Chapter 44: Chapter 44
“Banza mara hankali, To kema kwana nawa ne? Gara mu duk kusan tare zamu haihu mun huta. Ke kuwa ki yi ta fama” Taɓe baki Nana ta yi ta ce“an faɗa miki nima irin ku ce? Ke yaushe zaki haihu na ƙagu mu zo Yola”
Maimoon ta yi dariya tana sha cikinta wanda ya ɗan fito babu laifi ta ce“Ke banza wata biyar fa, ban kusa ba.” Tsaki Nana ta yi ta ce“sai ki yi ta fama ai, Bari ki ga na tashi uncle ya kusa dawowa.” Riƙe haɓa Maimoon ta yi ta ce“tooo kaji matar uncle. Je ki to, abinci zaki girka masa?” girgiza kai Nana ta yi ta ce“ke A’a kwalliya zan yi”
“Yau ke ce da kwana?” Maimoon ta tambaya tana murmushi. Gyaɗa mata kai Nana ta yi ta ce“Eh mana. Kuma kin ga mu dare ne” Jinjina kai Maimoon ta yi ta ce“to tashi ki je sai an jima ki gaida shi.” To kawai Nana ta ce sannan ta katse kiran, Ta rufe system ɗin ta tashi ta shige toilet. Wanka ta sake yi ta fito ta ɗauki wata rigar bacci mara nauyi fara ta saka, Ta shafa mai a jikinta sannan ta saka turare, bayan ta gama ta ɗauki lip gloss ta shafa a bakinta ta tsaya jikin madubi tana kallon kanta. Murmushi ta yi sannan ta koma ta zauna tana game. Sai wajen karfe 10 na dare sannan ta tashi dan ta daɗe da jin shigowar su, Ta nufa dakin kai tsaye tana tafe tana yan waƙoƙinta. Murɗa handle ɗin ƙofar ta yi bakinta ɗauke da sallama, Amsawa ya yi yana jikin mirror yana gyara kansa dan fitowarsa kenan daga wanka, Ta ƙarasa ciki tana zuwa ta rungumeshi ta baya tana murmushi. Hannunsa ya sanya ya jawota gabansa yana ƙare mata kallo, Ta yi kyau sosai, tayi ƙiba ta zama wata ƙatuwa kamar ba ƴar rigimar Nana ba. Hannunsa ya sanya ya fara ƙoƙarin goge lip gloss ɗin dake bakinta ya ce
“Baki son uncle ya samu salama ko?”
Turo baki ta yi tana janye nasa hannun a shagwaɓe ta ce“uncle ni kada ka gogen abuna.” Bai ce komai ba ya riƙo fuskarta ya zura bakinsa cikin nata ya fara kissing ɗinta. Ji ta yi ƙafafunta sun fara rawa, ta riƙe shi sosai tana sakin numfashi, Sun daɗe a haka kafin ya ɗauketa gaba ɗaya ya karasa gaban royal bed ɗinsa ya kwantar da ita. Tun tana biye masa sai da fara kuka dakyar ta samu ya rabu da ita ya koma gefe yana sauke numfashi. Ita ma juyawa ta yi tana shessheƙar kukanta, ta yi dana sanin biyo shi da ta yi, Dan da tasan abin da zai yi kenan da ba zata zo ba, After some minutes ya tashi ya nufi toilet abin sa. Wanka ya sake yi ya tsaftace jikinsa sannan ya dawo, Kallon ta ya dinga yi ganin har sannan bata daina kukan ba, Ya janyota jikinsa muryarsa a sanyaye ya ce
“C’mon mene ne kuma?”
Kamar jira take ta fara kukan da ƙarfi, Ya yi murmushi bai ce komai ya tashi da ita a jikinsa ya nufi bayi. Bayan ta fito ta gyara jikinta sai dai babu rigarta ko daya a ɗakin, Ya buɗe press ɗinsa ya zaro mata wata rigarsa armless yana kallonta ya ce
“Zo ki saka wannan.”
Kallon rigar ta yi sai kuma ta tura baki. Ya ƙaraso wajen ya bata, karba ta yi ta koma toilet ɗin, Bayan mintuna ta fito tana jan rigar dan ko cinyarta bata gama rufewa. Kallon ta ya dinga yi sai kuma ya yi murmushi ya ce“kuma ta yi miki kyau, ko na bar miki?” Ita dai bata ce komai ba ta karasa kan gadon ta yi kwanciyarta. Sai da ya gama duk abin da yake sannan shima ya kwanta, tana jin ya kwanta ta matso ta shige jikinsa, murmushi kawai ya yi yana shafa kanta ba’a ɗauki wasu mintuna ba bacci ya ɗauketa.
Ringing ɗin wayar da yaji ne ya sanya shi juyawa, Ya janyo wayar dake kan bedside drawer. Numbern Safwan ya gani, Ya ɗaga yana murmushi. Kafin ya yi magana Safwan ya ce
“Yayaaa…”
Girgiza kai Abdusammad ya yi jin yanda ya yi maganar kamar wani ƙaramin yaro ya ce“Kai! Kai! Ba zaka daina wannan banzar ɗabi’ar ba ko?”
Safwan dake kwance kan gado ya lumshe idanunsa ya buɗe kafin ya ce“To me nayi?”
“Dan iskanci da girmanka ka dinga wata shagwaɓa? Kai ba mace ba ba komai ba? Ko baka ga matarka nada ciki bane? Kuma haihuwa zata yi”
Murmushi Safwan ya yi ya ce“Allah ko Yaya? Ai nima na ƙagu Haule ta haihu, Allah ya sa ta haifi namiji na saka masa sunanka.” Murmushi shima Abdusammad ɗin ya yi kafin ya ce
“To Allah yasa. Amma ya kamata ka mayar da yarinyar nan daƙinta before ta haihu”
Shiru Safwan ya yi lokaci ɗaya jikinsa ya yi sanyi, Jin bai ce komai ba yasa Abdusammad ya ce
“Heyy are you there?”
Gyaɗa kansa ya yi sannan ya ce“Yaya ina son na maida ita, amma na san ba zasu bari ba. Babu wanda zai yarda, kuma nima bana son na cutar da rayuwarta. Wallahi Yaya ina son Haule, ina son zama da ita. To amma babu yanda na iya da ƙaddara!”
Girgiza kai Abdusammad ya yi a sanyaye ya ce
“Babu abin da zai faru. Ai kana shan magani, kuma idan har yarinyar ta amince zata iya dawowarta. Zai fi daɗi a ce a gidanka ta haihu, shi kansa abin da za’a haifa sai yafi samun nutsuwa”
Jinjina kai Safwan ya yi ya ce“Ban sani ba ko Haule zata yarda. Amma ni babu wadda nake tsoro sama da Hajiya Babba, ba zata amince ba.”
Numfasawa Abdusammad ya yi ya ce“Kada ka damu gobe idan Allah ya kai mu xan yi magana da Abba, za’a ga abin da za’a yi. Just keep pray kaji”
Gyaɗa masa kai Safwan ya yi ya ce“to Yaya na gode. Ina Nana?”
Kallon ta Abdusammad ya yi ya shafa kanta ya ce“bacci take.”
“A gaisheta, Da Noor.”
To kawai ya ce sannan ya ci gaba da jan shi da hira, Gajiya Abdusammad ya yi ya ce“kai mu dare ne. Sai da safe” Safwan ya yi dariya ya ce“To Allah ya tashe mu lafiya Yaya” Da Amin ya amsa sannan ya kashe wayar. Ya ja duvet ya rufe su sannan ya kashe bedside lamp ɗin duhu ya mamaye dakin, Addu’ar bacci ya yi mata sannan shima ya yi ya rufe idanunsa nan da nan bacci ya ɗauke shi.
Washegari da safe wajejen 10:00 Nana na kwance kan cinyar Abdusammad tana yi masa hira aka fara buga ƙofar ɗakin. Janyeta ya yi daga jikinsa ya tashi ya sauka daga kan gadon, Tsaye ya ga Zahra tana kallon sa. Ganin duk a ruɗe take yasa ya ce
“Lafiya dai?”
“A.aaliyu ke kiran ka”
Wayarsa dake hannunta ya kalla sai kuma ya karɓa ya kai kunne, Abdusammad ya yi shiru jin Aliyu bai ce komai ba yasa ya ce
“Buddy kana jina?”
Jan numfashi ya yi yana ƙoƙarin ɓoye kukansa ya ce
“Eh ina ji.”
Wata irin faɗuwar gaba yaji ta ziyarce shi, domin duk abin da ya saka Aliyu kuka to ba ƙaramin abu bane. Hankali a tashe Abdusammad ya ce
“Lafiya? Kukan me ka ke?”
Aliyu Ya girgiza kansa kukan na ƙoƙarin cin ƙarfinsa, Ya kasa koda magana. Tsaki Abdusammad ya yi a ɗan tsawace ya ce
“Malam idan ba zaka faɗa min abin da ya faru ba na kashe wayata”
Maimoon dake gefensa tana kuka ce ta karbi wayar muryarsa na rawa ta ce
“Uncl… uncle Yaya Safwan!”
Wata irin bugawa yaji zuciyarsa ta yi, Da ƙarfi ya ce
“Me ya same shi! Ina Safwan ɗin yake? Jikin nasa ne?”
Maimoon ta girgiza kanta cikin kuka ta ce
“We lost him,Ya mutu Uncle!”
Wani irin abu yaji ya tokare masa a ƙirji, Ya sauke wayar ƙasa har sannan Maimoon bata daina kuka ba. Kallon sa suka dinga yi ganin yan da ya yi shiru ba tare da ya ce komai ba, Nana ta taso ta ƙaraso wajen tana kallon sa.
“Uncle mene ne?”
Ta tambaye shi tana jan hannunsa, Ɗago idanun sa wanda suka rine ya yi ya kalleta lokaci ɗaya hawaye ya kawo kurmin idanun sa, Ya girgiza mata kai murya a sanyaye ya ce“Ya rasu!”
Da sauri Nana ta saki hannunsa, Zahra dake kusa da shi ta ɗago kanta tana kallon sa cike da tashin hankali ta ce“Innalil lahi wa ina ilayhi raji’una! Ya mutu kuma?” Gyaɗa mata kai kawai Ya yi, Nana ta yi dinga kallon sa can kuma ta fara ƙoƙarin barin wajen sai ganinta suka yi a ƙasa Sumammiya.
****
Yola/Nigeria.
Safiyar ranar Alhamis suka sauka a garin, wajejen ƙarfe 8:00 na safe suka ƙaraso cikin estate ɗin. Nana ta dinga kallon compound ɗin wanda yake cike da al’umma, Abdusammad bai sake kallon su ba ya yi gaba abin sa. Zahra kuwa kallon Nana ta dinga yi ganin ita ma ta yi gaba abin ta, Rashin sanin wajen wanda zata ya sanya ta ja hannun Noor suka nufi apartment ɗin su, Nana na shiga ta tarar da Haule zaune kan kujera tana sanye da hijabi sai kuka take kamar ranta zai fita. Maimoon da su Hamida na zaune gefen ta suna kukan suma, A sanyaye Nana ta ƙarasa dan ita har ta yi kukan ta gaji, Ta zauna a ƙasa ba tare da ta cewa kowa komai ba. Suma da idanu kawai suka dinga kallon ta can dai Maimoon ta ce“Nana kun zo?”
“Da gaske ya mutu? Da gaske Yaya Safwan ya rasu? Dan Allah Maimoon ki faɗa min!”
Nana ta yi tambayar hawaye na zubowa akan fuskarta, Maimoon ta rufe fuskarta da Hijabin jikinta tana kuka tana girgiza mata kai, Nana ta kalle ta sai kuma ta fashe da wani raunataccen kuka. Haka suka dinga kuka a wajen babu mai rarrashi dan suma su Amma kukan suke mutuwar Safwan ta girgiza kowa.
Abdusammad kuwa tun da ya zauna kusa da Abba bai ce komai ba, Bai kuma kalli kowa ba, Haka kuma ba kuka yake ba. Sai dai idanun sa sun kaɗa sun yi jajur kamar garwashi. Jijiyoyin kansa duk sun tashi, Ba lallai bane ka ga tashin hankalin da yake ciki. Domin babu alamar hakan akan fuskarsa, Cazbahar dake hannun sa kawai yaje ja a hankali yana motsa bakinsa. Cikin ransa kuwa shi kaɗai ya san abin da yake ji, Duk yanda yake da Safwan ko gawarsa bai samu damar gani ba, Ballantana ya yi masa kallon ƙarshe, rabon ba zasu haɗu ya sanya ya ƙi zuwa duk da yanda ya dinga takura masan.
****
Babu wanda mutuwar Safwan bata daka ba a gidan, Kowa jikinsa ya yi sanyi. Musamman Haule wadda ta kasa dawowa daidai duk da sati biyun da aka ɗauka, Kullum yini take cikin ɗakin Amma tana kuka, wani lokacin Nana ta dinga taya ta, wani lokacin kuma ta rarrasheta. Ta kasa mantawa dashi a ranta, Sam bata yi tunanin rabuwa dashi ba, bata yi tunanin Safwan zai mutu yanzu ba. Ɓangaren Siyama kuwa ita gaba ɗaya ta fice daga hayyacinta, Babu wanda yake zuwa wajenta, Ko gaisuwa ba’a wani zuwar mata, Sai ɗaiɗaikun mutane idan sun zo suke cewa a kai su wajen matarsa. Ta zama wata abar tausayi da ita, Ta rame ta yi baƙi, Ita kanta bata yi tunanin mutuwa Safwan zai yi ba, Duk da ta san bashi da lafiya sosai daurewa kawai yake amma bata yi tunanin abun zai zamar masa haka ba. Idan ta tuna ita ce wadda ta shafa masa cutar sai taji ta ƙara tsanar kanta, Ko kaɗan ta kasa sukuni, ko abinci bata ci, babu mai rarrashinta. Anty Khadijah ce kawai ke zuwa gidan ta zauna da ita, wani lokacin kuma Amal da Safeena su zo. Zahra kuwa idan ta shigo da safe ta ganta bata sake komawa, Gaba ɗaya ma ba shiga harkar jama’ar gidan take ba. A haka har Sati uku suka shige, Ranar wani Alhamis misalin ƙarfe 4:00 na yamma Anty Khadijah ta buɗe ƙofar parlourn ta shigo, Zahra na zaune kan sofa ta yi yin game a wayarta. Ta kalleta sai kuma ta ajiye wayar a gefe tana cewa
“Au Anty, Ke ce a gidan?”
Anty Khadijah ta ƙaraso ciki ta zauna kusa da ita ta ce“Eh wallahi Zahra ni ce. Daman cewa nayi bari na biyo na duba ki, naje wajen Siyama ne.” Zahra ta ce“Okay Bari na kawo miki ruwa”
Ta miƙe ta shige kitchen, Anty Khadijah ta bita da idanu, After some minutes ta dawo hannunta riƙe da plate mai ɗauke da kayan drinks. Ta ajiye mata a kan table sannan ta koma ta zauna, Murmushi Anty Khadijah ta yi ta ɗauki ruwa tana ƙoƙarin buɗewa ta ce
“Wai ke ya zaman naku?”
Taɓe baki Zahra ta yi ta ce“Wallahi gashi nan Anty, Babu wani daɗi. Ni dama jira nake komai ya lafa na miki magana, Ya ake ciki da kuɗin da ki ka sa na bayar?” Murmushi Anty Khadijah ta yi ta buɗe jakarta ta zaro wani ƙullin magani a baƙar leda ta miƙo mata tana cewa
“Kin ga wannan shi ne maganin, wallahi idan ki ka yi aiki dashi yanda zan faɗa miki to nan bada jimawa ba sai ya saketa!”
Ɗan zaro idanu Zahra ta yi ta dafe ƙirji ta ce“Saki kuma Anty? Na faɗa miki ba asiri ba kama shi zai yi ba. Wallahi shi ma ba’a zaune yake ba” Tsaki Anty Khadijah ta yi ta ce“Kaji banza, To wane ya ce miki shi za’a yi wa?” Zahra ta yi shiru kamar mai tunani, Can kuma ta ce“To wa za’a yi wa?” Wani murmushi Anty Khadijah ta yi tana juya ledar hannunta ta ce
“Mahaifiyarsa za’a bawa!”
Miƙewa tsaye Zahra ta yi tana kallon ta ta ce“Wai wa ki ke nufi? Hajiya Babba? So ki ke ya sakeni ni?” Wata uwar harara Anty Khadijah ta maka mata kafin ta ce“Ke daɗina dake bakya cin ribar zance, to wane ya ce miki zai sake ki? Ai ke da fita a gidan nan sai dai a mafarki, muddin ki ka yi amfanin da wannan, to wallahi ko a mafarkin ma ba zaki bar gidan nan ba.” Zahra ta dinga kallon ta jiki a sanyaye, Anty Khadijah ta miƙa mata ledar tana cewa“Ba fa wani abun zaki yi ba, kawai a abinci zaki zuba mata, Da zarar ta cinye shikenan! Sai yanda ki ka yi dasu duka” Zahra ta ɗan kalleta sai kuma ta amsa ledar tana kallon ta. Anty Khadijah ta gyara zamanta ta ce“Idan har kin yi yanda na ce to babu wanda ya isa ya raba ki da mijin ki, Ita kanta sai yanda ki ka yi da ita! Kawai a abinci zaki zuba. Ki duba girkin da tafi so ki yi mata, Idan ba haka ba ki ci gaba da zama ran ki na ɓaci a banza” Zahra ta sauke numfashi ta ce“Toh Anty. In sha Allah zan yi, ai abinci ne kawai, zan kai mata” Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya Anty Khadijah ta sauke kafin ta ce“To shikenan, Allah ya bada nasara. Ni bari ki ga na je” Ta ƙare maganar tana tashi tsaye. Itama Zahran miƙewa ta yi har sannan maganin na hannunta ta ce“Da wuri haka, da kin bari na gama abincin dare” Girgiza kai Anty Khadijah ta yi ta ce“A’a ba zan bari ba wallahi. Sauri nake, Wai ina yarinyar ne?”
Taɓe baki Zahra ta yi ta ce“ai kin san tun da muka zo gidan nan tana apartment ɗin su, bata taɓa kwana anan ba, daga mu sai shi.” Jin jina kai Anty Khadijah ta yi cike da fahimta ta ce“To kin ga idan kin yi komai yanda ya dace sai dai ta yi ta zama a can!” Murmushi Zahra ta yi a sanyaye ta ce“Kai Anty, da wuri haka?”
“Kina ɗauka wasa ne Zahra?”
Girgiza kai ta yi har sannan tana murmushi, Anty Khadijah ta ce“To ki gwada ki ga, wallahi zaki yi mamaki”
“In sha Allah Anty zan yi, gobe goben nan ma”
Zahra ta yi maganar tana kallon ta. Jinjina kai Anty Khadijah ta yi ta ce“To Allah ya kai mu, Sai mun yi waya” Sallama suka sake yi sannan ta fice daga parlon, Zahra ta koma ta zauna tana sauke numfashi.
****
Nana na zaune kusa da Haule wadda ta yi shiru ta yi nisa a cikin tunani aka buɗe ƙofar ɗakin, Atta ce ta shigo hannunta riƙe da wata warmer. Nana ta dinga kallon ta ba tare da ta ce komai ba, A gaban gadon ta zauna tana kallon Haule ta ce
“Zo nan maza ga abinci na kawo miki, Yarinya ki dinga zama a haka? Sai wani abu ya samu ɗan cikin ki? To da me zamu ji? Da rashin uban sa ko kuwa da ke?”
Ita dai Haule bata ce komai ba, Sai kallon ta take. Atta ta kalli Nana wadda ta yi shiru ita ma ta ce“Ke kawon faranti nan” Tura baki Nana ta yi tana miƙe ƙafarta ta ce“Ni fa Atta na gaji” Duka Atta ta kai mata tana cewa“Kin gajin uban ki? Dalla tashi ni!” Kamar zata yi kuka ta sauka daga kan gadon ta fice daga ɗakin. Zaune ta hange shi kan kujera, Abba na kusa da shi yana masa magana, Nana ta tsaya a wajen tana kallon sa, gaba ɗaya kamar bashi ba, Ya ɗan yi duhu ya kuma rame. Ta jima a wajen ganin bai ganta ba ya sanya ta nufi kitchen ɗin da sauri, Koda ta dawo parlourn bata same shi ba sai Abba kawai. Ta kalleshi ta ce“Abba!”
Kallon ta Abba ya yi ya ce“Na’am Nana”
“Ina uncle ya tafi?”
Ta tambaya tana kallon sa itama. Dan murmushi Abba ya yi yana miƙe tsaye ya ce“Naji ya ce apartment ɗin Hajiya Babba zai je” To kawai ta ce sannan ta nufi ɗakinta da sauri. Miƙawa Atta plate ɗin ta yi, Atta ta warce tana cewa“Ke ban da banza ina ta jiran ki yarinya mai ciki kin bar ta da yunwa?” Tura baki Nana ta yi ta ce“To wai ba gashi na kawo miki ba?” Harararta Atta ta yi ta ce“Ki je dan kan ki, Ke kin zauna sa’annin auren ki duk sun kusa haihuwa ana ta abun arziki ke kin zauna!” Tura baki Nana tayi ta juya tana cewa“Ni ina ruwana! Ni yar iska ce to?”
Riƙe haɓa Atta ta yi tana ƙoƙarin buɗe warmern gabanta ta ce“Kaji banza! Dan uba ki ƙarya ki ke yi ki ce baki san namiji ba, dama a ce bashi bane da sai na yarda!” Ita dai Nana kallon ta kawai take sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin. Babu kowa a parlorn dan haka ta fice da sauri, Tafiya ta dinga yi tana ɗan kalle-kalle. A bakin kofar gidan Hajiya Babba ta tsaya tana tunani, Can kuma ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Shi kaɗai ta hango kan kujera yana danna wayarsa, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ƙarasa ciki, Tsayawa tayi a gabansa a sanyaye ta ce
“Uncle!”
Jan hannunta ya yi ya zaunar da ita kan cinyarsa bayan ya ajiye wayar hannunsa ya ce“Na’am Nana, Kin ɓuya” Kwantar da kanta ta yi akan ƙirjinsa a shagwaɓe ta ce“To ai kaina baka nemana” ɗan waro idanunsa ya yi ya ce“Ni ɗin?” Gyaɗa masa kai ta yi, Ya ɗan murmushi ya ce“To na tuba. Ban samu sukuni bane, amma da zarar na samu ai zan neme ki” Shiru ta yi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa, Sun jima a haka kafin ta ɗago kanta tana kallon sa ta ce“Uncle!”
“Babyn uncle!”
Ya ce yana ɗaga mata gira.
Murmushi ta yi ta ce“ka ci abinci?” Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi shima, Ta ɗan haɗe rai ta ce“Ni wallahi baka ci ba!” Ɗan zaro idanu ya yi ya ce“Ni na ce miki?” Tana ƙoƙarin yin magana aka buɗe ƙofar parlourn, Sultan ne ya shigo sai kuma ya sunkuyar da kansa a sanyaye ya ce“Afwan pls” Ya juya ya fice daga parlon, Shiru Nana ta yi lokaci ɗaya jikinta ya yi sanyi, Abdusammad da ke lura da ita ya ce
“Mene ne?”
Girgiza masa kai ta yi ta ce“Ba komai.”
“Kin tabbata?”
Ya ce yana kafeta da idanu, Gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh uncle” Murmushi ya yi ya ce“Alright” Ya yi maganar yana jan kumatunta. Murmushi ta yi sai kuma ta sauka daga jikinsa ta ce“Na tafi kada Amma ta neme ni” Gyaɗa mata kai ya yi dan bai ji zai iya riƙe tan ba ya ce“Okay bye” ta ɗaga masa hannu sannan ta fice daga parlourn.
Da daddare bayan ya shiga gidan ya tarar da Zahra har ta yi shirin kwanciya. Bai ce komai ba ya juya zai bar dakin, Ta miƙe zaune ta ce“Doctor!”
Cak ya tsaya, Ta ɗan yi murmushi ta ce“Daman zan tambaye ka ne”
“Mene?”
Ya ce yana juyowa,
“Wane abinci Hajiya Babba ta fi so?”
Da ɗan mamaki ya ce“me zaki yi da sanin hakan?” Girgiza kanta ta yi ta ce“A’a fa kawai dai na tambaya ne, ka faɗa min idan ba damuwa” Numfasawa ya yi ya ce“Tuwon shinkafa miyar egusi” Murmushi Zahra ta yi ta ce“na gode.” murmushin shima ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin, Zahra ta sauke numfashi sai kuma ta kwanta.
****
Anty Khadijah na ƙoƙarin rufe jikinta da duvet wayarta dake gefen gadon ta fara ƙara, ta sanya hannunta ta dauka ganin lambar Kaddu ya sanya ta ɗaga wayar tana murmushi ta ce
“Ƙawata ya aka yi? Fatan komai na tafiya dai-dai?” Murmushi Anty Khadijah ta yi ta ce
“Ke dai bari, na bata kuma ta amsa, nan bada jimawa ba zan yi Wuff…”
“Dashi!”
Kaddu ta ƙarasa tana dariya, tuntsirewa da dariya Anty Khadijah ta yi ta ce
“Nan bada jimawa ba zan zama matar Abdusammad, Zahra kuma zata fito, ita da waccan yarinyar!”
Murmusawa Kaddu ta yi cike da nishadin jin abin da ta ce, Anty Khadijah ta ce“Ke ni sai da safe dare ya yi” Sallama suka yi sannan ta kashe wayar, Ta kwanta tana tunanin irin rayuwar da zata yi a gidan Abdusammad Idan ta aure shi.
****
Washegari da safe Nana na zaune gefen gado tana danna wayarta aka buɗe ƙofar ɗakin, Haule ce ta shigo hannunta riƙe da ƙaramin bowl, Nana ta kalleta amma bata ce komai ba. A gefenta ta ajiye ta juya zata fita, tashi Nana ta yi tana haɗe rai ta ce“Mene wannan?” A sanyaye Haule ta kalleta kafin ta ce“Atta ce ta kawo min, wai faten dankali ne.” Yatsine fuska Nana ta yi ta sauka daga kan gadon tana cewa“Taɓ, Ai sai ki yi ta zama tana kawo miki kayan ƙazanta kina ci.” Bata ce komai ba, Itama Nanan bata tsaya sauraren abin da zata ce ba ta fice daga ɗakin, Haule ta kalli bowl ɗin dankalin sai tiriri yake, Sai kuma ta sauke numfashi ta juya ta fice daga ɗakin. Zaune ta sameta a parlon ta kunna tv tana kalla tana cin chocolate, Haule ta nufi kitchen kai tsaye, Murfi ta ɗauko ta koma ɗaki. Ita dai Nana bata kalli inda take ba, After some minutes ta tashi tana ajiye ledar chocolate ɗin ta kunce veil ɗin data ɗaura a kanta ta yafa sannan ta fice daga parlourn. Apartment ɗin Maimoon ta nufa, Koda ta shiga zaune ta sameta akan kujera ta dafe cikinta wanda ya fito sosai. Nana ta ƙarasa ciki ta zauna tana cewa



