Chapter 5: Chapter 5
Runtse idanunta ta yi saboda jin furucinsa, tayaya ma zai ce bata fahimta ba? Ya san yanda ita ma take ji a cikin ranta ne? Ya san irin son da take masa? Me yasa yake nanata ita yarinta ta mata yawa? Why?.
“Nana baki ji na?”
Maganar Junaid ta dawo da ita daga tunanin da take, numfasawa ta yi sai kuma a hankali ta ce”na fahimta mana, nima ina sonka, kuma ka san da haka, da ba don son da nake maka ba babu yanda za’a yi nayi abin da na san iyayena ba zasu ji daɗi ba idan suka ji, da ba zan fito nazo dan na haɗu da kai ba. Dana haƙura da koda kiran ka ne, amma ka san me? Bana iyawa, idan nayi tunanin na rabu da kai nabi zaɓin dangina sai zuciya ta dinga faɗa min ba dai dai bane hakan, sai ta dinga kwaɗaita min irin alkkharanka, sai ta dinga tuna min baya. Wallahi sir ina sonka, tun ban san mene ne son ba, tun ban fahimci abin da yake nufi ba, amma ya zan yi? So ka ke na bijirewa gidanmu? ko kuwa na kai ka nace su aura min kai?”
Junaid ya dinga kallonta yana nazarin kalamanta, yanda take magana wani lokacin har tsoro yake bashi, maganganunta suna shige shekarunta, ta iya tsara zance. Agogon dake maƙale a hannunta ta kalla sai kuma ta ce”ba’a san na fito ba a gida” Junaid ya sauke zazzafan numfashi kafin ya saita nutsuwarsa ya ce”ba haka nake nufi ba Nana, what I mean is koda sau ɗaya ne ki gwada faɗawa iyayenki abin da ke cikin ran ki, ki gwada sanar dasu akwai wanda ki ke so, tun da har yanzu ba’a yi maganar wanda zaki aura ba. I
Maybe idan ki ka yi haka ke ki samu a bar ki da wanda ki ke so, daga sanda ki ka tambaya ni kuma zan fara zuwa gidanku, tun ana korata na tabbata wata rana ba za’a koreni ba Nana” ya ɗan yi shiru yana karantar yanayinta, ganin kamar ta fara ɗaukan abin da yake cewa ya sanya ya ci gaba da faɗin” ki samu ki yi maganar da mahaifiyarki cikin nutsuwa da fahimta, na san ba zata ƙi ba, domin da wuya ki ga iyaye mata suna son irin wannan auran haɗin. Ki yi mata magana yanda zata fahimceki ba da sauri ba sannan kuma ta sigar da zata ji daɗi, ba wai da hargagi ba, na tabbata idan har ki ka yi hakan zamu iya cin nasara!”
Sauke numfashi ta yi tana kallonsa dan har cikin ranta taji ta gamsu da abin da ya ce dan haka ta ce”shikenan I’ll give it a try in sha Allah, zan yi maganar da Amma idan na koma gida”
Murmushin jin daɗi Junaid ya yi ya ce”yauwa Nana, shiyasa nake sonki” dariya ta yi tana rufe fuskarta, ya girgiza kansa sannan ya koma ya buɗe motarsa. Wata leda ya fito da ita sannan ya dawo ya miƙa mata yana fadin”your favorite” kallon ledar ta dinga ba tare da ta amsa ba, ya sake cewa”karbi mana” girgiza kanta ta yi ta ce”ba’a san na fito wajen ka ba, idan aka ganni da leda dole ne a tambayeni” Junaid ya ce”bafa wani abun ba ne, naman kaza ne na siyo miki” murmushi ta yi ta ce”tom nagode, amma ka bar shi” Babu yanda bai yi da ita ba amma taƙi yarda ta amsa ledar daga ƙarshe ya hakura ya bar ta dan Nana ta fi shi gardama. Sallama suka yi ta koma gida shi kuma ya bar wajen cike da begenta, koda ta shiga parlon zaune ta sami Aunty Ramlah tana danna wayarta, tana ganinta ta ce”daga ina ki ke ne?” a ɗan rabe ta ce”a’a…a’a daman recharge card naje siyowa zan yi waya nawa ya ƙare” Aunty Ramlah ta ɗago ta kalleta sai kuma ta ce”shi ne ba zaki faɗa min na miki transfer ba?” ɗan murmushi ta yi ta ce”ai kina bacci shiyasa” taɓe baki ta yi ta ce”to kin samo katin?” gyaɗa kanta ta yi tana shirin zama suka ji ana knocking. Koda ta buɗe gate man ɗin gidan ne tsaye yana ganinta ya ce”Yauwa hajiya wai Nana ta zo in ji Sultan zasu tafi” okay kawai ta ce sannan ta mai da ƙofar ta rufe, Aunty Ramlah da bata motsa ba ta ce”mene?” tura baki ta yi ta ce”wai Yaya ne ya zo yana jirana”
“Da wuri zaku tafi kenan?”
Gyaɗa kanta kawai ta yi sannan ta nufi cikin ɗaki ta ɗebo sauran abin da ta bari, ko minti goma bata ƙara a gidan ba suka yi sallama ta fito. Zaune ta sameshi cikin mota idanunsa zube kan titi kuma cikin glasses kamar ɗazu. Buɗe motar ta yi ta shiga ba tare da ta ce komai ba, shima ɗin bai yi magana ba ya yiwa motar key suka bar unguwar.
Tafiyar mintuna talatin ta kawo su gida. Nana ta sauke ajiyar zuciya jin ya gama parking ta fara ƙoƙarin buɗe motar ta sauka, gam ta jita a rufe dan haka ta juyo tana kallonsa kamar zata yi kuka ta ce”Yaya dan Allah ka buɗe min na fita” banza ya yi mata ya ci gaba da danna wayarsa, gajiya ta yi da magiyar ta koma ta zauna tana takure jikinta waje ɗaya kamar daga sama taji ya ce
“Wane ne wanda ya tsaida ke ɗazun?”
Sai taji gabanta ya yi wata irin faɗuwa, nan take miyan cikin bakinta ya ƙafe ta dinga kallonsa amma ta gagara furta koda kalmar ‘A’ ce, a fusace ya juyo ya daka mata wata irin tsawa mai firgitarwa yana kallonta jijiyoyin kansa dun sun mimmiƙe idanunsa ya yi wani irin jaa, ko ba’a faɗa maka ba kasan ransa ya gama ɓaci. Kasa magana ta yi sai rawa jikinta yake, rabon da a yi mata irin wannan tsawar har ta manta, ganin bata ce komai ba ya sanya ya sake daka mata wata razananniyar tsawar ya ce”Ba da ke nake magana ba!” fashewa ta yi da kuka, bata yi aune ba kawai ta ji ya sauke mata mari akan fuskarta, iyaka rikicewa Nana ta rikice, ta kasa koda kukan saboda tsananin azabar marin sai jan numfashi take, tun da take a rayuwarta babu wanda ya taɓa marinta sai yau, dan haka ta fice hayyacinta. Sultan ya dinga kallonta yana wani irin huci kamar zaki, har wani ruwa ne ya kwanta a cikin idanunsa saboda masifa. Cikin tsananin ɓacin rai ya ce”Yau sai kin faɗa min wane ɗan iskan ne yake zuwa wajenki, tun da har kin yi girman da zaki dinga haɗuwa da maza. Wallahi tallahi ba zaki bar motar nan ba har sai kin faɗa min alaƙar ki dashi!”
Nana ta dinga kallonsa hawaye na sauka kan fuskarta, ganin yanda ya kafeta da idanu ya sanya ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da shessheƙar kuka. Ɗauke kansa ya yi daga kallonta ya zubawa compound ɗin gidan ido, ƙoƙarin saita kansa yake amma zuciyarsa a cunkushe take, he just can’t believe a ce Nana na kula wani, wanin ma a wajen estate, how? Furzar da numfashi ya yi daga bakinsa sannan ya juyo yana sake kallonta. Kuka take sosai, fuskarta ta yi jajur, ɗauke kansa ya yi sannan ya ce”baki shirya tafiya gida ba kenan?” kasa magana ta yi sai hawaye dake fama zuba kan fuskarta kamar an buɗe famfo, kwafa ya yi ya ce”wato ga ɗan iska yana magana ko? shi yasa ki ka min banza nayi ta yi ko? wane ne wanda na gan ki dashi? wane ne wanda ya baki yanki har da kalaman soyyaya a jiki? wane shi? A ina yake? har kin yi girman da ki ke ganin zaki fara soyyaya?”
Da sauri ta kalleshi amma bata ce komai ba, harararta ya yi ya ce”I’m talking to you, har kin girma?” Tura baki ta yi muryarta na rawa ta ce”n..nifa ba wani abun bane, ai kowa yana da wanda yake so, to nima shi nake so, kuma shi zan aura, naga…”
Wata irin tsawa ya daka mata ba tare da ya san ya yi hakan ba, ya dinga mata wani irin kallo yana huci kafin ya ce”shi zaki aura? Da gaske? Daman ke zaki yanke wanda zaki aura? ke ki ke da wannan alhakin bamu sani ba?”
Murguɗa masa baki ta yi ta ce”ai Abba zan faɗawa kuma na san zai yarda” Sultan kasa magana ya yi sai kallonta da yake baki buɗe ganin bai ce komai ba ya sanya ta ɗan ɗago kanta ta kalleshi, har sannan kallonta yake da alama dai abin faɗa ya rasa. Wayarsa xe ta fara ringing hakan ya dawo dashi daga tunanin da ya tafi, kallon screen ɗin ya yi ganin sunan Hameed ya sanya ya ɗauka, maganar 2mins suka yi ya kashe wayar bai sake bi ta kan Nana ba ya sauka daga motar, ganin haka ya sanya itama ta sakko ta nufi hanyar gidansu da sauri.
****
Babu kowa a parlon sai tv dake aiki ita ɗaya, kai tsaye ɗakinta ta shige tana zuwa ta faɗa kan gado ta fashe da kuka. Maganganun Junaid ne suka dinga dawo mata, sai kuma maganganun Sultan wanda suka sake tuna mata irin ƙalubalen dake gabanta, tana nan kwance har aka fara kiran sallahr magriba. Ta tashi ta shige toilet ta yi wanka sannan ta ɗauro alwala, sauya kaya ta yi zuwa doguwar riga mara nauyi sannan ta gabatar da sallahr, ta daɗe tana rokon Allah akan ya taimaketa ya kuma yi mata zaɓi nagari kafin daga bisani ta tashi ta naɗe laddumar ta fito daga ɗakin jiki a sanyaye ta nufi ɗakin Amma.
Zaune ta sameta kan ladduma tana jan carbi, ta ƙarasa ta zauna a kusa da ita ba tare da ta ce komai ba, sai da ta kai inda zata tsaya sannan ta juyo ta kalleta ta ce”kin dawo?” gyaɗa mata kai Nana ta yi, Amma ta dinga kallonta ganin yanda fuskarta ta yi jajur yasa ta sake cewa “meya sami fuskarki?” A sama Nana ta ji maganar dan bata yi tunanin Amma zata tambayeta ba, dan haka ta shiga kame-kamen abin cewa
“U…un… Wani kwaro ne ya hau min kan fuska shine ya cijeni kuma da zafi sosai”
Amma ta kalleta ba dan ta yarda da abin da ta ce ba, sai ta taɓe baki ta ce”Ya Ramlan?”
“Tana nan klao, ta ce tana gaishe ki”
“Ina amsawa”
Amma ta ce tana jawo wayarta daga kan drawer, shiru wajen ya ɗauka ita tana danna wayarta ita kuma tana tunanin ta inda zata fara sanar mata halin da take ciki. Above 5mins kafin ta gyara zamanta muryarta a sanyaye ta ce”Amma!” ɗago idanu ta yi ta kalleta sai kuma ta ce”ina jin ki lafiya?” gabanta na tsananta faɗuwa ta ce”daman ina son nayi wata magana da ke ne” Ajiye wayar hannunta ta yi tana mai da hankalinta gareta ta ce”okay Ina ji” Nana ta dinga wasa da fingers ɗinta tana tunanin ta inda zata fara, kusan 3mins bata ce komai ba, hakan yasa Amma ta jawo wayarta tana cewa”shikenan idan baki da abin faɗa tashi ki bani waje” girgiza kanta ta yi, sai kuma ta sauke nunfashi ta ce”daman… Daman akwai wani malamin makarantarmu ne, sanda muna Aun, to shi ne.. shi ne..!”
Amma ta dinga kallonta tana jiran taji me zata ce, ganin ta yi shiru ya sanya ta ce”shi ne me? Ina jin ki?”
Fashewa ta yi da kuka tana cewa”shi nake son na aura Amma! Ni shi nakeso, bana son auran zumuncin da ake yi mana, ni shi zan aura dan Allah ki faɗawa Abba”
Tashi tsaye Amma ta yi tana mata wani irin kallo cike da tashin hankali da kuma ɓacin rai ta ce”Nana kin san me ki ke faɗa? Har yaushe ki ka yi girman da har ki ka san ki ce ga wanda ki ke so? A nan gidan? Wane kalar hauka ne yake damunki? so ki ke ki ja min masifar da ba zan iya da ita ba ko me? wato a ce yata ta bijire ko? kina son a saka ubanki a bakin duniya ko? To bari kiji koda wasa kar na sake jin makamanciyar wannan maganar a bakin ki Nana, wallahi idan ba haka ba sai ranki ya yi mugun ɓaci! Sai na saɓa miki fiye da yanda ki ke zato. Kuma Allah nagode maka daya sanya ki ka faɗi wannan maganar naji, daman nan bada jimawa ba za’a ɗaura aurenku, ki bar gabana kafin ki dauko min maganar da ba zan iya da ita ba”
Da sauri ta ɗago idanunta wanda ke zubar hawaye ta kalli Amma, furucinta na ƙarshe shi ne abin da ya dagula nutsuwarta, aure! Aure za’a musu? Innalil lahi wa ina ilayhi raji’un, ta dinga maimaitawa cikin ranta, kafin ta tashi tana kallon Amma bakinta na rawa ta ce” ki yi hakuri, banida niyyar ɓata miki rai Amma, wallahi daman sai da na faɗa masa ba zaku yarda ba, amma ya ce na gwada, Amma naji ba zan sake miki maganarsa ba, amma dan Allah kada ki saka a min aure yanzu, banaso Amma, bana so dan girman Allah, ki taimakeni Amma!”
Wani irin wawan mari Amma ta sauke mata tana huci ta ce”kin ji an tambayeki abin da ki ke so? ko kuma wanda baki so? ko daman ni ce nake zaɓar lokaci da kuma wanda zaku aura? Idan baki bar ɗakin nan ba sai ranki ya yi masifar ɓaci Nana! Leave my side!”
Wata irin azaba ce ta yi mata yawa, ga zafin mari ga kuma zafin kalaman Amma, madadin ta fita daga ɗakin sai kawai ta durƙushe a wajen ta riƙe ƙafafun Amma cikin matsanancin kuka take faɗin
“Ki yi hakuri Amma, ki yi hakuri ki taimakeni Amma! Ki yi hakuri Ammaa..!”
Kasa cewa komai ta yi, kawai ta janyeta daga jikinta ta fice ta bar ɗakin, Nana ta dinga bin ƙofar da kallo tana wani irin kuka kamar ranta zai fita, ita ba rabuwarta da Junaid ne abin da ya fi damunta ba, maganar auren da aka yi shine tashin hankalinta. Wa zata aura? Wa aka zaɓa mata? Da wa zata yi rayuwa??..
****
Sultan ya dinga kallon Papa yana jin wata irin zufa na keto masa duk da ac dake ɗakin, ganin bai ce komai ba ya sanya Papa ya sake faɗin “lafiya dai Sultan?” girgiza kansa ya yi dan bakinsa ya gagara magana, Papa ya ce”saboda haka ina fatan ka zama miji nagari a wajen matarka, ka bata kulawa iyaka iyawarka, ka sota, ka ƙaunaceta, kamar yanda kaga muna yi da iyayenku” zazzafan numfashi ya sauke kafin ya shiga jinjina kansa. Papa ya ce”kana iya tafiya” ko rufe bakinsa bai yi ba Sultan ya tashi ya fice daga ɗakin da sauri, A corridor ya haɗu da Juwaira wadda take tafe hannunta riƙe da tray, sannu da zuwa ta yi masa amma ko ta kanta bai bi ba ya shige ɗakinsa ya rufo ƙofar. Dakyar ya ƙarasa gefen gado ya zauna yana sauke numfashi, bai san sanda hawaye suka fara zuba kan kuncinsa ba, ashe ba zai samu Nana ba? Ashe ba zai zama mijinta ba? Wane irin dangi ne wannan? Wace irin al’ada ce wannan? Kenan baka da yancin zaɓar matar da zaka yi rayuwa da ita? haka zasu ci gaba da rayuwa? Ya ilahi. Maganganun da Sultan ke yi kenan cikin zuciyarsa, a fili kuwa bakinsa kamar an rufe shi da gam haka yake ji, ya gagara cewa komai, ya gagara furta wata kalma ballantana yaji sauƙi a ransa. Daga ƙarshe ma kwanciya ya yi kan gadon yana kuka kamar ƙaramin yaro.
****Mami ta dinga kallonta ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita ya sanya ta ce”Amrah zo nan” tasowa ta yi ta ƙaraso gabanta ta zauna kusada ita, rungumeta Mami ta yi tana faɗin”kukan na mene ne Amrah? Baki farin ciki?” kasa cewa komai ta yi, sai ma wani sabon kukan data fara, Mami ta dinga rarrashinta amma sam taƙi yin shiru, suna haka ya buɗe ƙofar ya shigo, Har ya zauna kallonsu yake da mamaki, ganin yanda take kuka ita kuma tana faman rarrashinta, Alhaji Abubakar kenan, mahaifin Amrah, kuma ɗan yaya a wajen Hajiya Khadijah, Mami kuma wadda ta kasance yarta ta biyu wato Fatima, yaransu kuma su ne Amrah da Sa’eed. Mami ta kalleshi ta ce”yauwa gara da Allah ya shigo da kai dan wallahi nagaji da rarrashinta” Daddy ya ce”me aka mata?”
“Akan maganar auren nan ne, tun da aka yi maganar shikenan take faman kuka”
Da mamaki Daddy ya ce”and kukan ne mene ne? wa ya ɓata mata?” Mami ta girgiza kanta ta ce”ban sani ba wallahi” tsaki ya yi yana mai da idanunsa kan Amrah ya ce”Ke Amrah!” ɗago kanta ta yi sanin halinsa yasa ta ce”na’am Daddy”
“Lafiyarki? Ko an yi miki wani abun ne?” Girgiza kanta ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce”a’a kawai kaina ne yake ciwo” Jin jina kansa ya yi ya ce”okay bari na kira Sultan ya zo ya dubaki” da sauri ta ce”a’a Daddy idan na kwanta ma zai daina”
“And what are you waiting da baki kwanta ɗin ba?” Daddy ya yi magana babu yabo babu fallasa, tashi ta yi jiki a sanyaye ta bar parlon, ya bita da kallo sai kuma ya yi tsaki ya ce”i don’t know what wrong with this childrens wallahi” Mami ta sauke numfashi kana ta ce”Allah dai ya kyauta” .
****
Hameed ya girgiza kansa still looking at her ya ce”amma Hajiya ni sai naga daman ba haka aka yi ba, ko mu ba za’a tambayemu ba at least a tambayi yaran, kowacce dole akwai wanda take ganin idan aka aura mata she’s will be okay ko?” Hajiya Babba dake zaune kan sofa tana jan cazbaha ta ce”Yanzu da aka zaɓawa kowa mene ne ai bu Hameed? Kowacce ɗan uwanta aka bata, zata fara sonsa bayan aure, yanda zaku kyautata musu shi ne zai sanya su so ku” Hameed ya numfasa sannan ya ce”shikenan Hajiya, Allah yasa haka ne mafi Alkhairi” murmushi ta yi dan daman tasan shi bashida matsala ta ce”Amin, Allah ya baku zaman lafiya” a sanyaye ya ce”Amin” sannan ya tashi , dai-dai nan Aliyu ya shigo parlon bakinsa ɗauke da sallama. Amsawa suka yi sannan ya ƙaraso ya gaida Hajiya ta amsa sannan ya zauna, Hajiya ta ce”Aliyu lafiya dai?” murmushi ya yi ya ce”Alhamdulillah Hajiya, daman mun yi waya da Buddy ne ya ce gobe yana tafe in sha Allah”
Ba Hajiya Babba ba har Hameed sai da ya yi murmushi sannan ya ce”da gaske Yaya?” gyaɗa masa kai Aliyu ya yi ya ce”haka ya ce min, kuma nasan tun da ya ce haka to zai zo ɗin” Hameed ya jinjina kansa ya ce”Tom Allah ya kawo shi lafiya” da Amin ya amsa sannan ya haye sama da sauri. Hajiya Babba data kasa ɓoye farin cikinta ta ce”shi da kansa ya ce maka zai dawo ɗin?” gyaɗa mata kai Aliyu ya yi ya ce”Eh Hajiya yana nan tafe in sha Allah” ajiyar zuciya ta sauke ta ce”to Allah ya kawo shi lafiya” Amin ya ce sannan ya miƙe yana kallonta ya ce”zan je wajen Abba ya ce na faɗa masa zai zo” toh ta ce sannan ya juya ya fita.
A bakin ƙofar shiga apartment ɗin ya ganta hannunta riƙe da warmer, tana ganinsa ta sunkuyar da kanta murya na rawa ta ce”s..sannu da zuwa Yaya” ɗan murmushi ya yi ya ce”yauwa Maimuna ina zuwa?” ba tare da ta ɗago ba ta ce”Hajiya zan kai wa abinci” Aliyu ya jin jina kansa ya ce”okay kai mata ki zo ina jiranki” toh kawai ta ce sannan ta shige gidan da sauri. Ko minti biyu bata yi ba ta fito ta sameshi tsaye inda ta bar shi, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta sake sunkuyar da kanta ta ce”Yaya gani” Aliyu ya ɗan kalleta sai kuma ya yi murmushi ya ce”muje to” bata musa masa ba suka fara tafiya a jere, sai dai tunaninta yana wani wajen daban, Sun kusa kai wa Apartment ɗin sannan ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin “Maimuna” saurin ɗago kanta ta yi dan duk sanda ya kirata da wannan sunan sai taji zuciyarta ta buga, ya tsaya cak yana kallonta ya ce”Are you happy or not?” kasa cewa komai ta yi sai sunkuyar da kai take, hawaye ya fara sauka kan fuskarta. Ɗan rage tsawonsa ya yi ya leƙa fuskarta ganin yanda take kuka ya sanya ya ce”haushi ki ke ji kema?” girgiza kanta ta yi, ya ce”to tell me meyasa ki ke kuka? uhm” kasa cewa komai ta yi har sannan sai kuka take a hankali, Aliyu ya sauke numfashi kafin ya ce”okay tun da ba zaki faɗa min ba daina kukan, kin ga Abba zai tambayeki me ki ke wa kuka” gyaɗa masa kai ta yi sannan ta shiga share hawayenta da gefen mayafin dake jikinta. Ya ɗan yi murmushi kafin ya ce”to muje” daga haka suka ci gaba da tafiya.
****
Ƙarfe 9:10pm aka buɗe ƙofar ɗakin, kwance take har sannan akan gado sai hawaye take, Abba ya dinga kallonta kafin ya ƙaraso cikin ɗakin ya zauna gefen gado ya ce”Nana lafiya?” da sauri ta ɗago kanta, ganin Abbanta ya sanya ta tashi zaune, ta ƙarasa wajensa kawai ta rungumeshi tana fashewa da kuka. Abba ya dinga shafa kanta ba tare da ya ce komai ba, kuka take bana wasa ba, har wani jan numfashi take kamar zata shiɗe. Abba ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce”mene ne? faɗa min”
Cikin kuka ta ce”Abba wai aure za’a yi mana?” Da mamaki yake kallonta kafin ya ce”wane ya faɗa miki wannan maganar Nana?” Cikin shassheƙar kuka ta ce”Amma ce, Amma ta ce aure za’a yi mana” numfasawa ya yi sai kuma ya jinjina mata kai ya ce”haka ne, an kusa muku aure in sha Allah” sake fashewa ta yi da wani sabon kukan, Abba ya ce”mene ne kuma?”
“Abba ni bana son aure karatu nake son nayi, bana son nayi aure yanzu dan Allah Abba”
Ɗan murmushi irin na manya ya yi kafin ya ce”in dai karatune zaki yi a gidan mijinki, amma nan ba da jimawa ba zaki yi aure Nana”
Tashi ta yi daga jikinsa, ta sauko daga kan gadon ta tsuguna a gabansa tana kuka ta ce”dan Allah Abba kada ka bari a yimin aure yanzu, ka bari nayi karatu Abba, bana son aure wallahi”
Bai ce komai ba sai kawai ya tashi ya fice daga ɗakin, Nana tabi bayansa da kallo sai kuma ta sake fashewa da wani kukan tana dafe kanta.



