Chapter 36: Chapter 36
Ta ce a sanyaye. Murmushi kawai Amma ta yi sannan ta koma kitchen ɗin, Nana ta tashi tabi bayanta. Tsaye ta sameta tana ƙoƙarin zubawa Haule abinci, Ta jingina da jikin cabinet sannan ta ce
“Amma nima zan sake cin abincin.”
Yanda ta yi maganar a shagwaɓe ya sanya Amma ta kalleta, Ta haɗe rai ta ce“Wanda ki ka bar min fa? Ko ba cewa ki ka yi kin ƙoshi ba.?”
Tura baki Nana ta yi kafin ta ce“To ai yanzu ya sake bani sha’awa.”
“To ba zaki ci ba!”
Amma ta yi maganar tana harararta. Zumɓura baki ta yi ta ƙarasa wajen freezer ta buɗe ta ɗauki coke sannan ta fice daga kitchen ɗin, Amma ta bita da kallo sai kuma ta girgiza kanta tana tsaki.
****
Bayan sallar isha’i suna zaune a babban parlourn Hajiya Babba. Papa ya numfasa kafin ya ce“To mene dalilin daya sanya ya yi haka? Akan me zai saketa? Me ta yi masa.?” Shiru parlourn ya ɗauka, Can dai Sultan ya ce“Nifa daman Papa ba tun yau ba na fuskanci sauyi daga gare shi. Safwan ya sauya kamar bashi ba, rabon da na gan shi har na manta.”
“Sauyi? Wane sauyi ne da har zai iya sakin yarinya ba tare da ta masa wani laifi ba? Kuma saki mafi wulaƙanci har saki uku. Wannan shi ne sauyin?”
Abba ne ya yi maganar a zafafe. Papa ya ce“Ya isa haka Ahmad, dole a bi komai a sannu. Yanzu dai idan ya dawo daga asibitin sai aji dalilinsa na yin haka.”
“Babu buƙatar jin dalilinsa, Tun da har ya riga da ya yanke hukunci to magana dashi bata da amfani. Ku bar shi, ku manta dashi kawai dan Allah…”
Hajiya Babba ta yi maganar cikin wata irin murya mai nuna asalin damuwar da take ciki. Abdusammad ya girgiza kansa zai yi magana ta ɗaga masa hannu. Miƙewa tsaye ta yi tana kallon sa ta ce
“Kar ka damu ƙaddarata ce a haka. Mahaifin ku ya tafi ya bar ni daku, Ya huta bai san abin da ke faruwa ba. Duk abin da Safwan ya yi kai ne ka bashi dama, A matsayinka na babba ka iya watsa mana ƙasa a ido, Ka auri wadda ka san ba yar danginka bace. Baka damu da wane hali zan shiga ba, Baka damu da kallon da za’a dinga yi min ba, Sannan kuma ka koyawa ƙaninka rashin yin biyayya a gare mu”
Dakatawa ta yi saboda hawayen dake zubowa daga cikin idanunta, Ta sanya hannunta ta goge kafin ta ci gaba da faɗin
“Ba komai. Na haƙura, kuma mun haƙura gaba ɗaya, daman duk abin da muke yi, muna yi ne saboda ku, saboda gobenku data ƴaƴa yanku, Amma tun da hakan bai zama abin da zai saka ku ga ƙimar mu ba. Babu komai, A yi lafiya!.”
Hajiya Babba na gama faɗin hakan ta nufi sama da sauri. Shiru parlourn ya ɗauka, kowa da abin da yake tunani. Abba ya kalli Abdusammad wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa ba tare da ya ce komai ba, Dafashi Abba ya yi, ya ɗago runannun idanunsa ya kalli Abba. Girgiza masa kai Abba ya yi dan haka ya mai da kansa ƙasa, Allah ne kaɗai yasan yanayin da yake ciki a sannan. Shi kaɗai ya san abin da yake ji a cikin zuciyarsa, Bai taɓa tunanin Hajiya Babba zata zubar da hawaye akan su ba, Sai gashi duk haƙuri irin nata ta buɗi baki ta faɗi irin wannan maganganun.
Atta ce ta miƙe tsaye tana kallon su duka ta ce“Ai shikenan, Gobe idan Allah ya kai mu zamu koma gida nida ita.”
“Amma Atta da kin bar ta anan, Ai kin ga…”
Daga masa hannu ta yi, Fuskarta babu walwala ta ce“kada ka ƙarasa Ahmadi, Gobe da Haule zan tafi naje na bawa iyayenta haƙuri.”
Shiru ya yi bai sake cewa komai ba, Ta bar parlourn itama. Tashi ya yi ya ƙarasa inda Abdusammad yake tsaye ya ce“taso muje.”
Miƙewa ya yi suka bar parlour. Suna zuwa compound ɗin gidan Abba ya saki hannunsa sannan ya ce“Na san zaka ji babu daɗi. Kamar yanda mu ma muka ji babu daɗi, amma ka sani abin da ta faɗa gaskiya Abdusammad. Da baka auro wata ba Safwan ba zai taɓa wannan tunanin ba, A rayuwa shi Babba har kullum madubi ne, kuma abin koyon na ƙasa dashi. Kai ne babba kuma kai ka fara fito da wannan abun. Yanzu ka ga irin matsalar da muke gudu ko?”
Girgiza kansa ya yi hawaye na biyo kan fuskarsa ya ce“Na gani Abba. Yanzu ya zan yi? Hankalina a tashe yake, Ya za’a yi a ce Hajiya na zubar min da hawaye, ban san hakan me yake nufi ba. Abba idan har bata so wallahi zan iya rabuwa da Zahra, Domin samun farin cikinta.”
Wani murmushi irin na manya Abba ya yi, Ya dafashi sannan ya ce“Akan me zaka saketa? Kana ganin sakinta zai zama abin da zai sauƙaka wannan matsalar? Idan ka saketa ita laifin me ta yi maka? Kana ganin baka cuceta ba?.”
Shiru Abdusammad ya yi, Abba ya ce“Kawai ka ci gaba da addu’a kana neman yafiyar ubangiji, Amma maganar saki sam bata taso ba, kuma ba zan taɓa bari ka yi hakan ba.”
Ƙarasowar Papa ya dakatar da maganar tasu, Ya tsaya yana kallon Abba ya ce“Ahmad yarinyar nan ta zauna a wajenka, Saboda ba zai taɓa yiwuwa Atta ta tafi da ita ba. Gara ta zauna a nan muga abin da hali zai yi.”
Jinjina kai Abba ya yi kafin ya ce“Nima abin da nayi tunani kenan. Idan Allah ya kaimu gobe zan yi magana da Safwan”
“Ku bari zan masa magana yanzu.”
Abdusammad ya yi maganar jiki a sanyaye. Girgiza kai Papa ya yi ya ce“a’a wani ɓacin ran zaka janyo, ka je gida kawai.” Dan murmushin ƙarfin hali ya yi ya ce“Babu abin da zai faru Papa, idan Allah ya kai mu gobe ma zan bar ƙasar.”
“Da wuri haka?”
Papa ya yi maganar da mamaki dan bai san da batun tafiyar ba, Gyaɗa masa kai Abdusammad ya yi sannan ya ce“Eh. Abubuwane suka fara yin yawa acan ɗin, so i have to go.”
Jinjina kai Papa ya yi kafin ya ce“Haka ne. To Allah ya yi jagora, amma bada sassafe ba dai?”
“Da wuri maybe ma around 7:00am mun tafi.”
Papa ya ɗan yi shiru can kuma ya ce“To Allah ya kaimu goben da lafiya.” da Amin ya amsa sannan ya juya zai bar wajen, kamar kuma wanda ya tuna wani abu sai ya dawo, Abba ya ce“lafiya dai?”
“Nana bata koma gida bane, naga kuma dare ya fara yi bari sai na bika mu tawo tare.”
Jinjina kai Abba ya yi kafin ya ce“Eh dan kusan ka san halinta yanzu sai ta ce tsoro take ji.”
Koda suka je a ƙofar apartment ɗin ya tsaya, Abba da ya shiga ya kira masa ita. Yana tsaye a ƙasan balcony ta fito hannunta riƙe da mayafinta tana ƙoƙarin yafawa akan doguwar rigar jikinta. Bayan ta ƙaraso waje ta kalleshi ta ce“uncle ni sai an jima zan dawo fa.” bai ce komai ba ya ja hannunta suka fara tafiya, Ko nisa basu yi ba ta tirje a wajen ya juyo yana kallonta da shanyayyun idanunsa. Ganin yanda take yarfe hannu yasa ya ce
“What?”
“ƙafan uncle, zafi take min. Wallahi ba zan iya tafiyar ba”
Da buɗe idanunsa ya yi kamar ba zai magana sai kuma ya ce“To sai ki yi ya ya?”
“Ka goyani.”
Ta ce a shagwaɓe. Harararta ya yi ya ce“Abokin wasanki ne ni?. C’mon my friend!”
Madadin ta tawo sai kawai ya ga ta nemi waje ta zauna, ta harɗe ƙafafunta ta fara kuka a ƙarfi. Baki buɗe yake kallonta, ganin tana son tara masa jama’a ya sanya ya ɗan durƙusa dai dai tsayinta ya ce“Tashi muje mana, zan siya miki abin daɗi.”
Maƙale kafaɗa ta yi kafin ta ce“a’a ni sai ka goyani…” Ya jima yana kallonta ganin yanda ta yi da fuska kamar jaririya, agogon hannunsa ya kalla ganin dare ya fara yi ya sanya ya ɗan yi tsaki. Sannan ya juya mata baya ba tare da ya ce komai ba, Jin ta yi shiru ya sanya ya ce
“Kin hau ko sai nayi tafiyata?.”
Da sauri ta mike ta tattare rigarta ta hau bayan nasa, Ya mike tsaye yana rike da ita. Hannayenta ta sanya ta zagaye wuyansa, Ta ɗora kanta akan faffaɗan bayansa tana dariya. Yana jin ta amma bai ce mata komai ba, Sun yi nisa sosai ta ɗan leƙo fuskarsa ta ce
“Uncle.”
“Uhm” ya ce yana ci gaba da tafiyarsa.
“To da kana goya Anty Zahra?”
Shiru ya yi yana tunanin dalilin tambayar, Can kuma ya girgiza kansa ya ce“A’a.” dariya ta sake yi ta koma ta yi lamo a bayansa sannan ta ce“yauwa Uncle ɗina, ai ni kaɗai ka ke so ko?” shiru ya yi mata gudun ya bata amsa ya zama fitina. Bata damu da rashin amsawar da ya yi ba ta ce
“Ita kuwa Maimoon Yaya Aliyu baya goyata. Kuma ma ita cikine da ita” ta ƙare maganar tana tuntsirewa da dariya, Duk yanda yake jin ransa a dagule bai san sanda ya yi murmushi ba. Ya girgiza kansa bai ce komai ba. Suna zuwa bakin ƙofar ya ce“sauka!” ta sake ƙanƙameshi a shagwaɓe ta ce“ni sai ka kai ni sama.” girgiza kansa ya yi ya ce“sauka na ce!” Ta sake maƙale kafaɗa tana kwanciya a bayansa. Wata azabbabiyar tsawar daya daka mata ce ta sanya ta sauka daga bayan ba shiri. Ta nufi cikin gidan da gudu tana kuka, Tsaki ya yi sannan ya shiga parlon. Zahra na zaune akan sofa ita da Noor, Ta yi masa sannu da zuwa ya amsa sannan ya ƙarasa ya ɗauki Noor ya ɗorata a cinya, Kama gemunsa ta yi wanda ya zame mata dabi’a ta ce
“Abbie gobe zamu tafi?”
Jan kumatunta ya yi ya ce“Yeh!”
Ta yi dariya har sai beauty point ɗinta suka loma sannan ta ce“yauwa Abbiena ɗan albarka. Daman ina son naje naga su Abeeha” Murmushi shima ya yi ya ce“tom zaki gansu nan kusa. Muje ki kwanta kin ga da wuri zamu tafi ko?” gyaɗa masa kai ta yi ya miƙe da ita a hannunsa suka nufi sama, Zahra ta bi su da kallo.
Nana na shiga daƙinta ta faɗa kan gado ta fashe da kuka har sannan jikinta bai daina rawa ba, Ba’a taɓa yi mata tsawar data gigitata irin wannan ba. Ta dunƙule waje ɗaya tana ci gaba da kukanta a haka har bacci ya ɗauketa.
Around 10:20 na dare aka fara knocking ƙofar, Da mamaki ya dinga kallon ƙofar sai kuma ya janye laptop ɗin dake gabansa ya miƙe ya nufi ƙofar ya buɗe. Tsaye ya gan shi a wajen, Bai ce komai ba ya matsa daga wajen ƙofar. Safwan ya sauke numfashi sannan ya shigo ciki, komawa Abdusammad ya yi ya zauna kan kujera yana jiran ya ji abin da zai ce. Jiki a sanyaye Safwan ya zauna kujerar dake kusa da ta sa, Ya sunkuyar da kansa. Sun ɗauki mintuna a haka kafin Abdusammad ya ce
“Idan baka da abin faɗa zan tashi.”
Sauke numfashi Safwan ya yi kafin ya ce
“Na san na aikata ba dai-dai ba Yaya. Amma ina da hujjata ta yin haka, kuma Hujjar ta kai na aikata haka. Domin abin da nayi shi ne dai-dai, Na san babu wanda zai fahimceni a cikin su, amma ina da tabbacin kai zaka fahimta shiyasa na zo wajenka Yaya.”
Safwan ya yi shiru yana kallon Abdusammad, Da ɗan mamaki Abdusammad ya ce
“Hujja! Safwan mene hujjarka? Akan me zaka sake ta? Me ta yi maka? Ka san halin daka saka mutanen gida?. Ka san me Hajiya ta ce akan haka? Akan me zaka yi abu babu neman shawara?”
Tuni hawaye suka fara wanke masa fuska, Ya tashi ya dawo kujerar da Abdusammad yake ya tsuguna a wajen, ya ɗora hannayensa akan cinyarsa cikin kuka ya ce
“Yaya bani da wata mafitar ne. Ba zai yiwu na ci gaba da zama da Haule ba, Yaya ina da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV! Ta ya zan iya zama da ita a haka?”
Abdusammad bai san sanda ya ture shi daga jikinsa ya miƙe tsaye ba. Fuskarsa ɗauke da mabayyanin tashin hankali ya ce
“What! Me ka ce Safwan? Hiv kamar ya ya? Yaushe kuma a ina ka samu cutar!?.”
Abdusammad ya jera masa tambayoyin yana tsare shi da idanu. Jan numfashi Safwan ya yi kafin ya ce
“A sanda na auri Siyama. Ita ce wadda take ɗauke da cutar ta shafa min ba tare da ita ma ta san tana da ita ba. Ita kuma Haule bata da ita, saboda na kira likita ya gwada ya tabbatar min da bata da cutar, shiyasa na saketa saboda kada na cuceta!”
Ya ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka. Durƙusawa Abdusammad ya yi ya ɗago shi yana kallon sa ya ce“Ita Siyaman take da Hiv? How? A ina ta samu?”
Girgiza kai Safwan ya yi kafin ya ce
“Nima bana ce ba Yaya. Amma kawai abin da na sani ban samu Siyama a matsayin budurwa ba, Wannan ke nuni da cewa a wani wajen ta shafa itama. Saboda haka idan har ina son na zauna lafiya dole na rabu da Haule, bana son na cutar da ita, bana son na shafa mata. Wallahi shiyasa na saketa ba dan wani abu ba Yaya!”
Girgiza kai Abdusammad ya yi cike da mamaki da kuma tashin hankali ya ce“to ta ya ita Haule bata shafi cutar ba? Ko kana son ka ce bata da iddarka?” Girgiza kai Safwan ya yi still crying ya ce
“A’a tana da ita. Saboda Haule ce ta fara tarewa kafin Siyama, Bayan Siyama ta zo sai naji bana son mu’amala da Haule, bana son ta zo inda nake. Wannan dalilin ya sanya na ƙaurace mata, Sai daga baya kuma na gano ina da wannan cutar shi ne ya sake sakawa na bar ta din. Na san zaka fahimceni Yaya, wallahi tallahi bani da niyyar cutar da rayuwar Haule, kuma bani da niyyar bijirewa gidanmu, na ɗauki wannan ɗin a matsayin Ƙaddara! Wadda ba zan iya guje mata ba.”
Rungumeshi Abdusammad ya yi yana shafa kansa, Safwan ya sake fashewa da wani matsananci kuka. Shi kansa Abdusammad ɗin kukan yake, saboda Safwan na ɗaya daga cikin abin da yafi soyuwa a gare shi. Yana son sa tun yana ƙarami, ƙaunar da yake masa ya sanya ya mayar dashi ɗan ɗakinsa, musamman daya kasance suna kama da juna. Koda wasa bai son yaji an ce wani abun ya sameshi yanzu zaka ga hankalinsa ya tashi, A yanzu kuwa sai yaji kamar shi ne ƙaddarar ta faɗawa. Sun daɗe a haka kafin daga bisani Abdusammad ya ɗago shi ya shiga goge masa hawayen fuskarsa ya ce
“Shikenan na gane, kuma na fahimceka Safwan. Kada ka damu komai zai zo da sauki, zan saka a ɗoraka akan magani sai ka dinga zuwa US check up. Saboda haka ka kwantar da hankalinka, and zan faɗa musu yanda zasu fahimta. Duk da gobe da wuri zan tafi, bayan sallahr asubah zamu yi magana dasu, Kada ka damu kaji. Abin da ka yi shi ne dai-dai, Allah ya baka da lafiya”
Sake rungume shi Safwan ya yi kafin ya ce“Amin Yaya. Nagode sosai, dan Allah ka ce duk su yafe min, ji nake kamar mutuwa zan yi Yaya”
Girgiza kai Abdusammad ya yi yana shafa bayansa ya ce“In ji wane? Ka taɓa jin cuta ta kashe mutum? Sai dai kwanansa ya ƙare. Saboda haka bana son na sake jin makamanciyar wannan maganar a bakin ka kaji!”
Gyaɗa masa kai ya yi, Ya yi shiru suna sauke numfashi.
Daren ranar kasa baccin kirki Abdusammad ya yi, gaba ɗaya ji ya yi duniyar tayi masa babu daɗi. Dan haka ya dauro alwala ya fara sallar nafila har aka fara kiran sallar asuba. Bayan sun fito daga masallaci ya sanya suka tsaya, Ya kuma yi musu bayani yanda zasu fahimta. Sosai jikin su ya yi sanyi Abba ya ce
“Abin da ya yi shi ne dai-dai. Allah ya gajarta walaha, In sha Allah zamu yi magana da Hajiya Babba gobe.” Jinjina kai Abdusammad ya yi sai kuma ya ce“Yauwa Abba, ni ka ga da wuri zan tafi. Amma in sha Allah nan bada jimawa ba zan zo” A haka suka rabu kowa ya yi hanyar gidansa jiki a sanyaye. Yana komawa ya nufi ɗakin Nana, Koda ya shiga zaune ya hangeta jikin gado sanye da hijabi. Ya ƙarasa ciki ya zauna gefen gadon yana kallon ta, Bayan ta abin da take ta tashi ta naɗe laddumar sannan ta nufi can ƙarshen gadon ta zauna jiki a sanyaye ta ce
“Ina kwana?.”
Shiru ya yi bai amsa ba, Ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers ɗinta. Ya dade yana kallonta kafin ya ce“zo nan.”
Komawa kusa da shi ta yi ta zauna kanta a ƙasa. Ya ɗan yi murmushi ganin yanda ta nutsu kamar ba ita ya ce
“mene ne? Haushina ki ke ji?”
Girgiza masa kai ta yi, Ya jawota jikinsa ya ce
“Shikenan ba zan ƙara ba. Kin ji Nanata”
Kamar jira take ta ɓare masa baki ta fara kukan data saba. Ya yi shiru yana saurarenta, Can kuma ya ce“To ya isa haka ki tashi ki shirya” banza ta yi masa ta ci gaba da kukanta. Ya ɗago fuskarta ya riƙe cikin tafin hannunsa ya ce“Idan baki min shiru ba zan saka ki mai dalili.” Tura baki ta yi ta janye fuskarta, Ya tashi tsaye yana riƙe da cazbaha a hannunsa ya ce“Ki shirya kin ji. Ina zuwa”
A sanyaye ta ce to sannan ya juya ya bar ɗakin.
****
Misalin ƙarfe 6:30 ne na safe, gaba ɗaya jama’ar estate ɗin suka taru a compound ɗin gidan. Kamar yanda ranar da ya zo suka taru haka ma yau ɗin suka sake taruwa, Sai da ya yi Sallama da kowa sannan ya nufi wajen Hajiya Babba, Jiki a sanyaye ya yi mata sallama, Ta amsa babu yabo babu fallasa. Noor dake hannunsa ya ɗaga mata hannu, Murmushi Hajiya Babba ta yi ita ma ta daga mata hannun. Jiki a sanyaye ya bar wajen, A bayan mota ya sakata sannan ya sake ma su Abba sallama. Nana kuwa dakyar ta bar jikin Amma tana kuka, ko ranar da aka tafi da ita gidan bata yi kuka kamar yau ba, Dakyar Amma ta rarrasheta ta shiga motar. Tsayawa ya yi yana karewa estate ɗin da kallo, kamar yau ya zo gashi har zai koma. Ya sauke numfashi sannan ya nufi cikin motar bayan an bude masa, Shiga ya yi yana sake daga musu hannu. Atta kuwa komawa gefe ta yi ta zauna ta dinga rusa kuka, a haka har motocin suka fara fita daga gidan ɗaya bayan ɗaya kamarkamar yau ya zo gashi har zai koma. Ya sauke numfashi sannan ya nufi cikin motar bayan an bude masa, Shiga ya yi yana sake daga musu hannu. Atta kuwa komawa gefe ta yi ta zauna ta dinga rusa kuka, a haka har motocin suka fara fita daga gidan ɗaya bayan ɗaya kamar dai yanda suka shigo, Ajiyar zuciya suka sauke sannan kowa ya nufi hanyar gidansa.
Around 4:00am jirgin nasu ya sauka a JFK airport na New York. Bayan sun fito daga ciki suka tarar da jerin motocin dake jiransu wanda aƙalla sun kai guda 10. Ita dai Nana sai sake jan mayafinta take saboda ɗan yayyafin da ake, Abdusammad ya shiga cikin wata Bentley black colour, Nana tabi bayansa itama. Ganin haka ya sanya Zahra yin gaba, ta buɗe wata motar ta shiga hannunta riƙe da Noor wadda ta yi bacci, Nan da nan kuma motocin suka bar wajeni.
Park avenue road,
Upper East side,
New York.
A dai-dai bakin wani madaidaicin gate motocin suka ɗan tsaya, kafin daga bisani gate ɗin ya fara zugewa da kansa, Wani irin ƙaton gida ne iya ganinka, wanda ta wajen ba lallai ka yi tunanin ya kai girman haka ba. A tsakiyar compound ɗin gidan na biyu motocin suka yi parking dan iya nan ne mota ke tsayawa, Sai a sannan Abdusammad ya sauke numfashi sannan ya zare seat belt ya buɗe motar ya fito. Jiki a sanyaye ita ma Nana ta fito tana ƙarewa compound ɗin kallo, Gurin an ƙawatashi da furanni masu kyau da ƙamshi irin su white rose da lavender. Ta ja lumsassun Idanunta ta rufe tana shaƙar iskar wajen mai daɗi, Duk yanda take jin babu daɗi data bar gida sai da ta manta. Ta gyara tsaiwarta ganin Zahra ta fito har sannan tana rike da Noor, Gaba ya yi suka fara bin sa a baya, Duk inda ya shige sai ma’aikatan wajen sun gaishesa a haka har ya shiga third gate ɗin wanda yake da launin golden, Wani irin haɗaɗɗen compound ne mai kyau da tsari. Ya lumshe idanunsa sakamakon iskar data doke shi mai ɗauke da ƙamshin mint da fresh flowers. A hankali yake taka pathway ɗin wanda ya ɗan lanƙwashe har zuwa ga kofar entrance ɗin gidan, Nana kuwa tun da ta shigo idanunta ke kan fountain ɗin dake ɓangaren damanta, Sai zubar da ruwa yake duk da yayyafin da ake, ga wasu leds masu kyau da haske dake ƙawatashi. A gefensa kuma flowers ɗin orchids da ross sun ƙara taimakawa wajen ƙawata wajen ɗin, Ta janye idanunta tana kallon ɗaya side ɗin, ƙananun bishiyun marble da cherry blossom ne, daga gefensu suka wasu red leds ne waɗanda ke kawowa suna ɗaukewa. Ɗaga kanta ta yi ta hangi dogon ginin gidan, lokaci ɗaya kuma ta sauke kan nata ta ci gaba da tafiya. Sai da ya saka password a jikin ƙofar entrance ɗin wadda ta kasance ta glass sannan ta zuge a hankali, Ya tura kansa ciki bakinsa ɗauke da sallama da ba lallai sun ji ba.
Ɗaya bayan ɗaya suka shiga, Nana ta tsaya tana ƙarewa ƙaton parlourn kallo, Wasu Italian sofas ne a ciki yayinda marble tiles ya yi kamar carpet a wajen, A tsakiyar parlon kuma crystal chandelier ce mai bada launin golden. Daga can left side kuma pione ground ne, wanda aka ƙawata shi da kayan sauti masu tsada. Nana ta juya ta kalli gefenta da dama daga jikin bango, fireplace ne wanda ke ci a hankali, kuma shi ne ya taimaka wajen raguwar sanyi a parlon.
Ɗaga kanta ta yi tana kallon staircase ɗin da suke can nesa da ita, Bene huɗu ne a wajen, Biyu a haɗe, biyu kuma a rarrabe. Ya jima tsaye a wajen kamar ba zai magana ba sai kuma ya juyo yana kallon su duka
“Nana here it’s ur apartment. Ki je ki huta”
Ya ƙare maganar yana nuna mata benan dake right hand side ɗin biyun, Zahra kuwa gaba ta yi abin ta dan already ta san nata ɓangaren. Shima bai tsaya jiran amsar Nanar ba ya nufi nasa ɓangaren da sauri dan a mugun gajiye yake, Tamkar gunki haka Nana ta tsaya a wajen. Can kuma ta tura baki ta nufi hanyar benan daya nuna mata tana tafe kamar wadda kwai ya fashewa a jiki.
A hankali ta dinga taka fluffy rug ɗin dake cikin ƙaton parlourn, komai na ciki coffee and white ne, kaya masu kyau da kuma tsada, Tun daga kan kujeru har zuwa kayan wutar dake ciki, gaba ɗaya sai taga ashe parlourn ƙasa ba ma kyau ne dashi ba. Ta ja dogon numfashi ta sauke hannayenta riƙe da ƙugunta, daman tuni veil ɗin abayar ya zame ya dawo kafaɗarta sai hula ce kawai akan. Ta ja jikinta a sanyaye ta nufi ƙofar data gani wadda take da tabbacin nan ne bedroom ɗin.



