Chapter 38: Chapter 38
Girgiza kai Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“Ba zaki gane ba Kaddu. Ya raina min hankali ne fa, Idan ba rainin hankali ba ina shi ina ni Khadijah? Ina yake da abin da zai aureni? Wannan abun shi ne yake ƙonamin rai wallahi.”
Kaddu ta ja tsaki sannan ta ce“Kin ji ko? To mene na ɓata ranki anan. Kawai ki bar shi mana. Ki kwantar da hankalinki zamu samo wani nan ba da jimawa ba, Yo ko maza sun ƙare me zaki yi da wannan gajan? Ai ke daga nan sai new York in sha Allahu.”
Murmushi Anty Khadijah ta yi ta nemi waje ta zauna kafin ta ce“Har naji sanyi a raina ƙawata.” Kaddu ta kashe mata ido daya sannan ta ce“Yauwa ni bana son naga kina saka kan ki cikin damuwa.” Anty Khadijah ta dauki ruwan da aka ajiye mata tun ɗazu ta balle murfin ta hau sha.
****
New York.
Basu suka dawo gidan ba sai wajen ƙarfe 7:00 na dare. Abdusammad ya sauke Noor dake hannunsa sannan ya ce“maza ki je ki shirya, Zan je nayi sallah.” To kawai ta ce tana riƙe da ledar dake hannunta, Ya ɗan kalli Zahra wadda ranta ke haɗe har sannan sai kuma ya juya ya fice daga parlon.
“Bari naje na kai wa Anty Nana nata.”
Noor ta yi maganar tana ɗaukan ɗaya daga cikin ledojin da guard ɗin ya ajiye a parlourn, wata irin tsawa Zahra ta daka mata ta ce
“Kin bar nan ko sai ci ubanki!”
Bata saba da irin haka ba dan haka ta fashe da kuka ta yar da ledar hannunta, Zahra ta yi tsaki ta wuce sama ta bar ta a wajen. Har ya dawo daga sallah bata daina kukan ba, Ya ƙarasowa wajen yana kallon ta da mamaki ya ce
“Noorie me aka miki?”
Cikin kuka ta ce“Ummi ta min tsawa Abbie, Kaina zafi yake min.” Ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan, Sosai ransa ya ɓaci dan ko da wasa baya son yaga an ɓatawa yaro rai. Ya durƙusa daidai tsayinta yana goge mata hawayen kafin ya ce
“Shikenan ya isa daina kukan kinji, Ke da zaki ci gaba da zuwa school gobe?”
Tuni ta manta da batun tsawar ta washe baki tana dariya ta ce“Abbie ina son naga Afeefa.”
Murmushi ya yi ya ja kumatunta ya ce“Okay zaki ganta ai, Maza je ki ɗaki.” Sakin hannunsa ta yi ta nufi saman da gudu, Ya bita da kallo kafin ya miƙe tsaye. Kallon apartment ɗin Zahran ya yi, Kamar ya shige sai kuma ya nufi sama. Zaune ya sameta gefen gado tana danna wayarta ya ƙarasa ciki ya tsaya a jikin madubi hannayensa harɗe a ƙirjinsa ya ce
“Akan me zaki dinga yiwa yarinya ƙarama tsawa? Me ta yi miki?.”
Ɗago kanta ta yi da kalleshi sai kuma ta sake sunkuyar da kai tana ci gaba da danna wayarta. Ba ƙaramin mamaki ta bashi ba, dan Zahra bata saba haka ba, Ya yi shiru yana kallon ta kafin ya sake cewa
“Zahra dake nake magana fa…”
Miƙewa tsaye ta yi a fusace tana kallon sa ta ce“To bani da ikon yi mata tsawa ne? Ko ka manta nima ƴata ce? Laifin ta min shiyasa nayi mata!” ta ƙare maganar a mugun fusace. Shiru ya yi yana kallon ta, ganin haka ya sanya ta ɗauki wayarta ta fice daga ɗakin kamar zata tashi sama. Ya daɗe tsaye a wajen yana mamakin abin da ta yi, Can kuma ya sauke numfashi ya juya ya bar ɗakin shima.
Wajejen ƙarfe 8:00 na dare ya fito sanye da ƙananun kaya, Kai tsaye kuma apartment ɗin Nana ya nufa. Kwance ya hangeta tsakiyar gado sai juyi take gaba ɗaya ta yamutse bedsheet ɗin, Ya ƙarasa ciki yana kallonta ya ce
“Nana mene haka?”
Jin bata bashi amsa ba ya sanya shi hawa kan gadon, hannunsa ɗaya ya sanya ya jawota. Kamar jira take ta saki wani marayan kuka tana riƙe shi, Da mamaki yake kallon ta, Ya janyota jikinsa gaba ɗaya yana kallon fuskarta ya ce
“Nana mene ne? Meke damunki?”
Ya yi tambayar yana taɓa jikinta, Zafi yaji sosai dan haka ya sake cewa“Baki da lafiya? Mene yake miki ciwo.?”
Cikin shassheƙar kuka ta ce“Uncle ka kaini wajen Abbana, ni gida zani.”
“To zan kai ki, Yanzu faɗa min meke damunki?”
Rufe idanunta ta yi hawaye na zubowa ta cikinsu ta ce“cikina ne yake min ciwo.”
Girgiza kansa ya yi ya ce“Sannu to, kwanta ina zuwa.” Ya kwantar da ita sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin, Tashi ta yi da kyar ta sakko daga kan gadon, Ta yi durƙusa a wajen ta ɗora kanta a gefen gadon kamar me kneel down. Har ya dawo tana haka, Ya ajiye drip ɗin hannunsa da allurar ya tsaya yana kallon ta, can kuma ya ce
“Ke cikinki ke ciwo ko mararki?”
Kamar daga sama taji tambayar tasa, Ta ɗago idanunta da kyar tana kallon sa. Ƙarasowa wajen ya yi ya zauna gefen gadon ya ɗagota ya zaunar da ita a jikinsa ya ce
“Mararki ne ke ciwo ko cikin ki?”
“Marata…”
Ta ce cikin shessheƙar kuka. Dungure mata kai ya yi kafin ya ce“shi ne zaki ce min cikin ki? Me ki ke ɓoyewa?” Ita dai bata iya magana ba saboda ciwon da yaci ƙarfinta. Ya kwantar da ita akan gadon sannan ya tashi ya fice, After 5mins ya dawo hannunsa riƙe da mug da wata injection, Ya ajiye allurar kan waɗancan sannan ya zauna kusa da ita, Ɗagota ya yi da hannu ɗaya ya jinginata da jikinsa ya ce
“Oya drink it.”
“Ni ba zan iya sha ba.”
Ta yi maganar tana yarfe hannu, Haɗe rai ya yi ya ce“zan makeki, drink it my friend!” kuka ta fara yi a hankali, Ya kai mata mug ɗin bakinta, Dakyar ta buɗe bakin ta fara sha a hankali. Ko rabin shayin bata sha ba ta ɗauke kanta, Ya sake miƙo mata fuskarsa a haɗe ya ce
“Yaushe na fara wasa da ke?”
Toshe bakinta ta yi tana girgiza masa kai, Ya janye hannun daga kan bakinta kamar jira take ta fara wanke shin da amai. Shiru ya yi yana kallon ta ganin yanda take kwarara aman har da na abincin da taci ɗazu, gaba ɗaya ta ɓata masa jikinsa, ta ɗora kanta akan ƙirjinsa tana sauke numfashi idanunta a lumshe. Hannunsa ya sanya ya dafa kanta a sanyaye ya ce
“Sannu.”
Bata ce komai ba, Ya tashi da ita a jikinsa ya nufi toilet, Zaunar da ita ya yi sannan ya fara ƙoƙarin zare mata kayan jikinta. Ta yi saurin riƙe hannunsa tana kuka a hankali, Haɗe rai ya yi ya doke hannunta sannan ya ƙarasa zare mata rigar dake jikinta. Wata irin ajiyar zuciya suka sauke a tare, Ya yi saurin ɗauke kansa daga kan ƙirjinta wanda lokaci ɗaya yaji yana neman tada masa da hankali, sam bai yi tunanin yarinyar ta kai haka ba. Ya kawar da tunanin daga ransa ya miƙar da ita tsaye, Da kansa ya yi mata wankan sannan ya saka mata bathrobe, Ta sake kwantowa jikinsa tana maƙalƙalesa. Ɗaukanta ya yi ya fice daga banɗakin, Ya zaunar da ita kan doguwar Kujerar dake gefen gadon sannan ya yaye bedsheet ɗin ya naɗeshi ya kai toilet ya saka cikin washing machine. Bayan ya fito ya dauƙo sabon bedsheet ya shimfiɗa akan gadon sannan ya ɗaukota ya kwantar da ita akai, Ta dunƙule jikinta waje ɗaya saboda sanyin da take ji, Press ɗinta ya buɗe ya dauko mata wata yar ƙaramar riga mara nauyi, Ya haɗo mata da pant da kuma pad. Ajiyewa ya yi a gefen gadon ya fara ƙoƙarin jawota, saurin riƙe hannunsa ta yi kamar zata yi kuka ta ce
“Zan yi da kaina uncle.”
Ko saurarenta bai yi ba ya jawota gaba ɗaya, Ya kunce bathrobe ɗin ta yi saurin shigewa jikinsa tana sakin kuka a hankali, Girgiza kansa ya yi sannan ya ɗauko rigar ya zura mata. Bayan ya kammala ya juya ya fice daga ɗakin, After 15mins ya dawo cikin wasu sabbin kayan fuskarsa ta sake fresh da alama wanka ya sake, Ya ƙarasa wajen injection ɗin daya ajiye ya fara haɗawa, Nana ta dinga kallon sa da ɗan mamaki, bayan ya gama haɗawa ya hawo kan gadon hannunsa riƙe da syringe ɗin, Ta yi saurin tashi zaune duk da jikinta babu ƙwari, Ganin tana neman guduwa ya sanya ya riƙota, Ya jawota jikinsa fuskarsa a haɗe babu alamar wasa. Kuka ta saka masa ta fara yarfe hannu, Ya jingina da fuskar gadon yana kallon ta, Cikin kuka ta ce
“Uncle dan Allah kada ka yi min allura ban so, zafi take min.”
Kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce
“Baki son allurar?”
Saurin gyaɗa masa kai ta yi tana hawaye, Ya ɗan taɓe baki sai kuma ya ce“To kina son na baki sweet?” gyaɗa masa kai ta sake yi, gaba ɗaya fuskarta a shagwaɓe take tamkar jaririya sai narke masa take. Ya zaro wata chocolate a aljihun wandonsa yana kallonta. Ta haɗiye yawu tana kallon ledar chocolate ɗin, ɓarewa ya yi ya kutsuro yana kallonta ya ce
“Haa.”
A hankali ta buɗe bakin nata, Ya saka mata chocolate ɗin ta fara taunawa a hankali tana lumshe ido. Murmushi ya yi sannan ya ɗauke kansa, Ta kwanta akan ƙirjinsa tana ci gaba da tauna chocolate ɗin, sam bata san ya dauƙo allurar ba, Ya ɗan janye rigarta dan daman ta tattare, ya ɗora tsinin allurar a jikinta sannan ya yi bismillah ya yi mata. Wani irin ƙara ta saki tana ɗagowa daga jikinsa, Ya yi saurin saka bakinsa cikin nata yana shafa bayanta, Kuka ta dinga yi tana ƙoƙarin cizonsa a bakin, Shi dai ya yi shiru yana tsotsar lips ɗinta a hankali. Ta ci gaba da kukanta tana dukansa a ƙirji, Ya ɗan yi murmushi yana riƙe hannunta. Cikin yan mintuna kuma jikinta ya fara saki, Ta mai da kanta ƙirjinsa har sannan bai zare bakinsa daga nata ba, Itama ta fara tsotsar nasa lips ɗin a hankali a haka har bacci ya yi awon gaba da ita. Sai da yaga baccin nata ya fara nisa sannan ya janyeta daga jikinsa ya kwantar da ita, Ta saki ajiyar zuciya tana turo baki gaba wanda yake ta sheƙi, Murmushi kawai ya saki ya ɗan ja kumatunta a fili ya ce
“Rigimammiya!”
Ya gyara mata duvet ɗin ya rufeta gaba ɗaya sannan ya sauka daga kan gadon, Remote ya ɗauka ya ƙaro gudun ac sannan ya kashe leds ɗin dakin ya juya ya fice. A parlour ya samu Zahra tana bawa Noor abinci, Ya zauna ɗan nesa dasu. Ta sauka daga jikin Zahra hannunta riƙe da ƙaramin plate mai ɗauke da chips ta nufosa, Murmushi ya yi yana ajiye wayar hannunsa ya ce
“Noorie.”
“Abbie ka bani abinci.”
To kawai ya ce sannan ya ɗauketa ya ɗorata kan cinyarsa. Ya fara bata abincin tana masa hira, wani ya amsata wani kuma ya yi shiru. Zahra kuwa ta dinga kallon su ba tare da tace komai ba, daga ƙarshe ta tashi ta bar parlourn. Da idanu ya bita sai kuma ya ci gaba da abin da yake, bayan ya gama bata abincin ya sauketa yana cewa
“Oyah muje ki kwanta. Dare ya fara yi”
“Abbie ka ɗaukeni to!”
Ta yi maganar tana miƙo masa hannu, Murmushi kawai ya yi sannan ya ɗauketa ya fara juyi da ita, ta dinga dariya tana ƙanƙamesa. Kafin daga bisani ya nufi apartment ɗin Zahran da ita.
****
Nigeria.
Safwan ne zaune kan kujera idanun sa zube akan Haule wadda ta sunkuyar da kanta ƙasa, Tun da ya shigo yake kallon ta. Ya kasa gane wane yanayi yake ciki, farin ciki ne ko kuwa baƙin ciki? Ya ɗan numfasa kafin ya ce
“Allah ya sauke ki lafiya, Ya bamu mai albarka.”
A zuciya ta amsa da amin dan bakinta ya yi mata nauyi, Ya ɗan yi jim sai kuma ya tashi yana ajiye ledojin dake hannun sa ya ce
“Sai da safe.”
Sai a sannan ta ɗago kanta ta kalle shi da runannun idanunta, Tayi saurin sauke su ƙasa kafin ta ce
“Allah ya tashe mu lafiya.”
Da amin ya amsa sannan ya juya ya bar parlourn, Haule tabi bayansa da kallo kuka na tawo mata. Yana fita Amma na fitowa daga dakin, Ta ƙaraso wajen jin shessheƙar kukan Haulen, Zama ta yi gefenta ta dafata ta ce
“mene ne abun kuka kuma Haule?”
“Amma shikenan na rabu da Yaya Safwan? Shikenan ba zamu tafi gida tare ba? Ni ban ce sai ya zo inda nake ba. Kawai ya maidani gidansa, zuciyata zafi take min Amma!…”
Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka. Shiru Amma ta yi tana saurarenta cike da tausayawa, Can dai ta ɗan bubbuga bayanta ta ce
“Kaddara ce ta haɗaku, kuma ita ce ta raba ku. Ba zai yiwu ki ci gaba da zama da Safwan ba Haule, Saboda dalilin yana da ƙarfi. Ki sakawa ran ki haƙuri, har Allah ya saukeki lafiya ki samu wani mijin ki yi aurenki.”
Haule ta sake fashewa da wani sabon kukan tana faɗawa jikin Amma, Ta dinga rera kukanta kamar ranta zai fita. Ita kanta bata san sanda ta fara son Safwan ba, bata san kuma dalili ba. amma ji take kamar ta tashi tabi bayansa, kamar taje ta roƙe shi akan ya maidata daƙinta. Sun ɗauki lokaci a haka kafin Amma ta ɗago fuskarta ta fara goge mata hawayen ta ce
“Kuka yanzu ba naki bane Haule, ki kwantar da hankalin ki. Ko dan lafiyar abin da ke cikinki.”
A hankali ta gyaɗa kanta, Amma ta ce“Tashi ki shiga ciki, idan aka yi Isha’i sai ki je apartment ɗin Hajiya Babba dan ta ce tana nemanki.”
“ko naje yanzu?”
Haule ta yi tambayar a sanyaye,
“Baki gaji ba?”
Amma ta ce tana kallon ta, gyada mata kai ta yi ta ce“Eh Amma zan iya zuwa.” Numfasawa ta yi kafin ta ce“to tashi ki je Allah ya tsare” Haule ta amsa da amin sannan ta miƙe tana gyara zaman hijabin jikinta ta fice daga parlon, Amma ta bita da kallo sai kuma ta girgiza kanta. Nana ce ta faɗo mata arai, dan haka ta jawo wayarta dake kan table ta fara dialing numbernta, sai dai har ta katse ba’a ɗauka ba dan haka ta mayar da wayar ta ajiye ta tashi ta koma ciki..
Tsaye ta hangesu bakin apartment ɗin Hajiya Babban, ta ƙarasa a sanyaye tana sunkuyar da kanta. Kasa shigewa ta yi dan haka ta ɗan durƙusa ta ce
“Hamma ina yini?”
Sultan ya kalleta dan bai ma ganeta ba, can kuma ya ce“au Haule lafiya kalau, ke ce a daren nan?” gyaɗa masa kai ta yi kafin ta kalli Amrah ta ce“Sannu ya jikin?”
“Da sauƙi Alhamdulillah.” cewar Amrah tana murmush, Safwan ne ya kalleta kamar ba zai magana sai kuma ya ce
“Ina zaki je da daren nan?”
Sai da taji zuciyarta ta buga, Ta ɗan runtse idonta murya can ƙasa ta ce“Hajiya Babba ke kirani.”
“Okay, amma idan kin daɗe ki kwanta anan kawai. Ki daina yawo” toh kawai ta ce sannan ta bar wajen a sanyaye. Sultan ya girgiza kansa yana kallon Safwan fuska babu annuri ya ce
“amma ka cutar da yarinyar nan wallahi. Ni ban so ma wannan cikin ba, yarinya ƴar ƙarama zata zama bazawara har da ɗa…”
Shi dai Safwan bai ce komai ba, dan shima zuciyarsa ba wani daɗi ta yi masa ba. Can dai ya ce
“Goben zan shigo asibitin.”
Sultan ya ɗan harararesa sannan ya ce“kada ma ka shigo, ka zauna ka kashe kanka. Kusan 1 week ina maka magana amma kana shareni” girgiza kai Safwan ya yi cikin sanyin murya ya ce“ba zaka gane bane. Zan zo dai”
“Allah yasa.” cewar Sultan, Ya ɗan yi murmushi sannan ya kalli Amrah dake ta yatsine fuska ya ce“Sai da safe, Allah ya raba lafiya.” da Amin ta amsa sannan ya sake yiwa Sultan ɗin sai da safe ya bar wajen, Sultan ya ɗan kalleta ganin ta durƙusa ya ce
“mene ne?”
“Yaya nagaji, cikina zafi yake min.”
Riƙo hannunta ya yi ya ce“Sorry muje gida.” ta ɗan gyaɗa kanta sannan suka fara tafiya a hankali.
****
Gibson Jalo.
Anty Khadijah ta ɗan kalli Umma sai kuma ta yi dariya ta ce“Ai Umma na kusa auren da gaske in sha Allah. Nan bada jimawa ba zaki ga an fara zancen auren” Umma ta ɗan taɓe baki ta ce“Yo Khadijah kalar wannan zancen yau na fara jin sa a wajenki?.” Anty Khadijah ta yi murmushi ta ce“Allah wannan karon da gaske nake Umma”
Umma ta ce“To Allah ya tabbatar da alkhairi.”
“Amin kuma kin ga…” maganar ta tsaya saboda wayarta dake ringing, Ta ɗan kalli screen ɗin wayar ganin sabuwar lamba ya sanyata ɗagawa, Ta ce
“Hello.”
“Assalamu alaiki.”
Tashi Aunty Khadijah ta yi ta haye sama da sauri, Ɗakinta ta shiga ta saka key ta rufe sannan ta ce
“Akan me ka ke kirana? Bana faɗa maka ni ba sa’ar aurenka ba ce?”
Girgiza kansa ya yi yana murmushi can kuma ya ce“Khadijah kenan, daman kiran ki nayi na nemi yafiyarki. Wallahi bada wani abu nayi wannan maganar ba, amma ina son ki yi haƙuri ki yafe min.” Anty Khadijah taja wani dogon tsaki kafin ta ce
“An faɗa maka ni irin waɗanda zaka yiwa wayo ce? To bari kaji wallahi koda wasa ka sake kirana sai nayi maka rashin mutunci, Wani ƙazami da kai!”
Bata jira amsar da zai bata ba ta sauke wayar daga kunne ta katse kiran tana jan wani dogon tsaki. Tsabar takaici ya sanya ta yi wurgi da wayar ta faɗa tsakiyar gado, Ta nemi gefe ɗaya ta zauna tana tunani. Ta fuskanci idan bata yi maganin mutumin nan ba sai ya sakata a masifa, Ta yi kwafa ta tashi ta fice daga ɗakin gaba ɗaya..
****
Safwan ya dinga kallon Siyama ganin yanda ta ɗan haɗe rai, Ya girgiza kansa ya ce
“Ba wai dawowa zata yi ba fa. Kawai dai na faɗa miki ne”
Taɓe baki ta yi ta nemi gefe ɗaya ta zauna tana kallon sa ta ce“Ai saboda ita ka ɗauka da muhimmanci gashi har ta samu ciki a ɗan zaman da ku ka yi tare, amma ni da baka ɗaukeni a bakin komai ba ai gashi ka bar ni sai dai naci na kasayar!”
Safwan ya dinga kallonta da mamaki, can kuma ya ce“Siyama ban gane me ki ke nufi ba? Daman ni ne wanda nake da alhakin samun cikin ki ko rashin sa? Mene nawa a ciki?.”
Tashi tsaye ta yi tana harararsa ta ce“A’a ba kai bane, ya za’a yi ya zama kai daman! Amma ka sani wallahi idan dan ka zalunceni ka ke min haka Allah ba zai bar ka ba. Ai nima matarka ce, kuma nima ina son naga na haihun, amma shi ne ka fifita ƴar uwarka akaina…” Ta bar parlourn da sauri tana kuka, Safwan ya bita da kallo sai kuma ya sunkuyar da kansa yana sauke numfashi. After some minutes kuma ya tashi yabi bayanta. Zaune ya sameta gefen gado sai kuka take a hankali, Ya ƙarasa ciki ya tsaya a zauna akan drawer yana kallon ta ya ce
“Ina son ki gane wannan ba laifina bane Siyama, ban kyamace ki ba, ban guje ki ba. Na ɗauki hakan matsayin ƙaddararmu gaba ɗaya dani dake, amma ki sani ba ni ne wanda ke bada haihuwa ba, tsarin Allah ne. Kuma shi yaga damar ya hukunta Haule ta samu ciki, Shi ne ya yi mata kyautarsa, dan haka ki daina damun kan ki, idan Allah ya so sai ki ga ya sake bamu wasu. Kuma ai a ganina abin da zan haifa kamar naki ne, duk abin da Haule ta haifa karɓarsa zan yi, mu raine shi tare. Kin ga zamu samu ɗa mai lafiya…”
“Ai daman dole ka ce haka, dole ka ce kana son ka samu ɗa mai lafiya. Saboda ni ba zan iya haifar maka ɗan ba, ko kuma baka son irin wanda zan haifa kai da danginka. Shi ne zaka ce min tsarin Allah ne!”
Safwan ya yi shiru yana kallon ta, sam bata fahimci abin da yake nufi ba, dan haka ya taso daga inda yake ya dawo gefenta ya zauna. Hannunta ya riƙe cikin nasa murya a sanyaye ya ce
“Ba haka bane Siyama. Wallahi ko yau Allah ya baki ciki zan yi farin ciki, kamar yanda nayi farin ciki dana Haule. Kuma ai likita ya faɗa mana zamu iya haifar ya’ya wanda basu da cutar, dan haka ki daina damun kan ki dan girman Allah”
Siyama ta sanya ɗayan hannunta ta goge hawayenta, cikin shessheƙar kuka ta ce“Ai shikenan. Allah ya sauketa lafiya.”
Murmushin jin daɗi ya yi dan daman ya san zata fahimce shi ya ce“Amin, Ya bamu wasu Ya’yan.” da amin ta amsa sannan ta ce“muje ka ci abinci.” To kawai ya ce duk da ba yunwa yake ji ba, Ta tashi tana riƙe da hannunsa ta ce“muje to” Ya gyaɗa mata kai bayan ya miƙe tsaye suke fice daga ɗakin.
****
New York, America.
Zahra na zaune tana danna wayarta ya shigo, Sanye yake da pyjames white colour ya ɗaure kansa da ribbon, Ya ƙaraso ciki ya zauna gefen gadon yana kallon ta.
“Sannu da zuwa.”
Ta ce a sanyaye bayan ta ajiye wayar a gefenta. Babu yabo babu fallasa ya ce“Yauwa.” shiru wajen ya ɗauka can kuma ta ce“Ko na kawo maka abinci?” girgiza kansa ya yi yana kallonta ya ce“A’a thank you.”
“But you didn’t eat anything fa. Ko dai Nana ta baka abinci?”
Sake girgiza kansa ya yi ya ce“a’a ban ci komai ba, Nana ma bata jin daɗi.” Zahra ta kalleshi a karo na farko ta ce“me ya sameta?” zare ribbon ɗin kansa ya yi ya ce“nothing serious fa, wai cramps ke damunta”
Zahra ta girgiza kanta a sanyaye ta ce“Allah ya sawwaƙe.” Amin kawai ya ce, can kuma ya ce“yau mene ya same ki?” girgiza kanta tayi tana murmushi ta ce“babu komai fa, kawai mood swings ne” Abdusammad ya ɗan taɓe baki sai kuma ya jawota jikinsa ya ce
“shi ne zaki dinga wani shareni?”
Murmushi ta yi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa ta ce“to ai kai ma sharenin ka yi.” ta ƙare maganar tana shagwaɓe fuska, Ɗago kanta ya yi ya ce“da gaske?” Ta gyaɗa masa kai tana sake narkewa a jikinsa, Murmushi ya yi ya ce“to yanzu zan daina share kin” murmushi ta yi ta ɗago kanta tana kallon sa ta ce“gobe Noor zata tafi school, dan haka da wuri zan tashi.”
Gyaɗa kansa ya yi ya ce“haka ne to dan haka sai ki kwanta da wuri, naga ta damu ta koma da sai ta bari sai ta huta.” Zahra ta ce“wannan ƴar taka mai wutar ciki, ya za’a yi ta jira?” ta ƙare maganar tana murmushi. Dariya ya yi ya ce“Eh ai ke ta gado” Zahra ta ɗan kalleshi da mamaki ta ce“a haba dai ni doctor”
Murmushi ya yi ya ja hancinta ya ce“Eh mana.” Zahra ta maƙale kafaɗa ta ce“a’a sai dai idan kai ta gado wallahi.”
“Ko?”
Ya ce yana ƙoƙarin kwanciya, Ta ɗan yi murmushi sai kuma ta kwanta a gefensa…



