Chapter 46: Chapter 46
“Muje gida tukun”
“But Abba ai bata ji sauki ba, Ya za’a yi mu tafi gida da ita a haka? At least ta samu lafiya”
Abba ya gama gane ba fahimta yake ba, Dan haka ya shafa kansa ya ce
“To shikenan sai a dawo da ita. Muje yanzu kaji”
Bai ce komai ba yabi bayan Abba dan tuni Aliyu ya fice da ita. A compound ɗin Hajiya Babba suka yi parking, Abba ya fito yana kallon Abdusammad wanda ko motsi bai yi ba, Zagayowa ya yi ya kama hannunsa ya fito daga motar ya ce
“Abdussamad muje”
Gyaɗa masa kai kawai ya yi sannan suka nufi cikin gidan Hajiya Babba, Shimfiɗe ya samu Noor akan carpet an rufeta da farin kyalle har kanta, Ya yi saurin sakin hannun Abba ya ƙarasa ya yaye kyallen cikin ɓacin rai ya ce
“Bana son irin haka! Kada wanda ya sake rufe min ƴa, akan me?!”
Shiru duk suka yi, Hajiya Babba da ke zaune ta dinga kallon sa, Tausayi ya bata ta san irin son da yake yi wa Noor ɗin, Ta san irin shaƙuwar da ke tsakaninsa da ita. Dan haka ta san dole zai shiga hali na ɗimuwa. Abba ne ya yi ƙarfin halin zuwa gabansa ya dafa shi, Abdusammad ya ɗago idanunsa ya kalleshi sai kuma ya tashi tsaye ya ce
“Abba ka ce su daina rufe min ita, akan me? Me ta yi musu? Yarinyar nan karama ce sai ta kasa numfashi?”
Girgiza kai Abba ya yi yana jin wani irin zafi a ransa, Ya dafa shi hawaye na ƙoƙarin fitowa daga cikin idanunsa ya ce
“Abdul ka yi haƙuri kaji! Allah shi ne ke bada haihuwa, Shi ne ke bamu ɗa, kuma shi ne ke karɓa a duk sanda ya so, Duk mai rai mamaci ne, dole sai kowa ya mutu. Dan haka ka ɗauki haƙuri, Allah ya yi mai ƙaramin kwana ce, Allah ya yi ba zaka girma da ita ba, Ka yi haƙuri!”
Janye hannun Abba ya yi daga jikinsa ya ce“Bangane ba Abba, meya sameta to?”
“Ta mutu!”
Abba ya faɗa kai tsaye, Wani irin abu ne ya zo ya tokare masa a ƙirji, Ya ja wani irin dogon numfashi sai kuma ya dafe kansa saboda sara masan da ya yi. Abba ya riƙe shi ya ce
“Ka nutsu dan Allah.”
Jinjina kansa ya yi ya juya yana ƙoƙarin komawa inda take, Sai dai kafin ya ƙarasa yaji kamar an daki ƙirjinsa sai gashi a ƙasa a sume.
A hankali ya shiga buɗe idanunsa wanda suka yi masa nauyi, Motsin da taji ya sanyata riƙe shi muryarta a sanyaye ta ce
“Uncle.”
Kallon ta ya yi amma bai ce komai ba, Nana ta shiga goge hawayenta tana kallon sa. Buɗe kofar ɗakin aka yi, Abba ya shigo yana kallon su ya ce
“Nana ya tashi ne?”
A sanyaye ta gyaɗa kanta tana janye hannunta daga nasa, Abba ya ƙaraso wajen ya zauna gefen gadon yana kallon sa ya ce
“Abdul ya jikin?”
Lumshe idanu Abdusammad ya yi kafin ya ce
“Abba da gaske Noor ta mutu?”
Wani irin abu ne ya tsayawa Abba arai, Ya jinjina masa kai a sanyaye. Bai ce komai ba ya sake rufe idanunsa, Abba ya kalli Nana wadda ke kuka a hankali ya ce
“Tashi ki je ina zuwa.”
Toh kawai ta ce sannan ta mike ta fice daga ɗakin, Abba ya gyara zamansa yana kallon sa sosai a nutse ya ce
“Ka yi haƙuri Abdusammad, na sani babu daɗi, kowa ma yaji babu daɗi. Amma dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri, kayi mata addu’a, Allah yasa mai ceto ce.”
A hankali ya tashi zaune, Abba ya dinga kallon sa jin bai ce komai ba. Can ya sauke numfashi ya ce
“Ba komai Abba, Na sani Allah ya jiƙanta.”
Sosai Abba yaji sanyi a ransa, dan ya san tun da ya ce haka to ya bar zancen. A sanyaye ya sauka daga kan gadon ya nufi toilet, Abba ya tashi ya fice daga ɗakin shima.
Ban da kuka babu abin da Zahra ke yi tun bayan da aka sanar da ita mutuwar Noor ɗin, Ta zama tamkar wata zararriya, Ta rasa inda zata kama. Tunanin ta ɗaya, maganin da ke cikin abincin ne ya kashe Noor ɗin? To akan me? Dama maganin mutuwa ne?. Tana nan zaune aka buɗe ƙofar ɗakin, A hankali ta ɗaga idanunta tana kallon sa. Tsaye yake ya harɗe hannayensa a ƙirji, Idanunsa sun ɗan janye sun yi jajur dasu. Sai da gabanta ya faɗi saboda irin kallon da taga yana yi mata, Ya sauke nunfashi ba tare da ya ce komai ba. Itama kasa magana ta yi sai hawaye dake zubowa kan fuskarta, Sun daɗe a haka sai kawai taga ya juya ya fice daga ɗakin without saying anything. Zahra ta dinga kallon wajen daya bari cike da mamakin abin da ya hana shi maganar, Yana fita ɗakinsa ya nufa, Ya zauna gefen gado ya yi shiru yana tunani, Can kuma ya tashi ya shige toilet.
****
Washegari da safe wajejen ƙarfe 8:00 aka kai Noor, Tun da suka dawo bai ce da kowa komai ba ya nufi cikin gidansa. Yinin ranar babu wanda ya gan shi, A ɓangaren Zahra kuwa suna zaune a parlourn ta ita da Anty Khadijah, Amal, Safeena da kuma Siyama. Ta yi kuka har ta gaji, Ta suma yafi sau biyar, Daga ƙarshe ta haƙuri ta yi shiru sai kukan zuci. Haka ma Nana ta yi kuka har ta gaji, Duk yanda Amma ta yi da ita ƙin cin abinci ta yi, Sai kuka sai tunani. Bayan kwana uku kowa ya watse, Sai wanda abun ya shafa. Ranar Litinin around 9:00am Aliyu da Sultan suka shigo parlour, Yana zaune gefen Abba ya yi shiru idanunsa a lumshe. Hajiya Babba na zaune akan kujera tana kallon su, Bayan sun zauna suka gaisar da kowa sannan wajen ya yi shiru. Papa ne ya fara cewa
“Sultan muna jin ka”
Sauke zazzafan numfashi Sultan ya yi kafin ya ce
“Papa na rasa abin cewa, Wane ya sanya guba a cikin abinci?”
Shiru duk suka yi, Can dai Abba ya ce
“Sultan kun duba sosai kuwa? Guba kuma? Me ta ci? Wane ya bata abincin?”
“Ni ne na bata!”
Kamar daga sama suka ji muryar tasa, Kallon sa duk suka yi, amma ga mamakin su sai suka ga basu yake kallo ba, Hasalima idanun sa a lumshe suke. Abba ne ya ce
“To a ina aka samu guba Abdusammad?”
Sai a sannan ya buɗe idanun sa, Sosai suka yi jaa, Hawaye ya kwanta a cikinsu. Ya sauke numfashi sannan ya ce“Nima ban sani ba Abba. Pls excuse me!”
Ya yi maganar yana miƙewa tsaye, Bai tsaya jiran abin da zasu ce ba ya fice daga parlourn da sauri. Shiru duk suka yi suna mamakin abin da ya faɗa ɗin, Papa ya sauke numfashi yana girgiza kansa ya ce
“Allah ya kyauta.”
“To a ina aka samu guba a cikin abincin? Ni ban gane ba”
Aliyu ya yi maganar a dame, Ajiyar zuciya Papa ya sauke sannan ya ce
“Kawai abar maganar tun da baya so a yi.”
“But Papa…”
Ɗaga masa hannu Papa ya yi, Ya miƙe tsaye yana gyara zaman rigarsa ya ce“Ya isa haka nace!”
Ya yiwa Hajiya Babba sallama sannan ya fice daga parlourn, Ita ma tashi ta yi ta nufi sama ba tare da ta ce komai ba. Abba ya kalli Aliyu wanda ya yi shiru ya ce
“Ka bar maganar ka ji, Zan yi masa magana”
Gyaɗa masa kai ya yi a hankali, Abba ya tashi ya fice daga parlourn shima. Taɓe baki Sultan ya yi ya ce“Ai shikenan, amma wallahi Yaya guba ce a ciki, Kuma a abin da ta ci ne.”
Da mamaki Aliyu ya ce“To akan mene yasa baya son a yi maganar?”
Girgiza kai Sultan ya yi ya ce“Nima ban sani ba Yaya, But definitely there is something fishy.”
Shiru Aliyu ya yi can kuma ya gyaɗa kansa ya ce“Dole na nemo mene ne. I’m coming” Ya ƙare maganar yana tashi tsaye, Sultan bai ce komai ba har ya fice daga parlon, Shima ya tashi yabi bayansa.
****
Nana na zaune kan gado ta yi shiru tana tunani, Amma ta buɗe ɗakin ta shigo tana kallon ta.
“Naana.”
Amma ta kira sunanta, A hankali ta buɗe idanunta, a sanyaye ta ce“Na’am Amma!.”
“Ki tashi ki yi breakfast.”
“Na ƙoshi”
Ta ce a hankali, Da mamaki Amma ke kallon ta, Can kuma ta ce“Da ki ka ci me?”
Bata ce komai ba sai yamutse fuska take, Amma ta harareta ta ce
“Malama tashi na ce!”
Madadin ta tashin sai kawai ta fara kuka, Amma ta yi tsaye tana kallon ta. Can kuma ta ƙarasa gaban gadon ta zauna ta jawota, Faɗawa jikinta tayi tana sakin wani marayan kuka, Amma ta dinga shafa kanta without saying anything, Cikin kuka Nana ta ce
“Amma shikenan Noor ta mutu ta bar mu? Shikenan Amma, ba zan sake ganinta ba? Amma ya zan yi?”
Girgiza kai Amma ta yi, Ita ma jikinta a sanyaye ta ce“ki yi hakuri Nana, Allahn daya bamu ita shi ne ya ɗauketa, Babu yanda zamu yi sai dai mu yi haƙuri kin ji. Ki daina kuka”
Bata ce komai ba ta ci gaba da kukanta tana jikin Amma, After some minutes Amma ta ɗagota ta ce
“Tashi muje ki ci abinci.”
Bata yi musu ba ta tashi daga jikinta, Amma ta sauka daga kan gadon tana riƙe da hannunta suka fice daga ɗakin.
****
Ya jima zaune gefen gadon yana jujjuya pen ɗin hannunsa, Can dai ya sauke numfashi ya tashi ya ɗauki car key ɗinsa ya fice daga ɗakin. Zahra na zaune akan sofa a ƙasa ta zuba uban tagumi, Ya ƙaraso parlourn yana kallon ta ya ce
“Zahra ko zaki rakani?”
A sanyaye ta kalle shi, dan rabon da ya yi mata magana tun ranar da Noor zata mutu, Ta yi saurin gyaɗa masa kai tana tashi tsaye. Bai ce komai ba ya ja ya tsaya, ta gane abin da yake nufi dan haka ta nufi sama da sauri, After some minutes ta dawo sanye da hijabi har ƙasa, Ya nufi waje tana biye dashi. Wata black Lexus ɗinsa dake compound ɗin gidan ya shiga, Zahra ta buɗe passenger seat ɗin ta shiga a hankali. Sai da ya yi warming motar sannan ya bar gidan, Tun da suka fara tafiya babu wanda ya ce komai, Can dai ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin
“Can i ask you?”
Gyaɗa kanta ta yi kafin ta ce
“Eh doctor.”
Jinjina kansa ya yi sannan ya ce“Zahra faɗa min, ina miki wani abu wanda baki so?”
Da ɗan mamaki ta kalleshi can kuma ta ce“But doctor…”
Kallon ta ya yi wanda ya sanyata yin shiru, Ya ɗan yi murmushi kafin ya ce“Kawai tambaya nayi fa” A sanyaye ta girgiza kanta ta ce“A’a doctor, kana zaune dani saboda Allah, baka cutar dani, kai mutum ne wanda kowa yake so. Kana da kyan hali, kana da kawaici, Sannan kuma kana da ilimi. A duk zaman da muke tare baka taɓa cutar dani ba, Ina jin daɗin zama da kai, Hasalima wasu lokutan ni ce nake ɓata maka.” Zahra ta ƙare maganar tana murmushi, Sai da ya sha kwana sannan ya jinjina kansa ya ce
“Really?”
Ta sake gyaɗa kanta tana murmushi. Murmushin ne shi ma ya kwace masa, Ya gyaɗa kansa fuskarsa a sake ya ce“Kenan ban cutar dake? Kin tabbata?” langwaɓar da kai ta yi ta ce“Eh mana doctor.” Shiru Abdusammad ya yi kamar me tunani, Can kuma ya sake kallon ta ya ce“kin tabbatar da hakan Zahra?” Shiru Zahra ta yi jin abin da ya sake cewa. Ta tura baki tana kallon titi ta ce
“Ni ka bar wannan tambayar doctor”
Bai sake cewa komai ba ya ci gaba da tuƙinsa hankali kwance, Ta ɗan kalle shi ta gefen ido sai kuma ta ɗauke kanta. Sam bata san inda suke nufa ba, Dan hankalinta gaba ɗaya baya wajen, Tana can tunanin Noorie sai ji ta yi ya kira sunanta.
Ɗago kanta ta yi ta kalle shi, Fuskarsa a ɗan cure babu yabo babu fallasa, Ya ɗan numfasa cikin nutsuwar da ta gama ratsa shi ya fara cewa
“Kin faɗa da kan ki ban cutar da ke ba Zahra, Bana yi miki abin da baki so sai dai idan da rashin sani. Ina zaune da ke tsakani da Allah, ina zaune dake saboda ina son ki, saboda na yaba da hankalin ki, naji zaki iya zama uwar Yayana”
Zahra ta yi shiru tana tunani sa, ta girgiza kanta a sanyaye ta ce
“Doctor na sani, wallahi na sani.”
“But why? Akan me zaki kashe mahaifiyata? Akan mene ne Zahra? Me nayi miki.”
Girgiza kanta ta fara yi cikin tashin hankalin daya ziyarceta ta ce
“Wallahi! Wallahi! Wallahi ban yi niyyar kasheta ba! Wallahi doctor ban yi niyya ba, Bana nufin kowa naka da sharri, na rantse maka da Allah…!”
“Idan haka ne me yasa zaki saka mata guba? Akan mene? Kin jawo na rasa ƴata, na rasa Noor Zahra! Kin kasheta da hannun ki. Kin kashe ƴar da muka haifa, Yarinyar da nake so fiye da komai, Yarinyar da nayi burin ganin girmanta,Me yasa Zahra?”
Tuni hawaye ya fara zubowa kan fuskarta, Sai girgiza kai take tana kuka, Tama kasa magana saboda tashin hankali. Jin bata ce komai ya sanya shi jan numfashi yana ƙoƙarin saita nutsuwarsa ya ce
“Ba zan tambaye ki ba, Ba zan nemi naji dalili ba. Na haƙura, na yafe miki Zahra, Na yafe miki har gaban abada wallahi.”
Ita dai bata ce komai ba sai kukanta take ci gaba da yi, Ya zaro wata farar welfolded paper daga aljihunsa ya ɗora mata akan cinya, Zahra ta kalli takardar sai kuma ta kalle shi, Ji ta yi tana neman rasa nutsuwar, Ta girgiza kanta cikin wani irin kuka ta ce
“Na shiga ukuna, Dan girman Allah, dan Allah, Dan Annabi kar ka rabu dani. Na shiga uku Doctor, Wallahi ban yi niyyar cutar da Hajiya Babba ba, Ban san maganin yana kisa ba, Anty Khadijah ce ta bani wai zai saka ta dinga sona. Wallahi ban san na kisa bane…”
Ta ƙare maganar tana sakin wani raunataccen kuka, Girgiza kansa ya yi muryarsa a ɗan dausashe ya ce
“Ba komai Zahra, Duk abin da ki ka yi ba zan rike ki ba. Naji daɗi daya kasance Noor ta fara cin abincin kafin Hajiya Babba, Duk da naji ciwo, naji zafi, naji raɗaɗin rashinta. Amma da ace Hajiya Babba ta rasu gwara Nooriya, Domin ita ni kaɗai zan yi rashin ta, ni kaɗai na san zafinta, Ita kuma Hajiya Babba gaba ɗaya dangin mu ne zai yi rashi. Ko da gangan ki ka yi, ko kuma bada saninki ba, Na haƙura na yafe miki Zahra. Amma ba zan iya ci gaba da zama dake ba, Domin zan ta kallon ki da abun, sannan ba zan iya kyautata miki ba, Sannan bana son dangina su riƙe ki idan suka ji wannan labarin, Tun asali na aureki bada yardar su ba, dan haka duk abin da ya faru zasu dinga ɗora laifin akaina. Ki yi haƙuri amma ni Abdusammad Muhammad Shuwa na sakeki saki ɗaya, na sake ki saki biyu, na sake ki saki uku! A zaman da muka yi da ke, idan na cutar dake Allah ya saka miki, idan kuma ni ki ka cutar to na yafe miki har abada, Ina miki fatan Alkhairi a ragowar rayuwar ki Zahra!.”
Zahra ta dinga kallon sa hawaye sai biyo fuskarta yake, Ta girgiza kanta cikin tashin hankali ta ce
“Na shiga ukuna doctor, Dan Allah dan Annabi kada ka bar ni, Kar ka rabu dani. Wallahi ina sonka, Ina son ka sosai fiye da tunanin ka, Idan ka rabu dani ya zan yi?”
Kallon ta kawai Abdusammad ya yi, Shi kansa zuciyarsa a dagule take. Ya numfasa sannan ya ce“Ko da na so zama da ke to ba zai yiwu ba Zahra, dole ne sai mun rabu. Ba zan iya ci gaba da zama dake ba domin zan ta tunawa da abubuwa da dama, ke kan ki kin san ba zan iya ba. Kin kashe Noor da hannun ki, Ta ina ki ke tunanin zan ci gaba da zama da ke? Bayan haka da a ce ba Noor ce ta ci ba da Hajiya Babba ki ka kashe, Zahra ba zan iya ba!”
Ya ƙare maganar yana girgiza kansa, Bata sake cewa komai ba, ta kifa kanta akan cinyarta tana kuka kamar ranta zai fita. Above 5mins kafin ya sauke numfashi ya juya yana kallon titin Gibson’s jalon wanda yake shiru babu hayaniya, Muryarsa a nutse ya ce
“Allah ya sani ban sake ki dan na tozarta ki ba, Babu yanda zan yi ni. Ki yi haƙuri”
Ɗago kanta ta yi tana kallon sa, Lokaci ɗaya ta shiga goge hawayenta. Cikin shessheƙar kuka ta ce“Na sani doctor, Ba komai Allah yasa haka ne mafi alkairi. Amma nima ka sani, ban zauna da kai da niyyar cutarwa ba, na soka domin Allah doctor, na yarda ƙaddara ce zata rabamu, Na gode doctor!…”
Ta yi shiru tana jan numfashi, Bai iya cewa komai ba, Dan a duk sanda damuwa ta yi masa yawa baya iya magana. Tsawon mintuna biyu kafin ta buɗe motar ta zura kafarta daya a waje, Juyowa ta yi tana kallon sa ganin har sannan idanun sa na kan titi. Ta sauke numfashi sai kuma ta fice daga motar ta rufe masa, Jiki a sanyaye ta juya ta fara tafiya hannun ta riƙe da wayarta da kuma divorced paper ɗinta. Sai da ta buɗe gate ɗin gidan ta shiga sannan ya juyo ya kalleta, Ta mayar da gate ɗin ta rufe. Zazzafan numfashi Abdusammad ya sauke sannan ya dauƙe idanun sa. Ya jima zaune cikin mota yana saƙa da warwara kafin daga bisani ya yiwa motar key ya yi reverse ya bar unguwar.
****
Amma ta dinga kallon ta ganin taƙi cin abincin tun ɗazu, Ta girgiza kanta a ɗan fusace ta ce“Wallahi Nana ba zan iya ba, Ba zaki tayar min da hankali ba. Akan me? Wannan damuwar ki ke zai saka wanda ya tafi ya dawo ne? Ba ki da tawakkali?”
Kallon ta kawai Nana ta yi da idanun ta wanda suke a kumbure, Amma ta tashi ta dawo gefenta ta janyo tray ɗin dake kan table ta ce
“Ki ci abinci ko kuma yanzu na kira Babanki.”
Ta ɗan kalli tray ɗin sai kuma ta sake langwabar da kanta kamar zata yi kuka ta ce“Amma ni bana jin yunwa fa”
Shiru Amma ta yi ta zuba mata idanu, Ganin haka ya sanya Nana tura baki kamar an mata dole ta ce
“To zan ci fa.”
Ita dai Amma bata sake cewa komai ba, Nana ta ta shige kitchen, After some minutes ta dawo hannun ta riƙe da mug. Ta dawo ta zauna sannan ta dauki tea flask ɗin ta tsiyaya shayin kadan, Sugar kawai ta saka sannan ta fara sha a hankali. Amma ta ajiye mata tray ɗin gefenta ta tashi ta shige ɗaki, Da idanu kawai Nana ta bita sai kuma ta sanya hannu ta fara cin wainar kwan, Ko loma uku bata yi ba ta cire hannunta. Shayin ma a wajen ta bar shi ta tashi ta nufi ɗakinta. Toilet ta shige ta fara amai, Sai da ta amayar da duk abin da ta ci sannan ta wanken bakinta ta fito tana sauke numfashi. Kwanciya ta yi gefen gado ta lumshe idanun ta, cikin yan mintuna bacci ya ɗauketa.
****
Kiraye-Kirayen sallar magribar da aka fara shi ne ya sanya shi tashi zaune, Tun bayan daya dawo daga gidan su Zahra bai sake fita ba, anan ɗaki ya yi sallolin sa. Ya ɗan yi jim sai kuma ya tashi ya zura slippers ɗin dake gaban gadon ya nufi bandaƙi, Wanka ya yi sannan ya ɗauro alwala. Yana fitowa ya buɗe press ɗinsa ya dauƙi wata embroidery jallabiya nude colour ya saka, sannan ya shafa mai da turare bai tsaya gyara kansa ba ya dauƙi ƙaramin counter dake gefen mirror ya fice daga ɗakin. Kai tsaye masallacin dake estate ɗin ya nufa,Bayan an idar da sallah suka fito tare dasu Papa.
Abba dake lura da yanayin sa tun sanda ya shigo ya kalle shi ya ce
“Abdul mene ne?”
Girgiza kai ya yi a sanyaye ya ce
“Ba komai Abba.”
Ya bashi amsa yana ƙoƙarin saita nutsuwarsa. Ɗan murmurshi irin na manya Abba ya yi kafin ya ce
“Alright, Ina son magana da kai”
Jinjina kansa ya yi ya ce“Nima dama Ina son zan yi magana amma a gidan Hajiya Babba.”
“Lafiya dai?”
Papa ya tanbaya yana kallon sa, Girgiza kansa ya yi ya ce
“A’a nothing serious, kawai dai ina son maganar ne.”
Jinjina kai Papa ya yi ya ce“Okay to a bari sai an idar sallahr isha’i”
To kawai ya ce sannan ya yi mus sallama ya nufi apartment din sa, Da idanu Abba ya bi shi dan ya lura akwai abin da ke damun sa. Suka yi sallama da Papa sannan ya nufi apartment din sa, Yana shiga ya tarar da Haule a parlour ita da Amma suna hira, Suka yi masa sannu da zuwa ya amsa. Ganin yana kallon su ya sanya Amma ta ce
“Lafiya dai yallaɓai?”
Girgiza kansa ya yi ya ce “Ba komai, Ina Nana ta ke?”
“Tana ɗakinta”
Ta bashi amsa tana kallon sa,
“Kira min ita.”
Ya yi maganar yana zama kan sofa, To kawai Amma ta ce sannan ta tashi ta nufi ɗakin Nanar, Haule na ƙoƙarin tashi ya girgiza kansa ya ce
“Yi zaman ki mana, yanzu zan tashi.”
Sunkuyar da kanta ta yi sannan ta ce to, Ba’a fi 2mins ba Amma ta dawo parlourn ta zauna tana cewa
“Gata nan”
Ko rufe baki bata yi ba Nana ta fito tana gyara zaman mayafin abayar dake kanta, Kujerar da yake ta ƙarasa ta zauna tana kallon sa ta ce
“Abba gani”
“Ki je wajen Abdusammad.”
Kallon sa ta dinga yi, can kuma ta ce to sannan ta tashi tana shirin komawa ɗaki ya ce
“Ina zaki je?”
“Wayata zan dauƙo” ta ce tana nuna masa ɗakin,Okay kawai ya ce, Ta juya ta nufi ɗakin.. after some minutes ta dawo hannunta riƙe da wayar ta sauya riga, Ta yi musu sallama sannan ta fice daga parlourn. Sai a sannan ya tashi ya nufi ɗakin sa, Amma ta bi bayansa..
Jiki a sanyaye ta murɗa handle ɗin kofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama, Babu kowa a parlourn, komai a nutse. Ta nufi sama kai tsaye, ɗakinsa ta buɗe ta shiga. Zaune ta same shi kan sofa ya jingina da jikin kujerar idanunsa a lumshe kamar me tunani, Ya rame sosai, Kamar ba shi ba. Ya ɗan yi duhu, Ta sauke idanunta sannan ta ƙarasa ciki, Zama ta yi gefen sa a sanyaye ta ce
“Uncle.”
A hankali ya buɗe idanun sa, Ya ɗan kalleta da mamaki ya ce“Nana yaushe ki ka zo?”
Tana kallon sa ta ce“Yanzu, Na zo ban ga kowa ba. Kuma naga kamar tunani ka ke, Me ka ke tunani?”
Ta yi maganar tana leƙa fuskarsa, Girgiza mata kai ya yi ya ce“Ba komai Nana.”
Yanda ya kira sunan nata a sanyaye ya sake tabbatar mata da akwai abin da ke damun sa, Ta haɗe rai ta ce
“To ba zaka fada min ba? Na daina kula ka!” ta ƙare maganar tana tura baki, Bai ce komai ba ya mai da kansa jikin kujerar yana sauke numfashi, Kallon sa ta dinga yi, can kuma ta miƙe a fusace ta ce
“To na tafi tun da ba zaka fada min ba. Kuma nima ba zan sake faɗa maka abuna ba!”
Murmurshi kawai ya yi ya sanya hannunsa ya jawota ta faɗo jikinsa, Ƙoƙarin tashi ta fara ya sake matseta ya ce



