Chapter 3: Chapter 3
Abba da kansa ya kai ta motar ya kwantar da ita sannan ya rufe ƙofar yana faɗin”take care son” Sultan ya yi murmushi ya ce”in sha Allah Abba” daga haka ya shige motar ya juya ya bar compound ɗin. Sai da suka fita daga estate ɗin gaba ɗaya sannan ya yi parking, ya juyo yana kallonta fuskarsa a haɗe kamar bai taɓa dariya ba ya ce”
“Malama rufe min baki, sai shegen son jiki ki ka ajiye, ki tashi zaune tun kafin ranki ya ɓaci” Nana ta dinga kallonsa hawaye na biyo kan fuskarta, daman tasan haka zai yi mata idan sun rabu da Abba. Kwafa ya yi ganin bata tashin ba ya juya ya ci gaba da driving ɗinsa. A babban parking space ɗin specialist hospital yola ya yi parking motar, ya sauka ba tare da ya kalleta ba. Sai da ya fito sannan ya buɗe back seat ɗin ya dinga kallonta, kwance take kamar matacciya sai sauke numfashi take. Ya gyara tsaiwarsa sannan ya ce”sakko” shiru ta yi masa ba dan bata ji maganar tasa ba, sai dan ba zata iya bashi amsa ba. Ya ɗan haɗe rai ya ce”ina magana da gunki ne Nana?” sai a sannan ta ɗago kanta, tana kallonsa da idanunta wanda suka kumbura ta ce”wallahi Yaya ba zan iya tafiya ba” ta yi maganar da iya gaskiyarta, baki buɗe Sultan ke kallonta sai kuma ya ce”to yanzu ya ki ke son nayi miki?” madadin ta bashi amsa kawai sai ta sake fashewa da wani sabon kukan, tana dafe mararta. Ganin da gaske take ya sanya ya zura kansa cikin motar ya jawo hannunta. Ya fito da ita daga motar, ganin ta yi baya zata faɗi ya sanya ya jawota jikinsa ya riƙeta sosai. Ƙoƙarin rufe motar ya yi idanunsa ya sauka akan kujerar ganin yanda gaba ɗaya ta ɓaci da stain, ya girgiza kansa sai kuma ya mai da idanunsa kanta, ya rufe motar sannan ya janyeta daga jikinsa ya jingina da motar gudun kada ta ɓata masa jiki. Idanunta a rufe yake tana sauke numfashi dakyar ko ba’a faɗa maka ba kasan ba ƙaramar wahala take sha ba. Sosai ta bashi tausayi dan hakan ya kwantar da muryarsa cikin sanyi ya ce” ki daure ki taka kinji, kin ga jikinki ya ɓaci da sai na ɗaukeki” shiru tayi har sannan bata daina hawaye ba, ya sake cewa “Nana”
Gyaɗa masa kai kawai ta yi sannan ta buɗe idanun nata, hannunta ya riƙe suka fara tafiya a hankali har suka shiga cikin reception na asibitin. Gaisheda shi nurses suka fara yi, ya dinga amsawa cike da fara’a. Wata nurse ya samu ya ce ta raka Nana ɗaki yana zuwa, ta riƙe hannunta sannan ya nufi hanyar office ɗinsa.
****
Ƙarfe 8:20am Aliyu ya shigo parlon, zaune ya samesu suna breakfast, ya ƙarasa yaja kujera ya zauna idanunsa zube kan Hajiya Babba ya ce”ina kwana Hajiya?” Da murmushi a fuskarta ta ce”lafiya kalau Aliyu ka tashi lafiya?”
“Alhamdulillah” ya ce a takaice.
“Good morning Yaya”
“Good morning Bro”
Suka gaida shi a tare, ɗago kansa ya yi ya kallesu. Hameed ne da Safwan, ya ɗan yi murmushi sannan ya ce”morning ya kuke?”
“Alhamdulillah” Cewar Hameed yana miƙewa. Kallonsa duk suka yi kafin Aliyu ya ce”ina kuma zaka je?” Hameed ya ce”wallahi Bro I have alot to do ne a office, shiyasa nake sauri na tafi” jinjina kai Aliyu y yi sannan ya ce”Alright a dawo lafiya” Amin ya ce sannan ya mai da idanunsa kan Hajiya ya ce”Sai na dawo Hajiya”
“Allah ya bada abin da ake nema”
Ya amsa da murmushi sannan ya dafa Safwan ya ce”Barrister sai na dawo” harararsa Safwan ya yi sannan ya ce”Judge a dawo lafiya” dariya suka yi duka sannan ya juya ya bar wajen. Aliyu ya bishi da kallo har ya fita sannan ya ce”sometimes idan Hameed na yin abubuwa sai naga kamar Buddy wallahi” Safwan ya ajiye spoon ɗin hannunsa yana cewa”wallahi nima haka Yaya, irin halayensu ɗaya, kawai dai Yaya ya ɗan fisa rashin son hayaniya” Aliyu ya ce”Eh shi ne kawai abin da ya raba su, shi Buddy baya wasa, shi kuma Hameed yana son wasa” Safwan ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce”Wai yaushe zai dawo Yaya? Wallahi we miss him alot” Ɗan murmushi Aliyu ya yi sannan ya ce”to sai dai ka tambayeshi dan ni ban sani ba” Safwan ya tashi yana cewa”Ni babu ruwana” dariya kawai Aliyu ya yi, Hajiya da ke cin abincinta tun ɗazu ta ce”zai maka faɗa ne dan ka tambayeshi?”
Safwan ya ce”Hajiya kin fa san halin kayanki, yanzu sai ya ciremin supsidy”
Murmushi irin na manya ta yi ta ce”kuna gulmarsa sai na kira shi na faɗa masa” haɗe hannaye Safwan ya yi kamar zai yi kuka ya ce”Allah ya huci zuciyarki Hajiya Babba mai makkah da Madina, sai na dawo” daga haka ya yi gaba yana faɗin”Yaya sai na dawo” Allah ya tsare Aliyu ya ce yana murmushi. Hajiya Babba ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Aliyu ta ce”yaushe ya ce maka zai dawo?” sai da ya yi sipping ruwan dake hannunsa sannan ya ajiye cup ɗin ya kalleta cike da nutsuwa ya ce”cewa ya yi wai abubuwa sun yi masa yawa yanzun, amma zai duba ya gani” Hajiya ta yi shiru ba tare da ta sake cewa komai ba, sai dai yanayinta gaba ɗaya ya sauya. Lura da hakan ya sanya Aliyu ya dafa hannunta cikin sanyin murya ya ce”don’t worry Hajiya, ni zan saka ya dawo in sha Allah” jinjina masa kai kawai ta yi sannan ta tashi ta bar wajen, ya bita da idanu sai kuma ya girgiza kansa.
****Ƙarfe 2:15 na rana ya turo ƙofar ɗakin, kwance take kan gadon ta rufe idanunta. Ya ƙaraso ya tsaya a gabanta, kallonta ya dinga yi ganin how beauty she’s da take baccin, ya ɗan yi murmushi yana jin wani sabon so da ƙaunarta a cikin zuciyarsa, idan har ba’a aura masa Nana ba bai san halin da zai shiga ba. Yanzu idan ba ita aka zaɓa masa ba fa? ya yi tambayar cikin zuciyarsa, kawar da tunanin ya yi yana jin ƙirjinsa na wani irin zafi. Ya sunkuya ya taɓa wuyanta, babu zafi sosai sai ɗan ɗimi da ba’a rasa ba. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya juya zai bar ɗakin
“Yaya Sultan”
Yaji ta kira shi a hankali, juyowa ya yi yana kallonta ba tare da ya amsa ba, ganin yanda ya kafeta da idanu ya sanya ta ɗan sunkuyar da kanta a sanyaye ta ce”ka maidani gida” wani irin kallon rainin hankali ya dinga yi mata kafin ya harɗe hannayensa a ƙirji still looking at her ya ce”idan naƙi fa?” shiru ta yi bata bashi amsa ba, ya zabga mata wata uwar harara sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Sai a sannan ta ɗago kanta tana murguɗa masa baki a fili ta ce”tun da dai nasan hanya sai nayi tafiyata” daga haka ta sake komawa ta kwanta tana lumshe idanu, tun gurin asuba sai yanzu taji mararta ta yi sauƙi, shiyasa take mugun tsoron ganin ƙarshen wata ya yi dan idan ta tashi menstruation ɗaiɗaikun mutane ne da ba zasu sani ba a cikin estate ɗin su, dan ciwo take kamar me naƙuda. Koda a ce tana Aun to sai an dawo da ita gida ko kuma Abba ya sanya Sultan ɗin yaje ya dubata a can.
Tana nan kwance after 10mins wata nurse ta shigo, kallonta ta yi fuskarta cike da fara’a ta ce”Nana ya jikin?” ɗan murmushi ta yi ta ce”da sauƙi sister Zahra” Nurse ɗin ta gyaɗa kai ta ce”ai gashinan nagani, dan ɗazu da alama bakisan inda kanki yake ba, kedai sannu. Kina cikin irin matan da ake jarraba da ciwon mara yayin al’ada, ciwo kamar na haihuwa” langwaɓar da kai Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce”wallahi sister Zahra ji nake kamar zan mutu, ni dama bana period wallahi! Daman ni juya ce!” Tuntsirewa da dariya Zahra ta yi, Nana ta dinga kallonta sai kuma ta haɗe rai dan ta tsani a dinga mata dariya. Sai da tayi mai isarta sannan ta ce”Ban da shirme irin naki Nana wane ya ce miki juya bata period?” tura baki ta yi ta ce”nima haka naji”
“Ki ka ji a bakin wa?”
Zahra ta tambayeta, ɗauke kai ta yi ba tare da ta bata amsa ba. Sanin tun da tayi hakan ba magana zata yi ba ya sanya ta ce”Daman doctor ya ce nazo na tafi dake” bata ce komai ba ta sakko daga kan gadon, mayafin rigar data gani a gefen gadon ta ɗauka ta yafa sannan ta yi waje ba tare da ta sake bi ta kan Zahra ba, murmushi kawai Zahra ta yi sannan tabi bayanta.
Tsaye ta sameshi a reception suna magana da wani likitan, ya dinga kallonta fuskarsa babu alamar walwala ya ce”kin zo kin shige ko sai na makeki anan wajen” tura baki ta yi sannan ta nufi hanyar fita daga asibitin tana tafe tana waiwayensa, ganin bai tawo ba ya sanya tana fita daga ƙofar reception ɗin taja ta tsaya kusa da wata flower. Ta dinga kalle-kallen sauran flowers ɗin da aka ƙawata wajen dasu, cike da sha’awa.
Tun daga nesa yake kallonta da mamaki fal akan fuskarsa, he just can’t believe ace ita yake gani, kasa jurewa ya yi ya nufi inda take tsaye da sauri har yana tuntuɓe, daga gefenta ya tsaya ya harɗe hannayensa a ƙirji cikin shaky voice ya ce
“Nana!”
A ɗan firgice ta kalli side ɗin dan bata san da mutum a tsaye ba, sai dai wanda ta gani ya sanya ta ɗan ja baya. Murza idanunta ta yi ko mafarki take amma koda ta sake buɗesa shi ta gani tsaye gabanta cikin kyakkyawar shigarsa sai murmushin da yake ƙara masa kyau yake. Girgiza kanta ta dinga yi nan take hawaye ya cika idanunta, muryarta na rawa ta ce”si…sir…sir Junaid!” sake faɗaɗa fuskarsa ya yi duk da yanda yake jin ransa a cunkushe ya ce”Nana, kin gani ko?mena faɗa miki? Idan har ke rabona ce zan sake ganinki, and gashi na ganki that’s means we destined to be together.”
Kuka ta fara yi, kuka na farin ciki bana baƙin ciki ba, kukan da ke nuna irin so da ƙaunar da take masa, cikin shessheƙar kuka ta ce“sir daman zan sake ganinka? kana can kana rayuwarka ko?”
Saita nutsuwarsa ya yi jin kukan na neman kwace masa shima, ya ce“ina can cikin begenki da kuma tunaninki Nana, bana iya baccin yanda ya kamata. Kullum tunanina yanda zan samu haɗuwa da ke, Nana ki bani dama nazo gidanku, ki bani dama na gabatar da kaina a wajen iyayenki, na tabbata zasu karɓeni” fashewa ta yi da kuka tana ci gaba da kallonsa, she wish zata iya bashi wannan damar, ta juya tana kallon ƙofar reception ɗin gudun kada Sultan ya fito. Ganin bata ganshi ba ya sanya ta juyo tana kallonsa ta ce“Sir baka gane halin da nake ciki ba ko? Baka gane abin da nake ta faɗa maka ba ko? They won’t allow me! Ba zasu taɓa barina da kai ba ni na sani…”
“Amma ai baki gwada ba Nana! At least give it a try, koda sau ɗaya ne ki gwada faɗa musu kina da wanda ki ke so, ki gwada sanar dasu abin da ke cikin ranki ki ga”
Ta dinga kallonsa amma ta kasa cewa komai, numfasawa ya yi sannan ya sake cewa“me ya kawo ki asibiti?” a ɗan rarrabe ta ce“da…da Yayana muka zo”
“Ba dai shi zaki aura ba?”
Junaid ya yi tambayar a sanyaye, girgiza masa kai ta yi, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce“yanzu ina zan sake ganinki Nana? Akwai abubuwan da nakeson faɗa miki” shiru ta yi kamar me tunani, Junaid ya sake faɗin
“ko zaki je gidan Aunty ɗinki? Sai mu haɗu acan”
Da sauri ta kalleshi dan ta gane in da yake nufi, sun saba haɗuwa acan idan taje hutu daga Aun.
“Kin yi shiru Nana”
Muryarta na rawa ta ce“But sir…”
Katseta ya yi ta hanyar faɗin “just for me Nana, saboda ni!”
Ta runtse idanunta tana jin zuciyarta nayi mata wani irin suya,
“Nana ko…”
“shikenan I’ll”
Ta faɗa tana goge hawayen fuskarta wasu na sake zubowa, ɗan murmushi ya yi sannan ya ce“thank you, yaushe zaki je, gobe?”
“zan kiraka ranar da zan je, cause ba za’a bar ni na fita ba gobe”
Ta faɗa a sanyaye. Junaid ya dinga kallonta yana jin kamar ya tafi da ita amma sanin hakan ba mai yiwuwa bane ya sanya ya ce“okay, zan jira kiran ki” gyaɗa masa kai kawai ta yi, ya sauke numfashi ya ce“i love you Nana”
Kuka na ƙoƙarin kwace mata ta ce“love you too sir”
Juyawa ya yi ya bar wajen da sauri jin hawaye na ƙoƙarin zubo masa. Ta dinga bin bayansa da kallo har ya nufi parking space ɗin asibitin.
“Nana!”
Muryar Sultan ta daki kunnuwanta, sai da ta ɗan firgita, ta sake goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta juya tana kallonsa. Bin ta ya dinga yi da kallo sai kuma ya taɓe baki, bai ce komai ba ya kama hannunta suka nufi hanyar fita daga asibitin, mamaki ya sanya ta kasa yin shiru duk yanda take jin zuciyarta a dagule ta ce“Yaya ina zamu je? Where’s ur ride?”
Cak taga ya tsaya, ya saki hannunta ya juyo yana kallonta fuskarsa a tamke kamar bai taɓa dariya ba ya ce“which ride? Bayan motar da ki ka gama ɓata min da ƙazanta” Saurin kallonsa ta yi ya gyaɗa mata gira, ta sunkuyar da kanta tana jin wata irin kunya na rufeta, she wish ma bata tambayeshi ba, da wannan amsar daya bata. Lura da yanda jikinta ya yi sanyi ya sanya ya ci gaba da tafiya yana ɗan murmushi, ta dinga bin sa a baya kamar babu laka a jikinta.
Napep ya tsaida musu ya shiga ciki, ganin yanda ta tsaya yasa a fusace ya ce“sai nazo na ɗauke ki ne?” bata ce komai ba ta shiga ta zauna ta takure jikinta a gefe ɗaya ta zuba uban tagumi, ya kalleta sai kuma ya dauke kansa. Sai da suka zo off Girei road sannan ya sauka daga napep ɗin ya tsallaka ya shiga wani eatery dake ɗaya side ɗin, har ya dawo bata san ya fita ba dan zuciyarta tana can gurin masoyinta Junaid, tun da suka rabu take tunaninsa, tana jin ina ma ta bishi sun tafi tare.
“Keee!”
Sultan ya yi maganar yana kallonta, da sauri ta karɓi ledar da yake bata murya a sanyaye ta ce“an gode”
“me ki ke tunani?”
Girgiza kanta ta yi ta ce“babu komai” taɓe baki ya yi bai sake bi ta kanta ba har me napep ɗin ya yi parking a bakin estate ɗin. Sauka suka yi ya miƙa masa kuɗin sannan ya nufi ciki, ta dinga bin sa a baya kamar raƙumi da alaka har suka kawo gidansu dan shi ne a farko sannan nasu Sultan, tsayawa ya yi yana kallonta ya ce“tafi gida to” bata ce komai ba ta juya ta nufi ƙofar ta dinga knocking, sai da yaga ta shiga sannan ya yi gaba shi ma.
Amma ta dinga kallonta kafin ta ce“sannu ya jikin?” murya a sanyaye ta ce“da sauƙi” daga haka ta dire ledar akan table ta nufi hanyar ɗakinta. Koda ta shiga ciki zare Abayar dake jikinta ta yi, ta ajiye kan drawer ta kwanta kan gadonta tana sauke numfashi. Duk da yanda ta gaji amma kasa bacci ta yi, tunanin Junaid yaƙi barinta, ko dai ta gwada abin da ya ce mata? Ta dinga saƙa haka aranta har bacci ɓarawo ya saceta. Koda aka yi la’asar Amma ta shigo ta sameta a zaune kan ladduma, hakan yasa bata sake ce mata komai ba ta juya ta fita, haka ta ƙarasa yinin ranar sukuku kamar wadda aka zane, ko wajensu Maimoon da take zuwa kullum bata je ba. Haka ma gurin Hajiya Babba.
Around 8:00 na dare Abba ya shigo ɗakin da kansa, kwance ya sameta ta yi shiru tana tunani, ya zauna gefen gadon ya taɓa fuskarta yana faɗin “ya jikin naki?” tashi tayi zaune sannan ta ce”Abba sannu da zuwa” yawwa ya ce, sannan ya miƙa mata ledar dake hannunsa. Karɓa ta yi t dinga kallon ledar kafin ta sanya hannunta ta buɗe, kwalin waya ta gani ta zaro tana murmushi, iphone 13pro max ce sabuwa, ta saki wani irin ihu tana rungumeshi. Dariya kawai Abba ya yi ya ce“now you are happy ba?” gyaɗa masa kai ta yi tana sake rungumeshin ta ce“thank you so much Abbana, Allah ya biya maka buƙatunka na Alkhairi, ya baka abin da ka ke nema, ya jiƙan iyayenka, ya faranta maka yanda ka ke faranta min”
Murmushin jin daɗi ya yi, wannan shi ne dalilin daya sanya baya gajiya da yiwa tilon ƴar tasa abu, koda abin dole ne akansa idan har ya yi mata sai ta yi masa irin wannan addu’ar. Ya shafa kanta cike da so da ƙauna ya ce“Amin ya hayyu ya Ƙayyum Khadijah, kema Allah ya yi miki albarka” ɗago kanta ta yi tana cewa“Amin Abbana” daga haka ta mayar da kwalin ledar ta sauka daga kan gadon tana faɗin “bari naje na nunawa su Maimoon” murmushi kawai Abba ya yi sannan ya tashi ya fito daga ɗakin, da gudu ta yi waje saboda jikinta har rawa yake taje ta nuna musu wayarta.
Ta kusa kai wa gidan haske ya ɗauke, ko ina na gidan ya yi wani irin duhu, wani irin tsoro taji ya kamata, da alama solar ce ta samu matsala dan su basu san wutar nepa ba. Tun da suka tashi bai fi sau uku ta taɓa ɗaukewa ba, shi ma kuma by mistake ne sai kuma yau. Rasa yanda zata yi tayi, dan duhu na ɗaya daga abin da take tsoro a rayuwarta. Ta dinga juyi a wajen ta kasa gaba ta kasa baya, ledar hannunta ce ta fadi ƙasa ta sunkuyar da sauri tana lalubenta, dakyar ta sameta tana ɗago kanta taji ta a gaban mutum, ihun ta buɗe baki zata yi taji an rufe mata bakin, ya fizgota ta fado jikinsa. Tsabar yanda ta tsorata ya sanya ta sume a wajen daidai nan hasken ya dawo ko ina ya yi tarr dashi.
Sultan ya dinga kallon fuskarta yana murmushi, sakinta ya yi faɗi a wajen sannan ya buɗe gorar ruwan dake hannunsa ya tsiyaya mata shi tas, a firgice ta buɗe idanunta tana sauke ajiyar zuciya saboda sanyin ruwan data ji. Ganin ƙaton mutum ta yi tsaye akanta fuskarsa babu yabo babu fallasa, sanye yake da ƙananun kaya hannunsa riƙe da empty bottle ɗin sai kuma ledar takeaway. Ganin yanda take kallonsa baki buɗe ya sanya ya ce”kin tashi anan ko sai nabi ta kanki na wuce” tura baki ta yi sannan ta tashi tana kaɗe jikinta murya can ƙasa ta ce”saboda mugunta”
“Me ki ka ce?”
Sultan ya tambayeta yana kafeta da idanu, girgiza kanta ta yi tana ɗaukar ledar wayarta ta ce”ni ba magana nayi ba” daga haka ta juya ta ci gaba tafiya. Da kallo ya bita har ta tura ƙofar ta shiga, ya sauke numfashi sannan ya nufi part ɗin Hajiya Babba. Zaune ta samesu a parlon suna kallo, kusan kowa na gidan yana nan, Maimoon, Juwaira, sai kuma Suhaila. Tana ganinta ta tashi tana cewa”kece da daren nan?” gyaɗa mata kai Nana ta yi sannan ta ce”eh abu nazo nuna miki”
“Na ganki a jiƙe? A wannan sanyin”
Maimoon ta tambayeta ganin yanda take rawar sanyi, kamar zata yi kuka ta ce”to ba Yaya Sultan bane ya watsa min ruwan sanyi” da mamaki Maimoon ta ce”me ki ka masa? Kema ki ci gaba da shiga harkarsa”
Tura baki ta yi tana zama kan sofa ta ce”to ni harkarsa na shiga, kawai fa wuta ce ta ɗauke shi ne naji tsoro ashe shi kuma yana wajen, shi ne ya watsa min ruwa”
Taɓe baki ta yi ta ce”ikon Allah. Me zaki nuna min?”
Ledar hannunta ta miƙa tana washe baki ta ce”Abba ya bani ɗazu”
Maimoon ta buɗe ledar ganin kwalin waya ya sanya ta saki ihu tana dariya ta ce”woww irin wayar Hameeda” gyaɗa mata kai Nana ta yi ta ce”nima haka nace, yanzu ya bani nace bari nazo na nuna miki” .
Maimoon ta dinga juya wayar fuskarta ɗauke da mabayyanin farin ciki ta ce”wallahi na taya ki murna ke kam, daman ni ce nake da waya”
A ɗan dame Nana ta ce”wai har yanzu Yaya Sultan bai bari kin yi waya ba?”
“Wallahi ya hanata, kuma muma ya hana mu”
Juwaira ta bata amsa daga zaunen da take. Kamar su ɗaya da Maimoon sai dai ita ce ƙarama dan Maimoon ta bata wajen 2yrs. Juyawa Maimoon ta yi ta zabga mata harara kana ta ce” dake nake magana da zaki saka min baki?”
Kama bakinta ta yi tana cewa”Allah ya baki haƙuri” daga haka ta ci gaba da kallon da take. Ɗan tsaki Nana ta yi ta ce”yaran nan sun fiye raini wallahi, sai kace mu haka muke yiwa na gaba damu”
Da sauri Juwaira ta kalleta sai dai bata ce komai ba, Maimoon ta yi murmushi tana faɗin”bar ta dai, ni yanzu tashi muje wajensu Hameeda sai a buɗe wayar”
Miƙewa Nana ta yi tana faɗin”muje dan nima na ƙagu na buɗe wayar” okay ta ce sannan ta ware mayafin data ɗaura ta yafashi suka fita suna tafe suna hira har suka kawo apartment ɗin su Hameeda.
Tsayawa suka yi a bakin ƙofar gidan suna kalle-kallen juna, Nana ta ce”after you” harararta Maimoon ta yi ta ce”wallahi ba zan shiga ba, nasani ko Daddy baya nan, kin san dai halin faɗan Mama” Nana ta ce”to me zata magana, daga zuwa wajen Hameeda?”
“Ki fara shiga ke dai”
Haɗe rai ta yi ta ce”to tsoron me nake ji ni, wallahi shigata zan yi” daga haka ta murɗa handle ɗin ta shige, Maimoon ta dinga kallon ƙofar ganin har wajen 2mins bata fito ba ta sauke ajiyar sannan itama ta shiga.
Zaune ta sameta kusa da Mama suna magana, ta ƙarasa ta tsuguna kusa da kujera a sanyaye ta ce”Mama ina yini?” Kakar jira take kuwa ta ce”lafiya Maimuna, wannan shigar fa?” Ta ƙare maganar tana kallonta, Maimoon ta kalli kayan jikinta, riga da wando ne kuma basu wani kama jikinta ba. Jin tayi shiru ya sanya Mama ta sake faɗin “I’m talking to you fa” muryarta na rawa ta ce”na…Nana ta zo tace na rakota nan shiyasa kuma…kuma ban hau sama ba”
Mama ta dinga kallonta babu yabo babu fallasa ta ce”saboda haka ya sanya ki ka fito kamar ƴar arna right? Wato kun dawo daga boarding zaku zo ku dinga yi mana irin wannan halayen ko? To na sake gani” shiru duk suka yi dan daman idan da sabo sun saba da faɗan Mama.
Shiru parlon ya ɗauka na wasu sakwanni, kafin Mama ta rufe littafin dake hannunta ta zare glasses ɗin ta kalli Nana ta ce”baku san hanyar ɗakin nata bane?” Da sauri suka tashi suka bar parlon. Ta bisu da idanu sai kuma ta girgiza kanta a fili ta ce”Allah ya kyauta”.
Suna shiga ɗakin Maimoon taja ta tsaya tana sauke numfashi, Hameeda na tsaye jikin dressing mirror tana shafa mai da alama daga wanka ta fito, ta kallesu ganin kamar an koro su ta ce”lafiya dai? Daga ina?” Tskai Nana ta yi ta nemi gefen gado ta zauna. Ta kalleta sai kuma ta kalli Maimoon wadda ke tsaye har sannan tana sauke numfashi sai kawai ta fashe da dariya. Kallonta suka dinga yi, ta ɗaure kanta tana cewa”Mama ce ta muku faɗa right?”



