⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 39: Chapter 39

Around 2:00 na dare ta buɗe idanunta, Ta tashi zaune ta dakyar saboda ciwon da marar ke mata, ta ɗora hannunta akan mararta tana kuka a hankali. Ta daɗe zaune a wajen kafin ta sauka daga kan gadon dakyar, Ta kunna bedside lamp nan da nan haske ya gauraye ɗakin, kalle-kalle ta dinga yi ganin bata ganshi ba ya sanya ta zura slippers ɗinta ta nufi waje a hankali. Kai tsaye apartment ɗinsa ta nufa, Ta tsaya bakin ƙofar tana murza idanunta wanda har sannan bai gama wartsakewa ba. A hankali ta fara knocking ƙofar tana kiran sunansa, Sai dai har bayan mintuna biyar babu alamar za’a zo a buɗe, Nana ta fashe da sabon kuka tana ɗan buga ƙafafunta, ita kaɗai ta san azabar da take ji. Ta juya ta sauka daga benan, Tsayawa ta yi a wajen tana kallon benan Zahra, lokaci ɗaya kuma ta hau tana tafe tana dafe mararta. Knocking ta dinga yi kamar zata jijjige ƙofar. Abdusammad ya janye Zahra daga jikinsa ya tashi zaune yana kallon ƙofar da mamaki. Itama Zahra buɗe idanunta ta yi dan ba wani nauyin bacci gareta ba,

“Kin ji?”

Ta gyaɗa masa kai tana hamma, bayan ta rufe bakinta ta ce“waye to?”

“Ko Noor ce?” Y tambaya yana sauka daga kan gadon, Zahra ta gyara zamanta tana jiransa. Ya ƙarasa ya buɗe ƙofar. Da mamaki yake kallonta, ganin yanda ta yi tsaye a wajen tana murza idanunta tana kuka, Ya ɗan ware idanunsa kafin ya ce

“Mene ne Nana?”

Cikin kuka ta ce“uncle ni bana son kwana ni kaɗai, kuma cikin ciwo yake min…” ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan, Zahra ta taso tana kallon sa ta ce

“mene ne?”

Ya ɗan girgiza kansa bayan ya bar jikin ƙofar, Nana ta gani tsaye tana kuka. Ta kalleshi ta ce“Lafiya dai?”

“Uncle ni tsoro nake ji. Ka zo mu tafi tare”

Daga shi har Zahra suka kalleta, Ta janye hannunta daga idanun tana kallon su sai kuma ta ɗauke kai tana tura baki. Abdusammad ya ce“zo nan.” jiki a sanyaye ta ƙarasa gabansa, Ya sanya hannunsa na dama ya taɓa wuyanta. Zazzaɓi ne sosai a jikinta, Ya ɗan girgiza kansa kafin ya ce“to ki zo ku kwanta da Zahra anan.” A hankali ta kalle shi sai kuma ta sunkuyar da kanta tana maƙale kafaɗa, Zahra ta ɗan yi murmushi ta ce“Kawai doctor kaje.” wani banzan kallo ya watsa mata kafin ya kalli Nana ya ce“koma ki kwanta to. Babu abin da zai same ki” Cikin kuka ta ce“Allah ni ba zan iya kwanciya ni kaɗai ba, Tsoro nakeji. Kuma ai bani da lafiya…” Ta sake fashewa da kuka, Haɗe ransa ya yi in a serious tone ya ce

“koma nace!”

Ganin babu wasa akan fuskarsa ya sanyata ficewa daga ɗakin, Ya mai da ƙofar ya rufe ya koma kan gadon. Zahra ta dinga kallon sa kafin ta ce“amma ka ce bata da lafiya fa, da kaje wajenta.” Bai bata amsa ba ya yi kwanciyarsa, dan ya riga da ya san halin Nana, rashin son zaman lafiya ne kawai irin nata. Zahra bata sake cewa komai ba itama ta koma ta kwanta. Nana ta dinga kallon ƙofar hawaye na sakkowa kan idanunta, Ta juya ta fice daga parlourn ta koma ɓangarenta. Kwanciya ta yi akan gadon ta dinga kuka tana juyi, can kuma ta tashi ta gudu ta nufi banɗaki. Amai ta yi ta wanke bakinta ta dawo ɗakin ta kwanta, ko kaɗan ta kasa bacci sai juyi take tana kuka, tun da ta fara period bata taɓa yin irin wannan ba. Saboda ba’a taɓa barinta babu magani, idan bata yi bacci ba babu wanda zai kwanta a gidan, ko tsakar dare ne sai Abba ya fita ya kai ta asibiti. Ta sake rushewa da kuka tana jin haushin biyoshin da ta yi, tana nan kwance har aka fara kiraye-kirayen sallar asuba a masallacin gidan, ta dinga ƙoƙarin tashi zaune amma ta kasa, daga ƙarshe kuma bacci ya ɗauketa.

Murɗa handle ɗin ƙofar ya yi bakinsa ɗauke da sallama, Ya shigo ciki ya mai da ƙofar ya rufe yana kallon ta, gaba ɗaya ta rufe jikinta da bargo ko kanta ba’a gani. Ya ɗan girgiza kai sannan ya ƙarasa ciki ɗakin, zama ya yi gefen gadon ya sanya hannunsa mai maƙale da counter ya ɗan taɓa ta ya ce

“Ke Nana.”

Shiru bata amsa ba, Ya janye bargon yana kallon ta, ba bacci take ba, amma idanunta a rufe suke sai hawaye dake zubowa ta gefensu. Hannunsa ya kai ya taɓa wuyanta yaji har sannan da zafi sosai, Ya tashi ya fice daga ɗakin ba tare da ya ce komai ba. Bayan kusan mintuna goma ya dawo hannunsa riƙe da wani ƙaramin tray, Ya jawo table ya ajiye sannan ya koma ya zauna yana kallon ta ya ce

“Taso.”

Ba zaka taɓa cewa da ita yake ba, dan ko buɗe idanunta bata yi ba. Sai shessheƙar kuka da take a hankali, Murmushi ya yi sai kuma ya sanya hannunsa ɗaya ya ɗagota. Kamar jira take ta fashe da kuka tana ƙoƙarin janye hannunsa, sai dai rashin gwarin jikinta ya sanya ta gagara yin hakan. Ya zaunar da ita akan cinyarsa yana kallon ta ya ce

“ina miki magana kina share ni?”

Ɗauke kanta ta yi tana ƙoƙarin sauka daga jikinsa, Ya riƙe gam ya ɗago fuskarta ya ce“me aka miki?” bata san sanda ta sake fashewa da kuka ba, Ta fara dukansa tana cewa

“Ni ka rabu dani, ni bana so kana taɓa ni. Wallahi sai na faɗawa Ammata, ni gidanmu zan tafi…”

Ban da murmushi babu abin da yake, Ya riƙe fuskarta cikin tafukan hannunsa ya ce

“Yaushe zaki tafi gidan?”

Kallon sa ta yi, ganin yanda yake murmushi ya sanyata ɗauke kanta tana sake rushewa da wani kukan, Janyo fuskarta ya sake yi ya rungumeta ya ce

“Shikenan ya isa haka. Ki yi shiru kin ji”

“ka mayar dani gida”

Ta ce tana kuka, Shafa kanta kawai ya yi ya ce“tom zan mai da ke. Zo ki ci abinci”

“A’a ni ba zan ci ba ɗin.”

Ɗago fuskarta ya yi ya ce“tashi nace, je ki wanke bakinki ki zo ki ci abinci” sake maƙale kafaɗa ta yi tana shirin yin magana taji ya daka mata tsawa, Da sauri ta sauka daga jikinsa ta nufi toilet ɗin tana kuka. Sai da ta tsaya a banɗakin ta gama kukanta sannan ta wanko bakin ta fito,Ta zauna a gefe ta sunkuyar da kanta. Mug ɗin tea ɗin ya miƙo mata ya ce

“ki shanye tas kar ki rage min ko kaɗan.”

Kallon tea ɗin ta dinga yi fuska a yatsine, can dai ta kai shayin bakinta ta yi saurin ɗaukewa tana yarfe hannu ta ce

“zafi fa uncle.”

Kallon ta ya yi, sai kuma ya miƙa mata hannu, ta bashi shayin tana kallon sa. Doke hannunta ya yi ya jawota jikinsa ya karbi mug ɗin, bakinsa ya sa ya ɗan hura mata shayin sai kuma ya miƙa mata bakinta ya ce

“Haaa.”

Buɗe bakin ta yi ya fara bata, ko rabi bata sha ba ta ɗauke kanta ta ce“ni Allah na ƙoshi.”

“shanye ko na mareki”

Kamar zata yi kuka ta ce“na ƙoshi wallahi.” Ya ajiye mug ɗin akan tray ɗin sannan ya janyo plate ɗin soyayyen dankalin, Da kansa ya dinga bata shi ma har ta kusa cinyewa sannan ta ce“na ƙoshi.” bai ce komai ba ya ajiye plate ɗin yana kallonta ya ce“zo ki kwanta to.”

Kamar jira take ta rarrafa kan gadon ta yi kwanciyarta tana lumshe idanu. Ya ɗan kalleta sai kuma ya tashi ya fita hannunsa riƙe da tray ɗin, after 2mins ya dawo hannunsa riƙe da syringe, Ya zauna gefenta bayan ya ɓoye syringe ɗin a bayansa ya ce“dawo nan ki kwanta.” ya yi maganar yana nuna mata cinyarsa, Son jiki irin nata ya sanya ta taso ta ɗora kanta akan ƙirjinsa ta zagaye hannunta a bayansa ta rufe idanunta. Shiru ya yi yana kallon ta, sai da yaga ta fara bacci sannan ya zaro syringe ɗin, Ya sauke wandon jikinta ya saita allurar ya tsira mata. Wata irin ƙandarewa ta yi tana sakin kuka, Ta gasa masa cizo a ƙirji tana kuka. Murmushi kawai ya yi ya ɗauke syringe ɗin yana shafa kanta ya ce

“Sorry yi baccin ki.”

Bata ce komai ba, sai kukanta da take ƙasa-ƙasa dalilin baccin daya fara ɗaukanta, Shima ya yi shiru idanunsa a lumshe har bacci ya ɗauketa. Saukar numfashinta daya fara ji ya sanya ya ɗan kalleta, bacci take hannunta ɗaya a baki ta kwaɓe fuska, Ya girgiza kansa ya janyeta ya kwantar kan gadon sannan ya tashi ya rufeta da duvet. Ganin tana motsi ya sanya ya koma ya zauna, ta yi juyi sannan ta ci gaba da baccinta. Sauke numfashi ya yi sannan ya rage gudun ac ya juya ya fice daga ɗakin. Kai tsaye ɗakinsa ya nufa yana zuwa ya yi kwanciyarsa dan shima baccin yake ji.

****
It’s been a months da zuwansu New York, gaba ɗaya aiki yayi masa yawa. Kusan kullum baya shigowa gidan sai dare sosai, shiyasa basa wani ganinsa idan ba asuba ce ta yi ba. Ɓangaren Zahra abun nata kullum gaba yake, yau a zauna lafiya gobe ta tada balli. Shi dai baya biye mata, dan bama shi da lokacin tsayawa faɗa da ita. Nana ce kawai ki biye mata idan ta dawo daga makaranta baya nan su yi ta tashin hankali, Yau ma kamar kullum tana zaune a main parlourn tana chatting, Abdusammad ya sauko daga ƙasa yana kallon ta ya ce“baki shirya ba?” miƙewa ta yi tana kallon sa ta ce“kai nake jira fa.” Ya kalli Noor dake zaune kusa da ita ta yi shiru ya ce“zo” ta shi ta yi ta koma wajensa ta tsaya ya ɗauketa ya ce“me ki ke so?”

“Abbie chocolate zan ɗauko nida Afeefa da Sumshi”

Ya ɗan ware idanunsa yana murmushi ya ce“iyye iya su kaɗai zaki ɗaukowa?” ta gyaɗa masa kai tana kwanciya a jikinsa. Bai sake ce mata komai ba ya kalli Nana wadda ke sakkowa daga sama hannunta rike da jakarta. Ƙarasowa ta yi ta tsaya tana rike da wayarta ta ce

“uncle na gama.”

Okay ya ce sannan ya kalli Zahra ya ce“Madam muje.” Fuskarta a haɗe ta ce“ita kuma ina zata je?” ta yi maganar tana nuna Nana, Ɗauke kai Nana ta yi dan bata da lokacinta. Ya ɗan kalleta da mamaki ya ce“ina zamu je dai zaki ce”

“To ai naga dai yau ba kwananta bane ballantana ta bika unguwa. Dan Allah wallahi ba zata je ba!”

Zahra ta yi maganar tana zabgawa Nana harara. Kafin ya yi magana Nana ta ce“to ai sai ki hanani zuwan, wallahi sai naje”

Kallon su ya dinga yi ganin zasu fara halin nasu ya ce“kun ga ni babu wadda zata ɗaga min hankali. Naji ba kwananta bane, kenan idan ba kwananta bane ba zata bi ni wani waje ba?” gyaɗa masa kai Zahra ta yi ta ce

“Eh wallahi ba zata raka ka ba. Idan tana so aje da ita shopping ko wani waje sai ta bari sai ranar da ka ke daƙinta ku je, amma yau ranata ce nida ƴata Allah ba zata bimu ba.”

Taɓe baki Nana ta yi tana kallon sa taji me zai ce. Ya ɗan yi shiru can kuma ya ce“shikenan tunda abun haka ne, duk ku zauna an fasa zuwa. Da Noor kawai zan je”

“Ohho sai dai a fasa ɗin amma muddin dani wlh ba zata ba!”

Zahra ta yi maganar tana zama akan sofa, Nana ta kalleshi cike da masifa itama ta ce“to ai idan ka je da Noor kamar ka je da ita ne. Sai ka tafi kai kaɗai” Girgiza kansa ya yi ya ce“wannan ne kuma baku isa ba.!”

Daga haka ya nufi waje hannunsa riƙe Noor, Zahra ta mike tana kallon ta ta ce“kin ga ko? Ai ke baki isa ki na hana abu kuma ayi ba. Kuma wallahi kamr yanda na faɗa miki sai kin san kin auri mijina, sai kin yi dana sanin aurensa, wallahi duk wani abu dana san zai ƙuntata miki sai na saka shi ya yi sa, sai kin gwammace ace baki yi aure ba!”

Dakewa Nana ta yi duk da kukan dake neman kwace mata, ta zabga mata harara ta ce

“To idan kin fasa. Na auri mijin naki, na aure shin, kuma babu abin da ki ka isa ki yi min. Wallahi baki isa ba! Idan ma akwai wadda zata yi dana sani to ke ce bani ba, ke bare wadda ya auro ki daga waje. Wadda ta aure shi saboda kwadayin abun hannunsa, ke ce zaki fita ki bar ni a gidan nan. amma ni dai ƙarya ne na bar gidan nan saboda ke!”

Zahra ta dinga kallon ta ganin yanda take gasa mata magana, can ta yi kwafa tana matsowa kusa da ita ta ce

“Ai ko zan nuna miki ke baki isa ba, ni da ya auro ni a wajen na fiki ƙima da mutunci a wajensa. Ke da aka yi masa auren cushe? Ko an faɗa miki bamu san yanda aka yi bane? Ko kin manta? Ballagazar yarinya wadda ta gama zubar da mutuncinta a waje. Shashasha mai bin maza kawai! Wadda iyayenta basu bata tarbiyyar data kamata ba! Lalatacciyar yarinya wadda lalatattun iyaye suka haifeta!”

Tuni Nana ta fara hawaye, ta cakumi wuyan rigarta tana kallon ta ta ce“Ke kin isa ki zagar min iyaye! Wallahi ƙarya ki ke! Sai dai idan kece latattun iyaye suka haifeki! Ubanki da uwarki ki ke zagi ba dai nawa ba, Banza…”

Wasu zafafan maruka taji an sauke mata a both checks ɗinta, Ta haɗiye ragowar maganar ta dafe kuncinta tana jan numfashi. Tsananin azaba ya hanata koda kuka, ya fizgota daga jikin Zahran yana mata wani irin kallo fuskarsa a haɗe ya ce

“abin da ki ke yi kenan? Abokiyar wasanki ce ita? Sa’arki ce da ki ke yi mata haka? Zagi? Zagi Nana!?”

Zahra ta fara sharar hawaye tana kallon sa ta ce“gara da Allah yasa ka dawo ka gani yau a gabanka. Idan na faɗa maka ai nasan ba yarda zaka yi ba, kullum haka take min, kullum idan har baka nan ta dawo daga makaranta haka take zama tana zagina, ya za’a yi na jure? Nana fa? Ya za’a yi a ce Nana ke zagina! Ni fa…” .

Zahra ta fashe da kuka, Fuskarsa a haɗe take, idanunsa sun sauya kala, ko ba’a faɗa ba ka san ransa ya yi matuƙar ɓaci. Ya hankaɗeta yana kallon Zahran ya ce

“Muje!”

Jiki a sanyaye ta ɗauki wayarta tabi bayansa, Nana ta kasa ko da kallonsu saboda idanunta da suka ƙi buɗuwa. Sai da suka fita sannan ta zube a wajen ta saki wani marayan kuka, ban da raɗaɗi da azaba babu abin da fuskarta ke yi, ta daɗe a wajen tana dafe da kuncinta kafin ta tashi ta haye sama da gudu. Tana shiga daƙinta ta faɗa kan gado ta ci gaba da kuka kamar ƙaramar yarinya, Koda wasa bata yi tunanin zai mareta ba, bayan kuma ba laifinta bane..ita ta fara zaginta, Ta dunƙule jikinta waje ɗaya tana sake fashewa da wani sabon kukan, da gaske baya sonta, da gaske Zahra yake so. Nana ta ci gaba da kukanta tana dana sanin yarda da auren, dama bata dawo ba sanda ta garin gidansu Khadijah, dama ba gidan taje ba duniya ta shiga. Da babu wanda ya ganta, ta ci gaba da kukanta kamar ranta za fita. Tafi awa kwance a wajen kafin ta tashi ta zura slippers ɗinta ta shige toilet. A gaban madubi ta tsaya tana kallon fuskarta, gaba ɗaya shatin hannunsa ne akan fuskarta, Sai jini a gefen bakinta. Cikin kuka ta kunna sink ɗin ta tara hannunta ta ɗebi ruwan ta wanke bakinta sannan ta wanke fuskarta. Bayan ta gama ta fito ta koma ta kwanta tana kuka a hankali.

****
Anty Khadijah ce zaune kan sofa tana kallon Kaddu, Can ta ce“to ya za’a yi yanzu?” Kaddu ta ce“wallahi kin ga naje na karbo miki wannan maganin ma, wai ki saka ki a tea ki sha. Kina nan zaki gan shi ya zo har gidan nan” Anty Khadijah ta yi shiru kallonta kafin ta ce“to Zahra fa? Na yi magana da ita ta ce min wai tana shan maganin, to amma har yanzu ban ji ya saketa ba!” Kaddu ta yi murmushi ta ce“me ki ke ci na baka na zuba? Ai tunda aka ce miki zai saketa wallahi sai ya saketan. Kin manta yanda aka yi lokacin auren Siyama? Ai indai malam Garba ya faɗi abu to kamar ya faru ne.” Anty Khadijah ta ce“To shikenan, bani nasha yanzu ma.” Kaddu ta buɗe jakarta ta zaro ƙullin maganin ta miƙa mata. Tashi Anty Khadijah ta yi ta shige kitchen, Kaddu ta bita da kallo har ta fito hannunta riƙe da mug, a gabanta ta kwance maganin ta juye shi tas a ciki sannan ta saka spoon ta juya ta kafa kai ta shanye. Kaddu na murmushi ta ce“inda biyan buƙata?”

“Rai ba’a bakin komai yake ba!”

Anty Khadijah ta bata amsa, suka tuntsire da dariya a tare suna tafa hannu.

****
Siyama ta shigo ɗakin tana kallon sa, ajiye ledar hannunta ta yi ta ce“ko na kira maka Sultan ne?” Safwan dake kwance yana rawar sanyi ya girgiza mata kai, Ta zauna gefen gadon ta ce“to tashi ka sha maganin.” murya can ƙasa ya ce“Bani wayata”

Siyama ta juya ta ɗauko wayar dake kan drawer ta miƙa masa. Dakyar ya tashi zaune ya jingina da jikin gadon, Ya yi dialing numbernsa, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga. Abdusammad da ke zaune kan kujera ya ce

“Safwan ya jikin?”

Madadin ya bashi amsa sai kawai ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro. Abdusammad ya tashi tsaye hankali a tashe ya ce

“mene ne? Me ya faru?”

“Yayaaa…”

Ya kira sunansa cikin kuka.

“Na’am Safwan.”

Ya amsa a sanyaye, Safwan ya ja numfashi ya sauke ba tare da ya yi magana ba. Abdusammad ya sake cewa“ina jin ka, me ya faru?”

“Yaya mutuwa zan yi. Wallahi mutuwa zan yi, dan Allah ka zo kaji”

Girgiza kai Abdusammad ya yi sanin halin rakinsa ya ce“Ban son raki fa. Wane ya ce maka cuta mutuwa ce? Ka nutsu, zan saka a shirya maka Flight, zuwa next week sai ka tawo”

Safwan ya ja numfashi sannan ya ce

“Allah Yaya mutuwa zan yi, ka zo kafin na mutu.”

Tsaki Abdusammad yayi ya ce

“ranka zai ɓaci Safwan, kai ƙaramin yaro ne?”

Murmushin ƙarfin hali Safwan ya yi ya ce

“to shikenan Yaya.”

“kana shan maganin dai yanda ya kamata right?”

Safwan ya gyaɗa masa kai kamar yana gabansa sannan ya ce

“Eh ina sha.”

Abdusammad ya jinjina kansa ya ce

“ka ci gaba da sha to, idan na koma gida zamu yi waya.” To kawai Safwan ya ce sannan ya kashe wayar, Siyama ta dinga kallon sa sai kuma ta yi murmushi ta ce

“Ji yanda ka ke kwaɓe fuska”

Harararta ya yi ya ce“dan baki san ciwon da nake ji ba” yanda ya yi maganar ya sanyata dariya, Ta ce“ka ganka kuwa?” Ya dauke kansa yana sakin ajiyar zuciya.

****
Basu dawo gidan ba sai wajen 8:00 na dare, Ya miƙa mata Noor dake bacci ya ce“Kai ta ɗaki ina zuwa.” Karɓarta Zahra ta yi tana murmushi ta ce“ina zaka je?”

“fita zan yi.”

Ya yi maganar yana juyawa. Zahra ta kalli security ɗin da ya shigo da kayayyakin da suka siyo, Ya ajiye a parlourn sannan ya fita. Sama ta nufa tana rike da Noor, Ta kwantar da ita akan gadonta sannan ta zare mayafin jikinta ta nufi toilet, Bayan ta fito ta zauna gefen gado dan already sun yi sallah a masallaci. Numbern Anty Khadijah ta yi dialing bayan ta ɗaga ta ce

“Anty Ya gida?”

Anty Khadijah dake kwance kan gadonta ta yunƙura ta tashi zaune tana cewa

“Zahra muna nan kalau”

Zahra ta jinjina kanta tana murmushi ta ce

“Anty daman kiran ki nayi na faɗa miki wallahi maganin da ki ka bani yana aiki. Yau dana sake sha da safe kin ga ɗazu a gabana ya mareta har sau biyu, kuma yanzu ma da muka dawo ko nemanta bai yi ba.” Anty Khadijah ta yi murmushi ta ce“to bana faɗa miki ba daman? Yanzu zaki ga ko kwana daƙinta ba zai dinga yi ba, ballantana ki ji ance tana da ciki.” Zahra ta ɗan yi dariya ta ce

“to ai Anty babu abin da ya taɓa shiga tsakaninsu fa, shi har yanzu baya yi mata kallon matarsa.” Anty Khadijah ta yi shiru kamar mai nazari can kuma ta ce

“amma kina ganin haka babu matsala Zahra?”

Zahra ta ɗan girgiza kai ta ce“eh babu matsala mana Anty, kin ga ai bani da damuwar ko ta samu ciki ko wani abu. A haka har ta gaji ta saka ya saketa”

Anty Khadijah ta sauke numfashi ta ce“haka ne kuma. To Allah ya sake rufa asiri”

Zahra ta yi murmushin jin daɗi ta ce“amin Antyna. Ki gaida su Umma”

“Ba zaki kirata ba?”

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“kin san halin faɗanta. Yanzu idan nayi kiranta ba zata bari mu yi hira ba zata fara min wa’azi kawai na kirata gobe.”

“Oh ku dare ne ko? To Allah ya kai mu” da Amin ta amsa sannan ta kashe wayar, Zahra ta ajiye wayar gefenta ta yi shiru tana tunani, ita kaɗai kuma ta fara murmushi saboda tunawa da abin da Abdusammad ɗin ya yiwa Nana.

****
Nana na zaune gefen gado Around 9pm taji an fara knocking ƙofar, Ta ɗaga kumburarrun Idanunta ta kalli ƙofar sai kuma ta sauke kanta. Tana jin sa har ya gaji ya bar jikin ƙofar, Ta koma ta kwanta ta fashe da wani sabon kukan, yini ta yi tana kuka. Takaici ya hanata yin shiru, Ta jima a haka kafin ta tashi ta shiga banɗaki, ta wanko fuskarta ta dawo ta zauna gefen gadon ta zuba uban tagumi. Abdusammad kuwa yana barin jikin ƙofar ɗakin Zahra ya nufa, Ya sameta zaune ta sauya kaya zuwa na bacci da alama wanka ta yi, tana ganinsa ta fara murmushi. Babu yabo babu fallasa ya ce

“Zahra mene ya haɗa ki da Nana ɗazu?”

Da ɗan mamaki take kallon sa, Ya ɗaga mata gira ya ce“Eh. Mene ya yi causing faɗan naku?”

Zahra ta ɗan juya Idanunta kafin ta ce“amma kusan a gabanka aka yi komai doctor, babu abin da nayi mata. Kawai daga muna magana akan fitar shi ne fa ta fara zagina, kuma ai ba yau suka fara min irin haka ba. Duk ƙannenka sun raina ni”

“Kina nufin baki ce mata wani abu mara daɗi ba?”

Ya yi tambayar yana kallonta. Zahra ta girgiza kanta ta ce“babu abin da na ce mata, yama za’a yi na tsaya ina faɗa da Nana?”

Numfasawa ya yi ya girgiza kansa ya ce“To bana son kina biye mata, ke da kan ki kin san yarinya ce. Kuma kin san halinta ba tun yau ba, Nana ba son zaman lafiya take ba, dan haka duk abin da zata yi kada ki sake biye mata.”

Rau-rau ta yi da idanu kamar zata yi kuka ta ce“kenan goyan bayanta ka ke?”

Wani irin kallo ya watsa mata wanda ya sanyata sunkuyar da kanta. Ya tako har gabanta yana kallonta fuska a ɗaure ya ce

“Babu wadda nake goyan baya a cikin ku. Ku duka matana ne, kuma duk wadda ta yi ba dai-dai ba zan mata magana. So behave ur self”

Zahra ta yi shiru har sannan bata ɗago kanta ba, Ya juya ya fice daga daƙin. Taɓe baki ta yi sannan ta yi kwanciyarta.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *