Chapter 24: Chapter 24
Shiru Abdusammad ya yi yana kallon Papa. Ya ɗan bubbuga kafaɗarsa sannan ya juya suka bar wajen. Harɗe hannayensa ya yi a ƙirji yana jin wani irin abu cikin ransa, mamaki da damuwa sun yi masa yawa, idan ya tuna cewa yanzu Nana matsayin matarsa take amsawa sai yaji gabansa ya faɗi.
“Ya rabb!”
Ya furta yana furzar da zazzafan numfashi daga bakinsa. Dafashi Aliyu ya yi ganin yanda ya damu yasa ya ce“Buddy ka daina damuwa kaji dan Allah. Always Allah’s plan is the best”
Kallonsa ya yi da gajiyayyun idanunsa ya ce“Buddy Nana fa. Nana fa”
“to mene a ciki?”
Ɗauke kansa ya yi yana kallon mutanen dake ta faman kai koma a compound ɗin sannan ya ce“ba zaka fahimta ba” taɓe baki Aliyu ya yi ya ce“da ka fahimtar dani ai” kallonsa kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba. Sultan ya ƙaraso wajen hannunsa riƙe da babbar rigarsa wadda ya daɗe da cirewa. A gefensu ya tsaya jiki a sanyaye ya ce
“Yaya”
Kallonsa Abdusammad ya yi ba tare da ya ce komai ba. Cike da damuwa Sultan ya ce“Yaya Nana fa? A ina za’a ganta?” numfasawa Abdusammad ya yi sai kuma ya dafa kafaɗarsa ya ce“za’a ganta kaji” daga haka ya kalli Aliyu ya ce“bari naje wajen Abba”
“muje tare”
Aliyu ya faɗa yana tattare babbar rigarsa. Ok ya ce sannan ya yi gaba Aliyu ya bi bayansa. Sultan ya jima tsaye kafin ya sauke numfashi ya nufi hanyar apartment ɗinsu.
****
Fitowa ta yi daga kitchen hannunta riƙe da plate tana murmushi ta kalli su Aunty Khadijah dake ta faman dariya ta ce“yau dai murna har kunne” Aunty Khadijah ta gyara zamanta tana kallonta ta ce“ai yau ko bacci ban jin zamu iya. Wannan abu. Kai Allah na gode maka”
Ta ƙare maganar tana ɗaga hannunta sama alamar godiya ga Allah. Murmushi Zahra ta yi bayan ta zauna ta ce“amma tafiya zaku yi ko? Tun da kun ga yanzu ku surukai ne” jinjina kai Siyama ta yi ta ce“eh fa Aunty. Gara mu tafi, to amma ke naga baki damu ba”
Taɓe baki Zahra ta yi ta ce“akan me zan damu to? Yarinyar da aka aura masa bagidajiya ce, ke bayan haka ma anan zata zauna mu kuma US zamu koma. To kin ga ba zan kirata kishiyata ba ai”
Gyaɗa kansu suka yi sai kuma Aunty Khadijah ta dafata ta ce“koma tare zamu zauna ai ba zamu bari ta yi nasara akan ki ba. Mu da muke da malamai” shiru Zahra ta yi can kuma ta janye hannunta daga jikinta ta ce“a’a Aunty ni babu ruwana da bin malamai ko bokaye. Kawai dai na san ba zata zama kishiyata ba” ta ƙare maganar tana haɗe rai. Murmushi kawai Aunty Khadijah ta yi dan ita yanzu bata da wata damuwa. Safeena da ke zaune tun ɗazu ba tare da ta ce komai ba saboda takaici ta miƙe tana ɗaukan jakarta ta ce“ni zan yi gaba”
“ba zaki bari mu tafi tare ba?”
Amal ta tambayeta da mamaki. Gyaɗa mata kai Safeena ta yi fuska babu walwala ta ce“a’a tafiya zan yi, ni ba zan zauna ba” daga haka ta juya ta nufi hanyar fita daga parlon. Taɓe baki Siyama ta yi ta ce“ni na rasa abun da ke damunta wallahi.” Aunty Khadijah ta bita da harara sannan ta ce“Allah ya raka taki gona”
Suka tuntsire da dariya a tare. Ban da Zahra wadda lokaci ɗaya taji lamarin auren ya dameta.
****
Tura ƙofar ɗakin ya yi bakinsa ɗauke da sallama, cikin tashin hankali ya ƙarasa gaban gadon ya dafashi yana faɗin
“Subhanallahi. Abba! Abba!”
Ya ɗago shi ya jingina shi da jikinsa, ban da tari babu abin da Abba ke yi, idanunsa a rufe jikinsa sai wani irin rawa yake. Aliyu ya ƙaraso ciki hankali tashe ya ce
“mene ne? Me ya same sa?”
Girgiza kai ya yi bayan ya miƙe riƙe dashi ya ce“i don’t know bari muje asibiti” daga haka ya fice daga parlon da sauri. Aliyu ya dafe kansa a sanyaye ya ce“Ya Allah” sannan yabi bayansu da sauri.
A hankali ta fara buɗe idanunta wanda suka yi mata nauyi, ta dinga kallon ɗakin da take kwance, Lokaci ɗaya kuma ta tashi zaune a ɗan firgice. Da sauri Mama ta riƙeta tana faɗin
“kin tashi”
Amma ta dinga kallonta, can kuma ta saki wani kuka tana fadin “Mama Nana, me ya sa Nana zata yi haka? Wane ne wanda ta yarda dashi haka! Mama zuciyata zafi take min. Innalil lahi wa ina ilayhi raji’una”
Amma ta yi maganar tana sake rushewa da wani kukan. Sake riƙeta Mama ta yi cike da tausayinta ta ce“yi haƙuri Rabi’ah, ki yi haƙuri dan Allah” cikin kuka ta kalli Mama ta ce“to ina take? Yanzu shikenan ba zata yi aure ba? Babu wanda zai aureta. Wallahi ban bar Nana tana fita ban sani ba, ban santa da yawo ba, ban san yaushe haka ta faru ba. Iya kar ƙoƙarina ina yi akan tarbiyyarta. amma me yasa? me ya sa zata yi mana haka? Me yasa zata yi fatali da tarbiyyar da muka bata..”
Mama ta yi shiru tana sauraren sautin kukanta. Ta san tabbas ba ƙaramin abu ne, ba abu ne wanda zuciya zata iya dauka ba, ace yarka daka haifa aka samu da irin wannan ƙazaman hotunan. Garin ya ya? wane ya yaudari Nana har ta yarda dashi haka?. Mama ta sauke numfashi sai kuma ta mai da idanunta kan Amma a sanyaye ta ce
“ki bar zubar da hawayenki, domin shi ɗin masifa ne gareta. Addu’a zaki yi mata, kuma ki yi mata fatan Alkhairi”
Amma ta jinjina kanta wasu hawayen na sake zubowa ta ce“ina son na ganta. Ina son naga Nana Mama, ina so na tambayeta meyasa ta yiwa rayuwarta haka? ina son ta faɗa min dalilinta na tafiya ta bar mu. Ina son na ganta Mama…” ta sake fashewa da wani raunataccen kukan tana ɗora kanta a cinyar Mama. Kasa cewa komai ta yi dan tasan dole ta yi kuka, ta dinga shafa bayanta a hankali.
****
Ana kiran sallar la’asar Ummi ta shigo ɗakin, ta dinga kallonta ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita. Tun bayan da aka gama ɗaurin aure bata yi shiru ba, dan haka ta saki ƙofar ta ƙarasa ciki tana ci gaba da kallonta. Zama ta yi gefen gadon ta riƙo hannayenta a sanyaye ta ce
“Maimoon”
Ɗago kanta ta yi a hankali tana kallon Ummi, gaba ɗaya idanunta sun kumbura sun yi jajur dasu. Har wani janyewa sukayi saboda azabar kuka, Ummi ta girgiza kanta sai kuma ta shiga share mata hawayen tana faɗin
“kukan ne har yanzu? me ki ke wa kuka kuma?”
Samun kanta ta yi da faɗawa jikin Ummin ta sake fashewa da wani sabon kukan, Ummi ta dinga kallonta ba tare da ta ce komai ba. Above 5mins kafin ta fara rage sautin kukan dan kanta. Sai a sannan Ummi ta ɗagota tana murmushi ta ce “Shikenan ya isa haka, ki tashi ki yi wanka ki ci abinci, sai ki je apartment ɗin Hajiya Babba”
Gyaɗa mata kai kawai Maimoon ta yi dan ita sam ba wannan ne ya dameta ba. Ummi ta tashi tana cewa“bari na kawo miki abincin” da sauri ta mike ita ma tana ƙoƙarin yafa mayafinta ta ce“a’a zan je gurin Hajiya Babba” Ummi ta yi shiru can kuma ta ce“abincin fa?”
“na ƙoshi”
Ta ce a sanyaye. Ummi bata sake cewa komai ba barta ta fita, dan ta san daman ba lallai bane ta iya cin abincin a sannan.
Tafiya ta dinga yi tana kuka, ta rufe fuskarta da mayafin kanta ko gabanta bata gani. Ji ta yi an riƙeta tayi saurin ɗago kanta ba tare da ta buɗe idanun nata ba, Aliyu ya dinga kallonta ganin tana shirin faɗuwa. Hannunsa ya sanya ya janye mayafin ya dawo goshinta, sai a sannan ta kalli fuskarsa, ta yi saurin sunkuyar da kanta. Kallonta ya dinga yi can kuma ya ce
“ki kula kar ki faɗi”
Gyada masa kai kawai ta yi ya saketa ta yi gaba da sauri. Da idanu kawai ya bita sai kuma ya juya ya nufi inda ya yi parking motarsa dan komawa asibitin.
Ta ƙofar wajen kitchen ta shiga gudun kada ta haɗu da mutane, sai dai ga mamakinta Safwan ta gani tsaye a wajen ya jingina da jikin flowers da alama tunani yake yi. Ta dinga kallonsa cike da tsana sai kuma ta juya zata bar wajen, kamar daga sama taji ya ce
“Maimoon!”
Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya ƙaraso gabanta ya tsaya ba tare da ya ce komai. Ganin mintuna biyu sun shuɗe bai yi magana ba ya sanya ta ratsa ta gefen shi zata shige, ya yi saurin riƙe hannunta kafin ya ce
“Wait pls!”
Tsayawa ta yi har sannan bata kalleshi ba, ya numfasa sannan ya ce“na san zaki ce ban yi dai dai ba. Wallahi babu yanda na iya ne Maimoon, ban so na faɗawa kowa ba, amma ina son Siyama, ina son na aureta. Ba zan iya bari na rasata ba, kin ga…”
“Ya isa haka Ya Safwan! Ya isa!”
Maimoon ta faɗa a mugun tsawace, wanda ya tilasta shi yin shiru ba tare da ya gama faɗar abin da ke bakinsa ba. Ta dinga wani irin huci hawaye na zubowa kan farar fuskarta, lokaci ɗaya kuma ta cakumeshi cikin ɓacin rai ta fara faɗin
“Kai mugu ne! Kai azzalumi ne Yaya Safwan! Ka cuceta. Ka cuci rayuwarta! Wallahi ko wanda ya sanya aka yi hotunan na bai kai ka lefi ba. Akan me zaka yaudareta? Akan me zaka sa ta bar gida? Akan me zaka yi mata alƙawarin rufe sirrinta sannan kuma ka buɗashi a gaban kowa? Me ya sa zaka tozarta ta?. Me ya sa? Me yasa Yaya Safwan?”
Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi. Kasa magana Safwan ya yi, sai hawaye da yake zubowa daga idanunsa. Har sannan Maimoon na rike da kwalar rigarsa. Suka dinga kuka a tare kamar ƙananun yara, shi kansa bai san dalilin daya sanya ya fito da hotunan ba, dan bai manta alƙawarin da ya yiwa Nana ba. Bai manta sanda ta tsaya a gabansa ba tana kuka ta ce
“Yaya Safwan zan tafi, zan haƙura da komai. Zan bar gidan nan kuma ba zan sake dawowa ba, zan tafi kamar yanda kace, zan ɗorawa kaina laifin cewa ni ce bana son aurenka. Amma dan Allah, dan Annabi kada ka bari kowa ya ga hotunan, ka ƙonasu kamar yanda kace, kada ka bari Abbana ya gani, kada ka bari dan Allah…”
Ta ƙare maganar tana durƙushewa a gabansa. Safwan ya runtse idanu yana jin wani irin zafi a zuciyarsa, da gaske bai kyauta mata ba, da gaske ya yaudareta. Yanzu kowa laifinta yake gani, ya cutar da rayuwarta. A ina zai ga Nana ya nemi gafararta? Me ya sa bai tambayi inda zata je ba?.
Sakinsa Maimoon ta yi ta ɗauki mayafinta wanda ya faɗi ta juya zata bar wajen, da sauri ya sake biyota yana cewa
“Kin san inda Nana ta tafi?”
Kamar ba zata kulashi ba sai kuma ta juyo tana kallonsa ta ce“mene ne abun da ya shafeka da inda ta tafi? ko zaka bita can ne ka dawo da ita domin kowa ya tsaneta?” girgiza kansa ya yi a sanyaye ya ce“a’a zan bata haƙuri ne”
Da wani mamaki Maimoon ta dinga kallonsa, can kuma ta girgiza kanta ta ce“haƙuri? haƙuri zaka bata saboda ka cuceta? to wallahi koda na san inda Nana take ba zan taɓa faɗa ba! Ba zan bari kowa ya sani ba!”
Daga haka ta juya ta bar wajen a fusace kamar zata tashi sama. Safwan ya bita da kallo zuciyarsa cike da damuwa.
****
Around 5:00 na yamma ta fito daga kitchen ɗin hannunta riƙe da wata ƙatuwar warmer, ta ajiye akan table sannan ta ɗauki mayafinta da ke kan sofa ta yafa, sai baza ƙamshi take. Ta ɗauki warmer ta fito daga apartment ɗin kai tsaye kuma apartment ɗin Hajiya Babba ta nufa.
Zaune ta samu mutane ana ta hira, Hajiya Babba na zaune kan sofa two seater ita da Atta. Jiki a sanyaye ta ƙarasa ciki dan sam bata ji daɗin ganin Attan ba, ɗaya bayan ɗaya ta dinga gaisar da mutanen parlon, suka amsa cikin fara’a sannan ta tsuguna gaban Hajiya Babba ta gaisheta itama. Fuska a sake ta amsa mata, ta kalli Atta ta gaisheta. Ciki-ciki ta amsa tana ɗauke kai, Zahra bata damu ba dan daman ta san haka zata yi ta mai da kallonta ga Hajiya Babba ta ce“hajiya daman abinci na kawo miki” ta tura mata warmer. Murmushi Hajiya Babba ta yi ta ce“tom nagode Fatima” Zahra ta murmusa sannan ta mike tana shirin fita. Ɗaya daga cikin matan da ke zaune ta kalleta sai kuma ta kalli Hajiya Babba ta ce
“au wannan ce matar tasa ta farko?”
Kafin Hajiya Babba ta yi magana Atta ta yi saurin faɗin “ita ce. Yaje ya auro bare, to da Allah yasa yanzu ya wanke kansa ya auri yar danginsa. Abun nan ya min daɗi, daman can ni ina nake son ya aura wallahi, sai dai aka fi ƙarfina ashe dai rabonsa ce. Yarinya yar dangi ga kyau ga diri” Atta ta ƙare maganar rai a sake. Murmushi duka suka yi banda Hajiya Babba, Zahra ma na tsaye dan ta kasa tafiya, Ɗaya bafulatanar ta ce
“oh naganeta, yarinyar ita ce wadda suka zo ruga tare ko? Ai daman aradu sun dace da juna. Ni na ɗauka ma a sannan ɗin matarsa ce”
Atta ta girgiza kanta ta ce“a’a sannan bai aureta ba, ai ni gara da Allah yasa aka yi haka ma. Dan da ya auri Haule gara Nanar”
Wani irin abu ne ya zo ya tokarewa Zahra a ƙirji, ta juyo tana kallon Atta a firgice. Kasa ɓoye tashin hankalinta ta yi bakinta na rawa ta ce
“Hajiya… Atta me ki ka ce?”
Tsuke fuska Atta ta yi ta ce“cewa nayi gara daya auri Nanar!”
A mugun firgice ta dawo gaban Atta, ta zube tana kallonta bakinta na rawa ta ce
“Babba…ban gane ba, wa ya aura? wa Doctor ya aura Atta?”
Atta ta bata amsa kai tsaye. Wani irin zaman yan bori Zahra ta yi a wajen, ta dinga kallonta hankali tashe, nan take hawaye suka fara zubar shar daga cikin idanunta. Sam ta kasa gane abin da Atta ke nufi, ta kasa gazgata maganarta. Dan haka ta rarrafa gaban Hajiya Babba ta dafata cikin wani irin yanayi wanda yafi kama dana tashin hankali ta ce
“Hajiya bangane me Atta ta ce ba. Wa Doctor ya aura?”
Dafata Hajiya Babba ta yi babu yabo babu fallasa ta ce“Naanah ya aura, ɗiyar Ahmad.”
Wani irin abu ne ya zo ya tokarewa Zahra a ƙirji, ta kasa koda haɗiyar yawu sai kallon Hajiya Babba take. Can kuma ta sake cewa“Hajiya daman ba Haule zai aura ba? Daman Naanah zai aura?”
Girgiza kai Hajiya Babba ta yi kafin ta ce“Eh Haule zai aura. Amma saboda matsalar da aka samu ya sanya ya fasa auren Haule, aka maye gurbinta da Naana. Ita kuma Haule ta auri Safwan da kuma ƙanwarki!”
Shiru Zahra ta yi tana tunani, gaba ɗaya sai taji kamar mafarki take wanda zata farka taga babu abin da ya faru. Ta dinga sauke numfashi da sauri da sauri hawaye na biyo kuncinta, ganin yanda jikinta ya yi sanyi ya sanya Hajiya Babba cewa“tashi ki je. Idan ya dawo sai ya miki bayani yanda zaki fahimta” kasa cewa komai ta yi, ta miƙe da kyar tana dafe kanta saboda sara matan da ya yi, a daddafe kuma ta fice daga parlon. Atta ta bita da harara sannan ta ce“ai daman ni na san ba son auren zata yi ba! Kuma babu yanda ta iya wallahi. Idan bata yi wasa ba ma sai ya saketa” kallonta kawai Hajiya Babba ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ta sauke numfashi a sanyaye ta ce
“Allah ya kyauta”
****
Zahra na komawa apartment ɗinta ta haye sama da sauri, daƙinta ta shiga ta rufe ƙofar sannan ta fara dialing numbern Aunty Khadijah hannunta na rawa. Ringing ɗaya ta ɗauka, kafin ta yi magana Zahra ta yi saurin cewa
“nashiga uku aunty, na shiga ukuna!”
Da mamaki Aunty Khadijah ta ce
“Lafiya dai Zahra?”
Cikin kuka Zahra ta ce“ya aureta! Wallahi ya aureta Aunty. Ya zan yi da raina? Taya zan jure ganin Nana matsayin matar mijina? Nana fa aunty!”
Aunty Khadijah da bata gane inda zancen ya dosa ba ta ce
“kin ga Zahra nutsu ki min bayani. Wace ya aura? Kuma wane ki ke magana akai?”
Girgiza kai Zahra ta dinga yi cikin tashin hankali ta ce
“Nanah mana! Doctor ya auri Nana, ashe da ita aka ɗaura masa aure ɗazu.”
A firgice Aunty Khadijah ta tashi daga zaunen da take ta ce
“what?!”
Zahra ta gyaɗa mata kai kamar tana gabanta. Cikin shessheƙar kuka ta ce
“Eh Aunty. Wallahi ita aka aura masa, yanzu Nana ce kishiyata, wayyo Allah na zuciyata aunty, wallahi ba zan iya ba. Mutuwa zan yi Aunty”
Ta ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka.
Shiru Aunty Khadijah ta yi tana ayyana irin abin da zasu yi, jin yanda Zahra ke kuka kamar ranta zai fita yasa ta yi ƙasa da murya ta ce
“Ya isa haka Zahra. Zaki iya fitowa yanzu?”
Girgiza kanta ta yi ta ce“a’a ba zan iya ba wallahi”
Aunty Khadijah ta sauke numfashi sannan ta ce
“tom shikenan. Ki bari gobe da safe zan zo sai mu san yanda zamu yi Kinji, ki daina kukan”
Shiru Zahra ta yi tana shessheƙar kukanta. Aunty Khadijah ta sake ƙasa da murya cikin sigar rarrashi ta ce
“ki yi haƙuri kin ji. Ki ɗauka kamar ba’a miki kishiya ba, in dai ina da rai ba zan bari yarinyar nan ta tare ba”
Zahra ta gyaɗa kanta a sanyaye ta ce“tam Aunty.”
Jin ta kwantar da hankalinta ya sa ta sake cewa“to ki daina kukan, ki share hawayenki”
To kawai Zahra ta ce sannan suka yi sallama. Ta wurgar da wayar tsakiyar gado sannan ta durƙushe a wajen tana fashewa da wani sabon kukan, idan ta tuna yanzu ita da Nana suna ɗaya suke amsawa sai taji zuciyarta ta tsinke.
****
Tsaye suke a ward ɗin asibitin kowa ya yi jigum-jigum, Sultan ne ya fito hannunsa riƙe da wata takarda ya ƙaraso wajen, da sauri Abdusammad ya ƙarasa wajensa ya amshi takardar without say anything. Warware ya yi ya karanceta tas sai kuma ya ɗago kansa cike da damuwa ya ce
“Ya jikin nasa to?”
Numfasawa Sultan ya yi kafin ya ce“da sauƙi za’a ce. But har yanzu bai farfaɗo ba”
Miƙa masa takardar ya yi sai kuma ya nufi ɗakin da aka kwantar da Abban.
Kwance ya sameshi idanunsa a rufe yana sauke numfashi a hankali da taimakon na’urar da aka saka masa. Abdusammad ya riƙe hannunsa na dama yana jin zuciyarsa sam babu daɗi. Abba na ɗaya daga cikin mutanen da ya fi ƙauna a duniya, idan ka cire Hajiya Babba babu wanda ya kewa kallon mahaifi sama da Abba, he’s not just his father but a friend. Yanda suke zama su yi hira da Abba koda Hajiya Babba baya yi, dan haka ganinsa cikin wannan halin babu abin da yake face tada masa hankali. Idan kuma ya tuna Nana ce sanadiyyar wannan abun sai yaji zuciyarsa ta sake ɓaci, sai yaji dama ya bar nan yaje ya dawo da ita gida ya nuna mata kuskuren abin da tayi. Furzar da zazzafan numfashi ya yi daga bakinsa still looking at Abba’s face.
Ƙarar na’urar da yaji ce ta sanya shi gyara tsaiwarsa, ya dinga kallon Abba wanda yake ƙoƙarin buɗe idanunsa. Da sauri ya zauna a gefen shi har sannan yana riƙe da hannunsa ya ce
“Abba!”
A hankali Abba ya buɗe idanunsa wanda suka yi jajur dasu, ya kalli Abdusammad sai kuma ya sake rufesu. Jiki a sanyaye Abdusammad ya ce
“Abba ka yi haƙuri dan Allah, kar ka damu kan ka kaji”
Shiru Abba ya yi kamar ba zai magana ba can kuma ya ce.
“Abdul”
“Na’am Abba”
Ya amsa kamar zai yi kuka. Numfasawa Abba ya yi ya sake buɗe idanunsa akansa, a hankali kuma ya kai hannunsa na hagu wanda aka maƙala masa canola ya shafa fuskarsa yana murmushi ya ce
“karka damu kaji, I’m fine”
“you are not Abba. Kalleka fa, baka da lafiya Abba, dan Allah ka daina damuwa kaji. I’m promise, I already promised cewa zan dawo da Nana. Zata dawo gida Abba!”
Ya yi maganar hawaye na kawowa cikin idanunsa.
Lumshe idanu Abba ya yi wanda ya bawa hawayen dake cikin idanunsa damar sakkowa kan fuskarsa, ya girgiza kansa a sanyaye ya ce
“bana son ganin Nana Abdul. Bana son ta dawo, just leave her, bana son na sake ganinta har abada!”
Da wani irin mamaki Abdusammad ke kallonsa, lokaci ɗaya ya shiga girgiza kansa kafin ya ce
“a’a Abba. A’a, zaka sake ganinta, zata dawo gida. Komai zai shige kamar bai faru ba”
Shiru Abba ya yi yana kallon gefe, dan ko kaɗan baya son magana akan Nana. Idan ya tuna ta zuciyarsa zafi take masa, dan haka ya fawallawa Allah komai zai kuma manta da ita, duk da ya san hakan ba ƙaramin abu bane.
A tare suka shigo ɗakin bakinsu ɗauke da sallama, Abdusammad ya amsa a sanyaye dan babu lallai ma sun ji. Papa ne ya tsaya a gefensa a sanyaye ya ce
“Ahmad!”
Ɗago kansa ya yi ya kalleshi sai kuma ya sakar masa murmushi, Papa mai yi mamakin haka ba dan ya san halin Abba, da wuya ka gane halin da yake ciki. Da wuya ka gane asirin zuciyarsa, duk abin da ya kai shi ga barin a gane damuwarsa to ba ƙaramin abu bane, yana da zurfin ciki fiye da tunani, wannan dalilin ya sanya Nana ta yi gadonsa. Baka taɓa jin damuwarsu cikin sauƙi.
Murmushin Papa ya mayar masa kafin ya ce
“stop pretending Ahmad, ya jikin naka?”
Lumshe idanunsa ya yi ya buɗe ya ce“Alhamdulillahi”
Papa ya jinjina kansa sannan ya ce“Allah ya ƙara sauƙi, ya kuma kiyaye gaba”
Amin duka suka ce. Sannan suka yi masa ya jiki suma, ya amsa a sanyaye.
Kallon Sultan ya yi wanda ke tsaye kusa da Hamid ya ce
“Sultan zamu iya tafiya gida ko?”
Girgiza kai ya yi ya ce“a’a Abba. Har yanzu baka da lafiya fa, kawai kana daurewa ne, ba za’a iya sallamarka ba”
Abdusammad ya jinjina kai ya ce“Eh. Sai ka samu sauƙi sosai Abba”
Shiru Abba ya yi yana kallonsu sai kuma ya ce
“Alright but you have to go, Kun bar matayenku a gida”
Girgiza kai Hamid ya yi ya ce“idan muka tafi kai fa Abba?”
Murmushi kawai ya yi sai kuma ya ce“ba komai. Ku je kawai”
Girgiza kai Abdusammad ya yi ya ce
“A’a ku kawai ku tafi. Zan zauna dashi”
Da sauri Abba ya kalleshi sai kuma ya girgiza kansa ya ce“a’a ku je duka”
Shiru Abdusammad ya yi dan ba tafiyar zai ba. Papa ya ce su tafin tun da jikinsa da sauki, suka yi masa sallama sannan suka tafi.



