ta ce
“nashiga ukuna, ya zan yi da raina. Allah ka yafe min”
Ta faɗa tana ƙara sautin kukan nata.
****
A can compound ɗin Hajiya Babba kuwa jama’a ne a cike na birnin Yola dama cikin ƙauyuka, sai shige da fice ake ana kai komo, kowa ka ganshi tsaf dashi babu alamar babu ko talauci a tare da duk wani ɗan dangin Shuwa.
Angwayen duk sun yi shiga iri ɗaya, Shadda gezner milk colour an yi aikin sirfani da brown ɗin zare, sai baza manyan riguna ake, ko ina ka gifta sai ƙamshi ne ke tashi. Papa kuma da Abdusammad irin kaya ɗaya suka yi da Abba. Hajiya Babba ma ta ci kwalliya cikin wani tsaddajen lace ɗinkin boubou. Ta yafa mayafinta aka sai zuwa dibar gaisuwa ake, haka ma Atta irin kayan Hajiya Babba ne a jikinta amma ita sam ta kasa zama sai shiga take tana fita. Atta ta leƙa dakin dasu Maimoon ke zaune kowacce da lace irin na Nana a jikinta, ta dinga kallonsu ganin babu mutuniyarta a ciki yasa ta ce“Ke Maimuna ina Nana?” Maimoon ta miƙe tana gyara mayafinta ta ce“har yanzu bata zo ba bari naje na kirata” to kawai Atta ta ce sannan ta saki ƙofar ɗakin. Moon ta zura takalmanta wanda suka kasance pink colour sannan ta fice daga ɗakin.
Sanda ta fito har an baza carpet a compound ɗin Hajiya Babba dan daman a nan ne ake daura auren, Ta shige da sauri tana jan mayafinta ya rufe kanta.
Koda ta shiga ɗakin zaune ta samu Nana sai kuka take, ta rufe ƙofar da key sannan ta ƙarasa ciki tana kallonta ta ce“Nana wani abun kuma?”
Ɗago kanta ta yi hawaye sai zubowa yake daga idanunta ta ce”na shiga uku Maimoon, na shiga ukuna, mutuwa zan yi” da mamaki Maimoon ke kallonta, lokaci ɗaya taji gabanta ya yi wata irin faɗuwa, ta zaune gefenta tana rike hannunta ta ce“ki faɗa min mene ne? Meya faru?”
Kasa magana ta yi sai kuka da take kamar ranta zai fita, ta ɗora kanta akan cinyar Maimoon tana ci gaba da kukanta.
Ƙarfe 10:20 Safwan ya ƙaraso wajen yana gyara zaman babbar rigarsa, idanunsa ya sauka kan mutane da ke zaune a compound ɗin kowanne jira yake a zo a ɗaura auren. Ya yi jim sai kuma ya ƙarasa inda su Aliyu ke tsaye ya tsaya, kallonsa Aliyu ya dinga yi ganin yanda idanunsa suka yi jajur ya ce
“Safwan ko kai ma kukan auren ka yi?”
Cike da zolaya ya yi maganar, dan haka Hamid ya yi dariya ya ce“ai kasan ɗan auta ne zai auri yar auta za’a ga shagwaɓa” suka yi dariya duka. Shi kuwa Safwan kasa dariyar ya yi, murya can ƙasa ya ce“Yaya nifa na fasa auren nan”
Aliyu da yaji kamar daga sama ya ce“me ka ce Safwan?” ɗago kansa ya yi ya ɗan kalleshi sai kuma ya ce
“cewa nayi na fasa auren nan, ni ba zan auri Nana ba!”
”What!”
Hamid ya yi maganar yana zare idanu, sai kuma ya girgiza kansa yana dafa kafaɗarsa ya ce“kai dallah kar ka kawo mana wasa anan kaji”
“Wasa? Kuma kawai sai nayi wasa? Wallahi na fasa auren nan, ba zan auri Nana ba!”
Ya ƙare maganar yana zazzaro idanu. Aliyu da yaga abun nasa na neman zama na gaske ya riƙe shi ya ce“Safwan lafiya?”
“kawai a tara kowa a Apartment ɗin Hajiya wallahi ba ita zan aura ba!”
Daga haka ya fizge jikinsa ya yi hanyar balcony ɗin Hajiya. Kamar wasu marasa wayo haka suka dinga bin sa da kallo, cike da mamakin furucin nasa, Aliyu ya numfasa ya ce“bari dai na samu na yi magana da Papa” daga haka ya bar wajen shima. Sultan kuwa shiru ya yi dan daman tun ba yau ba ya lura da take-taken Safwan ɗin.
****
Tsaye suke gaba ɗaya a parlon, Abba, Papa, Sultan, Aliyu, Hamid, Atta, Hajiya Babba, Mama. Idanunsa duka akan Safwan wanda ke tsaye tsakiyar ɗakin, kansa a sunkuye, Papa ne ya yi ƙarfin halin faɗin
“Safwan me ka mayar da mutane? Abokan wasanka?”
Shiru ya yi bai ce komai ba, dan tun ɗazu suke tambayarsa amma ya gagara cewa komai. A fusace ya buɗe ƙofar parlon ya shigo, kai tsaye wajen Safwan ɗin ya karasa yana zuwa ya ɗaukeshi da mari har guda biyu sannan ya cakumi kwalar rigarsa yana masa wani irin kallo cike da tsananin ɓacin rai ya ce



