Chapter 45: Chapter 45
“Sannu matar nan!”
Harararta Maimoon ta yi tana murmushi ta ce
“Yauwa sannun ki ƴar nan”
Nana ta tuntsire da dariya kafin ta ce“Me ki ka dafa?”
“Ni bani nayi girki ba, Ya Aliyu ne ya yi idan zaki ci”
Waro idanu ta yi tana murmushi ta ce“Shi Yaya Aliyun ne ya yi miki kirki ki ka ci? Lallai!”
Taɓe baki Maimoon ta yi ta ce“To mene ne? Ai shi ne yake girki yanzu, Saboda ni ba zan iya ba, wahala nake sha.” Jinjina kai Nana ta yi tana riƙe da haɓarta ta ce
“Eh lallai! Kin isa”
“Idan ba zaki ci ba ki tashi ki girka naki daban”
Tashi ta yi ta zare mayafin kanta ta nufi kitchen tana cewa“To tun da yunwa nake ji ai dole nayi girki.”
Ita dai Maimoon kallon ta kawai ta yi sai kuma ta ɗauke idanunta, Nana na shiga kitchen ɗin ta fara buɗe-buɗen kaya tana duba abin da zata dafa, Can dai ta yanke shawarar yin shinkafa da wake dan tana ɗaya daga cikin abincin da take so. Sai da ta tsince waken wanda ya kasance manya sannan ta wanke ta zuba a tukunya ta ɗora, Ta koma parlour tana kallo time to time tana zuwa tana dubawa, Bayan ya dahu ta zuba shinkafar wadda bata da yawa sannan ta saka gishiri da maggi ta rufe, Ta tsaya ta fara yanke-yanken kayan lambunta har ta gama, ta wanke sannan ta ajiye gefe. Bayan ta sauke abincin ta zuba a plate ta zuba salad ɗin data yanka da cabbage da cucumber ta ɓare kwai guda biyu ta ɗora akai, Robar yajin da tagani a wajen ta ɗauka ta fito parlour, Turus ta yi ganin Aliyu zaune shi da Abdusammad, Maimoon na zaune tana kallon su, Jiki a sanyaye ta ƙarasa parlourn ta ajiye wayar plate ɗin akan table ta koma ta zauna kusa da Maimoon.
“Nana daman kina nan?”
Gyaɗa masa kai ta yi sannan ta ce“Eh Yaya ina nan, ina kular maka da matarka” wata harara Maimoon ta watsa mata kafin ta kalleshi a shagwaɓe ta ce“Wallahi Yaya ƙarya take, tsokanata kawai take.” Taɓe baki Nana ta yi ta mai da Idanunta kan Abdusammad wanda bai ce komai ba tun ɗazu ta ce
“Unclee…!”
Ɗaga mata gira ya yi ya ce“Na’am”
“Ba zaka kulani ba?”
Ta tambaya tana marairaice fuska. Ɗan murmushi ya yi sannan ya yi mata alama da ta zo da hannu, Ta tashi jiki a sanyaye ta ƙarasa inda yake ta zauna gefensa. Dafa kanta ya yi murya a nutse ya ce
“Ƴar rigimar uncle”
Jingina kanta ta yi akan kafaɗarsa ta ce
“Uncle…”
Murmushi ya yi ya ce“Nana kar sunan ya ƙare”
Turo baki ta yi ta ce“To ba zan kira ka ba?” Girgiza mata kai ya yi yana kallon plate ɗin data ajiye ya ce“Ni na nace miki?” Murmushi ta yi ta tashi daga wajen tana kallon Maimoon dake kallon ta, Ta ɗauki plate ɗin ta koma inda yake ta zauna tana miƙa masa ta ce
“Uncle ga abinci da kaina na girka maka, anan gidan wai Yaya Aliyu ne yake girki..” ta ƙare maganar tana dariya, Kallon ta ya yi sai kuma ya kalli Aliyu wanda ke murmushi, Fuskarsa a tsuke ya ce
“Kai ne ka koma girkin abincin?”
Gyaɗa masa kai ya yi kafin ya ce
“Eh mana, tun da bata da lafiya ai dole na taimaketa.” Jinjina kai Abdusammad ya yi yana shafa gemunsa, Aliyu ya kalli Maimoon ya ce
“Tashi muje ciki ki kwanta”
Jiki a sanyaye ta miƙe ya yi gaba yana riƙe da hannunta, Gaba ɗaya kunyar Abdusammad ɗin ta rufeta. Shi kuwa ɗauke kansa ya yi yana taɓe baki. Bayan sun bar wajen ya mai da idanunsa kan Nana wadda ke danna wayarta, kamar ba zai magana ba sai kuma ya sanya hannu ya karbi wayar yana kalla, Game take as usual, Ya ɗan yi murmushi ya ce
“Ke ba zaki taɓa girma ba ko?”
Turo baki ta yi ta kawo hannu zata amshi wayar, Ya ɗauke yana tsuke fuska ya ce“Ina wasa da ke?”
“Uncle ka bani wayataaa.!”
Ta yi maganar kamar zata yi kuka, Bai ce komai ba ya zura a aljihunsa yana ɗauke kansa, Ta dinga kallon sa sai kuma ta fara hawaye tana cewa
“Ka bani dan Allah.”
Ba zaka taɓa cewa dashi take ba dan ko kallon ta bai yi ba, Ganin tana shirin ɓare baki ya sanya shi kallon ta fuskarsa a tamke babu alamar wasa ya ce
“Kina min kuka ina buge ki anan, Ɗauka abincin ki.”
Ya yi maganar yana nuna mata plate ɗin data ajiye a ƙasa. Kasa cewa komai ta yi, ganin yanda ya yi da fuska, Ya dauko plate ɗin abincin ya ɗiba a spoon yana kallonta ya ce
“Haaa..”
Kallon sa ta tsaya yi, Ya ajiye spoon ɗin ya rankwasheta a goshi, Dafe goshinta ta yi tana marairaice fuska kamar zata yi kuka. Ya sake diban abincin ya kai mata baki, Babu yanda ta iya haka ta buɗe bakin, Ya dinga feeding ɗinta har ta kusa cinyewa. Bayan ta gama ya ɗora mata plate ɗin akan cinyarta sannan ya ce
“Oyah tashi anan. Sai da safe”
“Sai da safe kuma? Yanzu fa rana ce”
“To ko zaki bi ni ne?”
Ya yi maganar yana miƙewa tsaye, Gyaɗa masa kai ta yi duk da bata san inda za shin ba. Bai ce komai ya juya ya fice daga ɗakin, Ta ajiye plate ɗin a wajen ta biyo bayansa tana gyara zaman mayafin kanta. A compound ɗin ta same shi yana shirin buɗe motar sa, Ta ƙaraso wajen da sauri tana cewa
“To ba zaka tsaya ni ba?”
“Za dai ki bi ni ki ka ce?”
Ya yi tambayar yana ƙoƙarin shiga motar, Gyaɗa masa kai ta yi. Ya jinjina kansa ya ce“Zagayo to” Da sauri ta koma ɗaya side ɗin ta buɗe ta shiga tana murmushi. Shi dai bai ce mata komai ba ya yi motar key suka bar compound ɗin. Tun Nana na kallon titi tana murmushi har sai da ta fara kallon sa da mamaki, ganin tafiya kawai suke yasa ta ce
“Uncle.”
Sam bai ji ta ba, Saboda yanda ta yi maganar a can ƙasa shi kuma yana bin karatun Alkur’anin da ya kunna. Ta sanya hannunta ta taɓa shi ta ce“Unclee…!” Sai a sannan ya ɗan kalleta, Ya rage volume ɗin karatun ya ce
“Mene ne?”
“Ina zamu je?”
Ta ce kamar zata yi kuka, Ɗan murmushi ya yi ya ce“Sai da ke zan yi.” Dariya ta yi ta ce
“Sai dani kuma? Ni ɗin?”
Gyaɗa mata kai kawai ya yi sannan ya ƙara volume ɗin karatunsa, Ita ma bata sake cewa komai ba ta mai da kanta jikin mirror tana kalle-kalle. A bakin wani ƙaton mansion ya ɗan yi parking, Nana ta dinga kallon gidan dan bata taɓa ganinsa ba. Horn ya danna aka zo aka buɗe gate ɗin, Ya tura hancin motar ciki. A tsakiyar compound ɗin gidan ya yi parking sannan ya kashe motar ya sakko, Nana ta buɗe side dinta ta fito tana karewa babban compound ɗin kallo. Iyakar haɗuwa wajen ya haɗu, Ya ja hannunta suka nufi main entrance ɗin gidan, Wani katon parlour ne wanda aka ƙawatashi da kujeru na alfarma, Sai tv babba sai curtains masu kyau da tsada, Bai zauna a parlourn ba ya ja hannunta suka nufi sama. Ita dai Nana sai bin sa take da kallo duk inda ya yi, Wani ɗaki ya buɗe ya shiga yana rike da hannunta, Babban bedroom ne mai ɗauke da furnitures da kuma kujera, ya saki hannun ta yana ƙoƙarin kwance agogon hannun sa..
“Bari na kwance ma”
Yaji saukar muryarta tana ƙoƙarin taɓa hannunsa. Bai ce komai ba ya dinga kallon ta har ta kwance agogon ya juya ya bar wajen ita kuma ta nufi gefen gado ta zauna tana riƙe da agogon. Tana nan zaune har kusan 20mins kafin ya fito daga toilet yana sanye da bathrobe, Nana ta dinga kallon sa dan bata yi tunanin wanka ya yi ba. Press ya buɗe ya ɗauki wasu kaya masu sauƙin nauyi ya saka sannan ya dawo gefen gadon yana kallon ta ya ce
“Ba zaki yi wanka ba?”
Girgiza masa kai ta yi kafin ta ce“Nayi ai.” Bai ce komai ba ya hau tsakiyar gadon ya kwanta, Ta daɗe zaune a wajen kafin taji ya ce
“Baki jin bacci?”
Kallon sa ta yi sai kuma ta girgiza masa kai duk da baccin data fara ji. Ya ɗan yi murmushi sannan ya jawo hannunta, A gefen sa ya kwantar da ita ya zame mayafin kanta gashinta mai kyau wanda ya sha gyara ya bayyana, A hankali ya kai hannunsa ya fara shafa gashin, Nana ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe idanun ta. After some minutes ta fara ƙoƙarin tashi zaune jin abin da yake yi ta ce
“Uncle mu tafi gida!”
Hannu ɗaya ya sanya ya dawo da ita ya kwantar yana murmushi ya ce
“Ba rakoni ki ka yi ba?”
Girgiza kanta ta yi jin yana ƙoƙarin jan rigar jikinta ta ce“a’a ni gida zan je! Wallahi gida zan je uncle…”
Bai tsaya saurarenta ba ya haɗe bakinsu ya fara sauke mata wasu irin kisses masu tsayawa a rai, Nana ta dinga ƙoƙarin kwace kanta amma hakan ya gagara dan ƙarfi ya sakar mata. Tun tana dauriya da shi har sai da ta fara kuka, amma sam bai san tana yi ba ya ci gaba da abin da ya yi niyya.. Sai da dan kansa ya haƙura ya koma gefe yana sauke numfashi.
****
Basu suka dawo gidan ba sai wajen karfe 6:00 na yamma, Yana gama parking ta buɗe motar ta fita babu ko sallama, Murmushi kawai ya yi yana girgiza kansa sannan ya yi gaba, Bayan ya fito daga motar yana ƙoƙarin shiga gidan Noor ta tawo da gudu ta rungumeshi tana dariya. Sunkuyawa ya yi ya ɗauketa yana murmushi ya ce
“Noor ina ki ka je?”
“Naje wajen Anty Juwaira ne Abbie.”
Jinjina kansa kawai ya yi sannan ya buɗe kofar suka shiga, Babu kowa a parlourn sai tashin ƙamshi da yake. Ya kalleta ya ce“Muje ciki ko?” gyada masa kai ta yi suka nufi upstairs tare, Zahra dake kitchen tana girki sam bata ji shigowar su ba. Ta ƙarasa kwasar kayan abincin ta fita dasu ta ajiye a parlourn, Da sauri kuma ta koma kitchen ɗin, ledar maganin data zuba ta ɗauka ta yar a shara sannan ta gyare ko ina ta fito. Zaune ta same shi a parlour yana danna wayarsa, ta dinga kallon sa da mamaki can kuma ta ce
“Doctor dama ka dawo?”
Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh na dawo, Ai naga kamar kina aiki ne” Murmushi ta yi ta ce“Ai na gama ma, Daman abincin Hajiya Babba ne.”
“Kin yi abincin ne?”
Gyaɗa masa kai ta yi tana murmushi, Ya ɗan jinjina kansa fuskarsa a sake ya ce“Su Hajiya masu surukai. To maza ki kai mata”
“Zan fara wanka ne”
Toh kawai ya ce, Ya nufi sama da sauri. Ko minti biyar bata yi da hawa ba Noor ta sakko tana riƙe da teddy ƙato a hannunta, Ta ƙaraso wajensa tana dariya ta ce“Abbie!” Murmushi ya yi ya ja kumatunta ya ce
“Nooriya!”
“Abbie yunwa nake ji!”
Ta yi maganar tana yatsine fuska, Girgiza kansa ya yi ya ce“Da gaske? Ko zaki ci tuwo to?” gyaɗa masa kai ta yi, Ya kalleta sai kuma ya kalli inda Zahra ta ajiye warmern ya ce
“To bari na baki.”
Daga haka ya tashi ya ƙarasa gaban warmern, A kitchen ya saka ta ɗauko plate ya buɗe warmern farko, Tuwon shinkafa ne wanda ya yi kyau an zuba shi a ledoji, Ya ɗauki ɗaya ƙarami ya raba biyu ya saka mata rabi dan ya san ba cin abinci take ba, Sannan ya buɗe ɗayan ya ga miyar egusi ce lafiyayya, Da ɗan yawa ya zuba mata miyar ya miƙa mata, Karɓa ta yi sannan ta yi masa kiss a kumatu ta ce
”Thank you Abbie.”
Murmushi kawai ya yi sannan ya tashi ya koma kan kujera ya zauna, Itama ta koma can kujerar da ke kusa da tv ta zauna ta fara cin tuwon tana lumshe ido.
Amma ta dinga kallon ta babu yabo babu fallasa ta ce“Shi ne ki ka yi wannan daɗewar?” Sunkuyar da kanta ta yi a sanyaye ta ce“Eh fa Amma. Kuma ai har da uncle ma yana can” Taɓe baki ta yi ta tashi tana kallon ta ta ce“Tashi ki dafa min shinkafa”Toh kawai ta ce sannan ta miƙe ta nufi kitchen duk da yanda take jin jikinta babu gwari. Ruwan shinkafar kawai ta ɗora ta fito ta dawo parlour ta zauna tana jiran ya tafasa, Haule dake zaune kan kujera ta kalleta ta ce“Nana ɗazu Atta ta ce na kira ki” Kallon ta Nana ta yi tana riƙe da wayarta ta ce“To ni ba zan je ba wallahi, haka kawai ta dinga zagina.” Ita dai Haule bata sake cewa komai ba ta ci gaba da kallon ta, After some minutes ta tashi ta koma kitchen ɗin dan duba abin da take.
****
Zahra ta sakko tana kallon Noor dake cin tuwon a hankali dan daman ita ba gwanar cin abinci ba ce, Da mugun mamaki ta ƙaraso wajen, Ta ɗago kanta hankali a ɗan tashe ta ce
“Ke! Wane ya baki wannan abincin?”
Noor ta kalleta ganin yanda take zare ido ya sanyata sunkuyar da kanta, Ta daka mata tsawa ta ce
“Ba magana nake miki ba?”
Sai a sannan Abdusammad ya kallesu dalilin tsawar da yaji, Ya buɗe baki cike da mamakin ganin yanda ta cakume yarinyar ya ce
“Zahra lafiya dai?”
Kallon sa ta yi sai kuma ta mai da Idanunta kan Noor ta ce“Ba zaki faɗa min ba? A ina ki ka samu tuwo?”
“Abincin da zaki kai wa Hajiya Babba ne na ɗibar mata tana jin yunwa, mene?”
Wani irin abu ne ya zo ya tsaya mata a ƙirji, Ta saki rigar Noor tana jin zufa na yanko mata, Abdusammad da ke lura da ita ya ce“Ko akwai wata matsala ne?”
Girgiza masa kai Zahra ta yi tana ƙoƙarin magana Noor ta saki wani irin ihu tana wurgi da plate ɗin hannun ta. Da sauri ya taso ganin yanda take ƙandare jiki tana dafe da cikinta, Zahra ta yi saurin durƙusawa gabanta ta riƙeta tana jijjigata, Yana zuwa ya sanya hannunsa ya ɗauketa ya zauna akan kujerar ya riƙe fuskarta ya ce
“Ke Noor! Noor mene ne?”
Ɗan ƙaramin hannunta ta saka ta riƙe nasa muryarta na rawa ta ce
“Ab…Abbi… Abbiena..”
Wani irin faɗuwar gaba yaji ya ziyarce shi, Ya riƙeta sosai a jikinsa ya ce“Mene ne?”
Kasa magana ta yi sai kuka da take a hankali, Ya kalli Zahra wadda ke kuka ita ma ya ce“Kawon ruwa” Toh kawai ta ce sannan ta nufi kitchen da gudu, Abdusammad ya tallafi fuskarta a hannunsa yana kallon ta ya ce
“Nooriena, Me ya faru?”
Ta kasa magana sai hannunsa data ɗora kan cikinta ta runtse ido, Kallon cikin ya yi sai kuma ya taba wuyanta yaji wani irin zafi, Gaba ɗaya sai ya rikice, dan bai san abin da ya sameta ba. Ya girgiza kansa ya ce
“Cikin ki ne yake miki ciwo?”
Gyaɗa masa kai ta yi tana ƙoƙarin magana sai ga dafara ta fara fitowa daga Bakinta. Abdusammad ya miƙe tsaye da ita a hannunsa cikin wani irin yanayi mai kama da tashin hankali ya ce
“Noorie stay still, Bari na kai ki asibiti.”
“Abbiena…!”
Yaji ta kira sunansa idanunta na neman rufewa, Hannunsa ya sanya ya bubbuga fuskarta ya ce“Na’am Noor!” Bata ce komai ba ta buɗe Idanunta wanda hawaye ke zubowa ta gefensu ta kalle shi, Sai kuma ta sake rufewa. Ji ya yi ta kwanto a jikinsa, Jikinta ya saki gaba ɗaya, Da wani irin tashin hankali ya ɗagota ya tallafeta a hannunsa yana girgizata ya ce
“ke! Ke Noor! Noor!”
Shiru babu amsa, Ya sauketa a wajen ya shiga taɓa jikinta, Babu alamar tana numfashi. Zahra ta dawo parlourn hannunta riƙe da cup da ruwa, Ta yi saurin sakin su a ƙasa ganin yanda yake kiran sunan Noor ɗin bata amsawa. Durƙushewa ta yi a gabansu ta fara ƙoƙarin tashin ta tana kuka, Abdusammad ya yi jim sai kuma ya ɗauketa ya fice daga parlourn da sauri. Da gudu Zahra ta biyo bayansu, Ta tarar har ya shiga back seat tabi bayansu da sauri.
****
Amma ta toshe hancinta saboda ƙaurin da taji, Ta ƙarasa gaban gas ɗin dakyar ta buɗe tukunyar. Gaba ɗaya shinkafar ta yi baƙi ta babbake, Sai ƙauri ke tashi, ta kashe gas ɗin sannan ta juya ta fice daga kitchen ɗin rai ɓace tana kiran sunan Nana..
A parlour ta sameta tana baccinta hankali kwance, Amma ta kai mata duka tana kiran sunanta a fusace. Buɗe idanu Nana ta yi ta dinga kallon Amma sai kuma ta tashi zaune tana mitsitsika idanu, Amma da ranta yake a ɓace ta ce
“wani sabon iskancin ne ya sanya ki ka bar min abinci ya babbake? Meke damunki Nana?”
Saurin rufe bakinta ta yi da hannunta sai kuma ta tashi tsaye tana ɗaukan hular ta ta ce“Wallahi bacci ne ya ɗaukeni Amma..” ta nufi kitchen ɗin da sauri, Tana shiga ta samu Amma ta kashe gas ɗin, Ta buɗe tunkuyar sai kuma ta yi saurin rufe bakinta tari na tawo mata. Rufewa ta yi ta juya ta fice daga ɗakin, A tsaye ta samu Amma inda ta bar ta, Ta dinga kallon ta ganin irin yanda ta haɗe rai, Jiki a sanyaye ta ce
“Ki yi haƙuri Amma, wallahi….”
Dakatar da ita Amma ta yi ta hanyar ɗaga mata hannu, Rai ɓace ta fara cewa
“Wato ke ba zaki taɓa hankali ba? Ba zaki nutsu ba? Mene ne amfanin auren da ki ka yi? Haka ki ke a gidan mijin ma kina bari ana zagina. Ace common white rice ba zaki iya dafawa a nutse ba? Uban ki ki ke yi?”
Girgiza kai Nana ta yi jiki a sanyaye ta ce
“Dan Allah Amma ki yi haƙuri, baccin ne ya ɗaukeni ban sani ba.”
“Ai dole bacci ya ɗauke ki! Dole mana! Tun da baki san abin da ki ke ba. To na rantse duk ranar da ki ka sake yimin irin wannan abun sai ran ki ya yi mummunan ɓaci, Kuma ki sani daga yau har ranar da zaki bar garin nan ke ce zaki dinga girka abinci, Ke zaki dinga aiki, duk wani abu da ki ka san ana yi a gida kece zaki dinga yin sa. Idan kin so ki ci gaba da ba dai-dai ba!”
Amma ta ƙare maganar tana harararta, Sai kuma taja tsaki ta bar wajen, Ita dai Nana bata iya ko motsi ba, Dan ta san halin faɗan Ammar. Sai da taga ta shige daƙinta sannan ta ƙarasa kan kujera ta zauna, Ko minti biyu kuma bata yi ba ta kwanta wani baccin ya sake ɗauketa..
****
Tun da aka shiga da ita yake kai komo a wajen, Zahra kuwa sai kuka take ta ɗora hannunta aka. Kusan 30mins kafin Sultan ya buɗe ƙofar ɗakin ya fito, Da Sauri Abdusammad ya ƙarasa gabansa muryarsa a dake ya ce
“Ya jikin nata? What happened to her?”
Kallon sa Sultan ya dinga yi, ya kasa cewa komai. Abdusammad ya ɗan kanƙance idanunsa kafin ya ce
“Sultan mene haka? Do i look like ur mate?”
Girgiza masa kai ya yi, Abdusammad ya kalle shi sai kuma ya sanya hannu ya hankaɗeshi daga wajen ya buɗe ƙofar ɗakin ya shige. Zahra na ganin haka tabi bayansa da sauri, Sultan ya sauke wani zazzafan numfashi hawaye na biyo idanun sa.
Kwance Abdusammad ya sameta, Sai dai ya kasa gane dalilin daya sanya suka rufeta har fuska, Ya ƙarasa gaban gadon ya zauna ya buɗeta. Fuskarta fresh kamar wadda ke murmushi, asalin kamarta dashi ya sake bayyana, Ya kai hannunsa ya taɓa ta a sanyaye ya ce
“sorry ƴar gidan Abbie, zaki samu sauƙi.”
Zahra dake tsaye ɗan nesa dashi ta kalleta jin abin da ya ce. Ta sauke ajiyar zuciya tana dafe ƙirjinta, Sultan ne ya shigo ya tsaya a ɗaya side ɗin gadon yana kallon su, Ganin yanda yake ta nanata zata samu sauƙi. Sun daɗe a haka kafin Abdusammad ya mai da bargon ya rufeta amma ban da fuskarta, Ya tashi tsaye yana kallon Sultan ya ce
“Me ya sameta?”
Kallon sa kawai Sultan ya yi idanunsa cike taf da hawaye. Abdusammad ya girgiza kansa rai ɓace ya ce
“Sultan yaushe ne na fara wasa da kai?”
Jiki a sanyaye ya girgiza kansa yana ƙoƙarin ɓoye damuwarsa ya ce
“Yi haƙuri Yaya. But we lost her!”
Tamkar mafarki, ko kuma almara haka Abdusammad yaji kalaman Sultan na ƙarshe. Ya ɗan ware idanun sa yana son fahimtar abin da ya ce, Sultan ya sake Girgiza kansa wannan karon hawaye na zubowa kan fuskarsa ya ce
“Yaya a ina Noor ta samu guba? Wane ya bawa Noor abinci? A ina ta samu guba!”
Wani irin ihu Zahra ta saki sai gata a ƙasa Sumammiya, Abdusammad da ya kasa koda motsi daga inda yake ya sunkuyar da kansa sai sauke ajiyar zuciya yake akai akai. Da sauri Sultan ya nufi inda Zahra take yana kallon ta, Sai kuma ya fice daga ɗakin da sauri, Not too long suka dawo tare da wasu nurses mata guda uku, Akan wheelchair suka ɗorata suka fita daga ɗakin. Har sannan Abdusammad bai motsa daga inda yake ba, Gumi ne kawai ke tsatsafo masa duk da acn dake wajen, Zuciyarsa ta kasa yarda da abin da Sultan yake, Tunanin sa ya tsaya cak, ƙwaƙwalwarsa ta toshe. Yana nan tsaye har after 15mins Sultan ya dawo, Ya dinga kallon sa cike da tausayawa, Ya san ba lallai a fahimci halin da yake ciki ba, domin kuka ko magana baya ɗaya daga cikin abin da yake yi yayin da baƙin ciki ya yi masa yawa. Sultan ya sauke numfashi ya ƙarasa inda Noor take ya rufe mata fuskarta, Yana ƙoƙarin ɗagowa yaji Abdusammad ya riƙe hannunsa gam, Cikin wata irin kakkausar murya ya ce
“Don’t ever try that!”
Sultan bai ce komai ba ya janye jikinsa ya bar ɗakin, Abdusammad ya zauna gefen gadon ya ɗaukota ya ɗora a jikinsa, Ya sanya hannunsa ya tallafi fuskarta muryarsa a sanyaye ya fara cewa
“Noorie! Noorien Abbie, Kina jina ko? Kina ji ko? Ai ƙarya suke yi na sani, babu abin da ya same ki, kina nan tare da Abbie, Ba zaki bar ni ba na sani. I know!”
Bata bashi amsa ba, Domin bata jin abin da yake cewa, ruhin ta ya yi ƙaura daga gangar jikinta, Jin bata ce komai ba ya sanya shi girgiza kansa yana ɗan murmushi ya ce
“Fushi ki ke yi da Abbie? Ki yi haƙuri kin ji. Next time zan kawo ki asibiti da wuri, But…!”
Sai ya sami kansa da yin shiru, Ya zubawa kyakkyawar fuskarta ido yana kallon ta, ba zaka taɓa cewa bata raye ba, Kamar bacci take..irin baccin data saba yi da yamma ta tashi bayan magriba, Wani lokacin kuma idan ta yi baccin shikenan sai gobe. Yana nan zaune sama da mintina ashirin bai sani ba, Shi kansa bai san a wane hali yake ba. Idanunsa dai har sannan na kan fuskarta, Buɗe kofar ɗakin aka yi, Ya daga idanunsa yana kallon su. Abba ne ya shigo sai Aliyu a bayansa, Ya yi saurin cewa
“Yauwa Abba zo kaji wai Noor ce taci guba? A ina Noor ta samu guba?”
Girgiza kai Abba ya yi ya janye Noor daga hannunsa ya miƙawa Aliyu, Abdusammad zai yi magana Abba ya kama hannunsa a sanyaye ya ce



