Chapter 40: Chapter 40
Koda ya fita ɗakinsa ya shiga, Ya duba keys ɗin ɗakunan ya zari guda ɗaya. Yana zuwa ya saka key ɗin ya murɗa, cikin sa’a kuwa yaji ya buɗe dan ba’a jiki ta bar keyn ɗin ba, Sam Nana bata ji alamun buɗe ƙofar ba saboda kukan da take. Sai mutum ta gani a gaban gadon, Ta yi saurin tashi zaune, ta koma can ƙarshen gadon ta dunƙule jikinta waje ɗaya. Kallon ta ya dinga yi sai kuma ya zauna gefen gadon, murya a sanyaye ya ce
“Ke zo nan..”
Sake matse jikinta ta yi tana kuka a hankali, Ya sake kiran sunanta ta yi masa banza. Ganin yana nufota ya sanya ta sauka ta ɗaya side ɗin gadon. Ya dinga kallonta lokaci ɗaya ya haɗe ransa ya ce
“Baki ji me nace bane? Zo nan!”
Ya daka mata tsawa. Sosai ta firgita amma hakan bai sa taje inda yake ba, Ta fara tafiya hankali da niyyar fita daga dakin, Cikin yan sakanni ya tashi ya fizgota ta faɗa jikinsa. Kokawar kwace kanta ta dinga yi, sai dai sam ta kasa, saboda ba ƙarfinsu ɗaya ba. Ya matseta a ƙirjinsa yana watsa mata wani irin kallo ya ce
“Kin nutsu ko sai na sake marin ki?”
Ci gaba ta yi da kokawarta tana kuka kamar ranta zai fita, Komawa ya yi ya zauna har sannan bai saketa ba. Ya sanya hannunsa ya rufe mata baki sannan ya ce
“Ki nutsu ki faɗa min me ya faru. Me ta yi miki? Akan me ki ka zageta…”
Ya saki bakinta yana janyeta daga jikinsa, Tashi tsaye ta yi tana kallon sa cike da masifa ta ce
“Bazan nutsun ba, kuma ba zan faɗa maka ba ɗin! ai sanda ka mareni baka tambayi me ya faru ba. Ko ce maka aka yi banida hankali? To wallahi ba zan yarda ba, kuma sai na tafi gidanmu. Wallahi sai na faɗawa Abbana!…”.
Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan, da mamaki ya dinga kallonta dan tun da yake da ita bata taɓa faɗa masa magana irin haka ba. Ya miƙe tsaye yana kallonta ya ce
“Ni? Ni ki ke cewa ba zaki nutsu ba? Ni ki ke yiwa ihu aka?”
Ɗora hannayenta ta yi akan ƙugunta tana kallon sa idanunta babu alamar shakka ko tsoro ta ce
“Eh kai ɗin!”
Wani irin gudu ta saka ganin ya yo inda take, ta shige banɗaki ta murɗa key ɗin ta bar shi a jiki. Tsayawa ya yi a wajen yana kallon ƙofar toilet ɗin, Ya daɗe tsaye a wajen sai kuma ya juya ya fice daga ɗakin. Sai da ta tabbatar da ya tafi sannan ta buɗe ƙofar, Ta fito da gudu ta rufe ƙofar ɗakin ta saka key ta bar shi a jiki, sannan ta koma ta zauna gefen gadon ta kifa kanta akan cinyoyinta ta fashe da wani sabon kukan.
Washegari da safe ta shirya cikin wasu riga da wando na jeans da t-shirt, ta ɗaura after dress akai ta ɗauki jakarta ta fito. A parlour ta same su suna breakfast, Ko kallon inda suke bata yi ba ta nufi ƙofar fita daga parlon, Zahra ta bita da kallo sai kuma ta taɓe baki. Tashi ya yi yana shirin barin wajen, Ta ajiye pork ɗin hannunta ta ce“A’a ina zaka je?” bai bata amsa ba ya juya yabi bayan Nanar, Zahra ta bisu da kallo sai kuma ta ɗauke kanta. Can ya hangota tana tafiya toward direction ɗin fita daga first gate ɗin, Yabi bayanta da sauri har ya kamota, Janyo hannunta ya yi yana kallonta fuska babu walwala ya ce
“Ina zaki je?”
Kallon sa ta yi, sai kuma ta janye hannunta daga nasa ta ce“makaranta.” daga haka ta juya ta ci gaba da tafiya. Abdusammad ya dinga kallonta cike da mamaki, can dai ya sake bin bayanta ta fizgota wannan karon babu alamar wasa ya ce
“Daman haka ki ke tafiya makarantar? Kin fi abinci?”
Tuni hawaye ya fara wanke fuskarta, Ta fizge hannunta ta ce“Ni bana so abincin naku. Ba zan ci ba, kuma bana son a kai ni makarantar, bana buƙatar taimakonka, ka rabu dani!”
Ta ƙare maganar a fusace. Kasa cewa komai ya yi, ganin tana sake shirin barin wajen ya fizgota ta faɗa jikinsa, kuka ta saka tana dukansa. Ya matseta a jikinsa yana kallon ta ya ce
“Ni ki ke yiwa rashin kunya ko? Zan yi maganin ki.”
Daga haka ya fara tafiya da ita har suka fita daga gate ɗin, Kafin ya ƙarasa wajen parking space ɗin guards dake zazzaune suka taso suka nufo wajen, Ya miƙa ma drivern hannu ba tare da ya ce komai ba. Ya gane mai yake nufi dan haka ya miƙa masa key ɗin, Ya ƙarasa gaban wata Rolls-Royce fara ƙal ya danna key ɗin nan take ta yi ƙara. Passenger seat ya buɗe ya zurata sannan ya mayar ya rufe, Ya zagaya ɗaya side ya buɗe ya shiga. Sai da ya yi warming motar sannan ya yi reverse ya fice daga gidan.
Har suka kusa zuwa Columbia babu wanda ya ce komai a cikinsu, Barin ma Nana data juya kanta gefe ɗaya tana kallon titi. Dan tun bayar wayar da suka yi da Anty Ramlah ta faɗa mata yanda zata yi bata sake ɗaga hankalinta ba. A gefen titi ya yi parking sannan ya sauka daga motar, ita dai inda yake bata kalla ba ballantana ta yi masa magana. After 10mins ya dawo hannunsa rike da leda, Ya ɗora mata kan cinyarta sannan ya yi wa motar key suka ci gaba da tafiya. Har suka ƙarasa makarantar Columbia ɗin, A parking space yayi parking, Ta buɗe motar tana ƙoƙarin fita taji ya ce
“Make sure kin ci abinci, and when zaku tashi?”
Bata kalleshi ba tana ƙoƙarin ɗaukan jakarta ta ce“2:00pm.” ta ce tana sauka daga motar, Da idanu kawai ya bita sai kuma ya girgiza kansa yana murmushi. Ita baya yarda ba fushi take yi, Sai da yaga ta nufi department ɗinsu sannan ya juya ya bar school ɗin. Nana na shiga class ta samu ƙawarta Surry wadda ita ma yar Nigeria ce take zaune da mijinta a new York ɗin, Ɗaga mata hannu ta yi Nana ta ɗan yi murmushi sannan ta ƙarasa inda take. Zama ta yi gefenta, Surry ta janye glasses ɗin dake idanunta, Fara ce tas kuma kyakkyawa ta sakar mata murmushi ta ce
“Yau baki makara ba Nana? Ko Uncle ne ya kawo ki?”
Ta yi tambayar cike da zolaya, dan kusan kullum tana bata labarin uncle yafi sau 20. Nana ta gyaɗa mata kai fuskarta babu walwala ta ce“Eh, na tashi da wuri ne yau.” Surry ta yi shiru tana nazartar yanayinta, can kuma ta ce“what’s wrong Nana?” Bata ji abin da ta ce ba, saboda tunanin data fara. Surry ta taɓata ta ce
“Nana…”
Kallon ta ta yi tana murmushi, Surry ta sake cewa“meke damunki?” Girgiza mata kai Nana ta yi tana ƙoƙarin kawar da zancen ta ce“ba komai fa. Kawai bana jin daɗi ne, Dr Makh bai shigo ba?” Surry ta taɓe baki ta ce
“Ina tambayar ki wani abun kina faɗan wani abun, Ƙarya ne ki ce babu abin da ke damunki Nana. Ba haka ki ka saba zuwa makaranta ba, and what’s wrong with ur face? Wane ya mareki” sai a sannan Nana ta kai hannunta kan kuncinta, bata yi tunanin tabon bai baje ba dan bata kalli madubi ba ta fito. Surry ta kamo hannunta ta ce“Tell me meke damunki?” Sake girgiza kai Nana ta yi dan ko kaɗan bata son ta fitar da sirrinta, Ta buɗe jakarta ta ɗauko water bottle dinta ta buɗe ta sha ruwan sannan ta ce
“Babu komai fa, kawai mun ɗan samu saɓani ne da kishiyata.”
“Shi ne ta mareki?”
Surry ta yi tambayar tana kallon ta, girgiza kai Nana ta yi, lokaci ɗaya hawaye ya fara zubowa kan fuskarta, cike da ƙunci da baƙin ciki ta ce
“Uncle ne ya mareni…”
Ta ƙare maganar kuka na kwace mata. Surry ta kalli ɗaiɗaikun student ɗin dake shigowa da basu shige mutun uku ba, sai ta matso kusa da ita sosai ta rike hannunta dake kan fuskarta ta ce
“Saboda ita ya mareki? Me ki ka mata?”
Girgiza kai Nana ta yi tana kuka ta ce
“Ita ta fara zagina, ita ce ta fara tsokanata. amma kuma ita bai daketa ba, ni kaɗai ya daka, wallahi bana son auren nan, bana son zaman nan, gidanmu zan tafi. Ni ba zan koma ba!”
Surry ta ɗan girgiza kanta tana kallon ta cike da tausayawa, zata bawa Nana kusan 3yrs dan ta fita wayo sosai duk da girmansu ɗaya. Ta sanya hannunta ta fara goge mata hawayen kafin ta ce
“Idan ki ka bar gidan sai ki je ina?”
Nana ta buɗe jakarta ta zaro passport ɗinta har da visanta ta ce“Gida zan tafi. Ba zan zauna ba, ni bana son auren, bana son uncle.”
Surry ta yi shiru can kuma ta ce“Idan ki ka tafi kin bar mata gidan kenan? Kin yarda ta ci nasara ta koreki? Unbelievable, Ba haka ya kamata ki yi ba. Dole ki zauna a gidan dole ki nuna mata kece amarya kuma mijinta na sonki, Wallahi Nana uncle ɗin nan yana son ki, kuma kema kina sonsa. Kawai kuna wahalar da kan ku ne, Ki bari a tashi zan faɗa miki duk yanda zaki yi, da kansa zai dawo ya baki haƙuri.”
Nana ta sake goge hawayenta sannan ta ce“Baya sona wallahi, uncle baya sona. Alfarma ya yimin nida iyayena ya aureni, ba dan yana sona ba. Kin taɓa ganin amaryar da mijinta bai damu da ita ba? Ko sanda aka kaini gidansa babu ruwansa dani, baya kwana a ɗakina, a haka har kwanana ya ƙare. Kuma koda muka zo nan bai taɓa kwana a ɗakina ba, sai dai duk ranar da nake da girki naje ɗakinsa na kwanta, ita kuma duk ranar kwananta har daƙinta zai bita. Gaba ɗaya baya sona, idan nayi waya da sisters ɗina suna bani labarin yanda suke zaune da sauran yayyenmu, kowacce mijinta na sonta kuma yana kulawa da ita, duk da ba auren soyayya bane. amma ni a nan….”
Ta yi shiru saboda kukan da yaci ƙarfinta, Surayyah da taji tausayinta ya rufeta ta jawota jikinta, Nana ta ci gaba da kuka kamar ranta zai fita.
****
Nigeria.
Aunty Khadijah ce zaune bayan ta idar da sallar magriba, wayarta dake kan gado ta fara ringing, zare hijabin ta yi sannan ta hau kan gadon ta janyo wayar. Sabuwar lamba ta gani, dan haka ta ɗaga ta ce
“Assalamu alaikum.”
Daha ɗaya ɓangaren ya gyara tsaiwarsa ya ce
“wa’aiki assalam da Khadijah, kina lafiya.” sosai ta ɗau muryarsa, amma madadin ta fusata sai ta samu kanta da yin murmushi ta ce
“Ina nan kalau Alhamdulillah.”
Ya jinjina kai sannan ya ce
“Daman ina ƙofar gidanku ne, nazo mu ɗan zanta.”
Aunty Khadijah ta ce“tom gani nan” daga haka ta kashe wayar, tashi ta yi tana murmushin da bata san dalilin sa ba, Ta ƙarasa press ɗinta ta fiddo wata dakkakiyar shadda maroon colour sai sheƙi take. Ta zare kayan jikinta ta saka shaddar ta feshe jikinta da turaruka kala-kala, kwalliya sosai ta yiwa fuskarta sannan ta ɗauki wayarta bayan ta yafa mayafi ta fito daga ɗakin.
Umma na zaune tana lazumin bayan magriba taga Aunty Khadijah ta fito. Ta dinga kallon ta da mamaki ta ce
“Khadijah ina kuma zaki je?”
Murmushi Anty Khadijah ta yi ta ce“daman baƙo nayi Umma, shi ne zan je.” Umma ta jinjina kanta ta ce“to a dawo lafiya.” amin ta ce sannan ta juya ta fice tana murmushi, Amal dake zaune kan kujera tana danna waya ta kalleta sai kuma ta taɓe baki. Tsaye ta same shi jikin gate ɗin gidan, ta ƙarasa tana kallon sa saboda wadataccen hasken da yake wajen. Shima kallonta yake yana murmushi, Ta ɗan durƙusa ta ce
“Ina yini?”
Malam Garba ya yi murmushi yana gyara rawanin kansa ya ce“lafiya lau Hajiya Khadijatul kubra. Ya su Mama?” Anty Khadijah ta sake murmushi ta ce“suna nan kalau, ta ce ma na gaishe ka.” Malam Garba ya jinjina kansa ya ce“Allah sarki, ina amsawa sosai da sosai.” shiru wajen ya ɗauka, can kuma ya ce“daman fa zuwa nayi mu ɗan gaisa yauwa, naga kwana biyu kin janye ƙafa” Anty Khadijah ta girgiza kanta ta ce“Ayyah abubuwane suka min yawa. Na gode amma” Jinjina kansa ya yi ya ce“Ba komai. Aaa ba komai, bari na koma”
“Da wuri haka?”
Ta yi maganar tana murmushi, gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh gara naje. Sai kuma wani lokacin” Anty Khadijah ta ce“To na gode.” Tana tsaye har ya bar wajen sannan ta koma cikin gidan.
****
Suna tsaye da Surry har mijinta yazo ɗaukanta. Ta kalli Nana wadda ke mata hira ta ce“Ga Albee ya zo, zan tafi. Kin dai ji duk abin da na faɗa miki ko?” gyaɗa mata kai Nana ta yi ta ce“tom sai monday.” Surry ta yi murmushi sannan ta bar wajen, Basu daɗe da tafiya ba motarsa ta yi parking. Sarai ta gan shi amma ta ɗauke kanta, Gajiya ya yi da jiranta ya fito daga motar, sanye yake da wasu English wears na Gucci masu kyau da taushi, wanda suka dace da weathern damunar da ake ciki, Gashin kansa ya zubo gefen kafaɗunsa dan bai daure shi ba. Har gabanta ya ƙaraso yana kallonta ya ce
“Sai na zo nace ki tawo?”
Kallon sa ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta tace“ban ganka bane.” Shiru ya yi yana kallonta dan ya san ƙarya take ta ganshi, Ya ce“to muje.” Ya yi maganar yana karɓar jakar hannunta, ita dai bata ce komai ba ta yi gaba, ta shiga motar tana jiransa. Bayan ya shiga ya ajiye jakar a jikinsa yana kallon ta fuskarsa a sake ya ce
“Kin daina fushin?”
Kallon sa ta yi, kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“Fushi kuma?” Ɗauke kansa ya yi ganin tana shirin raina masa hankali, Ita ma ta mai da kanta ga jikin glass ɗin ƙofar tana kallon garin wanda ya ɗan yi duhu kamar hadari na kwance. Har suka je gida babu wanda ya yi magana, yana gama parking bata jira shi ba ta sauka daga motar ta nufi cikin gidan. Da idanu kawai ya bita sai kuma ya zare key ɗin ya fito hannunsa riƙe da school bag ɗin tata ya nufi cikin gidan shima. Ko a parlour bai sameta ba, dan haka ya nufi apartment ɗinsa kai tsaye. Da daddare wajen ƙarfe 10:00 na dare ya fito ganin har sannan bata zo ba, kuma ranar kwananta ne. Kai tsaye apartment ɗinta ya nufa, a buɗe ya samu ƙofar ya shiga yana kallonta. Zaune take tsakiyar gadonta tana danna system ɗin dake gabanta, Ya zauna gefen gadon ya ce
“Nana baki ga dare ya yi bane?”
“Nagani.”
Ta ce ba tare da ta ɗago kanta ba. Abdusammad ya ɗan yi shiru ganin ko kallon sa bata yi ba, bai taɓa ganin ta yi masa haka ba. Hasali ma bai taɓa ganinta in a serious mood irin haka ba, Ya numfasa kafin ya ce
“Ina jiran ki naji shiru, tashi mu tafi.” sai a sannan ta ɗago ta kalle shi. Fuskarta a haɗe babu alamar wasa ko kuma yarintar daya saba gani, Bakinta sai sheƙi yake dalilin lip gloss ɗin data saka, wanda duk cikin shawarwarin da Surryn ta bata ne. Lokaci ɗaya yaji jikinsa ya yi sanyi, Ta ɗauke kanta ganin irin kallon da yake matan. Rufe system ɗin ta yi ta sauko daga kan gadon, Riga ce mara nauyi a jikinta, wadda ta tsaya iya gwuiwarta, fararen ƙafafunta sun fito sosai. Ajiye laptop ɗin ta yi a kan drawer ta juyo tana shirin barin wajen, Tsaye ta gan shi a gabanta. Sai da ƙirjinta ya buga, amma ta dake ta haɗe fuska babu alamar wasa ta ce
“uncle ka matsa.”
Janyota jikinsa ya yi ya fara ƙoƙarin kai bakinsa ga nata, ta sanya hannayenta duk biyun ta ture shi tana cewa“Ni bana son irin haka uncle. Ka daina min wallahi”
Ganin yanda ta yi maganar ya sanya shi yin murmushi, kamar wanda ya tuna wani abu sai ya saketa ya ce“shikenan zo mu tafi” Barin wajen ta yi sannan ta ce“to muje.” daga haka ta yi gaba yana biye da ita a baya. Sai da suka je tsakiyar parlour sannan ta ja ta tsaya. Ya juyo yana kallon ta yace
“Mene ne?”
Ɗan kwaɓe fuska ta yi ta ce“Na manta wayata.”
Ya ce“to zaki je ki dauko ne?” gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh ina zuwa.” daga haka ta juya ta koma ɗakin, Yana nan tsaye har bayan mintuna biyar amma bata dawo ba. Ya juya yana kallon ƙofar sai kuma ya ƙarasa wajen, Sai dai me? Yana murɗawa ya jita a rufe, Ya ɗan bubbuga ƙofar ya ce
“Nana! Nana!”
Shiru babu amsa, tana zaune gefen gadon tana jinsa. Ya dinga kiran sunanta ta yi banza, har ya gaji ya bar wajen. Ta koma ta yi kwanciyarta ta ja duvet ta rufe jikinta, hannunta ta sanya ta kashe side lamp ɗin dake gefen gadon, nan take duhu ya mayaye ɗakin, Ta lumshe idanunta nan da na bacci ya ɗauketa.
Tun daga wannan ranar kuma bata sake bari wani abu ya haɗa su ba, da safe idan ta tashi bata tsayawa jiransa take tafiyarta makaranta. Haka idan ta dawo ko zama a parlourn bata yi ballantana ya ganta. Gaba ɗaya ta zama kamar ba ita ba, koda ya shigo daƙinta bata yarda ta kula shi daga Eh sai A’a, duk abin da Surry take faɗa mata shi take yi, sosai kuma hakan ya dameshi. Dan yanzu ta tashi daga Nanar daya sani yarinya mai rigimar banza, ta zama wata daban wadda magana ma bata dameta ba. Idan kaji tana dariya to a waya ne ita da Amma ko kuma su Maimoon, Ɓangaren Zahra kuwa abun sai a hankali, yau a zauna lafiya gobe abu yaci tura. Kwata-kwata bata wani ganinsa da mutunci, ganin haka ya sanya shima ya tarkatasu ya watsar da lamarinsu gefe, idan ya shiga apartment ɗin kowacce da safe baya sake nemansu sai idan wadda take da kwana taje ɗakinsa, a haka har kusan wata guda ya shuɗe.
Ranar wata Juma’a around 9pm ya shigo ɗakin yana sanye da kayan bacci, Zahra na zaune gefen gado tana kitsema Noor dake bacci kanta. Ya ƙaraso ciki ya tsaya a bakin gadon yana kallon su, sau ɗaya ta kalle shi ta ɗauke kai, Ya numfasa sannan ya nemi gefen gadon ya zauna. Har ta gama mata kitson bai ce komai ba, Ta ɗauketa ta fita da ita daga ɗakin, After some minutes ta dawo ta zauna gefen gadon tana shirin kwanciya taji ya ce
“Zahra ina son magana dake.”
Fasa kwanciyar ta yi ta koma ta zauna tana kallon sa babu yabo babu fallasa ta ce“To ina ji.”
“Akwai abin da nake miki ba daidai bane da har ki ka sauya haka? Ko akwai abin da na rage ki dashi da ki ka koma kaurace min? Did i done something wrong to you?”
Abdusammad ya jera mata tambayoyin yana kallon ta a nutse. Wani murmushin takaici Zahra ta yi ta ce“Au tambaya ka ke doctor? Baka sani ba kenan? To bari kaji ba wani abun bane kawai na gaji da zama da kai ne! Wallahi na gaji. Bana son zaman nan”
Da mamaki yake kallonta, Can kuma ya girgiza kansa ya ce“Zahra ƙarya ki ke wallahi, ƙarya ne ki ce kin gaji da zama dani. Cause i know you love me, kamar yanda nake sonki, ke kan ki shaida ce na aureki ne saboda ina son ki. Na bijirewa dangina saboda ke, dan Allah Zahra kada ki ce zaki bar ni. Kada ki ce zaki gujeni”
Ya ƙare maganar yana ƙoƙarin rungumeta, Ture shi ta yi tana watsa masa wani kallo ta ce
“Kada ka sake kuskuren taɓa ni, bana so nace maka.”
Miƙewa tsaye ya yi wannan karon a fusace ya ce“idan na taɓa ki me zaki yi? Ko kin isa ki hanani na taɓa ki ne?”
Tashi tsayen itama ta yi tana kallon sa ta ce“Ai ko ba zaka taɓa ni ba, kuma idan ka manta bari na tuna maka. Yau ba kwanana bane, sai kaje wajen ita yarinyar daka aura ka kwanta da ita amma wlh ba dai ni Zahra ba!”
Ta ƙare maganar tana zabga masa wata uwar harara. Gyaɗa kai Abdusammad ya dinga yi cike da mamakinta ya ce
“Oh haka ki ka ce?”
Ta gyaɗa masa kai tana faɗin“Eh haka na faɗa!”
“To bari ki ji, ke baki isa ki hanani nayi abin da nayi niyya ba. Idan naso yin abu ban ga wadda zata hanani ba, kuma da ki ke maganar Nana, ita yarinya ce ƙarama. Bata san komai ba, dan haka ni ba azzalumi bane da zan cutar da ƴar mutane. Amma ke dole ne nayi yanda nake so dake!”
Ƙoƙarin magana take taji ya hankaɗata, Duk yanda Zahra ta so kwatar kanta kasawa ta yi dan ba ƙaramin ƙarfi ya saka mata ba, a dole ta rabu dashi. Bayan ya gama abin da ya yi niyya ya tashi ya fice daga ɗakin ya bar ta a wajen, Ta dinga kuka saboda muguntar da ya yi mata, Baƙin cikin kalmar daya faɗa ta sanyata sake rushewa da kuka. Tana cije laɓɓanta da ƙarfi.
Koda ya koma ɗakinsa bai tarar da Nana ba kuma daman ya san ba zata taɓa zuwa ba, koda kuma yaje kiranta ba zata biyo shi ba,dan haka ya faɗa banɗaki ya yi wanka ya fito ya sauya kaya ya yi kwanciyarsa. Washegari da safe ya kama Saturday, ranar Nana bata da lecture dan haka ko ƙasa bata sakko ba, tana daƙinta a kwance saboda sanyin da ake.
Zahra na zaune kan sofa tana tunanin yanda zata yi, ba zata taɓa bari abin da ya ya mata ya tashi a banza ba. Dan haka ta miƙe ta huce sama, Daƙinta ta shiga ta zauna gefen gadon tana sake maimaita maganar daya faɗa mata, Can dai ta miƙe ta ɗauki veil ɗinta ta yafa sannan ta fito, bata ko tambayeshi ba ta fice daga gidan, After 30mins ta dawo da wata ƙaramar leda. Shiryawa ta yi cikin wata doguwar riga ta abaya nude colour, Ta yi simple make-up a fuskarta sannan ta nufi ɗakin Noor, tana zaune da maid ɗin dake kula da ita suna hira ta shigo. Ta taso da gudu ta rungumeta ta ce
“Ummi”
Murmushi Zahra ta yi ta ɗauketa ta ce“Muje ki raka ni unguwa.”
“Ummi da Abbie zamu je?”
Girgiza mata kai Zahra ta yi ta ce“Abbie na gida za’a bar shi ya huta, dani dake zamu je.”
Tura baki Noor ta yi ta ce“ni na fison har da Abbie” Zahra ta ja kumatunta ta ce“Eh ai gobe dashi zamu je, yau amma mu kaɗai zamu, har da gidansu Afeefa.” washe baki ta yi tana dariya ta ce
“Da gaske Ummi?”
Zahra ta gyaɗa mata kai bayan ta ajiyeta kan kujera. Ta ɗauki ledar data shigo da ita a gefen gadon sannan ta juya ta fita. Kitchen ɗin saman ta shiga ta haɗa coffee kamar yanda ta san zai masa, ta haɗa da hamburger guda biyu a plate. Buɗe ledar ta yi ta dauko wani tablet ta ɓalli guda huɗu ta zuba a coffee ɗin, ta ɗan jira har ya narke sannan ta ɗora a tray ta fita..
Side ɗinsa ta nufa ta murɗa ƙofar parlourn ta shiga, Zaune ta hangeshi kan sofa yana operating system ɗin dake gabansa. Ta yi sallama sannan ta ƙarasa ciki, Ya ɗago fuskarsa ya ɗan kalleta. Murmushi ta sakar masa bayan ta ajiye tray ɗin kan table ɗin gabansa ta ce



