⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 42: Chapter 42

Tashi tsaye ya yi yana ƙoƙarin rike hannunta ya ce“to muje.” fashewa ta yi da kuka ta faɗa jikinsa ta ce“kafata zafi take min uncle, ba zan iya tafiya ba. Ka ɗaukeni…” ta ƙare maganar tana sake narke masa, Tamkar Hajiya Babba ce ta yi masa maganar haka ya shiga gyaɗa kansa kafin ya ce

“Okay tawo”

Daga haka ya ɗauketa kamar yar baby ya nufi toilet ɗin da ita. Zahra ta dinga kallon ƙofar toilet ɗin zuciyarta na wani irin tafarfasa, Ta tashi ta fice daga ɗakin tana ganin duhu-duhu, Tana shiga daƙinta ta faɗa kan gado ta fashe da wani irin kuka na zallar takaici, har ita Abdusammad zai wulaƙanta a gaban Nana? Ita zai yi wa irin wannan abun. Ta sake rushewa da wani sabon kukan tana dafe ƙirjinta.

Da kyar ta yi sallar tana koke-kokenta wai ita zafi ƙafarta zata ɓalle, shi dai sai rarrashinta yake kamar zai maidata ciki. Gaba ɗaya tausayinta ya cika shi, Ya jawota jikinsa ya rungume yana sakin ajiyar zuciya ya ce

“Ki daina kukan, ko kina son uncle ya daina son ki?”

Banza ta yi masa kuma bata daina kukan ba. Ya girgiza kansa dan daman Nana maje birni ne, balle da aiken sarki. Jira take a taɓata ta fara damun rayuwar mutane. Duk yanda ya yi da ita akan taci abinci ƙi ta yi a sannan ma, Daga ƙarshe ya haɗe ransa yana kallon ta babu alamar wasa ya ce

“Wallahi idan har baki ci abinci na baki magani ba, sai na sake miki abin da nayi.!”

Kallon sa ta yi ganin how serious he is ya sanya ta shiga girgiza hannayenta tana kuka ta ce

“A’a uncle, wallahi mutuwa zan yi. Ka yi hakuri”

Ɗauke kansa ya yi saboda dariyar da ta so bashi, Ya fuske ya janyo plate ɗin daya zuba mata gasasshiyar kazar sai tiriri take saboda da zafinta, Ya ɗauki tsoka ɗaya ya kai mata baki ya ce

“Open ur mouth.”

Kallon sa ta tsaya yi, Ya ajiye plate ɗin a gefe ya fara ƙoƙarin zuge zip ɗin dake gaban rigarsa. Wani irin ihu ta saki ta yi saurin rungumeshi tana kuka ta ce“zan ci wallahi, dan Allah ka bari!”

Ɗagota ya yi daga jikinsa ya tura mata plate ɗin ya ce“cinye yanzun nan.” ta kalli plate ɗin sai kawai ta sake fashewa da kuka, Da ɗan mamaki yake kallonta. Kafin ya yi kwafa ya janye plate ɗin ya fizgota ta faɗo jikinsa, Kafin ta yi wani yunkuri taji ƙarar farkewar rigarta, Ya keta rigar tun daga sama har ƙasa. Kasancewar babu komai a ciki ya sanya shi haɗiyar yawu yana ƙarewa surar jikinta kallo, Ta runtse idanunta tana ƙoƙarin rungume shi ya mai da ita ya kwantar akan gadon. Ban da kuka babu abinda take yi, ta sanya hannayenta duk biyun ta rufe ƙirjinta tana ci gaba da kukanta. Tsaki ya yi lokaci ɗaya ya fizge hannunta, Ya kai bakinsa kan nipples ɗinta. Tun yana abu da wasa sai taga ya fara komawa na gaske, Ta ware iya muryar da ubangiji ya yi mata tana yi masa kuka, Tana yi tana cizonsa amma duk a banza. Wannan karon ma sai da ya samu abin da yake so sannan ya mirgina gefe yana sauke numfashi. Ko motsi Nana bata yi, numfashin ma da kyar yake fita, idanunta a rufe sai hawaye dake zubowa a gefensu. Sai da ya daɗe kwance a wajen kafin ya tashi ya nufi toilet, Bayan ya gyara jikinsa ya dawo ya tsaya a gaban gadon yana kallon ta. Jiki a sanyaye ya sunkuya ya ɗauketa ya koma toilet ɗin, Cikin ruwan da ya haɗa mata ya zurata,Ta zabura tana ƙoƙarin fitowa daga ciki. Riƙeta ya yi sosai yana shafa kanta, Ta langwaɓar da kanta tana ci gaba da hawayenta. Da kansa ya gyara mata jikinta sannan ya sako mata bathrobe ya fito da ita, Sai da ya sauya bedsheet sannan ya kwantar da ita. Sanin ba zata karbi abincin ba ya sanya bai wahalar da kansa ba, Ya haɗa injection ya yi mata sannan ya rufeta da duvet. Ba’a jima ba ya ji saukar numfashinta, ya yaye duvet ɗin yana kallon kyakkyawar fuskarta wadda ta kumbura, Ya saki wani yalwattacen murmushi yana jin so da ƙaunar yarinyar a cikin ransa, Kissing kumatunta ya yi a fili ya ce

“Allah ya yi miki albarka.”

Ya saki duvet ɗin yana murmushi sannan ya tashi daga wajen, Ƙaro gudun ac ɗakin ya yi sannan ya rage mata hasken ya juya ya fice daga ɗakin. A parlournsa ya zauna aka kawo masa abinci, Ya ci sosai saboda ji ya yi cikinsa ya rarake, bayan ya gama ci ya tashi ya koma ɗakin. Sai da ya kalleta sannan ya nufi toilet ya wanko bakinsa sannan ya fito, Har sannan baccinta take, duk da kana jin yanayin sautin numfashin zaka san ba baccin me daɗi take ba. Ya fice daga ɗakin kai tsaye kuma apartment ɗin Zahra ya nufa.

Zaune ya sameta tsakiyar gado ta kifa kanta akan cinyarta tana kuka a hankali, Ya tsaya a tsakiyar ɗakin yana ƙare mata kallo. Ɗago kanta ta yi ta kalleshi da idanunta wanda suka yi luhu-luhu saboda kuka, Ya ɗan yi jim kafin ya fara cewa

“And this should be the last time da zaki sake shiga harkar yarinyar nan idan har kin san ba zaman lafiya zaku yi ba. Duk abin da ki ke nayi miki shiru ne kawai na ɗauke kaina ba dan ban san gaskiya ba, ina sane koda yaushe nake bata rashin gaskiya just to see zaki gyara. Amma na fuskanci ba zaki sauya ba, saboda kin canja halaye, da ba haka ki ke ba. Idan har ki ka sake shiga inda take ki ka nemeta da faɗa wallahi sai na saɓa miki Zahra! I’ll show you the other side of me. Bana son tashin hankali, idan zaku iya ku zauna lafiya. Idan kuma kun ba zaku zauna lafiya ba ni zan saita ku, dan na san maganinku!”

Ya ƙare maganar yana yi mata wani kallo, Lokaci ɗaya kuma ya juya ya fice daga ɗakin. Kwafa Zahra ta yi hawaye na zubawa kan fuskarta. Ta yi kwanciyarta tana jin wani irin baƙin ciki da takaici kamar zata mutu, ji ta yi ina ma bata aure shi ba. Ina ma bata san shi ba, da babu abin da zai haɗata da wannan ɓacin ran. Ta kifa kanta jikin pillow tana kuka kamar ranta zai fita.

Daren ranar bai yi wani baccin kirki ba, dan Nana bata bar shi ya huta ba. Daga wannan sai ta ce wancan, daga wannan kukan sai ta komawa wani, daga ƙarshe ma tashi zaune ta yi ta ce sai ya kira mata Abbanta ta faɗa masa. Abdusammad ya dinga kallon ta can kuma ya ce

“To zan kira shi amma fara zuwa ki kwanta!”

Maƙale kafaɗa ta yi tana kuka ta ce“Ni ba zan bacci ba sai ka kira min Abbana! Ni ka kira min shi.”

Dafe kansa ya yi ya ce“idan baki zo kin kwanta kin daina min rigima ba wallahi zan bata miki”

Ko saurarensa bata yi ba ta ci gaba da kukanta. Ya tashi ya fice daga ɗakin, After some minutes ya dawo hannunsa riƙe da wani ɗan ƙaramin remote. Ya koma ya kwanta ya juya mata baya, sannan ya danna remote ɗin. Lokaci ɗaya wasu irin ƙwaruka masu kama da kyankyaso suka fara tashi a cikin ɗakin, kasancewar da haske sosai ya sanya idanunta ya sauka akan su. Ganin suna ƙaruwa ya sanya ta tsaya da kukan, Ta kalle shi taga ya juya baya, Tashinsa ta fara yi muryarta na rawa ta ce

“uncle! Uncle ka ga.”

Janyeta ya yi daga bayansa sannan ya ce“Dan Allah Nana ki bar ni na huta.”

“Uncle kalli, kalle su kaga!”

Kallon ƙwarukan ya yi ya sake matsa remote ɗin hannunsa nan take suka cika ɗakin sai tashi suke, Ya ɗan ware idanunsa kafin ya kalleta ya ce

“Nana kamar kyankyaso?”

Kafin ta yi magana wani ya tawo ta inda take, Ta saki wata razananniyar ƙara ta faɗa jikinsa tana kuka. Murmushi ya yi sannan ya fara ƙoƙarin ɗagota amma sam taƙi yarda, Ya kwanta ta shige jikinsa ta rufe su da duvet tana kuka, hannayensa ya sanya a bayanta ya sake jawota jikinsa fuskarsa babu alamar wasa ya ce

“Kwanta kar su kama ki”

Gyaɗa masa kai ta yi tana sake ƙanƙameshi. Ya dinga shafa bayanta yana murmushi shi kaɗai, Shiru ta yi tana sauke numfashi, after 5mins ta ɗago kanta tana kallon gemunsa ta ce

“uncle sun tafi?”

Girgiza mata kai ya yi ya ce“kina so su hau miki jiki?” saurin girgiza kanta ta yi tana hawaye, Ya dafa kanta ya ce“To ki yi baccin ki, ba zan bari su zo nan ba.” Toh kawai ta ce sannan ta koma ta yi lamo a jikinsa, Da gaske duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi, cikin ƴan mintuna ya yi maganin rigimar tata. Dan daman ya san babu abin da take tsoro sama da kyankyaso, after some minutes yaji saukar numfashinta, Ya kalli fuskarta dake kan ƙirjinsa sai kuma ya yi murmushi ya rufe idanunsa nan da nan bacci ya ɗauke shi shima.

Washegari yini ta yi a kwance ko parlour bata fito ba, iyakar maganar da ya yi da ita akan ta zo suje ƙasa ƙin yarda ta yi. Har ya gaji ya fita ya bar ta, Ta na nan zaune around 5:00 na yamma wayarta ta fara ringing. Hannunta ta saka ta janyo wayar ta kai kunne bayan ta ɗaga. Daga can ɓangaren Amma ta ce

“Nana”

Ji ta yi kamar ta yi tsuntsuwa taje Nigeria ta rungume Ammarta. Sanin babu hali ya sanya ta sauke numfashi murya a sanyaye ta ce

“Na’am Ammata.”

Amma ta yi shiru jin muryarta a sanyaye ta ce“lafiya dai Nana? Ko wani abun na damun ki?”

Girgiza kai Nana ta yi dan ba iya faɗa mata zata yi ba ta ce“ba komai kawai a kwance nake.” Amma ta ce“To shikenan, Daman kiran ki nayi naga kwana biyu baki kirani ba” Murmushi Nana ta yi ta ce“Makaranta ce take hanani sakewa, shiyasa.” Amma ta jinjina kanta ta ce“haka ne Allah ya taimaka, ki dinga dagewa.” A sanyaye ta ce“Amma yaushe zaki zo?” ware idanu Amma ta yi kafin ta ce“Ni ce zan zo ɗin Nana?” turo baki Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce“dan Allah Amma ki zo. Kin ga babu wanda yake zuwa inda nake tun da na zo, kuma…”

“Kuma me?”

Amma ta ce tana gyara zaman wayar a kunnenta. Girgiza kai Nana ta yi ta ce“Kuma ai ban san kowa ba, uncle kawai na sani fa. Ko hira bana yi da kowa”

“Ina ita Zahran?”

Tura baki Nana ta yi ta ce“Uncle ya hanani kulata, Ya ce idan na sake kulata zai zaneni.” Da ɗan mamaki Amma ta ce“duka kuma? Akan me? Me ki ke mata?” ta jera mata tambayoyin tana jiran amsar da zata bata. Cikin shassheƙar kuka Nana ta ce“to ba ita ce take fara zagina ba, dan Allah Amma ai kin ga sai na rama ko?” Girgiza kai Amma ta yi dan daman ta san za’a rina ta ce

“Nana! Nana! Nana ban son kina neman magana. Na san halin ki da rashin kunya, baki son a zauna lafiya, so ki ke a dinga kawo ƙarar ki? Kina son Abbanki ya dinga fushi a kan ki ne?” Girgiza kanta ta yi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce

“wallahi Amma babu abin da nake mata. Ita ce take zagina, kuma ta ce sai uncle ya sakeni. To shi ne na rama”

Ta ƙare maganar tana goge hawayenta. Amma ta ce

“Ko me zata ce ki daina tankata, kada ki bata amsa. Ki yi shiru da bakin ki”

“To ai daman na daina kulatan fa Amma.”

Jinjina kai Amma ta yi ta ce“Yauwa haka yafi, Ki nutsu kuma, kada ki dinga son jikin ki. Idan baki da lafiya ki dinga faɗawa Abban Noor ɗin” Gyaɗa mata kai ta yi kafin ta ce“Tom Amma.”

“Ya isa daina kukan ɓaure.”

Murmushi ta yi tana sake goge hawayenta ta ce“na daina Amma.” Jinjina kai Amma ta yi ta ce ta ce“Allah ya miki albarka.” da Amin Nana ta amsa sannan suka ci gaba da hirarsu.

****
Zahra na zaune kan kujera a parlornta wayarta dake hannunta ta fara ringing, Ta ɗaga tana murmushi ta ce“Hello Anty” Anty Khadijah dake jan numfashi kamar wadda ke kuka ta ce“Zahra kina ji?” Gyara zamanta ta yi jin muryar tata ta ce“Anty lafiya dai? Me ya same ki?”

“Zahra bana son auren Malam Garban nan, wallahi bana so. Gashi ɗazu sun zo sun kawo kuɗin aure nan da 2 weeks za’a ɗaura auren…”

Tashi tsaye Zahra ta yi tana girgiza kanta ta ce

“Haba dai Anty. Wallahi ba zaki auri wannan mutumin ba! Ya ma za’a yi ki aure shi? Idan ma wani asirin ya yi miki sai dai ya faɗa kansa wallahi Anty. amma ke dai kin fi ƙarfin aurensa”

Cikin kuka Anty Khadijah ta ce“nima na san da haka Zahra. Wallahi ni ba sa’ar aurensa ba ce, akan mene ma zan aure shi?”

Zahra ta yi shiru tana jin zuciyarta a dagule, Anty Khadijah ta ja numfashi ta ce“kina ji? Amma kina shan maganin nan?” Girgiza kai Xahra ta yi a sanyaye ta ce“Wallahi a’a Anty, kwana biyu kin ga ban sha ba. Ni mantawa ma nake dashi” Anty Khadijah ta yi shiru can kuma ta ce“To ki ɗauko ki shanye yanzu, saboda bana son ya kai wani satin zai lalace.” To kawai Zahra ta ce sannan suka ci gaba da tattauna maganar auren…

Sai bayan sallar magriba sannan ya shigo gidan, Kai tsaye ɗakin Nana ya nufa dan ranar kwanan Zahra ne. Ya sameta zaune ƙasan gado tana danna wayarta bayan ta idar da sallah, Ƙarasawa ciki ya yi ya ajiye ledar dake hannunsa ya zauna gefen gadon yana kallon ta fuskarsa a sake ya ce

“Hey baby.”

Ɗago kanta ta yi ta kalle shi, Ya sakar mata murmushi yana miƙa mata hannu. Tura baki ta yi ta tashi ta koma can ƙarshen gado ta zauna, Murmushi ya yi sannan ya juya inda take yana kallon ta, Fuskarta a haɗe babu alamar wasa. Ya hau tsakiyar gadon ya zauna kusa da ita yana jan kumatunta ya ce

“Wa ya taɓa min ƴar rigimata?”

Janye hannunsa ta yi tana tura baki, Ya sake kai hannunsa zai taɓa ta. Tsam ta tashi daga wajen ta koma wani ta zauna tana kallon sa, Ya girgiza kansa ya sake bin ta, Ƙoƙarin sauka take daga kan gadon ya jawota jikinsa. Tura shi ta fara yi kamar zata yi kuka ta ce

“Ni Allah uncle bana so. Ni ka bari”

Sake matseta ya yi a jikinsa yana kallon ta ya ce“Ni zaki dinga sharewa?” Ɗauke kanta ta yi tana kallon wani wajen, Ya yi kwafa kafin ya janyo fuskarta ya ce

“Idan ki ka sake ɗaukewa sai na baki mamaki.”

Ganin babu alamar wasa akan fuskarsa ya sanya ta fasa ɗaukewa, ta sunkuyar da kanta nan take hawaye suka fara zubowa kan fuskarta. Waro idanunsa ya yi yana kallonta kafin ya ce

“me kuma nayi miki?”

Cikin kuka ta ce“Ni bana so, bana so kana taɓani wallahi. Ka daina!”

Kallon ta kawai yake. Can kuma ya yi murmushi ya ce“Yanzu warning ki ke min or what Nana?” tura baki ta yi tana ƙoƙarin kwace kanta. Ya sake matseta yana kallonta ya ce“ai sai kin amsa min yarinya.” marairaice fuska ta yi ta ce

“uncleee!”

“Auntyyyy..!”

Ya ce yana kwaikwayon muryarta. Tuntsirewa Nana ta yi da dariya tana kallon sa, Shima dariyar yake. Ta duke shi a ƙirji ta ce“ni ka daina kwaikwayon magana ta Allah!”

Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“To na bari Aunty.”

“Ni bana sooo!”

Ta ce a shagwaɓe.

Murmushi kawai ya yi yana ɗora kansa a wuyanta ya ce“Zo ki ci abinci.”

Turo baki ta yi kafin ta ce“ni bana ci” Bai ce komai ba ya janyeta daga jikinsa ya sauka daga kan gadon, Ledar daya shigo da ita ya ɗauko ya miƙo mata. Ta karɓa tana kallon sa, sai kuma ta buɗe, washe baki ta yi ta ɗago kanta tana kallon sa ta ce

“Laaa kaza?”

Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh bashin kazar ki ce.”

Turo baki ta yi ta tura masa ledar ta ce“bana ci”

“A kan me?”

Ta koma ta kwanta ta ce“kawai bana ci.”

Murmushi ya yi ya sanya hannunsa ya jawota, Ya ɗago kanta ya ce“Ko dai ki ci ko kuma…”

“Zan ci wallahi!”

Ta katse shi da sauri. Ta ɗauki ledar kazar ta buɗe ta fara ci tana taunawa a hankali, Ɗago kanta ta yi taga yana kallonta. Ta dauko tsoka ɗaya ta miƙa masa tana tauna ta bakinta ta ce

“Cii”

Yanda ta yi maganar ne ya bashi dariya, Ya ja kumatunta ya ce“Am full” bata sake cewa komai ba ta kai naman bakinta tana rausaya kai. Tashi ya yi yana kallonta ya ce“sai da safe.”

To kawai ta ce a sanyaye, Ya juya ya fice daga ɗakin. Sai a sannan ta ture ledar gabanta ta kifa kanta akan cinyoyinta ta fashe da kuka tana birgima a wajen. Haka ta gaji da kukan ta haƙura ta tashi ta shige bayi ta wanko bakinta sannan ta yi wanka ta fito, Wasu riga da wando masu sulɓi ta ɗauka ta saka sannan ta yi kwanciyarta. Ta dade tana juye-juye kafin bacci ya ɗauketa, Abdusammad koda ya fita ɗakin Zahra ya shiga ya ce mata yana apartment ɗinsa. Amma har wajen ƙarfe 12 na daren bata zo ba dan haka ya yi kwanciyarsa. Washegari ma bai zauna a gidan ba saboda aiki da ya ya masa yawa, Zahra kuwa ko inda yake bata je ba. Ko Noor bata kai school ba tayi kwanciyarta a ɗaki doing nothing. Nana na zaune akan sofa wajejen ƙarfe 7:00 na dare, wayarta ta fara ringing, numbern Abba ta gani, Ta ɗaga ta kai kunne tana murmushi.

“Happy birthday daughter!”

Cewar Abba muryarsa cike da farin ciki. Tuntsirewa da dariya Nana ta yi dan ita har ta manta ma, Can kuma ta tsuke fuska ta ce

“Abba yau birthday ɗina babu celebration”

Murmushi ya yi ya ce“Uncle ɗin ki bai miki ba?” taɓe baki ta yi ta ce“uncle ɗin bai ma sani ba.”

“Haba?”

Abba ya yi maganar yana murmushi, Sake tura baki ta yi ta ce“Abba ina birthday gift ɗina?”

Abba ya ce“To yanzu Nana ta ina zan baki birthday gift? But tell me what do you want, Sai na siya miki duk randa ki ka zo na baki.” Ɗan juya Idanunta ta yi kamar mai tunani ta ce“Yauwa Abba ina son ka siya min teddies da kuma sabon system!” Girgiza kai Abba ya yi yana murmushi ya ce“Nana kenan, you will never change. To naji” Dariya sosai ta yi ta ce“Yauwa Abbana thank you, Allah ya ƙara maka arziki, Ya baka lafiya ingantacciya!” Lumshe idanunsa ya yi yana jin zuciyarsa wasai babu damuwa ya ce

“Amin ya rabbil alameen Nana Khadijah, Allah ya miki albarka ya zaunar min da ke lafiya, Ya kaɗe sharri daga cikin aurenku. Ya baki ya’ya na gari”

Sunkuyar da kanta ta yi tana murmushi ta ce“Abba idan na haihu sai na bar muku ɗan ko?” Dariya ta bashi, Ya ce“Zaki bar min ɗan?” Ta gyaɗa kanta ta ce“Eh Abbana! Sai na bar muku kai da Amma.” Murmushi sosai ya yi ya ce“To Allah ya baki ya’yan Nana” Ta yi murmushi ta ce“Amin Abbana” Sun daɗe suna hira kafin ya kashe wayar. Ta sauke numfashi jin ana kiran sallah ta tashi ta shige bedroom ɗinta, Alwala ta yi ta gabatar da sallah sannan ta yi kwanciyarta dan ba yunwa take ji ba. Tana jin convey ɗinsa, Amma bai shigo gidan ba har sai da aka idar da sallahr Isha’i. Tana kwance tana kallon wata Chinese drama ya shigo dakin, Ta amsa sallamar ciki-ciki. Zama ya yi gefen gadon yana kallon ta ganin ko ɗago kanta bata yi ba, Ya ɗan yi murmushi ya ja yatsun ƙafarta ya ce

“Heyyy”

Ɗago kanta ta yi ta kalle shi sai kuma ta tura baki, Ya girgiza kansa ya ce”wato ke kullum baki so a zauna lafiya ko? Haka ake yiwa miji aka ce miki?”

Ɗauke kanta ta yi tana zumɓura baki gaba. Ya taso ya dawo kusa da ita ya janye system ɗin ya rufe yana kallon ta ya ce“faɗa min yau kuma mene ne? Wa ya taɓan ƴan matana?” Janye hannunta ta yi ta ce“Ni bana so..”

Haɗe rai ya yi babu alamar wasa ya ce“baki son me?” ta kalle shi amma bata ce komai ba. Tashi ya yi yana faɗin “tun da baki da abin cewa sai da safe.” Ganin da gaske tafiya zai yi ya sakata tashi tsayen itama, Ta kira sunansa cikin shessheƙar kuka, Juyowa ya yi yana kallonta da mamaki ganin hawaye akan fuskarta. Ya dawo ya riƙe hannunta ya ce

“Mene ne?”

Fashewa ta yi da kuka ta shige jikinsa tana cewa“Ba kai ne ba, baka san yau birthday ɗina ba? Kuma Abba ya ce kai ne zaka min birthday cake…”

Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan, Wani lafiyayyen murmushi ne ya kwace masa, Ya dafa bayanta yana ƙoƙarin saita kansa kafin ya ɗago fuskarsa a haɗe ya ce

“Ni bani da abin yi zan tsaya wasa? Sakeni ni” Ya janyeta daga jikinsa, Bai tsaya jiran abin da zata ce ba ya juya ya yi ficewarsa. Nana ta bi shi da kallo sai kuma ta koma gefen gado ta zauna tana fashewa da wani irin kuka..

Koda yaje dakin Zahra zaune ya sameta tana waya, Ya tsaya har ta gama kafin ya ce“Madam kwana biyu abun ne ya motsa?” Girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce“Ba komai fa doctor” Ya yi shiru yana kallon ta can kuma ya sauke numfashi ya ce“Alright bari naje ina zuwa.” To kawai ta ce ya juya ya fice, Ta bi shi da kallo sai kuma ta taɓe baki.

Nana na kwance gefen gado Around 9pm taji ana knocking ƙofar, Ta goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta sauka daga gadon. Koda ta buɗe ƙofar Maid ta gani tsaye, Ta sunkuya ta gaisheta kafin ta ce“Madam ana kiran ki” Nana ta ɗan kalleta da kumburarrun Idanunta ta ce“ina?”

“Downstairs”

Ta bata amsa kai tsaye. Okay kawai ta ce sannan ta mai da ƙofar ta rufe, Ta koma ta ɗauki hularta akan gadon ta zura slippers a ƙafafunta sannan ta fito daga ɗakin.

Da mamaki ta dinga kallon ƙasan, ganin duhu ya mamaye ko ina, Ta ɗan yi jim a bakin stairs ɗin benan, kafin a hankali ta fara takawa. Sai da ta sauka kasan sanan ta tsaya cak saboda bata ganin gabanta, Ta ɗan waro idanunta saboda inuwar mutum data gani. Muryarta na rawa ta ce

“wa… waye?”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *