⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 12: Chapter 12

Ajiyar zuciya ta sauƙe ta gagara amsawa, kiransa ne ya shigo wayarta ta ɗan tsaya tana kallon kiran kafin a hankali ta ɗaga kiran ta kai wayar kunnenta wani siririn hawaye na gangaro mata a hankali tace “hello…..”

Wani irin ajiyar zuciya Sadiq ya sauƙe daga ɗayan ɓangaren jin Muryarta “Ni’eema” ya faɗa can ƙasan maƙoshinsa, if shes not mistaken ji tayi ma kamar muryarsa na breaking, “Na’am” ta amsa wasu hawayen na sake gangaro mata da bata san dalilinsu ba, the only thing da ta sani shine she’s not ready for ko wani irin alaƙa wacce ta wuce wanda ke tsakaninsu tun farko da saɗiq.shes not ready for this, Shiru ne ya gitta tsakaninsu ba wanda yace komai for seconds kafin yayi breaking silence ɗin, a hankali yake magana “i thought idan kika ganni ull be happy, na ɗauka zaki yi farinciki, i wanted to suprise u but i ended up hurting u which was not my intention, amma dan Allah ina so ki faɗa min me na miki? Miye laifina da yasa kika ƙi saurarata all these days, Ni’eema i was going nuts, bansan ya zan miki misali ba, dont do that again pls” shiru ya ɗanyi na wasu sakanni kafin ya cigaba “banso nayi proposing haka ba Ni’eema i wanted to make it beautiful da zaki tuna har abada but bani da yadda zanyi, Ni’eema ina sonki, Na rantse miki bazan iya rayuwa babu ke ba, ya zanyi?” Ya tambaya a hankali muryarsa na karyewa, bayan hannunta ta sa ta share hawayen fuskarta, to ita me xata ce? Ce masa zatayi a matsayin aboki kawai ta ɗauke sa mafi kusanci da ita? Idan ta masa haka ta masa adalci kuwa? But still idan ta karɓi soyayyarsa ta ma kanta adalci? dan tabbass bata shirya ma all this drama yanzu ba, akwai tarin tambayoyi da take so ya amsa mata amma ta kasa buɗe bakinta ta furtasu

“kinyi shiru pls kice wani abu mana” ya katse mata shirun da tayi da muryarsa, ajiyar xuciya ta sauƙe ta kasa magana “are u crying?” Ya tambaya almost immediately, ta kasa magana sai ma wasu hawayen da suka sake gangaro mata, “Ni’eema?” Cikin ƙaramar muryarta tace “Na’am” “kuka kike yi? Kema Bakya so na koh?” da sauri ta girgiza masa kai kamar yana gabanta, “ki buɗe bakinki ki min magana pls, u dont know what ignoring me does to me wallahi Ni’eema”
Shiru ta masa taƙi magana “Ni’eema bance ki so ni dole ba, u dont have to love me back am not asking for that, amma ni ki barni in so ki pls allow me to love you, Ni’eema….” sheshsheƙar kukanta ya sa ya dakata da maganar da yake ƙoƙarin faɗa yayi shiru ya kasa cigaba kuma ya kasa bata haƙuri, sun kai few minutes a haka a hankali yace “baki yarda da ni ba koh? Look Ban kira dan na saka ki kuka ba Ni’eema, i just needed u to believe me, thats all” “i believe you, na yarda da kai sadiq, and i missed you” ta faɗa a hankali “meyasa kayi ghosting ɗina? Bana iya kiranka baka replying messages ɗinka i was afraid bayan kasan kai kaɗai nake da shi da zan faɗa ma komai nawa?”
Shiru yayi da har sai da ta duba kiran taga yana kan wayar “zan iya zuwa na ganki gobe?” Gyaɗa masa kai tayi kamar yana gabanta kafin a hankali tace “eh” bai sake cewa komai ba yayi shiru, itama shirun tayi tana kallon bedside lamp na ɗakinta dake bada dim light, “sai da safe” ta faɗa tana katse shirun nasu, “kar ki kashe kiyi baccinki i want to listen to u sleep, ɗan dariya kaɗan tayi tana gyara kwanciyarta “are u for real?” “ eh mana, kin raina irin son da nake miki koh Ni’eema, baki san yadda kika ɗaga min hankali ba these days koh? Yau da na samu kika ɗaga wayata ai am never letting go” dariya tayi amma ta gagara cewa komai cause ita wannan hirar feels awkward a wajenta ba haka suka saba magana da sadiq ɗinta ba, can ganin da gaske yake ba zai kashe wayar ba ya sata faɗin “Sai da safe kaima kayi bacci, am hanging up now” “Ni’eee…..” kashe kiran tayi tana murmushi ba tare da ta jira ya ƙarasa ba, ta lumshe idanunta, amma ta gagara bacci, ta rasa ya zatayi da buƙatar sadiq, buɗe idanunta tayi tuna yace zai zo gobe, to ina zaizo? Ai bai san address ɗin gidan Faɗeela ba kuma bai tambayeta ba, wayarta ta sake janyowa da niyyar tura masa address ɗin, har tayi typing ɗin address ɗin gidan Faɗeelar sai kuma ta goge “zan tura masa gobe idan ya sake tambaya” ta faɗa tana komawa ta kwanta ta rungume pillow ɗinta a ƙirji ta lumshe idanunta.

Washegari wajen sha biyu suna zaune suna hira da faɗeela a palour, Nasir kuma ya fita aka danna door bell, tashi tayi daga zaunen da take ta bar faɗeela dake gyara kwanciyarta akan kujera tana canza channel ta wuce bakin ƙofar ta buɗe, tana kallon Jamilu da ya danna door bell ɗin da ɗage masa gira alamar ya aka yi? Yace “ina wuni hajiya, wani ne yazo wai yace gurinki yazo amma bamu buɗe masa ƙofar ba nace ba na tambayeki ko kina tsammanin baƙo ne baki sanar ba”

Da mamaki take kallonsa “Wajena kuma?” “Eh hajiya” ɗan shiru tayi, to wa zaizo wajenta? Kallon Jamilu tayi da ke jiran umarninta tace “kace masa ya kirani a waya ko ma waye” “toh hajiya” ya faɗa yana juyawa ya koma gate, ita kuma ta koma ciki tana kallon faɗila da ke tambayarta waye? Zama tayi akan kujera tana faɗa mata yadda sukayi da Jamilu, Faɗila tayi dariya “to ko dai sabon suruki nayi ne? Ke dama ni banga alamar kina kula kowa ba” tura baki tayi dai-dai wayarta na ringing, ta zubawa wayar idanunta bata ko ƙyaftawa, sai kuma ta ɗaga kiran ta kai kunne, ɗan shiru tayi na seconds kafin tace “bashi wayar..” then , “Jamilu barshi ya shigo hes my friend” ta faɗa tana kallon faɗeela dake kallonta itama tana jiran bayani, tana kashe wayar ta dubi faɗeela tana ƙaƙalo murmushi, “friend ɗina ne fa ashe anty faɗeela tun a newyork wannan sadiq da nake faɗa miki rannan?” Faɗeela ta zaro ido “haba? Ya akayi ya san gidan? Ko ke kika bashi address, ashema kina expecting zuwansa shine kike yi kamar baki san kowa zai xo ba” faɗeela ta faɗa tana harararta, ɗan shiru tayi “um da na bashi ai ban ɗauka zai zo yau bane anty faɗeela” “to ko dai sonki yake?” Faɗeela ta katse ta tana kallonta “ah ah fa kamar yadda na faɗa miki hes just a good friend” ta faɗa tana miƙewa “be careful dai Na’ima kinji?” “In sha Allah besides sati biyu ya rage in cika 18 fa anty faɗila i’m not a kid” harararta faɗila tayi “a Newyork ɗinku ba, amma anan dai haryanzu ke yarinya ce ƙarama ma kuwa” dariya tayi ta wucewa ɗakinta faɗeela ta bita da kallo kafin ta mayar da kanta tv.

A jikin motarsa ta same shi a tsaye looking handsome kamar ko yaushe, she can’t deny the fact cewa Sadiq Namiji ne da ko Wace nace zata so a rayuwarta, he’s so handsome kuma Yana da nutsuwa Sosai Wanda shiyasa take mamakin yadda yake behaving kwanan nan, har ta ƙaraso kallonta yake yi, ba irin kallon da ya saba mata ba wanda ya sa duk ta jita uncomfortable, murmushi ta ƙaƙalo masa tana ƙarasowa inda yake ta gaishe sa ya amsa still yana kallonta, “ko zamu je ka zauna?” Ta tambaya a hankali, ganin bai amsa ba sai kallonta yake ya sa tayi gaba zuciyarta na bugawa, wai miye hakan ne? Ta faɗa a zuciyarta, ɗan dakatawa tayi ta juyo tana kallonsa, ganin ya taho ya sa ta juya ta cigaba da tafiya, garden din gidan ta kaishi, ta ja masa kujera ɗaya cikin uku dake wajen da ɗan table ya zauna, ta ɗan kalle shi “ina zuwa” daga haka ta juya ta koma cikin gida ya bita da kallo, bata jima ba ta dawo ta ajiye kyakkyawan tray ɗin hannunta kafin ta ƙarasa ta zauna akan kujera tana kallonsa, kwata kwata sai taji ta gagara magana ba kamar da ba da itace ma mai maganar a koda yaushe sai dai yayi ta saurararta saboda yadda ta sake da shi, buɗe drink ɗin yayi ya tsiyaya a cup yana cigaba da kallonta ya kai bakinsa ya kurɓa bai ce mata komai ba, tana wasa da gyalenta ta kalleshi “amma ta yaya ka san address ɗin, i dont remember telling u” ɗauke idanunsa yayi daga kanta ya ajiye cup ɗin ya mayarda bayansa ya jingina da kujerar ya cigaba da kallonta, “kuma ta yaya kasan Ina lagos? Har ka san makarantar da na ke? Pls answer me sadiq” “does it even matter?” Ya tambaya yana ɗauke kansa daga kanta ya mayar kan grass ɗin dake wajen, “it does” ta faɗa tana kallonsa, murmushi yayi kaɗan amma bai ce mata komai ba, da mamaki take kallonsa ganin yaƙi kallonta yanzu kuma, cikin more serious tone tace “ka faɗamin dan Allah” fingers ɗinsa ya saka akan table ɗin yana ɗan bubbugawa a hankali amma baice mata komai ba kuma yaƙi kallonta, “shikenan, since u dont wanna talk zan koma gida” ta faɗa tana miƙewa tsaye, ɗago idanunsa yayi ya dube ta har tazo zata wuce da sauri ya riƙo hannunta ya miƙe tsaye “Ni’eema, not just lagos ko ina kika shiga a duniya i’ll find you thats just how much i love you, duk abinda kake so ull find a way Idan ma babu way u’ll create it” ƙwace hannunta tayi ta juyo tana kallonsa, ɗurƙusawa taga yayi akan gwuiwowinsa tun kafin ma tayi magana “Ni’eema ina sonki, ba tun yau ba tun kafin jiya, idan bakya so na i wont force u, amma ina so ki bani dama in koya miki sona, ki yafe min idan na miki ba daidai ba” zuwa lokacin idanunsa sun kaɗa sun yi ja, sosai take kallonsa da mamaki ba kuma ƙaramin mamaki ba, cause he’s making issue out of nothing, ita tun farko da ta ƙi kulashi ba wai dan ya mata wani babban abu bane kawai to show him bata ji daɗin rashin nemanta da yayi ba for months, yadda ya dinga behaving ne ya dinga bata tsoro and now this?, kallonta yake yi kamar yadda take kallonsa “meyasa kake haka? Ni ai bance bana sonka ba, tambayarka kawai nake yadda kasan abubuwan da ba ni na faɗa maka ba kuma ba kada wanda zai faɗa maka bayan ni, dan Allah ka tashi”

“okay kina nufin kin amshi soyayyata and we’re officially girlfriend and boyfriend? U means there’s us now”

gyaɗa mishi kai tayi a hankali tana rufe fuskarta, ya miƙe tsaye da sauri yana dunƙule hannunsa, he wish he can hug her right now amma bazai yiwu ba, yana murmushi yana kallonta yace

“na miki alƙawari bazaki yi dana sani ba Ni’eema, bazan bari kiyi dana sani ba”
sake gyaɗa masa kai tayi tana murmushi

“to ki zo ki zauna pls kar ki tafi ki barni”

ɗan tsayawa tayi tana kallonsa ya ƙarasa ya ja mata kujeran yana kallonta, a hankali ta ƙarasa ta zauna ya koma ya zauna a nashi yana kallonta ƙuri, tun da take a rayuwarta bata taɓa jinta soo uncomfortable kamar yadda take jinta yanxu ba daurewa kawai take yi tana amsa masa maganganunsa da wasu ba ganewa ma take yi ba, har sai kusan 2 kafin ya tafi, shima da ƙyar ta lallaɓa shi ya tafi, ta wuce cikin gida tana sauƙe ajiyar zuciya.

Kwanakin da suka biyo baya bazata iya kwatanta yadda suka zo mata ba, cause sosai sadiq ya sako ta a gaba, from phone calls to messages, wani lokacin ta biye masa, wani lokacin kuma tayi ignoring, duk da ya ce mata ya koma kaduna but duk wata hanya ta zai nuna mata irin son da yake mata bi yake yi, ita kanta ta rasa gane tana son sadiq ko ah ah, harta faɗeela yanzu ta san da zaman sadiq dan babu abinda Na’ima ta ɓoye mata, faɗeela kanta ta rasa gane kan Na’imar na tana son guy ɗin ko ah ah, sai kawai ta bata shawara tayi istikhara idan alkhairinta ne Allah ya tabbatar mata da shi.

Yau a makare ta tashi, wanda ta jima rabonta da ta makara, ko alarm ɗinta da yayi ƙara bata ji ba, gashi tana da class ƙarfe tara, a gurguje ta shirya da yake ba sallah take ba ta ɗauko jakar makarantarta tana duba inda ta ajiye wayarta, a kan gadon ta ganshi ta duba charge ɗinta taga just 6 percent, cije lips ɗinta tayi a hankali tana runtse ido, ya akayi ta manta batayi plugging charge ba, saka shi tayi a cikin tote bag ɗinta, pad ɗinta da saura gadgets ɗinta da duk suke gadon ta kalla tayi tsaki ta ɗauka tayi plugging ɗinsu a charge ta juya ta fita a ɗakin, ganin bata ga faɗeela a palour ba ta ƙarasa dining a hankali ta haɗa shayi, ko rabin cup bata iya sha ba ta wuce kitchen ta ɗau box ɗin snacks ɗinta ta saka a jakarta ta fice a gidan, yusuf da yaga fitowarta ya buɗe mata mota yana murmushi

“hajiya yau fa mun makara”

“wallahi kuwa yusuf, ina kwana?”

Ta faɗa tana shiga motar ya kulle ƙofar yana amsa gaisuwarta ya zaga ya shiga mazauni driver suka bar gidan.

Bata samu first lecture ba sai second ta samu, Tunda suka fito daga lecture ɗin around 12:30 ta fara jin ƙishin ƙishin ɗin second lecture wont take place, ba su yi confirming ba sai 1, wata ƙawarta da suka fi ɗan shiri a class ɗin ta zauna kusa da ita

“kin ji wai Dr. Ajayi bazai samu zuwa ba”

kallonta kawai Na’ima take yi har ta ɗau jakarta ta fita a class ɗin kamar yadda sauran student ke fita, ta sauƙe ajiyar zuciya tana ciro wayarta dan kiran yusuf wanda dama tace masa lecture biyu zatayi ya dawo ya ɗauke ta by 4.

Wani ajiyar zuciya ta sauƙe tana kallon wayar ganin ya mutu gashi bata taho da power bank ɗinta ba, to ko dai ta tafi masallaci ta jira har 4 ɗin? Atm card ɗinta ta ciro daga jakarta ta riƙe a hannu, kawai gwara tayi withdrawing kuɗi ta wuce gida she cant wait har 4 bayan ba komai take a makarantar ba ga wayarta a kashe, tana riƙe da atm ɗin ta fito tana tafiya a hankali da tote bag ɗinta rataye a kafaɗarta, glasses ɗin idanunta ta gyara tana nufar gate bayan tayi withdrawing kuɗi wajen wani mai p.o.s, bata tashi nadamar fitowa ba sai da taga bata ga alamar mota ba a area ɗin wajen kwata kwata banda waɗanda ke wucewa, kasancewar yawanci kawo su ake yi shiyasa babu wasu masu taxi a wajen, gashi wayarta ta mutu ba halin tayi bolt ko ta kira faɗeela, dakatawa tayi da tafiya ta juya ta kalli gate ɗin school ɗin da har ta basa tazara with the hope ko zata samu mota, wata zuciyar tace mata ko ta koma cikin makaranta ta nemi ko cafe tayi plugging wayarta, ta sauƙe ajiyar zuciya why didnt even she think of this tun farko, tsayawa tayi tana kallon wajen kafin ta sake sauƙe ajiyar zuciya dan bazata iya cigaba da tsayuwa a rana ba, ta juya da niyyar komawa.

wata sleek range rover ce ta paka dai dai saitinta bayan ta wuceta ta dawo, windows ɗin duka a tinted bata ganin wanda ke cikin motar, dakawatawa tayi tana kallon motar da mamaki ta ɗan matsa baya kaɗan da tunanin ta gudu ko ta tsaya?.

Rolling down ɗin windown yayi yana kallonta, da tsananin mamaki take kallonsa, cause shine least person da tayi tunani a wajen, kallonta kawai yake yi amma ta kasa karantar fuskarsa da expression ɗinsa more especially da yake idanunsa na cikin dark glasses, sai can kuma kamar dole yace “me kike yi anan?” Ƙyafta idanunta tayi, “um… gida zan tafi” kallonta yayi daga sama har ƙasa “walking?” Ɗan kunya taji ta gyara tsayuwarta, “my phone bettery died, shiyasa bazan iya kiran yusuf ba” ɗauke kansa yayi bai ce komai ba, ya mayar kan hanya bai kuma ja motar ya bar wajen ba, ya danna wani button murfin motar yayi clicking alamun yayi unlocking motar amma baice ta shigo ba.

Kusan 2 minutes bata shiga ba ya ɗaga kanshi ya kalleta “do i have to tell u to get in?” Shiru tayi tana kallonsa kafin ta ƙaraso ta buɗe gaban motar ta shiga tana ƙarewa interior ɗin cikin motar kallo, ƙamshin cikin motar ya doketa ta ɗan gyara zamanta tana kullo ƙofar, automatically motar ta kulle kanta, bai sake ce mata komai ba ya tada motar ya soma driving ba tare da ya kalle ta ba, sai da suka yi nisa sosai kafin ta ɗan kalleshi ta gefen idanu, driving ɗinsa kawai yake yi da hannu ɗaya yayi resting bayansa a kujerar kamar bai san tana cikin motar ba

“kar ki sake fita ba waya, this is Lagos what do u think ure doing?”

Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba yana zaga uturn ɗin da ke gabansa, gyaɗa masa kai kawai tayi

“i wasnt planning to, lecture ɗin got cancelled ban san ya zanyi bane”

ta gefen idanu ya kalleta bai ce komai ba, ta zubawa hannunsa idanu tana kallon yadda yake juya steering ɗin kafin ta kalli tsadadden agogon dake kan fari tass ɗin hannun nasa, ɗauke kanta tayi ta mayar window tana kallon traffic, har suka iso gida, horn yayi Jamilu ya leƙo sai kuma ya koma da gudu ya buɗe gate ɗin, sai da yayi parking a harabar parking kafin a hankali ba tare da ta dube shi ba tace “ thank you”. “Ure welcome” ya faɗa shima a hankali, buɗe lock ɗin motar yayi, ta sa hannu ta buɗe kofar ta sauƙa, kafin ta rufe ƙofar ta jiyo muryarsa “look..” dakatawa tayi da rufe ƙofar tana kallonsa, shima ita yake kallo, “dont tell Nasir i dropped u” gyaɗa masa kai tayi “okay bye” ya faɗa yana ɗauke kansa, rufe masa motar tayi ta matsa gefe tana kallon motar though yanzu bata ganinsa, har ya tada motar ya fice a gidan kafin ta wuce cikin gida tana ji kamar sai yanzu take iya shaƙar numfashi da kyau.

Sannu a hankali karatunta ke tafiya, though accounting wasn’t a cup of cake but Ba abinda zata ce sai Alhamdulillah, Duk da between lectures ɗinta, assignment da constant waya da suke yi da Mami kusan kullum har ma da Dad, sadiq ba ƙaramin matsa mata yayi ba, bai taɓa mata tsawa, ko ya zage ta ba, but somthing about him feel suffocating, duk da ya koma kaduna amma bayi da maraba da yana Lagos.

Mu’amalarta da mutane dayawa baya so musamman course mates ɗinta maza kai harma da wasu matan, tana mamakin a inda yake sanin abubuwa da dama da take ciki, kuma ko ta tambaya baya taɓa bata straight amsa sai ma jaddada mata da yake cewa duk abinda kake so dole ka san abinda yake ciki. Many times ta so yin maganar da faɗila sai kawai ta share cause bata san me zata ce ba, tunda haryanzu faɗilar ma ta kasa gane kan soyayyar tasu.

Abu ɗaya da ta lura da shi game da sadiq shine yana da matuƙar kishi da har abin kan bata tsoro, sannan ko hoto ta tura masa sai ya tambayeta who shes smiling at a hoton in dai ba camera take kallo ba, wani lokacin sai dai ta share shi kawai dan zuwa yanzu abin ya fara damunta, sai dai irin soyayyar da yake nuna mata da yadda yake sake jaddada mata bazai iya rayuwa babu ita ba kan sa ta share duk waɗannan, haka kawai zai baro kaduna ya zo Lagos just to see her, sometimes ya faɗa mata, sometimes kuma sai dai kawai ta ganshi, ba ƙaramin sabo bane ya sake shiga tsakaninsu, dan har haɗa ta yayi da Mamarsa a waya sannan sunyi waya da sisters ɗinsa sau ɗaya suma,wanda duk bata ji alamun matsala tare da su ba, Nasir da faɗila sosai suke kula da ita, 18th birthday ɗinta was a blast, dan sosai su Faɗila suka making mata shi a memorable one, duk da ba wai sunyi throwing party bane amma she was so happy, Sadiq shima sosai yayi gwaninta just to make her happy which he did.

Ko da suka yi hutun semester Abuja ta tafi wajen Maminta wanda tun kwana biyu kafinnan tayi booking flight ɗinta, A can ta cinye hutun sati uku da aka basu wanda da ƙyar Mami ta lallaɓata akan komawa school da hutunsu ya ƙare.

Hutun da tayi a Abuja a lokacin ne suka yi first very serious fight ɗinsu da sadiq wanda ya sa ta fara doubting anya tayi dai dai na karɓar soyayyarsa kuwa? Bata san yadda yayi ya samo gidansu na Abuja ba ta dai ganshi kawai yazo, kuma Sam bai tambayeta address ba sannan bai ce mata zai zo ba, she wasnt suprised at all wanda ya gane inda take a Lagos without contacting her ba abin mamaki bane idan ya gane inda take a Abuja. Ko da yace mata Family business ya kawo sa bata ce masa komai ba duk da ta san ba gaskiya bane, ita dai ta san something about him is off amma bazata iya cewa ga abin ba, sadiq a gareta mai kulawa ne duk wani abu in dai ya shafeta baya wasa da shi sam, sannan duk abinda ta nuna bata so ya barshi kenan, yana da Nutsuwa sosai kuma bashi da yawan magana, dan yawanci idan sun haɗu sai dai yayi ta kallonta, tana rasa miye yake tunani a cikin kansa, dan sau dayawa gani take kamar ya tafi tunani ne ma sai tayi abinda zaisa ya dawo duniyar da take,yana da ibada, infact qualities ɗin sadiq suna da yawa.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved