Chapter 31: Chapter 31
Ana idar da sallar isha’i Atta na shigowa parlon, Ta dinga ƙarewa ko wace kusurwa kallo kafin ta taɓe baki ta shiga kiran sunan Amma. Amma da ke kitchen ta fito hannunta riƙe da spoon da bata san ta ɗauko ba saboda kiran Attan. Ganin ita ce tsaye a tsakiyar parlon ya sanyata sakin murmushi kafin ta ce“Atta ke ce da daren nan?”
“Yo ba dole ki ganni da daddare ba, kin ƙule ƴa a ɗaki kamar zaki mayar da ita ciki. Cewa nayi da la’asar za’a kaita amma gashi har ana sallar magriba babu ita babu labarinta, to zuwa nayi na tafi da ita.” Murmushi kawai Amma ta yi dan ba zata iya da halin Atta ba ta ce“ai tana ɗaki Nanan”
Bata sake kallon inda take ba ta nufi hanyar ɗakin Nanar tana gyara mayafinta da ke sakkowa kafaɗarta. Suna zaune a ɗakin, Ban da ƙamshi babu abin da ke tashi. Wani irin sassayan ƙamshin humra ne wanda ya hadu dana turaren kwalba haɗi dana kabbasa. Ita kanta Anty Ramlah da ba ita aka sakawa turaren ba ƙamshi take, Nana na zuane gefenta ta rufe fuskarta da wani golden ɗin mayafi mara kauri, sai shessheƙar kuka take a hankali. Atta ta shigo ɗakin babu ko sallama, Turus ta yi ganinsu zaune, ta ƙarasa ciki tana kallon su ta ce
“A’a wallahi kul Ramlah ki ke ko wa? Akan me zaki riƙe min ƴa anan? Yarinya za’a sadata da ɗakin mijinta kin zo kin wani sakata a maƙata ko me ki ke ce mata ohho?”
Murmusawa Anty Ramlah ta yi tana tashi daga wajen ta ce“Allah ya huci zuciyarki Atta. Gata anan ai mun gama”
”Ku ka gama me? Hala dai ba wani mugun abun ki ka kitsa mata ba.?”
Atta ta yi maganar tana ɗage lulluɓin dake kan Nanar, Kifa fuskarta ta yi a tsakanin cinyoyinta tana ƙara volume ɗin kukanta.
Ɗago kanta Atta ke son yi amma fur taki yarda, ta saketa tana yin baya ta ce“a’a wallahi ki je dan kan ki. Tashi ni muje a kai ki ɗakin mijinki”
Tamkar ta sake tura Nana haka ta sake rushewa da wani sabon kukan, Anty Ramlah ta koma ta riƙe hannunta dake cikin mayafin ta ce“Ba na ce miki ki daina wannan kukan ba? Taso maza.”
Sake kwace hannunta ta yi tana ci gaba da kukanta. Anty Ramlah ta yi tsaki ganin tana son bata musu rai ta ce
“Ran ki zai ɓaci kuma Nana tashi na ce miki!”
Ta ƙare maganar a tsawace, Harararta Atta ta yi cikin tsawa ita ma ta ce“A’a dakata! Ya yarinya ita kaɗai ubanta ya mallaka zaki dinga mata tsawa? Ƴar da za’a lallaɓata ko kin manta gidan miji za’a kaita?”
Ko saurarenta Anty Ramlah ba ta yi ba ta ja hannun Nana ta sakko da ita daga kan gadon. Lace ne a jikinta mai kyau da tsada golden mai ratsin coffee, ɗinkin doguwar riga wadda ta kama mata jiki. Anty Ramlah ta gyara riƙon da ta yi mata bayan ta sauke mata mayafin ta ja hannunta suka bar ɗakin, Da idanu Atta ta bi su can kuma ta biyo bayansu kamar zata faɗi saboda sauri. A parlon suka sami Mama wadda shigowarta kenan don tafiya da Nana, Anty Ramlah ta miƙa mata hannunta. Riƙewa Mama ta yi kamar jira Nana take ta sake fashewa da kuka, Amma da ke tsaye ta ƙarasa gabanta. Ɗaga mayafin ta yi tana murmushi mai haɗe da hawaye ta ce
“Haba Nanata ki daina kin ji. Yanzu kin zama babba fa” Sake fashewa ta yi da kuka ta faɗa jikin Amma ta ƙanƙameta, ita kanta Ammar kasa bata haƙuri ta yi dan ita ma kukan take, koda wasa bata yi tunanin nan kusa zata kai Nana ɗakin miji ba. Sai gashi yau zata rabu da ita, duk da ba nisa zata yi ba sai taji kamar zasu rabu ne. Anty Ramlah ce ta ƙarasa wajen ta janye Nana daga jikinta cikin son kwantar mata da hankali ta ce“Yi haƙuri mana Yaya. Idan kina kuka to ita ta ina zata yi shiru?” Gyaɗa mata kai Amma ta yi tana goge hawayenta. Mama ta sake riƙe hannun Nana tana kallon su ta ce“to Ramlah ko zaki biyo mu ne?” Girgiza kai Anty Ramlah ta yi dan ta san sai sun fara kaita apartment ɗin Hajiya Babba ta ce“a’a kawai ku je, Allah ya bada zaman lafiya.” da Amin suka amsa duka sannan suka yi waje, Atta ta bi bayansu da sauri. Kai tsaye apartment ɗin Hajiya Babba suka nufa da ita, koda suka shiga gaba ɗaya sauran suna zazzaune, Papa, Abba, Hajiya Babba, Aliyu. Mama ta shiga da ita ta zaunar da ita can kusa da Hajiya Babba sannan ita ma ta nemi kujera ta zauna, Papa ya buɗe wajen da addu’a sannan aka yi salati, kafin ya fara magana ya ce“Ina Abdusammad ɗin kuma?”
“Yana hanya Papa.”
Aliyu ya bashi amsa da sauri, ko rufe baki basu yi ba ya buɗe ƙofar parlon ya shigo. Nan da nan ƙamshi turarensa ya gauraye parlon, sanye yake cikin wata dakkakiyar shadda Madam gezner ash colour, Ya ɗaura hular zanna akansa. Ɗinkin babbar rigar ya amshe jikinsa sosai ya zauna akan a jikin aka ɗinka, ƙafafunsa sanye da Gucci shoes ash colour, Idan aka ce ka yi rating nasa to tabbas za’a iya bashi ɗari a ciki goma. He looks quite and elegant, Duk da fuskarsa a haɗe take babu annuri hakan bai hana kyansa bayyana ba, farar fatarsa sai sheƙi take, kana ganinsa kada ango sabon aure. Ya saki ƙofar ganin yanda suke kallonsa ya sanya ya sake tsuke fuskarsa, Kujerar da Aliyu ke kai ya ƙarasa ya zauna sannan ya gaishe su ɗaya bayan ɗaya, suka amsa a sake sannan Papa ya fara bayanin da zai yi. Nasiha sosai ya yi musu daga shi har ita, kana ya yi fatan Alkhairi, Hajiya Babba ma ta yi tata maganar sannan Atta. Abba kuwa cewa ya yi bashi da abin faɗa, dan haka Mama ta rufe taron da addu’a suka shafa.
Bayan an kammala komai Mama ta miƙe tana shirin wucewa gidanta, Atta ta yi saurin cewa“to idan ki ka tafi kuma wa zai kai yarinyar ɗaki?”. Kafin Mama ta yi magana ya miƙe yana kallonsu fuskarsa a sake saɓanin ɗazu ya ce“no need Atta. Zan tafi da ita” ya yi maganar babu alamar damuwa ko kunya akan fuskarsa, Jinjina kai Papa ya yi ya ce“hakan ma ya yi, ku je kawai Allah ya bada zaman lafiya.”
Da Amin ya amsa sannan ya nufi inda Nana ke zaune, kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce“taso mu tafi” ya ƙare maganar yana miƙa mata hannunsa na dama, Ta cikin mayafinta ta ga hannun nasa, amma ta ƙi ɗora nata ta mike tsaye tana kuka ƙasa-ƙasa ta yi gaba. Bin bayanta ya yi bayan ya sake musu sallama, Abba ya lumshe idanunsa yana jin wata nutsuwa na saukar masa, at least dai ya aurar da ƴarsa. Cikin zuciya ya furta
“Alhamdulilah, ur home is blessed Nana.”
A fili kuwa kasa cewa komai ya yi, sai jingina kansa da ya yi da jikin kujera. Atta kuwa haɗe rai ta yi ta tashi ta haye sama dan sam ba haka ta so ba, ta so ne ta je gidan saboda ta ga Zahra. Da idanu Papa ya bita dan ya riga da ya gama gano shirinta ya girgiza kansa yana murmushi, tashi Aliyu ya yi ya musu sallama sannan ya nufi sana sashin. Su kuma suka ci gaba da maganarsu.
Tafiya suka dinga yi yana gaba tana bin sa a baya, gaba ɗaya ta kasa yin sauri, ga matsewar da lace ɗin jikinta ya yi mata, ga kuma gajiya, ga yunwa dan sam bata samu damar cin abincin ba. Ganin yanda ya yi gabs abin sa ya sanyata tsayawa, ta dinga kallon sa ganin ko sau ɗaya bai waiwayo ba, Tana tsaye a wajen har ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shige ciki. Silalewa ta yi a wajen ta fashe da kuka, ita wace irin Amarya ce? Babu wanda ya rakota gidanta, sannan kuma shi kansa mijin ba zai iya jiranta ba ballantana ya jera da ita. Ta kifa kanta akan cinyoyinta tana kuka kamar ranta zai fita. Abdusammad na shiga ya mai da ƙofar yana shirin rufewa, sai a sannan ya lura da cewa bata bayansa, ya ɗan ware Idanunsa sai kuma ya saki ƙofar da sauri. Dube-dube ya dinga yi a balcony ni ɗin amma sam bai hangeta ba, dan haka ya fara tafiya yana kalle-kalle. Ya yi nisa ya hangeta tana tafiya a hankali, ya ɗan ja tsaki sannan ya ƙara saurinsa. Gabanta ya sha yana kallonta fuska a haɗe ya ce
“Ke mene ne haka? Ina zaki je?”
Banza ta yi masa, ta matsa ɗaya gefen ta ci gaba da tafiyarta tana kuka fuskarta rufe da mayafinta, Rai ɓace ya sake yin gaba ya jawota ta dawo gabansa yana kallonta fuska babu alamar walwala ya ce
“Yaushe na fara wasa da ke Nana?. Shige mu tafi!”
Cikin kuka ta ce“Wallahi ba zan bika ba, ni gida zan koma. Ai baka sona”
Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka, Kallonta ya dinga yi yana mamakin abin da ta ce, can kuma ya saki murmushi ya kamo hannunta ya ce“sai ina son ki zaki bi ni kenan?” ƙoƙarin kwace hannunta take sai dai rikon da ya yi mata bana wasa bane, dan haka ta ci gaba da kukanta tana cewa“Ni wallahi ba zan zauna da ku ba.. Ni wajen Ammata zan koma” ta juya tana shirin tafiya, Dafe kansa ya yi ganin tana son wahalar dashi a banza. Ya juyo da fuskarta ba tare da ya zare mayafin data rufe fuskar ba ya ce“Kina son na makeki anan ne?”
Madadin ta bashi amsa sai kawai ya ga ta zauna a wajen, ta sake rushewa da wani sabon kukan tana ƙoƙarin birgima a ƙasan. Wani dogon tsaki ya ja ganin tana shirin raina masa hankali yasa ya sunkuya kamar zai mata magana kawai taji ya ɗauketa tamkar Baby ya fara tafiya da ita, zille-zille ta fara yi tana son kwace kanta, sai dai sam bai bata wannan damar ba ya sake matseta da jikinsa yana ci gaba da tafiya. Ta dinga kuka tana cilla ƙafafunta har suka ƙarasa gidan, ya murɗa handle ɗin ƙofar da hannunsa ɗaya sannan ya shige ciki da ita.
A parlon ya direta yana watsa mata wani mugun kallo ya ce“Idan wasa nake miki ki sake fita.” tura baki ta yi, Ta ɗan janye mayafin nata ba sosai ba, ɗaya bayan ɗaya ta dinga ƙarewa komai na parlon kallo. Ko ina tsaf dashi sai tashin ƙamshi yake, Ya nufi hanyar upstairs ba tare da ya sake bi ta kanta ba. Gajiya ta yi da tsaiwar, cikinta ban da ƙugin yunwa babu abin da yake. Ta kalli hanyar upstairs ɗin sai kuma ta nufi wajen da sauri, A corridor ɗin saman ta tsaya, ta dinga ƙarewa ɗakunan kallo dan babu inda bata sani ba. Extra room ɗin ta buɗe ta shiga, kamar yanda ta yi tunani kuwa anan ne aka zuba mata kayan furnitures ɗinta da Abba ya siya mata. Ta ƙarasa ciki tana sauke numfashi, Cire mayafin ta yi ta ajiye a gefen gadon, Ta zame ɗankwalin lace ɗin ta ajiye shima sannan ta hau gadon ta zauna tana sauke numfashi.
Koda ya shiga ɗakin zaune ya sameta gefen gado ta yi shiru tana tunani, tun bayan kiran da Umma ta yi mata taji jikinta ya yi sanyi kalau. Ya karasa ciki yana kallonta ya ce“Zahra”
Ɗago kanta ta yi ta kalleshi da kumburarrun Idanunta wanda suka sauya kala, wata embroidery Atampa ce a jikinta mai pattern, ɗinkin t boubou mai kyau. Sai dai sam babu walwala akan fuskarta, Ya tsaya a gaban gadon yana kallonta ya ce“Tashi muje ƙasa.”
“Sun kawota ne?”
Ta tambaya a sanyaye, Jinjina mata kai ya yi dan bai ji zai iya magana ba. Zahra ta miƙe a sanyaye ta yafa mayafin dake hannunta sannan ta yi gaba. Ya sauke ajiyar zuciya sannan yabi bayanta.
Da mamaki ya dinga kallon parlon ganin wayam babu Nana babu dalilinta, Ya dafe kansa yana tunanin Allah ya sa ba wani wajen ta sake fita ba, gaba ɗaya so take ta wahalar da rayuwarsa. Ɗan tsaki yaja sai kuma ya nufi ƙofa fita daga parlon, Zahra ta bi shi da idanu tana mamakin inda zai je. Babu in da bai duba ba a compound ɗin amma bai samu Nana ba, kuma shi ba zai iya zuwa Apartment ɗin ba yanzu ya ce ina take. Ya tsaya yana tunanin yanda zai yi, Can kuma ya juya ya koma gidan, yana shiga parlon ya tsaya turus ganinta da ya yi tsaye tana rarraba idanu. Ya ƙarasa gabanta da sauri kamar zai daketa ya ce
“Ina ki ka je?”
Hawayen da yake maƙale cikin kurmin idonta ne ya shiga zirarowa kan fuskarta. Ta kwaɓe fuska kamar ƙaramar yarinya ta ce“Uncle cikina”
“Ina miki wata maganar kina min wata? Na ce ina ki ka je.?”
Tura baki gaba ta yi ta ce“Ni fa babu inda naje, ɗakina na tafi.” ya maka mata wata uwar harara sannan ya nufi kujera ya zauna, kamar jira take tabi bayansa ta zauna kusa da shi ta ɗora kanta gefen kafaɗarsa, ƙoƙarin janyeta ya dinga yi amma sam taƙi yarda, ta zura hannayenta duk biyun ta cikin hannunsa ta riƙe shi gam. Zahra ɗauke idanunta ta yi kamar bata gansu ba, Ya sauke numfashi kafin ya yi gyaran murya cikin nutsuwar data gama ratsa shi ya fara musu nasiha, Duk wani abu wanda ya kamata ya sanar musu akan haƙƙin zaman tare sai da ya sanar musu, daga bisani ya yi wa Nana faɗa dan ya san tsaf zata iya nemar fitina. Sannan ita ma Zahra ya yi mata nata faɗan daban, Bayan ya kammala ya sanya suka yi addu’a sannan ya miƙe yana janye Nana daga jikinsa ya ce
“Sai da safe.”
Ya yi maganar yana kallon su duka, Tashi Nana ta yi ta ce“uncle.” kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce“mene ne?”
“Ni ina kazata?”
Ɗan mitsi-mitsi ya yi da idanunsa kafin ya ce“kaza? Kazar me?”
Kamar zata yi kuka ta ce“to ba amarya ba ce ba ni? Kuma ai ana siyawa Amarya kaza. Kuma ni naga baka siya min ba” tsuke fuska ya yi ya gyara tsaiwarsa yana kallonta sosai ya ce“yaushe na fara wasa da ke Nana?” sunkuyar da kanta ta yi saboda kaifin da idanunsa suka mata, Ya ja dogon tsaki sannan ya nufi upstairs da sauri. Shiru Nana ta yi tana kallon ƙasa, ta maƙale hawayenta gudun kada Zahran ta gani ta nufi saman ita ma, Zahra kuwa tashi ta yi jiki a saluɓe tabi bayansu, kowa ɗakinsa ya shige daban. Nana na zuwa ta faɗa kan gado ta fara birgima tana kuka, To ina aka taɓa kai Amarya ba’a siya mata kaza ba? Daman haka ake auren?. Ta sake rushewa da wani sabon kukan, Ji tayi kamar ta tashi ta yi tafiyarta, sai dai sanin dare ya yi ya sanya ta fasa ta ɗauki aniyar gobe da sassafe zata yi wucewarta. Da wannan tunanin ta tashi ta zame kayan jikinta sannan ta nufi toilet ɗin da yake dakin, wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala kamar yadda ta saba duk dare, tana fitowa ta nufi press ɗinta inda aka jera mata kayanta sabbi ta buɗe. Wata sleeping dress ta ɗauko mara nauyi ta saka sannan ta nufi kan gadon, ta kwanta ta ja lallausan duvet ɗin ta rufe gaba ɗaya jikinta. Gajiya da kuma yunwar da take ji su ne suka taimaka wajen hanata bacci, ta dinga juyi akan gadon tana riƙe da cikinta, can kuma ta miƙe kamar wadda aka zabura ta tashi ta nufi toilet. Ƙaƙarin amai ta dinga yi amma kasancewar babu komai a cikinta ya hana aman zuwa, ta gaji ta kuskure bakinta ta dawo ɗakin. A wahale ta koma ta kwanta, ta ci gaba da mata gungun ɗinta a wajen har bacci ɓarawo ya ɗauketa. Da asubah ya shigo ɗakin bayan ya dawo daga Masallaci, kwance ya hangeta ta dunƙule jikinta waje ɗaya. Ya girgiza kansa sannan ya ƙarasa ciki, ɗan dukanta ya yi da hannunsa yana faɗin
“Nana! Ke Nana!”
Dakyar ta buɗe idanunta, ta kasa tashi saboda ciwon da cikinta ke mata. Daga kwance ta dinga kallon sa tana murza idanunta, Ya kafeta da idanu ya ce“tashi ki yi sallah” ya juya ya fice daga ɗakin ba tare da ya sake cewa komai ba. Da idanu kawai Nana ta bi shi sai kuma ta rufe idanun, hawaye suka fara zirarowa ta gefen idanun. Ta daɗe a haka har sai da gari ya fara haske sannan ta yunƙura ta tashi, ta zura slippers ɗin dake ƙasan gadon sannan ta nufi toilet tana tafe kamar iska zai hureta. Wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala ta fito tana gyara ɗaurin towel ɗin jikinta, a hankali ta ware idanunta lokaci ɗaya kuma ta saki wani ihu ta sanya hannayenta duk biyun ta rufe fuskarta. Da mamaki ya dinga kallonta can kuma ya miƙe ya karasa wajen ganin yanda take abu kamar wata zararriya, duk tunaninsa wani abun ta gani dan haka ya jawota jikinsa gaba ɗaya ya rungumeta. Ai kamar ya sake turata haka ta ci gaba da ihunta tana ƙoƙarin janye jikinta, kallonta ya yi jin towel ɗin dake jikinta na neman kwancewa, Ya sanya hannunsa na hagu ya riƙe shi gam kafin ya ce
“Ke lafiyarki? Mene ne?”
Janye jikinta ta yi tana ci gaba da kukanta, Ya kai hannu ya taɓa wuyanta yana cewa“ko baki da lafiya ne?”
“Ni ka fita uncle!”
Ta yi maganar cikin kuka. Da mamaki yake kallon ta sai kuma ya ce“me yasa?”
“to babu kyau ganin tsirarar mutum, kuma sai ka shigo ban saka kaya ba?” Cewar Nana ta sake ƙanƙame idanunta ita a dole ba zai ganta ba. Wani dogon tsaki ya ja, ya dinga kallon ta rai ɓace, to me take tunani? A ɗan fusace ya ce
“mene ne a tsirarar naki da har zan kalla?.”
Turo baki ta yi tana ɗan buɗe idanunta, ganin yanda ya haɗe ransa ya sanyata sakin idanun. Ta bar wajen da sauri, Press ta buɗe ta ɗauki Abaya sannan ta koma toilet ɗin. Takaici da baƙin ciki ne ya sanya shi fita daga dakin, a ransa yana jinjina haukanta.
Koda ta fito daga bayin samu ta yi baya nan, ta sauke ajiyar zuciya tana rike da veil ɗin Abayar. Can kuma wata zuciyar ta ce mata
“To wane bai san jikin ki ba? Bayan hotunan ki da kowa ya gama gani? Da gaske yake mene ne abun ɓoyewa a jikin ki?.”
Nana ta ja dogon numfashi lokaci ɗaya hawaye na kawowa cikin idanunta. Tabbas bai cancanci ta ɓoye jikinta ba, dan kowa ya gama gani. Ta koma gefen gado ta zauna ta haɗe kanta ta gwuiwa ta fashe da kuka. Ta jima sosai a wajen har sai da ta yi mai isarta sannan ta tashi, ta koma toilet ta wanke fuskarta sannan ta fito, veil ɗin rigar ta yafa akanta, ta sake shi loosely sannan ta fito daga ɗakin. Bata samu kowa a main parlon ba dan haka ta yi ficewarta ba tare da damuwa ba. Kai tsaye apartment ɗinsu ta nufa, tana zuwa ta tsaya a bakin ƙofar ta dinga knocking, sai dai har bayan mintuna goma babu alamar za’a zo a buɗe. Dan haka ta juya ta bar wajen tana yan matan hawayenta. Rasa inda zata je ta yi, gashi yunwa na neman illatata, dan haka kawai ta nufi apartment ɗin Hajiya Babba dan ta san nan ne kawai a buɗe. Bakinta ɗauke da sallama ta murɗa handle ɗin ƙofar, Hajiya Babba da ke zaune kan sofa ta amsa tana kallonta da mamaki. Jiki a sanyaye Nana ta ƙarasa ciki ta durƙusa har ƙasa ta gaisheta.
“Nana lafiya dai? Ina Abdusammad ɗin?”
Hajiya Babba ta yi tambayar tana kallon ta bayan ta zauna gefenta. Madadin ta bata amsa sai kawai ta fashe da kuka tana faɗawa jikinta, Hankalin Hajiya Babba ya tashi ta ɗagota tana faɗin
“mene ne? Me ya yi miki?”
Kasa magana ta yi saboda kukan da ya ci ƙarfinta. Dai-dai nan Atta ta fito daga kitchen hannunta riƙe da madaidaicin plate mai ɗauke da soyayyen dankalin turawa, Ta ƙaraso wajen da sauri tana faɗin
“wa nake gani kamar ƴar gidan Ahmadi?”
Gyada mata kai Hajiya Babba ta yi kafin ta ce“Eh ita ce Atta.”
“Subhannallahi, Ba dai yaron nan har ya aikaceta ba babu tausayi, mu sam lokacin mu ba haka ake ba wallahi tallahi, sai yarinya ta girma sannan. Amma saboda jaraba ta ya’yan yanzu da an kai musu yara sai su haike musu, wannan ai magunta ce fisabilillahi.”
Atta ƙare maganar cikin kunfar baki. Shiru Hajiya Babba ta yi dan ita ma abin da ta ya zo ranta kenan. Ta sake ɗago Nana da ke kuka kamar ranta zai fita ta ce“Ya isa haka Nana. Faɗa min me ya yi miki?”
“To me za ki tambayeta kuma fisabilillahi, bayan ga abu nan ƙiri-ƙiri?”
Atta ta jawo hannun Nana tana makon ta ta ce“Saboda Allah Hadiza faɗa min me ya yi miki? Ni wallahi yanzu sai na shirya naje na ci masa mutunci. Ina ganinsa kamar mai hankali ashe ba haka bane?”
Dakyar Nana ta kwace jikinta saboda yanda Attar ta cacumeta, Ta yi baya tana fadin
“Ni ki cikani jikin ki duk ƙashi!”
Ta yi maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan. Mitsi-mitsi Atta ta yi da idanu kafin ta ce“Ji min ruɓaɓɓiyar yarinya! To a shekaruna idan ba’a samu ƙashi a jikina ba me za’a samu?”
Babu wanda ya tanka ta a cikin su, dan haka ta yi shiru tana kallon su. Hajiya Babba ta kalli Nana murya a sanyaye ta ce“faɗa min me ki kewa kuka?”
Nana ta fara murza idanunta tana ƙoƙarin tsagaitawa da kukan ta ce“Hajiya ko ba uncle bane. Tun jiya ban ci abinci ba! Kuma yunwa ta kusa kasheni” Da mamaki Hajiya Babba ta ce“babu abinci kuma? Baki ci abinci ba?” gyaɗa mata kai Nana ta yi tana kuka. Hajiya Babba ta girgiza kanta kafin ta kira wata maid, bayan ta zo ta ce ta kawo mata abinci. Ba’a fi 5mins ba ta dawo hannunta riƙe da tray, Ta ajiye gabansu sannan ta juya ta bar parlon. Nana ta zame ta sauka kasa ta ja tray ɗin, tea flask ɗin ta buɗe ta tsiyaya tea ɗin sannan ta saka sugar kaɗan ta fara sha. Dakyar take haɗiyewa yana ƙoƙarin dawo mata saboda yunwar data riga da ta gama cinyeta, ta ajiye mug ɗin sannan ta fara cin soyayyen Irish potato ɗin tana haɗawa da kwan. Tass ta cinye sannan ta miƙe tana gyatsa, Hajiya Babba da ke jan counter ɗin hannunta ta ce
“kin ƙoshi?”
Gyaɗa mata kai Nana ta yi, ta karasa kan doguwar sofa ta kwanta nan da nan bacci ya ɗauketa. Hajiya Babba ta dinga kallonta ganin yanda take ta kwaɓe fuska a cikin baccin. Kafin daga bisani ta ɗauke kanta tana murmushi.
****
Ringing ɗin wayar data ji ne ya sanyata fitowa daga parlon, ta kalli Haule dake kallon tv sai kuma ta kalli inda ta ajiye wayar tata. A ɗan fusace ta ce“ke baki ga ana kirana ba? Ba zaki iya zuwa ki faɗa min ba?” jiki a sanyaye Haule ta kalleta sai kuma ta ce“Allah shi baki haƙuri” ta yi maganar tana ɗauke kai, Kwafa Siyama ta yi sannan ta ƙarasa ta ɗauki wayarta ta koma kitchen ɗin. Ganin sunan Mommynta ya sanya ta ɗaga, Aunty Khadijah da ke zaune gefen gado ta ce
“Siyama ya gidan?”



