⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 13: Chapter 13

Saura sati ɗaya ta koma Lagos Ranar tana zaune a garden ɗin gidan Maminta dake Abuja tare da Fahad dake shan fruits shima a kan kujera yana kallonta yana jin labarin da take basa na makaranta, daga inda suke tana iya hango makeken gate ɗin gidan da masu gadi dake zaune a wajen cikin uniforms, Fahad na murmushi Yana kallon yadda take magana ya lumshe idanunsa ya buɗe “i missed this u know?” Shiru tayi tana kallonsa, all the years da baki girma a gabanmu ba, sai yanzu muke sanin daɗinki Na’ima, i wish kina nan since” ɗan dariya tayi “ji yadda kake magana serious” ta faɗa tana ɗan harararsa na wasa da murmushi ɗauke a fuskarta, zuba mata idanu yayi yana kallonta kafin ya ɗan shafa kansa “faɗila ta cuce ni gaskiya” “why” ta faɗa tana kallonsa, “saboda ta ɗauke min ke mana, i wont be seeing u sai kunyi hutu dan ni ba iya zuwa Lagos zanyi ba, ko da yake at the end of the day zaki iya gani na ma a Lagos ɗin” ba tare da ta gane inda maganarsa ta dosa ba tace “its because tafi kowa sona shiyasa, kuma ina son zama da ita ai” ɗan matsowa yayi kaɗan yana kallon cikin idanunta “wa yace miki tafi kowa sonki?” Blinking idanunta tayi ta rasa me zata ce masa, dai dai nan aka buɗe gate, tunda motar ta shigo take bin motar da kallo, Sadiq? Cause daga fara Hutunta zuwa yau wannnan shine zuwansa na uku, miƙewa tsaye tayi fahaɗ da ke kallonta shima ya miƙe tsaye, sai kuma ya juya parking space yana kallon guy ɗin da ke jingine da jikin motarsa yana kallonsu, “who’s he?” Fahad ya tambaya yana kallon yadda sadiq yayi folding hannunsa a ƙirji yana kallonsu, tana gyara mayafin kanta tace “hes my friend” daga haka ta wuce shi ta tafi wajen sadiq ɗin fuskarta babu yabo babu fallasa, har ta ƙaraso kallonta yake yi, “baka ce min zaka zo b…..” “waye shi?” Ya faɗa a nitse yana kallon cikin idanunta, juyawa tayi ta kalli Fahad da shima ke tsaye a inda ta barsa har lokacin yana kallonta, “yaya na ne” “karya kike yi! wani irin yaya? U told me kece first wajen Mami” tana kallonsa itama tace “eh cousin brother ɗina ne, yayan anty faɗila da nake wajenta a Lagos” wani kallo da yake mata ya sa ta ɗan matsa baya tana riƙe da gefen gyalenta, juyawa yayi ya kalli Fahad da har lokacin yana tsaye yana kallonsu kafin kawai ya juya ya shiga motarsa, “Sadiq…” tuni har yayi wa motar key, tayi saurin matsawa daga jikin motar ya ja motar ya nufi gate, tsaye tayi a inda take tana bin gate ɗin da kallo shocked, har aka buɗe masa ya fice da motarsa kamar zai tashi sama, miye hakan ke nufi? Juyawa tayi ta kalli yaya Fahad da ke tsaye ya rungume hannunsa, ta ɗaga ƙafarta a hankali ta fara tafiya, kafin ta ƙaraso inda yake ya juya ya wuce cikin gida, dakatawa tayi tana kallonsa har ya buɗe ƙofar Main palour ya shige kafin ta sauƙe ajiyar zuciya, ta ƙarasa ta ɗauke tray ɗin cupcakes da sauransu ta nufi cikin gidan, kitchen ta wuce ta kai tray ɗin tana satan kallon Mami da Fahad ɗin da ke palourn, tana fitowa daga kitchen ɗin ta ganshi yana yi ma Mami sallama zai wuce gida, tsayawa tayi a jikin kitchen ɗin tana kallonsa har ya fita, kamar wata mara gaskiya ta ƙaraso cikin palourn Mami na kallonta tace “Lafiyarki kam?” Gyaɗa mata kai tayi ba tare da ta amsa ba ta wuce sama.

Kwana biyu sadiq yayi bai kirata ba, ko ta kirasa baya ɗauka kuma baya replying messages ɗinta, shima Yaya fahad bai kuma zuwa gidan ba kuma yaƙi ɗaukar wayarta shima, sosai taji ta damu? To wai me sadiq ke nufi, kar ta
Kula yaya Fahad ko me? Ai abune kuma da bazai yiwu ba, a kwana na uku tana zaune Mami na kwance mata dogayen kalaba dake kanta wayarta yayi ƙara, da sauri ta kalli wayar, ganin sadiq ke kiranta ta tura baki amma taƙi ɗauka, Mami ta dubi wayar sannan ta dube ta, “waye Sadiq?” Mami ta tambaya tana warware mata gashinta, “friend ɗina ne Mami tun a newyork” shiru Mami tayi “why arent u answering the phone then?” Itama shiru tayi, kafin a hankali ta soma faɗa ma Mami duk abubuwan da suka faru tun daga farko, ɗan dakatawa da abinda take yi Mami tayi, “sai aka yi yaya?” Ta tambaya jin Na’imar tayi shiru “shine da yazo rannan ya ga yaya Fahad kawai yayi zuciya ya tafi” cigaba da warware mata gashin Mami tayi, “be very careful Na’ima, kuma idan aurenki yake so yayi me yasa bazai samu iyayenki ba?” Tura baki Na’ima tayi “Ni fa ba aure zanyi yanxu ba Mami, bayan ma ko gama sch banyi ba” “haba? Ashe sai angama school ake aure, sanda na auri babanki ni na gama school ɗinne?” Nan da nan mood ɗinta ya canza ta ɓata rai bata sake cewa komai, zuwa lokacin ya kira ya kai sau 7, sannnan ga messages da yake ta shigowa, Mami ta miƙe bayan ta kama mata dogon gashin nata ta saka mata band a jiki, “gobe zamu je ki wanke kan nan a miki kitso” gyaɗa kai tayi tana kallon Mami har ta fita a ɗakin kafin ta janyo wayar, tana ɗagawa, kafin ma tayi magana ya rigata “im so sorry Ni’eema , im sorry, i’m sorry please” lumshe idanunta tayi, wai shi sadiq kam wani irin mutum ne? Jin tayi shiru yace “xan iya zuwa anjima muyi magana?” “Kana Abuja kenan har yanxu?” Ta faɗa can ƙasa ƙasa “Noo ina kaduna, but i can drive, besides ba nisa ai” “hmm” ta faɗa a hankali “i said i’m sorry fa Ni’eema” “sai kazo” ta faɗa a hankali kafin ta katse kiran ta jinginar da kanta da gado.

Yana ajiye wayar ya juya akan gadon yana janyo wayar da yayi mirrowing da nata yana cigaba da binciken da yake yi, ganin calls ɗin da ta ma Fahad wanda ko ba’a faɗa masa ba yasan so called cousin ɗinta da tace ne yasa ya runtse idanunsa yana cije lips ɗinsa. Jin an buɗe ƙofar ɗakin yasa ya juya yana kallon ƙofar da idanunsa da har sunyi ja, ganin Mama ce ya sa ya koma ya kwanta baice komai ba, ta ƙaraso gefen gadon tace “Sadiq” kallonta yayi baice komai ba, “tashi ka zauna magana nake so muyi da kai” ta faɗa tana zama a gefen gadon, miƙewa yayi a hankali ya jingina bayansa da gadon, singlet ne kaɗai a jikinsa da dogon wando, murɗaɗɗen jikinsa a bayyane wanda kana gani kasan yana workout sosai, Mama na kallonsa tace “Sadiq kana zuwa ganin likitanka kuwa?” Ɗauke kansa yayi daga kallonta “i’m fyn” hannunshi ta riƙo cikin nata “tun da ka dawo banga alamar ure fyn ba sadiq, ure begining to behave kamar wancan lokacin, bana son abinda ya faru ya sake maimaita kansa, kasan kanka sadiq why not let the girl go?” Kallonta kawai yake yi “ina sonta Mama, more than my life” Mama ta sake riƙe hannunsa “haka kace akan Mimi, Safiyya, da Humayra ma Sadiq, me yasa bazaka ji tausayi na ba? I know its not ur fault duk abinda ya faru ba laifinka bane, bance laifinka bane, amma bana son wani abu ya sake samunka sadiq, kasan yadda muka shawo kan wancan sadiq” “ita ba irin su bace Mama, babu abinda zai same ta, i promise” shiru kawai tayi tana kallonsa cause gani take kamar kawai repitition ne na abinda ta riga ta san yadda zai ƙare, “shikenan, all the best, Allah ya maka albarka, yaushe zaka fara zuwa aiki, kaga aiki yama Umar da Maryam yawa ya kamata ka koma bakin aiki” “in sha Allah” kawai ya faɗa yana murza tafin hannunsa da ta sake masa, miƙewa tayi “bari in sa Rahila ta kawo maka tea” daga haka ta fita a ɗakin, a kitchen ta samu Rahila dake aikin goge goge, “Rahilaa ki kai ma yayansu tea ɗakinsa, zan hau sama na kwanta, Rahila kar na sauƙo raina ya ɓaci na faɗa miki, dan dama kin saba sakani magana” ta faɗa tana fita a kitchen ɗin ba tare da ta jira jin me Rahilar ke faɗa ba, ajiye goge gogen tayi ta soya ƙwan ta haɗa masa shayin ta ɗaura a tray kafin ta janyo hijab ɗinta daga kan ƙofa ta saka ta nufi ɗakinsa, ko ƙwanƙwasawa bata yi ba kawai ta tura ƙofar ɗakin ta shiga da sallama, ɗago kansa yayi ya kalli ƙofar, tsayawa tayi daga bakin ƙofa riƙe da tray ɗin tana kallonsa ganin irin kallon da yake mata “ke baki da hankali ne? Ba zaki yi knocking a baki izinin shigowa ba sai ki shigowa mutum ɗaki haka, sai an shigo ciki ne ake sallama aka ce miki?” Ya faɗa yana kallonta ransa a ɓace dan dama can zuciyarsa bata bar suya ba na kiran fahad da yaga Na’ima tayi, ajiye tray ɗin tayi daga bakin ƙofa ba tare da tace masa komai ba ta juya da niyyar fita daga ɗakin da mamaki yake kallonta, ganin tana shirin barin ɗakin yace “ke zo nan” da gudu ta ƙarasa fita a ɗakin ta janyo ƙofar da ƙarfi ya sake baki yana kallon ƙofar sannan ya kalli tray ɗin da ta ajiye a ƙasa kusa da ƙofar, komawa yayi ya kwanta ya rufe idanunsa yana sake jin ɓacin rai, sai kuma ya miƙe kawai ya wuce toilet.

Ƙarfe tara na dare agogon newyork, Suhaila ce ke sakkowa daga bene da wani nylon wando da ya kamata da jacket sai wata ʼyar ƙaramar jaka a hannunta da wasu dogayen takalma, waya kare a kunnenta, ganin ta nufi ƙofa Mummy ta dube ta “hey where to?” Dakatawa tayi tana katse wayan da take yi ta juyo “haba Mummy dan Allah, this is Newyork fa, wai ace bani da freedom ɗin fita sai an tambayeni ina zanje? Besides am not a kid, nafi 18 fa, im 20, ai ko Na’ima ta kai 18 yanzu kuma baza’a dinga ce mata ga inda zata je ko bazata je ba, ni gaskiya bana son irin abinda kike min ɗinnan wallahi” daga haka ta nufi ƙofa ta buɗe ta fita, kallon ƙofar kawai Mummy keyi cause tun tafiyar Na’ima abubuwa suka dagule mata, kwata kwata Suhaila ta sake lalacewa, bata jin maganar kowa, saboda dama duk focus ɗinta akan Na’ima ne da yadda zata ɓata wa Na’imar rai, yanzu kuma da batanan ko zama a gidan bata yi, ko makaranta taƙi komawa kuma sun jima da resuming , gashi Dad ɗinma kwata kwata ya bar shiga harkar kowa a gidan, gashi nan ne dai ba ya wani walwala, sosai take nadamar saka baki da tayi Dad ya mayarda Na’ima Nigeria, dan ta tabbata yanzu tana can tana rayuwar farinciki ta barta da mashayin ubanta, duk da yanzu ba sosai ya cika sha ba ko ta bashi ma sai yace mata he’s not drinking today, hes not drinking tomorrow, wanda ita yawanci tafi son ya sha ɗin in har zata masa wata magana mai muhimmanci, zuwa yanzu ta fara tunanin considering buƙatar Dad ɗin na komawa Nigeria, dama tunda ta aure shi basu sake zuwa ba, da Mami dama suke zuwa tunda suka rabu kuma bai sake zuwa ba, amma yanzu da yake yar gwal ɗinsa tana can har ya fara maganar komawa Nigeria, wai hes tired of Newyork, a halin yanzu itama tana ganin kawai gwara su koma ɗin, ko dan Suhaila ta dawo hayyacinta, sannan duk yadda zatayi idan sun koma Nigeria zata yi Na’ima ta dawo gabansu dan sai da ita take samu tana manipulating ɗinshi yadda ya kamata, kuma dama bai kamata ta bata damar rayuwar farinciki ba, sai yanzu take ganin wautarta, ta sauƙe ajiyar zuciya tana kashe wutan palourn ta wuce sama dan kwanciya.

Ko da sadiq ya zo da yamma har palour Mami tace ta shigo dashi, hakan kuwa tayi, yana zaune a palourn ta cika masa gabansa da kayan motsa baki ta koma ɗaya kujeran ta zauna tana kallonsa, ɗago idanunsa yayi yana kallonta ya ɗage mata gira alamun what? Tayi murmushi “babu” ta faɗa tana ɗauke kanta daga kallonsa, “Um Ni’eema” kallonsa tayi “umm” “tell me the truth guy ɗinnan waye shi?” Haɗe rai tayi tana kallonsa “amma yanzu ka gama cewa ure sorry kuma meyasa kake sake ɗauko maganar da mun riga mun gama ta?” Kallonta kawai yake yi, buɗe baki yayi da niyyar Magana aka buɗe ƙofar palourn, Fahad ya tsaya daga bakin ƙofa yana kallonsu. Ɗauke kansa sadiq yayi ya mayar kan Na’ima dake kallon Fahad ɗin, sake kallon Fahad ɗin yayi da shima Na’imar yake kallo kafin ya maida kansa ya jinginar da kujera ya lumshe idanunsa, ƙarasowa ciki Fahad yayi yana ƙaƙalo murmushi ya zauna akan ɗaya daga kujerun wajen yana Murmushi
“Sannu” ya faɗa yana kallon sadiq, ɗago kansa yayi ya kallesa, da ƙyar yace “yauwa Sannu” “ina wuni yaya Fahad, ya su Yusrah?” Naima ta faɗa tana kallonsa dan shima tun ranar bai kirata ba kuma bai xo gidan ba which is so unlike him “Lafiya lau, Mami fa?” “Tana sama” Miƙewa yayi ya wuce sama duk suka bishi da kallo “so are u leaving me for this guy?ure done with me now?” Wani kallonsa take kafin ranta a ɓace tace “sadiq please, meyasa kake son maida abinda ba komai ba an issue, na faɗa maka hes my cousin brother, but har yanzu sai maimaita maganar kake yi” miƙewa yayi tsaye yana kallonta “im not here to fight with u Ni’eema amma ni na san akwai abinda ke tsakaninki da shi, cousin brother ɗinki ne yasa kuke kallon juna irin haka? Bayan gani a gabanki Ni’eema?”, juyawa ya ɗanyi ya furzar da iska kafin ya juyo, “kinsan ina sonki, Ni’eema…” sai kuma yayi shiru bai ƙarasa ba “okay kana so in faɗa maka gaskiya? Sadiq ure very insecure, ni yanzu na fara tunanin ma u dont trust me, sadiq kana bani tsoro, kace min u love me and ni da kaina nayi accepting soyayyarka, meyasa bazaka kwantar da hankalinka ka yarda dani kamar yadda na yarda da kai ba?” hawaye ya gangaro mata, “i need time to process duk abinnan da ke faruwa, am trying sadiq…” ɗaga mata hannu yayi, idanunsa sunyi jaa, “to nace bana son mu’amalarki da guy ɗinnan, u can talk to kowa a cousins ɗinki banda wannan” tana kallonsa tace “bazan iya ba, Cause….“ hannunsa na rawa ya sa ɗaya hannun ya riƙe ɗayan da ke rawa kawai ya juya ya nufi ƙofa ba tare da ya jira ta ƙarasa ba, da idanu ta bishi hawaye na gangaro mata, amma ta gagara binsa har ya fice a palourn, ta ƙarasa jikin ƙofar da ya bari a buɗe da sauri tana kallon yadda yake tafiya har ya ƙarasa motarsa, ya shiga, ya daɗe kafin ya tada motar yayi reverse ya fice a gidan, “ya Allah he should be save pls” ta faɗa tana share hawayen fuskarta, tana juyowa taga fahad a tsaye a jikin steps, bata san for how long yake wajen ba ko yanzu ya sauƙo, ƙarasowa palourn yayi yana ɗan Murmushi, “Ni’eema..” da gudu ta wuce sama tana fashewa da sabon kuka ya bita da kallo kafin ya juya shima ya fice a gidan.

Juyawa Amira tayi ta dube sa fuskarta a haɗe tana sake tura baki ganin ko kallon inda take baya yi sai ma driving ɗinsa da yake yi yana bin karatun alqur’ani dake tashi a speaker ɗin motar a hankali. Ta ɗauke kanta ta mayar window wani baƙinciki na sake turniƙe ta, ita bata san me zatayi a gidansu ba da haka kawai daga dawowansa daga so called business trip ɗinsa zai saka ta a gaba sai taje, mutanen da ba sonta suke ba, Saif ma da tace a barshi a gida da Mary da kansa ya ɗauko sa, ta juya ta kalli seat ɗin baya inda Saif ɗin ke game a ipad ɗinshi, wayarta ta ciro daga jakarta ta shiga chatting ba tare da itama ta sake shiga harkarsa ba, har suka iso gidan, ko da yayi parking ƙin sauƙa tayi, tayi zamanta a cikin motar tana latsa wayarta, sauƙa yayi daga motar ya zaga ya buɗe gidan baya yana kallon Saif har ya sauƙo kafin ya rufe ya ƙarasa ya buɗe gidan gaba yana kallonta, tura baki tayi yana kallonta fuskarsa expressionless yace

“Sauƙo Madam”

saukowa tayi ya rufe motar sanann ya ƙarasa ya riƙe hannun Saif ya nufi cikin gidan da shi, ta bi su a baya tana kallonsu, her boys, maza biyu masu matuƙar muhimmanci a rayuwarta, mazan da tafi so duk duniya, irin white shirt dake jikinsa shi yake jikin Saif, sai dai trousers ɗinsu ne kaɗai ba ɗaya ba kasancewar da kansa ya shirya Saif ɗin a ɗakinsa bayan ya sa Mary ta kawo masa shi.

Har ya tura ƙofar palourn ya shiga tana biye da shi, kujera ta samu ta zauna tana kallonshi ganin ya nufi sama, kamar ta tashi ta bishi sai kuma ta haƙura ta zauna tana sake haɗe fuska, kusan mintuna ashirin tana zaune ita kaɗai, jin takun sakkowarsu ta ɗaga kai tana kallon Ammi dake sauƙowa matakalan, ta mayar da kallonta gareshi har suka ƙaraso cikin palourn, zama Ammi tayi tana kallon Amira ganin bata gaishe ta ba yasa tace

“Ya gida Amira” sai a lokacin ta ƙaƙalo murmushi

“Ina wuni, mun same ku lafiya?” Ammi ta gyaɗa kai

“Lafiya Lau” tana mayarda kallonta ga Saif dake kwance lamo jikin babansa ya ɗaura kansa a wuyansa yana kallonta

“Come here Saif” sauka yayi ya tafi jikinta, Ahmad ya miƙe yana kallon Ammi,

“Sai na dawo Ammi” “okay ba damuwa” ta amsa masa tana kallonsa, yana nufar ƙofa yace “ina su Yasmeen?” “Na aike su” bai sake cewa komai ba ya fice a palourn, har ya isa motarsa yana ƙoƙarin buɗewa ya jiyo muryar Amira a bayansa

“Albi..” juyawa yayi yana kallonta da mamaki, ya jingina da motar yana kallon yadda take tahowa da sauri sauri, har ta ƙaraso tana kallonsa

“ina zaka tafi toh ka barni?” Kallonta kawai yake yi “Ah ah ni kam bazaka tafi ka barni ba, ai mun gaisa da Ammin kawai in ɗauko Saif mu tafi gida”
yana kallonta strictly yace

“juya ki koma cikin gida, ure not leaving gidannan sai dare!”

Wani irin kallonsa take irin wasa kake kafin without saying another word kawai ta juya ta wuce cikin gidan fuuuu kamar zata tashi sama, ya bita da kallo kafin ya juya ya shiga motarsa ya bar gidan, bai wani yi nisa ba jin ransa duk ya dagule ya ciro wayarsa a aljihunsa yayi dialing number ɗin Yasmeen, yana driving da ɗaya hannun, tana ɗagawa yace “kuna ina?” “Yaya Ammi ce ta aike mu, ina wuni yaya” bai amsa gaisuwar nata ba yace zuwa yaushe zaku dawo?” Tana kallon Rahama tace “yanzu ma driver ya ɗauko mu mun kusa gida” “in how many minutes?” Duba agogon hannunta tayi “umm maybe 5”

okay ya faɗa yana katse kiran, juya kan motar yayi ya koma gidan, yana parking a harabar suma aka buɗe musu gate, driver na parking suka fito tare suna nufo sa da murmushi a fuskarsu duka,

“ina wuni yaya”

suka sake haɗa baki wajen faɗa

“Je ki ɗauko min Saif, dont let his mum notice, make it fast”

ya faɗa yana kallon Yasmeen” juyawa tayi ta kalli ƙofar shiga gidan kafin ta juyo ta kallesa ganin kallonta yake yasa tace “toh yaya” ta juya ta nufi cikin gidan, Rahama zata bita yace

“jira ta anan”

gyaɗa masa kai tayi ta koma ta jingina da ɗaya daga motocin wajen, ba’a jima ba sai ga Yasmeen da Saif tana ɗauke da shi a kafaɗarta, ta zo ta ajiyeshi tana kallon Ahmad

“wasnt hard at all Mamarsa kamar Ammi ta kaita sama” bai kulata ba ya buɗe front seat yana kallon Saif, shiga yayi ya maƙala masa seat belt kafin ya zaga ya buɗe ƙofar motarsa, ya shiga ya rufe suna kallon motar har ya fita da ita agidan, juyawa sukayi suka nufi cikin gidan suma.

Yana hawa kan titi ya dubi Saif dake kallonsa yana kallon Titi, shafa kansa yayi yana kallonsa kafin ya mayar da hankalinsa kan tuƙin da yake yi, can yace

“Ina Saif yace in kaishi jiya?” Washe baki Saif yayi yana kallonsa da ƙoƙarin zare belt ɗin ya miƙe tsaye a kujerar, hannu ɗaya ya sa ya mayar dashi yana tuƙi da hannu ɗaya

“Anty naeeeeeeeema”

ya faɗa yana kallon baban cike da Murna, shima yana ɗan kallonsa yace

“why her Saif? Uve been disturbing my peace tunda na dawo saboda ita”

“yes because i promised her papa, and promise is a dept u told me that” kallonsa kawai yake yi kafin yayi murmushi

“sure”

“zamu je?” Ya tambaya cike da Murna, gyaɗa masa kai yayi yana juya kan motar zuwa Pan atlantic dan yasan bata koma gida ba yanzu, kuma dama bashi da niyyar zuwa gidan at all

yana parking a ƙofar dept ɗinsu ya jinginar da kansa da kujera yayi shiru just staring into space

“to muje mu ganta mana Papa,” Saif ya faɗa yana riƙe hannunsa, juyawa yayi ya kallesa

“lets wait here, she’ll come when she’s done”

komawa yayi ya zauna kamar wanda ya fahimci mai Ahmad ɗin ya faɗi, jinginar da kansa yayi da kujera yana danna wayarsa, ilai kuwa basu jima a motar ba dan basu fi 10 minutes sai gata, tana sanye da abaya sakakke mai tsadan gaske yet simple, ta yafa gyalen ta yadda ya fito da baby face ɗinta sosai a bit loose, ƙafarta cikin flat shoe, as always tote bag ɗinta na kafaɗarta sai pastel blue starnley cup ɗinta dake hannunta, she looks tired and pretty and the same time.

Kwata kwata bata lura da motarsu ba da yake ma motar is tinted, a hankali take tafiyarta iska na kaɗa beige abayar jikinnata, lost a cikin duniyarta, kamar daga sama taji

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved