Chapter 23: Chapter 23
Ashe daman baka da mutunci? Ashe baka da hankali ban sani ba? Are you out of ur sense!”
Ya ƙare maganar a tsawace yana jijjigashi, gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun tashi sai huci yake kamar mayunwacin damisa. Abba ne ya ƙaraso wajen ya riƙe hannunsa ba tare da ya ce masa komai ba, Abdusammad ya fizge hannunsa ya ce
“Abba dan Allah rabu dani! Mu yaron nan zai zubarwa da mutunci! Da can bai ce ba zai aureta ba sai yau da aka tara dubban al’umma a waje? Shi ya isa?” ya ƙare maganar yana huci, sai kuma ya sake cakumar Safwan ya ci gaba da faɗin
“To wallahi tallahi sai ka aureta! Kai baka isa ka ce ba zaka aureta ba”
Ya hankaɗa shi har sai da ya kusan faɗuwa Papa ya tare shi. Gaba ɗaya parlon ya ɗauki tsit babu wanda ya yi magana. Safwan ya numfasa sai kuma ya ce
“Ni fa Abba ba wani abun nace ba, kawai cewa nayi ba zan auri Nana ba! Kuma ita ma yarinyar a kirata a tambayeta ta ce ba zata aureni ba, kaga kuwa babu amfanin na auri wadda bana ra’ayi kuma bata ra’ayina, dan haka dan girman Allah kada ku tilasta min, wallahi ba zan iya auren Nana ba, akwai wadda take cikin raina tun ba yau…”
Bai ƙarasa maganar ba Abdusammad ya rufe shi da duka ya shaƙe nasa wuya cikin masifa ya ce“to kar ta so kan, ko tana so ko bata so wallahi sai an yi auren nan!”
Aliyu ne ya janyeshi daga jikinsa yana fadin “Ya isa haka Buddy, abi komai a hankali” banza Abdusammad ya yi masa ya fizge jikinsa yana kwafa. Abba ya sauke numfashi sannan ya kalli Safwan ya ce
“Ka san da baka sonta ka bari muka tara jama’a Safwan? And wait, wane ya ce maka sai kana sonta sannan zaka aureta? Mu ba haka tsarinmu yake ba, kuma ku baku isa ku zo ku lalata mana tsari ba! Dole ne ka auri Nana!”
Safwan ya dinga kallon Abba dan yana matukar ganin girmansa kuma baya jin zai iya sa’insa dashi. Dan haka ya sunkuyar da kansa murya a sanyaye ya ce“ka yi haƙuri Abba wallahi ba zan taɓa auren Nana ba!”
Hajiya Babba ce ta ƙaraso wajen ta dinga kallonsa sai kuma ta dauke shi da wani marin cikin matsanancin ɓacin rai ta ce“Mu zaka wulaƙanta Safwan? So ka ke a yi mana dariya? To wallahi idan har ka sake wannan maganar sai dai ka nemi wata uwar amma bani Khadijah ba!”
Da sauri ya ɗago kansa hannunsa dafe da kuncinsa, Hajiya Babba ta maka masa wata uwar harara tana barin wajen, Papa ne ya sauke numfashi sai kuma ya ce“su wane a ciki?”
“Yaran ne”
Mama ta bada amsa. Papa ya kalli ƙofar sai kuma ya ce“to su fito” ok kawai Mama ta ce sannan ta ƙarasa ta buɗe ɗakin, suna zaune kowacce ta yi shiru jiki a sanyaye dan duk abin da ake faɗa suna ji. Mama ta ce musu su fito sannan ta bar wajen, a sanyaye suka shiga fitowa ɗaya bayan ɗaya, suka ƙaraso parlon suka tsuguna cike da ladabi. Papa ya dinga kallonsu sai kuma ya ce
“Ina Nana?”
“tare muka fito ta ce bari taje ta manta wayarta.”
Maimoon ta yi maganar kanta a ƙasa, Papa ya ɗan numfasa sai kuma ya kalli Abba ya ce“kira Rabi’ah ta tawo da Nana nan” ok kawai Abba ya ce sannan ya zaro wayarsa a aljihu ya yi dialing numbern Amma, ringing ɗaya ta ɗauka dan wayar na hannunta, Abba ya ce
“Ki zo da Nana apartment ɗin Hajiya yanzu”
“Dama bata tafi ba?”
Amma ta tambaya da mamaki, Eh kawai Abba yace sannan ya katse kiran, Amma ta tashi ta nufi daƙinta. Sai dai me koda ta buɗe babu Nana babu alamarta, ta girgiza kai sannan ta buɗe ɗakin Nanar, ga mamakinta sai ta tarar nan ma bata nan. Amma ta dawo parlon tana kallon Aunty Safiya ta ce“Aunty Nana bata fita ba kuwa?”
“Nana gaskiya bata fita ba, na dai ga ta shiga daƙinta ɗazu”
Amma ta ɗan ja siririn tsaki sai kuma ta koma ɗakin, ganin bata ciki yasa ta nufi toilet tana cewa“Nana ke Nana” jin bata amsa ba yasa ta ce“yi sauri Abbanki na jiranki” daga haka ta koma gefen gado ta tsaya, tana nan tsaye har bayan mintuna biyar kiran Abba ya sake shigowa wayarta, ta daga ya ce
“jiranki fa muke”
Amma ta ce
“ban ganta a ɗakin bane, I thought tana toilet kuma naji shiru”
Rai ɓace Abba ya ce“to ba zaki duba ba?” Amma ta ce to sannan ta kashe wayar, toilet ɗin taje ta murɗa sai ta ga wayam babu alamar mutum. Ta juyo tana faɗin
“To gidan ubanwa ta shiga so take ya yi ta…”
Maganar ta tsaya cak saboda takardar data gani akan gado iska sai kaɗata take, ta ɗan ware idanunta tana mamakin abin da ya kawo takardar, sai kuma ta ƙarasa a hankali ta ɗauka tana ƙarasa wareta. Amma ta buɗe idanunta sosai tana karanta rubutun dake jikin takardar kamar haka;
_Abba, Amma dan Allah ku yi haƙuri, ba zan iya ci gaba da ɓata muku rai ba, ba zan bari kuji mummunan labari akaina ba, nasan ba zaku jure ba. Ina fatan koda kun ga abin da za’a nuna muku ya kasance bana wajen, Ban tafi dan son raina ba, a’a na tafi ne dan babu yanda zan yi, ba zan iya jure ganin halin da zaku shiga ba. Dan Allah dan Annabi ku yafemin, wallahi ko me za’a nuna muku ba haka abun yake ba, idan Allah ya so watarana zan muku bayanin komai, idan kuma ban sake ganinku ba, ina roƙon ku daku manta dani. Ku manta da kun haifi ƴa kamata, ku manta dana rayu tare daku. Dan Allah ku manta da NAANAH!_
Amma ta dinga kallon takardar cikin tashin hankali, ilahirin jikinta rawa yake. Ta girgiza kanta sai kuma ta fice daga ɗakin da gudu. Kai tsaye apartment ɗin Hajiya Babba ta nufa tana tafe kamar zararriya, gaba ɗaya bata cikin hankalinta. Koda ta tura ƙofar tsaye ta samesu sun yi jigum-jigum da alama zuwan Nanan suke jira. Ta ƙarasa ciki kai tsaye kuma wajen Abba ta nufa tana faɗin
“Kaga! Kalli kaga”
Ta ƙare maganar tana miƙa masa takardar hannunta, Abba ya dinga kallonta da mamaki sai kuma ya karɓi takardar ya buɗe. Sai da ya sake kallon Amma da ke tsaye tana girgiza kanta sannan ya mai da idanunsa kan takardar ya fara karantawa.
Wata irin zufa ce ta dinga keto masa tun daga tsakiyar kansa, Ya kasa cewa komai hannunsa sai rawa yake, ganin haka yasa Abdusammad ya ƙaraso gabansa ya zare takardar ba tare da y ce komai ba. A fili kuma ya karanceta tas, ban da salati da sallalami babu abin da ke tashi a parlon, Su Hamida kuwa sai kuka suke kamar ransu zai fita. Atta ma ta ɗora hannu aka cikin tashin hankali ta ce
“*** wace irin masifa ce wannan? Ina yarinyar nan ta shiga? Mun lalashe”
Ta ƙare maganar tana sakin kuka. Sultan kuwa girgiza kansa kawai yake yana tunanin abin da yasa Nana ta yanke wannan ɗanyen hukuncin. To mene ne abun da take magana akai? wane zai fadi wani abu akanta. Lokaci ɗaya ya mai da idanunsa ka Safwan wanda babu alamar fargaba ko tashin hankali a tare dashi. Ya girgiza kansa yana tabbatar da cewa tabbas akwai abin da ya haɗata da Safwan ɗin.
Abba da ƙafafunsa suka fara gagarar ɗaukansa ya yi baya kamar zai faɗi, Abdusammad ya tare shi da sauri yana fadin
“Abba stay still pls”
Riƙe hannunsa Abba ya yi yana jinjina masa kai. Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi, idanunsa sun kaɗa sun yi jajur, amma babu alamar tashin hankali a tare dashi a zahirance. Hajiya Babba da tun ɗazu bata ce komai ba ta numfasa sannan ta kalli Abba ta ce
“Aje a gabatar da ɗaurin auren, babu abin da zai hana Safwan auren Nana!”
Kusan a tare duk suka kalleta, Safwan ya girgiza kansa lokaci ɗaya hawaye ya kawo cikin idanunsa ya ƙarasa gabanta ya tsuguna murya a tausashe ya ce
“Dan Allah dan Annabi Hajiya kada amin dole, wallahi ba zan iya auren Nana ba! Ba zan iya ba, dan girman Allah a bar wannan maganar!”
Ya ƙare maganar yana haɗe hannayensa alamar roƙo. Ɗauke kai Hajiya Babba ta yi kamar bata ji abin da ya ce ba, dan haka yaja jikinsa da rarrafe ya ƙarasa inda Abba yake tsaye, ya dafa ƙafafunsa cikin kuka ya ce
“Abba na san kana da fahimta, na san kai ubane. Kuma zaka fahimci abin da nake nufi, wallahi tallahi ba zan iya auren Nana ba, kuma bani da burin sanar da ku wani abu game da haka. Dan haka dan Allah dan Annabi abar maganar aurena da ita”
“Kai ka isa, wallahi sai ka aureta! Kuma ita ma duk inda ta shiga sai ta fito! Dole ne a ɗaura wannan auren!”
Abdusammad ya yi maganar yana fincikoshi. Safwan ya dinga kallonsa hawaye na zubowa daga kan fuskarsa, ganin yanda ran Abdusammad ɗin ya ɓaci yasa ya ce
“A”a Yaya kada mu fara haka da kai, kada mu yi dan Allah. Ina jin maganarka, ina ganin girmanka. Ba zan so na ɓata maka rai ba, dan haka dan Allah ku fahimceni”
Wani irin kallon ka zama mahaukaci Abdusammad ya dinga yi masa can kuma ya sake shi ya girgiza kansa ya ce“ko kaɗan ban yi tunanin irin wannan daga wajenka ba Safwan. Wallahi ban taɓa tunanin zaka zo da irin wannan maganar ba, ka bani kunya! Ka bani kunya Safwan!”
Ya ƙare maganar a tsawace.
Shiru parlon ya ɗauka kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa, Amma ta yi zaman dirshan gefen Hajiya Babba sai kuka take kamar ranta zai fita, tunaninta shi ne ina Nanarta ta shiga? Me ya sa ta tafi ta bar su?.
Papa ne ya numfasa sannan ya tako daga inda yake ya zo gaban Safwan, ya sanya hannunsa na dama ya dafashi murya a ɗan cunkushe ya ce
“Safwan meyasa ba zaka iya auren Nana ba? Na san dole kana da hujjarka ta yin haka. Idan har ka faɗa mana hujjar kuma muka duba muka da abin da ka faɗa kana da gaskiya ba za’a maka dole ba, domin tun da har ka furta ba zaka aureta ba koda an yi auren ba za’a samu zaman lafiya ba”
Safwan ya dinga kallonsa fuskarsa caɓa da caɓa da hawaye kamar karamin yaro. Ya janye hannun Papa daga jikinsa sannan ya yi taku biyu gabansa ya ja ya tsaya, muryarsa a sanyaye ya ce
“Papa ba zan auri Nana ba, akwai wadda nake son na aura, kuma yau nake son a ɗaura mana auren da ita.”
Da wani irin mamaki suka dinga kallonsa. Sultan ya girgiza kansa a fili ya ce“daman na san wannan ne shirin ka, amma baka da hankali Safwan!” ya yi maganar rai ɓace. Papa ne ya ɗaga masa hannu sannan ya mai da idanunsa kan Safwan ya ce“ina jin ka, idan har ka faɗi hujjar da ta dace na yarda zaka auri wadda ka ke so”
Da sauri ya juyo ya kalleshi. Papa ya gyaɗa masa kai alamar tabbatarwa. Shiru Safwan ya yi yana tunanin mafita, can kuma ya nufi hanyar upstairs, da gudu Maimoon ta tashi ta ƙarasa inda yake ta rike babbar rigarsa ta baya tana kuka. Lamarin da ya sanya hankalin kowa ya koma kansu, Safwan ya juyo yana kallonta da mamaki, ta sake ruƙunƙumshe tana kuka ta ce
“A’a Yaya, dan girman Allah kada ka yi haka. Kada ka yi haka kaji”
Sosai jikin Safwan ya yi sanyi, ya janyeta daga jikinsa hawaye na biyo kan fuskarsa. Kuka take sosai gaba ɗaya ta birkice kanta, Ya yi shiru yana tunani sai kuma ya fara ƙoƙarin sakkowa daga saman. Maimoon ta sauke ajiyar zuciya sannan ta biyo bayansa tana kuka a hankali. Ganin yanda kowa ke kallonsa yasa ya sunkuyar da kansa yana kallon Papa ya ce
“I’m sorry Papa”
Murmushin takaici Papa ya yi kafin ya ce“sorry? Sorry for what Safwan?”
Kasa cewa komai ya yi, lokaci ɗaya ya shiga lalubar aljihunsa, cikin yan sakanni ya zaro envelope ɗin. Ban da kallonsa babu abin da ake a ɗakin, ita kuwa Maimoon mutuwar tsaye ta yi dan ko kukan ta gagara yi, ta tabbata asirin Nana ya gama tonuwa.
Papa ya dinga kallon envelope ɗin da Safwan ya bashi ba tare da ya ce komai ba. Safwan ya goge hawayen fuskarsa sannan ya ce
“wannan dalilin ya sanya ba zan iya auren Nana ba! Kuma na san idan ku ka gani zaku tabbatar da gaskiyata”
Daga haka ya sake sunkuyar da kansa. A hankali Papa ya buɗe envelope ɗin ya zaro hotunan gaba ɗaya, Sai dai abin da idanunsa suka gane masa sune suka sanya shi cikin wani hali na kiɗima da tashin hankali. Ya yi baya kamar zai faɗi Hamid ya tare shi yana amsar hotunan, ɗaya bayan ɗaya ya dinga buɗe su zufa na keto masa. Papa kuwa zaman daɓaro ya yi kan sofa ya tallafi fuskarta da duka hannayensa biyu, ban da innalil lahi babu abin da yake maimaitawa cikin ransa.
Sultan ne ya ƙarasa wajen Hamid ya fizge hotunan yana buɗe su, ya kasa ɓoye tashin hankalinsa a fili ya shiga furta
“Innalil lahi wa ina ilayhi raji’una, Ya subhanallahi!”
Ya ƙare maganar yana jifa da hotunan. Ban da kallonsu babu abin da sauran ke yi, Maimoon kuwa sai ajiyar zuciya take saukewa ta ruƙube a jikin bene. Abba ne ya sunkuya ya ɗebi hotunan dan gabansu suka faɗo, Ya dinga buɗe su ɗaya bayan ɗaya. Baya ya yi ya faɗi ƙasa, jikinsa sai rawa yake, Abdusammad ya sunkuya da sauri yana kallonsa ganin kamar bata cikin hayyacinsa ya amshi hotunan. Waro idanunsa ya dinga yi akan ko wane daya daga cikin su, Lokaci ɗaya ya miƙe tsaye ya ƙarasa wajen Safwan ya shaƙeshi yana faɗin
“Tell me ina ka samu wannan? Wane ya baka? A ina ka samu Safwan?”
Ya ƙare maganar yana jijjigashi kamar zai tsinke masa jiki. Girgiza kai Safwan ya yi bai ce komai ba, Abdusammad ya hankadashi sannan ya koma in da Abba yake ya riƙe shi yana faɗin
“Abba kada wannan ya dameka kaji, nothing will happen”
Wani murmushi mai ciwo Abba ya yi sannan ya dafa Abdusammad ya miƙe, sai da ya kalli kowa na parlon da idanunsa wanda suka kusa rufewa sannan ya yi murmushi mai haɗe da hawaye. Ba ƙaramin mamaki da kuma tausayi ya bawa kowa ba, domin rabon da ya zubar da hawaye tun mutuwar late Muhammad Shuwa, dan haka ba kowane ya taɓa ganin hawayen nasa. Amma ce ta taso da sauri ta ƙaraso gabansu kamar zararriya ta ce
“mene ne? Me ya samu Nana?”
Ganin babu wanda ya ce mata uffan yasa ta dinga kallon kasa cikin sa’a kuwa idanunta ya sauka kan hotuna guda biyu, kusan yar tsere suka yi da Sultan sai dai kafin ya ɗauka hoton ta riga da ta ɗauka. Ta dinga kallonsu tana girgiza kanta bakinta na wata irin rawa ta ce
“a… A’a… Wannan ba Nana ba ce, ba Nanata bace..ba ita ba ce wallahi!”
Sai kuma ta zubar da hotunan ta koma inda Abba yake tsaye ta riƙe kwalar rigarsa cikin tashin hankali ta ce
“Ahmad ka faɗa min, ka faɗa min gaskiya, ai ba Nana ba ce ba ko? Ba ita ba ce ba ko! Ni nasan ba ita ba ce, wannan ba Nanata ba ce, ka sanar dani dan Allah”
Ta ƙare maganar tana rushewa da wani raunataccen kuka. Abba rasa abin yi ya yi sai kawai ya rungumeta a jikinsa yana sauke numfashi a hankali, murya can ƙasa ya ce
“Ki yi haƙuri Rabi’ah”
Da sauri ta ɗago kanta tana kallonsa sai kuma ta ce“Nana ce?”
Jin bai ce mata komai ba ya sanya ta sake sakin wani marayan kukan ta ce“ka faɗa min mana!”
A hankali ya shiga gyada mata kai, Amma ta dinga kallonsa kai kuma ta yi baya ta faɗi ƙasa Sumammiya. Cikin hanzari Mama dasu Maimoon suka yi kanta. Abba kuwa kasa koda motsi ya yi sai numfashi yake saukewa. Da hannu ya yiwa Safwan alamar ya zo, ya ƙaraso kansa a ƙasa dan kunyar haɗa idanu yake da Abban. Shafa kansa Abba ya yi muryarsa a kusan ƙarye ya ce
“Safwan ni na amince ka auri wadda ka ke so, ba kai ba bana fatan kowani daga cikinku ya auri Nana!”
Da sauri duk suka kalleshi, Papa ya miƙe idanunsa sun yi jajur shima. Zai yi magana Abba ya ɗaga masa hannu ya ce”a’a Yaya kada ku hana shi dan Allah, Ni ina neman wannan alfarmar a bar shi ya auri wadda yake so”
Rungume shi Safwan ya yi yana kuka, ya rasa farin ciki zai yi ko kuma baƙin ciki. Abba ya shafa kansa yana murmushin ƙarfin hali. Can ya ɗago kansa yana kallon Abba ya ce“Abba koda ba yar cikin gidan nan bace?”
Gyaɗa masa kai kawai Abba ya yi dan ya fara daina ganewa, Safwan ya yi murmushi mai haɗe da hawaye ya ce“to daman ƙanwar matar Yaya nake so”
Da mamaki Abdusammad ya dinga kallonsa, lokaci ɗaya kuma ya girgiza kansa ya ce“kai ka isa, ba zaka aureta ba wallahi, ba zaka auri wadda ba yar danginmu b!”
Rufe masa baki Abba ya yi ya ce“a’a Abdusammad ka yi kaffara, zai yi aurensa. Wannan alƙawarina ne, ku je ku gabatar da komai, a ɗaura auren kowace cikin farin ciki zan je na huta”
Kasa cewa komai suka yi, gaba ɗaya wajen tausayinsa suke, ko bai faɗa ba sun san ƙarfin hali kawai ya ke. Ya juya yana ƙoƙarin tafiya, sai dai sarawar da kansa ya yi masa ya sanya shi dakatawa, ya dafe kan yana kiran sunan Allah. Ji ya yi an riƙe shi ya ɗago jajayen idanunsa yaga Abdusammad ne, murya a sanyaye ya ce“bari na raka ka Abba” daga haka ya gyara riƙon da ya yi masa. Kasa cewa komai Abba ya yi har suka fice daga parlon.
Har ɗakinsa ya kai shi ya zaunar dashi kan gado sannan ya zare masa hular kansa ya ajiye gefe, Abba ya sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan ya jingina da jikin gado, ya lumshe idanunsa lokaci ɗaya hawaye suka fara sintiri akan fuskarsa. Shiru Abdusammad ya yi yana kallonsa cike da tausayawa, can kuma ya tsuguna a gabansa ya riƙe hannunsa jiki a sanyaye ya ce
“please Abba, kada ka damu kan ka, ni nayi maka alƙawarin zan dawo da Nana, zata dawo cikin aminci”
Dakyar ya iya buɗe idanun nasa, dan da gaske jikinsa ya yi sanyi sosai, ya dafa kan Abdusammad yana murmushi mai haɗe da hawaye ya ce
“me yasa ta yi haka Abdul? Why? Bata san halin da zan shiga ba, yau da safe na tashi da farin ciki, irin farin cikin da baya misaltuwa. Naji ni cikin annashuwa da nutsuwar zuciya saboda ina tunanin zan aurar da tilon ƴata wadda Allah ya bani matsayin amana.” Abba ya yi shiru saboda kukan dake neman tawo masa, ya numfasa sannan ya ci gaba da fad’in “sai dai sam ban yi tunanin Nana zata tafi ba, ban yi tunanin zata bari na tozarta idon duniya ba. I feel ashamed Abdul…na tursasa yara dayawa sun yi auren dangi, domin samar da al’umma mai kyau, sai dai ƴata dana haifa ta guji hakan. Na gayyaci mutane domin su tayani farin ciki sai dai yanzu ban san da wane idanu zan kallesu na ce musu an fasa auren Nana ba, na kuma faɗa musu cewa Nana ta gudu ta barni..” ya dakata saboda tarin daya turnuƙeshi. Abdusammad ya riƙe shi sosai yana hawaye shima ya ce“a’a Abba, dan Allah kada wani abun ya sameka”
Murmushi kawai Abba ya yi yana kallon enlargement ɗin hoton Nana dake maƙale a jikin bangon ɗakinsa, lokacin bata fi 3yrs ba, tana tsaye hannunta riƙe da teddy bear ta kwaɓe fuska kamar mai shirin kuka. Wasu zafafan hawaye ne suka shiga sakkowa kan fuskarsa, Ya lumshe idanunsa sannan ya sake buɗe su ya ce
“Ashe bani da rabon aurar da ɗiyata, haka Allah ya ƙaddara min, shiyasa ya bani Nana ita kaɗai”
Da sauri Abdusammad ya girgiza kansa ya ce“a’a Abba ya zaka ce haka? Me zai hana ka aurar da Nana? Nace maka zan dawo da ita”
Girgiza kai Abba ya yi cikin kuka ya ce
“To ko ta dawo wane zai aureta Abdul? Nobody! Babu wanda zai auri Nana! Babu mai iya aurenta”
Yanda ya yi maganar a mugun sanyaye shi ne ya ƙara bawa Abdusammad tausayi, gaba ɗaya Abba ya yi loosing hope. Agogon hannunsa ya kalla sai kuma ya ce“kaje domin kai ne a bigirena, just go”
Dakyar Abdusammad ya miƙe yana sake kallon Abba. Ganin haka yasa Abba yin murmushi ya ce“kar ka damu I’ll be fine. Just go”
Jiki a sanyaye ya juya ya fice daga ɗakin, Abba ya numfasa sannan ya kwanta a gefen gadon yana lumshe idanunsa.
A balcony ya tsaya ya goge hawayensa da hanky sannan ya nufi apartment ɗin Hajiya Babba kamar babu abin da ya faru. A zaune ya samu su Papa da angwayen dan haka ba’a tsaya sake ɓata lokaci ba aka gabatar da ɗaurin auren.
****
Tsaye suke jikin ƙarfen bene, Aliyu sai kallonsa yake ganin yanda ya yi shiru kamar me tunani. Ya numfasa sannan ya ce
“Buddy are you sure abin da ka yi shi ne daidai?”
Buɗe gajiyayyun idanunsa ya yi akan Aliyu sai kuma ya ɗauke kai yana kallon gefe, Aliyu zai sake magana Papa da Baba Lawan na Njomboli suka ƙaraso wajen, dafashi Baba ya yi cikin jin daɗi da farin ciki ya ce
“Allah ya yi maka albarka Abdusammad, ya sanya albarka cikin auren, tabbas abin da ka yi shi ne dai-dai. Kuma muna alfahari da kai”
Jinjina kansa ya yi jiki a sanyaye ya ce“Amin Baba. But ina jin kamar ban yi dai dai ba idan ya kasance ni ne na auri Nana, wallahi ban taɓa yi mata kallon wadda zan aura ba, ban taɓa kallonta matsayin mace bama. Kawai ganinta nake kamar ƴata, yanda zan yiwa Noor abu haka nake ganin zan yiwa Nana, ya zata ji idan aka ce mata ni ne wanda aka ɗaura mata aure dashi?”
Ya ƙare maganar da damuwa sosai akan fuskarsa
Dafashi Papa ya yi kafin ya ce“mun sani Abdusammad kuma abin da ka yi shi ne dai-dai. Ahmad ba zai manta da wannan abun ba, ka share masa hawayensa sannan ka fitar dashi kunyar jama’a. Gefe guda kuma ka wanke kanka akan aurenka na farko wanda ka yi bada yardar danginka ba. So you don’t need to be worry kaji”



