⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 34: Chapter 34

“wash, wasa-wasa da nisa fa daga apartment ɗin ku.”

Ita dai Nana bata ce komai ba ta ajiye warmern a ƙasa sannan ta zauna gefenta. Shiru Khadijah ta yi tana kallon ta, Nana ta ɗan yi murmushi ta ce

“Na ɗauka ba zaki zo ba. Ya su Ameema?”

“mene ya same ki Nana?”

Khadijah ta tambayeta tana kafeta da idanu. Girgiza kai Nana ta yi a sanyaye ta ce“bakomai fa” wata uwar harara ta maka mata kafin ta ce“nabi ba komai da gudu. Just tell me my friend!”

Shiru Nana ta yi tana kallon ta, ba zata taɓa iya faɗa mata ba abin da uncle ɗin ya yi mata ba. Dan ta san hakan ba daidai bane, Jin yanda ta yi shiru ya sanya Khadijah cewa“Idan kina ganin na takura ki bar shi kawai.”

“Mimi baki ji ba wai na auri uncle? Bai baki mamaki ba? Dan Allah kuma sai na zauna da uncle?”

Nana ta jera mata tambayoyin tana kallon ta. Murmushi Khadijah ta yi ta ce“To mene? Ni daɗi naji wallahi, saboda na san zai kula dake fiye da kowa a gidan nan.” Taɓe baki Nana ta yi kafin ta ce“to ta ina zai kula dani ɗin? Bayan kuma yana da mata.”

Kallon ta Khadijah ta yi, kamar ba zata yi magana ba can kuma ta ce“ke wait! Ba matar dana gani a ƙasan ba ce Zahra?” gyaɗa mata kai Nana tayi. Khadijah ta ce“kenan ita ce kishiyarki yanzu?” nan ma sake gyaɗa mata kan tayi. Khadijah ta gyara zamanta sannan ta ce“Yanzu tsaya wani abun ya taɓa haɗaki dashi? Ai na san kin gane me nake nufi” girgiza mata kai Nana ta yi dan ta fuskanci abin da take nufin. Khadijah ta ce“But why? Bazai taɓa yiwuwa ba!.” Da mamaki Nana ke kallon ta, can kuma ta ce“Mimi me ki ke nufi ne? Ni ban gane ba”

Kamo hannunta Khadijah ta yi ta sake matsowa kusa da ita yanda zata fahimce abin da zata faɗa ta fara cewa“kina ji…”

****
Anty Khadijah ce zaune gaban Malam sai Kaddu a gefenta, Ganin sai dube-dube yake bai ce komai ba ya sanya ta ce“Malam lafiya dai?” ɗago kansa ya yi bakinsa ɗauke da asiwaki yana taunawa ya ce“an gama. Bukatar ki zata biya, zaki aure shi, sannan kuma waccan yarinyar zata fito daga cikin gidan ke kuma ki maye gurbinta.” wani kyakkyawan murmushi Anty Khadijah ta yi, Ta juya ta kalli Kaddu, itama murmushin take kafin ta ce

“To malam abun sadaƙa fa?”

Girgiza kansa ya yi ya ce“Kamar dai yanda aka saba. Sai dai wannan karan zan baki wani abu da zaki yi amfani dashi” Ko kaɗan bata damu ba ta ce“Tom Malam, an gode Allah ya ƙara girma.” Murmushi kawai ya yi yana kallonta ta ƙasan ido yana suɗe baki. Anty Khadijah ta kalli Kaddu ta ce“To zaki jira mu ko tafiya zaki yi?” girgiza kai Kaddu ta yi ta ce“no I’ll wait.”

To kawai ta ce sannan ta miƙe ta nufi ɗayan soron, Shima ya tashi yana tattare babbar rigarsa yabi bayanta.

****
Khadijah ta dinga kallon ta ganin yanda take abu kamar wadda bata da kala, Ta ɗan ja tsaki ta ƙarasa gabanta ta karɓi plate ɗin ta ce

“kin tsaya sai wani tafiya ki ke kamar kwai ya fashe miki.”

Tura baki Nana ta yi, Ta ƙarasa gaban tukunyar ta buɗe, Saurin matsawa ta yi daga wajen tana dariya ta ce“Mimi kin ga.” Khadijah dake jera plate ɗin akan tray ta ce“mene?”

“Ya dahu wallahi”

Ajiye plate ɗin ta yi ta ƙaraso gaban tunkuyar, Leƙawa ta yi taga yanda fried rice ɗin ta yi kyau ko a ido, Ta yi murmushi tana kallon Nana ta ce“ai kuwa, ashe kin iya girkin iskanci ne.” dariya kawai Nana ta yi, ta mayar da murfin ta rufe taja ta tsaya, Khadijah ta koma ta ɗauko tray ɗin tana kallon ta ta ce“A nan parlourn zan ajiye ko a ɗaki?”

“ko a parlourn zai fi ina ga.”

Okay kawai Khadijah ta ce sannan ta fice daga kitchen ɗin. Nana tabi ta da kallo, lokaci ɗaya maganganun Khadijah suka fara dawo mata. Murmushi ta yi can kuma kamar wadda ta tuna wani abu ta tura baki. Tana nan tsaye har Khadijahn ta dawo. Ta dinga kallon ta sai kuma ta wuce ta ɗauko wata sabuwar warmer ta ƙaraso wajen tunkuyar ta ce“kina nan tsaye har sai ya dawo ma.”

“To ai ba yanzu yake dawowa ba.”

Nana ta yi maganar a ɗan ƙufule, Sai da ta gama zuba shinkafar a cikin warmern ta mayar da rufe sannan ta ce“to zauna sai ya dawo, dalla ki je ki yi wanka.”

Tura baki ta yi ta ce“nifa wallahi tsoro nake ji.”

Sak Khadijah ta yi tana kallonta, can kuma ta ce“tsoro? Tsoro fa ki ka ce Nana. Kenan duk abin da nayi ya tashi a banza kenan?”

“To dan Allah ya zan yi? Uncle ne fa.”

“Da yake uncle ɗin ki amma yanzu mijinki ne.”

Saurin kallonta Nana ta yi, Ta gyaɗa mata kai fuska babu walwala. Bata sake cewa komai ba ta yi waje, Khadijah ta bita da idanu sai kuma ta girgiza kanta tabi bayanta. Nana ta fita daƙinta ta shige, ta daɗe tsaye a tsakiyar ɗakin kafin daga bisani ta sauke numfashi ta nufi toilet. Wanka ta yi ta fito tana tsane ruwan jikinta da towel, Gaban dresser ɗinta ta ƙarasa ta fara shafe-shafen mayuka. Bayan ta gama ta saka turaren da Amma ta bada aka kawo mata, nan da nan ɗakin ya gauraye da sassayan ƙamshi. Yar simple make-up ta yiwa fuskarta ta shafa lip gloss, Bayan ta gama ta ƙarasa gaban press ɗinta ta buɗe. Shiru ta yi tana kallon jerin kayan da suke cikin press ɗin a jere, Tana nan tsaye aka buɗe ƙofar. Khadijah dake tsaye tun ɗazu tana kallonta ta ce“wai har yanzu baki ga kayan da zaki saka bane?” juyowa ta yi tana kallonta kamar zata yi kuka ta ce“To dan Allah me zan saka?” taɓe baki Khadijah ta yi ta ƙaraso ciki tana kallon ta, tsayawa ta yi kusa da ita tana ƙarewa press ɗin kallon. Ta jima a tsayen can kuma ta jawo wata doguwar riga, Miƙawa Nana ta yi tana murmushi ta ce“ki saka wannan zai miki kyau” amsa Nana ta yi tana shafa rigar, ta juya ta koma toilet. Murmushi kawai Khadijah ta yi sai kuma ta koma kan kujerar dake jigin gadon. Bata jima ba ta fito tana sanye da Egyptian Abayar nude colour, wata mai flower a ƙirji da kuma hannun rigar. Tashi tsaye Khadijah ta yi tana murmushi ta ce

“wowww! Kin ga yanda ki ka yi kyau?”

Murmushi Nana ta yi ta ƙarasa jikin madubi, Ita kanta ta san rigar ta yi mata kyau. Ta kai hannunta ta shafa rigar tana murmushi ta ce“nayi kyau?”

Gyaɗa mata kai Khadijah ta yi, ta karɓi veil ɗin rigar dake hannun Nana ta ce“Zo na ɗaura miki.” To kawai Nana ta ce, Khadijah ta ɗaura mata ɗankwalin mai tuta a gefe. Wani irin kyau ta yi kamar ba ita ba, Khadijah ta ja kumatunta ta ce“Sai dake kyakkyawar matar uncle” wani irin fari Nana ta yi da ido suka tuntsire da dariya a tare.

****
A dai-dai round about ɗin ta tsaya, Ta juya tana kallon Kaddu dake gefenta ta ce“Ba gida zaki yi bane?” girgiza mata kai Kaddu ta yi tana shafa wayarta ta ce“A’a akwai wanda zai zo ya ɗaukeni kawai saukeni anan.” okay Anty Khadijah ta ce, Kaddu ta buɗe motar tana shirin sauka, kamar wadda ta tuna wani abu sai kuma ta koma ta zauna ta ce“Mantawa nayi zan tafi. Yanzu ya za’a yi wai?”

“Yanda muka shirya mana. Dole Zahra ta fito daga gidan, idan Allah ya kaimu gobe zan yi je gidan na kai mata maganin.” Jinjina kai Kaddu ta yi kafin ta ce“Eh ki yi da sauri. Saboda kada su bar ƙasar” wani shu’umin murmushi Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“ai idan ki ka ga an bar ƙasar nan to da ni ne bada Zahra ba!”.

Murmushi Kaddu ta yi ta ce“Nagode ƙawata. Ki ce nan bada jimawa ba zamu fara ƙirga dollars?” Anty Khadijah ta sake murmushi tana cije laɓɓanta ta ce“Ai idan ki ka ce dollars kaɗan ma kenan, Ke idan da abin da yafi kuɗi wallahi sai kin same shi. Ai ko ke zaman ƙasar nan sai ya gagareki, Ballantana kuma ni, Daga Us nayi uk, daga uku na yi Paris, daga Paris nayi Qatar. Woww!”

Tuntsirewa da dariya suka yi a tare. Kaddu ta ce“tom Allah ya tabbatar ya nuna mana” da Amin ta amsa, Kaddu ta sauka daga motar tana murmushi, Anty Khadijah taja motar ta bar wajen. Bata fi 2mins a tsaye ba wata babbar mota ta yi parking a wajen, Kaddu ta gyara tsaiwarta tana murmushi kafin ta nufi inda motar take..

****
Ana shirin kiran sallar magriba suka fito, Khadijah ce a gaba sai Nana dake biye da ita, Sai haɗe rai take. A bakin ƙofar parlon suka tsaye, Khadijah ta dafatan ganin yanda ta haɗe rai ya sanyata murmushi kafin ta ce

“To wai mene abun haɗe ran? Da ban zo bafa”

Kamar zata yi kuka ta ce“To dan Allah ba sai ki kwana ba. Daga zuwanki”

Waro idanu Khadijah ta yi, Ta girgiza kanta ta ce“flight ɗin safe zan bi zuwa Kano. Kin ga ai ba zan kwana ba, Ke dai ki bari nan bada jimawa ba zan zo idan kuma kun tafi US shikenan”

“Ni ba zan bisu ba”

Cewar Nana a shaƙe. Taɓe baki Khadijah ta yi ta ce“To sai ki yi ta zama a gida ai. Ni kin ga tafiyata, ki koma ciki”

“Ba zaki zo na rakaki wajen Maimoon ba?”

Tsayawa Khadijah tayi akan stairs ɗin balcony ɗin, Ta juyo tana kallonta kafin ta ce“To ai baki tambaya ba.”

Tuni Nana ta ware mayafin dake kanta ta yafa ta yi gaba tana cewa“Ke ni ba’a hanani fita ba.” Murmushi kawai Khadijah ta yi sai kuma tabi bayanta.

Maimoon na riƙe da turaren wuta aka buɗe kofar parlourn, Duk zatonta Yaya Aliyu ne ya dawo. Ganin su Nana ya sanya ta ajiye kaskon ta nufosu tana murmushi ta ce“Laaa amarya ce da ƙawarta?. Sannunku da zuwa” Murmushi suka yi Nana ta janyeta daga jikinta tana cewa

“Ni bari kar ki shafa min ciki”

Harararsa Maimoon ta yi tana riƙe da hannun Khadijah ta ce“Ai ba sai na shafa miki ba, nan bada jimawa ba zaki ganki dashi”

“Bakin ki ya sari ɗanyen kashi!”

Cewar Nana bayan ta zauna kan ɗaya daga cikin luxury sofa ɗin dake zagaye da parlon. Maimoon bata sake bi ta kanta ba ta shige kitchen, Drinks ta kawo musu sannan ta sake komawa. Nana ta kalli Khadijah wadda ta yi shiru ta ce“Ke kar ki sha”

“A saboda me zaki hanata sha?”

Ta tsinkayi muryar Maimoon ɗin a kanta, Komawa ta yi ta jingina da jikin kujera ta ce“To sai ta cika cikinta da abinci”

“To ina ruwanki?”

Maimoon ɗin ta sake tambayarta a fusace. Harararta Nana ta yi sanin halin jarabarta ta ce“Da ruwana ɗin, Kuma wallahi sai na faɗawa Yaya Aliyu.”

Wani dogon tsaki Maimoon ta ja sannan ta ƙarasa gaban Khadijah da kanta ta zuba mata ruwan a glass cup ta miƙa mata, Khadijah ta karɓa tana murmushi sannan ta sha. Hira suka dinga yi da Khadijahn kasancewar ta santa sosai a Aun, Ita kuwa Nana ko kallon inda suke bata yi ba, hankalinta na kan wani movie da ake haskawa a mbc max. Suna nan zaune har after 15mins Khadijah ta miƙe tana kallon agogon dake maƙale a parlourn ta ce“Bari naje kar dare ya yi min”

Miƙawa Maimoon ta yi ta ce“Ayya daga zuwanki?” murmushi Khadijah ta yi ta ce“Wallahi da shigewa ma fa zan yi, Nana ce ta ce mu zo.” sai a sannan ta mai da Idanunta kan Nana wadda ke kallon tv,Ta yi murmushi kamar ba ita ta gama yi mata masifa ba ta ce“Hajiya Nana irin wannan kwalliya haka? Ki ce amarcin ake zubawa.” ba zaka taɓa cewa da Nana take ba dan ko inda take bata kalla ba, Maimoon ta kalli Khadijah wadda ita ma take kallon Nanar sai kuma ta ce“kin san halin mutuniyar. Ina zuwa Mimi”

Okay kawai Khadijah ta ce, Maimoon ta bar parlour da sauri, Sai a sannan Khadijah ta ƙarasa Kujerar da take ta zauna tana murmushi ta ce“Haba mana Nanar uncle fushi fa ba naki bane”

“Ce miki nayi fushi nayi?”

Ta yi tambayar tana kallonta, Girgiza kai Khadijah ta yi, Nana ta sake ɗauke kanta ba tare da ta sake cewa komai ba. Itama Khadijahn shiru ta yi dan ta fuskanci abun ne ya motsa, ba’a wani jima ba Maimoon ta dawo parlourn hannunta riƙe da wata leda mai ɗan fadi,Ta miƙawa Khadijah dake tsaye ta ce

“Sorry dan Allah ba yawa kin ji.”

Murmushi Khadijah ta yi kafin ta amsa ta ce“Allah sarki Maimoon uwar kyauta. Thank you, Allah ya raba lafiya” Da Amin ta amsa, Nana ta miƙe ta yi waje without say anything. Da idanu duk suka bita, Sai kuma Maimoon ta dafata ta ce“kada ki biye mata kin san halinta” murmushi Khadijah ta yi ta ce“nii I’ll not.” Suka sake sallama sannan ta bar parlour, Koda ta fita tsaye ta hangeta gaban motar da aka kawota ta cake a wajen kamar wadda aka dasata, Khadijah ta girgiza kanta sai kuma ta ƙarasa wajen, Buɗe motar ta yi ta shiga bayan Nanar ta matsa, Ta kalleta ta ce“Sai an jima.”

“Ki gaida su Mami”

Ta yi maganar a shaƙe.

“Zasu ji” cewar Khadijah tana rufe motar, drivern ya ja motar suka bar wajen, Da idanu Nana tabi motar tasu har suka ɓacewa ganinta, ta sauke numfashi sannan ta nufi hanyar komawa apartment ɗinta.

Tunda ta tawo ta hangeshi tsaye gaban motarsa, da alama dawowarsa kenan. Dan haka ta ƙara saurin da take dan ba son magana take dashi ba, Cikin rashin sa’a idanunsa ya kalli inda take, Kasancewar da wadataccen haske a wajen kuma gari bai gama duhu ba ya sanya ya ganeta, Gaba ta yi ba tare da ta kalli ko inda yake ba. Safwan ya biyo bayanta da sauri yana kiran sunanta, Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba. Ya karasa gaban nata yana haki saboda saurin da ya yi kasancewar ba lafiya gare shi ba. Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta masu ɗauke da zanen henna har sannan, Safwan ya ja dogon numfashi ya sauke kafin ya ce

“Nana na san na aikata kuskure, na karya alƙawarin da nayi miki. Amma dan Allah ina neman afuwarki, ki yafe min, wallahi zuciyata ta kasa samun sukuni. Na kasa samun abin da nake so, koda yaushe tunanin ki nake, ina tunanin abin da nayi miki. Dan Allah dan Annabi Nana ki yafe min.”

Ya ƙare maganar cikin wani irin sanyin murya. Sosai taji jikinta ya yi sanyi, Duk da riko ta kasance ɗabi’arta amma taji zata iya yafewa Yaya Safwan ɗin, dan haka ta sauke numfashi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce

“Ni na riga da na yafe maka Ya Safwan. Na san duk abin da ya faru ƙaddara ce, kuma ban isa na guje mata ba, dan haka ka daina damuwa akan wannan abun, Ya riga da ya shige har abada.”

Ajiyar zuciya Safwan ya sauke yana jin wani abu na faɗa masa wanda da ya tokare masa a ƙirji, Ya jinjina kansa kafin ya ce“Allah sarki, nagode sosai Nana, Allah ya baku zaman lafiya da Yaya, Ya kaɗe fitina a cikin auren ku. Ya baku zuri’a ta gari.”

“Amin na gode Yaya.”

Ta amsa cikin wani irin yanayi, Ita kanta ta gaza gane abin da hakan ke nufi. Zuciyarta sai bugawa take, sun ɗauki a ƙalla mintina biyu babu wanda ya ce da wani ƙala, can dai Safwan ɗin ya ce“Tom sai da safe Nana, Allah ya bamu alkhairi.”

Kamar jira take ta ce“Amin ya rabbi.”

Daga haka ya matsa mata ta yi gaba.

“Nana!”

Safwan ya sake kiran sunanta, Juyowa ta yi ta kalleshi. Ya tako har gabanta ya ce

“Mantawa nayi zan faɗa miki ki dinga addu’a Nana. Ki riƙe addu’a kin ji” gyaɗa masa kai ta yi kafin ta ce“Tom in sha Allah Yaya” Murmushi kawai ya yi, Ta dinga kallonsa ganin yanda kamarsa da Uncle Abdusammad ta fito. Ya ce“tom jeki” gyaɗa kanta kawai ta yi sannan ta juya ta ci gaba da tafiya, Shima ya koma inda ya bar key ɗin motarsa ya dauka sannan ya nufi cikin gidansa.

****
Gajiya ta yi da jiransa ta yi kwanciyarta akan sofa, nan da nan kuma wani bacci ya ɗauketa. Sai kusan ƙarfe 10:30 na dare ya shigo gidan, Kai tsaye kuma ɗakinsa ya nufa, Ya watsa ruwa ya fito ya koma ƙasa. Kasancewar Zahra ke girki ya sanya ya zauna a ƙasan, Ta kawo masa abinci, fuskarsa a sake suka ci tare. Bayan sun gama wani guard ya shigo hannunsa riƙe da ledoji guda biyu, A gabansa ya ajiye sannan ya juya ya fice. Abdusammad ya tura mata ɗaya daga cikin ledojin, Karɓa ta yi ta buɗe gasasshiyar kaza ce a ciki guda biyu, Sai ice-cream na roba manya guda biyu. Ta yi murmushi ta ce“to an gode Allah ya ƙara arziki.” da Amin ya amsa sannan ta tashi ta kwashe kaf kayan da suka yi amfani dasu ta kai Kitchen, Koda ta sake dawowa a tsaye ga ganshi ya kalleta ya ce“sai da safe ko.”

Murmushi ta yi duk da yanda take jin babu dad’i ƙasan ranta haka ta daure ta ce“tom Allah ya tashe mu lafiya.” Amin kawai ya ce sannan ya nufi upstairs hannunsa riƙe da ɗaya ledar. Sai da ya yi jim a bakin ƙofar kafin ya murɗa handle ɗin a hankali, Kwance ya hangeta kan sofa ta rufe fuskarta da hannayenta. Sam bai yi tunanin bacci take ba, Dan haka ya ƙarasa ciki ya ajiye ledar hannunsa akan table sannan ya taɓa ta ya ce

“Nana! Nana!”

Kasancewar bata da nauyin bacci ya sanyata buɗe idanunta, Ta tashi zaune tana murza idanun, lokaci ɗaya kuma ta zabura ta sauka daga kan kujerar. Bai ce mata komai ba ya gyara zamansa kan kujerar, Ta koma can nesa dashi ta zauna sannan ta ce“Sannu da zuwa”

“Yauwa!”

Ya ce ba tare da ya kalleta ba. Shiru wajen ya ɗauka, Ta dinga kallon sa ganin yanda ya yake danna wayarsa hankali kwance. Can dai ta miƙe tuna abin da Khadijah ta ce mata, Ta nufi dining area ɗin dake cikin parlon, ta gefen ido ya kalleta sai kuma ya ci gaba da abin da yake. Ɗaya bayan ɗaya ta kwaso kayan tsaf ta jera akan dining, Bai san sanda ya ajiye wayar hannunsa ba ya dinga kallon ta da mugun mamaki. A gabansa ta tsuguna ta ɗan kalleshi sai kuma ta dauke kanta ta dauko plate ta ce

“Me zan zuba maka?”

Abdusammad da mamaki ya kusa daskarar dashi ya girgiza kansa a sanyaye ya ce“Girki ki ka yi Nana? Wane ya saka ki girki?” Ya jera mata tambayoyin har sannan idanunsa akan ta yana mamakin abun. Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta kamar ba ita ba ta ce“Ni ce na dafa maka, ai kai mijina ne kuma ni zan dinga yi maka girki yanzu.” ta yi maganar a shagwaɓe. Murmushi ya yi yana girgiza kansa ya ce

“To naji nagode Nana, amma ni yanzu na ƙoshi naci abinci.”

Da sauri ta kalleshi, lokaci ɗaya annurin dake man fuskarta ya ɓace, Ta yi sak tana kallon sa. Kamar ba zata yi magana sai kuma ta ce“Shi ne kaci abincin? To a ina kaci abincin?”

“To ay ban san kin yi girki ba Nana. Zahra ce ta dafa naci a ƙasa”

Da wani irin mamaki take kallon sa, nan da nan hawaye ya cika fuskarta, Ta tashi daga wajen ta koma can ƙarshen parlourn ta silale a ƙasa ta fashe da wani raunataccen kuka. Abdusammad ya dinga kallonta lokaci ɗaya kuma ya tuna abin da ya ce, Ya kai hannunsa ya rufe bakinsa ya ce

“Na jangwalo masifa.”

Ya miƙe yana shirin zuwa wajen da take, Tana ganin haka ta mike tsaye tana wani irin kuka kamar zararriya ta ce

“Ni kada ka zo kusa dani! Kada ka zo inda nake! Tun da ita kake so, Ai daman ita ce matarka. Ni kuma baka sona, Saboda ni ba irin wadda ka ke so ba ce, Shi ne kaje ka ci abincinta bayan kuma kwana na ne, Shi ne kaje ka ci abincinta tun da ita ka ke so…”

Ta kasa ci gaba da maganar saboda kukan da yaci ƙarfinta, Girgiza kansa ya yi yana tsaye a inda yake ya ce“Ba haka bane Nana, ban san kin dafa abinci ba ai, dana sani ba zan ci a wajenta ba. Ke kuma ki ka ce min baki iya girki ba ko..”

“Ai daman saboda haka kaje ka ci a wajenta, saboda ni ƙazanta zan yi maka. Daman ai ita ka ke so, Kuma ita ka ke fara zuwa ka gani, ni kuma babu ruwanka dani. Wallahi ba zan yarda ba!”

Ta ƙare maganar cikin gunjin kuka, Sake yo gaba ya yi a ƙoƙarinsa na son zuwa inda take, Ta daka uban tsalle ta bar wajen da gudu. Bedroom ɗinta ta shige ta garƙame ƙofar da maƙulli, Ya dafe kansa sai kuma ya nufi wajen gudun tashin hankali yasa ya taya a bakin ƙofar muryarsa a sanyaye ya ce

“Look Nana, ba nace miki ban sani ba, Ki buɗe ƙofar ki ji. Ki daina kukan”

Tana tsaye jikin ƙofar sai kukanta take, Jin bata ce komai ba ya sanya shi sake cewa “To shikenan ki buɗe ƙofar zan baki abin daɗi, har kaza na siyo miki kin ji ki buɗe ƙofar”

A hankali ta tsagaita da kukan, Ta matsa daga jikin ƙofar har sannan tana shessheƙar kuka, Jin ta fara yin shiru ya sanya ya ce

“Yauwa buɗe kin ji Nanata, Yar ƙaramar matar uncle ɗinta. Buɗe kin ji”

“Ka miƙo min kazar kawai”

Ya tsinkayi muryarta. Shiru ya yi sai kuma ya ce“to ai kin ga babu window anan, ki buɗe ƙofar sai na miƙo miki na tafi.” Shiru ta yi tana jin kamar ta buɗe ƙofar, Ta goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta ce“to ina kazar?”

“Bari na ɗauko”

Ya ce a hankali. Daga haka ya koma inda ya ajiye ledar kazar ya ɗauko ya dawo bakin ƙofar sannan ya ce

“Gata a hannuna, Buɗe sai ki karɓa.”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *