Chapter 49: Chapter 49
“Wannan ya zama karo na ƙarshe da zan ganta haka, Idan ba zaka iya kula da ita ba to ka bar ta anan ka yi tafiyar ka.”
“Ki yi haƙuri.”
Ya ce a sanyaye, Bata sake cewa komai ba ta ci gaba da karatun azkar ɗinta. Ƙarasawa ya yi gaban Nana ya miƙa mata hannu, Ta ɗora nata hannun akan nasa sannan ta miƙe tsaye,
“Da gaske dai ciki gareta kenan? Amma wannan akwai mugunta a lamarin, Yarinyar kwaya nawa take? Dan jaraba ba zaku bar yara su girma su yi hankali ba sai ku haɗa su da wahala.”
Wata uwar harara ya zabga mata sannan ya juya ya fice daga ɗakin, Atta ta bi shi da kallo baki buɗe sai kuma ta ce
“Uban ka Muhammad shi ka ke harara bani ba wallahi!”
Shi dai Aliyu sai dariya yake, Ya juya ya fice daga parlon shima. Tsaye ya same shi a balcony ɗin gidan sai masifa yake mata, Ya ƙaraso yana kallon sa ya ce
“Haba Buddy yarinya ce fa”
“Yarinya? Ita yarinya bata da hankali ko? Bata san dai-dai da rashin sa ba ko?”
Ita dai Nana sai kuka take a hankali, Ya saki hannunta cikin daka tsawa ya ce
“Kin tafi daga nan ko sai na make ki!”
Da sauri ta juya ta fara tafiya, Duk da jikinta babu kwari. Aliyu ya bita da kallo sai kuma ya girgiza kansa dan ya san rashin haƙurin ɗan uwan nasa ya ce
“Gaskiya kada ka ce zaka dinga mata haka, She’s too young, Kuma ka san halin wawtar ta, Ba lallai ma ta gane abin da ta yi ba dai-dai bane.”
Kallon sa kawai Abdusammad ya yi amma bai ce komai ba, Dan ba ƙaramin ɓata masa rai ta yi ba, Sam bai so kowa ya san da maganar cikin ba, Shiyasa ma bai kai ta asibitin ba tun da ya gane ya bari idan sun koma US ya kai ta. Amma gashi ta zo ta sanya kowa ya gane
“Wai Buddy ma ya aka yi haka? Garin ya har wannan ƴar ta samu ciki ne? Yarinya da kake yiwa kallon ƴar ka?”
Aliyu ya ƙare maganar yana murmushi, Wani irin banzan kallo Abdusammad ya dinga yi masa, Sai kuma ya juya ya bar wajen kamar zai tashi sama, Aliyu ya dinga dariya kamar zararre kafin ya nufi hanyar nasa gidan shima.
Zaune ya sameta a parlour ta rufe fuskarta da hannunta sai kuka take ƙasa-ƙasa. Ya dan yi siririn tsaki sannan ya ƙarasa gabanta, Kallon ta ya dinga yi kafin ya sauke numfashi ya ce
“Nana!”
Ɗago kanta ta yi ta kalle shi, Sai kuma ta sake mai da idanun ta ƙasa. Abdussamad ya ce
“Ke ba zaki yi hankali ba ko? Ba zaki nutsu ba ko!”
Tashi tsaye ta yi tana kallon sa hawaye cike akan fuskarta ta ce“Ni ka mai dani gida, Ni wajen Amma zan kwana.”
Takaici ne ya ishe shi, Ganin bama abin da yake mata magana akai bane a gabanta, Cikin tsawa ya ce
“Yaushe na fara wasa dake Nana? Uban me ya fitar da ke ɗazu? Wa ki ka tambaya?”
Ganin yanda ya kafeta da manyan idanun sa ya sanyata sunkuyar da nata, Tana jan yan yatsun hannunta ta ce
“Yunwa nake ji, Shiyasa naje waje Hajiya Babban. Kuma…!”
“A saboda baki san inda nake ba ko? Ko kuma ba zaki iya kirana a waya ba ko?”
Ita dai bata ce komai ba sai shesshekar kuka da take. Ya yi kwafa ya ce
“wallahi duk ranar da ki ka sake fita wani wajen ban sani ba sai kin gane baki da wayo! Sai na ɓata miki! Shashasha kawai!”
Ya ƙare maganar cikin ɓacin rai, Bai kuma cewa komai ba kuma ya juya ya fice daga parlourn. Da idanu Nana ta bi shi sai kuma ta fashe da wani sabon kukan ta nufi sama da gudu, Ɗakinta ta shiga ta faɗa kan gado ta dinga rera kukanta tana birgima. Ta gaji da kukan daga ƙarshe bacci ya dauketa.
Bata farka ba sai kusan ƙarfe 10:00 na dare, Ta tashi tana mutsutsuka idanu, Ta jima a zaune kafin ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet. Wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala, Ta fito ta shirya cikin wasu riga da wando masu taushi, Ta gyare gashin kanta sannan ta saka hula akanta. A jikin madubi ta tsaya tana karewa kanta kallo, Ta ita kanta ta san ta sauya, Ta zama babba, Jikinta duk ya buɗe, Ga wani uban haske data ƙara kamar wadda ke mai. Ta sake wani sihirtaccen kyau, Tura baki ta yi sannan ta juya ta bar wajen, Ta gabatar da sallah sannan ta koma gefen gado ta zauna tana jawo wayarta, Lambar Khadijah ta yi dialing amma har ta gama ringing bata ɗauka ba, Ta ja tsaki sannan ta tura wayar gefe ta kwanta, Yunwa take ji ba kaɗan ba, Cikinta har wani zafi yake mata. Amma ba zata iya dafa abinci ba yanzu, Dan haka ta haƙura ta ɗora hannunta na dama akan cikin tana sauke numfashi. Around 10:50 na dare Ya buɗe ƙofar ɗakin, Shigowa ciki ya yi yana kallon ta ganin idanun ta a rufe. Ya ajiye ledojin hannunsa a ƙasa sannan ya zauna gefen gadon, Hannunsa ya ɗora kan wuyanta yaji zafi amma ba can ba. Ya janye hannun sannan ya ce
“Ke Nana!”
Shiru ta yi masa, Duk da ba bacci take ba. Ya sake kiran sunanta ta yi banza, Kallon ta ya dinga yi dan ya riga da ya san ba baccin take ba. Ya tashi tsaye yana kallon ta ya ce
“Idan ki ka bari na dawo ɗakin nan kina zaune ni da ke ne!”
Yana gama faɗin haka ya juya ya fice daga ɗakin, Sai da taji ya rufe kofa sannan ta buɗe idanunta, Ta dinga kallon ƙofar kafin ta tashi zaune tana tura baki. After some minutes ya dawo hannunsa riƙe da empty plates. Ya zauna gefen gadon ba tare da ya kalleta ba, Ledar daya ajiye ya buɗe ya dauko take away din, Jallof rice ce wadda taji wadatattun kayan hadi sai tiriri take. Ya juye a plate din sannan ya buɗe dayan, Turkey ne a ciki an yi ferfesun sa, Ya saka spoon ya ɗauka yanka biyu ya ɗora akai. Sannan ya miƙa mata yana kallon ta, Kallon plate din ta yi sai kuma ta kalle shi, Fuskarsa babu alamar wasa dan haka ta amshi plate din a sanyaye. Ɗaya ledar ya buɗe ya zaro wani take away ɗin, Tuwon shinkafa ne wanda ya tuƙu sosai kamar pounded yam, Ya saka guda biyu sannan ya buɗe daya robar miyan. Miyar agusi ce wadda taji naman kaza, Ya zuba a gefe sannan ya mayar ya ajiye. Sai da ya wanke hannunsa sannan ya yi bismillah ya fara cin tuwon, After some minutes ya ɗago yana kallon ta, Ko taba abincin hannuntan ba ta yi ba. Sai kallon sa da take kawai, Ya tsuke fuska ya ce
“Kina so na make ki ne Nana?”
Sunkuyar da kanta ta yi sai hawaye shar suka fara zubowa, Ya dinga kallon ta baki buɗe kafin ya ajiye plate ɗin hannunsa ya kalleta da kyau ya ce
“Mene ne kuma?”
Cikin shesshekar kuka ta ce
“Ni ba zan ci wannan ba, Ni bana so Wallahi!”
Ta ƙare maganar tana hawaye. Girgiza kansa ya yi sannan ya ce
“To me zaki ci?”
Da hannu ta nuna masa abincin gabansa, Ya ɗan yi shiru dan bai yi tunanin zai burgeta ba ya ce
“Wannan ɗin ki ke so?”
Sauran gyaɗa masa kai ta yi tana hawaye. Ya numfasa sannan ya dauko plate din ya miƙo mata yana faɗin
“Take it”
Karba ta yi tana kallon sa, Ya janye wanda ya fara bata ya ce
“Kuma idan baki ci ba sai na zane ki a gidan nan.”
Ita dai bata ce komai ba ta shiga goge hawayenta, Ya dauraye hannunsa yana shirin ɗaukan spoon ta ce
“Uncle ka bani a baki”
Kallon ta kawai ya yi sai kuma ya girgiza kansa, Ya karbi plate din ya ce
“Matso”
Babu musu ta matso kusa dashi sosai, Ya yi bismillah sannan ya gutsiri tuwon ya kai bakinta, A hankali ta buɗe bakin ya saka mata. Ta fara taunawa a hankali tana kallon sa, Loma uku taci ta fara jin tashin zuciya, Ya kawo mata tuwon ta yi saurin tare hannunsa, Da mamaki ya ce
“Mene kuma?”
“Na ƙoshi uncle”
Ta bashi amsa tana yamutse fuska, Haɗe rai ya yi kamar bai taba dariya ba ya ce
“Kin buɗe bakin ki ko sai na miki bugun da zaki kasa motsi a nan?”
Kamar zata yi kuka ta ce“wallahi uncle ba zan iya ci ba, Amai zan yi”
“Ci ki yi aman”
Ya faɗa yana sake miƙo mata tuwon, Ganin irin yanda ya haɗe ransa ya sanyata buɗe bakin nata, Ya saka mata tuwon yana harararta. Saurin toshe bakinta ta yi, Ta tashi da niyyar barin wajen ta ji ya rike ta, Girgiza masa kai ta dinga yi bakinta a rufe. Yaƙi barinta ta tashi, kuka ta saka tana ƙoƙarin kwace jikinta, Ya matseta a jikinsa ba tare da ya ce komai ba. Bata san sanda ta zare hannun nata daga kan bakin ba sai ganin amai tayi na zuba. Ta dinga kwarara amai tana riƙe da cikinta. Ban da kallon ta babu abin da Abdussamad ke yi, Gaba ɗaya ta wanke shi da amai, Ya kasa cewa komai, Ganin yanda ta galabaita sosai ya sanya shi jawota jikinsa, Kamar jira take ta ɗora kanta akan kirjinsa tana sakin wani irin wahalallen numfashi. Sai da yaga ta ɗan nutsu sannan ya tashi da ita a jikinsa suka nufi toilet, Wanka ta sake yi shi kuma ya gyara in da ta ɓata ya sauya bedsheet. Bayan ya gama ya fice daga ɗakin ya koma nasa, wankan shi ma ya yi sannan ya shirya cikin kayan bacci, Koda ya dawo ɗakin kwance ya sameta kan sofa tana daure da towel da alama tun da ta fito daga wankan take kwance a wajen, Ƙarasawa ya yi ya taba jikinta, Zafi yaji sosai. Ya girgiza kansa sannan ya ƙarasa press ɗin ta ya buɗe, Wata riga mai saukin nauyi ya dauko mata, Ya dawo ya taimaka mata ta saka sannan suka fice daga ɗakin. Ɗakin sa ya mai da ita, Ta kwanta akan royal bed ɗin sa ta lumshe idanu, Gaba ɗaya jikinta ciwo yake mata. Ga wani irin ciwo da mararta ke yi, Injection ya haɗo ya dawo ya zauna gefenta, Saurin tashi zaune ta yi duk da yanda take jin jikinta muryarta na rawa ta ce
“Uncle wa zaka yi wa allurar?”
Yana ƙoƙarin ɗaukan sringy ɗin ya ce
“Kaina zan wa”
Yana gama faɗin hakan ya jawota jikinsa, Kuka ta fara yi ta rike shi tana cewa
“Dan Allah uncle kada ka min allura, Wallahi bana so zafi fa”
Shafa dogon gashin kanta ya yi yana murmushi ya ce
“To shikenan zo ki kwanta”
“Ka fasa yi min?”
Ta tambaya tana hawaye. Bai ce komai ba ya yi kwanciyar sa, Ta ɗan yi jim tana kallon sa kafin ta kwanta a kusa dashi ita ma, Kasancewar a gajiye take yasa nan da nan bacci ya dauketa, Saukar numfashin ta da yaji ya sanya shi ɗaga kansa ya kalleta. Sai kuma ya tashi zaune ya dauko allurar, A hankali ya janye rigar jikinta ya sai ta allurar ya yi bismillah sannan ya yi mata, wata irin zabura ta yi ta tashi zaune, Ta dinga kallon sa sai kuma ta fashe da kuka. Murmushi ya yi ya jawota jikinsa ya rungumeta yana bubbuga bayanta ya ce
“Ya isa haka! Ya isa”
Cikin kuka ta ce
“Sai da nace bana so ka yi min, Wayyo Abbana zafi zai kasheni!”
Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan, Murmushi kawai ya dinga yi dan ya san halin rakinta. Ya kwanta har sannan tana jikinsa, A kunnenta ya raɗa mata wata magana, Ta daga idanunta ta kalle shi sai kuma ta sake ɓoye fuskarta a jikinsa, Shafa bayanta yayi a sanyaye ya ce
“Agreed?”
Makale masa kafaɗa ta yi tana ci gaba da kukanta, Ya girgiza kansa yana murmushi bai ce komai ba.
****
Washegari ta kasance ranar Lahadi, Bayan sallar azahar aka daura auren Anty Khadijah da Malam Garba. Gidan a cike yake da jama’a, Yawancin yan uwa da abokan arziki sun hallarci bikin, Musamman daya kasance an dade ba’a yi taro a gidan ba, Sai shige da fice ake, Ana shewa. Kowa na murna da Anty Khadijah ta samu miji, Ana ganin zata daina abubuwan da take ta zauna a ɗakin mijinta. Har mai dj aka ɗauko da Yamma ya zo compound ɗin gidan aka tashe, Amarya sai rawa take tana murna abin ta. Su Amal na tayata, Dan Siyama bata zo ba kasancewar tana takaba, Duk wannan bidirin da ake babu Zahra a ciki, tana sama a ɗakinta ta kulle, Yini ta yi zuciya babu daɗi, Gaba ɗaya mijinta ne ke faɗo mata, Sai kuma Noor, Shikenan babu wanda zata sake gani cikin su, Musamman Noor din, Kuma Anty Khadijah sai murnarta take zata tafi nata ɗakin mijin bayan ita ta rabata da nata. Wannan abun ya sanya Zahra yini tana kuka, Daga karshe ta kwanta, Sai dai sam baccin ya gagara zuwa, Data rufe idanun ta Abdussamad take gani. Haka ta dinga zama a ɗakin har bayan sallar magriba, Koda aka zo aka kirata su yi sallama da amarya ƙin fitowa ta yi, ta ce Allah ya bata zaman lafiya. Umma bata tilasta ta ba ta ce a rabu da ita, Anty Khadijah da abun ya ɓata mata rai ta nufi saman ba tare da an lura ba. Murɗa handle din ƙofar ta yi ta shiga, Ta samu Zahra na zaune kan dadduma tana jan carbi. Harararta ta dinga yi kafin daga bisani ta ce
“Wato Zahra baƙin ciki ki ke min da auren da nayi ko? Shi ne yasa ba zaki iya fitowa mu yi sallama ba ko? To ni gashi na zo. Allah ya bamu alkhairi, zan tafi ɗakin mijina. Kin san dama ita rayuwa juyi-juyi ce, Yau gareka gobe ga waninka, Da kece mai aure ni kuma bazawara, Sai gashi yau na zama mai aure ke kuma kin zama bazawara. To Ubangiji ya kawo miji a kusa, Na tafi!”
Anty Khadijah na gama faɗin haka ta juya ta fice daga ɗakin ba tare da ta jira jin amsar da Zahran zata bata ba. Ita ko Zahra kada koda motsi ta yi, Sai hawaye dake zubowa daga cikin idanun ta kamar an bude famfo. Tabbas ta yi wawta, Kuma ta yi nadama, Ta yi nadamar yarda da maganganun Anty Khadijah, Gashi yanzu ta cuceta. Ta bar ta a ruwa, Ta ɗora fuskarta a gefen gado tana fashewa da wani kuka mai sauti.
Daren ranar Malam Garba ya zo ya tafi da Anty Khadijah, Dan cewa ya yi baya son rakiyar amaryar nan, Suma basu takura kansu ba, aka bar shi ya tafi tare da ita. Gidan dai da suka saba zuwa da Kaddu nan ne gidan da zata zauna, Anty Khadijah ta dinga kallon soran gidan ganin ya tsaya anan yana buɗe wani daki dake wajen, Kamar ta yi masa magana sai kuma ta kasa, Ya buɗe ɗakin suka shiga. Da mamaki ta dinga kallon ɗakin, Ganin duk kayanta anan aka zuba su, Ɗakin yana da ɗan girma dan haka aka saka furniture da kuma kujeru guda biyu, Sai gas ɗin ta a gefe, Sauran kayan kuma aka bar su a corridor ɗin ɗakin. Dakyar ta nemi waje ta zauna dan gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, Ba haka suka yi dashi ba, Cewa ya yi akwai dakuna guda biyu a cikin gidan na tsohuwar matarsa ta uku da ya saka sai ta zauna a can. Dan haka koda aka zo jere har dashi aka jera kayan, Su kuma da suka koma babu wanda ya ce mata ga yanda gidan yake.
“Kin yi shiru Khadijah”
Maganar ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi, Kallon sa ta yi ta ce
“Afwan ban ji bane.”
Murmushi Malam Garba ya yi ya ce
“A’a ba komai ai, cewa nayi ki tashi ki yi sallah”
To kawai ta ce sannan ta miƙe, Kalle-Kallen ɗakin ta dinga yi sai kuma ta ce
“Babu banɗaki ne?”
Girgiza mata kai ya yi yana nuna mata wata yar siririyar ƙofa wadda ta sha tsatsa ya ce
“Ga shi can akwai mana. Ai banɗakin ki da ban babu ruwan ki da sabgar matan gidan” Jinjina kanta tayi sannan ta ajiye mayafinta a gefen kujera ta nufi banɗakin, Ɗan karami ne sosai, Amma a wanke yake sai kamshin hypo ne ke tashi, Dakyar ta iya yin alwalar a ciki ta fito tana yarfe hannu. Sallah suka yi tare sannan ya janyo ledar kazar daya shigo da ita, Ita dai tun da ta ci sau daya bata sake ci ba saboda gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake. Ta rasa wane irin hali take ciki, Farin auren Garba, Ko kuma dana sani. Ta rasa dalilin daya sanya ta yarda da auren ma,
“Khadijah lafiya dai?”
Ta tsinkayi muryarsa yana tambayrta. Bata ce komai ba ta tashi ta ƙarasa gaban wardrobe ɗin ta ta buɗe, Wata sabuwar rigar bacci ta dauka, Ya ce zai je cikin gidan ya dawo ta ce to sannan ya fita. Kafin ya dawo har ta gama shirin kwanciya ta zauna gefen gado ta zuba uban tagumi, Washe baki ya dinga yi yana dariya ya ce
“Kin ga yanda ki ka yi kyau kuwa?”
Da kyar ta ƙirƙiro murmushi ta yi masa ta ce
“Na gode sosai.”
Ya girgiza kansa ya ce “Ai babu godiya tsakanin mu Khadijah.”
Ita dai bata sake cewa komai ba, Taga ya nufi banɗaki. Jiki a sanyaye ta kwanta gefen gadon ta rufe idanun ta, Sam zuciyarta ta kasa nutsuwa, Gani take kamar a mafarki. Bayan ya gama shirin kwanciyar sa ya hauro kan gadon, Ta dinga kallon sa ganin yanda yake murmushi, Ita bata taɓa ganin muninsa ba ma irin ranar, tamkar wani naman daji haka take ganin fuskarsa. Babu yanda ta iya dashi haka ta yarda suka kwanta tare, Sai dai abin da Anty Khadijah ta fuskanta shi ne ya ƙara tayar mata da hankali, Bata taɓa sanin akwai irin wannan tashin hankalin ba. Ta inda Allah ya haramta ta nan ya dinga nemanta, Tun tana dauriya har sai da ta sume ba tare da ta san ta yi hakan ba. Shi kuwa ko a jikinsa dan ba yau ya fara hakan ba, Hasalima wannan shi ne tsarin gidan sa!.
****
Washegari da wuri Nana ta tashi don ranar zasu tafi, Ƙarfe 7:00 na safe ya shigo ɗakin yana sanye da riga da wando masu nauyi saboda sanyin da ake, Kallon ta ya dinga yi ganin yanda ta yi shiru ta zuba uban tagumi, Gabanta yar ƙaramar trolley ɗinta ce wadda ta gama haɗa komai nata. Ƙarasawa ya yi ya zauna kan drawer yana kallon ta ya ce
“Nana mene ne? Ko jikin ne?”
Kallon sa ta yi idanunta cike tab da hawaye, Muryarta a sanyaye ta ce
“Uncle ni ka bar ni anan dan Allah.”
Shiru ya yi yana kallon ta, Can kuma ya miƙe ya ce“Ba zan bari ba, Ki fito waje ina jiran ki” Daga haka ya dauki trolley din ya fice daga ɗakin. Da idanu ta bi shi, Hawayen da ke cikin idanun ta ya fara zubowa kan farar fuskarta, Ita ko kaɗan bata so ta bi shi, Saboda ta san zaman kadaice zata yi, Babu kowa ba kamar da ba da akwai Noor wadda suke hira tare, koma tana makaranta akwai Zahra duk da ba magana suke ba. Tana nan zaune har bayan mintuna sha biyar wayarta ta fara ringing, Ta kalli screen ɗin wayar ganin sunan uncle din ya sanya bata daga ba, Kawai ta tashi ta zura hijabin da ke gefenta sannan ta ɗauki wayar ta fice daga ɗakin.
A compound din Hajiya Babba ta same su, Kamar yanda suka saba tsayawa anan a duk sanda zai yi tafiya, Jiki a sanyaye ta ƙarasa wajen tana zuwa ta shige jikin Hajiya Babba, Rungumeta ta yi ta shafa kanta ta ce
“Allah ya tsare hanya kin ji”
Dakyar ta ce Amin saboda kukan da ke neman tawo mata. Ta janye jikinta ta ƙarasa wajen Abba, Rungume shi ta yi tana sakin kuka, Duk da sun gama sallama tun asuba, Ya ɗan yi murmushi duk da yanda shi ma yake jin babu daɗi tafiyar da zata yi ya ce
“Ba zaki daina rigima ba ko Nana?, Allah ya tsare hanya.”
“Abba dama na zauna anan…”
Ta yi maganar cikin kuka, Murmushi kawai Abba ya yi ya ɗago fuskarta ya fara goge mata hawayen sannan ya ce
“Ai darajar ko mace ƴa mace gidan mijinta Nana, Dan haka ni zan fi alfahari da ke idan kina daƙin mijin ki. Ki zauna lafiya kin ji”
Gyaɗa masa kai kawai ta yi, Ya ja kumatunta yana murmushi, Wajen Papa ta ƙarasa ta sake masa sallama, Sannan ta faɗa jikin Amma tana kuka kamar ranta zai fita. Ajiyar zuciya kawai Amma ta dinga saukewa, Dan ko kaɗan ba son tafiyar take ba, Dan babu yanda zata yi ne. Amma da anan za’a bar ta har ta haihu, Tausayinta kawai take ji, Nanar da bata iya kula da kanta yanda ya kamata ita ce zata kula da wani, Ta girgiza kanta jin yanda take ci gaba da kuka ta ce
“Ke ya isa mana, so ki ke a yi miki dariya?”
Girgiza kanta ta yi ba tare da ta ɗago kan ba, Amma ta ce“Ki zama yarinyar kirki Nana dan Allah, Ban da saka magana, Ban da rashin ji, Ki kula da kan ki da kuma lafiyar ki, Ban da neman magana.”
A sanyaye ta amsa da to sannan ta saketa, Ta ƙarasa wajen su Maimoon suka sake sallama sannan ta koma wajen Atta. Girgiza kanta ta yi ta ce
“A’a ba sai kin zo min ba, Kar ki shafa min ciki, Je ki kawai Allah ya sauke ki lafiya”
Ba Nana ce taji kunyar ba, Abdussamad ne da ke tsaye, Yaji kamar ya daskare a wajen saboda kunya, Musamman saboda su Abba da Papa da ke tsaye. Atta ta kalle shi ta ce
“Kai kuma kaji tsoron Allah, Ka dinga barin yar mutane tana hutawa. Yauwa, Dan bana son mugunta”
Wata uwar harara ya zabga mata sai kuma ya dauke kansa yana kwafa, Atta ta taɓe baki kafin ta ce
“Ohho! Kai ka ga zaka iya, Ni dai sai na faɗi gaskiya ko za’a kashe ni.”
Bai tanka ta ba, Aliyu sai murmushi yake, Nana ta sake musu sallama sannan ta buɗe motar ta shiga, Sai da ya sake yi musu sallama shi ma sannan ya shige motar, Driven yaja motar suka bar compound ɗin.
****
Wajejen ƙarfe 10:00 na safe ya shigo ɗakin, Har sannan tana kwance, Ya tsaya gaban gadon yana kallon ta ya ce
“Khadijah ba zaki tashi haka ba? Mutan gidan na ta jiran ki ki fito”
Dakyar Anty Khadijah ta kalle shi, Tsabar baƙin ciki kasa cewa komai ta yi, Ta tashi zaune ta nufi banɗaki kawai. Kallon ta ya dinga yi har ta shige, Bata jima ba ta fito ta dawo ta zauna gefen gadon
“Ki samu ki fito ku gaisa da kowa”
Toh kawai ta ce sannan ta juya masa baya, Shi ma bai sake cewa komai ya fice daga ɗakin. Sai kusan ƙarfe 12:00 na rana sannan ta fito daga ɗakin, Ta shirya cikin wata atampa glitter sai sheƙi take, Ta nufi cikin gidan dan ta jiyo hayaniyar jama’a, Abin da ta gani ne ya sanyata makalewa jikin bango, Gaba ɗaya matan gidan suna tsaye cirko-cirko suna kallo, Haka ma ya’yan gidan da basu tafi Makaranta ba, Malam Garba ne riƙe da ƙatuwar dorina sai dukan wata mata yake, Ita kuma sai tsala ihu take tana birgima a cikin ƙasar wajen. Ta dinga kallon sauran matan biyu da ke tsaye kamar gumaka,



