Chapter 53: Chapter 53
Cike estate ɗin yake da mutane, Na birni dana ƙauye, Ashe sunan matan gidan ake. Masu decorations na musamman aka ɗauko suka zo suka yi decorating wajen, Aka saka kujeru huɗu da bannern jarirai huɗu. Sai da masu jegon suka fito sannan aka fara gane su wane, Maimoon ce da Haule, Hamida da kuma Amrah, Sun ci kwalliya cikin wani uban su lace mai azabar kyau da tsada. Kowacce an yi mata make -up a fuska suna rike da jariran su, Suma mazan haka suka shirya cikin wata dakkakiyar shadda gezner brown colour, Sun yi ɗinki iri ɗaya har Abdusammad. Sai shige da fice kowa ke yi, Suna aka yi gagarumi dan haɗe shi aka yi, aka ce a bari duk su haihu sai ayi, Kasancewar Nana na da tazara dasu sosai yasa ba’a saka da ita ba, Maimoon Mace ta haifa, Hamida da Amrah ma haka, Haule kuma ta haifi namiji. Yar gidan Maimoon sunan Ummi aka saka mata, Suna ce mata Ummi, Ita kuma yarinyar Hamida sunan Hajiya Babba aka saka mata wato takwarar Nana, Suna ce mata Ikram, Ita kuma yarinyar Amrah sunan Mommynta aka saka ana ce mata Khairiyya, Shi kuma yaron Haule aka mayar masa da sunan mahaifinsa marigayi Safwan, Ake kuma kiransa da sunan. Taro aka yi bana wasa ba, aka ci aka sha aka watsa Naira, Da daddare kowa ya tafi sai ya’yan gidan kawai, Nana kuwa kuka ta dinga yi saboda gajiyar da ta yi, Ita sam bata saba kujiba-kujiba ba a gida, Daga kwanciya sai cin abinci take. Yau kuma ta zo ta sha uban wahala dan ko zama bata yi ba, Sai da Abdusammad ya siyo mata magani ta sha sannan ya samu ta yi bacci kan ƙafarsa. Sati ɗaya kawai suka yi ya cewa Hajiya Babba zasu wuce, Ta ce sai dai ya bar Nana a nan ya tafi ta haihu a gida. Da fari ƙin yarda ya yi, Saboda ya san Nanar ce ta kitsawa Hajiya Babba haka, Dan tun a New York take ce masa ya barta a gida, Sai da Papa ya shiga maganar sannan ya bar ta ya shige shi kadai, Ko sallama ko bai yi da ita ba. Ita ma bata damu ba saboda ganin ta da ta yi cikin yan uwanta tana shiga tana fita yanda take so.
**** Tunda cikin Nana ya shiga watan haihuwa babu wanda ya ƙara samun sukuni, Ko ciwon kai taji ta dinga kuka kenan tana raki, Dama tuni Amma ta koreta daga apartment ɗin ta, A cewar ta ba zata iya da iya shegenta ba, Ta yi zamanta a Apartment ɗin Hajiya Babba dan ita ce kawai ke yi mata yanda take so. Anan ma kullum sai sun yi faɗa da Atta, Duk dare Abba zai shigo ya ganta, Da safe ita kuma taje, Duk yanda take son magana da Abdusammad basa yi, dan iyaka kiran da zata yi masa ba zai ɗaga ba. Tana ji wasu lokutan suna waya da Hajiya Babba, Sai dai ta yi kasaƙe tana saurara ko zai ce a bata wayar, amma har su gama wayar ba zata ji ya ambaceta ba, Tun Hajiyar bata fahimta har sai da ta gane, Ranar wata asabar ya kira wayar suna zaune a parlour tare tana cin abinci. Bayan sun gama hira Hajiya Babba ta ce masa
“Arɗo kana sanin halin da Nana kuwa ke ciki? Yaushe zaka zo ne?”
Tun da yaji Hajiya Babba ta yi maganar to ya san Nanar na kusa, Dan haka ya yi gyaran murya ya ce
“Ba sai naji ba Hajiya, Kawai ki gaisheta, nan ba da jimawa ba zan zo. Akwai yarinyar da muka daidaita da ita ina son na zo mu yi zancen dake, bana son a ɗau lokaci mai tsayi.”
Bata san sanda ta fara dawo da abincin data zuba a bakinta ba, Hawaye suka fara ambaliya akan fuskarta. Girgiza kai Hajiya Babba ta yi dan ta san ya yi ne dan ya kunno ta, Musamman data saka wayar a handsfree. Jiki a sanyaye Nana ta tashi sum sum ta bar parlourn, Tana zuwa ta shige ɗakin Hajiya Babba ta saki wani raunataccen kuka ta fadi a wajen, Ihu ta dinga yi tana birgima, Hajiya ta kashe wayarta ta tashi ta bi bayanta, A kwance ta sameta tana kuka kamar ranta zai fita, Ta ƙarasa ta ɗagota ta ce
“Ke mene haka? Da wasa fa yake miki”
Bata yi magana sai kukanta da take yi, Hajiya Babba ta ce ta tashi su koma ƙasa, Ta miƙe tana ƙoƙarin tafiya ta dafe mararta saboda wani irin murɗawa da taji ta yi. Ƴar ƙara ta saki wanda ya sanya Hajiya Babba ta kalleta ta ce
“Mene ne?”
“Marata zata cire Hajiya, Shikenan zan mutu…”
Ta fara kuka kamar wadda ake duka, Ganin abun nata na gaske ne ya sanya Hajiya ta koma ƙasa ta ɗauki wayarta ta kira Sultan da Abba, Koda ta koma kwance ta sameta sai ihu take tana juye-juye wanda ya tabbatar da naƙuda ce ta zo mata. Abba ne ya ɗauketa ya kai har mota aka wuce da ita asibiti, Iyaka tashin hankali sun gan shi akan Nana, Dan ban da ihu babu abin da take. Duk wani makusancinta sai da ta kira sunansa, Abdusammad kuwa ta kira shi yafi sau ɗari. A haka har Allah ya hukunta ta haifi yaranta Mata guda biyu, Farare sol dasu kamar iyayensu. Gaba ɗayan su da Abdusammad suke kama, Idanun su ne kawai irin na Nana. Zo ka ga murna cikin Family ɗin Muhammad Shuwa, Kafin ka ce kwabo an cika asibitin da jama’a, Aliyu da kansa ya kira Abdusammad ya sanar da shi haihuwar bayan ya gama raina masa hankali. Ai ko awa bai ƙara ba ya fara shirye-shiryen dawowa Nigeria.
****
Kwana ɗaya da haihuwar ya zo, lokacin har an sallamesu sun dawo gida, Tana apartment ɗin Hajiya Babba har sannan. Duk yanda Amma ta so tafiya da ita kasawa ta yi dan kar aga zaƙewarta, Musamman da taga yanda Atta ke zuba rashin ta ido akan duk wanda ya yi maganar uwar ya’yan ko kuma ya’yan. Around 2:00 pm ya shigo parlourn bakinsa ɗauke da sallama, Atta na ganinsa ta saki guɗa tana murmushi ta ce
“Ga uban Ya’yan Allah ya kawo shi, Kai wannan ɗa ka ban mamaki. Ka ga yara Masha Allahu”
Shi dai Abdusammad Ban da murmushi babu abin da yake, Dan tun da aka sanar dashi haihuwar bakinsa ya zaga rufuwa, Nana ta ɗaga kai ta kalleshi, Ya daɗa wani irin girma, Kwarjini da kuma haiba. Ya ƙara zama babban mutum kana ganinsa ka san kwanciyar hankali da jin daɗi sun zauna. Ya ƙarasa kan kujera ya zauna idanunsa zube kan yaran da ke hannun Mama, Ɗaya bayan ɗaya ya gaishe su, Suka amsa sannan suka yi masa Barka. Mama da kanta ta tashi ta miƙa masa yaran duk biyun, ya amsa ya riƙe a hannunsa yana murmushi, Bai san kalar farin cikin da yake ciki ba shi kansa. Ji yake kamar ya tashi ya taka rawa da ya’yansa, Allah mai kyauta da ya ɗauke masa ɗaya sai ya bashi biyu a tare, Sun daɗe a hannunsa kafin su Aliyu suka shigo, Nan fa aka zauna ana faman hira da shafta. Duk wannan abun da ake babu bakin Nana a ciki, Hawaye taf cikin idanunta, Bata yi tunanin zai kasa yi mata magana ba, Daga ƙarshe ta tashi ta haye sama jiki a sanyaye. Hajiya Babba na lura dasu, amma bata ce komai ba. Sai da aka fara kiran sallar la’asar sannan suka tashi suka fita, Bai sake dawowa gidan ba sai bayan sallar isha’i, Hajiya Babba kawai ya iske a parlourn Kowa ya tafi gida, Ya zauna suna magana can dai ta ce
“Abdusammad mene haka? Me ke damun ka? Me yarinyar nan ta yi maka? Koma me ya haɗaku bai ci ka haƙura ba yanzu? Tun ka zo baka kalleta ba, Ballantana ka ce mata ya ta sauka ko ya jikinta, wace irin rayuwa ce wannan?”
Shiru ya yi yana sauraren Hajiya Babba, Ta dinga yi masa faɗa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Dakyar ya samu ta yi shiru bayan ta ce ya je ya ganta, Shi dai bai ce komai ya tashi ya nufi saman. Tana zaune gefen gado ta zuba uban tagumi, Yaran na kwance tsakiyar gadon suna bacci, Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo. Ta ɗaga kai ta kalle shi dan bata yi tunanin zai zo ɗin ba, Ƙarasawa ciki ya yi ya zauna gefen gadon yana kallon yaran, Can dai ya kalleta ya ce
“Ya jikin naki?”
Madadin ta bashi amsa sai kawai ta fashe da kukan dake cin ta tun ɗazu, Ya yi shiru yana saurarenta, Can dai ya tashi ya koma daf da ita ya kamo hannunta ya ce
“Ke tambayar ki nayi ya jikin ba ba cewa nayi ki isheni da kuka ba, Ke baki san kin girma ba yanzu? Baki gan ki da ya’ya ba!”
Kukanta ta ci gaba da yi, Ya rungumeta yana murmushi ya ce
“Thank you kin ji. Allah ya yi miki albarka Mamana, Kin sakani farin ciki, naji kamar na yi kuka Nana. Thank you kin ji, Allah ya albarkaci rayuwar ki data ya’yanmu, Ya sa nan gaba ki haifa min yan uku”
Ya ƙare maganar yana jan hancinta, Tura baki ta yi ta maƙale a jikinsa cikin kuka ta ce
“Uncle zafi kamar zan mutu. Bana so na sake haihuwa”
Shafa kanta ya yi ya ce“Sorry kin ji, ai next tare zamu raba zafin, yanzu ma dan kin gujeni ne.”
Bata ce komai ba sai shigewa jikinsa data sake yi, Tana jin wata irin nutsuwa ta musamman na saukar mata, Wadda take da nasaba da kewar mijin nata da ta yi. Sati ya zagayo aka yi gagarumin suna mai ban mamaki, Ko sunan su Maimoon da aka haɗe bai kai shi haɗuwa ba. Iyaka kuɗi Abdusammad ya ɓarnatar da dukiya, Komai na wajen bana masu ƙananan ƙarfi bane, Tun daga kan mai jegon da shigarta da kuma ya’yan, Kafin azo ga uban Ya’yan. Ɗaiɗaiku ne basu zo ba a dangi, haka ma abokansa da ke America duk sun zo, Har da su Zahra sai da suka zo sunan, Khadijah ma sun zo ita da Mami. Yara suka ci sunan Amma da Atta, Ake ce musu Habibti da Noor. Hotuna kuwa wanda aka manta ne kawai ba’a ɗauka ba, Duk irin rashin son mutane na Abdusammad haka ya saki jikinsa aka dinga ɗaukan hotuna, Ana ɗaukan su wani hoto shi da Nana Aliyu ya yi dariya ya ce
“Wai wannan ai kai ne Abul banin ɗin (Baban ya’ya mata)”
Murmushi kawai Abdusammad ya yi ya ce
“Faɗi ka ƙara.”
Kyaututtuka kuwa ba’a maganar su, Nana ta samu abubuwa masu tarin yawa na kayan barka, Abdusammad kuwa takardun Company ya danƙa mata a matsayin kyautarsa, aka saka ihu a wajen ana tafi. Sai dare sannan kowa ya watse ya tafi gida, Suma suka koma ciki dan huce gajiya.
****
Five years later(5).
Saukar su kenan daga jirgin, Tana rike trolley ɗinta ɗayan hannun kuma ta riƙe wata yarinya, Shima tafiya yake rike da hannun ɗaya yarinyar suka nufi inda driver ya zo ɗaukan su, Suna ƙoƙarin shiga mota taji an kira sunanta, Ba ita kaɗai ba har Abdusammad sai da ya juya dan ganin wanda ke kiran sunan matar tasa, Junaid ne a tsaye yana murmushi. Nana ta dinga kallon sa sai kuma ta ɗan saki fuskarta, Ƙarasowa gabansu ya yi suka gaisa da Abdusammad cikin fara’a, Ya durƙusa daidai tsayin Habibti dake rike da hannun Abdusammad, kyakkyawar baturiyar yarinya sai kallon rashin sani take masa, Ya miƙa mata hannu ya ce
“Hi”
Cikin siririyar muryarta irin ta yara ta ce
“Hello.”
Ya yi murmushi sannan ya miƙawa Noor ma, Kamar su ɗaya da juna, Idan har ba wani sanin su ka yi ba to zai maka wahala ka tantance su. Sai da Junaid ya gama yi masu wasa sannan ya mike tsaye yana kallon Abdusammad ya ce
“Yara sun girma Sir, Allah ya raya.”
Murmushi Abdusammad ya yi ya ce“Amin ya rabbi thank you.”
Sai a sannan ya kalli Nana ya ce
“Nana Allah ya raya”
Da Amin kawai ta amsa dan ta san Abdusammad ba son yaga tana hira da maza yake ba. Shi ma Junaid bai damu ba ya yi musu sallama ya juya ya bar wajen, Sai a sannan ta sauke idanunta ƙasa tana jin babu daɗi a ƙasan ranta wanda bata san dalilin sa ba. Mota suka shige kai tsaye kuma estate ɗin su suka nufa, Tun daga bakin estate ɗin zaka gane arziki ya ci uban na da, Domin gaba ɗaya an sauya mata fasali zuwa na wannan zamanin. Wani kallon sai ka shiga ciki, Apartment ɗin Hajiya Babba suka nufa dan anan ne ake taron kasancewar lokacin ƙaramar sallah ne ana taron family, Suna shigowa aka fara murna. Nana ta ƙarasa ta rungume Abbanta da gudu, Girgiza kai Abba ya yi ya ce
“Na ga ranar da zaki girma Nana”
Murmushi ta yi sannan ta koma ta rungume Ammarta, Amma ta ce
“Ni wallahi ba zaki ƙarashe ni ba, Ji yanda ki ka zama wata ƙatuwa kin fini” tura baki ta yi tana kallon jikinta. Da gaske ta zama babbar mace, Hamshaƙiya mai faɗa aji a gidan mijinta, Kai daka ganta kaga wadda ke hutawa. Ɗaya bayan ɗaya ta gai da mutanen parlour kafin ta ƙarasa ta faɗa jikin Hajiya Babba, Murmushi kawai Hajiya Babba ta yi ta ce
“Takwarata.”
A shagwaɓe ta ce
“Hajiyar mu mai Makkah da Madina”
Murmushi duka aka yi, Nana ta juya ta kalli Atta wadda ke tabar baki, Tashi ta yi tana zuwa ta rungumeta tana murmushi ta ce
“Attar mu, Har yanzu ba zaki mutu ba wai?”
Turata Atta ta yi tana mele baki ta ce
“Ki gani akan ki, In sha Allah ba zan mutu yanzu ba.”
Ban da dariya babu abin da jama’ar parlourn ke yi, Nana ta koma cikin sauran yan uwanta su Hajiya Maimunatu wanda aka girma, Sun wani nutsu kamar manyan gaske su basu yarda ba sun ajiye iyali dan Maimoon da Amrah Ƴaƴansu biyu, Hamida kuma nada ciki. Sai Haule wadda aka aurawa Saddiq ita ma ta ɗan ƙaramin goyo. Hajiya Babba ta dinga kallon su ɗaya bayan ɗaya can kawai ta fara murmushi mai haɗe da hawaye, Tashi Abdusammad ya yi ya koma kusa da ita ya zauna ya ce
“Hajiya lafiya?”
“Farin ciki nake Arɗo, Allah ya cika min burina, Wasiyyar mahaifin ku bata tafi a banza ba, Allah na gode maka, Allah ya yi muku albarka, Ya baku ikon ci gaba da tafiya akan wannan turbar ta zumunci, Ya ƙara muku arziki da wadatar zuci, Allah ya jiƙan magabantan mu, Ya sa sun huta. Mu kuma ya bamu ikon ci gaba da imani.”
Da Amin kowa ya amsa, Sannan aka ci gaba da hira. Da gudu Ikram ta shigo ta ƙaraso wajen Nana tana kuka ta ce
“Ammi kin ga Noor ko? Sai dukana take”
Girgiza kai Nana ta yi ta kwala wa Noor kira, Shigowa ta yi ta tsaya tana kallon su, Yanayin yanda ta yi kamar Nana na ƙarama, Nana ta haɗe rai ta ce
“Ban hana ki rashin ji ba? Ban ce ki daina dukan mutane ba?”
Tura baki yarinyar ta yi sai kawai ta saka kuka ta fadi a wajen tana birgima, Papa da ke kallon su tun ɗazu ya ce
“Allah mai iko, Dama duk abin da ka yi sai an yi maka. Yau ga Nana ta haifo mai irin halinta, To idan yar Nana taji magana a ina ta samu?”
“A wajen Babanta mana!”
Abdusammad ya amsa yana murmushi, Tuntsirewa da dariya aka yi duka Nana ta tura baki ta ce
“Ai shikenan!.”
*Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah. Anan zan ɗiga aya cikin wannan littafi mai taken NAANAH, Ina rokon Allah abin da na rubuta na daidai Allah yasa a ɗauka ayi amfani dashi, wanda kuma nayi kuskure Allah ya gyara mana baki ɗaya. I’m really really appreciate it, Na gode da ƙauna da kuma soyyayar da ku ka nunawa wannan littafi, Allah ya bar mu tare. Ku kasance dani Ameenatou I Ibrahim(Nanameera) Cikin Wani sabon littafin dan ganin abin da zan kawo muku. Tabbas ba zan baku kunya ba????????, Nanameera heart you guys❤️.*
© Nanameera.
Rate me



