⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 37: Chapter 37

Kamar yanda ta yi tunani haka ce ta faru, haɗaɗɗen bedroom ɗin mai ɗauke da furnitures kalan na parlourn, a shimfida farin bedsheet akan gadon yayinda aka ɗora duvet coffee colour. Ta jima tana ƙarewa ɗakin kallo kafin ta ajiye wayarta gefen gadon ta nufi banɗaki, Shima sai da ta tsaya ta gama dube-dubenta, ta karance duk shower set ɗin da aka ajiye sannan ta ɗauki wanda take ganin zai fi mata ta fara wankan dashi, tana gamawa ta ɗauro alwala sannan ta fito ɗaure da towel. Ta ƙarasa gaban dogon press ɗin da tagani ta buɗa. Yawancin kayan ciki English wears ne, sai dogayen riguna tsirari, ta ɗan tura baki sannan ta janyo wata riga doguwa wadda bata shige gwuiwarta ba ta zura sannan ta naɗe gashin kanta ta ɗaure da riboom. Rasa hijabin sallah ta yi, dan haka ta sake buɗe press ɗin ta ɗauko abaya da veil ɗinta ta saka sannan ta gabatar da sallolin da ake binta… Bayan ta idar ta zare doguwar rigar ta faɗa kan gadon, Taja duvet ɗin ta rufe har kanta tana jin wata nutsuwa na saukar mata, kasancewar ta gaji sosai ya sanya nan da nan bacci ya ɗauketa.

****
A hankali ta fara buɗe idanunta tana ƙarewa saman ɗakin kallo, leds ɗin a kunne suke har sannan duk da hasken daya gaureye ɗakin. Ta tashi zaune tana murza idanunta, Ba wai baccin ne ya isheta ba kawai tashin taji ta yi. Kallon gefenta ta yi inda Hasken ke shigowa da glass window ɗin dake wajen, Ta ɗauke kanta tana tura baki kafin daga bisani ta yaye bargon dake jikinta ta sauka daga kan gadon, kai tsaye kuma banɗaki ta nufa. Wanke fuskarta ta yi a jikin sink kafin ta ɗago kanta tana kallon madubi, Fuskarta ta ɗan kumbura dalilin baccin da tayi, ta kai hannu ta rufe bakinta saboda hammar data tawo mata. Sabbin brushes ɗin data gani ta ɓare ta ɗauki ɗaya sannan a ɗauka toothpaste ta zuba ta hau wanke bakinta. Bayan ta gama ta ɗauki mouth listener ta fesa sannan ta zare rigar jikinta ta fara wanka, Tana gamawa ta fito ɗaure da towel. Ta karasa jikin madubi ta fara dube-duben mayukan da suke wajen, can dai ta ɗauki wani olive lotion ta shafe jikinta dashi. Babu abin da ta saka bayan man ta buɗe press ɗinta, wata riga ta zaro a jakarta ta ɓare ta warwareta tana kalla. Doguwar riga ce mai manyan flowers a jiki, saman rigar an saka roba mai talewa, Ta daɗe tana juya rigar kafin ta sanyata a jikinta. Ba ƙaramin kyau rigar ta yi mata ba, Ganin babu dankwali a ciki ya sanya ta sauke gashin kanta ya sakko kafaɗarta. Sai ta yi kamar wata baturiya, Ta rufe press ɗin sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin. A balcony ɗin saman ta tsaya, ganin hanyoyin sun rabu. Kamar ta je ta duba sai kuma ta nufi ƙasa kai tsaye, Parlourn net kamar jiya sai tashin ƙamshi yake, Ta kalli hanyar benan Zahra ta taɓe baki lokaci ɗaya kuma ta nufi benan da taga Abdusammad ɗin ya hau jiya. Ba karamar benansu bane wanda ana hawa za’a tarar da parlour, wannan wata ƙofa ce ta glass gefenta da wasu maddane na sirri. Ta daɗe tsaye a wajen kafin ta ƙarasa ta fara knocking bell ɗin jikin ƙofar, Ganin ba’a zo an buɗe ba ya sanya ta koma knocking ɗin da hannu. After 5mins taji an fara buɗe ƙofar, Ta tura baki tana ɗauke hannunta daidai nan ƙofar ta buɗe. Fuskarsa ya zuro yana kallonta, Ta kalle shi ganin bai ce komai ba, daga gani ka san bacci yake dan idanun sa sun ɗan janye, kuma babu riga a jikinsa sai faffaɗan ƙirjinsa dake bayyane.

“mene?”

Ya tambaya a shaƙe. Kallon sa ta sake yi sai kuma ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers ɗinta, Ya yi shiru kamar mai tunani sai kuma ya matsa daga jikin ƙofar still looking at her ya ce“shige.” kamar jira take ta shige cikin, Ya Girgiza kansa sannan ya mayar da ƙofar ya rufe. Wata irin ajiyar zuciya Nana ta dinga saukewa a jere a jere, Idan kana neman inda aka kashe masa kuɗi to parlourn ɗakin ya kai. Ko makaho ya shafa ya san an ɓarnatar da dukiya a wajen, Wasu set ɗin kujeru ne white colour masu taushi ko a ido, Bango ɗakin mai zane-zanen abstract art na Paris,Ta sake lumshe idanunta saboda ƙamshin cherry blossom air freshener ɗin dake dukanta. Bai ce mata komai ba taga ya zo ya nufi bedroom ɗin, itama ta bishi da sauri. Colours ɗin da aka yi amfani dasu a parlourn sune a cikin ɗakin, Komai fari ne, rabin bangon ɗakin an yi zane irin na manyan artist, ga wasu manya manyan frames ɗinsa dake maƙale a kowace kusurwa ta ɗakin, Hotunan tamkar sa yi magana saboda girmansu. Gaban gadon ya ƙarasa ya zauna yana kallon ta, Ganin hankalinta baya wajen yasa ya ce

“Ke zo nan.”

Ƙarasawa gabansa ta yi da sauri ta zauna a gefen ta sunkuyar da kanta. Shiru ya yi kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce“mene ne?”

Girgiza kanta ta yi a hankali, Ya sake cewa“saboda ki takurani ki ka zo kina min knocking da safiyar nan?” ɗago kanta ta yi ta kalleshi sai kuma ta sake sunkuyar da kan nata kafin ta ce“uncle ai rana ya yi fa.”

“Karfe nawa?”

Ya tambaya yana ƙoƙarin kwanciya, Kallon agogon bango dake maƙale a sama ta yi ta ce“ƙarfe 11:20 na safe.” Hannunta ta ji ya jawo ya kwantar da ita gefensa sannan ya ce“Oyah ki koma bacci sai an jima zan tashi.” kwaɓe fuska ta yi dan ita har ga Allah bata ji zata yi wani bacci ba, Ganin ta juya tana kalle-kalle ya sanya ya jawota jikinsa ya ɗora kansa akan fuskarta yana jin yanda take sauke numfashi ya ce“cewa nayi ki yi bacci.”

“Unclee!.”

Ta kira sunansa a shagwaɓe, Ɗaga mata gira ya yi alamar mene ne?. Ta tura baki ta ce“to ai bana jin bacci”

“Yanzu zan saka ki ji shi to.”

Girgiza kanta ta yi da sauri, Taja duvet ɗin ta rufe har fuskarta tana sauke numfashi, Ya yi murmushi sannan ya kashe hasken ɗakin nan take ya koma kamar ba rana ba, Jan duvet ɗin ya yi ya rufe jikinsa, Ya dinga kallonta ganin yanda take ta raba idanu..

“Ba zaki yi baccin bane?”

“Zan yi.”

Ta ce kamar zata yi kuka, Ji ta yi ya jawota jikinsa sosai ya ɗora hannunsa a bayanta wajen kanta ya fara shafawa a hankali kafin ya ce

“Sleep.”

Gyaɗa masa kai kawai ta yi, ya ci gaba da shafa kan nata ba tare da ya ce komai ba. Kasancewar daman baccin ba isarta ya yi ba, Ta fara lumshe ido, yana kallonta duk abin da take a haka har baccin ya yi awon gaba da ita. Sai a sannan ya zare hannunsa, Ya gyara mata kwanciyar sannan shima ya rufe idanun sa ya koma baccin.

****
Nigeria.
Atta ce tsaye a compound ɗin gidan tana gyara mayafin rigar jikinta, Abba ya yi shiru yana jin abin da take cewa. Papa ne ya ce“Atta ai gara ta zauna anan ta yi idda, kin ga idan Allah ya yi ma sai ta samu wani mijin ta yi aurenta.” wata uwar harara ta maka masa kafin ta ce“To bama so, iyayenta zan maidawa ƴarsu. Bayan yaro ya riga da ya saketa? To zaman me zata yi muku kuma ban da son zuciya.” Shiru Papa ya yi dan ya fuskanci ba fahimtarsa zata yi ba. Abba ya taka har gabanta sannan ya ce

“Atta dan girman Allah ki je kawai zan kawo yarinyar nan da kaina daga baya.”

Shiru ta yi tana kallon sa, can kuma ta tsuke baki ta ce“Ai gara na tafi da ita Ahmadi, kawai ka bari na tafi da ita.” Girgiza kai Abba ya yi yana kallon Haule dake tsaye ta sunkuyar da kanta ya ce“Ki barta anan ɗin, zan kawota da kaina daga baya.” Taɓe baki ta yi ba dan ranta ya so ba ta ce“Ai shikenan tun da kafi ƙarfina. A faɗawa Khadijah na tafi”

Murmushi Abba ya yi ya ce“Tom in sha Allah, Allah ya tsare hanya ya kai ki lafiya.” Da amin ta amsa sannan ta ƙarasa gaban Haule ta dafata ta ce“Kar ki damu kin ji. Zan aura miki wani wanda ya fi shi kin ji” Haule bata san sanda ta fashe da kuka ba, Ta rungumeta Atta tana kuka kamar ranta zai fita. Allah ya sani tana son Safwan, a ɗan zaman da suka yi tare ta koyi ƙaunarsa. Burinta kullum ta gan shi, koda ba zai kulata ba, ashe zaman nasu ba zai yi tsayi ba. Itama Attan kukan take, Da kyar Abba ya rarrashesu ta bar jikinta, ta shige mota bayan an saka mata kayanta. Drivern yaja motar suka bar compound ɗin, Ban da kuka babu abin da Haule ke yi, Abba ya kalleta cike da tausayinta ya ce

“Ya isa haka, Je ki ciki.”

Bata ce komai ba ta nufi apartment ɗinsa, dan daman tun shekaranjiyan anan take.. Sai da ta tafi sannan Abba ya kalli Papa wanda ya yi shiru tun ɗazu. Papa ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce“Allah ya kyauta.” Abba ya amsa da Amin sannan kowa ya nufi hanyar gidansa jiki a sanyaye.

****
Anty Khadijah ta dinga kallon sa da mamaki ganin har sannan bai ce komai ba. Ta gyara zamanta dan ita kaɗai ta zo wajen ta ce“Ina jin ka malam, ka ce na zo cikin gaggawa me hakan ke nufi? Ko akwai matsala ne?” Girgiza kansa ya yi ya ce“Babu wata matsala Khadijah, daman ina son sanar dake wani abu ne.” Anty Khadijah da kanta ya fara ɗaurewa ta ce“To ina ji Allah dai yasa lafiya” Jinjina kansa ya yi yana murmushi ya ce“ai lafiya ma idan ki ka ce to ɗaya kenan.” Ita dai ta dinga kallon sa, Ya ɗan yi gyaran murya kafin ya fara cewa

“Wato Khadijah tun ranar dana fara ganinki naji ina ƙaunarki, naji sonki ya ɗarsu a zuciyata. Irin son nan mai tsanani, Ina son kasancewa dake Khadijah, bana gajiya da kallon ki, wannan dalilin ya sanya nake yawan gayyatar ki nan, saboda ƙaunar da nake miki. Ina son ki bani dama na zama abokin rayuwarki, na aureki mu zauna ƙarkashin inuwa ɗaya.!”

Wata irin zabura Anty Khadijah ta yi ta miƙe tsaye, Ta dinga watsa masa wani kallo bakinta na rawa. Miƙewa ya yi yana kallon ta, kafin ya yi magana ta ce

“Kai ɗin banza! Kai ka isa na aureka? Ashe ma mahaukaciya ce ta raine ni, wallahi kaci ƙarya! Dube ka, wani ƙazami dakai. To ko auren saurayi da budurwa ban auri lalataccen namiji ba ballantana yanzu.”

Ta ƙare maganar cikin bala’i, Shi dai bai ce komai ba sai kallonta da yake. Ta jujjuya a gabansa kafin ta ci gaba da faɗin

“Kalleni! Ni Khadijah nafi ƙarfin ka ce zaka aureni wallahi! Ban da ma ƙaddara ta kawoni wajenka kai baka isa ko ganina ka yi ba. To idan ka aureni sai ka ajiye ni a ina? A wannan kejin gidan naka? Dame zaka ciyar dani? Ko kana son kace min da wannan banzar lalatacciyar sana’ar taka? To ka kama kanka tun wuri. Na rantse makamanciyar wannan maganar na sake ji a bakinka sai na saka an ɓatar min da kai. Baka san hau ɗina bane…”

Taja wani dogon tsaki ta sunkuya ta dauki jakarta ta zura takalmanta ta bar soron a fusace. Malam Garba ya bita da idanu sai kuma ya girgiza kansa ya koma ya zauna yana sauke nunfashi…. Kasa haƙuri ta yi taje gida, Ta gangara gefen titi tayi parking ta zaro wayarta daga jaka ta hau kiran Kaddu. Sai dai har kiran ya katse bata ɗaga ba, Anty Khadijah taja wani dogon tsaki sannan ta yi wurgi da wayarta ta ci gaba da driving ɗin, Lokaci zuwa lokaci take yin kwafa ko kuma ta girgiza kanta, har wani cije baki take na zallar masifar dake cinta.

****
Amma ta dinga kallon ta ganin yanda take kukan har sannan, Ta ajiye mug ɗin a gefen drawer sannan ta hawo kan gadon. A hankali ta dafa kafaɗarta cikin son kwantar mata da hankali ta ce

“Ya isa haka Haule, Ki yi haƙuri ki yarda da ƙaddara. Haka Allah ya yi aurenku ba zai daɗe ba, ki daina damun kanki kin ji.”

Gyaɗa mata kai Haule ta yi bayan ta goge hawayenta, Amma ta yi shiru tana kallon yarinyar cike da tausayawa, Dole taji babu daɗi dan mutuwar aure ba ƙaramin abu bane. Ko faɗa kuke idan ku ka rabu sai kun ji a jikin ku, ballantana kuma ana zaune lafiya babu wani tashin hankali a ce miki an sake ki.

“Tashi ki je ki wanke fuskarki ki zo ga tea na kawo miki.”

Amma ta yi maganar a sanyaye. Toh kawai Haule ta ce duk da bata jin zata iya shan tea ɗin amma ta sauka daga kan gadon ta nufi hanyar banɗakin jiki a sanyaye, Wanke fuskarta ta yi ta fito ta ɗan ja ta tsaya a jikin ƙofar ta riƙe kanta. Amma dake lura da ita ta ce

“Lafiya?”

Girgiza mata kai ta yi, sannan ta fara tafiya hannunta dafe da kanta. Idanunta ne suka fara lumshewa, ta riƙe kanta da hannu bibbiyu saboda wata irin sarawa, Ganin haka ya sanya Amma tasowa sai dai kafin ta iso gabanta tuni Haule ta faɗi ƙasa a sume. Cikin tashin hankali Amma ta durƙusa a gabanta, Ta ɗagota tana kiran sunanta, lura da bata cikin hayyacinta ya sanya Amma tashi ta fice daga ɗakin da sauri.

****
Upper East side,
New York.

A hankali ya fara buɗe idanunsa, Ya kalli Nana wadda ta riƙe shi sosai fuskarta a kwaɓe kamar mai shirin yin kuka, Hannunsa ya sanya ya janyeta daga jikinsa sannan ya tashi zaune yana kallon agogon dake maƙale a ɗakin, Ƙarfe 1:20 na rana. Dan haka ya zame duvet ɗin daga jikinsa ya sauka daga kan gadon, bedroom slippers ɗin dake ƙasan gadon ya zura a ƙafafunsa sannan ya nufi toilet. Bayan kusan mintuna talatin ya fito yana tsane kansa da towel, Yayinda jikinsa ke ɗigar ruwa, Gaban mirror ɗin sa ya ƙarasa, Ya saka dryer ya busar da kansa sannan ya shafa mai, Bayan ya gama ya gyara kansa ya feshe jikinsa da turaren Arabian oud mai daɗin ƙamshi. Ya ƙarasa gaban katon press ɗin dake gefen mirror ya buɗe, kayane a jere a ciki, kowane abu an ajiye shi a mazauninsa. Wasu t-shirt da 3-quater ya dauƙo, Ya warware su daga jakarsu sannan ya saka. Rigar fara ce tas sai ƙaton hoton mage a jiki kamar ya yi magana, Wando kuma blue colour ne mai aljihu dayawa. Wata p-cap ya dauko white ya ɗora akansa, gashin kansa ya sauka a gefe da gefe na kafaɗunsa. Ya ɗan kalli kansa a jikin madubi yana suɗe lips ɗinsa yana kuma taunesu a lokaci ɗaya. Ta jikin madubin ya hangota sai wargaza gashin kanta take, Ya sauke numfashi kafin ya juya yana kallon ta. Ita ma kallon nasa take da lumsassun Idanunta, Ya ƙarasa wajen cikin takunsa na isa da tagama. Wayarsa ya ɗauka akan drawer ya ɗan danna ganin har sannan tana zaune yasa ya ce

“Idan na fita ba zan dawo ba sai dare.”

Miƙewa tsaye ta yi tana kallon sa, sai a sannan ta tuna da ƙofar key gareta. Ta nufi toilet da sauri gudun kada ya tafi ya barta. Sabon brush ta ɗauka ta wanke bakinta sannan ta wanke fuskarta ta goge da towel sannan ta fito. Bata gan shi a ɗakin ba, Taji gabanta ya yi wani irin faɗuwa. Kamar mara gaskiya haka ta fara leƙa kowace kusurwa ta ɗakin tana cewa

“Uncle… Uncle… Uncle!”

Wani zaburraren ihu ta saka jin an riƙeta, Ya yi baya yana murmushi ya ce“Matsoraciya kawai.” marairaice fuska ta yi kamar zata yi kuka ta ce“Uncle ka bani tsoro wallahi.” Bai ce mata komai ba sai murmushi da yake a hankali, Dimple ɗinsa na lotsawa kamar ka yi ajiya a wajen. shagala ta yi da kallon sa, ganin yanda asalin kyawunsa ya bayyana. Ya ja hancinta ya ce

“Bar kallona yarinya.”

Ji ta yi kamar ta nutse saboda kunya, Ta yi gaba ba tare da ta ce komai ba ta fice daga bedroom ɗin. Girgiza kansa ya yi sannan yabi bayanta shima, Tana tsaye ya saka password ɗin ya buɗe ƙofar sannan suka fito. Kai tsaye kuma downstairs suka nufa, Xahra dake zaune akan sofa ita da Noor ta dinga kallon su da ɗan mamaki dan bata san sanda Nanar ta je apartment ɗinsa ba. Ita kuwa Nana hannunta ta zura a tsakanin nasa, ta riƙe shi gam kamar wadda taga abun tsoro. Zahra ta ɗauke kanta tana ci gaba da nunawa Noor videon da suke gani. Yarinyar na ganinsa ta taso da gudu ta rungumeshi ya sunkuya ya ɗauketa ya ɗorata a kafaɗarsa yana murmushi ya ce

“Yarinya kin dawo gida ko?”

“Abbie gobe zan ci gaba da zuwa school?”

Ta yi maganar tana ƙoƙarin jan gashin kansa. Gyaɗa mata kai ya yi kafin ya ce

“Yeh! Idan naci abinci sai ki zo muje a siya miki kayan tafiya school ko?”

Sake ƙanƙameshi ta yi tana dariya ta ce

“Yeeee Abbie i love u so much!”

Ya ja kumatunta yana dariya ya ce“love you too my baby girl.” Ya ƙarasa kan sofa ya zauna yana kallon Zahra ya ce

“Madam ki shirya idan na gama cin abinci zamu fita.”

“Okay doctor.”

Ta ce a sanyaye sannan ta tashi ta bar wajen, Nana ta bita da kallo sai kuma ta taɓe baki na zauna can nesa dasu tana kallon su ganin yake ta yiwa Noor ɗin wasa ita kuma tana dariya. After some minutes aka fara shigo da abinci, Cikin ƙankanin lokaci aka cika tsakiyar parlourn da nau’in abinci kala-kala, Dan shi ya ce masu ba zai ci a dining ba. Nana ta dinga kallon su har suka gama suka bar wajen, Ita dai bata motsa daga inda take ba ballantana taje inda abincin yake. Ya sauke Noor daga jikinsa sannan ya zamo ƙasa ya zauna dan ba ƙaramar yunwa yake ji ba. Kallon abincin ya yi sai kuma ya kalli Nana dake zaune kan kujera ya ce

“Zo ki ban abinci.”

Da ɗan mamaki ta dinga kallon sa, kamar wadda ta tuna wani abu kuma sai ta taso ta ƙaraso wajen, Da kansa ya dinga nuna mata yanda zata yi har ta gama haɗa masa ta miƙa masa. Ganin tana shirin tashi yasa ya ce

“Ke ba zaki ci abincin ba?”

Girgiza kanta ta yi kafin ta ce“Ni na ƙoshi.”

“Ko?”

Ya yi maganar yana watsa mata wani kallo wanda ya sanyata shiga taitayinta. Kasa motsi ta yi, Ya ɗauki mug ɗin coffee ɗin ya kai bakinsa bayan ya yi bismillah. After ya cire daga bakinsa ya miƙo mata, Ta dinga kallon sa sai kuma ta saka hannu zata karba, Ya doke hannun yana sake matsowa dashi wajen bakinta. Jiki a sanyaye Nana ta buɗe bakinta ya bata coffee ɗin, Ta ɗan lumshe idanu saboda zaƙin da taji. Haka ya dinga shan coffee ɗin yana bata yana haɗawa da hamburger, Sai da yaji ya ƙoshi sannan ya zare hannunsa yana kallon ta ya ce

“Kin ƙoshi?”

Saurin gyaɗa masa kai ta yi dan daman tun ɗazu take jiran taji ya ce mata hakan. Ya zabga mata harara ya ce“to sai kin cinye wannan raguwar” Ya nuna mata ragowar wadda ke plate ɗin wadda tafi rabin guda. Marairaice fuska ta yi tana tura ragowar ta bakinta ta ce

“wallahi uncle na ƙoshi, zan yi amai.”

“To ki yi ɗin.”

Ya faɗa in i don’t care manner ɗin nan. Ganin ya ƙara dauƙowa yana nufo bakinta ya sanyata fashewa da kuka, Ta rufe bakinta tana girgiza masa kai. Kallon ta ya dinga yi can kuma ya mayar ya ajiye rai a haɗe ya ce

“Tashi ki bani waje.”

Kamar jira take ta tashi da gudu ta bar parlourn ta nufi benanta. Ya bita da kallo sai kuma ya girgiza kansa, A parlour ta fadi tana sauke numfashi, Ta dafe cikinta wanda take jin ya yi mata wani irin nauyi. Ita bata saba cin abinci dayawa haka ba, Duk haɗamarta abinci kaɗan ke isarta, Ta jingina da gefen kujera tana sauke numfashi.

Wajejen ƙarfe 3:00 na rana ya turo ƙofar ɗakin, Kwance ya hangeta cikin bargo ta lulluɓa har kanta, Ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonta ya ce

“Nana!”

“Na’am…”

Ta amsa muryarta na rawa. Sam bai fahimta ba dan ya yi zaton bacci ne akanta, Dan haka ya ce

“Taso muje unguwa.”

Girgiza kanta tayi tana daga kwancen da take ta ce“Ni bana so.”

Shiru ya yi yana kallonta, Ya ɗaga kafaɗarsa sannan ya juya ya fice daga ɗakin, Ta sake juyi ta koma can ƙarshen gadon tana runtse idanunta. Tsaye ya samu Zahra a parlourn tana gyarawa Noor bottle ɗin rigar sanyin dake jikinta, Ya ƙarasa ya ɗauketa yana faɗin

“Ya kamata mu yi sauri, cause naga garin da hadari sosai.”

Zahra tabi bayansa tana zura hannayenta cikin aljihun rigar sanyin dake jikinta.

****
Yola, Nigeria.

Amma ta dinga kallon takardar da mamaki kafin ta ce“Allah mai iko, kaji rabo?” Abba ya ɗan yi murmushi dan har cikin zuciyarsa yaji daɗin kafin ya ce“Allah mai yanda yaso. To Alhamdulillahi Allah ya raba lafiya.”

“Idan ka fita ka sanar da Safwan ɗin.”

Abba ya yi maganar yana kallon Sultan dake tsaye gefe ɗaya ya harɗe hannayensa a ƙirji, Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce“Ni da ba shiga harkarsa nake ba Abba.”

“A saboda me? To ko baka shiga harkarsa wannan saƙo ne na baka ka faɗa masa Haule tana dauke da cikinsa. Saboda haƙƙinsa ne a sanar dashi, koda ya saketa kuwa.” Jiki a sanyaye Sultan ya ce

“Tom Abba, in sha Allah zan faɗa masa. Allah ya raba da lafiya” Abba ya amsa da amin sannan ya kalli Amma dake tsaye hannunta rike da takardar har sannan ya ce

“Ki je ki sanar da Fatima, Idan na fita zan faɗawa Yaya. Sai a san yanda za’a yi a faɗawa Hajiya Babba”

Amma da lokaci ɗaya taji jikinta ya yi sanyi saboda Hajiya Babba da aka ambata ta ce“tom in sha Allah zan je.”

“Yanzu ki fara zuwa ki dubata, Bari muje.”

Okay kawai ta ce sannan ta nufi hanyar bedroom ɗin Nanar, Sultan ya sauke numfashi sannan ya juya ya
Fice daga parlon Abba na biye dashi.

****
Kaddu ta yi tagumi tana kallon Anty Khadijah dake ta zazzaga masifa tunda ta shigo. Ta yi shiru tana saurarenta har sai da taga ta tsagaitan dan kanta sannan ta ce

“Ke matsalata dake rashin sanin abin da zaki yi. To sai me dan yace yana sonki? Yana son ki aurar ki ya yi? Ko zai miki dole ne? Ni ban ga abin tashin hankali anan ba wallahi tallahi. Ba dai sai kin sake zuwa wajen nasa sannan har zai faɗi wannan maganar ba? Ai ba shi kaɗai ne malami ba, Gasu nan malamai da bokaye kamar jamfa a Jos, mene ne naki na tada jijiyoyin wuya dan Allah?”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *