Chapter 9: Chapter 9
Daga haka ya juya ya fice daga ɗakin rai ɓace. Amma ta tsaya a wajen tana kallonta ganin yanda take kuka, duk ta fice hayyacinta dan ba ƙaramin duka ya yi mata ba, ta sauke numfashi sai kuma ta juya ta bar ɗakin..
Tsaye ta same shi a ɗakinsa ya dafa study table, ta ƙarasa ta tsaya daga bayansa tana kallonsa a sanyaye ta ce”amma yallaɓai dukan nan bai yi yawa ba? She’s too small fa, beside ma kasan ba lafiya ne da ita cikakke ba!”
Kamar ba zai magana ba sai kuma ya juyo yana kallonta da idanunsa wanda suka yi jajur ya ce”kenan na barta ta dinga dauko mana magana? kin san wannan faɗace- faɗacen nata shi ne dalilin daya sanya na kai ta boarding school ba, to akan me zan bari ta dawo ta ɗora daga inda ta tsaya. Amrah fa mara! Sa’arta ce?”
Numfasawa Amma ta yi kafin ta ce”haka ne, amma dai bai kamata ka mata irin wannan dukan ba gaskiya, nayi shiru ne kawai saboda a gabanta ne, da ba zan barka ba wallahi, ka dinga tunawa da ita kaɗai muke da, duk abin da ya sameta mu ne a ciki!”
Ta ƙare maganar jiki a sanyaye, Abba kallonta kawai ya dinga yi sai kuma ya juya ya shige toilet ba tare da ya ce komai ba, itama bata damu da rashin maganar tasa ba ta juya ta fice daga ɗakin..
Bayan sallar isha’i Amma ta buɗe ɗakin ta shigo, tana kwance akan gadonta ta rufa da lallausan duvet, ta ƙaraso gabanta ta ajiye tray ɗin kan drawer sannan ta dafata a sanyaye ta ce”Nanata” shiru ta yi mata duk da taji abin da ta ce, Amma ta sake cewa”tashi kin ji, tashi” juyawa ta yi ta mai da kanta ɗaya side ɗin, Amma ta ɗan yi murmushi sannan ta yaye duvet ɗin ta leƙa fuskarta ta ce”taso mana yar autar Ammarta” sake dunƙule jikinta ta yi hawaye na sintiri kan kyakkyawar fuskarta. Amma ta janyo hannunta tana faɗin “taso mana” dakyar ta tashi zaune har sannan idanunta a rufe suke fuskarta ta yi jajur jikinta duk alamun jini ya kwanta, Amma ta dinga kallonta tana jin wani irin ɗaci a ranta, koda wasa bata san ganin abin da zai taɓa lafiyar tilon ƴar tata, shiyasa bata taɓa gwada dukanta komai zata yi sai dai ta mata faɗa. Ganin yanda take numfashi da kyar ya sanya ta ce”sannu, zo ki sha tea” girgiza kanta ta yi ba tare da ta ce komai ba, ta koma ta kwanta. Tashi Amma ta yi ta fito daga parlon, Abba na zaune da Abdusammad suna magana ta ƙaraso wajen, gaisawa suka yi dashi kafin ta maida idanunta kan Abba ta ce”Daman cewa nayi ko zaka je kaga jikin yarinyar, naji zazzaɓi sosai a jikinta”
Da sauri Abba ya ce”subhanallahi” daga haka ya miƙe, tashi shima Abdusammad ɗin ya yi yana faɗin “lafiya dai Abba?”
“Nana ce bata jin daɗi” ya yi maganar da damuwa akan fuskarsa. Girgiza kai Abdusammad ya yi ya ce”subhanallahi tana ina?” Daƙinta Abba ya nuna ya yi gaba sannan ya bi bayansa, Amma ta dinga kallonsu kafin ta bi bayansu itama. Ƙarasawa jikin gadon ya yi ya durƙusa ya taɓa jikinta kafin ya ce”Kee Nana!” da kyar ta buɗe idanunta dan da gaske zazzaɓi ne sosai ya rufeta, ya riƙe hannunta ta tashi zaune da kyar. Kallon jikinta ya dinga yi dan vest ce a jikinta, ya daga idanunsa ya kalli Abba da mamaki ya ce”wane ya daketa Abba?”
Murya a sanyaye Abba ya ce”ni ne” Abdusammad ya dinga kallonsa kafin ya ce”but why? me yasa zaka daketa Abba? she’s too young fa” girgiza kai Abba ya yi ya ce”raina ne ya ɓaci Abdusammad, na kasa danne fushina”
“Kome ta maka bai kamata ka daketa ba Abba, duka baya gyara, yanzu kaga ya taɓa lafiyarta”
Shiru shi dai Abba ya yi dan bashi da abin cewa tun da ya san ya yi laifin. Abdusammad ya kalleta a nutse ya ce”sannu, zaki iya tafiya?” kamar jira take ta shiga yarfe hannu tana girgiza kanta, ya durƙusa daidai tsayinta ya ce”oyaa hau muje” bata yi musu ba ta hau faffaɗan bayan nasa, ta zura hannayenta wuyansa ta rike shi sosai. Tashi ya yi yana riƙe da ita a bayansa ya ce”da safe na dawo da ita” okay Abba ya ce sannan ya fita daga ɗakin, Kamar jira Nana take ta sake narkewa a bayansa tana sauke numfashi a hankali.
****
Junaid ya sauke wayar yana yin tsaki, saurayin dake zaune gefensa ya ce”what?” rai ɓace ya ce”bata ɗaga ba, wallahi ji nake kamar naje na ɗauketa daga wancan kurkukun gidan nasu, yarinya bata isa ta sake ba!” Taɓe baki Al-ameen ya yi ya ce”kai ma wallahi kana bada maza, sai ka ce ita kaɗai ce yarinya mace, ga yan mata nan sai wanda ka zaɓa, kai da ka yi zaman Lebanon ma har a faɗa maka ganin mata zafafa” Harararsa Junaid ya yi ya ce”ita fa ba irin waɗancan matan ba ce, wannan so nake na aureta, amma danginta sun ƙi yarda, su a dole sai dai ta auri ɗan uwanta” wani murmushin mugunta Al-ameen ya yi ya ce”then baka san yanda zaka sameta ba?” kamar ƙaramin yaro Junaid ya gyaɗa masa kai, ya ɗan cije baki sai kuma ya ce”bani kunnenka ka ji” babu musu ya saki steering motar ya miƙa masa kunnen, Al-ameen ya raɗa masa magana sai kuma ya ɗago yana kallonsa fuskarsa ɗauke da murmushi.
Junaid ya dinga kallonsa da mamaki, Al-ameen ya ƙifta masa idanu yana faɗin”ya ka ji shawarar tawa?” Girgiza kansa ya yi yana jingina da kujerar motar ya ce”gaskiya i can’t” haɗe rai ya yi sannan ya ce”but why?” Junaid ya ɗauke kansa yana kallon tsirarin motocin da ke titin kafin ya ce”saboda ina sonta! aurenta nake son yi” tsaki Al-ameen ya yi yana faɗin”ai sai ka yi ta fama kuwa” shi dai Junaid bai ko kalleshi ba ballantana ya bashi amsa, zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa suna can tunanin dalilin daya hana Nana ɗaga kiransa.
****
Zahra na zaune gefenta ya dawo ɗakin hannunsa riƙe da injection, Nana na ganin haka ta sake matsawa jikinta a hankali. Tsayawa ya yi ya haɗa allurar kafin ya kalleta yana faɗin”tashi na miki” kasa cewa komai ta yi ta miƙe a hankali, skirt ɗin jikinta ya janye ƙasa sannan ya yi bismillah ya kafa allurar, runtse idanunta ta yi saboda azaba ta dinga yarfe hannu, ya janye empty sringy ɗin daga bayanta ya ajiye gefen dresser. Komawa ta yi ta zauna kusa da Zahra ta ɗora kanta akan cinyata, zazzaɓi ne sosai a jikinta dan haka Zahra ta ɗora hannunta akan bayanta tana taɓata a hankali. Juyawa ya yi ya fice daga ɗakin not too long kuma ya dawo hannunsa riƙe da wayarsa, kallonsu ya yi sannan ya ce”kin ci abinci?” gyaɗa masa kai ta yi a hankali duk da bata ci abincin ba, ya ɗan yi shiru can kuma ya ce”to ki gyara kwanciyarki sai da safe” ya ƙare maganar idanunsa ƙur akanta. Da taimakon Zahra ta gyara kwanciyar sannan ta rufa mata blanket, ta dinga sauke numfashi a hankali har bacci ya dauketa, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya juya ya bar ɗakin, ita ma ta tashi ta kashe hasken ɗakin sannan ta fita. Koda ta shiga ɗakinsa bata same shi ba dan haka ta tabbatar da yana gurin Noor dan duk dare sai ya shiga ya ganta kafin ya kwanta. Gefen gado ta zauna tana danna wayarta a hankali, ba’a fi 5mins ba ya buɗe ɗakin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Amsawa ta yi sannan ta ci gaba da danna wayarta, shi ma bai bi ta kanta ba ya nufi toilet dan watsa ruwa. Gajiya ta yi da jiransa ta tashi ta fita daga ɗakin ta koma nata, bayan 30mins ta kashe wayar hannunta ta tashi ta koma ɗakin. Zaune ta same shi gefen gado yana sipping coffee a hankali, ta ƙarasa ta zauna gefensa ta yi shiru, sai da ya gama ya ajiye mug ɗin sannan ta ce”wai me ya sameta ne? Naga jikinta duk a fashe” girgiza kansa ya yi sannan ya ce”Wallahi wai Abba ne ya daketa saboda ta yi faɗa” ɗan zaro idanu ta yi sai kuma ta ce”faɗa kuma, ita dawa?” kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce”wai da Amrah suka yi ɗan rigima sai ta mareta, shi ne shi kuma ya zaneta” Zahra ta langwabar da kai ta ce”Ayyah daman Nana bata son zaman lafiya tun tana ƙarama, amma nayi mamaki ma ganin tun da mu ka zo ba’a ce ta yi faɗa da kowa ba” murmushin da bai yi niyya bane ya kuɓuce masa, ya janye kafafunsa kafin ya ce”to ai an samu lafiya ne, shi ne yanzu take neman dawowa da halin nata” Zahra ta murmusa ta ce”shima Abba da ya yi haƙuri kwana nawa ne zata yi aurenta ta bar wajensa” Abdussamad ya dinga kallonta ba tare da ya amsa maganar tata ba. Ganin bai ce komai ba ya sanya ta ce”yauwa daman inason na tambayeka”
“Uhm ina ji” ya ce yana ƙoƙarin kwanciya, sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers dinta ta ce”dan Allah gobe ina son naje gurinsu Umma idan babu damuwa” jinjina kansa ya yi ya ce”daman jira nake naji zaki ce zaki ko sai na tuna miki, Allah ya kaimu lafiya” dariya ta yi ta ce”zan ce mana, kawai dai bari nayi mu ɗan kwana biyu tukun” sake jinjina kansa ya yi yana lumshe idanu dan ba ƙaramin bacci yake ji ba, ganin haka yasa ita ma ta haura kan gadon ta yi kwanciyarta.
Washegari da sassafe ta tashi ta je ɗakin da Nana ta kwana, sai dai bata sameta a ciki ba, dan babu ma alamar an kwanta ko ina tsaf yake. Tana ƙoƙarin juyawa suka kusa karo ya ɗan yi baya yana kallonta, fitowa ta yi tana cewa”wai ka ga na duba ban ga Nana ba a ciki”
“Bata ciki kuma?” Abdussamad ya tambaya da ɗan mamaki, gyaɗa masa kai ta yi ya ce”ko ta tafi ne?”
“Kuma sai ta tafi bata faɗa mana ba?” Zahra ta yi maganar a ɗan dame, jan kumatunta ya yi ya ce”ai da ke da Nanar ban san wanda ya fi wani son rigima ba, to mene zai hanata tafiya tun da ta san hanya abin ta?” Tana ƙoƙarin maganar suka ji an turo ƙofar, kamar haɗin baki suka kalli wajen a tare, tsaye take ita da Noor suna kallonsu, Zahra ta sauke ajiyar zuciya ta ƙarasa wajen da sauri tana faɗin”Nana na ɗauka tafiya ki ka yi ai?” girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce”ina kwana Aunty?” Murmushi ta yi ta ce”lafiya kalau ya jikin?”
“Da sauki” ta ce tana yin gaba, wajensa ta ƙarasa ta ɗan durƙusa cike da ladabi ta ce”ina kwana uncle?”
“Ya jikin?” ya ce yana zama kan sofa, bin bayansa ta yi tana faɗin”da sauki ya daina min zazzaɓin, sai jikina ne kawai yake ciwo” jinjina kansa ya yi ya janyo hannunta ya zaunar da ita gefensa a nutse ya ce”Nana me ya haɗa ki faɗa da Amrah?” sunkuyar da kanta tayi ba ta ce komai ba, ya juya yana kallonta sosai ya ce”baki ji bane?” Cikin shesshekar kuka ta ce”babu komai uncle kawai zagina ta yi fa, kuma ta mareni shi ne na rama”
“Me ya sa ki ka mareta bayan ta gaba take dake? Wannan ne abin da aka koya miki raina na gaba da ke?” Girgiza kanta ta yi tana murza idanunta, ya ce”kar ki sake faɗa da kowa kin ji yarinyar kirkina” yanda ya yi maganar cike da kulawa ya sanyata gyaɗa masa kai, Zahra dake tsaye bayansu ta yi murmushi. Ƙarasowa wajen ta yi tana riƙe da Noor, ya kama hannun yarinyar ya dorata akan cinyarsa yana murmushi ya ce”my angel” wasa ta fara yi da gemunsa tana dariya, Zahra ta nufi hanyar kitchen dan ɗora musu abun breakfast. Tashi Nana ta yi tana faɗin”na tafi uncle” haɗe fuska ya yi ya ce”dawo nan” ganin yanda ya yi maganar babu alamun wasa ya sa ta koma ta zauna tana kallonsa.
“Korar ki ake anan ɗin da ki ke sauri haka?”
Ya ƙare maganar yana harararta, sunkuyar da kanta ta yi tana murmushi, ya mai da idanunsa kan Noor ya ce”kin yi azkar?” gyaɗa masa kai ta yi cikin ƙaramar muryarta ta ce”mun yi da Aunty Nana” jin jina kansa ya yi ya ce”uhm, Aunty Nana ta iya ashe?” kamar jira take ta ce”eh Abbiey ta iya sosai, har ma fa karatun Qur’an muka yi, gashi muryarta da daɗi, kamar kai” daga shi har Nana dariya suka dinga yi, Ya ja kumatunta ya ce”to ko dai ita zata koma tutor ɗin ki?” gyaɗa masa kai ta yi tana wani juya idanu kamar babba ta ce”eh Abbiey, ta iya koya karatun”
“Na kai Abbiey?”
Nana ta yi maganar tana jawo hannunta, jin jina kanta ta yi tana murmushi, ya ɗan yi murmushi kafin ya ce”iyye au ta fini? Oya sauka ki koma jikinta to” sake narkewa ta yi a jikinsa ta dunƙule hannunta na dama ta daki ƙirjinsa ta ce”a’a fa Abbiey, babu wanda ya fika even Ummina sai dai ta biyo bayanka, u’re the best Daddy in the world” rungumeta ya yi tsam a jikinsa yana murmushi ya ce”daɗina dake hankali princess” dariya ta dinga yi ƙasa-ƙasa dai dai nan Zahra ta fito daga kitchen ɗin tana kallonsu ta ce”kun bar ni ina ta faman aiki ku kuma kuna nan kuna hira ko?” Tashi Nana ta yi tana fadin”Ayyah Aunty mu je na tayaki” taɓe baki ta yi ta ce”da can baki ce zaki tayanin ba sai da na roƙa? To ki yi zamanki, nima dai an jima zan je gidan namu yan’uwan tun da abun haka ne” tuntsirewa da dariya Nana tayi tana nufar kitchen ɗin ta ce”aaa kar ki kai mu in da Allah bai kai mu ba” Zahra ta yi murmushi ta ce”ai gaskiya ce” daga haka ta sake kallonsa ta ce”yallaɓai kai ba zaka taya mu ba?” Ɗan zaro idanu ya yi sai kuma ya kwaɓe fuska kamar ƙaramin yaro ya ce”a’a dai Ummi ku je ni zan zauna da princess” ko ƙarasa maganar bai yi ba ta fara jan hannunsa tana faɗin “ai ko sai ka taya mu wallahi!” Babu yanda ya iya haka ya tashi bayan ya sauke Noor ya nufi kitchen ɗin, ta yi murmushi sannan ta sauyawa Noor tashar cartoon ta bar wajen.
Nana ta dinga kallonsa ganin ya shigo kitchen ɗin, ya ɗan haɗe girarsa babu walwala ya ce”mene ne ki ke wani kallona?” Girgiza kanta tayi tana ƙoƙarin ƙunshe dariyar da ke cinta, y yi kwafa yana saka slice cucumber a bakinsa kafin ya ce”zan yi maganinki ne yarinya” ita dai bata ce masa komai ba har Zahra ta shigo, ta ɗan kallesu sai kuma ta nufi gaban cooker tana fadin”ku ka wani tsaya min a tsaye” gyara tsaiwarsa ya yi jikin fridge sannan ya ce”to ai bamu san me zamu yi ba Hajiya” sai da ta murɗe gas ɗin sannan ta ce”ga albasa nan ka yanka min, ke kuma Nana ki ferayen dankalin nan” toh Nana ta ce sannan ta ɗauki wuka ta fara abin da ta sakata. Zahra ta juyo tana kallonsa ganin har sannan bai ko motsa ba yasa ta ce”ai ko idan baka yi aiki a gidan nan ba yau ba zaka yi breakfast ba!” Kamar zai yi kuka ya ce”wai da gaske?”
“Abbiey da gaske nake” ta ƙare maganar tana matsowa gabansa, hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta ya dinga kallonta kafin a hankali ya kai bakinsa kan nata, saurin janyeshi ta yi tana rarraba idanu, ya ɗan haɗe fuska ya ce”mene?” da idanu ta nuna masa Nana wadda take faman feraya, ya taɓe baki sai kuma ya ce”and so?” Daga haka ya sake kai bakinsa, kasa hana shi tayi tana ji ya yi kissing ɗinta a deep one. Ƙarar kissing ɗin ya sanya Nana juyowa, amma ta yi gaggawar ɗauke idanunta ta ci-gaba da abin da take, cikin rashin sa’a wuƙar ta shige mata hannu saboda yanda ta diririce tamkar ita aka wa kiss ɗin. Ta saki ƴar ƙara tana janye hannunta, da sauri Zahra ta janye jikinta daga wajen ta ƙarasa gabanta, sai dai jinin data gani ya ɗan ɗaga mata hankali, ta ce”subhanallahi Nana garin yaya?” Ƙarasowa wajen ya yi ya kama hannun wanda yake ta zubar jini sai kuma ya ce”garin gulma ya sanya ki ka yanke ko?” wata irin matsananciyar kunya ce ta rufeta, ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba. Jan hannun ya yi wajen sink ya kunna ruwan, sai dai yana wankewa wani jinin na sake zuba, dan haka ya kashe kawai ya kalli Zahra ya ce”ban tissue” cikin hanzari ta zari tissue ɗin ta miƙa masa, ya naɗeta dayawa sannan ya ɗora a wajen, ta ɗan runtse idanu saboda zafin da taji. Cikin yan sakanni tissue ta jiƙe jagab da jinin ya ɗan yi tsaki sai kuma yaja hannunta bai ce komai ba suka fita daga ɗakin. Zahra ta yi kamar ta bi su taji ya ce”Madam concentrate on what you are doing” cak ta tsaya ba dan taso ba, ta juya ta ci gaba da aikin zuciya babu daɗi.
Ɗakinsa ya shiga da ita, ta ɗan lumshe idanu saboda wani sassayan ƙamshi daya cikata, ya ƙarasa gaban dresser nashi ya dauki wani perfume na kwalba ya buɗe, ƙoƙarin janye hannunta ta fara yi ganin yana shirin fesa mata kamar za ta yi kuka ta ce”Uncle zafi fa” banza ya yi mata ya feshe wajen da turaren, tsananin azabar da taji ya sanya ta faɗa jikinsa tana sakin wani marayan kuka, ɗauke kansa ya yi yana kallon gefe bai ce mata komai ba, ya mayar da turaren ya ajiye sannan ya janyeta daga jikinsa yana faɗin “next time ki tsaya gulma kin ji” daga haka ya juya ya nufi toilet, tura baki ta yi sai kuma ta koma gefen gadon daya sha gyara ta zauna, ta yi shiru tana tunanin yanda maganar, ita kaɗai ta dinga tura baki har kusan 5mins kafin ya fito fuskarsa a jiƙe da hannunsa, da mamaki ya dinga kallonta sai kuma ya ce
“Kee!”
Yanda ya yi maganar ya sanyata firgita ta sunkuyar da kanta ƙasa, fuska a haɗe ya ce”me ki ke min akan gado? Salon ki lalata min? Tashi my friend” ɗago idanunta ta yi ta kalleshi sai kuma ta ce”ayyah uncle zama nayi na ɗan huta fa” a ɗan tsawace ya ce”baki ji me nace ba? Tashi ki fita!” Da sauri ta tashi ta fice daga ɗakin, ya bita da harara sai kuma ya yi tsaki.
****
Bayan sun kammala breakfast ta tashi ta kwashe duk kayan ta kai kitchen sannan ta kalli Zahra ta ce”Aunty na tafi”
“Ke Nana ba zaki bari sai an jima ba?”
Girgiza kanta ta yi ta ce”zan je na ɗauki wayata ne, na san an yi min magana ta WhatsApp ban gani ba” Zahra ta ce”okay amma da kin bari an jima zan je gidanmu sai mu tafi tare ki rakani, kin ga kema kya ga gari ko?” Nana ta ɗan yi shiru tana tunani
“ki bita, This is great opportunity da zaki haɗu da Junaid!”
Wani ɓangare na zuciyarta ya sanar da ita hakan, Zahra ta sake cewa”Nana fa?”
Ɗan murmushi ta yi ta ce”Tom Aunty zan je” Zahra ta ce”yauwa yar gari, to je ki yi wanka sai ki bawa Atu tama Noor ” to kawai ta ce sannan ta nufi hanyar upstairs bayan ta kira Noor ɗin. Zahra ta mai da Idanunta kan Abdusammad da ke danna wayarsa hankali kwance ta ce”Yallaɓai kai zaka kai mu?” bai kalleta ba ya girgiza kansa ya ce”a’a driver ya kai ku dai, zan fita idan na dawo sai na biya na dauko ku, mun gaisa dasu Mommy ma” Zahra ta sauke numfashi kafin ta ce”okay tom bari na tashi naje na shirya kar mu yi late, idan zamu fita sai mu biya ta wajen Amma na faɗa mata ba?”
“Tare zamu fita da Abba, zan sanar dashi” cewar Abdusammad yana tashi daga wajen, okay kawai ta ce sannan ita ma ta nufi upstairs. Ɗakin da Nana take ta fara shiga ta sameta zaune ta yi shiru, ta dinga kallonta kafin ta ce“Nana baki shirya ba?” ɗan murmushi ta yi ta ce“yanzu zan shirya” okay kawai Zahra ta ce sannan ta juya ta fita, koda ta sake dawowa bata sami Nana a wajen ba sai ƙarar ruwa da taji wanda ya tabbatar mata da tana bayi, ta ajiye mata welfolded Abayar a gefen gado sannan ta fita. Ƙarfe 11:45 na safe Nana ta fito parlon sai zuba ƙamshi take, ta shirya cikin ash colour ɗin Abayar me manya flowers a jiki, ta yi rolling mayafin abayar akanta ta yi wani irin kyau. Zahra ta dinga kallonta tana murmushi kafin ta ce“kaga shuwar asali irin wannan kyau haka?” tura baki ta yi ta ce“ayyah Aunty Zahra banso wallahi” dariya Zahra ta yi tana gyarawa Noor hular kanta ta ce“to naji” shiru ta yi can kuma ta ce“yauwa aunty Zahra ina wayarki?” kan kujera ta nuna mata tana faɗin “gata can” okay kawai Nana ta ce sannan ta ƙarasa ta ɗauka, face id ne akai dan haka ta miƙa mata ta ce“ki cire min zan yi hoto” murmushi kawai Zahra ta yi sannan ta cire mata, ta karɓa ta fice daga parlon tana murmushi. Garden ɗin gidan ta ƙarasa ta shiga dial ta saka numbern Junaid wadda ta gama haddacewa sannan ta danna kira, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga, Junaid da ke tuƙi ya ce
“Hello wake magana?”
Ajiyar zuciya Nana ta sauke jin muryarsa, ta ɗan yi shiru har sai da ya sake magana ya ce
“hellooo”
“sir ni ce”
Junaid ya gangara gefen titi yayi parking sannan ya ce
“Nana ina ta kiran ki baki ɗaga wayata why?”
Numfasawa ta yi ta ce
“bana gida ne, ina wajen uncle ɗina”
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya ce
“okay, yanzu ya ake ciki?”
Sai da ta sake leƙawa ta tabbatar da babu wanda ya tawo sannan ta ce
“zamu fita da matarsa, zan kira ka idan mun je gidan sai ka zo”
Jinjina mata kai ya yi ya ce
“okay, shikenan zan kira ki”
Girgiza kanta ta yi da sauri ta ce
“no kar ka kirani, ni zan kira ka”
Okay ya ce sannan suka yi sallama ya kashe wayar. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta goge call log ɗin ta shiga Snapchat, ko hoto biyu bata yi ba Noor ta ƙaraso wajen da gudu ta ce”Aunty Nana ki zo in ji Ummi” okay ta ce sannan ta riƙe hannunta suka bar wajen, Zahra da ke bayan motar ta kalleta ta ce“hoton ya isa haka ai Nana zo mu tafi” murmushi kawai ta yi sannan ta zagaya ɗaya side ɗin ta shiga motar tare da Noor, drivern ya ja motar suka bar compound ɗin.
Abba ya ɗan yi murmushi kafin ya ce”like how kenan tayaya ka ke tunanin haka zai yiwu?” Abdusammad ya ɗan kalli compound ɗin gidan inda bishiyu ke kaɗawa da sauri da sauri saboda iskar da ake da sauri da sauri, ya sauke numfashi sannan ya ce“Abba so nake abar maganar auren nan dan Allah, yara ne ƙanana fa” ɗan murmushi irin na manya ya yi kafin ya ce“to mene ne dan an yi aurensu yanzun? sun kammala karatun secondary, to mene ne abin da za’a jira?” Abdusammad ya girgiza kansa ya ce“a’a Abba, at least ya kamata ace ko degree sun haɗa, kaga sannan sun ƙara hankali sai a musu auren” shiru Abba ya yi bai sake magana ba, shima Abdusammad ɗin bai damu da rashin maganar ba ya ci gaba da danna wayarsa.



