Chapter 27: Chapter 27
Da wani irin mabayyanin mamaki Abdusammad ke kallonsa, Ya girgiza kansa kafin ya ce“me kace Safwan?” Safwan kasa haɗa idanu ya yi dashi, muryarsa na rawa ya ce“Zahra ce ta bani Yaya” kusan mutuwar tsaye Abdusammad ya yi a wajen, tuni idanunsa suka kaɗa suka yi jajur, jijiyoyin kansa suka fito sosai. Ganin yanayin da yake ciki ya sanya Safwan tashi tsaye yana kallonsa ya ce
“Kayi haƙuri Yaya. Wallahi ban yi niyyar faɗa ba, ban so kowa yaji maganar nan ba. Sai dai son da nakewa Siyama shi ne ya sakani aikata hakan” ya ƙare maganar yana share hawayen dake zubo masa. Furzar da iska ya yi daga bakinsa kafin ya dafashi a hankali ya ce“ita Zahra wane ya bata?”
Girgiza kai Safwan ya yi kafin ya ce“ban sani ba wallahi, kawai zuwa ta yi ta kirani da daddare ta bani. Ban san wanda ya bata su ba”
Jinjina kai kawai ya yi sannan ya dafa kafaɗarsa ya ce“okay thank you.”
Daga haka ya janyeshi gefe ya fice daga ɗakin, da idanu Safwan ya bi shi sai kuma ya sulale a ƙasa ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro. Yana sauka parlon ya ga ta fito daga kitchen, ganin yana shirin fita ya sanya ta ce“Yaya na ɗora maka abinci ba dai tafiya zaka yi ba?” kallo ɗaya ya yi mata, wanda ya sanyata sunkuyar da kai. Kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce
“No need thanks”
Daga haka ya fice daga parlon kamar zai tashi sama. Tafiya ya dinga yi baya ko kallon gabansa, Allah Allah yake ya isa Apartment ɗin su yaje ya samu Zahra.
****
Sultan road, Kano state.
A tsakiyar compound ɗin gidan motar ta yi parking, Drivern ya buɗe ya fito sannan ya zagayo ya buɗe masa. A hankali ya zuro ƙafafunsa waje, yana ƙarewa gidan nasa kallo. Khadijah ta fito da wani irin gudu tana zuwa ta shige jikinsa tana ƙanƙameshi ta ce
“welcome back Dadyyyy!”
Rungumeta ya yi yana murmushi ya ce“Thank you Mimina”
Ta sake zagaye hannayenta a bayansa a shagwaɓe ta ce“Daddy shi ne baka dawo da wuri ba ko?”
Ɗago fuskarta ya yi da hannunsa na dama yana kallonta ya ce“abubuwane suka riƙe ni, kin je Yolan?” girgiza masa kai ta yi kafin ta ce“ai baka dawo ba shiyasa ban je ba. Nanar ma kuma tana nan”
Da ɗan mamaki ya ce“really?”
Ta gyaɗa masa kai dai-dai sanda Mami ta ƙaraso wajen ta kalleshi tana murmushi ta ce“sannu da zuwa Daddy” murmushin shima ya mayar mata kafin ya ce“Yauwa ya gidan?”
“Alhamdulillah ya hanya?” Ta sake tambayarsa. Amsa mata ya yi sai kuma ya mayar da kansa ga Khadijah ya ce“ina ji fasa bikin aka yi data zo?” kafin ta yi magana Mami ta ce“daga zuwanka zata isheka da magana anan, ku shiga ciki mana” tura baki Khadijah ta yi ta ce“to Mami yaushe rabon dana ganshi.”
“Muje ciki sai ki bani labarin” Daddy ya yi maganar yana riƙe da hannunta, to kawai ta ce sannan suka nufi cikin gidan.
Nana na zaune a parlon ta yi shiru idanunta zube akan tv duk da ba fahimtar abin da ake yi take ba suka shigo, ta tashi da sauri tana gyara mayafin rigar jikinta. Sai da ya zauna kan sofa sannan ta masa sannu da zuwa, ya amsa da murmushi a fuskarsa kafin ya ce
“Nana yaushe rabon dana ganki?”
Murmushi ta yi tana sunkuyar da kanta. Ya kalli Khadijah ya ce“zo ki ci gaba da bani labarin” kallon Nana ta yi dake tsaye sai kuma ta zauna gefensa ta ce“tam Daddy” Nana ta dinga kallonsu tana tuna sanda take zama da Abba haka tana masa hira a duk sanda ya yi tafiya ya dawo. Ganin kuka na son kwace mata ya sanya ta yi excusing kanta ta bar parlon da sauri. Mami ta bita da idanu cike da tausayinta sai kuma ta kalleshi ta ce“da dai ka fara cin abinci sai ta baka labarin tunda yana da tsayi” Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“ai bana jin yunwa, na sauka a Abuja” to kawai Mami ta ce dan ta san babu abin da zai hana bada labarin kuma. Khadijah ta gyara zamanta ta fara bashi labarin duk abin da ya faru in details, tun daga farko har ƙarshe. Sosai Daddy ya yi mamaki, sannan kuma yaji tausayinta. Ya sauke numfashi yana ganin yanda Khadijah ke hawaye, da kansa ya goge mata hawayen sannan ya ce
“Ya isa haka. In sha Allah komai zai zo da sauƙi Mimi”
Cikin kuka ta ce“Daddy tausayin Nana nake..gaba ɗaya kamar ba ita ba, ko hira bama yi, kullum sai dai ta yi ta kuka. Kuma ta ce tana son ganin Abbanta da Ammarta, amma tana tsoron ta koma gidan Yaya Safwan da Aunty Zahra su nunawa kowa hotunanta.”
Girgiza kai Daddy ya yi ya ce“zata koma in sha Allah, babu abin da zai faru. Kira min ita” to kawai ta ce sannan ta ta miƙe tana shirin barin wajen shima ya tashi ya ce“ko barta. An jima sai muyi magana, let me take a bath” tom kawai ta ce sannan ta nufi saman da sauri. Ya sauke numfashi yana kallon Mami ya ce
“But why baki kirani kin faɗa min ba Amina?”
“Abun ne babu dadin ji. Shi yasa na kasa kiranka wallahi” girgiza kai Daddy ya yi ya ce“a’a wannan ba hujja bace, yanzu duk inda iyayenta suke suna can suna nemanta. Kuma hankalinsu ba zai taɓa kwanciya ba, sannan kuma Allah kaɗai ya san baƙin cikin da suka shiga na guduwarta. Sam bai kamata abar wannan maganar haka ba” shiru Mami ta yi dan ita ta rasa abin cewa, tabbas ta san iyayenta ba zasu ji daɗi ba, to amma da ace sun ga abin da zai ɗaga musu hankali na har ƙarshen rayuwa gara ace iya wannan suka gani. Daddy bai sake cewa komai ba ya nufi hanyar upstairs.
Khadijah na shiga ɗakin ta samu Nana zaune gefen gado ta haɗe kai da gwuiwa sai kuka take a hankali. Jiki a sanyaye ta ƙarasa gabanta ta dafata sannan ta ce“Nana ki daina kuka” kasa ɗago kanta ta yi Khadijah ta zauna gefenta ta jawota jikinta tana kukan itama ta ce“koda da ƙaddararsa a rayuwa, ki ɗauka wannan ita ce ƙaddararki. Kuma komai ya yi farko zai yi ƙarshe, nan bada jimawa ba in sha Allah komai zai shige kamar ba’a yi ba. Dan Allah ki daina kukan nan” Cikin shassheƙar kuka Nana ta ce
“Na sani Mimi. Amma ya zan yi? Zuciyata zafi take min kullum, na kasa yarda da cewa ni ce na zama haka. Na kasa yarda cewa ni ce na bar gidanmu saboda tsoron tonan asiri. Na kasa yarda cewa sir Junaid ya cutar dani, mutumin dana bawa yarda fiye da kowa. Mutumin da nake masa kallon wanda zai zama garkuwata, mutumin dana so nayi rayuwar aure dashi…” taja numfashi ta sauke sannan ta ci gaba da faɗin
“Ya cutar dani Mimi. Ya ruguzamin farin cikina, koda ace babu wanda ya san da wannan maganar a gidanmu da wane ido zan dinga kallon Yaya Safwan? Kullum zai yi tunanin ni ba mutuniyar kirki bace. Wallahi da zuciya ɗaya naje duba shi, ban yi tunanin zai iya aikata haka gareni ba!”
Khadijah ta sake ƙanƙameta tana kuka, ta kasa magana saboda tausayin Nana daya cikata, can dai da kyar ta ce“na sani Nana. Na san ba zaki taɓa aikata irin haka da gangan ba, kuma suma yan gidanku zasu san haka, sai dai kin yi kuskure tun farko, ba’a taɓa bawa namiji yarda, bai kamata ace kin je duba shi dan an ce miki bashi da lafiya ba, wannan ba daidai bane. Koda kuma ya kama dole sai kinje sai ki tafi da wani, amma kin fita ba tare da kowa ya sani ba, sannan kuma kin dawo kin musu ƙarya, iya wannan ya isa Allah ya jarrabeki Nana.”
Lumshe idanu Nana ta yi, hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce“sai yanzu nagane hakan, sai yanzu nagane bai kamata na yarda da namiji ba matuƙar ba muharramina ba, ina jin kamar mutuwa zan yi wlh Mimi. Idan na tuna abin da ya yi min sai naji bana son ci gaba da rayuwa, ina ma na mutu na huta kawai…” ta sake fashewa da wani raunataccen kuka. Shiru Khadijah ta yi tana kukan ita ma, after some minutes ta ɗagota tana goge mata hawayen fuskarta ta ce
“Kina ji ki daina kukan, kada ciwonki ya tashi. Bari naje na dawo” gyaɗa mata kai kawai Nana tayi, ta tashi ta fice daga ɗakin da sauri, ita kuma Nana ta kwanta kan gadon a hankali tana lumshe idanunta..
****
A fusace ya tura ƙofar parlon ya shiga, babu kowa a ciki sai tv dake aiki. Ya haura sama kai tsaye ya shige ɗakinta, tsaye ya sameta jikin mirror tana shafa mai, Ya saki handle ɗin kofar da ƙarfi wanda ya sanyata juyowa ta kalleshi.
“Doctor”
Ta ce a sanyaye, ganin yanda yake kallonta ya sanya ta sunkuyar da kanta. Haka kawai taji gabanta na faduwa, ya ƙaraso tsakiyar ɗakin yana ci gaba da kallonta cikin wata murya mai nuna zallar ɓacin ran da yake ciki ya fara cewa
“ashe daman zaki iya haka Zahra? Ashe zaki iya cutar da Nana ban sani ba?”
Da sauri ta ɗago kanta, lokaci ɗaya kuma ta shiga girgiza masa kai da hannayenta ta ce
“wallahi a’a ba zan iya ba doctor, ba zan iya ba, Nana kamar…”
Tsawa ya daka mata wadda ta tilasta ta yin shiru, Ya ɗan kalli gefensa na dama zuciyarsa cikeda tarin ƙunci da bakin ciki, sai kuma ya sake takowa har gabanta yana kallonta cikin ido ya ce“bana son na sake jin wata magana daga bakinki. Kin bani mamaki, koda wasa ban taɓa tunanin zaki iya aikata haka ba Zahra! Ban yi tunani ba, yanda yarinyar ta ɗaukeki tamkar ƴar uwarta wadda take iya fadawa sirrinta ashe ke ba haka ki ka ɗauketa ba. Har zaki iya fitar da hotunan da ki ka san zasu iya lalata mata rayuwa su ɓata mata suna a idon kowa, kin ji kunya!”
Zahra kasa cewa komai ta yi sai kuka da take kamar ranta zai fita, ta durƙushe a ƙasa tana wani irin kuka mai kunji ta ce
“na tuba doctor, wallahi na tuba ba zan sake ba. Ni kaina banso na fitar da hotunan nan ba, domin kamar amana ne Nana ta bani saboda ta yarda dani. Tana ganin ba zan taba faɗawa kowa ba, sai dai…” ta yi shiru saboda kukan daya ci ƙarfinta.
“Sai dai me?”
Ya daka mata wata irin tsawa wadda ta sanyata gigita. Girgiza kanta ta yi still crying ta ce
“Idan ban yi haka ba Siyama ba zata samu Safwan ba, ba zai aureta ba! Shiyasa nayi haka saboda na dakatar da aurensu.”
Girgiza kansa ya yi yana jin wani irin haushinta kamar ya shaƙeta ya ce“kenan saboda son zuciyarki ki ka aikata haka? Saboda ƴar uwarki ta aureshi?”
Shiru ta yi tana kukanta. Ya shiga zagaye ɗakin hannunsa goye a bayansa, can kuma ya tsaya cak yana kallonta daga inda yake ya ce
“Kin cutar da ita shi kuma Allah ya saka mata. Kin hanata auren mijin ƴar uwarki ta kuma auri mijinki. Babu buƙatar a yi miki wani hukunci, iya wannan kaɗai ya isheki ki gane irin abin da ki ka aikata. Ya isheki ki fuskanci Allah na kishin bawansa, tun da kin cutar da ita ne ba akan laifinta ba!”
Sake durƙushewa Zahra ta yi tana ƙara sautin kukanta, tabbas Allah ya nuna mata ishara. Ya kuma sakawa Nana tun a duniya, ta miƙe da kyar tana ci gaba da kuka ta nufi inda yake. Da hannu ya dakatar da ita, idanunsa kamar garwashi saboda jan da suka yi ya ce
“kar ki kuskura! Stay away from me!”
Cikin kuka ta ce“dan Allah ka yi haƙuri, ka yafe min wallahi ba zan sake ba. Na sani na cutar da Nana kuma zan nemi yafiyarta, dan Allah doctor ka yi haƙuri kada ka ce zaka gujeni”
Cije laɓɓansa ya yi yana jin da ace duka ɗabi’arsa ce to babu abin da zai hana shi dukan Zahra. Ya ja dogon numfashi ya sauke yana ƙoƙarin saita kansa ya ce
“ni ki ka yiwa laifi?”
Girgiza masa kai ta yi, ya gyaɗa kansa sannan ya ci gaba da fad’in “to akan me zaki nemi yafiyata?.”
Shiru Zahra ta yi tana kallonsa hawaye sai zuba yake daga fuskarta kamar an buɗe famfo. Ya tako kusa da ita har tana jin sautin fitar numfashinsa ya ce
“Yarinya ce ƙarama. Yarinyar da bata gama sanin ciwon kanta ba, amma ke da girmanki da kuma hankalinki ki ka cuceta, ki ka mata zamba cikin aminci. Ki sani kar ki ɗauka iya hukuncin kenan, idan har Nana bata yafe miki ba to wallahi tallahi kin ji har na rantse babu ni babu ke!”
Manage this pls, I’m not feeling well????.
Ya ƙare maganar yana jefa mata wani mugun kallo, sunkuyar da kai ta yi tana shessheƙar kuka. Ya ratsa ta gefenta ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama, da idanu Zahra ta bishi sai kuma ta sulale a ƙasa ta rufe bakinta da hannunta tana kuka a hankali. Yana fita apartment ɗin Hajiya Babba ya nufa. Koda ya shiga bai samu kowa a parlon ba, dan haka ya haye sama. A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar, ya hangeta zaune gefen gado tana jan cazbaha a hankali. Numfasawa ya yi sannan ya karasa ciki, Hajiya Babba ta dinga kallonsa har ya zauna a gefenta. Ganin bai ce komai ba ya sanya ta dafa kansa ta ce
“Lafiya dai?”
Madadin ya amsa mata sai kawai taga ya shige jikinta, ya dinga sauke ajiyar zuciya a hankali. Ajiyar zuciyar ita ma ta sauke kafin ta sanya hannunta cikin sumar kansa ta fara hargitsata a hankali. Numfashi ya dinga saukewa yana jin wata nutsuwa ta musamman na saukar masa, ya dinga jin duk ƙunci da damuwar zuciyarsa na narkewa. Sun ɗauki mintuna masu tsayi a haka kafin ta ɗago kansa tana faɗin
“mene ne?”
Girgiza mata kai ya yi dan ya san bashi da hurumin sanar da ita abin da ke damunsa yanzu, dan shi ne wanda ya jawo komai. Ya sauke numfashi kafin ya ce
“bakomai Hajiya”
Kallonsa ta dinga yi sanin ƙarya ba ɗabi’arsa bace yasa ta girgiza kanta ta ce“Abdusammad kenan. Na san halinka fiye da kowa, ko ka manta ni na haifeka? Fuskarka ta nuna akwai damuwa a tare da kai, faɗa min mene ne.”
Ta ƙare maganar tana riƙe hannunsa na dama. Murmusawa ya yi cike da son kawar da zancen ya ce“Hajiya babu komai fa, kawai ina tunani ne akan Nana. Abba ya damu da ita fiye da ƙima, kawai yana sharewa ne, so ina son sanin inda take naje na dawo da ita gida.”
Zazzafan numfashi ta furzar kafin ta ce
“nima da tunanin yarinyar nan nake kwana nake tashi. Duk da ta ɓata mana sunan dangi hakan ba zai sa mu fasa nemanta ba, na tabbata yarinta da rashin jin magana sune suka yi tasiri a tare da ita har taje ta aikata abin da tayi.”
Shiru Abdusammad ya yi dan shi ya san abin da ya faru kuma bashi da niyyar sanar da kowa yanzu har sai sanda yarinyar ta dawo. Dan haka ya jinjina kansa ya ce
“nima i think so.” ya sauke ajiyar zuciya yana miƙewa tsaye ya ce“Allah ya kyauta”
Da Amin ta amsa tana kallonsa ganin ya tashin ta ce“tafiya zaka yi?”
Gyaɗa kansa ya yi ya ce“Eh. Zan je wajen Aliyu ne”
“Tam ka gaishe shi” ta ce tana ci gaba da jan cazbahar hannunta.
****
Da daddare suna zaune a parlon bayan sun gama cin abinci Daddy ya kalli Khadijah da ke kwance jikin Mami ya ce“Mimi je ki kira min Nana” to kawai ta ce sannan ta tashi tana gyara zaman hular sanyin kanta ta nufi upstairs. Miƙewa Adeel ya yi yana danna wayarsa, Daddy ya kalleshi ya ce
“son idan Allah ya kaimu gobe ka fita da wuri zaka yankar mana ticket”
Zare airpode ɗin kunnensa ya yi yana kallonsa ya ce“Daddy wata tafiyar kuma?”
Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“a’a zan je Yola ne”
“But ai da ka bari ka huta ko zuwa next week ne”
Adeel ya yi maganar a dame. Daddy ya ce“No dole naje gobe, ba abun da za’a ci gaba da jira bane” Adeel bai ji daɗi ba ganin Daddy na son stressing kansa. amma sanin bai isa ya hana shi ba ya sanya ya ɗaga kafaɗa ya ce
“anyway. Allah ya kaimu lafiya”
Bai kuma tsaya jiran amsarsa ba ya bar parlon. Mami ta bishi da kallo sai kuma ta mai da Idanunta kan Daddyn ta ce“Nima dai har zance ka bari sai next week ɗin” babu yabo babu fallasa ya kalleta ya ce“sai a ci gaba da zama da yarinya bayan ba’a san matsayin da take ba? Iyayenta na faman nemanta”
Girgiza kai Mami ta yi. Ya ce“to kin ga dole ne na mayar da ita ga iyayenta, da ina nan ma ba zan bari ta yi wannan satikan ba” Mami ta numfasa ta ce“Tom shikenan Allah ya kaimu goben lafiya” Dai-dai nan suka dawo parlon. Khadijah ce a gaba sai Nana dake biye da ita, ta zauna a ƙasa tana gyara zaman hijabin jikinta, Girgiza kai Daddy ya yi ya ce
“No! No! Tashi a ƙasa”
A sanyaye ta tashi ta zauna kan kujera idanunta a ƙasa. Khadijah ta koma kusa da shi ta zauna tana jingina da jikinsa wanda ya zame mata dabi’a. Numfasawa Daddy ya yi kafin ya mai da hankalinsa kan Nanar ya fara magana a nutse.
“Nana na kira ki saboda na miki magana akan abin da Khadijah ta faɗa min ɗazu. Garin ya aka yi haka ta faru Khadijah? Mene ya saka ki ka yarda da namiji? Baki san illar dake cikin hakan ba?”
Tuni hawaye suka fara zuba kan kyakkyawar fuskarta. Ta sanya hannunta ta goge cikin shessheƙar kukan ta ce
“Tsautsayi Daddy. Wallahi ban yi tunanin zai min haka ba, kawai na san ina son shi, kuma ina son na aure shi. Amma ban yi tunanin zai iya cutar dani ba, haka ita ma Aunty Zahra ban yi tunanin zata yi amfani dasu wajen cutar dani ba. Na san ban aikata abin da ya dace ba, amma ni na ɗauka hakan da nayi shi ne daidai.”
Ta yi shiru kuka na kwace mata. Girgiza kai Daddy ya yi still looking at her ya ce“ya isa haka. Daina kuka, duk abin da ya faru ya riga da ya faru, ƙaddara ce wadda ba’a guje mata. Duk da kin yi wawta da yarinta amma wannan ba zai zama matsala ba, in sha Allah gobe zan mayar dake gida!”
Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi, sai kuma ta fara girgiza kai tana kuka ta ce“a’a Daddy, dan Allah ka yi haƙuri. Tsoro nake ji, wallahi tsoro nake ji, Yaya Safwan yace sai ya faɗawa kowa idan har na dawo” ta ƙare maganar tana fashewa da kuka. Tashi Mami ta yi ta koma kujerar da take zaune ta riƙeta, Nana ta faɗa jikinta tana sakin wani marayan kuka. Shiru Daddy ya yi yana kallonsu can kuma ya ce“it’s enough. In sha Allah gobe zan mayar dake, kuma babu abin da zai faru, ni zan fahimtar dasu”
Cikin kuka Khadijah ta ce“Daddy idan kuma kowa ya ga hotunan fa?”
“To ai dole sai an gani ko nan kusa ko kuma nesa, idan haka ne kin ga ɓoyewar bashi da wani amfani”
Shiru Khadijah ta yi tana sharar hawaye. Ya mai da kallonsa ga Nana ya ce“Zo nan” sakinta Mami ta yi ta miƙe a sanyaye ta koma inda yake, gefensa na hagu ta zauna ya dafata cikin son kwantar mata da hankali ya ce
“Babu abin da zai faru kin ji. Ba zan bari kowa ya taɓa ki ba, ba zan bari su ji haushin ki ba. Amma ai na san kina son ganin Mamarki da Abbanki ko?”
A sanyaye ta gyaɗa masa kai sai kuma ta ce“eh Daddy Ina son na gansu, amma ina tsoron Yaya Safwan da Aunty zahra.”
Murmushi Daddy ya yi ya ce“to ki daina tsoron kowa. In sha Allah komai ya zo ƙarshe, zamu zauna dasu gobe a san yanda za’a yi kinji” gyada masa kai ta yi, Ya sanya hannunsa ya share mata hawayenta sannan ya ce“tashi ki je ki kwanta” Toh kawai ta ce sannan ta tashi a sanyaye ta haye. Khadijah ta miƙe tana shirin bin bayanta ya ce“ku kwanta da wuri saboda da wuri nake son mu tafi yanda zamu tadda kowa a gida” ta amsa masa da toh sannan tabi bayansa. Sai da suka bar wajen sannan ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Mami ya ce“ta bani tausayi, she’s still young girl” gyaɗa masa kai ta yi sannan ta ce“sosai. Dan ko Mimi ta girmeta, she’s just 17 fa” Daddy ya girgiza kansa ya ce“shiyasa, sam bata da wayo” Jinjina kai Mami ta yi ta ce“Eh nima na lura da haka.”
Koda suka shiga ɗakin zama suka yi suka ci gaba da rera kukansu a tare. Sai da suka yi mai isarsu sannan suka yi shiru dan kansu, Khadijah ta ce“Daddy ya ce mu kwanta da wuri yanda zamu iya tashi da wuri” toh kawai Nana ta ce a sanyaye sannan ta kwanta a hankali tana lumshe ido. Khadijah ma kwanciyar ta yi a ɗaya side ɗin dan daman sun gama shirin kwanciyar ta ja duvet ta rufe jikinta.
****
Da idanu ya dinga kallonsu sai kuma ya ɗauke kai, Aliyu ya kalli Maimoon dake tsaye a jikinsa ya ce“zaki iya shiga gidan?” gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh Yaya” Ya saketa sannan ya ce“Tom jeki ki huta kafin nazo” ta gaishe da Abdusammad ya amsa sama-sama sannan ta shige gidan. Sai da yaga ta bar wajen sannan ya gyara tsaiwarsa yana ƙarewa compound ɗin kallo iska mai daɗi sai kaɗawa take a hankali, Ya ɗan yi jim sai kuma ya kalli Aliyu wanda ke ta murmushi fuskarsa kamar gonar auduga, Ɗan mitsi-mitsi ya yi da idanu ya ce
“Lafiyarka dai?”
Madadin ya bashi amsa sai kawai ya ga ya ruƙunƙumeshi yana dariya, Abdusammad ya riƙe hannunsa ya ce“A’a wallahi nutsu, kar ka illatani” ɗago kansa yayi yana murmushi ya ce
“Buddy guess what?”
Ɗan juya idanunsa ya yi sai kuma ya ce“ni ban gane ba, kawai ka faɗa min”
Aliyu ya fara jan fingers ɗinsa kamar mace ya ce“soon zan zama father”
Ware idanu Abdusammad ya yi, lokaci ɗaya kuma ya saki wani kyakkyawan murmushi wanda ya daɗe bai yi irinsa ba. Ya kai masa duka yana fadin “amma kai akwai ɗan iska wallahi, har yaushe aka kawo maka yarinyar har ka mata ciki?” Harararsa Aliyu ya yi kafin ya ce“to mene ne a ciki? Ba dai matata bace?”
Ɗauke kai Abdusammad ya yi ya ce“ɗan iska kawai. Daman ni tun da naga kana wani maƙalƙale mata baka ko fita waje na san ba zaka shuka abin arziki ba. Kawai ka saka yarinya ta rainaka”
Tuntsirewa da dariya Aliyu ya yi sai kuma ya ce“nima kenan, kai naga yanda zaka yi”
Haɗe rai Abdusammad ya yi kamar bashi ba ya ce“kamarya ni? Da aurena da mutunci na” Dariya Aliyu ya yi ya ce“kai mana. Allah ne kaɗai ya san abin da zaka yiwa ƴar rainon taka idan an kawota, wa yaga show”
Wani mugun kallo ya watsa masa, ya ƙara masa da harara sannan ya yi tsaki ya ce”aikin banza. Kai daɗina da kai baka da hankali wani lokacin”



