⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 6: Chapter 6

Daren ranar babu wanda ya yi bacci wadatacce a cikinsu, kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa, kowacce da irin nata matsalar. Nana kuwa kwana tayi tana kuka, sai da aka fara kiran sallar asuba sannan ta tashi ta yi sallah ta shiga rokon Allah akan ya hana su haɗa auren nan da ita domin ko kaɗan bata son ta yi aure da yarinta. Washegari ya kasance asabar, dan haka babu wanda ya fita daga mazan gidan har mata, tana ta kwance har ƙarfe goma kafin kiran Junaid ya tayar da ita, kasa ɗaukan wayar ta yi dan tasan bata da wani amfani. Ta dinga kallon wayar har kiran ya katse, ganin wani sabo ya shigo ya sanya ta kashe wayar gaba ɗaya, ta sake fashewa da kuka. Amma ce ta shigo dakin tana sanye da wata doguwar riga ta lace, ta dinga kallonta kafin ta ce”da kin tashi shi ne baki fito ba?” shiru ta yi bata ce komai ba, Amma ta sake cewa” ki tashi ki fito zan aikeki” ji tayi kamar ta zunduma ihu ta cewa Amma ba zata je ba, dan ko kaɗan bata son fita daga ɗakin, amma babu dama, dan haka ta tashi ta shige toilet ɗinta ta yi wanka a gurguje ta fito. Doguwar rigar yadi ta sanya sannan ta dauki hijabi har ƙasa ta saka ta fito, zaune ta sami Abba a parlon yana karatun news, ta gaishe shi a sanyaye ba kamar yanda ta saba ba, amsawa ya yi shima kuma bai sake bi ta kanta ba ya ci gaba da abin da yake, Amma ta fito daga kitchen tana kallonta ta ce”ki je wajen Mama ki ce wai gaki” shiru Nana ta yi bata amsa ba kuma bata tafi ba, Amma ta zabga mata harara kana ta ce”baki ji ne ina magana” waje ta yi ba tare da ta amsa ba, Abba ya bita da kallo har ta fice sannan ya kalli Amma ya ce”ki bita a hankali” bata ce masa komai ba ta koma kitchen ta ci gaba da aikin da take.

Tafiya ta dinga yi a hankali tana tunane-tunanenta, har suka ƙaraso gabanta bata sani ba, sai da Maimoon ta riƙe hannunta sannan ta ɗago kanta da sauri tana kallonsu, kowanensu idanunsa a kumbure yake, basu ce mata komai ba suka ja hannunta suka ci gaba da tafiya. Har suka je garden ɗin babu wadda ta ce komai, ita dai Nana bin su take da kallo har suka shiga ciki, sai a sannan Maimoon ta saki hannunta ta ce”kin ji abin da ya faru ko?” gyada mata kai ta yi sannan ta ce”ke wa zaki aura?” shiru Maimoon ta yi bata amsa mata ba, ta juya ta kalli Hameeda ta ce”kefa Hameeda?” madadin ta amsa mata sai kawai ta fashe da kuka, ta faɗa jikinta, duk yanda Nana take jin jikinta babu kwari haka ta riƙe Hameeda itama kawai sai ta fashe da kuka. Amrah ce tayi ƙarfin halin cewa”ku daina wannan kukan kar wani ya zo ya ganmu” a fusace Nana ta ce”to a gani ɗin, wallahi ni ba zan auri wani ba idan ba Junaid ba! sai dai na mutu babu aure na rantse, amma ba zan auri wani ba idan ba shi ba!”

Kallonta suka dinga yi babu wanda ya tanka, Amrah ta dafa Hameeda dake kuka kamar ranta zai fita ta ce”da a ce za’a bar ni, da a ce zan iya dana bar miki Yaya Sultan Hameeda, wallahi da sai na barki kin aureshi, ni auri koma wane, domin nima ba shine zaɓin zuciyata ba, bashi nake so ba!” Da sauri Hameeda ta kalleta cikin kuka ta ce”na sani Amrah, na san zaki iya bar min shi, ko kaɗan ban ga laifinki ba, kawai zuciyata ce ta kasa yarda, na kasa haƙura dashi, ji nake kamar mafarki nake, kamar zan aure shi, amma na san har abada hakan ba zai faru ba, Allah ba haka ya so ba, bai ƙaddara ya zama mijina ba, Yaya Hameed shi ne zaɓin Allah kuma zaɓin iyayena” da sauri Nana ta ce”Amrah Yaya Sultan za ki aura? Ke kuma Hameeda Yaya Hamid za ki aura? To ke kuma fa Maimoon?”

“Ya Aliyu” Amrah ta bata amsa, shiru Nana ta yi lokaci ɗaya jikinta ya yi wani irin sanyi, ji tayi ta gaji da tsaiwar dan haka kawai ta zauna cikin ciyayin da ke wajen. Hawayen da bata san dalilin su bane suka dinga zuba kan fuskarta, kallonta duk suka dinga yi kafin Maimoon ta yi karfin halin cewa

“Me ki ke yiwa kuka Nana?”

“Yaya Sultan!”

Maganar ta suɓuce mata ba tare da ta yi aune ba.

Hamida ta durƙusa gabanta tana kallonta da mamaki ta ce”me ki ka ce Nana?” girgiza kai ta yi a sanyaye ta ce”nothing” daga haka ta miƙe ta bar wajen ba tare da ta sake kallonsu ba. Kai tsaye apartment ɗin su Hamida ta nufa kamar yanda Amma ta ce mata, koda ta shiga bata samu Mama a parlon ba dan haka ta nufi daƙinta kanta tsaye, bakinta ɗauke da sallama ta tura ƙofar ɗakin, Mama na zaune ƙasan gado tana karatun Alqur’ani, ta ɗago kanta tana kallonta ta ce”wa’alaiki assalam Khadijah shigo” jiki a sanyaye Nana ta ƙarasa ta zauna kusa da ita sannan ta ce”Mama ina kwana?”

“Lafiya kalau Nana”

Sunkuyar da kanta ta yi tana jan fingers ɗinta ta ce”daman Amma ta ce wai na zo” jinjina kai Mama ta yi, ta rufe Alkur’anin hannunta ta ajiye kan drawer sannan ta gyara zamanta cikin nutsuwa ta ce”eh ni na ce ki zo, daman zan yi wata magana da ke ne” sosai Nana ta ji jikinta ya yi sanyin barin yanda taga Mama na mata magana cikin kulawa. Mama ta numfasa sannan ta ce”Nana wane wanda ki ke so?” Da sauri ta ɗago kanta ta kalleta, kenan Amma ta faɗa mata abin da ya faru? ta tambayi kanta, Mama ta dinga kallonta ganin bata ce komai ba ya sa ta ce”ina jin ki faɗa min” cikin shessheƙar kuka Nana ta fara cewa”malamin mu ne a Aun, Amma kuma ta ce kar na sake kulashi” Mama ta jinjina kanta cike da gamsuwa sannan ta ce”meyasa ki ka fara son sa bayan kin san tsarin gidanku Nana? baki ganin za’a ga rashin kunyarki? duk cikin yan uwanki babu wanda ya yi miki sai a waje? Uhm. Ko kina son ki ɓata mana zumunci ne?” Da sauri ta shiga girgiza kanta tana jan numfashi ta ce”a’a wallahi Mama, bani da niyyar tarwatsa zumuncin da aka gida tun iyaye da kakanni, nima zan yi farin ciki idan har nabi wannan dokar, amma kuma…”

Ta sunkuyar da kanta kuka na kwace mata, Hannunta Mama ta kama ta riƙe cikin nata ta ɗago fuskarta tana kallonta ta ce”amma kuma me? ba zaki iya sadaukar da soyyayarki ba saboda danginki? ba zaki zo farin cikin mahaifinki ba? Na faɗa miki wani abu?; sanda aka ce za’a min aure ban yi shekarunki ba, I’m just a 17yrs old, aka aura min babansu Hamida, ban san shi ba, ban taɓa ganinsa ba sai a ranar da aka kawoni gidansa. And kamar ku muma boarding school aka kai mu tun daga Junior har candy. Saboda haka bamu saba da wasu mutane ba daga gida sai makaranta, a lokacin da muka dawo gida bayan mun kammala makaranta marigayi da kansa yake ɗaukanmu ya kai mu unguwa, duk inda ake shaƙawata sai da ya kai mu, har Umrah muka je. A sannan kuma na gamu da wanda nake so, sunansa Sagir, na so shi kamar ba zan daina ba, har cikin estate ɗin nan yake zuwa, time ɗin duk ba’a yi wadannan gine-ginen ba. Ya zo ba tare da kowa ya sani ba, kin san me aka yi? Rana ɗaya na dawo daga islamiyya aka ce an ajiye min kaya a ɗaki naje na saka, ban yi tunanin komai ba naje na shirya cikin leshin mai kyau da tsada, sai da na fito sannan Baba ya sa aka kirani ɗakinsa ya faɗa min an ɗaura min aure da babansu Hamida, ban ce komai ba a sannan duk da yanda na dinga ji a zuciyata, haka na haƙura nace to, aka ɗaukeni aka kawo ni gidan nan. Sai da dare ya yi sannan ya shigo na gansa, a lokacin bana son sa har cikin raina, amma ba zan iya ce masa ba, kuma ban isa na faɗawa wani ba, dan haka na riƙe abun a raina har zuwa sanda kyautatawarsa tasa na fara jin ƙaunarsa. Naji zan iya rayuwa dashi, rayuwa mai ɗorewa, na manta da cewa shi zaɓin iyayena ne, muka ci gaba da rayuwarmu cikin farin ciki da son juna”

Mama ta sauke nannauyan numfashi sannan ta ci gaba da faɗin”kin san me yasa na baki wannan labarin?” Nana ta girgiza kanta hawaye na sake zubowa kan kuncinta, Mama ta ce”saboda ki san ba komai ka ke so kake samu ba, a lokacin dana bijire na ce sai na auri Sagir da ban san me zai sameni ba. Ban san wace rayuwa zan yi dashi ba, amma biyayyar da nayi ya sanya Allah ya dubeni ya haɗani da wanda yake sona yake kuma tausayina. Ba dole sai kin auri wanda ki ke so ba, amma dole ne ki auri wanda yake ganin girmanki dana iyayenki, wanda ki ke da tabbacin ba zai cuceki ba a iya zamanki dashi. Kuma wannan shi ne irin mijin da muke fatan kowaccen ku ta samu, duk wadda ki ka ga an haɗata da wani, to an duba an ga wannan shi ne zai dace da rayuwarta ne, saboda haka ki zama mai biyayya Nana ba mai son zuciya ba. Ki sani wannan abun da ki ke shirin yi ba ƙaramin yaƙi bane, faɗa ne tsakanin zuciya da kuma al’ada, dan haka ba abu bane mai yiwuwa ki yi nasara a kai. Dan haka ina mai baki shawarar ki yi haƙuri da abin da aka tsara, ki ɗauka wannan shi ne Alkhairin rayuwarki”

Nana ta dinga gyaɗa kanta tana kuka, jikinta ya yi sanyi sosai kuma maganganun Mama sun shigeta, ita ma ta san ba lallai bane ta yi nasara akan abin da take so. Mama ta sanya hannunta ta share mata hawayen dake zuba sannan ta ce”ki daina kukan kin ji” sake jinjina kanta ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce”To Mama, ni daman na haƙura dashi amma dan Allah ki ce kada su aurar dani yanzu, tsoro nake ji mama, tsoro nake ji…”

Sosai ta bawa Mama tausayi dan akwai ƙalubale ba ƙarami ba a cikin auran yarinta, amma ta ɗan yi murmushi ta ce”mene ne abin tsoro Nana? Yayanki zaki aura fa, kuma kin san ba zai cuceki ba” girgiza kanta tayi ta ce”ni bana son aure yanzu Mama, ni karatu nakeson nayi, kuma ban san wa zan aura ba ma”

“Ba’a faɗa miki ba?”

Da sauri ta gyaɗa kanta, Mama ta ce”Safwan zaki aura Nana” sake fashewa ta yi da kukan da bata san dalilinsa ba, Mama ta ce”mene ne hakan?” kasa cewa komai ta yi, sai kuka take rusawa. Tashi Mama ta yi ta ce”ai shikenan” daga haka ta fice daga ɗakin, kwanciya ta yi a wajen ta ci gaba da rera kukanta kamar an kunna radiyo.

****
Ƙarfe 2:12 na rana baƙaƙen motocin suka fara shigowa cikin estate ɗin, nan da nan hayaniyar convey ta cika ko ina, a bakin apartment ɗin Hajiya Babba suka yi parking,black ride ne guda bakwai a jere, suna gama parking aka fara buɗe murfin kowace mota, sojoji ne suka dinga fitowa, kowannesu sanye da uniform da kuma bindiga. Suka jere a gaban motar da ke tsakiya wadda har sannan babu wanda ya fito, ƙofar da ke left side aka buɗe Aliyu ya fito daga ciki, sannan ya zagaya da kansa zuwa ɗaya side ɗin dai dai nan wani soja ya buɗe murfin, ƙafarsa ta dama ya fara sakowa wajen motar mai sanye da takalmin Gucci black colour sai sheƙi yake, sannan ya dafa murfin motar ya fito. Wani babban mutum ne mai cikar kamala da sura, wanda a ƙiyasi ba zai shiga 37-38yrs ba, fari ne tas kuma asalin kyakkyawa, kai tsaye ba za’a iya cewa bature bane haka kuma ba za’a ce bafulatani bane, fatarsa har wani ja take saboda tsananin fari. Yana sanye da wasu Tom ford suit black colour wanda suka tsaya a jikinsa kamar dan shi aka yi su, hannunsa maƙale da agogon Richard mille sai kyalli yake, idanunsa maƙale suke da Dita sunglasses, gashin kansa akwance har gaban kansa ya yi luf irin na larabawa, murmushi ya yi wanda ya sanya farare kuma rabbabun haƙoransa suka bayyana, kowane haƙori shi kaɗai yake ba tare da ya jingina da ɗan uwansa ba, sai kuma ƙatuwar wushirya a tsakiya. Yana da ƙasumba mai yawa kuma wadda tasha gyara sai kyalli take, iya ka haɗuwa da kuma tsafta wannan mutumin ya cikata. Kana ganinsa kaga babban mutum wanda ke ji da kansa, Aliyu ne yayi murmushi ganin yanda yake bin gidajen da kallo ya ce”Buddy muje mana” bai ce masa komai ba sai gaba da ya yi ya fara takawa cikin izza da taƙama.

Parlon Hajiya Babba a cike yake da mutanen gidan, su Papa, Abba, Daddynsu Hamida, Safwan, Hamid,Sultan, Mama, Amma, Ummi, Mami, da ma sauransu duk suna zazzaune suna jiran shigowarsa. Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga parlon, ya tsaya daga gefe yana bin kowa da kallo, kafin a hankali ya zare glasses ɗin idonsa. Manyan idanunsa suka bayyana ya dinga kallon kowa fuskarsa ɗauke da murmushi, da sauri kuma ya ƙarasa ciki yana zuwa ya shige wajen Abba yana rungumeshi.. Murmushi shi ma Abban ya yi yana shafa kansa ya ce”Yaron kirki” langwaɓar da kansa ya yi yana jin wata irin nutsuwa na saukar masa, ya daɗe jikin Abba kafin ya tashi ya ƙarasa wajen Papa, haka ya dinga bin su ɗaya bayan ɗaya yana gaishe dasu kafin ya ƙarasa wajen Hajiya Babba. Ya shige jikin mahaifiyar tasa yana lumshe idanunsa, kasa ɓoye farin cikinta ta yi ta dinga taɓa jikinsa tana murmushi. Above 5mins kafin ya tashi ya zauna gefenta yana kallon sauran ƙannen nasa, cike da girmamawa suka dinga gaishe dashi, yana amsawa cikin sakin fuska.

Abincin kala-kala aka dinga jerawa kan carpet, dan ranar a wajen zasu ci lunch tare, Abba ne ya ce”Abdusammad ina iyalin naka?” dafa kansa ya yi cikin daddadar muryarsa ya ce”suna mota Abba” Girgiza kai Abba yayi ya ce”a kira su mu gaisa ko” okay ya ce sannan ya kalli Aliyu ya ce”Buddy pls” ya gane me yake nufi dan haka ya taɓe baki ya ce”ni ɗan aikenka ne?” langwaɓar da kai ya yi ya ce”yi haƙuri kaje mana, ka ga ni baƙo ne and baƙonka Annabin ka” taɓe baki Aliyu y yi sannan ya juya ya fita. Kowa ya dinga murmushi a wajen dan daman an san halin dramar su. Tashi ya yi Hajiya ta kalleshi ta ce”ina kuma zaka je?”

“Wanka zan yi Hajiya”

Harararsa ta yi ta ce”daga zuwanka Abdu?” komawa ya yi ya zauna yana faɗin”okay Hajja mai Makka da Madinah na zauna” murmushi ta yi ta ce”da ya fi maka dai”

After 2mins Aliyu ya dawo hannunsa ɗauke da wata ƙaramar baturiyar yarinya wadda ba zata shige 5yrs ba, sai murmushi take, sai kuma wata mata wadda ba zata shige 27yrs ba a bayansa, tana sanye da Abaya black colour, wadda ta haska farar fatarta. Ƙarasowa ciki ta yi ta dinga gaida kowa cike da fara’a, suma suka amsa sannan ta nemi gefen kujera ta zauna, Abba ne ya karbi yarinyar yana mata wasa sai dariya take, ganin kamar bata jin Hausa ya sanya ya ce”Abdusammad bata jin hausa ne?” girgiza kansa ya yi ya ce”tana ji amma kaɗan, Zahra nayi mata”

“Kai baka mata kenan?”

Ɗago kansa yayi ya kalleshi sai kuma ya ce”ina ruwanka dani? Kaji da kanka da rashin aurenka ma” tuntsirewa suka yi da dariya Aliyu ya riƙe baki sai kuma ya ce”oh gori ka ke min kenan?”

“Yeh!”

Cewar Abdusammad yana kafeshi da idanu, taɓe baki ya yi ya ce”to kaci kan ka, nima dai soon zan yi auren nan”

“Better” ya ce a takaice sai kuma ya mayar da kansa wajen Abba suna ci gaba da hira.

Da sallama suka shigo parlon kowannensu sanye da hijabi, aka amsa sannan suka ƙaraso ciki, cike da nutsuwa suka gaishe shi ya amsa yana cewa”Maimoon ko?” ya ƙare maganar yana nuna Maimoon da hannunsa, gyaɗa masa kai ta yi a nutse ta ce”Eh Uncle” jin jina kansa ya yi ya ce”ashe nagane ki” sai kuma ya nuna Hamida ya ce”Amrah right?” Girgiza kanta tayi ta ce”a’a Hamida, ga Amrah nan” ta nuna Amrah da ke gefenta kai a sunkuye, dafe kansa ya yi ya ce”ya aka yi ban gane ki ba Hamida, yarinya mai ƙoƙari” murmushi kowa ya yi sannan ya kalli Amrah ya ce”ita kuma wannan daman bata magana kurma ce” dariya suka yi ban da Amrah wadda jikinta ke rawa,ya ce”yara duk sun girma, sai aure ba” Dariya aka yi suka tashi kowacce ta koma kusa da mahaifiyarta ta zauna, maids suka fara serving kowa, koda aka zuba masa nasa ƙasa ya sakko ya zauna ya tankwashe ƙafafunsa sannan ya yi bismillah ya fara ci, tasowa yarinyar ta yi daga jikin Abba ta dawo wajensa, akan cinya ya ɗorata sannan ya fara bata abincin kamar yanda ya saba. Turo ƙofar ta yi ta shigo, sai dai ganin yanda aka cika parlon ya sanya ta tsaya tana kallon kowa ɗaya bayan ɗaya,

“Nana”.

Da sauri ta kalli wajen sai kuma ta yi murmushi ta ƙarasa ta tsuguna gabanta ta ce”Aunty Zahra ina yini?” murmushi Zahra ta yi ta ce”ashe za ki gane ni, haka ki ka girma?” Murmushi Nana ta yi ta ce”eh mana, kin manta kin tura min pictures ɗinki” Zahra ta jinjina kai sai kuma ta ce”eh haka aka yi” tashi Nana ta yi ta ƙarasa gabansa ta tsuguna cikin sanyin murya ta ce”sannu da zuwa Uncle” ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya haɗe rai, sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta.

“Ina hijabin ki?”

Sai da gabanta ya faɗi jin yanda ya yi tambayar, bata ɗago kanta ba ta ce”yana gida” Abdusammad ya ce”tashi ki je ki dauko” jiki a sanyaye ta tashi ta bar parlon, Aliyu ya sauke numfashi ya ce”ga Sheikh ɗin gidan ya dawo, yara duk sai sun shiga nutsuwarsu”

Bai kalli Aliyu ba ballantana ya saka ran bashi amsa, ya ci gaba da cin abincinsa hankali kwance. Koda ya gama ci tashi ya yi bayan ya janye yarinyar da ke jikinsa yana cewa”Nur je ki wajen Ummi” gyaɗa kanta ta yi sannan ta koma jikin mahaifiyarta ta zauna, shi kuma ya kalli Hajiya ya ce”ina key ɗina Mama?” Kafin ta yi magana Safwan ya ce”an gyara komai Yaya, kuma a buɗe yake” ɗan kallonsa ya yi sai kuma ya ce”okay i see” daga haka ya nufi kofa ya fita daga parlon.

Ba’a fi 2mins ba ta dawo sanye da dogon hijabi, kalle-kalle ta dinga yi ganin bata ganshi ba ya sanya ta ce”ina uncle ɗin?” yanda ta yi maganar muryarta na rawa ya sanya mutanen wajen dariya, Zahra ta ce”yana apartment ɗinsa, ki je yanzu ya fita” toh kawai ta ce sannan ta juya ta fita da sauri. Ta fi 2mins a gaban kofar tana tunanin shiga ko ta haƙura, daga ƙarshe dai kawai ta tura kofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Babu kowa a parlon sai tv dake faman aiki, ko ina neat sai tashin ƙamshi yake, tsayawa ta yi a tsakiyar parlon kamar zata yi kuka ta shiga faɗin

“Uncle! Uncle! Uncle”

Shiru babu amsa, ta sunkuyar da kanta hawaye na biyo fuskarta, tura baki ta yi sai kuma ta juya ta fito daga parlon. Tsaye ta sami Amrah tana zazzare idanu, ta dinga kallonta sai kuma ta ce”mene ya kawo ki nan?” sunkuyar da kai Amrah ta yi tana ƙoƙarin ɓoye hawayenta ta ce”kin gan shi?” girgiza kai Nana ta yi still looking at her ta ce”na kira shi bai amsa ba, maybe wani abun ya ke, zan je sai na dawo an jima” Amrah ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta ce”daman Abba yake kiran ki” daga haka ta juya, Nana ta dinga kallonta tana mamakin yanda take abu kamar mara lafiya, sai dai kuma tunawa da ita da abin da ke gabansu ya sanya ta sauke numfashi sannan tabu bayanta..

Ƙarfe 4:15 na yamma ta fito daga ɗakin tana murza idanunta, Amma ta dinga kallonta sai kuma ta ce”sai yanzu ki ka tashi?” gyaɗa mata kai ta yi tana ƙoƙarin rufe bakinta saboda hammar da take yi, ƙarasowa parlon ta yi ta zauna gefen Amma murya a sanyaye ta ce”Amma wai Yaya Safwan zan aura?” Shiru Amma ta yi tana kallonta, Nana ta ɗora kanta gefen kafaɗarta sannan ta ci gaba da faɗin “Amma me ya sa sai shi? Ita Amrah Yaya Sultan zata aura, ita kuma Maimoon Yaya Aliyu, shi ne ni zan auri Yaya Safwan?” Har sannan Amma bata iya cewa komai ba, ba dan bata ji abin da ta ce ba, sai dan bata da abin fadar. Hawayen Nana suka dinga sauka kan kafaɗarta, wanda ya sanyata ɗagowa ta kalleta a nutse ta ce”to mene ne dan kin auri Safwan ɗin? Shi ma kamar sauran yake, yana da sauƙin kai ma fiye da na sauran” Tashi ta yi daga jikin Amma ta miƙe tana shirin barin wajen ta ce”ni bana sonsa” daga haka ta nufi ɗakinta. Da idanu kawai Amma ta bita sai kuma ta sauke numfashi, da tana da dama to da tabbas ba zata bari a aurar da Nana yanzu ba, amma sanin bata da wannan ikon ya sa ta kawar da tunanin daga cikin ranta, ta mai da Idanunta kan tv tana kalla duk da ba fahimtar abin da ake take ba. Tana nan zaune har bayan mintuna goma Nana ta sake fitowa daga dakin, wannan karon sanye take da Abaya baby pink ta yi rolling mayafin abayar akanta, Amma ta dinga kallonta ba tare da ta tambayeta inda zata ba, Nana ta ƙaraso gabanta murya a ɗan shaƙe ta ce”zan je wajen uncle” toh kawai ta iya ce mata, ta juya ta fice daga parlon.

Zaune ta hangeshi kan farar kujera a cikin flowers ɗin da ke garden, ta ɗan yi jim kafin ta ƙarasa wajen tana tafiya a hankali. Sultan na zaune yana danna waya ta ƙaraso gabansa, kujerar da ke gefen tasa ta ja ta zauna sannan ta ce”Yaya” yanda ta yi maganar a sanyaye ya sanya ya ɗago kansa, kallonta ya dinga yi ganin yanda fuskarta ta faɗa kamar ba ita ba, above 2mins kafin ya sauke numfashi ya ce”Nana ina zuwa?”

“Yaya Amrah zaka aura?”

Tambayar ta zo masa a bazata, dan haka ya gyaɗa mata kai kana ya ce”but why do you ask me?” Sunkuyar da kanta ta yi tana ƙoƙarin ɓoye hawayenta ta girgiza kanta. Sultan ya gyara zamansa yanda zai dinga kallonta sosai sannan ya ce”Nana”

“Na’am Yaya” ta amsa masa muryarta na rawa.

“Ɗago ki kalleni”

A sanyaye ta ɗago kanta ta kalleshi sai kuma ta sake sunkuyawa hawaye na zubowa kan kuncinta. Mamaki ne ya cika shi, ya dinga kallonta baki buɗe kafin ya yi ƙarfin halin cewa”kuka ki ke Nana? Mene ne ya sanya ki kuka?”

Girgiza masa kai ta yi tana goge hawayen da hannunta ta ce”babu komai” daga haka miƙe tana shirin barin wajen

“Kina sona ne Nana?”

Sultan ya yi maganar bayan ya miƙe tsayen shima. Wani irin dukan uku-uku ƙirjinta ya dinga yi, ta kasa magana haka kuma ta kasa barin wajen, takowa Sultan ya yi ya dawo gabanta yana kallonta ya ce”faɗa min kina sona ne? kin taɓa jin kina son na zama mijinki cikin estate ɗin nan? Or you daman u’re just pretending all this time!”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *