⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 32: Chapter 32

Ɗan taɓe fuska ta yi kafin ta ce“Gashi nan dai. Amma kin san me Mom?” girgiza kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“a’a sai kin faɗa”

“Ni fa wallahi ban ga kuɗin da ki ke magana ba. Safwan bashi da kuɗi kamar mijin Anty Zahra. Bana ganin zamu samu abin da muke so, and kuma kwanan nan gaba ɗaya bashi da lafiya, ko kusa dashi naje sai ya ce na tafi, ballantana na yi aiki da maganin da malamin ya bamu.” Shiru Anty Khadijah ta yi tana tunani, Siyama ta ci gaba da cewa

“wallahi Mom ban jin zan iya zaman nan. Cause gaba ɗaya ba yanda nake son namiji na gansa ba, kuma ni bana son zaman gida shi kuma ba zai bari na fita ba. Kin ga kuwa ai akwai matsala”

“Ke wace irin shashasha ce? Kina so ki ce min bashi da kuɗi ko me?” Anty Khadijah ta yi maganar rai ɓace. Girgiza kai Siyama ta yi ta ce“ba wai bashi da kuɗi ba, yana da shi, amma ba kamar mijin Anty Zahra ba. Ni wallahi dana sani ma shi na ce ba wannan ba”

Numfasawa Anty Khadijah ta yi ta ce“wannan duk daga baya ne, ko kina nufin zaki auri mijin Zahra ne ku zauna tare?” Girgiza kai Siyama ta yi ta ce“haba dai mu zauna tare, Ni ba zan iya zama da kishiya ba wallahi. Ita ma wannan dan ban ɗauketa kishiya bane, kin san bai taɓa kwana daƙinta ba.”

“kin ga wannan maganar bata waya ba ce, ki bari zan zo gidan na sameki.” Anty Khadijah ta faɗa saboda Umma da taga ta shigo ɗakin, to kawai Siyama ta ce sannan ta katse wayar, ta ajiye ta kan cabinet sannan ta ci gaba da abin da take.

Tana gamawa ta fito ta tsaya tana kallon Haule dake zaune har sannan a parlon ta ce“Tashi na aikeki” Toh kawai ta ce sannan ta miƙe ta zura hijabin da ke Hannunta. Siyama ta nuna mata warmern data ajiye a kitchen ɗin tana cewa“ki ɗauka ki kai wa Hajiya Babba, saura ki zauna magana.” Babu musu Haule ta shiga kitchen ɗin, ita kuma ta nufi sama don shiryawa saboda magriba ta tawo.

****
Around 9pm suna zaune a parlon, Noor na zaune a gefenta ta yi shiru tana kallonta ganin yanda take kuka kamar ƙaramar yarinya. Karasowa jikinta ta yi ta riƙeta cikin ƙaramar muryarta ta ce

“Anty stop crying! Stop plsss!”

Ta ƙare maganar tana sakin kuka ita ma, kallon ta kawai Nana ta yi sai kuma ta jawota jikinta tana ci gaba da kukanta. Suka dinga rera kukan a tare babu mai rarrashin su, wajejen 9:20 na daren aka buɗe handle ɗin ƙofar, Noor ta sauka daga jikinta da gudu ta ƙarasa inda yake ta rungumeshi. Durƙusawa ya yi dai dai tsayinta ya dinga kallon ta ganin yanda take kuka yasa ya ɗauketa yana faɗin “wane ya taɓa wa Abbie ƴar sa?” cikin shessheƙar kuka ta ce“Abbie kuka muke yi” yanda ta yi maganar cike da yarinta ya sanya shi murmushi. Ya zauna a kujerar da ke facing ta Nanar ya ɗorata kan cinyarsa ya ce

“Kuka kuma? Me yasa?”

Hannunta ta kai kan gemunsa tana murzawa a hankali ta ce“koba Anty Nana ba ce take kuka, to shi ne nake tayata.” Jinjina kansa ya yi sannan ya ce“Ai ko kin kyauta. Tashi ki je ki kwanta it’s already late” to kawai ta ce sannan ta yi masa kiss a goshi ta sauka daga jikinsa ta ce“good night Abbie”

“Allah ya tashe mu lafiya.” ya ce yana jan kumatunta. Murmushi ta sakar masa sannan ta ƙarasa inda Nana ke zaune ta ce“good night Anty.” gyada mata kai kawai ta yi, Noor ta nufi sama tana tafe da gudu. Sai da yaga ta bar wajen sannan ya zame jikinsa ya jingina da jikin kujerar yana kallonta ya ce“zo nan” jiki a sanyaye ta tashi ta ƙarasa wajen tana goge hawayenta wasu na sake zubowa. Ta zauna gefensa ta sunkuyar da kanta. Shiru parlon ya ɗauka na wasu mintuna kafin ya gyara zamansa yana kallonta sosai ya ce“mene ne kuma?” kamar jira take ta fashe da kuka, Ya dafe kansa a fili ya ce“oh ni Na shige su da Nana” ɗora kanta ta yi akan cinyarsa ta dinga rera kukan ta, ya yi shiru yana saurarenta kafin daga bisani ya ɗago kanta yana kallonta ya ce“rigimar mene ne? Me ki ke so?”

Cikin shassheƙar kuka ta ce“uncle ko ba kai bane” ta yi maganar a shagwaɓe yana sake narkewa a jikinsa. Hannunsa ya sanya yana share hawayen fuskarta ya ce“too me nayi miki?”

“Ba zaka siya min kaza ba?”

Shiru ya yi yana kallonta, can kuma ya ce“kazar mene ne Nana?”

Cikin son fahimtar dashi ta ce“kazar amarya mana. Maimoon ta ce min Yaya Aliyu ya siya mata kaza, kuma haka ma Hamida da Amrah suka ce min. To nima ba sai ka siya min ba dan Allah?” ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan. Murmushi ne ya kusa kwace masa, ya yi gyaran murya kafin ya ce“to ai ban shirya cin amarcin ba ballantana na siya kazar amarci”

“To uncle ka shirya karɓar amarcin mana. Sai ka siya min kazar kaji!”

Ta yi maganar tana marairaice fuska. Ɗauke kansa ya yi yana kallon gefe, bai san sanda wani kayataccen murmushi ya kwace masa ba. Nana ta sake matsawa jikinsa tana leƙa fuskar sa. Juyowa ya yi yana kallon ta, Lokaci ɗaya kuma ya tsuke fuska kamar ba shi ba. Langwaɓar da kanta ta yi taja hannunsa na dama ta ce“kaji uncle…” janye hannunsa ya yi daga nata yana cewa“to idan na shirya siyan kazar zan miki magana. Ni yanzu bani da kuɗin siyan wata kazar amarci” zaro dara-daran idanunta ta yi can kuma ta tsuke baki ta ce“uncle kai ne baka da kuɗin?” jinjina mata kai ya yi yana ƙoƙarin tashi daga kan sofar, Nana ta mike tana riƙe da hannunsa ta ce“wallahi kana da kuɗi, kuma ma bayan duk ka fi su kuɗi” girgiza kansa ya yi yana ƙoƙarin ɓoye dariyarsa ya ce“ni ɗin?” ta gyaɗa masa kai tana marairaice fuska. Taɓe baki ya yi ya saki hannunta ya ce“to ni bani da wani kuɗi, gara ki kama kan ki.” daga haka ya yi gaba ya barta tsaye a wajen. Ɗan buga ƙafafunta ta yi a ƙasa kafin ta ce“to ni wallahi so nake na ci kazar!” Ta ƙare maganar tana hawaye. Ko saurarenta bai yi ba ya haye sama abin sa. Ta koma ta zauna kan sofar tana matsar kwalla, Bayan wasu mintina Zahra ta sakko daga sama tana kallon ta. Can kuma ta shige kitchen abin ta, bata jima ba ta zo ta sake shigewa sama, Nana ta miƙe tana ɗaukan hular saƙin dake kanta ta nufi saman ita ma. Ɗakinta ta tashi ta ƙarasa gefen gado ta ajiye hular sannan ta zauna ta jawo wayarta da ke gefen pillow. WhatsApp ta shiga dan daman wifi ɗin ta a kunne yake, Ta yiwa Khadijah sallama. Ganin bata online ya sanya Nana jan ɗan siririn tsaki ta yi wurgi da wayar sannan ta miƙe. Toilet ta nufa bayan ta zame yar rigar dake jikinta, ta yi wanka sannan ta fito tana tsane jikinta da towel. Press ɗin ta ta buɗe ta ɗauki wata yar yalolon riga mara nauyi ta saka sannan ta nufi gaban mirror ɗinta ta shafa mai, Bayan ta kammala ta nufi kan gadonta ta faɗa tana sakin numfashi. A hankali ta dinga ɗaga ƙafafunta Salam kwanciyar ruf da cikin da ta yi, Tana nan kwance a haka har bayan kusan mintina goma wayarta ta fara ringing, Hannunta ta saka ta janyo wayar tana daga kwancen, Ganin numbern Mimi ya sanyata juyawa ta kwanta dai-dai sannan ta daga kiran. Khadijah da ke kwance kan nata gadon ta ce

“Hi Nana!”

Haɗe rai Nana ta yi kamar tana gabanta kafin ta ce

“Sai yau zaki nemeni?”

Murmushi Khadijah ta yi ta ce“Afwan baby girl,Yar autar Ammarta.” Taɓe baki Nana ta yi ba tare da ta ce komai ba. Suka ɗan yi shiru can kuma Khadijah ta ce“gobe zan koma Kano fa”

“Daman kina Yola?”

Nana ta tambaya tana ɗan zaro idanu. Gyada mata kai ta yi kafin ta ce“eh fa. Ai da muka tafi gidan friend ɗin Daddy naje so ina can all this while.” Tashi zaune Nana ta yi ta ce“amma shi ne ko sau ɗaya baki faɗa min ba? Khadijah ki zo gidanmu dan Allah. Ki zo bestie i have alot to talk wlh, Dan Allah ki zo”

Shiru Khadijah ta yi tana jin ta, Can kuma ta ce“To bayan na ce miki goben zan koma Kano?”

“Kenan ba zaki iya zuwa saboda ni ba?”

Nana ta tambayeta muryarta a sanyaye. Khadr ta yi murmushi sai kuma ta ce“alright zan ga abin da ya kamata nayi. Idan zan zo I’ll call you da safe”

Taɓe baki Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce“amma kin san an yi min aure ba?”

Tashi zaune Khadijah ta yi da mugun mamaki ta ce“da wa? Yaushe kuma Nana?” ta jera mata tambayoyin tana zaro idanu. Numfasawa Nana ta yi lokaci ɗaya hawaye ya fara zuba kan fuskarta, Can numfashinta da Khadijah ta yi yasa ta ce“Nana, Are you there?”

Gyaɗa mata kai ta yi kamar tana gabanta sai kuma ta sake jan numfashi cikin shessheƙar kuka ta ce“Idan kin zo gobe zan faɗa miki.” Gudun kada ta sakata kuka yasa Khadijah ta ce“tom shikenan, goben zaki ganni da wuri in sha Allah.”

“Tom sai kin zo.” cewar Nana, Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar, Jifa ta yi da wayar can ƙarshen gado, ta koma ta kwanta tana kuka ƙasa-ƙasa ji tayi gaba ɗaya maganar auren ta dawo mata sabuwa. Ta daɗe tana rera yan matan hawayenta har bacci ɓarawo ya yi gaba da ita.

Washegari da sassafe Anty Khadijah ta zo gidan, Lokacin Safwna na shirin fita, Ya gaisheta cike da girmamawa ta amsa sannan ya bar gidan. Siyama ta sauke numfashi tana kallonta ta ce“Mom welcome” Fuska babu annuri Anty Khadijah ta ce“ba wannan ya kawoni ba Siyama, muje ciki mu yi magana.” okay kawai ta ce sannan ta yi hanyar upstairs ɗin tana biye da ita. Kalle-kallen corridor ɗin ta dinga yi can kuma ta kalli Siyama da tayi gaba ta ce“Ina ita kishiyar ta ki?”

Cak ta tsaya sai kuma ta juyo ta ce“haba Mom ya za’a yi ki ganta anan parlour da safe? Ai indai mai gidan bai fita ba, ba zaki taɓa ganinta a waje ba.” jinjina kai ta yi ta ce“Hakan ma yana da kyau” Siyama ta ɗan yi murmushi sai kuma ta juya ta buɗe ɗakin.

Bayan sun zauna Aunty Khadijah ta ce“yauwa me ki ke cewa jiya a waya?” girgiza kai Siyama ta yi cike da damuwa ta ce“Mom wallahi ba Safwan ne wanda ya kamata mu rike a matsayin target ba. Mijin Anty Zahra shi ne wanda ya dace da buƙatar mu. Kin san kuwa tarin dukiyarsa? Kin san da Safwan yana bani ɗan labarin wasu daga cikin abin da ya mallaka sai da naji kaina ya yi min nauyi?. Idan fa kina neman babban mai kuɗi wanda ya amsa sunansa mai kuɗi, mai faɗa a ji to wallahi Abdusammad ne! Sam bamu yi dabara ba.”

Aunty Khadijah ta yi shiru na wasu sakwanni kafin ta sauke numfashi ta ce“To daman shi Safwan ɗin bashi da komai?” Siyama ta ce“ba wai bashi da komai ba. Yana da shi mana, Yana da arziki sosai shima, amma ba kamar wancan ba, duk fa a ƙarƙashin sa suke, kusan duk arzikin gidan nan ɗin nasa ne” Jinjina kai Anty Khadijah ta yi cike da mamaki ta ce“ikon Allah, ban ɗauka ya kai haka ba.”

“Ai wallahi Mom ya kai har ma ya wuce. Shiyasa fa kowa yake ganin girmansa a gidan nan, Ba zaki taɓa jin ya yi magana an musa masa ba. Kowa girmama shi yake har manya”

Anty Khadijah ta ce“To yanzu ke ya ake ciki dake? Babu wani labari? Ya kamata a ce kin samu ko ciki ne Siyama” Ɗauke kanta ta yi cike da takaici ta ce“Hmmm to Mom mene ne bana yi? Wallahi duk abin da muka shirya a gida babu wanda bana aiwatarwa, amma kin ganni ko sauyi ban ji a jikina ba. Kuma kin san me? Duk sauran da aka kai mu tare sun samu ciki, ina ga wannan Amran ce kawai bata samu ciki ba. Ni kaina abun sai ɗaure mun kai yake” Anty Khadijah da duk jikinta ya yi sanyi ta ce“Tab idan haka ne zama bai kamani ba. Dole na tashi tsaye, Gashi daman maganar babanki na nema ta dawo sabuwa, naji yan uwan babanki na ƙishin-ƙishin ɗin kai ni koto”

Zaro idanu Siyama ta yi sai kuma ta ce“to kuma yanzu me ki ka musu Mom?” taɓe baki Anty Khadijah ta yi ta ce“kema kya faɗa, babu abin da na musu. Shi kansa kuɗin da suke magana babu sun ƙare, Yanzu ban da gidan nan na wajenki bani da komai, ni dama yana rayen ya ci gaba da nemo mana. Amma dai nan kusa zan yi aure”

“Aure kuma Mom? Da girmanki?”

Siyama ta yi maganar a sanyaye. Wani banzan kallo Anty Khadijah ta watsa mata sannan ta ce“Ji min banzar ƴa? Har yaushe nayi girman da zan kasa aure? Akwai wani Alhaji dana samu yana da tarin dukiya nan bada jimawa ba zan aureshi, kin ga idan har mun samu yanda muke so ai babu buƙatar mu ci gaba da wannan abun, sai kawai ki kashe auren naki ki fito.”

Siyama ta girgiza kanta ta ce“a’a Mom ni ba zan kashe auren nan ba wallahi. Saboda ina sonsa har ga Allah.” Ta ƙare maganar tana harɗe hannayenta a ƙirji, Taɓe baki Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“to ai sai ki yi ta yi. Ni bari ki ga na tashi na tafi kar a zo a ganni a nan”

“Ba zaki je wajen Anty Zahra ba?”

Girgiza kai ta yi ta ce“ke bar ni da wannan shashashar, ko naje ɓata min rai zata yi a banza. Kin san ita yanzu duk Umma ta kuma canzata, ganin bukatata ta biya ya sa ban sake bi ta kanta ba.”

Siyama ta miƙe tana kallon ta ta ce“Allah sarki, wallahi tausayi take bani Mom. Kin san wannan Nanar ba mutunci gareta ba” Shiru ta yi tana tunani can kuma ta ce“to Allah ya rufa asiri, Ni babu ruwana. Daga nan ma gidan Kaddu na nufa”

“To muje na raka ki Mom” har ta yi gaba sai kuma taja ta tsaya, Siyama ta kalleta ta ce“mene ne Mom?”

“Babu wasu yan kudi a wajenki ne ki ban?”

Girgiza kai Siyama ta yi ta ce“wallahi bani da cash, amma zan miki transfer ɗazu Safwan ya bani nima.”

Jinjina kai Anty Khadijah ta yi ta ce“yauwa ai hakan yana da kyau. Ni har cash ɗin ma ki dinga amshewa, sanda muke tare da mahaifinki bai isa ya shigo da kuɗi ba sai na ɗauke ko ya bani ko bai bani ba. A haka na tara duk abin da ki ka ga na mallaka.”

Shiru Siyama ta yi jiki a sanyaye ta ce“Tom Mom.”

Anty Khadijah ta yi gaba Ita kuma ta ci gaba da bin ta a baya. Har compound ɗin su ta rakota, sai da ta shige motarta sannan ita ma ta juya ta koma ciki.

Ƙarfe 10:20 na safe ta sakko daga saman, Sanye take da wasu riga da skirt, rigar irin mai kama jikin nan, sai skirt ɗin na jeans mai ɗan kauri. Wata hula ce mai ado akanta, blue colour wadda ta yi matching da skirt ɗin. Ta yi simple make-up a fuskarta dan haka ta ƙara mata kyau. Bakin nan sai shining yake na lip gloss, kasancewar bakin nata pink colour mai ɗan zagaye kamar na liner ya sanya ta yi wani irin mugun kyau. Tun da ta sakko Zahra ke bin ta da kallo, Ita kuwa ko lura bata yi da ita ba ta nufi kitchen tana waƙar Alan walker ta Unity. Zahra dake kan kujera tana danna wayarta ta sauke numfashi, kalle-kalle Nana ta dinga yi a kitchen ɗin, ita ba wani iya girki ta yi ba dan ba yi take ba. Dan haka ta rasa abin da zata dafa ta ci, gashi yunwa take ji, haka ta ƙaraci kalle-kallenta a kitchen ɗin ta juya ta fito, Bata samu Zahra a wajen ba, dan haka ta nufi sama da sauri, master bedroom ɗin sa ta murɗa ta ji a rufe. Taja ta tsaya tana knocking a hankali, tafi minti biyar tsaye a wajen amma babu alamar za’a buɗe, kuma tasan yana ci dan yau saturday ne ba fita yake ba. Gajiya ta yi da tsaiwarsa ta juya ta bar wajen, tana ƙoƙarin shiga daƙinta ta ji kamar amon muryarsa, dan haka ta nufi ƙofar da sauri, ɗan kasa kunnenta ta yi ta ji da gaske muryarsa ne, dan haka ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shige kai tsaye. Zaune ta sameshi kan gadon, Zahra na tsaye jikin mirror tana masa magana tana murmushi. Buɗe ƙofar ɗakin da ta yi ya sanya su kallon ƙofar a tare, Tsaye take kusa da ƙofa, ta kafesu da idanunta fuskarta a ɗaure. Gyara zamansa ya yi yana kallonta ya ce

“Nana mene ne haka?”

Tura baki ta yi tana kare masa kallo, wata riga ce armless a jikinsa coffee colour mai zanen tiger a jiki. Gaba ɗaya surarsa ta bayyana, Tatoo ɗin dake gefen hannunsa na hagu ya fito raɗau, gargarsa kuma ta kwanta luf a farar fatar tasa. Ganin bata ce komai ya sanya ya sake cewa

“Mene na ce miki?”

Ɗauke idanun ta ta yi ta kalli Zahra da ke kallonta ita ma, sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin ta buga musu ƙofar. Baki a buɗe ya dinga kallon wajen, Zahra kuwa ta ɗauke kanta tana sauke numfashi, Ya sauka daga kan gadon ya zura ƙafafunsa cikin Gucci slippers ɗin da ke gefen gadon masu taushi, Ya zura hannayensa cikin aljihun 3-quater dake jikinsa sannan ya yi waje. Zahra ta bi shi da idanu sai kuma ta koma gefen gadon nata ta zauna.

A fusace ya tura ƙofar ɗakin, Ya sameta zaune gefen gado ta rufe fuskarta da hannunta sai kuka take a hankali, Karasowa ciki ya yi yana watsa mata wani mugun kallo ya ce

“And what is this? Baki da hankali ne ko me? Are you out of ur sense da zaki shigo mana ɗaki babu ko sallama ballantana ki yi alerting ɗin mu?.”

Ya ƙare maganar a zafafe, Shiru Nana ta yi masa dan ba zaka taɓa ɗauka da ita yake ba, Ya yi kwafa sannan ya sake cewa

“Na fuskanci sai na fara gyara miki zamanki a cikin gidan nan. Kina da buƙatar lesson”

Buɗe fuskarta ta yi wadda ta yi caɓa-caɓa da hawaye da majina ta ce“To ni ka sakeni mana, kawai ka sakeni, wallahi ba zan ci gaba da zama a haka ba. Tun ɗazu nake ta knocking a ɗakin ka ashe baka nan, kuma sai kaje wajenta” ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka, Da mamaki ya dinga kallon ta, can kuma ya sunkuya daidai tsayinta ya sanya hannunsa ya ɗago kanta ya ce

“Ban ji ba sake faɗa.”

Ɗauke fuskarta ta yi ta mike tsaye bayan ta goge hawayenta ta ƙarasa press ɗinta, wata yar ƙaramar trolley ta janyo ta buɗe sannan ta fara kaso kayanta ta fara zubawa ciki tana yi tana tsayawa share hawaye. Abdusammad kuwa tsayawa ya yi a wajen kamar gunki yana kallonta, Sai da ta cikata da kaya sannan ta mayar da rufe dakyar ta ɗagata ta fito da hannunta ta fara ja tana ƙoƙarin fita daga ɗakin.

A gabanta ta gansa yana watsa mata wani mugun kallo wanda ya sanyata sunkuyar da kanta tana ci gaba da hawayenta. Ya fizge trolley ɗin daga hannunta rai ɓace ya ce“Ina zaki je kenan?” a fusace ita ma ta ce“gidan mu mana, wallahi sai na tafi gida..Ni ba zan zauna kana zuwa wajenta ba, Allah tafiyata zan yi, ai daman ban ce ina sonka ba!”

Shiru ya yi yana son fahimtar abin da take nufi, Ya ja dogon numfashi ya sauke yana ƙoƙarin saita kansa ya ce“Saboda naje wajen Zahra shi ne zaki tafi? Idan ban je wajenta ba gurin wa zan je?.”

Ya ƙare maganar yana harɗe hannayensa a ƙirji, Cikin kuka ta ce“to nima ba matarka bace? Ai haka Abba ya ce min, kuma shi ne ka ke zuwa wajenta a haka?” Ta ƙare maganar tana nuna masa jikinsa, Kallon jikinsa ya yi da ɗan mamaki sai kuma ya kalleta ya ce“to me shigar jikina ta yi Nana?”

“To ni dan Allah zan iya zama a haka ne? Kuma ita ma sai ta saka riga yar ƙarama!”

Ta rushe da wani sabon kukan tana jan numfashi. Murmushi ne ya tawo masa, Ya ɗan ci mur yana takawa gabanta, gaba ɗaya ya gama gano inda ta dosa, Dan haka ya ɗago fuskarta yana kare mata kallo ganin yanda ta shagwaɓe ya ce

“Kenan ba zan je wajenta da kayan jikina ba? Ita ma kuma haka? To ai matata ce. Ko ke ɗin nan zaki iya zama a haka idan ina nan, ko baki sani ba?”

Ɗago idanunta ta yi da sauri ta kalleshi, lokaci ɗaya kuma ta shiga girgiza kanta kafin ta ce“a’a ni a’a wallahi, ba zan iya ba. Ni bana so”

“Ko?”

Ya ce yana kafeta da idanu. Tura baki ta yi gaba tana dauke kanta daga gare shi ta ce“ni Allah bana son iskanci.”

Jinjina kansa ya yi sai kuma ya ɗan yi baya ya ce“Dan kin zauna a gurina da karamar riga shi ne iskancin?” Sunkuyar da kanta ta yi sannan ta gyaɗa masa kai. Ya jinjina kansa sannan ya juya kamar zai fita, Key ya sakawa ƙofar ya rufe ruf sannan ya juyo yana kallonta ya ce

“To yanzu nake son ki yi iskancin!”

Daga haka ya nufota yana ƙoƙarin cire agogon dake maƙale a hannunsa.

Ja da baya Nana ta fara yi tana zazzaro idanu. Sai da ta kai ƙarshen bango ta maƙale tana kallon sa kamar zata yi kuka, Abdusammad ya yi wurgi da agogon kan gado ya matso dab da ita har suna jin hucin numfashin juna. Ta sunkuyar da kanta ƙasa bakinta na rawa ta ce“Nin…Ni dai uncle bana so wallahi, Dan Allah ka matsa.”

Shiru ya yi mata har sannan sai kallonta yake. Ya sanya hannunsa na dama ya ɗago fuskarta, Ya sauke wani zazzafan numfashi yana ƙarema kyakkyawar fuskarta kallo, Ita kuwa sai sake turo baki take tana ƙunƙuni. Ɗayan hannunsa ya kai ya shafi lips ɗinta, Ta yi saurin rufe idanunta lokaci ɗaya jikinta ya fara wani irin rawa kamar mazari. A hankali ya dinga shafar lips ɗin nata masu taushi, kafin daga bisani ya goge gaba ɗaya lip gloss ɗin data saka. Bata yi aune ba taki taji ya kai mata rankwashi aka, Ta dafe kanta da hannunta kamar zata yi kuka ta ce

“wayyo zafi fa uncle.”

Taɓe baki ya yi yana watsa mata wani kallo ya ce“kar na sake ganin kin shafa wannan abun kin ji abin da nace.?” Gyaɗa masa kai ta yi tana marairaice fuska. Ya ɗauke hannunsa daga kan fuskarta sannan ya ce“da ki ka je ɗakin nawa me zaki ce min?” Ya yi maganar yana ƙarasawa kan Italian bed ɗin nata, Ya zauna. Da sauri tabi bayansa ta zauna gefensa ta ɗora duka hannayenta biyu akan cinyarsa sannan ta ce“To ba yunwa nake ji ba uncle. Kamar zan mutu fa” Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba can kuma ya ce“To me ya hanaki cin abincin?”

“Uncle ai ban iya girki ba.”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *