Chapter 52: Chapter 52
Ta amsa cike da girmamawa. Shiru Nana ta yi can kuma ta ce“Alright thank you”
Ta ɗan sirina sannan ta ci gaba da tafiyarta, Jiki a saluɓe Nana ta koma daƙinta ta zauna. Yinin ranar ma haka ta yi shi a dame, Ko abinci kasa ci ta yi duk da yunwar da take cikinta, Sai wajen isha’i ta tashi ta sake wanka sannan ta yi sallah ta koma ta zauna. Ranar ma bai shigo gidan ba har bacci ya ɗauketa, Da asuba kuwa ta farka, Ta tashi tsam ta fice daga ɗakin gudun kada ya fita bata gan shi ba, Koda ta shiga ɗakin nasa samu ta yi ya tafi masallaci dan haka ta nufi banɗaki ta yo alwala ita ma, A ɗakin ta yi sallah dan akwai kayanta a ciki. Tana nan zaune har gari ya fara haske amma bai shigo ba, Dan haka kawai ta tashi ta fito waje ta tsaya. Ganin bashi da alamar shigowa ya sanya ta koma daƙinta zuciyarta kamar zata fito. Sai da suka jera kwana biyar suna wasan ɓuya dashi, Duk irin yanda take son ganin sa bata samun dama, Sai dai ta zauna ta yi ta kuka. Amani ta kirata yafi sau goma amma bata ɗauka ba, Daga ƙarshe ma blocking numbernta ta y, Ranar juma’a tana zaune ta zuba uban tagumi wayarta ta fara ringing, Kamr ba zata dauka ba sai kuma ta janyo wayar tana kallon mai kiran. Surry ce dan haka ta ɗaga ta kai kunne, Cikin faɗa ta fara cewa
“Nana baki da hankali ko? Baki san abin da ki ke ba ko? Akan me zaki biye wa su Amani? Bayan kina da tabbacin basu da ilimin addini. Kin san laifin wanda ya zubar da ciki kuwa? Ya za’a yi ki zubar da ciki ma? Kina hauka ne Nana? Kenan duk wanda ya baki shawara sai ki ɗauka, ba zaki tsaya ki tantance mai kyau da mara kyau ba. Nana kina son ubangiji ya dube ki kuwa?”
Allah sarki Nana, Tun da ta fara magana ta ke kuka, Ta san su Amanin ne suka faɗa mata abin da tayi. Surry taja dogon tsaki ta ce
“Ki bar wannan kukan da ba zai amfane ki ba, Yanzu ki faɗa min kin yi amfani da maganin? Kin zubar da cikin?”
Girgiza kai ta yi cikin kuka ta ce
“A”a”
Surry ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce
“To kada ki kuskura ki zubar, Ke kada ma ki sake sauraren abin da zasu ce miki”
“Tom. Ai ma Uncle ya ɗauke, kuma ya daina kulani, ko ganin sa bana yi a gidan nan”.
Cikin faɗa Surry ta ce
“To akan me ba zai daina kula ki ba Nana? Akan me? Ke ko tausayin sa bakya yi. Kina gani ƴar sa ce ta mutu ba’a jima ba, Yanzu akwai abin da yake buƙata sama da Ya’ya ne? Shi ne zaki zubar da ciki. Dole koma wane ya daina kula ki, wallahi ya yi miki da kauna ma, Da bai miki shegen duka ba, Ki nutsu ki kama kan ki wallahi, Idan ba haka ba ki gurguɗe auren ki.”
Cikin kuka Nana ta ce
“In sha Allah ba zan sake ba, Kuma ai inason na bashi haƙuri ne, amma bana ganinsa, kullum sai nayi bacci yake dawowa. Kuma da safe kafin na tashi yake fita, Yaƙi bari na ganshi”
Rage murya Surry ta yi yanda zata fahimceta ta ce
“Kina ji ki nutsu, Yau kada ki yi bacci, Ki san yanda zaki hana kan ki bacci har ya dawo.”
“To ai idan ya dawo ya ganni ba zai kulani ba, Ɗakinsa zai shiga ya rufe”
Shiru Surry ta yi tana tunani, Can kuma ta ce
“To yanzu ke je ɗakin nasa ki zauna, Kada ki yi bacci har ya dawo, Idan ya shigo sai ki san yanda zaki bashi haƙuri.”
Jiki a sanyaye Nana ta amsa sannan ta kashe wayar.
Da daddare tana ganin 9:00 ta yi ta tashi ta yi wanka, Ta shirya cikin kayan baccinta riga doguwa wadda ta tsaya iya gwuiwarta, Fararen ƙafafunta sun bayyana. Ta gyare gashinta sai Sheƙi yake, Hijabi ta ɗauka ta saka sannan ta fice daga ɗakin, Nasa ɗakin ta shiga ta zauna kan kujera ta yi shiru. Tun tana saka ran dawowarsa har sai da ta yi giving up, Ban da gyangyaɗi babu abin da take yi. Tashi ta yi ta buɗe balcony ta shiga, Ta dinga kallon ƙasan gidan gwanin ban sha’awa. Tana nan tsaye har after 25mins ta hango shigowarsa a mota, Nana ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin daɗi, Duk da bata san ta inda zata fara bashi haƙurin ba. Sake rufe balcony ɗin ta yi ta yi shiru tana jiransa, Tana ji ya shigo ya ajiye wayarsa da car key a gefen gado sannan ya nufi toilet. Ya jima kafin ya fito sanye da bathrobe, Ya buɗe press ɗin sa ya dauki boxer ya saka sannan ya tsaya yana shafa mai. Sai da ta yi addu’a kafin ta buɗe balcony ɗin ta fito, Sam bai ji sanda take zuwa ba sai kawai ji ya yi an rungume shi ta baya, Ta riƙe shi da iya ƙarfinta sai kuka take. Yi ya yi kamar bai san tana gun ba, Ya ci gaba da shafa man sa. Cikin kuka ta ce
“Dan Allah uncle ka yi haƙuri, Ba zan sake ba. Wallahi ba zan sake ba, Na daina, Na tuba uncle, Ba zan kuma yi maka ba. Ba zan sake ba wallahi, Na yi kuskure kuma ba zan ƙara ba, Ka yafe min dan Allah. Kada Mala’iku su dinga fushi dani…”
Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka, Ba zaka taɓa cewa da Abdusammad take ba, Dan ko kezau bai yi ba, ballantana ta saka ran zai ce wani abu. Sai da ya gama abin da yake gaban mirror ɗin sannan ya janyeta daga jikinsa ya karasa gaban gadon, Hawa ya yi ya zauna ya janyo laptop ɗin sa ya kunna ya fara operating ɗinta, Nana ta yi kamar statue a wajen tana kallon sa tana kuka. Can kuma ta ƙaraso ta tsuguna gaban gadon cikin kuka take faɗin
“Dan Allah uncle ka yafe min, Ba zan sake cewa zan zubar ba. Wallahi ban zubar ɗin ba, Ba zan ƙara ba. Ƙawayena ne suka ce wai baka sona saboda cikin, Idan na zubar zaka dawo yanda ka ke yi min da. Shiyasa na yarda, wallahi ba da wani abun ba, Dan Allah ka yi haƙuri, Kada ka faɗawa Abbana da Ammata. Dan Allah uncle…”
Tashi ta ga ya yi ya fice daga ɗakin, Tabi bayansa da kallo sai kuma ta kifa kanta jikin gadon tana ci gaba da kuka, After some minutes ya dawo hannunsa riƙe da mug, Ya koma ya zauna ya ci gaba da abin da yake yana sipping coffee ɗin a hankali. Bata fasa bashi haƙuri da magiya ba, Haka shima ko da wasa bai kalli inda take ba. A haka har ya kammala abin da yake a system ɗin ya rufeta ya ajiye gefe, Tashi ya yi ya fice daga ɗakin bai jima ba ya dawo ya shiga toilet, wanke bakinsa ya yi ya dawo ya haura saman gadon yana shirin kwanciya. Wata irin zabura Nana ta yi ta riƙe ƙafafunsa tana wani irin kuka kamar wadda aljanu suka shafa, Tama masa maganar sai kukan kawai take tana buga kanta akan ƙafafunsa. Ganin tana neman zare masa ya sanya shi janye ƙafafunsa, Ya ƙura mata idanu yana kallon ta can kuma ya tashi zaune muryarsa a dake ya ce
“Ɗagani”
Ai kamar ya turata haka ta ci gaba da da kukan tana ƙanƙameshi. Ya girgiza kansa sai kuma ya ce
“Me zan yi miki? Ki bar ni na huta mana, Ki yi abin da ki ke so. Ki dau duk hukuncin da ki ka ga ya dace miki, amma ki daina damuna. Ki bar ni dan Allah!”
Ya ƙare maganar a nutse, Ai kamar jira take ta shige girgiza kanta cikin kuka ta fara cewa
“Wallahi A’a uncle ba zan kuma ba, Na nutsu, Ba zan ƙara yi maka rashin kunya ba. Ba zan sake yin rashin jin magana ba, Zan zauna lafiya dan Allah ka yi haƙuri”
Taɓe baki ya yi still looking at her ya ce
“Kin ji na yi miki magana akan ki daina abin da ki ke? Kin ji nace Nana bari? Ai bana so ki bari. So nake ki ci gaba, Ki ci gaba da duk abin da ki ke, Ba dai burin ki hankalina kada ya kwanta ba? Ba dai burin ki ki dinga sakani damuwa ba? To ki je ki ci gaba. Zan auro wadda zata dinga jin maganata, Ta kuma dinga girmamani. Ki je ki yi abin da ki ke ganin ya dace da rayuwarki!”
Haba ai ji ta yi kamar ta faɗi ta mutu saboda baƙin ciki, Ta saki wata irin ƙara tana ƙoƙarin yin baya, Cikin zafin nama ya tarota gudun kada ta faɗa kansa, Ya jawota jikinsa jin ta daina numfashi. Kumatunta ya dinga taɓawa yana cewa
“Ke Nana! Nana! Open ur eyes. Nana! Mamanaa. Mamanaa! Open ur eyes kin ji, Da wasa nake miki, I’m just kidding, Ba zan auro wata ba, Stay still kin ji.”
Ko kaɗan Nana bata jin abin da yake cewa dan tuni ta sume a wajen, Ya kwantar da ita ya tashi cikin tashin hankali ya fice daga ɗakin, Da sauri ya dawo hannunsa riƙe da gorar ruwa mai sanyi, Ya buɗe ya yayyafa mata. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana wani irin numfarfashi, Ya ajiye ruwan a ƙasa ya hau kan gadon ya ɗauketa ya riƙeta a jikinsa. Ganin tana ƙoƙarin tashi ya sanya ya sake riƙeta ya ce
“Stay still kin ji, Da wasa nake miki. Babu abin da zai sa na sake aure”
Fashewa ta yi da wani raunataccen kuka,Ta ɓoye fuskarta a jikinsa cikin kuka take fadin
“Dan Allah uncle kada ka sake auren wata, mutuwa zan yi wallahi. Ka bari uncle ka ji,ba zan sake ba, ba zan kuma yi ba!”
Gyaɗa mata kai ya dinga yi dan tausayi ta bashi, Ya shafa kanta ya ce
“shikenan na haƙura Nana. Dama tuni na haƙura, baki ga ban miki faɗa ba? Na haƙura kinji. But ki saka a ran ki uncle ba zai taɓa kin ki ba, Ina son ki Nana! Ina son ki tun kina tsummanki, Ina son ki tun ranar da Amma ta haifeki, Da a lokacin na samu dama tuni zan aure ki Nana, Kawai nayi shiru ne saboda kada a ga son zuciyata. Na rayu da soyyarki Nana, a rashin ki na auri Zahra, kullum da tunanin ki nake kwana nake tashi, Aliyu ne kaɗai ya san abin da ke zuciyata, Shiyasa sanda na samu labarin aure ku na je Nigeria da tunanin yanda zan yi na mallake ki. Da yake Allah ya hukunta ina da rabon auren ki sai ya kawo wancan hatsaniyar, amma har na fitar da rai Nana. To ya za’a yi na ce bana son ki kuma? Ya za’a yi na ce haka Nana? Nafi kowa son ki, ko Abba sai da ya gane haka. Ina son ki sosai Nana, Sannan cikin da ke jikin ki babu abin da ya kara min illa ƙaunar ki, Ban taɓa son abu kamar yanda nake son ki ba Nana. Komai naki burgeni yake, Shirmenki, Wasan ki, Shagwaɓar ki, Tsiwar ki da kuma kukan ki. Ina son komai naki Nana, Ina son ki , Uncle na son ki! Uncle na son ki sosai Nana.”
Ji ta yi kamar zuciyarta zata fito, ta rasa wane irin hali take ciki, Farin ciki ko kuwa baƙin ciki, Ta kasa magana sai kuka da take kamar ranta zai fita. Ɗago fuskarta ya yi yana goge mata hawayen ya ce
“Ki yarda da uncle Nana, Duk abin da nake miki ba wai ina yi bane dan na cutar da ke. A’a ina yi ne saboda naga kin zama mutum, Idan da ta ni ne babu ruwana, Zan zauna da ke da halin ki wallahi. Amma jama’a nake ji Nana, Ina son ki zama mutum ki shiryu ki daina wasu abubuwan, Na yarda ki dinga yiwa uncle. Amma da zarar kin fita ki zama babbar mace, Matar minister of health Doctor Abdusammad M Shuwa, ki zama yarinyar kirki Nana.”
Gyaɗa masa kai kawai ta dinga yi tana shessheƙa kuka, Ya ɗan yi murmushi ya ja kumatunta ya ce
“My cry cry baby, Mamana sarkin kuka”
Hannunta ta saka ta rufe fuskarta, Ya ɗauke kansa yana dariya. Sun ɗauki mintuna a haka kafin ta ce
“Uncle”..
“Na’am Anty…”
Ya faɗa a sigar da ta yi maganar, Tura baki ta yi ta ce
“To nima ai ina son ka fa. Kuma ma shiyasa na ce bana son Yaya Sultan fa, Har muka yi faɗa da Amrah da ta ce tana sonka. Ai nima ina son ka, Shiyasa nake zuwa Apartment ɗin ku na zauna saboda na ganka. Kuma shi ne kai baka sona, kafi son Anty Zahr…”
Caraf ya kame bakin maganar da nasa, Ya fara kissing ɗinta cikin salo mai rikita wanda ake yi wa, Tuni suka fara hargitsa nutsuwar kansu. Muryarsa na rawa ya ce
“Nana i love you, I love you so much. I can’t do without you, Please Nana kada ki bar ni, Ki so uncle ɗin ki. Ki yi min wannan alfarmar, Kada ki bar ni Mamana!”
Cikin kuka ita ma ta ce
“Toh uncle, Nima ina son ka ai, Kuma ina sonka sosai. Ina son komai naka uncle, Nafi sonka wallahi, Nafi Hajiya Babba son ka, Nafi Yaya Aliyu da Abba son ka. Ni kaɗai nake son ka Uncle ɗina!.”
Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka mara sauti, Bai ce komai ba ya mai da bakinsa cikin nata yana kissing ɗinta as if his life depends on it. A daren ranar sun yi kamar su cinye junansu saboda ƙauna, Duk wani sirri da ke ɓoye sai da suka faɗawa junansu, Daga ƙarshe ta shige jikinsa tana sakin wata irin ajiyar zuciya mai nuna kwanciyar hankalin da take ciki.
****
Ranar wata talata suna zaune cikin ɗakin Siyama na kallon Anty Khadijah da ke faman kuka, Umma da ke zaune kan farar kujera ta roba sai jan carbin hannunta take ta girgiza kanta ta ce
“Khadijah ba zaki daina kukan nan ba? Ba zaki fawallawa Allah komai ba?”
Anty Khadijah ta girgiza kanta tana hawaye ta ce
“Umma na kasa, Zuciyata zafi take min, Umma ya zan yi da hakkin mutane? Ya zan yi Umma? Da wane ido zan dubi ubangijina? Na rasa wane irin tunani ma zan yi. Na cutar da ƴar uwata ta jini, Na rabata da gidan mijinta da kuma ƴarta saboda son zuciya irin tawa, Na cutar da ƴar dana haifa da kaina na kai ta inda aka lalata rayuwarta, wace irin uwa ce ni Umma? Wace irin zuciya gareni!”
Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan. Gaba ɗaya kuka suke, Zahra, Siyama, Safeena da kuma Amal. Umma ma daurewa kawai take saboda ƙarfin zuciya irin nata, Ta girgiza kanta zuciyarta cike da tausayin ƴar tata ta ce
“Ki gode Allah da ubangiji ya baki ikon ganin kuskuren da ki ke aikatawa, Ya kuma hukunta ki tun a duniya. Tabbas kina da rabon rabauta ne, Ba dan haka ba babu yanda za’a yi ki gane laifukan da ki ke aikatawar, Sai lokaci ya ƙure miki, A sanda babu damar da zaki gyara kuskuren. Amma a yanzu kina da wannan damar, Kuma kin nemi yafiyarta ta yafe miki, Allah ba zai kama ki da haƙƙinta ba, Ki ci gaba da istigfari na sauran laifukan da ki ka yi, Ba’a yanke tsammani da rahamar ubangiji, Allah mai yafiya ne. Kuma idan ya yafe baya kallon bawansa da abun, Mutum shi ne wanda yake cewa ya yafe kuma ya ci gaba da kallon ka da abun, Shi ko ubangiji idan ya yafe ya yafu. Ki ci gaba da tsarkake zuciyar ki, Ki kuma yi tuba na zahiri, Kada ki bari sheɗan ya sake cin galaba akan ki”
Sosai jikin kowa ya yi sanyi, Anty Khadijah ta amsa da to tana ci gaba da kukanta. Washegarin ranar aka sallameta daga asibitin, Duk da bata takawa sai dai a wheelchair, Koda suka dawo gida Siyama ce ke zama a daƙinta. Itama gaba ɗaya ta sukurkurce kamar ba ita ba, Ta yi baƙi ta rame, Ko ba’a faɗa ba an san ciwo ne yake ɗawainiya da ita. Duk da bata wasa da karbo magani, Cikin satin basu sami zama ba, Domin a cikin sa ne aka ɗaura auren Zahra da Bashir, Da kuma Safeena da Kamal. Kasancewar auren zumunci ne duk ya sanya ba’a yi wani taro ba, Zahra da kanta ta kira Abdusammad ta faɗa masa zata yi aure, Sosai ya yi mata murna. Ya kira Umma ya yi mata murna ita ma, Sannan ya tura 5m account ɗin Zahran ya ce ta bawa Umma, Godiya sosai suka yi masa, Aka sha shagalin biki kowace aka sadata da ɗakin mijinta, Gidan ya rage daga Anty Khadijah, Siyama sai Umma, Dan Amal ta koma makaranta. Kusan kullum haka zaka gansu a zaune sun zuba uban tagumi, Basu da aiki sai tunane-tunanen rayuwa, Umma ce ke kwantar musu da hankali wani lokacin, Tana faɗa musu komai me wucewa ne. Ranar da aka zo aka faɗawa Anty Khadijah Kaddu ta haukace kwana ta yi tana kuka, Sai a sannan ta sake gane girman laifin da suka yiwa Allah, Kaddu ta bata tausayi ba kaɗan ba, Duk da itama abar a tausayawan ce amma gara ita da hankalinta. Nakasa kawai ta samu, kuma tana ƙoƙarin mai da kanta mutuniyar kirki, Ana idar da sallahr asuba Umma ta shigo ɗakin tana kallon ta, Zaune take kan dadduma sai kuka take bayan ta idar da sallahr. Umma ta ƙarasa ta zauna gefen ta tana kallon ta ta ce
“Ki daina wannan kukan Khadijah, Ki mai da duk al’amuranki ga Allah, Ubangiji na son ki da rahama, Ki manta da abin da ya wuce.”
Cikin kuka ta ce
“Umma wani iri nake ji, Da Allah yaso da yanzu ina tare da Kaddu mun haukace ko? Na shiga ukuna, Umma dama na mutu, Dan Allah ki yafe min duk abin da nayi miki. Ki yafe min Umma”
Ta ƙare maganar tana ɗora kanta kan cinyar Umman, Girgiza kai Umma ta yi ta ɗora hannunta akan ta ta ce
“Na yafe miki Khadijah, Dama ban taɓa riƙe ki ba, Na san idan har ubangiji na karbar addu’ar da nake to tabbas wata tana zaki shiryu, Kuma gashi yanzu naga wannan lokacin. Allah ya yi miki albarka, Da ke da sauran ƙannen ki, Allah ya ci gaba da kare mu daga sharrin shaidan, Allah yasa mufi ƙarfin zuciyoyin mu, Da mu da sauran al’ummar musulmai baki ɗaya.”
Anty Khadijah ta sauke numfashi sannan ta ce
“Amin ya arrahamar-rahimin”
****
Nana ce zaune gefen gado tana zuba kaya a cikin trolley ɗin da ke gabanta, A sanyaye take komai tana nishi, Sakamakon cikin da ke jikinta wanda ya fito sosai. Abdusammad ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo yana kallon ta, Zama ya yi gefenta ya ɗauki sauran kayan ya ce
“Let me help you”
To kawai ta ce sannan ta ɗan matsar masa da trolley ɗin, Sai da ya kammala zuba kayan sannan ya rufeta. Ya juyo yana kallon ta, Kallon sa ita ma take, Tana sanye da doguwar riga ta abaya baby pink. Murmushi ta ga yana yi, Ta ɗan haɗe rai ta ce
“Uncle me ka ke wa dariya?”
Gyaran murya ya yi yana son fuskewa ya ce
“Nothing”
Ta sake zumɓura baki gaba tana kafe shi da idanu. Kallon ta ya sake yi sai kawai ya ɗauke kansa, Bai san sanda dariyar ta suɓuce masa ba, Ya dinga yi mata dariya yana kallon ta. Ita ko ta cika ta yi fam dan ƙaramin abu ne yake ɓata mata zuciya yanzun, Gaba ɗaya cikin ya mai da ta wata masifaffiya. A fusace ta ce
“Ni ai ba mahaukaciya ba ce da zaka dinga kallona kana min dariya.”
Ta ƙare maganar kamar zata yi kuka, Girgiza kansa ya yi cikin dariya da raha ya ce
“Kin san me? Gani na yi hancin ya yi kamar na Hippopotamus, Idanun ki sun sha kwalli kamar me bada maganin gargajiya…” Ya ƙare maganar yana tuntsire da wata sabuwar dariyar. Kuka ta saka ta fara dukansa ko ta ina tana cizonsa, Ya ci gaba da dariyarsa can kuma ya riƙe hannayenta still smiling ya ce
“Na tuba madam, Kin yi min kyau ne fa.”
Fashewa ta yi da kuka ta shige jikinsa tana cewa
“Ai naga ba haka ka ganni ba, Kuma wallahi bana son cikin ma.”
Dariya kawai ya yi ya rungumeta a jikinsa, Can ya shafa cikin nata yana jin yanda yaron cikin ke motsi ya ce
“Hiii unborn, Ka samu ka fito duniya mamarka ta bar ni da rigima”
Tura baki ta yi bata ce komai ba, Ya tashi da ita a hannunsa yana faɗin
“Madam haka ki ka zama? Kin ji nauyin ki kamar bag ɗin shinkafa”
Shiru ta yi masa dan ta san so yake ta yi maganar, a kwanakin nan ya mai da ita kamar wata kakarsa, Kullum cikin tsokanarta yake. Wani lokacin ta biye masa wani lokacin kuma ta yi masa kunnen uwar shegu, A haka suke fito daga gidan ya sakata a mota sannan shima ya shiga kai tsaye kuma airport suka nufa dan Nigeria zasu je suna.



