⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 25: Chapter 25

A can estate kuwa, Amma ce zaune gefen gado Aunty Ramlah na gefenta sai kuka take ƙasa-ƙasa. Aunty Ramlah ta sauke numfashi sannan ta ce

“Dan Allah Yaya ki yi haƙuri. Kaddara ce kuma ta riga da ta faru, babu wanda zai sauya hakan, ki yi haƙuri kin ji”

Cikin kuka Amma ta ce

“Ya zan yi na yi haƙuri Ramlah? Nana fa bata nan. Kuma kin ga hotunan da ake dangatawa da ita, har mahaifinta ya yarda. Ya za’a yi na samu natsuwa, ina so naga Nana, ina son na tambayeta ta faɗa min gaskiya”

Dafata Aunty Ramlah ta yi tana jin wani irin tausayin ƴar uwar tata ta ce“ki yi haƙuri Yaya. Na sani abu ne mai wahalar yarda amma ki sani duk abin da ki ka ji ko kika gani to gaskiya, don nima kaina na san yaron”

Da sauri Amma ta kalleta sai kuma ta riƙe hannayenta duk biyun cikin kuka ta ce

“Da gaske? Kin san shi Ramlah?”

Gyaɗa mata kai Aunty Rahmah ta yi. Amma ta matse hannayenta ta ce

“to kai ni wajensa dan Allah, kai ni na tambayeshi meyasa zai yiwa Nana haka. Kai ni na tambayeshi ina ƴata take!”

Kasa masa Aunty Ramlah ta yi sai kuka da take a hankali, ta rungumeta cikin shessheƙar kuka ta ce

“Ki yi shiru Yaya, in sha Allah komai zai shige”

Amma bata sake cewa komai ba sai kuka da take a hankali.

****
No. 045 Sultan road,
Kano State.

A hankali ta tura ƙofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama, Zaune ta same su gefen gado. Ta ƙarasa ciki tana kallonsu, Babbar mata ce da zata yi kaiwa 50 to above ɗin nan, fara mai ɗan jiki. Ta zauna ɗan nesa dasu har sannan idanunta na kan su,ganin yanda suka riƙe hannun juna sai kuka suke a tare. Ta ɗan numfasa sannan ta ce

“Nana”

A hankali ta ɗago idanunta ta kalleta, Mami ta yi mata alamar da ta zo da hannu, ta saki hannun Khadijah sannan ta tashi a hankali ta ƙarasa gabanta. Zama ta yi gefenta, Mami ta jata ta rungumeta tana shafa kanta, Ji tayi kamar a jikin Amma take dan haka ta sake fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Mami ta yi shiru ba tare da ta hanata ba. Khadijah sai kallonsu take tana kukan itama.

Above 5mins kafin ta ɗago kanta jin har sannan bata daina kukan ba, ta goge mata hawayen duk da wasu basu bar zuba ba ta ce

“Ya isa haka Nana. Kar wani abun ya sameki”

Sake shigewa jikinta ta yi cikin kuka ta ce

“Mami Ammata, Abbana.”

Sosai ta bawa Mami tausayi dan tun da ta zo babu abin da take cewa daya shige wannan. Ta shafa kanta a sanyaye ta ce

“Zaki koma kin ji, zasu ganki”

Girgiza kanta ta dinga yi tana cewa

“A’a Mami, ba zan iya ba. Ba zan iya komawa wajensu ba, na tozarta Abbana! Na wulaƙantashi gaban mutane, na san yana can hankalinsa a tashe. Gara na mutu Mami! So nake na mutu!”

Ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan. Kasa cewa komai Mami ta yi, dan ta san ko ta faɗa mata ba zata fahimta ba yanzu. Ita kanta bata ji daɗin guduwar da ta yi ba, sai dai idan ta tuna abin da ta faɗa mata sai taji sam bata da nutsuwa. Sai taji gara da ta bar gidan akan rashin son aure da ace an fitar da irin hotunan wanda zasu iya tarwatsa zuciyar duk wata uwa ko uba. Ganin ta fara rage kukan yasa ta ɗagota ta ce

“Ya isa haka tashi ki ci abinci sai ki kwanta” girgiza kanta ta yi ta ce“na ƙoshi Mami”

Mami ta yi shiru tana kallonta,can kuma ta mike tana kallon Khadijah ta ce“zo ki karɓar muku abinci” a sanyaye ta ce to sannan Mami ta fita. Ta tashi ta dawo gefen Nana ta riƙe hannunta cikin kuka ta ce

“Nana ki daina kuka kinji. In sha Allahu sai Allah ya saka miki”

Tari ta fara yi tana dafe saitin zuciyarta, lokaci ɗaya ta nemi fita daga hayyacinta. Da gudu Khadijah ta tashi ta fita tana kwalawa Mami kira, Mami dake tsaye a corridor ita da Adeel ta kalleta da mamaki ta ce

“Mimi lafiya?”

Girgiza kanta ta yi tana nuna mata hanyar dakin ta ce“Nana! Nana Mami”

Da sauri Mami ta yi hanyar ɗakin, Khadijah ta jawo Adeel da ke tsaye ta ce“Yaya zo muje kai ma”

Bai mata musu ba ya bi bayanta suka nufi ɗakin.

Tsaye suka tarar da Mami gabanta ta riƙeta ganin yanda take aman jini, suna shigowa ta kalleshi hankali tashe ta ce“Adeel zo ka ɗauketa mu kaita asibiti”

Shi kansa sai da hankalinsa ya tashi, ya dinga kallonta ganin how weak she’s yasa ya ƙaraso ya ɗauketa sannan ya yi waje da ita da sauri.

****
Washegari da sassafe around 8:00 Aunty Khadijah ta shigo parlon, zaune ta samu Zahra ta zuba uban tagumi. Kayan jiya ne a jikinta. Ta ƙarasa ta zauna kujerar dake facing tata tana kallonta ganin yanda ta fice hayyacinta, gaba ɗaya ta zama kamar ba ita ba, fuskarta ta wani irin zugewa. Idanunta sun kumbura, har wata ramar tashin hankali ta yi daga jiya zuwa yau, musamman daya kasance babu kowa a gidan dan tun jiya take zaune jiran Abdusammad ya shigo amma babu shi babu alamarsa. Noor kuma tana apartment ɗin Hajiya Babba. Numfasawa Aunty Khadijah ta sai kuma ta girgiza kanta ta ce

“Zahra! Zahra!”

Shiru babu amsa, dan babu alamar ma taji shigowarta. Dan haka ta taso ta dawo inda take ta zauna sannan ta ɗan jijjigata ta ce

“Zahraaa!”

A firgice ta kalleta, sai kuma ta sauke numfashi ta ce

“Aunty”

Kallonta Aunty Khadijah ta yi ganin duk ta birkice kanta ta ce

“mene ne haka? Ba cewa nayi ki bar damuwa ba?”

Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da fingers ɗinta lokaci ɗaya kuma wani kuka ya tawo mata, ta dinga rerashi ba tare da ta ce komai ba.

Kusan mintuna biyar kafin Aunty Khadijah ta ce

“yanzu kukan za ki ci gaba ko kuma shiru zaki yi mu san abin yi?”

Kallonta Zahra ta yi sai kuma ta fara share hawayenta da hannunta ta ce“na kasa haƙura ne aunty. Zuciyata ta kasa jurewa, ji nake kamar ba gaske ba, ji nake kamar zuciyata zata fito daga ƙirjina. Ya zan yi aunty?”

Dafata Aunty Khadijah ta yi sai kuma ta ce

“Dole akwai abin da zamu yi. Ba dai yarinyar bata gidan nan ba yanzu?”

Gyaɗa mata kai Zahra ta yi, ta numfasa ta ce

“To ba zamu bari ta dawo ba. Ta tafi kenan!”

Da mamaki Zahra ke kallonta sai kuma ta ce

“amma Aunty ban fahimceki ba.”

Dan murmushi Aunty Khadijah ta yi ta ce

“Cewa nayi ba zata dawo gidan nan ba. Koma ina ta tafi ba zamu bari ta dawo ba, ballantana har ta tare a matsayin kishiyarki”

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“ni dai babu ruwana Aunty, kada ki saka a yi mata wani abun. Babu ruwana wallahi!”

Tsaki Aunty Khadijah ta yi ta miƙe tsaye tana kallonta ta ce

“Ke daɗina da ke ba’a iya miki. Ina ƙoƙarin yin abin da zai taimakeki amma ke bakya gani, to sai me idan an yi mata asirin? Le dai ba burinki ta rabu da mijinki ba?”

Tashi itama Zahran ta yi tana kallonta ta girgiza kanta ta ce

“Ni ba ina nufin a cutar da ita bane. Kawai dai bana son ta zauna matsayin kishiyata, amma wallahi ba zan iya saka hannu cikin sake cutar da ita ba!”

Harararta ta yi ta ce“to ai sai ki yi ta yi, kina nan kuwa zata rabaki da gidan da ki ke taƙama dashi!”

Tura baki Zahra ta yi tana kallon wani wajen ta ce“ni dai babu ruwana!”

Aunty Khadijah bata sake saurarenta ba ta ƙarasa ta ɗauki jakarta inda ta ajiye ta yi waje fuuu. Sai da taga ta fita sannan ta koma ta zauna kan sofa ta fashe da kuka, ita sam bata da niyyar sake cutar da Nana. Amma ba zata iya zama da ita matsayin kishiya ba.

Tana nan zaune tana kuka aka buɗe parlon, ta ɗago kanta da sauri ganin wanda ya shigo. Sanye yake da kayansa na jiya sai dai babu babbar rigar, ta dinga kallonsa ganin yanda ya fice hayyacinsa. Kallo ɗaya ya yi mata ya nufi sama da sauri, ta bi shi da idanu sai kuma ta tashi tabi bayansa da sauri.

Tsaye ta same shi a tsakiyar ɗakinsa, ya zare rigar jikinsa sai fara singlet a jikinsa. A hankali ta saki ƙofar tana kallonsa, Ta ƙarasa gabansa muryarta a sanyaye ta ce

“Doctor”

Kallonta ya yi sai kuma ya ce“na’am”

Ƙoƙarin magana take amma ta kasa, sai rawa bakinta yake. Ya ɗan kalleta sai kuma ya ce

“I want to take shower”

Gyada masa kai ta yi hawaye na biyo kuncinta. Ya nufi toilet ba tare da ya sake kallonta ba, da idanu Zahra ta bi shi sai kuma ta zauna kan kujerar dake ɗakin, lokaci ɗaya ta haɗe kanta da gwuiwa ta fashe da kuka. Tana nan zaune har bayan mintuna ashirin ya fito daga toilet ɗin yana goge kansa da towel, Ya kalleta sau ɗaya sai kuma ya nufi wajen dresser tashi. Cikin yan mintuna ya shirya cikin wasu kananan kaya t-shirt fara da jeans blue colour. Ya gyara sumar kansa sai sheƙi take, turaren arabian oud ya fesa sannan ya dauki wayarsa yana shirin fita. Zahra na ganin haka ta mike da sauri bakinta na rawa ta ce

“Dd… Doctor!”

Cak ya tsaya lokaci ɗaya kuma ya juyo yana kallonta. Sunkuyar da kanta ta yi ganin yanda fuskarsa take babu alamar walwala. Ya gyara tsaiwarsa yana kallonta sosai ya ce

“Ina ji”

A sanyaye ta ce

“Daman i just want to ask you ne”

Gyaɗa mata kai ya yi ya ce

“uhm..”

Ta ɗan numfasa tana ƙoƙarin riƙe kukanta ta ce

“wai da gaske ka auri Nana?”

“Eh”

Ya bata amsa kai tsaye, Durƙushewa Zahra ta yi a wajen, ta haɗe hannayenta duk biyun alamar roƙo ta ce

“Dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri. Kada ka aureta doctor, ka rufa min asiri, wallahi ba zan iya zama da Nana matsayin kishiya ba. Ba zan iya ba doctor, na san baka sonta! Na san dole aka maka, ba yin kanka bane!”

Ban da kallonta babu abin da Abdusammad ke yi, sam babu alamar damuwa akan fuskarsa. Ya yi mata alama data tashi, babu musu ta mike tana kuka har sannan. Furzar da numfashi ya yi kafin ya ce

“Ki yi haƙuri!”

Ya yi maganar yana juyawa, ganin ya fice daga ɗakin yasa Zahra sake fashewa da wani kukan, lokaci ɗaya kuma ta bi bayansa da gudu, a parlon ta same shi yana shirin fita. Cikin kuka ta ce

“Kana nufin zaka zauna da ita? Zaka haɗa zuri’a da ita? Yarinyar da aka tabbatar da bata da tarbiyya! Yarinyar da kowa yaga hotunanta da namiji? Yarinyar da ke bin maza!”

Ta yi shiru tana girgiza kanta, sai kuma ta tako har gabansa ganin bai ko motsa ba. Cikin kuka ta ce

“Kada ka zauna da ita doctor, na san baka sonta. Na san wallahi baka son Nana dole aka maka, dan girman Allah ka saketa! Ka saketa mu yi komawar mu US, kada ka ce zaka haɗa zuri’a da lalatacciyar yarinya ka…”

“Shut up!”

Ya daka mata wata razananniyar tsawa wadda ta sanyata firgita. Gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun tashi, idanunsa sun kaɗa sun yi jajur sai huci yake, rai ɓace ya ce

“Kar na sake ji kin haɗata da wadannan munanan kalaman! Zan bata miki fiye da tunanin ki Zahra. And you know what? Babu wanda ya yi min dole sai na auri Nana, Ni ne na aureta saboda raɗin kaina, kuma kin san me yasa na aureta?”

Samun kanta ta yi da girgiza masa kai. Ya ƙara taku ɗaya gabanta wanda yasa suka yi kusa sosai har suka jin hucin numfashin juna ya ce

“Cause i love her! Na aureta ne saboda ina sonta! Ina son Naanah! Kuma ba zan taɓa sakinta ba! She’s my wife!”

Ya yi maganar yana watsa mata wani irin kallo. Girgiza kai Zahra ta yi ta riƙe shi a kiɗime ta ce“A’a wallahi na san baka sonta. Kawai dai ka faɗa ne, baka sonta wallahi!” ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka. Shiru Abdusammad ya yi yana kallonta, can kuma ya janye hannunta daga jikinsa ya juya ya fice daga ɗakin zuciyarsa a dagule babu daɗi. Zahra ta durƙushe a wajen tana kuka kamar ranta zai fita, she just can’t believe a ce doctor ya ce yana son Nana, how? Ta girgiza kanta tana tashi zaune ta ce“A’a impossible”Ta tashi da sauri ta haye sama.

Kai tsaye apartment ɗin Hajiya Babba ya nufa, ya murɗa handle ɗin bakinsa ɗauke da sallama, zaune ya same su suna tattauanawa. Ya ƙarasa ciki ya tsaya gefen kujera ba tare da ya ce komai ba. Papa ne ya ce

“Ya jikin Ahmad ɗin?”

Numfasawa ya yi kafin ya ce

“Da sauki Alhamdulillah, bacci ya daukesa ma”

Papa ya jinjina kansa sai kuma ya yi shiru. Atta ta ce ta girgiza kanta tana hawaye ta ce“oh ni Maryama, ko ina yarinyar nan ta shiga Allah masani”

Sultan ne ya yi saurin faɗin

“maybe ai tana wajen wanda aka hoton nasu tare”

Cikin kuka ta ce“to ina zamu san wane shi?”

“where are the pictures?”

Abdusammad ya yi maganar yana kallon Sultan dan shi ne ya ɗauke su. A sanyaye ya ce“suna ɗakina”

“Bring them”

Okay kawai ya ce sannan ya tashi ya fice daga parlon. Sai a sannan Hajiya Babba ta ce“Abdussamad a samu a yi reporting wajen yan sanda”

Okay kawai ya ce yana gyara tsaiwarsa. After some minutes Sultan ya dawo parlon hannunsa riƙe da envelope ɗin, ya miƙa masa ya karba yana faɗin

“Good job”

Murmushi kawai Sultan ya yi sannan ya koma ya zauna. Papa ya miƙe tsaye kana ya ce“bari naje na duba shi, we should talk later” okay kawai suka ce sannan ya fita daga parlon.

Abdusammad ya zauna idanunsa na kan Hajiya Babba ya ce“Hajiya”

“Na’am” ta amsa a sanyaye..

“Ina Safwan yake?”

Ya yi tambayar fuskarsa a ɗan haɗe.

Hajiya Babba ta kalli hanyar sama sai kuma ta ce“Da dai yana nan bai tafi ba, amma ban sani ba ko ya je gidansa wajen Haule. Tun da ita ɗayar yarinyar har yanzu basu kawota ba”

Miƙewa ya yi ya ce“okay bari naje sai an jima” daga haka ya fice daga ɗakin yana tafe cike da taƙama.

****
Papa ya yi shiru yana kallon Abba jiki a sanyaye. Can kuma ya girgiza kansa ya ce

“A’a Ahmad ba’a haka, yarinya ce ƙarama, akwai rashin hankali a tattare da ita. Bai kamata a ce ka ɗauki wannan mummunan hukuncin ba, beside ma yarinyar ta yi aure yanzu!”

Da sauri ya kalli Papa sai kuma ya ce

“Ta yi aure? Yaushe ta yi aure ban sani ba Papa? and wa ta aura?”

Murmusawa Papa ya yi sai kuma ya ce

“Wa ka ke tunanin zai share maka hawaye irin haka?. Abdusammad ne ya aureta, dashi aka daura mata aure”

Da wani irin mamaki Abba ke kallon Papa, sai kuma ya girgiza kansa ya ce

“Yaya ban da wasa, ka faɗa min da gaske Abdusammad ya aureta?”

Dafa shi Papa ya yi ya ce“Eh da gaske ne, kasan bama irin wannan wasan da kai ai”

Tashi Abba ya yi ba tare da ya ce masa komai ba ya zura slippers ɗin dake ƙasan gadon sannan ya yi waje da sauri, duk da yanda yake jin jikinsa babu daɗi.

Da idanu Papa ya bi shi sai kuma ya tashi ya biyo bayansa dan ganin inda zai je. A parlon suka ci karo dashi, Ya yi saurin riƙe kwalar rigarsa rai ɓace ya ce

“me yasa? Me yasa Abdul? Why? I said why!”

Ya ƙare maganar yana jijjigashi. Kallonsa kawai Abdusammad ke yi ba tare da ya san akan abin da yake magana ba, Amma da ke zaune ita da Aunty Ramlah suka miƙe tsaye. Ta ƙaraso wajen tana kallonsu, dai dai nan Papa ya fito daga ɗakin. Da sauri kuma ya ƙaraso gabansa yana ƙoƙarin janye hannunsa ya ce

“Subhanallahi Ahmad mene haka?”

Girgiza kai Abba ya yi yana sake matse kwalar rigarsa ya ce

“Ka faɗa min meyasa zaka yi haka? Me ya saka zaka aureta! Akan mene ne!”

Sai a sannan Abdusammad ya fuskanci inda ya dosa. Ya ɗan yi murmushi yana janye hannunsa ya ce“to mene ne Abba? Nana ce fa”

A tsawace Abba ya ce

“Nanan! Ita Nanan bana son ganinka da ita. Bana son kowace mu’amala ta haɗata da yan gidan nan, ta riga da ta bar cikin dangin nan, yanzu bata kasance daya daga cikin mu . Akan me zaka aureta Abdul? Ka san zafin da naji?”

Shiru ya yi yana kallonsa ganin da gaske yake faɗar maganganun, Ya riƙe hannunsa a sanyaye ya ce“Abba ka yi haƙuri mana”

“Ba zan yi ba!”

Ya ce a zafafe. Kallonsa suka dinga yi da mamaki, Amma da tuni hawaye ya wanke mata fuska ta ƙaraso wajen ta rike gefen rigarsa cikin kuka ta ce

“me ka ce? Ka cire Nana daga cikin dangin nan? Kenan ka zareta daga matsayinta na yar ka?”

Juyowa Abba ya yi yana kallonta sai kuma ya janye jikinsa ya ce“Eh haka nace!”

Daga haka ya koma ɗakinsa rai ɓace..

Silalewa ƙasa Amma ta yi ta fashe da wani raunataccen kuka, Aunty Ramlah ta riƙeta ba tare da ta ce komai ba. Numfasawa kawai Papa ya yi sai kuma ya fice daga parlon, Shi kuwa Abdusammad ciki ya shiga gurin Abba.

****
Ƙarfe 11:30 na safe Mami ta shigo ɗakin, suna zaune tare sai dai babu wacce ke magana cikin su. Mami ta girgiza kanta sai kuma ta ƙaraso ciki ta zauna kan sofa tana kallonsu duka ta ce

“Kukan ne har yanzu baku gama ba?”

Kallonta kawai suka yi ba tare da sun ce komai ba, Ta ɗan yi murmushi sai kuma ta ce“Nana kin ci abincin?”

Gyaɗa mata kai Nana ta yi a hankali dan har ga Allah ba son yin magana take ba. Mami ta sake cewa“to ku tashi ku shirya sai ku rakani”

“Ina zamu je Mami?”

Khadijah ta yi tambayar a sanyaye. Tashi Mami ta yi tana gyara zaman rigarta ta ce“idan mun je zaku gani” daga haka ta fice daga ɗakin. Khadijah ta bita da kallo sai kuma ta sauke numfashi tana kwanciya kan gadon ta ce“ni wallahi bana son fita” kallonta kawai Nana ta yi ba tare da ta ce komai ba. Can kuma ta tashi zaune ta ce

“Yauwa Nana to yanzu sir Junaid ɗin ya fitar da hotunan?”

A sanyaye Nana ta ce“ban sani ba Khadijah,ina ga ya fadawa su Abba. Na san Abba yana can yana jin haushina” ta ƙare maganar tana fashewa da kuka. Dafata Khadijah ta yi a sanyaye ta ce“ki daina kukan nan mana, kin ga dai jiya daga haka aka kai ki asibiti”

Cikin shessheƙar kuka Nana ta ce“to me zan yi? Ni gaba ɗaya bana jin daɗin rayuwar, wallahi da zan iya da sai nasha guba na mutu” saurin rufe mata baki Khadijah ta yi tana zare idanu, Nana ta janye hannunta daga kan bakinta rai ɓace ta ce

“Ni rabu dani”

Sake rufe bakin ta yi sannan ta ce“wallahi idan abin da zaki ce kenan ba za ki yi magana ba”

A fusace Nana ta hankaɗeta sannan ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet. Khadijah ta tashi zaune tana riƙe bayanta ta ce

“Banza mai son faɗa kawai”

****
Aunty Khadijah ce zaune kan sofa sai Sojan a gefenta, daga ɗaya kujerar kuma Safeena ce zaune sai Ummarsu. Kamar daga sama Zahra ta shigo parlon babu ko sallama, ta ƙarasa wajen Umma ta faɗa jikinta tana fashewa da kuka.

Umma ta riƙeta da mamaki ta ce

“Zahra’u lafiya? Mene ne?”

“Ba zan iya ba Umma, ba zan jure ba wallahi. Ba zan iya zama da Nana matsayin kishiya ba, Umma na shiga uku..”

Ta sake fashewa da kukan, Girgiza kai Umma ta yi cikin son kwantar mata da hankali ta ce

“Ya isa haka, tashi ki ji”

A sanyaye ta tashi ta zauna gefenta tana ci gaba da kukan, Umma ta dafata ta ce

“Duk abin da haƙuri bai baka ba to rashinsa ba zai taɓa baka ba Zahra’u, Idan baki hakura ba to me zaki yi?”

Cikin kuka Zahra ta ce

“umma ta ya zan jure zama da Nana matsayin kishiya bayan da ina mata kallon yar karamar ƙanwata, taya zan fara sharing mijina da ita? Wallahi ba zan iya ba!”.

Murmushi irin na manya Umma ta yi kafin ta ce“daman haka abun yake Zahra, sau dayawa abin da baka yi tunani ba shi ne yake kasancewa. Wani abun ƙaddara ce, wani kuma ganganci ne” Zahra ta tsaida kukan nata tana kallon Umma. Numfasawa Umma ta yi sannan ta ci gaba da faɗin

“Na san duk abin da ku ka aikata. Sai dai ban yi tunanin haka daga gareki ba, kin biye mata kun yi abin da ku ke ganin shi ne son zuciyarku, idan kuwa haka ne to dole ki yarda da abin da ya biyo baya.” Umma ta ƙare maganar tana kallonta, Sunkuyar da kai Zahra ta yi dan sam bata yi tunanin Umma ta san abin da ya faru ba, Umma ta girgiza kanta hawaye na biyo kuncinta ta ce

“Ban ji daɗi ba! Sam bai min daɗi ba ganin yanda ki ka lalata rayuwar yarinya, kin san me yarda ke nufi? Ya yarda da ke, ta aminta da ke, tana miki kallon ƴar uwa wadda zata iya fadawa kowace damuwarta. Amma kin yi amfani da wannan yardar kin cutar da ita, kin yi mata abin da zai jawo kowa ya tsaneta, bayan ke da kan ki kin san cewa bada gangan ta yi hakan ba. To me ki ke tunani Zahra? Allah ya barki, ki ci bulus?”

Umma ta girgiza kanta sai kuma ta ce

“Inaaa ba zai taɓa yiwuwa ba, shi daman a kullum sharri ɗan aike ne, duk abin da ka ƙulla zai dawo maka, Ubangiji na kishin bawansa, kuma yana ƙaunarsa. Dan haka ya yi mata sakayya,ya nufi mijinki da aurenta.”

Fashewa da kuka Zahra ta yi tana danasanin abin da ta aikata, ita kanta ta san bata kyauta ba, sannan bata san dalilin daya sanyata yin hakan ba. Ta ɗago kanta tana kallon mahaifiyar tata wadda ke hawaye itama. Umma ta goge fuskarta da hannunta wanda ke riƙe da cazbaha sannan ta ce

“Na yi ƙoƙarin baku tarbiyya tun bayan rasuwar mahaifinku, na yi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin kun zama ya’ya nagari, kun zama mutane nagari wanda kowa zai yi alfahari dasu. Sai dai a duk lokacin daya kasance babbar ƴata bata kasance mutuniyar kirki ba, dole sai sauran sun zama haka. Dole sai taja wasu daga cikin ƴan uwanta. Kamar yanda Khadijah ta jaku ku ke ƙoƙarin faɗawa halaka”

Umma ta ƙare maganar wani kukan na kwace mata, Safeena ce ta riƙeta tana kukan ita ma ta ce

“Dan Allah Umma ki yi haƙuri. Ki daina kuka kin ji”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *