⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 26: Chapter 26

Riƙe hannunta kawai Umma ta yi dan bata jin zata iya daina kukan a halin da take ciki, Zahra ta girgiza kanta tana kuka ita ma ta ce

“ki yi haƙuri Umma. Wallahi ba zamu sake ba, babu abin da zai sake faruwa in sha Allah”

Tashi Aunty Khadijah ta yi ta bar wajen dan sam bata ga abin kuka anan ba, Siyama ta ƙaraso wajen ta zauna a ƙasa tana kallon Umma ta ce

“Umma ki yi haƙuri dan Allah”

Ganin duk sun ruɗe suna kuka ya sanyata tsagaita nata kukan. Ta dafasu tana murmushi mai haɗe da hawaye ta ce

“shikenan ya shige, Allah ya yi muku albarka ya shirya ku”

Da Amin suka amsa suna goge hawayensu..

****
Bayan sallar magriba ta dawo gidan, gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, musamman yanda taga Umma na kuka akan su. Sai taji danasanin abubuwan data aikata. Koda ta shiga gidan bata samu kowa ba kamar yanda ta yi tsammani, dan haka ta shige daƙinta ta yi wanka ta zauna gefen gado tana tunani. Tana nan zaune har aka yi sallar isha’i ta gabatar da sallah sannan ta sakko ƙasa ta shiga kitchen. Jollof rice ta yi wadda taji kayan haɗi, ta yi haɗin salad sannan ta fito ta koma sama ta zauna dan ko kaɗan bata jin yunwa.

****
Ƙarfe 9:30 na dare ya shigo ɗakin, zaune ya hangeta gefen gado ta sunkuyar da kanta sai kuka take a hankali. Ya ƙaraso ciki yana kallonta, zama ya yi gefenta kafin ya ce

“Maimoon”

A sanyaye ta ɗago kanta ta kalleshi sai kuma ta mai da ƙasa tana shessheƙar kuka, Aliyu ya ɗan yi murmushi kafin ya kama hannunta na dama yana kallon red henna ɗin da aka zana mata wanda ya yi matuƙar kyau a hannunta, Ya kai hannun bakinsa ya sumbace shi yana lumshe idanu. Yana yin daya haifar mata da wani irin sanyin jiki, ta ɗago ta kalleshi a sanyaye. Ba tare da ya saki hannun ba ya janye mayafin da ta yi lulluɓi dashi, sannan ya ce

“tashi mu yi sallah”

Babu musu ta mike ta nufi toilet ta sake dauko alwala, bayan ta fito shi ma ya shiga ya yo alwalar sannan ya shimfiɗa musu ladduma. A tare ya ja su sallar nafilar bayan sun idar suka yi addu’a, daga bisani ya dafa kanta ya yi mata addu’o’i sannan ya tashi ya zare babbar rigar jikinsa yana kallonta ya ce

“Mu je ki ci abinci”

Girgiza masa kai ta yi a sanyaye ta ce“na ƙoshi”

Ya ɗan yi murmushi sai kuma ya kamo hannunta ya taimaka mata ta miƙe tsaye kafin ya ce“to muje ki ci kazarki” ya ƙare maganar yana jan kumatunta. Sunkuyar da kanta ta yi bata ce komai ba, ya ja hannunta suka fita daga ɗakin. Sosai Maimoon ta saki jikinta ta ci kazar bayan ta ƙoshi ta tashi ta bar wajen, Aliyu ya bita da idanu yana murmushi sannan ya biyo bayanta. Daren ranar haka suka raya shi cike da so da ƙauna, sam ba zaka ce ba auren soyayya suka yi ba, ya dinga riritata kamar kwai, ita kuwa sai sake narke masa take. A ɓangaren Sultan kuwa kasa taɓuka komai ya yi, ya dinga kallon Amrah da ke baccinta hankali kwance, gani yake kamar a mafarki. Zuciyarsa ta kasa aminta da cewa ya rasa Nana, idan ya kalli Amrah sai yaji damuwa ta sake masa yawa, ya so a ce Nana ce a wannan dakin, a kuma kwance akan wannan gadon, da shi kansa bai san halin da zai shiga ba. Ya ja idanunsa ya lumshe yana jin babu daɗi.

Washegari da sassafe around 7:30am aka fara buga ƙofar gidan, Aliyu ya janye jikinsa dakyar ya fita daga ɗakin bayan ya sake rufe Maimoon, yana buɗe kofar ya shigo yana kalle-kalle. Aliyu ya dinga kallonsa da mamaki sai kuma ya ce“Buddy lafiya?”

“Ina Maimuna?”

Da mamaki Aliyu ya ce“tana ciki”

“i want to see her”

Ya ce yana nufar dakin. Bin bayansa Aliyu ya yi da sauri, tsaye ya same shi gaban gadon ya harɗe hannayensa a ƙirji. Aliyu ya ƙaraso ciki yana kallon Maimoon ya ce

“Maimoon”

Dakyar ta buɗe kumburarrun Idanunta, ta ɗan zame duvet ɗin daga kanta tana kallonsa, idanunta daya sauka kan Abdusammad ne ya sanya ta fara ƙoƙarin tashi, zama Aliyu ya yi gefenta ya ɗagota ya jinginata da jikinsa, Abdusammad ya taɓe baki yana kallonta ya ce

“Ina Nana take?!”

“Nana kuma? Ya za’a yi ta san inda Nana take Buddy?”

Aliyu ya tambaye shi da mamaki. A tsawace Abdusammad ya ce

“Nace ina Nana take!”

Sunkuyar da kanta ta yi hawaye na biyo kuncinta, Ya gyaɗa kansa sai kuma ya ƙara taku ɗaya zuwa gabansu yana ware idanunsa sosai akanta ya ce

“don’t ever let me ask you again! Ina Nana take?”

Ganin yanda ta firgice yasa Aliyu dafata ya ɗago yana kallonsa ya ce

“Haba Buddy she’s not feeling well ka barta mana dan Allah” a fusace shima ya ce

“to ni ina ruwana? Mene ne nawa da rashin lafiyarta?”

Aliyu shiru ya yi yana kallonsa ganin yanda ya haɗe rai. Ya maida idanunsa kan Maimoon cikin sanyin murya ya ce“pls idan kin san inda take talk to him” sake fashewa ta yi da kuka tana maƙalewa jikin Aliyu ta ce

“wallahi uncle ban sani ba, ban san inda take ba!”

Wani irin kallon kin zama mahaukaciya Abdusammad ya dinga mata, can kuma ya gyaɗa kansa ya ce“okay!”

Daga haka ya juya ya fice daga ɗakin rai ɓace.

Aliyu ya bishi da kallo sai kuma ya maida idanunsa kan Maimoon, Ya shafa kanta a hankali ya ce“sorry ki daina kukan, ya tafi ai” gyaɗa kanta kawai ta yi ya taimaka mata ta kwanta dan har sannan zazzaɓi ne rau a jikinta.

Abdusammad na fita apartment ɗinsa ya nufa, ya samu Zahra zaune a parlon ta zuba uban tagumi kamar koda yaushe. Kallo ɗaya ya yi mata sai kuma ya haye sama dan ransa a ɓace yake, ta bishi da idanu kawai dan tasan kota kulashi ba amsawa zai yi ba. Tana nan zaune har after 15mins sai kuma ta tashi tabi bayansa, zaune ta sameshi gefen gado ya jingina da fuskar gadon idanunsa a rufe. Ta yi shiru tana kallonsa kafin taja jikinta ta ƙarasa inda yake a sanyaye, ta zauna gefen gadon ba tare da tace komai ba. Sun ɗauki lokaci mai tsayi a haka kafin ta ƙara matsawa kusa dashi, a hankali ta ɗora kanta akan faffaɗan ƙirjinsa. Ko motsi bai yi ba, ballantana ta saka ran zai kulata, dan ta tabbata ba bacci yake ba. A hankali ta zura hannayenta duk biyun a bayansa ta riƙe shi ƙam sai kuma ta fashe da kuka kamar ƙaramar yarinya. Duk yanda ya so yin shiru kasawa ya yi dan sam baya son jin kukan mace, ya ware idanunsa akanta kafin a hankali ya ɗagota yana kallonta da birkitattun idanunsa ya ce

“mene ne?”

Cikin kuka ta ce

“Doctor bana jin daɗi ne kawai. Dan Allah mu koma US”

Numfasawa ya yi kafin ya ce“in sha Allah zamu koma but not now”

“amma meyasa?”

Ta tambaya da damuwa sosai akan fuskarta. Sai da ya janyeta daga jikinsa ya miƙe tsaye yana gyara rigar jikinsa ya ce“cause i have alot to do” daga haka ya nufi toilet. Da idanu kawai Zahra ta bi shi sai kuma ta dauke kanta, ta zame jikinta ta kwanta akan gadon ta lumshe idanu..

Kusan 3 weeks kenan, abubuwa sun fara shigewa, sai dai wanda aka yiwa shi ne mai manta ba, duk matan sun tare gidan mazajensu har da Siyama wadda take ta faman gigi. Amma har sannan ta kasa daina zancen Nana, kullum bata da magana sai tata, koda yaushe cikin son ganinta take. Sai dai koda wasa bata isa tayi maganarta gaban Abba ba indai ba tana son ɓacin ransa bane, ko sunan Nana baya son yaji an ambata. Duk da ƙasan zuciyarsa bai manta da ita amma sam yaƙi bari mutane su gane hakan. A ɓangaren Maimoon kam kusan kullum cikin kuka take, dan har cikin zuciyarta bata san inda Nanan take ba, sam tunaninta bai bata ta tambayeta inda zata je a ranar. Gashi ta kasa samunta a waya, hasalima kullum ta kira wayar a kashe suke ce mata, wannan yasa har sannan ta kasa sakar jikinta duk yanda Aliyu ke nuna mata so da ƙauna.

****
Wasu ƙattin maza ne tsaye su huɗu, sun yi masa ƙawanya kowannesu hannunsa riƙe da bindiga sai zazzare idanu suke yi. Kasancewar fuskarsa a rufe take da wani abu mai kamada buhu ya sanya bai san su wane ba, dan ko numfashi baya samun damar yi. After 5mins aka buɗe ƙofar, nan take duk suka juyo suna kallonsa, cike da girmamawa kuma suka durƙusa a tare suka gaishe shi. Ya gyaɗa musu kai sannan ya ƙarasa gabansa ya janye buhun. Wani irin jan numfashi Junaid ya yi, ya sauke shi a wahalce fuskarsa ta yi jajur dan ba ƙaramin duka yasha ba, gaba ɗaya sun sauya masa kammani. Bai ƙarasa dawowa daidai ba yaji ɗaya daga cikinsu ya cafki maƙogaronsa cikin ƙaraji ya ce

“Hey ina yarinyar take?”

Kasa magana ya yi dan bai bashi damar haka ba, ganin yana neman rasa rayuwarsa ya sanya ya ce

“Stop!”

Cak ya tsaya ya kuma zare hannunsa, ya umarce su da su yi baya, kamar jira suke kuwa suka koma bayan. Ya dafashi yana zare face mask ɗinsa da ɗayan hannun, nan take kyakkyawar fuskarsa ta bayyana, gyara tsaiwarsa ya yi kafin a sanyaye ya ce

“Ina Nana take?”

Ganin yanda ya yi magana a dake ya sanya Junaid haɗiyar yawu, Ya girgiza kansa yana kallonsa cikin tashin hankali ya ce

“Nana kuma? Me ya samu Nana? Dan Allah kada ka cemin wani abun ya sameta”

Wani irin duka ya kai masa da ƙasan bindiga nan take haƙoransa uku na gaba suka zube, Ya dafe bakin yana jin wata irin azaba na kawo masa ziyara. Bai bari ya wartsake ba ya shaƙe wuyansa wannan karon cikin ɓacin rai ya ce

“Ina take? Ina ka kai ta?”

Girgiza kai Junaid kawai yake, dan sam bai san abin da yake magana akai ba. Ya dinga wani irin numfashi dakyar kamar zai mutu, sakinsa ya yi yana ɗauke kai ya ce

“kar ka bari na sake tambayarka tana ina?”

Junaid da azaba ke neman hallaka shi ya fashe da kuka jini na zubowa daga bakinsa ya ce

“Wallahi ban san me ku ke magana akai ba, Mene ne ya samu Nana? Dan Allah kada ku cemin wani abun ya sameta”

Ɗauke kai Abdusammad ya yi yana murmushi ganin yanda yake neman raina masa hankali. Junaid ya bishi da idanu yana fatan ya sanar dashi abin da ke faruwa.

Cikin wani irin zafin nama ya dawo gabansa ya ɗora hancin bindigar hannunsa a tsakiyar kansa yana kallonsa rai ɓace ya ce

“ina Nana take?”

Girgiza kai kawai Junaid yake, jikinsa sai rawa yake. Ya sake matse kunamar bindigar ya ce

“ka faɗa min ko na harbeka, kuma idan na kasheka na kashe banza!”

Bakinsa na rawa ya ce

“Waam… wallahi, wallahi ban sani ba, ban san Nana ta bar gidan nan ba”

Shiru ya yi yana kallonsa da ɗan mamaki, dan ya lura babu ƙarya a maganarsa ya ɗauke bindigar ya miƙewa ɗaya daga cikinsu sannan ya zaro hotunan da suke aljihunsa, buɗesu ya yi ya kara masa a fuska yanda zai gani ya ce

“ba kai bane wannan?”

Da mamaki Junaid ke kallonsa sai kuma ya kai hannu zai kwace hoton yana faɗin “ina ka samu wadannan hotunan?”wani banzan kallo Abdusammad ya watsa masa sannan ya mayar da hotunan envelope ɗin ya ce“ina Nana take?”

Junaid ya sake girgiza kansa a karo na barkatai kafin ya ce“wallahi ban sani ba! Ban san ma bata gida ba, yaushe ta bar gida?”

Kujera yaja ya zauna yana kallonsa sosai fuskarsa a haɗe babu alamar wasa ya ce“tell me ina ka haɗu da ita? And kada ka ɓoye min koda abu guda ɗaya ne” Junaid ya dinga kallonsa sai kuma ya sunkuyar da kansa, Da hannu ya yi musu alama dasu dawo suka dawo kansa suka tsaya kowanne yana riƙe da bindigarsa har sannan. A hankali ya daga idanunsa yana kallonsa sai kuma ya sake saukewa, kusan 2mins kafin ya buɗe baki ya fara bashi labarin duk abin da ya faru daga farko har zuwa ƙarshe.

Ban da kallonsa babu abin da Abdusammad ke yi, Junaid da ke kuka kamar ransa zai fita ya sake cewa“wallahi ban yi da niyyar cutar da Nana ba, sam bana nufinta da mugun abu”

Numfasawa Abdusammad ya yi yana saurarensa har sannan, gaba ɗaya kansa ya kulle, ya lura babu ƙarya a cikin zantukan Junaid. Ya tashi tsaye yana kallonsa ya ce

“baka nufinta da sharri amma ka iya ɗaukanta hotuna har kake mata barazana? Sannan baka nufinta da sharri har ka iya cutar da ita duk da cewa ita da zuciya ɗaya taje wajenka? Haka ne baka nufinta da sharri?”

Girgiza kai Junaid ya yi yana jin wanda irin ɗaci a ransa ya ce“wallahi bana nufin Nana da sharri, na san ban kyauta ba, kuma ban yi dai-dai ba. Amma nima zugar aboki ce ta yi tasiri akaina, sai bayan dana aikata abun sannan nafara danasani. Wallahi ban taɓa tunanin fitar da hotunan Nana ba, hasalima bayan wanda na tura mata bani da wasu, dan na goge ba zan juri kalla ba. Kawai na so yin amfani da hakan ne wajen sakata ta yi duk mai yiwuwa kar ta ga an rabamu.”

Ya sauke numfashi hawaye na gangarowa kan fuskarsa ya ci gaba da faɗin “sai dai hakan bai yi wani amfani ba. Na rasata, gefe guda kuma na haifar mata da baƙin ciki wanda zata dade tana tunawa, a yanzu banida wani buri daya shige naga Nana domin na nemi yafiyarta duk da na san ban cancanci hakan ba. Ta ɗaukeni masoyi na gaskiya ni kuma na cutar da ita, Dan Allah ina zan ga Nanaa?…”

Ya ƙare maganar yana sakin wani raunataccen kuka. Shiru Abdusammad ya yi can kuma ya furzar da iska daga bakinsa ya ce“kana son ka ce min baka san inda take ba?”

“wallahi ban sani ba. Ban ma san bata gida ba, ni tun ranar data kirani na ƙarshe ana i gobe ɗaurin auren ban sake magana da ita. Wane ya saceta? Dan na san Nana ba zata taɓa guduwa da kanta ba”

Junaid ya yi maganar yana kallonsa hankalina tashe. Zura hannayensa ya yi cikin aljihun trousern dake jikinsa kafin ya ce

“ta bar gida tun ranar ɗaurin aurenta da safe, kuma babu wanda ya san inda ta tafi. She’s afraid akan zaka fitar da hotunanta”

Girgiza kai Junaid ya yi yana jin wani matsanancin tausayinta ya ce“Allah sarki Nana, yarinya ce ƙarama. Ba komai take iya ɗauka ba, but wait ya aka yi ka san da maganar hotunan nan? Na tabbata Nana ba zata faɗawa kowa ba” Abdusammad ya ce“me ka ke nufi ba kai ne wanda ka bawa Safwan hotunan ba?” da mamaki Junaid ya ce“ban san shi ba, kuma ban bawa kowa ba. Ban da Nana babu wanda ya san da maganar hotunan nan, taya aka yi suka je hannun wani?”

Sai a sannan tunanin Abdusammad ya kawo wajen, a ina Safwan ya samu hotunan Nana? Wane ya bashi?. Ya girgiza kansa sai kuma ya kalli guards ɗin dake tsaye ya ce“ku ci gaba da tsare shi.” cike da girmamawa suka amsa sannan ya juya ya bar ɗakin, Junaid ya bishi da idanu..

****
A hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar bakinta dauke da sallama. Zaune ta hangeshi kan kujera yana operating system ɗin dake gabansa, ta sauke numfashi sai kuma ta ƙarasa ciki a hankali. A kan table ɗin dake gabansa ta ajiye mug ɗin sannan ta zauna gefensa. Ya ɗan kalleta sai kuma ya mayar da kansa ga system ɗin ba tare da ya ce komai ba. Itama Amma shiru ta yi ta sake zuba uban tagumi dan yanzu shi ne kaɗai abin da take yi, Abba ya kai hannunsa ya ɗauka tea ɗin ya fara sipping a hankali yana kallon abin da yake. Sai da kusan mintuna biyar suna shuɗe kafin ta sauke numfashi ta gyara zamanta tana kallonsa sosai ta ce“yallabai”

Juyo da idanunsa kanta ya yi yana kallonta ya ce“lafiya dai?” gyaɗa masa kai ta yi sai kuma ta ce“lafiya. Daman ina son nayi maka magana ne akan Nana naga…”

Dakatar da ita Abba ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu, lokaci ɗaya ya haɗe ransa kamar wanda ta yiwa zancen mutuwa. Ya kuma ce“idan wannan maganar ce kar ki yimin dan Allah”

Amma ta dinga kallonsa jiki a sanyaye lokaci ɗaya hawaye ya cika kurmin idonta ta ce“to idan ban maka ba wa zan yiwa? Kana ganin fa kusan wata daya babu Nana babu labarinta. Ko gidajen rediyo da aka kai report da station ba’a samu wani magana ba. To kuma ka ce ba zan maka maganarta ba?”

“To mene ne nawa da zaki yi min magana akanta? Kin ji na ce kina son na ganta? Kin ji nace ina son ta dawo?. To bari kiji ni babu a akan maganarta, sannan I’m warning you karki sake min maganarta! Kar ki sake Rabi’ah”

Abba ya yi maganar rai ɓace, ya tashi ya rufe system ɗin gabansa ya fice daga ɗakin ya barta zaune. Amana binsa kawai ta yi da kallo sai kuma ta fashe da wani irin kuka, kenan ba zai nemo mata yarta ba? Babu wanda ya damu da ɓatan Nanar?. Ta sake rushewa da wani sabon kukan tana dunƙule jikinta waje ɗaya.

****
A compound ɗinsu Aliyu motar ta yi parking, ya buɗe back seat ya fito yana karewa compound ɗin kallo kafin ya furzar da numfashi ya nufi cikin gidan. Maimoon na zaune a parlon hannunta riƙe da wayarta ya shigo, tana ganinsa ta miƙe tsaye a ɗan firgice ta ce

“Welcome uncle”

Ganin yanda ransa yake a haɗe babu alamar wasa ya sanya ta sunkuyar da kanta. Ya shigo tsakiyar parlon yana kallonta har sannan, zama ya yi kan sofa ya ce“zauna magana zamu yi” kallonsa ta yi da mamaki ganin yanda ya yi maganar ba’a sigar faɗa ba, dan haka ta koma ta zauna tana kallonsa har sannan. A nutse ya ce

“Maimuna”

Ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta a sanyaye ta ce “na’am uncle”

“zan tambayeki kuma ki tabbata kin sanar dani gaskiya. Kar ki ɓoye min koda abu guda ɗaya da ki ka sani”

Gyaɗa masa kai ta yi sai kuma ta ɗago fuskarta da hawaye ya fara zuba ta ce“tam uncle, zan faɗa maka duk abin da na sani wallahi”

Jinjina kansa ya yi kafin ya ce“mene ne abin da yasa Nana ta bar gidan nan? Who forced her? Wane yake treating ɗinta da hotunan, nd wane ya san da maganar hotunan har ta fita ta je wajen Safwan?”

Wata irin faduwar gaba ce ta ziyarceta. Ta haɗiye yawu da kyar sai kuma ta ce“uncle nima ban san wanda ke treating ɗinta ba, kawai dai na san Nana ta bar gidan nan a saboda tilastawar da Yaya Safwan ya yi mata. I was there da safen ya zo ya nuna mata hotunan ya ce idan har ta yarda aka ɗaura aurensu to sai ya fitar dasu kowa ya gani. Idan kuma ta bar gidan nan to ba zai faɗawa kowa ba, ya ce ta tafi idan aka gama maganar daurin auren sai ta dawo. Shi ne ta ce to saboda tsoron kada a fitar da hotunan da kuma barazanar da Junaid ke mata, yasa ta haƙura ta tafi duk da bata so, ta tafi ba tare da mun tambayeta inda zata je ba, wallahi uncle kullum da Nana nake kwana da ita nake tashi. Na kasa daina tunaninta, ko wane hali take?…”

Ta fashe da kuka tana girgiza kanta. Shiru ya yi yana saurarenta can kuma ya sauke numfashi ya ce“it’s alright. Kenan baki san wanda ya fitar da hotunan ba?” shiru Maimoon ta yi tana tunanin abin da faɗar gaskiyar tata zai haifar, what idan ya saki Zahra saboda haka? Ko kuma hakan yasa kowa ya tsaneta?. Ta girgiza kanta tana fatan kada gaskiyar ta bayyana, kallonta ya dinga yi sai kuma ya ce

“ya dai? Kin san wanda yake treating ɗinta da hotunan?”

Girgiza masa kai ta yi har sannan tana hawaye ta ce“ban sani ba uncle, kawai a wajen Junaid na san su” Abdusammad bai sake cewa komai ya miƙe ya fice daga parlon. Ta bishi da kallo sai kuma ta silale ƙasa ta fashe da wani sabon kukan tana jin tausayin Nana. Ko’ina take?.

****
Yana fita kai tsaye apartment ɗin Safwan ya nufa, ya ɗan tsaya a bakin ƙofar dan bai taɓa zuwa ba tun da ya tare, can kuma ya murɗa handle ɗin ƙofar bakinsa ɗauke da sallama. Haule ce kawai a parlon ta zuba uban tagumi dan bata ma san ya shigo ba, ya kalleta sai kuma ya sake sallama. Sai a sannan ta ɗago ta kalleshi lokaci ɗaya ta mike tsaye jikinta na ɗan rawa ta ce

“in…ina yini?”

Amsawa ya yi kafin ya ce

“Safwan fa?”

Haule ta sake sunkuyar da kanta ta ce“yana sama”

Kallon hanyar saman ya yi sai kuma ya sake kallonta ya ce“ok kira min shi”

“ai bahida lafiya. Ko tashi ma baya yi”

Ta yi maganar a sanyaye. Shiru Abdusammad ya yi can kuma ya nufi saman da sauri, ɗakin daya tabbatar shi ne nasa ya buɗe, Kwance ya hangeshi kan gadon ya lulluɓe jikinsa da ƙaton duvet. Siyama na zaune gefensa taci uban kwalliya sai kallonsa take, tana jin an buɗe kofar ta ɗago a fusace dan ta yi tunanin Haule ce. Sai dai ganin Abdusammad ya sanyata miƙewa a sanyaye ta ce

“Barka da zuwa Yaya”

Jinjina kansa kawai ya yi dan bai zo dan su gaisa ba, ganin idanunsa na kan Safwan ya sanya ta fice daga ɗakin ta basu waje. Ya karasa gabansa cikin takunsa na isa da taƙama. Ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonsa ya ce

“Safwan”

A sanyaya janye duvet ɗin daga kansa. Ya kalleshi sai kuma ya tashi zaune da kyar yana cije baki, Abdusammad ya dinga kallonsa ganin yanda ya rame ya lalace. Safwan ya ɗan yi murmushi wanda yafi kama da na ƙarfin hali sannan ya ce

“Yaya sannu da zuwa”

“Yauwa”

Ya amsa a takaice. Shiru ɗakin da ɗauka na wasu mintuna kafin ya numfasa yana kallonsa ya ce

“Nazo ne na tambayeka abu, kuma bana son ka ɓoye min komai daga ciki. Idan ka kuskura ka faɗa min abin da ba shi ba wallahi sai ranka ya ɓaci!”

Jin yanda ya yi maganar in a serious tone ya sanya Safwan kallonsa, bashi yake kallo ba, dan haka ya sunkuyar da kansa a sanyaye ya ce

“in sha Allah Yaya zan faɗa maka gaskiya”

“A ina ka samu hotunan Nana? Wane ya baka?”

Da wani irin mamaki Safwan ke kallonsaz lokaci ɗaya kuma ya yi kasa da kansa ya ce

“but Yaya…”

Ɗaga masa hannu Abdusammad ya yi sai kuma ya gyara tsaiwarsa yana kallonsa rai a haɗe ya ce“i’m just asking you, wane ya baka?”

Shiru Safwan ya yi yana tunanin abin yi, an ya ya ce Zahra ce? me hakan zai haifar? To amma idan har fadar na nufin dawowar Nana dole ya sanar dashi gaskiya. Dan haka ya numfasa ya ɗago yana kallonsa a sanyaye ya ce

“i’m sorry to say Yaya, Zahra ce ta bani!”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *