Chapter 4: Chapter 4
“Ya aka yi ki ka sani?”
Cewar Maimoon a sanyaye, taɓe baki Hameeda ta yi ta ƙaraso ta zauna kan drawer sannan ta ce”Mama fa nace miki, wane bai san halin faɗanta ba”
“Ai wallahi shiyasa nake tsoron zuwa wajenki, ta dinga faɗa” cewar Nana fuska a haɗe, ɗan murmushi Hameeda ta yi ta ce”sorry love, na ganku da dare?” Maimoon ce ta ƙaraso ta miƙa mata ledar tana cewa”waya Abba ya kawowa Nana, shi ne muka zo nuna miki fa” waro idanu ta yi tana karɓa ta ce”woww masha Allah, gaskiya na taya ki murna, ke Nana”
Nana ta ɗan juya Idanunta tana murmushi ta ce”ke dai bari, yau ji nake kamar ba zan iya bacci ba.” Hameeda ta ɓare ledar kwalin tana faɗin “sanda zaki yi baki sani ba, ranar da Yaya Hameed ya kawo min wayata haka naji” Maimoon ta ce”ki ka dinga dariya ba, ranar mun kusa haukacewa”
“Yauwa ai har pictures ɗinmu zaki turan dana Aun”
Nana ta faɗa tana janyo wayar Hameeda dake ƙasan pillow. Hoton Sultan ne akan screen ɗinta, yana sanye da kayan likitoci a airport ya yi murmushi, iyaka haɗuwa da kyau hoton ya haɗu. Nana ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, Maimoon ce ta lura ta taɓa ta tana cewa “what are you looking ne?” saurin ɗauke kanta tayi tana ɗan murmushi ta ce”hoton masoyin naki ki ka saka a screen?” Ta ƙare maganar tana kallon Hameeda.
Fizge wayarta ta yi tana harararta ta ce”ina ruwanki da wayata?” dariya Nana ta yi tana kallonta ta ce”haba dai daga naga hoto? Maimoon ki faɗawa Yaya Sultan wallahi Hameeda na ƙaunarsa”
Maimoon ta yi murmushi tana leƙa wayar Hameedan kafin ta ce”ikon Allah wayyo love! Nana kin ga wata ƙauna” tuntsirewa suka yi da dariya, Hameeda ta yi shiru tana kallonsu fuskarta a haɗe kamar ta fashe da kuka, sai da suka yi mai isarsu sannan suka yi shiru, ita dai ta ci gaba da buɗe wayar Nana duk da yanda take jin wani iri a ranta. Da kanta ta haɗa mata komai dan har da sim card a ciki, ta sai ta mata icloud sannan ta tura mata duk pictures da videos nasu, sai wajen 9:20pm sannan suka bar gidan kowa ya nufi hanyar gidansu. Koda taje gida bata ga kowa a parlon ba, dan haka ta shige ɗakinta ta rufe ƙofar, ajiye wayar ta yi a gaban drawer sannan ta shige toilet. Tana fitowa daga wanka ta shirya a gurguje sannan ta nufi kan gado ta kwanta tana riƙe da wayarta, kalle-kallen hotunan ta dinga yi har wajen goma saura, sannan ta shiga WhatsApp ɗin da Hameeda ta buɗe mata. Hira ta ɗan yi da few friends nata ana ta yaushe rabo, sun daɗe suna magana da Khadijah kafin ta fara jin bacci dan ta saba da wuri take kwanciya. Dan haka suka yi sallama ta kashe datar ta ajiye wayar gefen side drawer sannan ta kwanta abin ta..
Washegari ya kasance juma’a ce dan haka bata tashi da wuri ba, around 9 na safe ta fito parlon hannunta riƙe da wayarta tana dannawa tana murmushi. Abba ne zaune a parlon sai Sultan da shigowarsa kenan bayan kiran da Abban ya yi masa, sam bata lura dasu ba, dan hankalinta gaba ɗaya na kan wayarta saboda hirar da suke da Khadijah. Amma ta fito daga kitchen hannunta riƙe da ɗan madaidaicin tray me ɗauke da kayan tea, kallonta ta dinga yi har ta ajiye tray ɗin sannan ta kalleta ta ce”Nana!”
Da sauri ta ɗago kanta ta kalli Amman sai kuma ta ce”morning Amma”
“Baki da kayan kasawa ne?”
Amma ta yi tambayar, kallon kayan jikinta ta yi wata armless vest ce a jikinta sai wando wanda bai shige gwuiwarta ba, masu kala ɗaya, kanta ko ɗankwali babu dogayen kitson kalbar ya sakko kan kafaɗunta.
“Tambayarki nake”
Murya a ɗan shaƙe ta ce”a..ai daman yanzu zan sauya kaya”
Harararta Amma ta yi sannan ta nufi hanyar kitchen abinta, tura baki ta yi tana shirin komawa ɗakin Abba ya kira sunanta, dawowa ta yi ta ƙarasa parlon tana kallonsa ta ce”morning Abbana” murmushi ya sakar mata yana jan hannunta ya ce”morning daughter kin tashi lpy?” Sai da ta zauna a kusada shi sannan ta ce”Alhamdulillah, jiya kwana nayi ina tunanin wayata Abba” ya girgiza kansa jin zata fara shirmen ya ce”baki ga yayanki ba?” Sai a sannan ta ɗago kanta ta kalleshi, zaune yake kan sofa sanye da sport wear, ta ɗan tura baki murya can ƙasa ta ce”morning Ya Sultan” babu yabo babu fallasa ya ce”morning ykk?”
“Alhamdulillah”
Ta faɗa tana mai da Idanunta kan Abba ta ce”Abba dan Allah zan je gidan Aunty Ramlah an jima” shiru Abba ya yi yana kallonta can kuma ya ce”har kin ji sauƙi ne?” saurin gyaɗa masa kai ta yi ta ce”Eh naji sauƙi Alhamdulillah” numfasawa ya yi kana ya ce”shikenan Allah ya kaimu” murmushi ta yi tana kallonsa ta ce”Amin thank you Abba” murmushin shima ya yi sannan ya ce”ki shirya idan Sultan zai fita sai ya yi dropping ɗinki” da sauri ta kalleshi lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke, murya a sanyaye ta ce”Abba ba kai zaka kai ni ba?” jan kumatunta ya yi ya ce”i have alot to do Nana, kuma kin ga next week zan je Abuja dole nayi covering abubuwan da ke gabana” langwaɓar da kai ta yi ta ce”ayyah to Abba kawai sai na hau napep, na hutar da Yaya” girgiza kansa ya yi ya ce”a’a Sultan zai tafi dake”
Tura baki ta yi ta ce”amma Abba…”
“Nana!”
Ya kirata a ɗan tsawace, sunkuyar da kanta ta yi sanin halinsa ta ce”I’m sorry” fuska a haɗe kamar ba shi ba ya ce”tashi ki tafi” bata sake cewa komai ba gudun kada ya hanata ta tashi ta nufi ɗakinta a sanyaye..sai da ta bar wajen sannan ya kalli Sultan ya ce”dan Allah kar ka bari ta tafi ita kaɗai” murmushi ya yi ya ce”in sha Allah Abba” okay Abba ya ce sannan Sultan ya mike dai-dai nan Amma ta fito daga kitchen riƙe da wani tray, ganin yana shirin tafiya ya sanya ta ce”a’a kai what do you mean?” Shafa kansa ya yi yana ɗan murmushi y ce”tafiya zan yi Amma” harararsa ta yi ta ce” zauna ka yi breakfast my friend!” Ganin yanda ta haɗe rai babu alamar wasa ya sanya ya koma ya zauna ba dan yaso ba, ta yi serving ɗin su shi da Abba suka yi breakfast ɗin..
Tun da ta koma ɗaki take kwance tana yan matan hawaye, koda wasa bata son bin sa, to amma kuma tana son taje gidan Aunty Ramlah ko dan alƙawarin da ta yiwa Junaid, haka ta dinga tunane-tunanenta har wajen ƙarfe 11 na safe, sannan ta tashi ta nufi toilet, wanka ta yi ta shirya cikin wata atampa glitter mai coffee and pink, ɗinkin t-boubou da straight skirt, ta yi ɗaurin ture kaga tsiya wanda ya yi mata kyau sosai atampar ta haskata sosai. Kallon kanta ta yi a madubi sai kuma ta dauki eye pencil ta yi zagayen baki dashi, sannan ta saka a idonta ta shafa lip gloss nan take ta zama wata babbar mace mai aji da kyau, pink ɗin dan kunne da sarka ta saka sannan ta yafa coffee ɗin mayafi, ta dauki handbag coffee da takalmi golden ta saka. Sosai ta yi kyau abin ta kamar sabuwar amarya, ta ɗauki wayarta sannan ta fito parlon lokacin 12 na rana ta kawo kai, zaune ta sami Amma tana karatun Alkur’ani, tana ganinta ta rufe qur’anin kana ta ce”tun yanzu zaki tafi?” gyada mata kai ta yi ta ce”Eh haka Abba ya ce da wuri zai yi dropping ɗina, idan ya dawo sai ya biya ya ɗaukoni” Amma ta ce”to ki gaisheda Ramlam kuma kar ki kai dare” to kawai ta ce sannan ta nufi waje da sauri.
A compound ɗin ta iske Maimoon tana watering flowers tana ganinta ta ajiye butar tana murmushi ta ce”Hajiya Nana duniyar ƙawa, ina kuma zaki je haka?” She just roll her eyes sai kuma ta ce”gidan Aunty Ramlah zan je” Maimoon ta dinga kallonta sai kuma ta ce a hankali “wajen sir Junaid zaki je?” gyaɗa mata kai ta yi cikin raɗa ta ce”Eh zai zo can sai mu haɗu” Maimoon ta girgiza kanta ta ce”Nana baki tsoron abin da zai je ya dawo?” Taɓe baki ta yi ta ce”ni babu abin da nake tsoro in dai zan haɗu da sir Junaid ai shikenan” ƙarar buɗe ƙofar da suka ji shi ya hanata magana, a tare suka juya suna kallon wajen, Sultan ne ya fito, yana sanye da wani yadi mai shara-shara ɗinkin riga da wando, ya ɗora hula akansa idanunsa maƙale cikin shade glasses. Daga ganshi kaga rich and classic guy, ya ƙaraso wajen cikin takunsa na isa. Nana ta kalli Maimoon sai kuma ta ce”sai na dawo”
“Dashi zaku tafi?” Ta gyada mata kai. Fuska a haɗe kamar koda yaushe ya ce”sai nace ki zo mu tafi?” tura baki ta yi sannan ta yi gaba, ya bita da harara sai kuma ya yi gaba shima yana amsa addu’ar Maimoon..
Har suka fita daga cikin estate ɗin babu wanda ya ce uffan, ganin ya ɗauki hanya ya sanya ta ɗan ƙara sauri har ta cimmasa, murya a sanyaye ta ce”Yaya ina motar to? Nifa nagaji”
Hannunta ya riƙe cikin nasa ba tare da ya kalleta ba ya ce”mota, wace motar? Ai a ƙafa zamu tafi!”
Cak ta tsaya tana kallonsa da mamaki, shi kuwa ya haɗe ransa ya ce”mene haka?” kwantar da murya ta yi ta ce”Haba Ya Sultan sai ƙafata ta yi ciwo ai, dan Allah ka ɗauko motar ka ko ta tsaida mana napep” Sultan ya zare glasses ɗin idanunsa yana kallonta fuska a haɗe ya ce”ni nace ki lalata min mota da ƙazanta? To ba’a kawon daga car wash ba, saboda haka let’s go malama!” Muryarta na rawa ta ce”amma Yaya…”
“Shhhhhh!”
Sultan ya faɗa bayan ya ɗora hannunsa bisa bakinsa, kasa cewa komai ta yi amma tuni idanunta suka sauya kala, ya riƙe hannunta suka ci gaba da tafiya. Har suka zo babban titi bai ce komai ba, ita dai binsa kawai take duk da yanda take jin ƙafafunta kamar zasu ɓalle. Ganin suna shirin tsallaka titi ya sanya ta rikeshi da ɗaya hannun nata, juyowa ya yi yana kallonta sai kuma ya ce”lafiya dai?”
Cikin shassheƙar kuka ta ce”dan Allah Yaya Sultan ka samar mana napep, ko kuma ka maidani gida nagaji” harararta ya yi ya ce”ba zan yi ba” daga haka ya ja hannunta suka tsallaka titin. Ci gaba da tafiya suka yi, tana tafe tana gudu-gudu saboda yanda yake tafiya cike da zafin nama. Ana kiran sallar ƙarfe 1:00 na rana suka ƙaraso gaban wani babban masallacin juma’a, kallonta ya yi ya ce”zo ki zauna acan nayi sallah sai mu ci gaba da tafiya” saurin gyaɗa masa kai tayi dan daman neman wajen hutawa take. Sai da ya rakata har wajen data zauna sannan ya ce”kar ki kuskura ki bar nan, kuma kar ki kula kowa” gyaɗa masa kai ta sake yi, ya juya ya nufi cikin masallacin. Lumshe idanunta ta yi ta jingina da kujerar hawaye na zubowa kan kuncinta, iyaka azaba yau Sultan ya gana mata, bata saba tafiya irin haka a ƙasa ba, dan duk inda zasu je kai su ake yi.
Tana nan zaune har aka idar da sallar mutane suka fara fitowa, ta dinga bin su da kallo a ƙoƙarinta na son ganin Sultan, sai dai har bayan mintuna ashirin babu shi babu dalilinsa. Nana ta sauke idanunta kawai ta fashe da kuka, to ko dai tafiya ya yi ya bar ta anan? Wani ɓangare na zuciyarta ya sanar da ita hakan. Kawar da tunanin ta yi dan tasan ba zai tafi ya bar ta ba, ta ci gaba da kallon harabar masallacin tana jiran tsammanin fitowarsa. Ƙarfe 1:43pm ya ƙaraso wajen hannunsa riƙe da wayarsa, sam bata lura dashi ba dan idanunta a rufe suke tana faman hawaye. Ɗan murmushi ya yi sai kuma ya ce
“Nana!”
Da sauri ta ɗago bayan ta buɗe idanunta, kallonsa ta dinga yi amma bata ce komai ba. Gaba ɗaya ta birkice kamar ba ita taci kwalliya ta fito daga gida ba, ɗankwalin kan nata ma tuni ya kwance. Fuska a sake ya ce”kin yi sallah?” Girgiza kanta kawai ta yi, ya ce”but why? Ko baki yin sallar?” ɗago idanunta ta yi suka haɗa ido ta sauke nata ba tare da ta ce komai ba. Sarai ya san da bata sallahr amma ya tambayeta, jin tayi shiru ya sanya ya ce”ina magana da statue ne Nana?”
“Bana yi!”
Ta ce a takaice, murmushi ya yi sai kuma ya ce”alright, tashi mu tafi” dakyar ta miƙe saboda yanda ƙafafunta suka kumbura, ya riƙe hannunta suka bar wajen. Suna fitowa daga gate ɗin taga ya nufi wajen motarsa, ta dinga kallon baƙar motar da ke kyalli, ashe daman da motar ya zo? To ko yanzu aka kawo masa? Ta yi tambayar a zuciyarta..
“Shiga mana”
Maganar Sultan ta katseta. Bata ce komai ba ta buɗe murfin ta shiga front seat tana sauke numfashi, juyawa ya yi ya shiga driver seat sannan ya yiwa motar key ya yi reverse suka bar wajen. Har suka je Gimba road babu wanda ya ce wani abu, Nana sai faman matsa ƙafarta take tana runtse ido, ta gefen ido ya kalleta ba tare da ya ce komai ba. A No.34 state lowcost ya yi parking, daidai wani ƙaton gida, sai a sannan ya juyo ya kalleta ganin yanda take riƙe da ƙafar yasa ya ce”mene ne?” Jin yanda ya yi maganar cike da kulawa ya sanya ta saki jikinta a ɗan shagwaɓe ta ce”Yaya Sultan ƙafata zata cire zafi take min!” Ta ƙare maganar tana yarfe hannu, kallon ƙafafun ya yi sai kuma ya ce”to ko za ki shafa man zafi?” saurin gyaɗa masa kai ta yi, ya zaro kwalbar aboniki daga aljihunsa ya miƙo mata. Karɓa ta yi sai kuma ta ɗago ƙafafun nata tafara janye skirt ɗin, fararen ƙafafunta suka bayyana, Sultan dai sai kallonta yake ba tare da ya ce komai ba. Sai da ta buɗe cealing ɗin jikin kwalbar sannan ta cire murfin, ƙoƙarin shafawa ta fara yi amma sai taji gaba ɗaya ta matsu saboda yanda ta yi da ƙafafun nata, ɗago kanta ta yi ta kalleshi murya a sanyaye ta ce”Yaya ko zaka shafa min?”
“Baki da hannu ne?”
Langwaɓar da kanta ta yi kamar zata yi kuka ta ce”i can’t ne” bai sake cewa komai ba ya amshi kwalbar yana kallonta, saurin ɗoro ƙafafun nata ta yi tana shirin sauke su kan cinyarsa, ganin irin kallon da yake mata ya sanya ta ce”can i?” tsaki y yi ya jawo ƙafafun ya ɗora kan cinyarsa sannan ya fara shafa mata man a hankali yana bin ko ina yana shafawa, lumshe idanunta ta yi ta buɗe tana kallonsa, ɗago kansa ya yi ya kalleta ta yi murmushi tana dauke kanta, murmushin shima ya yi ya janye ƙafafun yana girgiza kansa. Sauke skirt ɗinta ta yi ta ɗauki jakarta tana kallonsa ta ce”Yaya na jiraka?” gyaɗa mata kai ya yi ta buɗe motar ta sauka tana ɗaga masa hannu, sai da yaga ta shiga cikin gidan sannan ya sauke zazzafan numfashi, gaba ɗaya ji ya yi wata irin kasala ta rufe shi, ya ɗan jima a wajen kafin ya yiwa motar key ya bar kofar gidan..
****
Nana ta dinga kallon Inteesar tana murmushi ta ce”ina Aunty take?” yarinyar da bazata shige 10yrs ba ta ce”tana ɗakin Daddy” okay Nana ta ce sannan ta gyara zamanta kan sofa ta maida idanunta kan tv inda ake haska wani cartoon a MBC 3, after 5mins sannan Aunty Ramlah ta buɗe ƙofa ta fito, washe baki ta yi tana kallonta ta ce”Nana ce a gidan?” murmushi ta yi tana kallonta ta ce”eh auntie ina yini?” Sai da ta zauna kan kujera sannan ta ce”lafiya kalao, Ya Amma?”
“Tana nan klao Aunty, ta ce na gaisheki.” Aunty Ramlah ta mike ta ce”ina amsawa” daga haka ta nufi kitchen, drinks ta kawo mata ta ajiye kan table ta ce”drink it Ina zuwa” okay kawai Nana ta ce, ta juya ta koma kitchen. Kunun aya ta ɗauka ta sha tana lumshe ido, ta gaji sosai kuma ga yunwa da take ji, wayarta ta zaro a jakarta ta kunna taga 3missed calls da wata number, tashi ta yi tana kallon Inteesar ta ce”bari naje toilet” okay ta ce sannan ta nufi hanyar ɗakinta ta shiga. Sai da ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta shiga dialing numbern, ringing biyu aka ɗauka daga ɗaya ɓangaren ya ce
“Nana you keep me waiting”
Ƙasa ta yi da muryarta ta ce”sorry, ina gidan yaushe zaka zo?”
Sir Junaid dake kwance kan gadonsa ya ce”zuwa 4 ya yi?”
Gyaɗa kanta ta yi kamar tana gabansa sai kuma ta ce”Eh nima yanzu nazo, zuwa sannan naci abinci na huta” okay ya ce sannan ta kashe wayar. Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon screen ɗin wayar sannan ta juya ta fice daga ɗakin.
Zaune ta sami Aunty Ramlah tana magana da Inteesar, ta ƙarasa ta zauna gefenta ta jingina daga jikinta, murmushi Aunty Ramlah ta yi ta ce”to mage sarkin son jiki, ni kar ki tausheni” a shagwaɓe ta ce”nagaji ne fa, Yaya ne ya sanya nayi tafiya a ƙafa”
“Wane yayan?”
“Yaya Sultan mana” cewar Nana. Aunty Ramlah ta gyaɗa kanta ta ce”shi ne ya kawo ki?” she just nodded her head tana sake narkewa a jikin aunty Ramlah, murmushi ta yi ta ce”to ko dai dashi za’a yi ne Nana?” saurin tashi zaune ta yi tana cewa”Allah ya kiyaye ni bana son sa” yanda ta yi maganar ya sanya Aunty Ramlah dariya sai kuma ta ce”to mene ne aibunsa? Sultan me hankali da nutsuwa, Ni zan iya cewa duk cikin samarin shuwa babu wanda ya kai shi” taɓe baki Nana ta yi ta ce”taɓ! Me zan yi dashi, mugu ne wallahi” harararta Aunty Ramlah ta yi ta ce”to ai duk wannan yanzu ne, kuma kin san ma’anar namiji ya dinga yi miki mugunta?” Shiru Nana ta yi sai kuma ta girgiza kanta, Aunty Ramlah ta gyara zama ta ci gaba da fad’in “idan har ki ka ga kuna zaune da namiji yana miki mugunta ko kuma yana takureki fiye da sauran yan uwanki that’s means yana da feeling akan ki, yana sonki ne. Kuma na fahimci haka a gurin Sultan” tura baki Nana ta yi ta ce”nifa Aunty ba haka bane, babu abin da zai haɗani da Yaya Sultan yaje can inda ake sonsa” murmushi kawai ta yi ta ce”ai shikenan, naji watarana kin cemin kina sonsa”
“Har abada ma wallahi” ta ƙare maganar tana tashi daga wajen.
****
Zaune suke cikin parlon kowa ya bada full attention ɗinsa zuwa ga abin da take cewa, Hajiya Babba ta sauke numfashi sannan ta ci gaba da faɗin
“Yanzu na riga da na yanke hukunci akan yanda za’a yi, idan kuma kuna ganin hakan bai yi ba sai a sauya”
Alhaji Kabir ya yi murmushi sannan ya ce”ai babu wani sauyi Hajiya, hakan ma ya yi Allah yasa haka ne mafi alkhairi ya kuma kai mu lokacin” Amin ta ce sannan ta maida idanunta kan Abba ta ce”kai fa Alhaji?” girgiza kai Abba ya yi fuskarsa ɗauke da mabayyanin murmushi ya ce”Alhamdulillah Hajiya, hakan ya yi dai dai, Allah ya kai mu da rai da lafiya ya kuma basu zaman lafiya” duka kowa ya ce Amin. Mama ta ce”to yanzu zuwa yaushe za’a saka kenan?” Hajiya Babba ta gyara zamanta sannan ta ce”ai wannan yana wajensu, ni dai nagama nawa”
Daddyn su Sultan wato Alhaji Kabir ya ce”i think zamu fara magana da yaran sai aji yaushe za’a tsaida, but before that yaushe Arɗo zai dawo? Akwai buƙatar ayi komai a gabansa”
Abba ya jinjina kai sannan ya ce”haka ne, in sha Allah zan masa magana ya sanya rana ya dawo, zaman ya isa haka”
Hajiya Babba ta ce”to wata kila ku yaji maganarku, amma na saka Aliyu ya masa magana ya ce masa wai yana da abubuwan yi ne dayawa acan” murmushi Abba ya yi ya ce”Allah sarki ai yana ƙoƙari sosai, amma duk da haka zai zo in sha Allah” Mama ta ce”Allah ya yarda ya kuma nuna mana” Amin suka ce sannan kowa ya tashi ya watse, Hajiya Babba ta sauke numfashi tana fatan wannan haɗin da ta yi ya zama mai albarka.
****Around 5:20 na yamma wayarta ya fara ƙara, tana zaune gefen closet ɗin Inteesar tana gyara mata kaya, ta daga idanunta tana kallon wayar da ke kan drawer, rigar da ke hannunta ta ajiye sannan ta tashi ta ɗauki wayar, ɗagawa ta yi kafin ta yi magana taji ya ce
“I’m outside”
Okay ta ce sannan ya kashe kiran, ta ɗan yi jim sai kuma ta sauke nunfashi ta koma ta ƙarasa kwashe kayan. Mayafinta ta ɗauka ta yafa bayan ta ɗan gyara fuskarta ta fito parlon, Inteesar ce kawai zaune tana game a tap ɗinta, Nana ta kalleta ta ce”Intee ina Mom?” Inteesar da idanunta ke kan tv ta ce”tana ɗaki bacci take” Ajiyar zuciya Nana ta sauke tana godiya ga Allah a ranta, a fili kuma ta ce”to bari naje na siyo recharge card kin ji” gyaɗa mata kai kawai tayi dan gaba ɗaya hankalinta na kan kallon da take, Nana ta fice daga parlon da sauri. Babu kowa a compound ɗin dan haka ta ƙarasa har wajen gate, ganin da gaske babu wanda ya shigo ya sanya ta fita daga waje ta tsaya, wayarta ta ɗago ta yi dialing numbernsa bugu ɗaya ya ɗauka murya a sanyaye ta ce”na zo ban ganka ba” sir Junaid da ke bayanta ya ce”gani a bayanki” da sauri ta juya tana kallon bayan nata. Tsaye yake jikin motarsa Camry yana sanye da wata shadda fara tas ɗinkin jamfa, ya ɗora hular zanna bukar akansa, sai kallonta yake hannayensa naɗe a ƙirji. Kallonsa ta dinga yi ko kiftawa babu ya yi mata kyau matuƙa, ta ƙarasa wajen har sannan bata dauke idanunta daga kansa ba, shima kuma kallonta yake dan ba ƙaramin kyau tayi masa ba. Sunkuyar da kanta ta yi a sanyaye ta ce”ina yini?” bai amsa ba sai gyara tsaiwarsa da ya yi yana kallonta ya ce”sorry na taso ki Nana” ɗan murmushi ta yi ta ce”babu komai sir” haɗe fuska ya yi ya ce”bana son wannan sunan” da sauri ta kalleshi sai kuma ta sake mai da kanta ƙasa ba tare da ta ce komai ba. Sun daɗe a haka kafin ya numfasa ya ce”kin san me yasa nace mu haɗu?” Girgiza masa kai ta yi ya gyaɗa kansa kana ya ce”good, ina son mu san abin yi ne Nana, ina son na san ta hanyar da zan iya mallakar ki, wallahi tallahi ina sonki Nana! Ina ƙaunar ki! Amma naga kamar ke baki gane hakan ba, yarinta ta hana ki fahimta”



