Chapter 50: Chapter 50
Sai da ya gaji dan kansa sannan ya hankaɗata da ƙafa, Ya juyo yana kallon sauran yana haki ya ce
“Cikin ku wata ta sake irin abin da ta yi, Wallahi sai kin raina kan ki a gidan nan! Ni ba zaka kawon wannan iskancin na ɗauka ba!”
Ya ƙare maganar yana haki… Babu wadda ta iya motsi a cikin su, Sai muzurai suke, Ya kalli Anty Khadijah da ta yi sak a fusace ya ce
“Ke ma dallah shige mu je an fasa gaisawar!”
Kallon sa ta dinga yi, Can kuma ta juya ta bar tsakar gidan. Zaune ta same shi a ɗakin ta sai haki yake saukewa, Ta ƙarasa gefen gado ta zauna ta zuba uban tagumi.
“Na shiga uku ni Khadijah, wace irin rayuwa na jawowa kaina?”
Wani ɓangare na zuciyarta ya yi mata tambayar. Rufe idanun ta ta yi tana sauke wani irin numfashi, Babu wanda ya fado mata a rai sai tsohon mijinta mahaifin Siyama. Mutun mai kirki da sanin ya kamata, Mutum mai addini da son ƴan uwansa. Amma sai da ta raba shi da kowa, Ta mallake shi daga ita sai ƴar ta. Runtse idanunta ta yi tana tuno wasu shuɗaɗɗun abubuwa da suka shige, Tana sake jin ina ma ace mafarki take ba gaskiya bane.
****
It’s been a while da komawar su New York, Kusan kullum tana kwance bata da lafiya, Koda ace lafiyar kalau ma to ba lallai bane ya gane dan ba zata fito ko parlour ta zauna ba. Ko kaɗan kuma basa wani shiri dashi saboda gaddamar ta, Kullum sai sun yi faɗa akan cin abinci, Ita ta ce ba zata ci ba saboda amai shi kuma ya rantse sai taci, Daga ƙarshe idan ta ci ta amayar sai bacci ya dauketa. Ranar wata Monday ta gama shirinta ta safe tsaf dan ranar ta tashi da sauki, Abdussamad ya shigo ɗakin da niyyar duba jikinta, Ya sameta tsaye tana shafa lip balm a bakinta. Ta ɗan rame kaɗan idanunta sun firfito saboda rashin cin abincin da take, Ya dinga kallon ta da mamaki kafin ya ƙaraso gaban mirror ɗin ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallon ta ya ce
“Madam ina zuwa?”
Kallon sa ta yi, Sai kuma ta tura baki ta ce
“Makaranta zan je, Ni na gaji da zaman gidan nan…”
Ta ƙare maganar kamar zata yi kuka, Sosai ta bashi dariya, Ya jinjina kansa ya ce
“Wato kin gaji da zaman gida ko? To zaki bini asibiti?”
Maƙale kafaɗa ta yi ta ce“Ni school zan tafi”
Matsowa kusa da ita ya yi, Ya riƙe hannayen ta duk biyun cikin nasa ya ce
“Ban son yawo fa Nana, ki yi zaman ki a gida mana”
Rau-Rau ta yi da idanu tana shirin kuka ta ce
“Dan Allah uncle ni zan je a haka. Ai na samu sauki fa”
Shiru ya yi yana kallon ta, Ta shige jikinsa a shagwabe ta ce
“Kaji uncle ɗinaa!”
Numfasawa ya yi sai kuma ya ɗago fuskarta ya ce
“But sai kin min alƙawari”
“Alƙawarin me?”
Ta ce da sauri.
“Idan kin dawo ba zaki wahalar dani ba zaki ci abinci!”
Kwabe fuska ta yi ta ce
“To ba cikin ne yake hanani cin abinci ba! Nima ina so naci fa, Kuma nagaji ma..”
Ta ƙare maganar tana turo baki gaba, Murmushi kawai ya yi sai kuma ya yi mata light kiss a baki ya ce
“Alright muje nayi dropping ɗin ki”
Cike da murna ta ce to sannan ta ɗauki jakarta suka fice daga ɗakin.
A compound din makarantar ya yi parking, Ta ɗauki jakarta da ledar chocolate din daya siya mata a hanya ta ce
“Uncle zaka zo ka ɗauke ni?”
Gyaɗa mata kai ya yi ya ce
“Karfe nawa zaku gama lecture din?”
“3pm”
Ta ce tana kallon sa, Shiru ya yi sai kuma ya ce“Okay idan zan zo I’ll call you”
“Ai zaka zo ma..”
Ta ce a shagwaɓe, Murmushi kawai ya yi ya ce“To naji, A yi karatu dayawa” Toh kawai ta ce sannan ta buɗe motar ta sauka, Ta daga masa hannu sannan ta nufi department ɗin su.
Karfe 1:30 na rana suka je cafeteria, Ita da wasu kawayenta Mu’ash da Amani, Kasancewar ranar Surry bata zo ba. Suka yi order abinci aka kawo musu, Nana ko loma uku bata yi ta fara amai, Har abin da taci da safe sai da ta amayar dashi, Su suka taimaka mata ta gyara jikinta sannan suka bar wajen. A kasan wani garden suka zaune, Amani ta dinga kallon ta ganin yanda ta jingina da jikin kujera ta yi shiru, Gaba ɗaya ta zama kamar ba ita ba. Taɓe baki ta yi ta ce
“Gaskiya Nana kina bani mamaki, Ke a haka zaki ci gaba da zama?”
Kallon ta kawai Nana ta yi da rashin fahimta, Ta gyara zamanta sannan ta ce
“To ya zan yi Amani? Kullum ma a haka nake, Ni na gaji ma wallahi, Ji nake kamar na mutu.”
Wani kallo Amani ta yi mata sai kuma ta ce
“Au to zauna, Ƴar ƙaramar ki dake ki wani fara haihuwa, Da kin haifi ɗa ko ɗaya ne shikenan zaki ga kin fara canzawa, Komai ya nemi ya ƙare miki. Ya ma za’a yi na bari na haihu? Ai ko Deen ya sani wlh ba zan haihu ba har sai na gama karatu, Na koma na zauna sannan na haifi ko ɗaya ne”
Mu’ash da ke danna wayarta ta ce
“Bare kuma ni! Kin ga yanzu dai shekarar mu biyu da aure ko? To sau biyu ina ɓari, Dana samu ciki nake zubarwa, Akan me? Tab!”.
Ita dai Nana kallon su kawai take can kuma ta ce
“To ni ai ban san yanda zan yi ba. Sai dai na bari idan na haihu nayi planning”
“Shi kuma wannan cikin fa?”
Amani ta tambayeta, Ɗan haɗe rai Nana ta yi ta ce
“Sai na haihu ai”
Jinjina kai Mu’ash ta yi ta ce
“Oh har sai kin jira kin haifi wannan cikin dai bai rufe wata biyu ba?”
Kamar zata yi kuka ta ce“To Mu’ash ya zan yi wai?”
“Ki zubar!”
Girgiza kai Nana ta yi muryata a sanyaye ta ce“Ni dai gaskiya ba zan iya ba. Uncle faɗa zai yi min..”
Wani dogon tsaki Amani taja kafin ta ce“amma ke dai baki da tunani wallahi! Ki ji min hauka, to bari zaki yi ya gane?” Kallon ta Nana ta dinga yi da rashin fahimta. Mu’ash ta ce“Nima abin da na gani kenan, Ya za’a yi ma ki bari ya gane. Ai kawai yi zaki yi a zuwan ɓarewa ya yi da kansa” Marairaice fuska Nana ta yi ta ce“Ni gaskiya tsoro nake ji, Idan kuma ya gane fa?” Takaici ne ya ishi Amani, A ɗan fusace ta ce“Ai sai ki bari ya gane ɗin!” Tura baki Nana ta yi bata ce komai ba. Mu’ash ta gyara zamanta ta ce“Kina ji Nana, Kawai za’a baki tablet ne ki sha, Da zarar kin sha 15mins sun yi yawa cikin zai ɓare.” Ita dai Nana bata ce komai ba sai kallon ta take, Mu’ash ta ci gaba da cewa
“Kin ga idan ya zube sai ki ce kema baki san garin ya ya ba, Sannan kada ki yarda ki sha yana gidan, Ki bari sai ya fita. Yanda zaki iya cewa faɗuwa ki ka yi, Kin ga shikenan kin huta, Bayan kwana biyu sai ki yi planning har ki gama karatun ki”
Kasa cewa komai Nana ta yi tana kallon su, Jikinta ya yi sanyi gaba ɗaya, Taji tana son zubar da cikin, amma tana tsoron abin da zai iya biyo baya. Can dai ta ce
“To zan fara shawara da uncle”
Baki buɗe suka dinga kallonta, Amani ta miƙe cike da takaici ta ce“Idan ban bar wajen nan ba sai baƙin ciki ya kasheni, Sai ki je ki yi shawarar dashi!”
Tana gama faɗin haka ta yi gaba fuuu kamar zata tashi sama. Da idanu suka bita, Sai kuma Mu’ash ta kalle ta ta ce
“Kina ji Nana, babu maganar shawara dashi, ai ba zai bar ki ba. Musamman da ki ka ce ƴar sa ta mutu, ba zai taɓa yarda ki zubar da cikin ba. Kawai ki zubar”
“To idan ya kamani fa?”
Ta yi maganar kamar zata yi kuka. Girgiza kai Mu’ash ta yi ta ce“Ba zai kama ki ba. Babu abin da zai faru”
Shiru Nana ta yi tana tunanin hukunci da zata yanke, Can dai ta numfasa ta ce“Ni dai wallahi bana so!”
Daga haka ta tashi ta bar wajen da sauri, Da idanu Mu’ash ta bi ta sai kuma ta girgiza kanta a fili ta ce
“Allah wadaran naka ya lalace, Nana! Nana!”
****
Bayan sallar isha’i tana kwance akan cinyarsa yana operating system ɗin gabansa, Kamar wadda aka tsikara haka ta mike zaune tana kallon sa ta ce
“Uncle”
“Uhm..”
Ya ce ba tare da ya ɗago kansa ba, Ɗan sosa kanta ta yi kafin ta kwaɓe fuska ta ce
“Dama tambayar ka zan yi”
Ɗago manyan idanunsa ya yi ya zuba mata, Ta yi saurin ɗauke nata. Babu yabo babu fallasa ya ce
“Nana ki bar ni na gama abin da nake dan Allah.”
“To magana zan yi fa”
Ta bashi amsa kamar me shirin fashewa da kuka, Rufe system ɗin ya yi dan ya san tun da ta fara haka ba zata bar shi ya ƙarasa ɗin ba. Ya jawota jikinsa ya ce
“Ina ji mene ne?”
Hannunsa ta saka ta fara murɗa lallausan gemunsa kafin ta ce
“Uncle wai ba zan iya karatu ba idan ina da ciki?”
Da sauri ya kalleta ya ce
“wane ya faɗa miki?”
Tura baki ta yi ta ce“Ni kawai ka faɗa min!”
Ɗauke kansa ya yi yana kallon saitin window, ya ce
“Me zai hana ki karatun ki Nana? Muddin kina da lafiya ai zaki iya zuwa makaranta, Sai dai idan kin kuka haihuwa ki ɗauki hutu”
Shiru ta yi tana nazari, Ya mai da idanunsa kanta ya ja kumatunta ya ce
“Wane ya ce miki ba’a karatu da ciki?”
Girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce
“Babu kowa”
“Ƙarya zaki min?”
Ya ce yana tsuke fuska. Sunkuyar da kanta ta yi, Ya girgiza kansa ya ɗago fuskarta ya ce
“Kwana biyu uncle ya yi missing Nanar sa”
Sarai ta gane abin da yake nufi, Dan haka ta fara ƙoƙarin sauka daga jikinsa amma ya riƙeta gam.
“Mene ne?”
Ya ce yana ƙoƙarin zare ribbon ɗin data tufke kanta dashi, Kamar zata yi kuka ta ce
“Uncle bacci zan yi”
“To kwanta”
Ya faɗa yana tura hannunsa cikin sumar kanta, Lumshe idanun ta ta yi, Saboda dadin susar da taji. Ya ɗauke system ɗin daga kan gadon sannan ya gyara mata kwanciyarta, Ya sanya hannunsa ya kashe hasken ɗakin nan da nan duhu ya mamaye ko ina.
****
Yola, Nigeria.
Yau wata ɗaya kenan da tariyar Anty Khadijah, Tana zaune gefen gadonta ta zuba uban tagumi aka yi sallama aka shigo, Ɗaga kanta ta yi tana kallon yaron da ke tsaye a kanta. Yana ɓare gyaɗar dake hannunsa ya ce
“Wai in ji Baba ya ce baki gama abincin ba yunwa yake ji?”
Tsabar baƙin ciki rasa abin ce masa tayi, Ta miƙe ta bar wajen tana kwafa. Tsayawa yaron ya yi yana kallon ta ganin ta koma kan kujera ta zauna, Ya juya ya fice daga ɗakin, After some minutes aka buɗe dakin aka shigo cikin ɗaga murya yana cewa
“Khadijah! Khadijah! Khadijah!”
Kallon sa kawai Anty Khadijah ta yi sai kuma ta ci gaba da danna wayarta, Rai ɓace Malam Garba ya ce
“Ke tsabar rashin mutunci kina ji ina miki magana kin yi min banza! Bayan na aiko yaro baki bashi amsa ba? Me ki ke taƙama dashi ne?”
Miƙewa tsaye ta yi a fusace ta ce
“Ban sani ba ɗin! Ba kuma zan yi bane, Wallahi ba zan ci gaba da dafa uban abinci ba a cikin gidan nan, Ban haifa ba babu wanda zan yi wa girki! Dan haka idan ma zaka nemi mai girka maka abinci ka nema ni ba yar iska ba ce…”
Saukar marukan da taji shi ne abin da ya sanya ta yi shiru da maganar tata, Ta sanya hannayenta duk biyun ta rike kuncinta tana kallon sa. Can kuma ta ce
“Na rantse da Allah baka isa ba! Wallahi ba zan yarda ba! Kai ka isa ka dinga dukana”
Ko rufe baki bata yi ba ya hau ta da duka ta ko ina, Tun tana ƙoƙarin kwacewa har sai da ta ƙasa koda motsi a ƙasan ya sanya ƙafarsa ya take hannunta cikin masifa da kumfar baki ya ce
“Ke har kin isa a gidana? Ban auri wadda zata ɗaga min murya ba! Duk ranar da ki ka kara yi min irin haka wallahi sai na karya ki”
Ya yi ball da ita kamar ya samu ƙwallo, Ta bugu da jikin gado, Ya juya har ya kai ƙofa sai kuma ya dawo yana kallon ta ya ce
“Kuma idan baki tashi kin fito ba wallahi na dawo sai kin raina kan ki!”
Ya zabga mata harara sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Tsananin azaba ta sanya Anty Khadijah kasa motsi a wajen, Ga ciwon da jikinta ke mata, Ga kuma na duka. Yau kusan kwana uku kenan kullum sai ya yi mata mugun duka da zarar ɗan abu ya haɗa su, Ta dinga kuka a wajen tana numfarfashi, Tafi awa ɗaya kwance kafin ta iya tashi zaune. Gefen bakinta sai jini yake sakamakon marukan da ya yi mata, Dakyar ta lallaɓa jikinta ta tashi ta shige banɗaki, Wanke fuskarta ta yi dan babu wadataccen ruwan da zai ishe ta ta yi wanka. Ta dawo ta kwanta akan kujera tana gursheƙen kuka. Bayan mintuna goma ta tashi tunawa da abin da ya ce, Dan ta san idan ya dawo wani sabon dukan zai mata. Ta dinga takawa dakyar ta fito daga ɗakin, Kasancewar yammacine ya sanya soron ya ɗan yi duhu, Ta nufi soron da yake zaune dan ta tambaye shi abin da za’a girka ɗin. Maganar data jiyo ya sanyata tsayawa cak a bakin ƙofar, Muryar Kaddu taji tana bala’i tana masa magana, Malam Garba ya yi murmushi ya ce
“Ke ki rufe min baki idan har ba so ki ke na ɓatar da ke ba!”
Kaddu da ke tsaye tana jijjiga ƙugu ta kalle shi ta ce
“Idan ka fasa! Dan girman Allah kada ka fasa ɓatar dani, Ka manta duk abin da nayi maka. Haka muka yi da kai? Wallahi baka isa ba, Yanda ka ce zan auri mutumin nan idan na bawa Khadijah wannan maganin ka aureta to wallahi sai ka saka na aure shi! Dole ne wannan, Mahaukaciya ma zaka mayar dani kenan!”
Da wani irin mamaki Anty Khadijah ke sake buɗe idanun ta, Ji ta yi kunnuwanta na neman jiye mata wani tashin hankali, Ko dai ba Kaddun data sani ba ce? .
Malam Garba ya girgiza kansa yana wata irin muguwar dariya, Lokaci ɗaya kuma ya tamke fuska ya ce
“Dani zaki ja? Me ki ke tunani? Na saka kin min aiki akan Khadijah saboda na biya ki da wanda take shirin aure?.” Ya tuntsire da dariya sannan ya ci gaba da faɗin
“Har abada ba zaki aure shi ba, Ke bama zaki yi aure ba. Haka zaki yi ta gararamba a gari, Shi kansa barikin sai an daina nemanki. Kuma babu abin da ki ka isa ki yi min, Ni Garba ni ne me abin yi, Idan na so a yau sai nayi abin da zai sa ba zaki kwana da rai ba!”
Wata irin shewa irin ta yan bariki Kaddu ta yi ta tafa hannu sannan ta ce
“Ai ko zan nuna maka wace Kaddu! Zan shayar da kai mamaki! Wallahi ina da bokayan da sai sun kashe min kai! Kuma ka jira abin da zai biyo baya. Zaka gani!”
Tana gama faɗin haka ta zura takalmanta ta yi waje ko mayafin bata yafa ba, Ban da dariya babu abin da Malam Garba ke yi, Ya dinga girgiza kansa yana daga zaune. Juyawar da zai yi suka haɗa idanu da Anty Khadijah, Ya tashi tsaye yana kallon ta a ɗan daburce ya ce
“Kkk… Khadijah!”
Girgiza kanta ta dinga yi hawaye na zubowa akan fuskarta, Ya tako har gabanta yana kallonta ya ce
“Kina ji”
Anty Khadijah bata ce komai ba ta juya ta nufi hanyar daƙinta, Tana kai wa bakin ƙofa ta faɗi a ƙasa Sumammiya. Malam Garba ya yi kanta da gudu yana kiran sunanta.
****
Zahra na zaune kan kujera a parlour tana danna wayarta aka buɗe ƙofar dakin, Shigowa suka yi bakin su ɗauke da sallama. Ta amsa da fara’a tana fadin
“Laaa Yaya sannun ku da zuwa”
Babban ciki ne ya amsa da
“Yauwa Zahra’u”
Suka zauna kan kujera ta miƙe tana fadin “Bari na kira Umman” To kawai ya ce sannan ta nufi sama da sauri. Buɗe ɗakin Umma ta yi ta shiga, Ta sameta zaune kan dadduma tana jan carbi, ƙarasawa ta yi ta zauna gefen gadon tana kallon ta ta ce
“Umma kin yi baƙi”
Sai da ta ƙarasa lazumin da take ta shafa sannan ta juyo ta kalleta ta ce“Su wane?”
“Yaya Bashir ne, Da Kamal ƙaninsa”
Da ɗan mamaki Umma ta ce
“Ikon Allah yaushe Bashir ya dawo?”
“Kamar rannan naji a group ɗin gida an ce ya dawo”
Sai da ta miƙe ta naɗe daddumar sannan ta ce
“Allah sarki bari naje mu gaisa”
To kawai Zahra ta ce, sannan ta kwanta gefen gadon, Ita kuma Umma ta fice daga ɗakin. Wayarta ta ɗauka ta shiga gallery tana kallon hotunan Noor, Can kuma ta kai kan wani hoton Abdusammad wanda yake zaune cikin office ɗin sa, Sanye da suit, Bai ma san ta dauki hoton ba sanda ta taɓa zuwa asibiti wajen sa. Iyaka kyau hoton ya yi kyau musamman yanda ya yi murmushi yana ƙoƙarin mata magana, Ji ta yi wani iri a jikinta, Ta yi saurin ajiye wayar a gefe, Cikin yan mintuna sai ga hawaye na zubowa gefen idanunta. Tabbas ta yi kewarsa, tana kan yi kuma, Kullum sai ta tuna shi, Idan ba shi ba to Noor. A duk sanda ta tuna shi sai taji ina ma ta tashi ta bi shi, ina ma bata dawo ƙasar nan ba, Ina ma ƙaddara bata rabata dashi ba, Har yanzu bata daina sonsa ba. Kamar yanda ta san shi ma bai daina sonta ba, Kawai dai yana ƙoƙarin mantawa da ita ne. Haka ta dinga tunanin sa a wajen tana sake-sake a zuciyarta, Can kuma ta ɗauki wayar kamar wadda aka yi wa dole haka ta hau dialing numbern sa. Ganin har ta katse bai ɗauka ba ya sanyata ajiye wayar, wasu zafafan hawaye suka ci gaba da zubowa kan fuskarta. Daga karshe ma tashi ta yi ta fice daga ɗakin ta koma nata.
****
New York.
Nana na zaune kan sofa tana kallon tv kasancewar ranar Saturday ne babu lecture taji wayarsa na ringing, amma har ta katse bata tashi a inda take ba. Tunawa ta yi da chocolate ɗin ta ta jiya da suka siyo ta miƙe ta nufi cikin ɗakin ta, Ledar gaba ɗaya ta dauko ta dawo parlour, Samu wayar ta yi tana ci gaba da ringing. Ta ajiye ledar kan kujera sannan ta nufi inda wayar take, Kafin ta ɗauka ta katse, Ta ɗan yi tsaki sai kuma ta koma ta zauna da wayar a hannunta, kasancewar ta san password ɗin ya sanya ta cire dan ganin wanda yake kira. Koda ta shiga call log ɗin sunan Buddy ta gani a sama, Ta taɓe baki tana ƙoƙarin ajiye wayar idanunta ya sauka akan sunan dake ƙasan na Aliyun.
“Zahra!”
Ta faɗa a fili tana sake ware idanun ta kan screen ɗin, Mamaki ne ya kusan kasheta, Duk da ta san da ba haka ya yi saving numbernta ba. Amma ta san bashi da wata mai irin sunan, Dan haka ta danna kira dan ganin wacece. Har ta gama ringing ba’a ɗauka ba, Tayi kamar ta ajiye wayar sai kuma ta sake danna kiran, Sai da ta kusan katsewa sannan aka ɗaga, Daga ɗaya bangare Zahra ta ce
“Hello, Salamu alaikum.”
Wani irin abu ne ya zo ya tokarewa Nana a ƙijri, Ta kasa koda haɗiyar yawu, Jin ba’a yi magana ba ya sanya Zahra ta yi ƙasa da murya ta ce
“Docco… Doctor!”
“Algunguma! Muguwa azzaluma, mai kashe mutane! Uban me yasa ki ke kiran sa? Me zai miki? Ko shi ma kashe shin zaki yi? To wallahi Uncle yafi karfin ki! Banza kawai, Dangin masu kisa!”
Da mugun mamaki Zahra ke sauraren kalaman Nanar, Dan bata yi tunanin ita ce ta ɗaga wayar ba, Ta kasa cewa komai tana jin wani irin zafi a zuciyarta. Cike da masifa Nana ta ci gaba da faɗin
“Na rantse duk ranar da ki ka sake kiran mijina sai na yi miki abin da ba zaki manta dani ba! Banza kawai masu kashe mutane! Dangin da babu Allah a ransu!”
“Nana!”
Ya kira sunanta a tsawace. Kallon sa ta yi ganin yanda ya yi tsaye a wajen yana kallonta da mamaki, Kafin ya ƙaraso ya karɓe wayar yana faɗin
“Ke dawa? Wa ki ke zagi haka?”
Ƙoƙarin fizge wayar ta fara yi tana cewa
“ni ka bani, Ka bani na zageta! Kwartuwa mai kiran mazajen mutane!”
Wata irin tsawa ya daka mata wadda ta sanyata shiga cikin hankalinta, Ta tsaya tana kallon sa. Sai a sannan ya kalli screen ɗin ya ga sunan wadda ke kiran, Bai ce komai ba ya juya ya bar wajen da wayar a hannunsa. Nana ta dinga bin sa da kallo kamar wata zararriya, Tama kasa gane abin da ya yi. Shi ko cikin ɗakin ya koma sannan ya kai wayar kunne muryarsa a nutse ya ce
“Zahra lafiya dai ki ka kirani?”
Zahra da taji wani irin abu ya tsaya mata a ƙirji ta kasa magana, Sai shessheƙar kuka da take. Ya gyara tsaiwarsa ya ce
“Subhanallahi lafiya dai? Ko wani abun ya faru?”
Girgiza masa kai ta yi tana ƙoƙarin ɓoye kukanta ta ce
“Doctor ba komai, kawai kiran ka nayi na gaishe ka”
Ta ƙare maganar hawaye na yar rige-rigen sauka kan fuskarta. Jinjina kansa ya yi dan yana da fahimta ya ce
“Allah sarki to ya ku ke? Ya Umma?”
“Tana nan kalau”
Ta bashi amsa a sanyaye, Ya gyaɗa kansa kafin ya ce
“To ki gaishe min da ita. Na gode, Sai an jima”
Ji ta yi kamar kar ya katse wayar, Amma ta dake ta ce
“Tom in sha Allah, Na gode.”
Daga haka ta kashe wayar. Ajiyar zuciya Abdusammad ya sauke sannan ya girgiza kansa, Ya zura wayar cikin aljihun trousern da ke jikinsa sannan ya fito daga ɗakin. Durƙushe ya samu Nana a wajen sai kuka take, Ya yi kamar ya wuce sai kuma ya nufi inda take. Tsayawa ya yi a gabanta yana kallonta fuska babu walwala ya ce
“And this should be the last time da za’a kirani a waya ki ɗauka, Koma wane kar ki sake ɗaga min waya. Sannan kada ki sake zagin wani tun da bake ya kira ba, Bana son tashin hankali. Ki nutsu ki kama kan ki! Idan ba haka ba sai na ɓata miki fiye da tunanin ki wallahi!”
Ya ƙare maganar a ɗan zafafe, Ita dai ko ɗago kanta bata yi ba, Ya ja tsaki sannan ya juya ya fice daga parlon. Sai a sannan ta ɗago idanun ta wanda suka yi jajur, Ta kalli hanyar ƙofar sai kuma ta fashe da wani raunataccen kuka.



