Chapter 35: Chapter 35
A hankali ta zare key ɗin dake jikin ƙofar, ta ɗan buɗe kaɗan ta zuro hannunta na dama ta ce“Bani ga hannuna.” yanda ta yi maganar ya kusa sanya shi tuntsirewa da dariya amma ya dake ya miƙa mata kazar, Tana ƙoƙarin ƙarba ne taji ya jawo hannun nata gaba ɗaya. Ta zunduma ihu jin ya buɗe ƙofar ɗakin duka, Ya shigo ciki har sannan yana rike da hannun nata da kuma ledar kazar, Ƙoƙarin janye nata hannun ta dinga yi, sai dai irin riƙon da ya yiwa Hannun bana wasa bane. Dan haka ta kasa, Da ɗaya hannun nasa ya ɗagata cak bai sauketa ko ina ba sai kan gadon, Ya saki hannunta yana ƙoƙarin zama, Juyawa ta yi tana shirin barin wajen taji ya jawota ta faɗo jikinsa. A hankali ya sanya duk hannayensa biyu ya rungumeta a faffaɗan ƙirjinsa, Nana ta fara ƙoƙarin janye jikinta tana kuka a hankali, Murmushi ya yi ya ja hancinta ya ce
“iyye! Ƴar yarinyar ƙarama zata min wayo. Kin san shekarun dana baki kuwa?”
Ko saurarensa bata yi ba ta ci gaba da kukanta, Ya kalli ɗan ƙaramin bakin nata wanda ya sha lip gloss sai sheƙi yake. Haka kawai yaji tsigar jikinsa na tashi, Koda wasa bai son yaga mace ta saka lip gloss musamman idan yana da alaƙa da ita, Yanzu zai yi jikinsa na neman sauyawa. Ya fara ƙoƙarin kai hannunsa domin ya goge mata, danƙon da yaji yasa ya tabbatar da ba kaɗan ta shafa ba, kuma ba lallai ya fitan a hakan ba, Dan haka ya ɗago fuskarta da hannunsa ɗaya. A hankali kuma ya durƙusar da kansa daidai fuskarta, Lokaci ɗaya kuma ya ɗora bakin nasa akan nata ya fara tsotsa a hankali. Wata irin zabura Nana ta yi, Ta ƙamkameshi tana jin wani irin fitsari na tawo mata, sai da ya suɗe kaf man leɓan bakin nata sannan ya sanya ɗayan hannunsa ya buɗe bakin nata, Cikin hanzari kuma ya zura bakin cikin nata. Kusan sumewa Nana ta yi jin yanda yake sauke mata wasu azababbun kisses, nan da nan jikinta ya saki ta gagara koda motsa ɗan yatsanta ne. Jin hannunsa akan ƙirjinta ya sanya sakin wani marayan kuka, Cikin ikon Allah ta sanya hannayenta duk biyun ta ture shi, Kasancewar jikinsa a sake yake ya sanya ya yi baya, Ta tashi da gudu ta shige toilet ta rufe ƙofar gam. Tashi ya yi ya biyo bayanta ya tsaya a bakin ƙofar muryarsa a ɗan shaƙe ya ce
“Kee! Nana! Nana!”
Ban da kuka babu abin da take, Ta sulale a ƙasan bayin tana kukanta, Buɗe gajiyayyun idanunsa ya yi akan ƙofar kamar ba zai magana sai kuma ya ce
“Ki ka ce na shirya cin amarci na siyo miki kaza. To gashi na kawo miki ai”
Girgiza kanta ta dinga yi cikin kuka ta ce“a’a uncle ni bana son kazar, wallahi bana so! Bana son kazar amarcin, ka ɗauki kazar ka tafi da ita.”
Sauke zazzafan numfashi ya yi jikinsa har wani rawa yake ya ce
“Ai baki isa ba! Tun da ki ka yarda na kawo kaza dole ki fito naci amarcin!”
Sake rushewa ta yi da wani sabon kukan ba tare da ta ce komai ba, Ya yi shiru yana sauraren sautin kukan nata kafin ya sake cewa“Idan ki ka bari na buɗe ƙofar nan da kai na sai na baki mamaki!” Sake cure jikinta ta yi waje ɗaya ta sanya hannunta ta rufe bakinta tana ci gaba da kukanta a hankali. Above 5mins kafin ya sauke numfashi ya juya ya bar ɗakin, Tana jin ƙarar rufe ƙofa amma sam taƙi tashi ta fito, Dan tunaninta ba tafiyar ya yi ba. Tana nan zaune har kusan ƙarfe 11:00 na dare, Bacci ya fara ɗaukanta a zaunen, Gajiya ta yi dan kanta ta tashi ta buɗe ƙofar toilet ɗin a hankali tana leƙa ɗakin. Ganin da gaske babu kowa a ciki ya sanya ta fito, Kai tsyae kuma wajen ƙofa ta nufa ta murɗa key kuma ta bar shi a jiki, Sannan ta koma ta cire kayanta ta ɗauki na bacci ta saka ta hau kan gadon, Ko ta kan ledar kazar dake wajen bata yi ba. Ta duƙunƙune jikinta da duvet sannan ta rufe idanunta, Sai dai kuma sam baccin yaƙi zuwar mata gani take idan ta rufe idanunta Abdusammad zai dawo ɗakin ne. Dan haka ta fara kuka a hankali, A haka har bacci ɓarawo ya saceta.
Washegari around 9am ya tsaya jikin ƙofar, Kamar ya tafi sai kuma ya fara knocking a hankali. Nana dake zaune ƙasan gado ta jingina kanta da jikin gadon ta ɗago kanta a firgice, Kallon ƙofar ta dinga yi jiki a sanyaye. Ya ci gaba da knocking dan duk tunaninsa bacci take yi, Ganin bata da niyyar buɗewa ya sanya ya ce
“Nana! Nana! Nana!”
Kasa amsawa ta yi, Nan da nan jikinta ya fara rawa. Dan ita har ga Allah yanzu tsoronsa take, Ta miƙe ta koma can ƙarshen gado ta zauna tana ci gaba da kallon ƙofar. Gajiya ya yi da bugun ya ce“Idan ki ka bari na ɗauko maƙulli na bude ƙofar sai ranki ya ɓaci!.”
Tura baki gaba ta yi ta sunkuyar da kanta, Ya bar jikin ƙofar, Shirun da taji an yi ya sanya ta miƙe a hankali ta ƙarasa gaban ƙofar. Ta kasa kunnenta a jikin ƙofar amma bata ji alamar yana nan ba, Dan haka ta zare key ɗin ta buɗe ƙofar ta leƙa a hankali. Cikin rashin sa’a taji ya turo ƙofar da ƙarfi, Ta yi baya ta faɗi cikin ɗakin. Tsayawa ya yi a bakin ƙofar yana ƙare mata kallo, Ta miƙe da gudu ta nufi hanyar toilet, Sai dai kafin ta kai ga ƙarasawa ya sanya ƙafa ya taɗeta, ta yi baya zata faɗi ya riƙota ta faɗa jikinsa. Wata irin zabura Nana ta yi tana ƙoƙarin kwace jikinta, Ya haɗe fuska babu alamar wasa ya ce
“Kin nutsu ko saina mareki?”
Girgiza kanta ta fara yi tana hawaye ta ce“Dan Allah uncle ka yi hakuri, Dan girman Allah wallahi ba zan sake ba. Ba zan ƙara ba, Ka sakeni!”
Ta ƙare maganar tana kuka. Bai ce mata komai ba ya jata har gaban gadon, ya zauna sannan ya zaunar da ita gefensa har sannan babu alamar walwala akan fuskarsa ya ce
“Ni abokin wasanki ne da zan dinga kiran ki kina ji ki min banza? am I play with you?”
Girgiza kanta ta yi a hankali tana sunkuyar da kanta, Ya yi kwafa sannan ya ce“Duk ranar da ki ka sake min irin haka sai na ɓata miki, Kinji abin da na ce.?”
Gyaɗa masa kai ta yi nan ma, Ya yi shiru yana kallon yanda take ta rawar jiki, Ɗauke kansa ya yi yana karewa ɗakin kallo. Lokaci ɗaya idanun sa ya sauka akan ledar kazar dake kan drawer, Miƙewa ya yi ya ƙarasa wajen ya ɗauko ledar ya dawo. Nana na ganin haka ta fara ja da baya, Buɗe ledar ya yi yaga babu abin da ta taɓa a ciki, Ya mayar ya ajiye a ƙasa sannan ya ce
“Kin ci kazar?”
Saurin girgiza masa kai ta yi ta ce“A’a wallahi, Ban ci maka ba uncle. Ban ci ba wallahi!”
Ta ƙare maganar tana kuka, Sake haɗe rai ya yi kafin ya ce“Me yasa? Ba cewa nayi ki ci ba?”
“Na ƙoshi, Ni bana ci.”
Ta yi maganar a sanyaye. Taɓe baki ya yi kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce“To ni yunwa nake ji, Tashi ki mana warming ɗinta sai ki kawon” Jikinta har rawa yake ta mike, ta ɗauki ledar sannan ta fice daga ɗakin. Ya bita da kallo sai kuma ya girgiza kansa yana murmushi.
****
Zahra ta dinga kallon Anty Khadijah da mamaki can kuma ta ce“Lafiya Anty da safen nan?” haɗe rai Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“Dallah magana na zo mu yi dake.” Zahra ta kalli hanyar sama sai kuma ta kalli Anty Khadijah ta ce“Doctor yana nan, muje waje.” Taɓe baki Anty Khadijah ta yi sai kuma ta juya ta fice daga parlourn tana taunar cew gum, Zahra ta sauke numfashi sannan tabi bayanta dan daman hijabi ne a jikinta.
A ƙasan wata bishiya suka zauna kan fararen kujeru, Zahra ta yi shiru tana jiran taji abin da Anty Khadijahn zata ce. Ita kuwa Aunty Khadijah Shiru ta yi tana kallon Zahra kamar yanda malamin ya ce mata, After some minutes Zahra ta ce
“Anty mene ne? Naji kin yi shiru.”
Numfasawa Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“Daman akan maganar auren nan naki ne, na ce wai kin haƙura zaki zauna da kishiya kenan?”
Shiru Zahra ta yi kamar mai tunani, Anty Khadijah ta yi murmushi sannan ta ce“Ki yi tunani Zahra. zamanku da ita ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba, Saboda kin san ita yar uwarsa ce, a gabanki zai dinga nuna mata tafi ki, kuma ma ban da abin ki ya za’a yi mutum ya zauna da yarinyar da ya raina. Har da ke fa aka yi rainonta, Ace kuma yanzu ta zo ta aure mijinki, Tana kwana ɗaki ɗaya dashi, Haba wannan abu har ina!”
Aunty Khadijah ta ƙare maganar tana kallon Zahra to see her reaction. Zahra da duk abin duniya ya dameta ta girgiza kanta jiki a sanyaye ta ce “To ya zan yi Anty? Dole nayi hakuri kamar yanda Umma ta ce min. Da badan na shiga na fita na saka Siyama ta auri Safwan ba da Nana bata auri mijina ba, kin ga ashe Allah ne ya mata sakayya, Dole na yi haƙuri.”
Taɓe baki Anty Khadijah ta yi ta ce“To kenan zaki ci gaba da zama a haka kamar wata mara yanci kenan?”
Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“A’a. Na san doctor ba zai taɓa fifita Nana akaina ba, saboda ya san me yake, Yana da ilimi kuma yana aiki da iliminsa. Har zuwa yanzu ban ga ya yi min wani abu da ke nuna rashin kyautatawa ba.!”
Anty Khadijah ta yi shiru can kuma ta gyaɗa kanta ta ce“Haka ne, To Allah ya ƙara haɗa kan ku.”
“Amin Aunty.”
Zahra ta yi maganar a sanyaye, Anty Khadijah ta ce“Amma duk da haka bai kamata ki zauna haka babu wani abun tsare jiki ba. Kin san ita kishiya muguwar aba ce, Shiyasa na karbo miki wani magani ki samu ki jiƙa da ruwan ɗimi ko shayi ki sha, Babu abin da zai sameki in sha Allah.” Ta ƙare maganar tana laluba jakarta, Zahra ta yi shiru tana kallon ta har ta dauƙo wani ƙullin magani karami. Zahra ta karɓa sannan ta ce“To Anty Nagode sosai Allah ya ƙara girma.” Da Amin ta amsa sannan ta ce“Yaushe zaku koma ne?” Zahra ta yi murmushi ta ce
“Gobe idan Allah ya kai mu.”
Zaro idanu Anty Khadijah ta yi ta ce“Da wuri haka? Amma shi ne baki zo gida ba?”
Zahra ta ce“Nima jiya da daddare yake faɗa min, An jima ai zan zo in sha Allah.” Anty Khadijah ta jinjina kanta tana ƙoƙarin miƙewa ta ce“To Allah ya kai mu.” Tashi ita ma Zahran ta yi ta amsa da Amin sannan ta ce“Ba zaki je wajen Siyama ba?” girgiza kai Anty Khadijah ta yi ta ce“a’a yau ai ba wajenta na zo ba, Sauri nake akwai inda zan je.”
Zahra ta yi murmushi ta ce“To Anty ki gaida gida.”
“Zai ji. Dan Allah Zahra kada ki yi wasa da maganin nan!” Gyaɗa mata kai ta yi tana murmushi ta ce“in sha Allah Anty.” Daga haka suka sake sallama ta nufi motarta ita kuma ta koma ciki.
****
Bakinta ɗauke da sallama ta shigo dakin, Ya amsa a hankali sannan ya kalleta.
“Na gama uncle.”
Ta ce tana wasa da fingers ɗinta, Jinjina kansa ya yi sannan ya tashi tsaye ya ce“okay muje” bata ce komai ba ta juya ta koma parlourn, Yabi bayanta shima. Durƙushe ya sameta gaban kayan tea ɗin data ajiye, Ta hada masa tea ɗin kamar yanda ta san yana sha sannan ta miƙa masa inda ya zauna. Ta jawo masa bowl ɗin data zuba kazar da kuma plate ɗin data zuba Irish potato ɗin data soya, Kallon ta kawai yake har ta gama ajiye komai ta tashi ta koma kan kujera ta zauna, Ya kalleta kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce
“Ke ina naki abincin?”
“Na ƙoshi.”
Ta ce a takaice, Haɗe rai ya yi ya ce“zo nan.” y nuna mata gefen sa, Kasa masa musu ta yi ta taso ta dawo wajen ta zauna ta sunkuyar da kanta, Ya dauko wani mug ɗin ya tsiyaya mata rabin shayin nasa sannan ya tura mata gabanta. Ita dai ba ce komai ba, Ya yi bismillah sannan ya kai tea ɗin bakinsa, Kallon sa ta dinga yi kamar ta samu tv, Ya kalleta ya ce“Wasa nake miki?” Sai a sannan ta ɗauki mug ɗin ta kai bakinta dan ba ƙaramar yunwa take ji ba, kasancewar jiya bata ci abinci ba ta zauna jiransa. Ganin shayin kawai take sha ya sanya ya ce“Ba zaki ci abincin ba?” Ya kare maganar yana tauna naman dake bakinsa, Girgiza masa kai ta yi kafin ta ce“Ni bana ci, na ƙoshi.”
Ya dinga kallon ta can kuma ya ce“Da ki ka ci me?”
“Ni bana ci, Ba zan ci ba.”
Yanda ta yi maganar tana yatsine fuska ya sanya shi murmushi, Ya ce“Saboda me?”
Kamar zata yi kuka ta ce
“To ba ka ce idan naci kazar sai ka ci amarcin ba, ni kuma bana so. Dan haka ai ban ci kazar taka ba ko?” Ta ƙare maganar tana kallon sa hawaye ya cika kurmin idonta. Sosai ta bashi dariya amma ya dake ya ce“To ai ko kin ci ko baki ci ba ni sai naci amarcin yarinya, Dan haka it’s better for you ki ci abincin ki.”
Shiru Nana ta yi tana kallon sa, nan da nan hawaye ya fara zubowa akan fuskarta. Abdusammad kuwa ɗauke kansa ya yi yana kai naman bakinsa ya fara taunawa a hankali, Yana jin yanda take shessheƙar kuka a hankali, Ya juyo yana kallonta sai kuma ya janye kanta ba tare da ya yi magana ba ya buɗe bakinta da hannunsa, A hankali kuma ya kai nasa bakin ya juye mata kaf naman dake bakinsa. Wani irin jan numfashi Nana ta yi, Ya saketa ya ɗauke kansa, Ta dinga kallon sa tana kuka kuma taƙi tauna naman, Kamar ba zai magana sai kuma ya ce
“Cinye nace”
Cikin kuka ta ce“wallahi ni ba zan ci ba. Ni bana so, Ni ka bar ni kawai!”
Ganin yanda duk ta daga hankalinta ya sanya shi yin murmushi kafin ya ce“Shikenan na fasa cinye abin ki.” Ya tura mata bowl ɗin gabanta, Kallon sa ta yi taga ya gyaɗa mata kai. Ta ɗauke idanunta hawaye na sake zubowa ta fara tauna naman, Tashi ya yi ya koma kan kujera ya zauna dan ya ƙoshi, ita kuwa gyara zamanta ta yi a ƙasan ta fara cin kazar tana lumshe ido, kasancewar naman kaza na daga cikin abin da take so. Sai da ta kusa cinyewa sannan ta fara gyatsa, Dan haka ta haƙura ba dan ta daina mata daɗi ba, Ta ɗauki ruwa ta sha sannan ta tashi ta koma kujerar daya zauna ta zauna ita ma, Kallon ta ya yi sai kuma ya dauke kansa ya mayar kan tv inda yake kallon aljazeera, Ta fara lumshe ido saboda ƙoshin da tayi ga kuma sanyin ac dake dukanta.
“Bacci zaki yi?”
Ta ji ya tambayeta, Gyaɗa masa kai ta yi ya ce“Zo ki kwanta” ya nuna mata cinyarsa, Kamar jira take ta matsa kusa da shi ta ɗora kanta akan cinyarsa ta sanya hannayenta duk biyun ta zagaye ƙugunsa. Ta rufe idanunta tana shirin baccin ta ji ya ce
“Ki yi baccin idan kin tashi sai ki je wajensu Amma, cause gobe zamu shige.”
Cikin magagin bacci ta ce“Uncle ka bar ni anan.”
Kallon ta ya yi sai kuma ya girgiza kansa ya ce
“Naƙi ɗin. Tare zamu tafi in sha Allah, Da a ce baki da visa ne shi ne zan bar ki amma tun da kina da tare zamu tafi.”
Tura baki ta yi tana ƙoƙarin rufe idanunta ta ce
“Ni ba ran bika ba.”
Murmushi kawai ya yi sai kuma ya ja dogon hancinta ya ce“To bari muga.” bata sake cewa komai ba ta fara baccinta, Shima ɗin bai sake mata magana saboda saukar numfashinta da ya fara ji.
****
Safwan na zaune gefen gadonsa, hannunsa rike da wata farar takarda yana dubawa, Can kuma ya linke takardar ya ja idanunsa ya lumshe, hawaye suka fara zirarowa ta gefen idanun sa. Yana nan zaune aka buɗe ƙofar dakin, bai daga kansa ba dan duk zatonsa Siyama ce, Haule ta ƙaraso ciki hannunta riƙe da ruwan gora ta tsaya gaban gadon tana kallon sa, Ta jima a tsaye ganin bai buɗe idanunsa ba ya sanya ta ce
“Hamma!”
Muryarta da yaji ya sanya shi buɗe idanun sa, Ya kalleta ba tare da ya ce komai ba. Haule ta sunkuyar da kanta ta ce“Ga ruwan in ji Anty Siyama.” Jinjina kansa ya yi sai kuma ya miƙa mata hannu, Ta miƙa masa ruwan ya karba sannan ya ce“Nagode!.” bata ce komai ba taja ta tsaya, Safwan ya buɗe ledar dake gabansa ya fara zaro drugs ɗin, ɗaya bayan ɗaya ya dinga ɓalla yana sha har ya kammala. Ita dai Haule sai kallon sa take cike da tausayi, Bayan ya kammala ya ajiye empty bottle ɗin akan drawer. Sai a sannan ta sauke ajiyar zuciya ta juya zata fita taji ya ce
“Haulat!”
Cak ta tsaya, kafin ta juyo tana kallonsa, Da hannu ya yi mata alama da ta zo. Ta dawo gefensa ta zauna ta sunkuyar da kanta. Safwan ya dinga kallon ta ba tare da ya ce komai ba, Ita ma ɗin bata yi yunkurin yin wata magana ba, Can dai ya numfasa ya ce
“Haule ina son ki yafe min kin ji, Ki yafe min abin da na yi miki da kuma wanda zan miki, Dan Allah kin ji…”
Ya yi shiru hawaye na biyo kuncinsa, Haule da hankalinta ya tashi ya girgiza kanta tana kuka ta ce
“Babu abin da ka yi min Hamma, idan ma kuma ka yi min to na yafe maka. Wallahi ban taɓa riƙe ka ba, Na yafe maka Hamma!.”
Cikin shassheƙar kuka ya ce“Kin yafe min Haule? Har zuciyarki kin yafe min?” gyaɗa kanta ta yi tana hawaye itama. Safwan ya ja numfashi ya sauke sannan ya janyo takardar dake gefensa ya miƙa mata, Sai da taji gabanta ya faɗi, Amma ta karba ba tare da ta ce komai ba. Safwan ya jingina da jikin gadon sannan ya ce
“Ki je ki kai wa Hajiya Babba, Ko kuma Yaya Abdusammad duk wanda ki ka samu kin ji.”
Gaba ɗaya sai taji jikinta ya yi sanyi, wani irin sanyi wanda bata san dalilinsa ba, Ta miƙe hannunta riƙe da takardar ta ce“To Hamma Safwan.” yanda ta fadi sunan nasa ya sanya shi rufe idanun sa, ƙirjinsa na tsananta bugu, Ta juya ta fice daga ɗakin ya bita da kallo lokaci ɗaya kuma ya fashe da wani irin kuka kamar ƙaramin yaro. Tana fita Siyama ta shigo ta tsaya gaban gadon tana kallon sa, Ta daɗe a tsayen har sai da taji ya fara daina kukan ya koma jan numfashi sannan ta ce
“Ka sake tan?”
Gyaɗa mata kai ya yi ba tare da ya buɗe idanunsa. Siyama ta yi murmushi sannan ta ce
“Better!”.
Shiru Safwan ya yi bai ce mata komai ba, Siyama ta sake cewa“Yanzu ka ga sai muyi zaman mu tare, babu wadda zata sake shigowa gidan nan da sunan mata. Ni kaɗai na isheka” Jinjina kai kawai ya yi kafin ya zame ya yi kwanciyarsa akan gadon, ta daɗe tsaye a wajen kafin daga bisani ta juya ta fice daga ɗakin. Haule na fita ta nufi apartment ɗin Hajiya Babba tana tafe tana tunani, Haka kawai taji zuciyarta bata yarda da takardar ba. Dan haka ta ja ta tsaya a wajen tana ƙoƙarin warwarewa, Abdusammad ta hango tsaye shi da Aliyu suna magana. Sai kawai ta fasa buɗewa ta nufi wajen da sauri, Kallon ta suka dinga yi har ta ƙaraso wajen ta gaishesu suka amsa sannan ta ce
“Arɗo daman Yaya Safwan ya ce na baka.”
Kallon takardar da take miƙo masa ya yi, Sai kuma ya kalli fuskarta. Can dai ya karɓi takardar ya warwareta.
_Ba sai na faɗi dalilina ba, amma ina son ku yafe min. Ni Safwan Muhammad Shuwa na saki Matata Haule saki ɗaya, saki biyu. Ina fatan zata yafe min abin da nayi mata, Safwan Mhd shuwa._
Da wani irin mamaki Abdusammad ya ɗago ya kalli Haule, ganin yanda tashin hankali ya bayyana ƙarara akan fuskarsa ya sanyata cewa
“Arɗo lafiya? Ko wani abun ya samu Hamma?”
Bai iya bata amsa ba, Aliyu ya karɓi takardar ya karanta, Ban da innalil lahi babu abin da yake ja. Ya kalli Abdusammad wanda ya yi shiru yana tunani ya ce
“Me yasa zai yi haka? Mene yake damun Safwan? Ni gaba ɗaya na kasa gane kansa.”
Bai bashi amsa ba, dan idan har ransa na ɓace baya iya magana. Dan haka Aliyu ya yi shiru yana kallon sa, Above 5mins kafin ya sauke wani zazzafan numfashi ya kalleshi ya ce“Kai ta apartment ɗin Abba. Ina zuwa” bai tsaya jiran amsar Aliyun ba ya yi gaba abin sa. Da idanu duk suka bi shi , Haule ta ce“Hamma me ya faru?” yanda ta yi maganar a sanyaye ya bawa Aliyu tausayi, Shikenan ya mayar da yarinya ƙaramar bazawara?. Ya sauke numfashi sai kuma ya ce“Ba komai muje.” Jiki a sanyaye tabi bayansa suka nufi apartment ɗin su Nanar.
****
Zahra ce tsaye gaban gadonta tana ƙoƙarin yafa mayafi akan atampar dake jikinta wayarta ta fara ƙara, Ɗauka ta yi ganin lambar Anty Khadijah ta ɗaga ta kai kunne kafin ta yi magana Anty Khadijah ta ce
“Zahra kin yi amfani da maganin kuwa?”
Dafe kai Zahra ta yi dan har ta manta ta ce“wayyo Anty wallahi har na manta. Bari na ɗauka na sha yanzu zan tawo gida ma”
Anty Khadijah ta ce“Okay ki yi maza ki sha sai ki tawo.” Ohk Zahra ta ce sannan ta kashe wayar, A jaka ta sakata sannan ta ɗauki maganin dake kan dresser ɗinta ta nufi parlour, Ruwan zafi ta ɗan zuba a cup sannan ta kwance maganin ta zuba, ta saka cokali ƙarami ta juya sannan ta kafa kai ra shanye tas. Bayan ta gama ta ɗauki ruwa ta sha sannan ta fita ta koma saman.
****
Nana na zaune kan cinyar Amma tana danna wayarta aka yi knocking ƙofar, Amma dake haɗa turaren wuta ta ce“Nana je ki ga wane” To kawai ta ce sannan ta sauka daga jikinta ta ɗauki hularta data faɗi ta saka sannan ta nufi ƙofar. Koda ta buɗe tsayawa ta yi tana kallon su, Aliyu ya ce“Nana zata zauna anan zuwa an jima.” Kallon Haule ta yi sai kuma ta ce“Tam Yaya.” Aliyu ya juya ya bar wajen, ta matsa daga jikin ƙofar sannan ta ce“Zo ki shige.” Babu musu Haule ta shigo parlourn a sanyaye. Amma ta dinga kallon ta kafin ta yi magana Nana ta ce “Yaya Aliyu ne ya ce ta zauna a nan zuwa dare.” Amma ta ce“Tom shigo ki zauna mana.”
“Ina yini?”
Haule ta yi maganar bayan ta durƙusa, Da murmushi Amma ta amsa sannan ta ce“Ya gidan?”
“Alhamdulillah.”
Cewar Haule, Amma ta ce ta zauna kan kujera sannan ta zauna ta sunkuyar da kanta. Itama Nana komawa ta yi ta zauna kusa da Amma ta ci gaba da game ɗin da take yi, Bayan Amma ta gama abin da take ta miƙe ta nufi kitchen. Ta dawo hannunta riƙe da plate mai ɗauke da drinks, table ta ja gaban Haule sannan ta ajiye mata ta ce
“Maza ki sha bari na kawo miki abinci.”
“Na gode Amma.”



