⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 7: Chapter 7

Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi, ya gyaɗa mata kai fuskarsa babu yabo babu fallasa. Ganin bata ce komai ba ya sanya ya ɗan furzar da iska daga bakinsa kana ya ce”shikenan, ai yanzu ma komai ya ƙare, zan auri wadda ba ita ce zaɓina ba, zan auri wadda ban taɓa mata kallon daya shige na ƙanwa ba, zan auri wadda ba lallai bane nayi farin ciki iya tsawon rayuwata”

Cikin shassheƙar kuka ta ce”a’a Yaya, ni ban taɓa jin sonka ba, amma naji babu daɗi da aka ce min Amrah zaka aura, ban sani ba ko hakan na nufin na soka, ko kuma kawai ina maka kallon yaya ne all the time, Yanzu ma da nake kuka ba wai ina yi bane saboda na rasa ka, a’a ina kuka ne saboda irin kaddara ɗaya ce take bibiyarmu, kamar yanda zaka auri wadda baka ra’ayinta haka nima zan auri wanda bana so, wanda ko a mafarki ban taɓa tunanin zai zama miji a gareni ba. Sai dai gara kai namiji ne, kana da damar auren wadda ka ke so koda bayan wannan auren, amma ni wannan auren tamkar ƙarshen labarina ne, irin karshe mara kyau da ba’a fatan samu!”

Daga haka ta yi gaba da sauri kamar zata faɗi ta bar wajen, Sultan ya dinga bin ta da kallo har ta ɓacewa ganinsa, ya runtse idanunsa yana jin zuciyarsa na masa wani irin suya da raɗaɗi, taya zai bar ta? Ta ya zai fara rayuwar aure da Amrah bayan Nana tana raye?

“Innalil lahi wa ina ilayhi raji’un”

Ya furta yana mai neman taimakon Allah akan masifar da take tunkarosa.

****

Yana zaune kan ɗaya daga cikin luxury sofa ɗin da suka zagaye parlon ta fito daga kitchen, kai tsaye wajensa ta ƙaraso tana tafiya kamar babu laka a jikinta ta zauna gefensa. A hankali ta ɗora kanta bisa ƙirjinsa tana lumshe idanu saboda ƙamshin turaren daya gama cika ta, sanye yake da wata farar riga armless wadda ta fito da kowace sura ta jikinsa, ƙaton tatu ɗin da ke damtsensa na hagu ya bayyana, hoton zaki aka zana a jiki, sai kuma maciji ya faso kansa, abun gwanin ban sha’awa, Ajiye wayar da ke hannunsa ya yi jin yanda take sake narkewa a jikinsa yasa ya ce”lafiya dai?” Ya ƙare maganar yana jan kumatunta, sake lumshe idanu ta yi a karo na biyu cikin wata sassanyar murya mai kashe zuciyar wanda ake yiwa ta ce”Yallaɓai nawa, Abu Noor ɗina, mijina abin alfaharina, Allah ya kula min da kai, ya kare ka sharrin maƙiya, ya raba ka da Hajiya lafiya” bai san sanda ya saki wani yalwattacen murmushi ba, ya ɗago fuskarta da hannunsa yana kallonta ya ce”Amin ya rabbi Zahra” daga haka ya ɗora bakinsa kan nata ya mata light kiss dai dai nan Nana ta turo ƙofar ta shigo, da sauri ta saki handle ɗin tana sauke idanunta ƙasa. Zahra ta tashi tana gyara zamanta a ɗan dabarbarce ta ce”un..Nana… Nana ke ce?”

“Ku yi hakuri ban san kuna nan ba na shigo”

Cewar Nana ta juya zata bar parlon,

“Kee zo nan!”

Sai da taji hantar cikinta ta kaɗa saboda yanda taji ya yi kiran nata, ta juyo a hankali ba tare da ta yarda ta kalleshi ba. Gyara zamansa ya yi kan kujerar ya kafeta da idanu, a hankali ta ƙaraso wajen ta tsuguna gabansa muryarta na rawa ta ce”ga…gani uncle”

Matsowa ya yi ya riƙe kunnenta da ke cikin mayafi fuskarsa a haɗe ya ce”baki iya sallama ba?” Girgiza kanta ta yi tana ƙoƙarin fashewa da kuka ta ce”nayi sallama wallahi, baku ji ni bane” Tashi Zahra ta yi tana kallon su ta ce”bari na ɗauko wayata” daga haka ta nufi hanyar upstairs a nutse, da idanu ya bita sai kuma ya sauke idanunsa kan Nana dake faman shessheƙar kuka ya ce”oh baki daina halin naki ba kenan ko?” shiru ta yi bata bashi amsa ba, ya saki kunnenta ya koma ya gyara zamansa.

Wayarsa ya ɗauka ya ci gaba da dannawa yayinda take tsugune har sannan kanta a ƙasa, after 5mins ya ajiye wayar ya ɗago ya ɗan kalleta, hannunsa ya miƙa mata ba tare da ya ce komai ba, ɗago kanta ta yi ta kalli hannun sai kuma ta ɗora nata akai ta miƙe tsaye, gefensa ya zaunar da ita kana ya ce”kin yimin shiru ko kuwa?”

Kamar ƙaramar yarinya haka ta dinga sauke ajiyar zuciya tana rage kukan nata, sai da ya ga tayi shiru gaba ɗaya sannan ya girgiza kansa ya ce”u will never change ko Nana?” sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta, taɓe baki ya yi ya ce”kurma ki ka zama?” da sauri ta ɗago kanta sai kuma a sanyaye ta ce”Uncle sannu da zuwa”

Kallonta kawai ya yi sai kuma ya ɗauke kansa, ta ɗan yi murmushi sannan ta sake cewa”uncle ina tsarabata?”

“Daga zuwana ɗazu? To ban zo da ita ba” tura baki ta yi ta ce”ai nasan ka siyo mana ko Uncle, ka siya min da Abaya?” ɗauke kansa yayi yana murmushi ya ce”kin bada kudin ne?” girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce”to ai ni ka san banida kuɗi” yanda tayi maganar da iya gaskiyarta ya sanya shi dariyar da bai shirya ba, ya ce”to nima ban dashi ai”

Langwaɓar da kanta ta yi tana murmushi ta ce”kaii kana da kuɗi dayawa ma kuwa”

“Nace miki?” Ya tambayeta muryarsa a sake, girgiza kanta ta yi tana murmushi ta ce”ai kowa ya sani, ko a goggle aka yi searching AM Shuwa za’a ganka”

“Ko?”

Ya sake faɗa a takaice, gyada masa kai ta yi dai dai nan Zahra ta dawo parlon hannunta riƙe da wayarta. Kallonsu ta yi tana murmushi ta ce”amma dai yau Nana a nan zaki kwana ko?” Da sauri ta girgiza kanta, Zahra ta ce”haba dai, ba zaki zauna wajen Uncle ɗin naki ku yi hira ba? Ko yanzu kin girma?” Murmushi kawai Nana ta yi bata ce komai ba, tashi ya yi ba tare da ya sake bi ta kansu ba ya haye sama, Zahra ta zauna in da ya tashi tana kallon Nana ta ce”wai Nana naga kin girma” kwaɓe fuska ta yi kamar zata yi kuka ta ce”kaii Aunty Zahra, ni ɗin!”

Jinjina kai Zahra ta yi cikin zolaya ta ce”eh mana, gashi za’a miki aure, ai wadda ta girma ita ake yiwa aure” shiru Nana ta yi bata ce komai ba, lokaci ɗaya yana yinta ya sauya, daga na farin ciki zuwa na damuwa. Zahra ta lura da hakan dan haka ta riƙe hannunta cike da damuwa ta ce”mene ne? Ko dai u’re not happy about it?” kasa ɓoye damuwarta ta yi duk yanda ta yi ƙoƙarin yin hakan, ta faɗa jikin Zahra tana fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi. Hannunta duka biyun ta sanya ta rungumeta tana jin yanda take kukan kamar ranta zai fita, shafa bayanta ta dinga yi da hannu ɗaya tana cewa “yi hakuri Nana, faɗa min mene ne?” Cikin kuka ta ce”aunty bana son sa, ni bana son auren, bana so a yimin aure yanzu, tsoro nake ji Aunty..”

Ta ƙare maganar tana sake ƙanƙameta, sosai Zahra ta ji tausayinta, ta yi shiru na wasu mintuna kafin ta yi karfin halin cewa”haba Nana mene ne abin da ki ke tsoro ɗin? Ɗan uwanki zaki aura fa, mu ma ba duk haka muka yi auren ba, sanda na auri Uncle naki ban fi 18yrs ba, yanzu kusan shekaru tara kenan, ai a haka zaki saba, da an yi auren zaki daina jin tsoron kin ji” girgiza kanta ta dinga yi tana kuka ta ce”a’a Aunty ni bana so, karatu nake so nayi, bana son auren nan, mutuwa zan yi idan aka yimin wallahi!”

“Keee!”

Suka ji muryar Abdusammad a kansu, da sauri ta saketa jikinta na rawa, Zahra ta dinga kallonsa ganin yanda ya haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba, idanunsa ƙur akan Nana wadda ta sunkuyar da kanta sai kuka take a hankali, bai ce komai ba ya durƙusa gabanta yana kallonta ya ce”why?” ɗago kanta ta yi kawai ta shige jikinsa shima tana sake sakin wani sabon kukan, kasa cewa komai ya yi yana jin yanda hawayenta duk ya jiƙa masa riga. Ganin taƙi daina kukan ya sanya ya zauna ta sake shigewa jikinta tana ci gaba da kukanta.

Sai da ta yi shiru dan kanta ta fara sauke ajiyar zuciya sannan ya ɗago kansa ya kalleta, ta rufe fuskarta a jikinsa dan haka ya sanya hannunsa na dama a hankali ya ɗago kanta, fuskarta a jiƙe da hawaye haɗi da majina sai sauke numfashi take, ya ɗan girgiza kansa kafin ya goge mata da gefen hannunsa yana cewa”ba zaki girma ba ko? komai kuka ki ke masa” tana jin sa amma bata buɗe ido ba ta ci gaba da shessheƙar kukanta a hankali. Tashi ya yi bayan ya janyeta daga jikinsa ya kalli Zahra dake zaune tun ɗazu tana kallonsu ya ce”zan je wajen Aliyu” to kawai ta ce a sanyaye. Ya mai da idanunsa kan Nana dake zaune a kujerar ya ce”taso mu tafi” bata yi masa musu ba ta tashi ta riƙe hannunta cikin nasa sannan suka bar parlon.

Har suka ƙaraso apartment ɗin Aliyu babu wanda ya ce komai a cikinsu, ya samu Aliyu zaune cikin garden dashi da Maimoon, tana ganinsa ta miƙe muryarta na ɗan rawa ta ce”barka da yamma uncle” ba tare da ya kalleta ba ya ce”Barka” ta bi ta gefensu ta bar wajen da sauri. Zama ya yi kan farar kujera yana kallon Aliyu babu yabo babu fallasa ya ce”and what’s this? mene zaka kira yarinya apartment ɗinka? kome zaka tattauna da ita ba kai ya kamata kaje gidansu ba?” Aliyu ya ɗan yi murmushi ya ce”to malam naji ba zan sake ba” harararsa Abdusammad ya yi ya ce”kana ɗaukan maganata wasa ba? kai a matsayinka da shekarunka kana ganin ya dace ka dinga keɓancewa da mace wadda ba muharramarka ba?” Dafe kansa ya yi ya ce”oh my god, naji ba zan sake ba, shikenan?” taɓe baki ya yi ya ce”idan ma ka sake mene nawa a ciki?” Daga haka ya kalli Nana da ke tsaye a wajen kamar statue ya ce”tafi gida” bata ce komai ba ta juya ta bar wajen da sauri. Aliyu ya ɗan kalleta sai kuma ya mai da idanunsa kan Abdusammad ya ce”wannan yarinyar ko kai ne ka haifeta sai haka” kwalin dabinon da ke wajen ya farka ya ɗauka guda ɗaya ya sanya bakinsa bayan ya yi bismillah sannan ya ce”to ai ni ɗin na haifeta, kuma ma da ace nayi auren wuri ai da na haifi kamarta, she’s 16 fa yanzu”

“Bata ma cika ba”

Aliyu ya yi maganar yana dariya. Shiru ya yi kamar me tunani sai kuma can ya ce”ni ko na tambayeka mana” Aliyu ya gyara zamansa ya ce”ina ji”

“Yaushe aka yi maganar auren yaran nan?”

Kallonsa ya yi sai kuma ya ce”wani abun ya faru ne?”

Haɗe rai ya yi ya ce”amsa zaka bani malam”

Murmushi Aliyu ya yi sannan ya ce”ba’a fi 3days ba, nan da 1 month za’a ɗaura auren idan Allah ya kai mu” jin jina kai Abdusammad ya yi kafin ya sake cewa”da wa da wane za’a musu auren?”

Murmushi kawai Aliyu ya yi sannan ya ce”dukansu mana, Maimuna, Hamida, Amrah sai kuma Nana”

“Nana dai?”

Gyaɗa masa kai ya yi, ya zare kwallon dabinon daga bakinsa kana ya ce”wannan yarinyar? Ba sun girmeta ba?” Aliyu ya ce”eh ita ce ƙarama a cikinsu, sa’ar Juwaira ce fa, kawai dai tana da garin jiki ne shiyasa ta shiga cikinsu, kuma ita ma ta kammala karatun secondary” taɓe baki ya yi ya ce”and saboda haka yasa za’a aurar da ita yanzun? Wane ya bada wannan shawarar?”

Aliyu ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce”masu bada shawarar aurar da ya’yan gida mana, su Uncle ne da Hajiya” tashi ya yi yana gyara zaman rigar jikinsa kafin ya ce”I’ll talk to them in sha Allah, ya kamata a ɗan bar irin wannan auren haka nan”

Tashi shima Aliyun ya yi a ɗan dame ya ce”haba Buddy, me ya sa koda yaushe ka ke Ƙoƙarin creating problems ne? haka fa ka yi akan aurenka, ka je ka auri Zahra duk da ka san ba’a irin wannan auren, ba ka yi shawara da kowa ba, ka yanke hukunci sannan yanzu ma ka ce zaka yi magana akan auren yara?”

Ɗauke kansa ya yi ba tare da ya ɗauki maganar Aliyun da muhimmanci ba ya ce”eh na auri Zahra saboda ita nakeso, and na yaba da hankalinta da kuma tarbiyyarta, saboda haka yasa na aureta duk da bata kasance ƴar cikin wannan dangin ba. Ba wai ina son tayar da hankalin dangi bane, a’a ina so ne naga sun yi abin da ba za’a tauyewa wani ko wata haƙƙi ba! yanda ban yarda da auren zumunci ba haka ba zan bari a tilastawa yara auren zumunci ba! Idan ma za’a yi to a zauna a yi zube ban kwarya kowacce ta faɗi wanda take so kafin sannan a aura mata shi, idan kuma ba haka ba sai dai a haƙura da auren wlh!”

Ya ƙare maganar a ɗan zafafe, sai kuma ya bar wajen, Da idanu kawai Aliyu ya bi shi yana tunanin maganganunsa, Allah ya kiyaye dai kada ya tada tarzoma irin ta wancan lokacin, Aliyu ya yi maganar a ransa yana sauke numfashi sai kuma ya juya shima ya bar wajen.

Kai tsaye apartment ɗinsa ya koma, sanda ya shiga zaune ya tarar da Noor jikin Zahra tana danna wayarta, tana ganinsa ta sakko daga jikinta da gudu ta zo ta riƙe ƙafafunsa cikin muryarta ta yarinta ta ce”welcome Abbiey” hannunsa ya sanya ya ɗauketa ya ɗagata sama ya yi juyi da ita, ta dinga sheƙa dariya wadda ta fito da asalin kyanta da kuma kamarta dashi, kafin daga bisani ya mai da ta kafaɗarsa yana murmushi ya ce”thank you my baby girl, yau kin yini wajen su Hajiya Babba ko?” gyaɗa masa kai ta yi tana kwanciya a kafaɗar tasa ta ce”ina can wajen Hajiya da su Aunty Juwaira, muna ta wasa” sauketa yayi yana faɗin”yarinyar ƴar gata, je ki wajen Ummi” da gudu ta tafi shi kuma ya nufi hanyar upstairs da sauri. Da idanu kawai Zahra ta bishi sai kuma ta sauke numfashi ta kalli Noor ta ce”baby zo nan ki kwanta” hawa jikinta ta yi ta kwanta kasancewar ta gaji sosai ya sanya nan da nan bacci ya ɗauketa. Zahra ta dinga shafa kanta har baccin nata ya yi nisa sannan ta ɗauketa ta haura sama da ita. A bedroom ɗinta ta kwantar da ita, ta rufa mata duvet saboda sanyin yamman daya buso, sannan ya fita daga ɗakin kai tsaye kuma nasa bedroom ɗin ta nufa.

Zaune ta sameshi kan sofa yana danna system ɗinsa, ya zare rigar jikinsa duk da sanyin da ake, faffaɗan ƙirjinsa ya bayyana mai ɗauke da zanen tato a jiki, wajen ya yi luf da kwantaccen gashi wanda ya ƙara masa kyau. Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zauna a ƙasansa ganin bai kalleta ba ya sanya ta ce”wane ya taba min kai ne?” ta ƙare maganar tana ƙoƙarin taɓa fuskarta, janye hannunta ya yi yana faɗin “babu komai” Zahra da ɗan murmusa kafin ta ce”kamar ban sanka ba? Dan Allah me aka yi maka?” Ɗago dara-daran idanunsa ya yi ya zuba mata, ta yi saurin sunkuyar da mata saboda kwarjinin da ya yi mata, hannunta ya kamo yana faɗin “har yau baki daina jin kunyata ba?” Murmushi ta dinga yi ƙasa-ƙasa, ya tashi yana riƙe hannunta ya ce”zo ki ji” miƙewa ta yi tabi bayansa kamar yanda ya umarceta.

****
Bayan sallar magriba tana zaune a parlon tana karatun wani novel mai taken “Wrong decision” wayarta dake gefenta ta fara ƙara, ta gefen ido ta kalli wayar ganin numbern ya sanya bata ɗauka ba, ta mai da Idanunta kan karatun duk da ba fahimta take ba. Amma na zaune opposite ɗin ta tana buɗe sabbin mayafan data siyo ɗazu taji wayar nata ringing, ɗan tsaki ta yi ba tare da ta kalleta ba ta ce

“ki ɗaga kiran ko kuma ki kashe wayar kin daman”

Toh kawai ta iya cewa sannan ta ɗago wayar ta saka ta a Flight mode ta mayar ta ajiye, after 5mins Amma ta tashi bayan ta gama haɗe veils ɗin ta diba ta nufi daƙinta, tana rufe ƙofar Nana ta tashi ta ɗauki wayarta da gudu ta fita daga cikin parlon. A jikin balcony ta tsaya ta leƙa compound ɗin bata ga kowa ba sannan ta kunna wayar ta danna numbern da aka yi kiran, buga ɗaya aka ɗauka daga ɗaya ɓangaren Junaid ya ce

“Why aren’t picking my calls?”

Murya can ƙasa ta ce”an hanani ne a gida”

Junaid ya ɗan yi shiru kafin ya numfasa ya ce”kin faɗa musu abin da nace miki?” Gyaɗa kai ta yi kamar yana gabanta sannan ta ce”eh”

“Me suka ce?”

Ya faɗa a takaice.

“They refused!”

Ta yi maganar babu gwarin gwuiwa.

Furzar da iska ya yi daga bakinsa har taji a cikin wayar kafin ya ce”yanzu kenan ya za’a yi?”

Girgiza kanta ta yi ta ce”nima ban sani ba, ina ga kawai mu haƙura sir”

“Mu haƙura? Nana ko dai daman baki sona ne?”

Girgiza kanta ta yi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce”A’a ina sonka mana, amma ba zan iya bijirewa gidanmu ba, koda na gwada ba zan yi nasara ba sai dai na ɓata kaina a wajen kowa, sannan Ammata ta ce kar na sake maganar idan har ta isa dani, kaga dole nayi shiru. Bana son abin da zai tada hankalin yan gidanmu, zan haƙura na auri wanda suka zaɓa min koda hakan na nufin rugujewar farin cikina!”

Junaid ta dinga kallon screen ɗin wayar baki buɗe, he can’t believe a ce ta haƙura da sauri haka, jin an ɗauki lokacin bai ce komai ba ya sanya ta kalli wayar ko kiran ya katse, gani ta yi yana kan layi dan haka ta sake maidawa kunnenta a sanyaye ta ce

“Zan yi haka ba wai dan bana sonka ba, sai dan na kare mutuncin iyayena da kuma gidanmu gaba ɗaya”

Runtse idanunsa ya yi yana jin kalamanta kamar tana ɗiga masa dalma ne a cikin zuciya, koda wasa bai yi tunanin rabuwa da ita nan kusa ba, kuma ba zai taɓa barin hakan ta kasance ba. Ya saita nutsuwarsa kafin ya ce

“Shikenan Nana naji, amma ina son na ganki idan har babu damuwa”

Muryarta a ƙarye ta ce”again kuma sir?”

Gyaɗa kansa ya yi sannan ya ce”eh Nana, ina son magana da ke, koda hakan na nufin magana ta ƙarshe tsakaninmu, ki min wannan alfarmar Nana!”

Lumshe idanunta ta yi hawaye na zirarowa kan kuncinta, ta sauke ajiyar zuciya tana jin ba zata iya rejecting ɗinsa ba ta ce

“Shikenan sir, I’ll, a gidan Aunty Ramlah?”

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce”eh ko anan ɗin ma, zan faɗa miki sanda nakeson mu haɗun sai ki zo”

Ta numfasa sannan ta ce”okay sir”

“Thank you Nana”

Ta gyaɗa masa kai sannan ta kashe wayar, kifa kanta tayi jikin ƙarfe hawaye na zubowa kan fuskarta kamar an buɗe famfo, ji take kamar ta je ta fadawa Abbanta bata son Yaya Safwan sir Junaid take so. Amma ta san ko ta faɗa ba zai taɓa tasiri ba, sai dai ya haddasa gaba tsakaninta dashi, domin Abba na ɗaya daga cikin wanda suka riƙi wannan al’adar kamar addini. Ta jima a wajen kafin ta ɗago kanta jiki babu kwari ta koma gida, zaune ta sami Amma a parlon tana cin abinci, ta dinga kallonta sai kuma ta ce”ina ki ka je?”

Sai da taji zuciyarta ta buga, ta ɗan haɗa kalmomin bakinta da kyar ta ce”da….daman naje waje ne zan yi waya, kuma nan babu network”

“Dawa ki ke wayar?”

Amma ta yi tambayar tana kai spoon ɗin shinkafar bakinta, rasa abin cewa ta yi dan bata yi tsammanin zata mata tambayar ba, jin bata ce komai ba ya sanya Amma ta ce”baki ji me nace ba ne?”

“eh?”

Nana ta yi maganar tana kallonta, harararta ta yi kafin ta ce”kina tunanin banza da wofi baki ji me nace ba right?” ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, tsaki Amma ta yi ta ce”je ki ɗebi abinci ki ci my friend, and kada ki daina tunani ki bari hawan jini ya kamaki” sauke ɓoyyayiyar ajiyar zuciya ta yi sannan ta nufi kitchen ɗin da sauri tana godewa Allah a ranta.

****
Ummi ta dinga kallonsa ganin yanda yake maganar da zallar gaskiyarsa yasa ta ce”Sultan! Sultan! Sultan!” ɗago jajayen idanunsa ya yi ya kalleta murya a ciki ya ce”na’am Ummi”

“Sau nawa na kira ka?”

Kallonta ya yi sai kuma ya ɗauke kansa yana huci, kwafa ta yi sannan ta ce”kar ka jawo min magana, kar ka jawon abin da zai dameni, ni ban aikeka ba, mahaifinka shi ne babba a wajen zartar da wannan hukuncin, saboda haka dole ka yarda dashi. Kar ka je ka yi abin da zai zo ya ɓata zumunci”

Tashi tsaye ya yi yana kallonta muryarsa a dake ya ce”nifa ba ɗauko miki magana zan yi ba Ummi, ni babu abin da zan yi, kawai zan fadi gaskiyata ne, ni ba za’a min auran dole ba wallahi! Kamar yanda Yaya Abdusammad ya dage akan ba zai ba kuma a ka bar shi haka nima ba zan yarda ba wallahi, saboda wannan ba adalci bane, shi an bar shi ya auro wadda yake so sannan dan an zo kan mu a ce za’a ci gaba da auren zumunci, wallahi ba zamu yarda…”

Marin da Ummi ta sauke masa shi ne ya hana shi ƙarasa faɗar abin da ke bakinsa, ya dinga kallonta hannunsa dafe da kuncinsa, cikin tsananin ɓacin rai take kallonsa tana nuna shi da yatsa ta ce

“Wallahi idan na sake jin makamanciyar wannan maganar a bakinka sai na saɓa maka fiye da tunaninka! Dole ne ka yi biyayya ga manyanka! Da kai da Abdusammad ba abu ɗaya bane! Kuma ba zaku taɓa zama ɗaya ba, dan haka kai baka isa ka ce zaka ɓata abin da aka gida shekara da shekaru ba! Idan kuma har ka ce zaka yi hakan to sai dai ka nemi wata uwar ba dai ni ba!”

Kallonta ya dinga yi ba tare da kiftawa ba, Ummi ta yi tsaki sannan ta juyar rai ɓace ta bar wajen, sauke idanunsa ƙasa ya yi yana ƙoƙarin mai da hawayensa, dakyar ya ja ƙafarsa ya bar wajen jiki a sanyaye. Abba ya dinga kallonsa yana jin jina kai har ya kai ƙarshen maganar sannan ya sauke numfashi ya ce”yanzu me ka ke nufi Abdusammad?” gyara zamansa ya yi kana ya ce”yauwa Abba, what i mean is kada a tilastawa yaran nan, a bari su zaɓi wanda suke ganin zasu iya rayuwa dashi. Saboda aure ba fa ƙaramar magana ba ce, rayuwa ce wadda ake tunanin a yi ta har abada, so idan har za’a ɗorasa a bisa son zuciya ina ganin za’a samu matsala ne babba ba ƙarama ba” Girgiza kai Abba ya yi yana ƙoƙarin tashi daga kan sofar ya ce”kana so ka ce a bar magana auren nan? Kada a musu aure ko me ka ke nufi?” da sauri ya ƙaraso gabansa ya ce”a’a Abba ba wai haka nake nufi ba, ina son dai a tambayi kowacce wanda take so a cikinsu, haka suma mazan a tambayesu”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *