Chapter 2: Chapter 2
Wayar da yake taɓawa ya dakatar ya ɗago ya kalleta, fuskarsa babu yabo babu fallasa yace
“Morning, har kin shirya?”
Sai da ta ja kujera ta zauna bayan ta ajiye jakanta a wani kujeran daban kafin ta gyaɗa masa kai tana ɗaukan cup dan haɗa ma kanta shayi, the table was then quite kowa ya maida hankali kan cin abincin da ke gabansa, Mummy ce tayi breaking silence ɗin ta hanyar ajiye cup ɗin hannunta tana kallon Na’ima tace
” Baby i heard there’s fundraiser a school ɗinku this Friday, for the senior classes, hope ure going to participate dan banji kince komai akai ba u didn’t even mention it to me nor ur dad”
Dakatawa da tauna toast ɗin da ke bakinta tayi tana kallon Mummy kafin ta ɗan kalli Dad, cup ɗinta ta ɗauka ta kurɓi shayin da Ke ciki bata ce komai ba.
Kallonta Dad Yayi kafin ya maida kallonsa ga Mummy “a fundraiser for prom tickets?”
“Yeah, yana da kyau tayi participating she’s in her final grade, kuma it’s for the seniors”
Da sauri Na’ima ta ajiye cup ɗin tana ƙirƙiro murmushi ta gyaɗa kanta
“Eh dama zanje, it’s not a big deal”
“Meyasa baki faɗa min ba tun da farko?” Ya tambaya ya na zuba mata idanunsa da suke nan sak nata.
Kafin tayi magana Mummy ta rigata
” Maybe it slipped her mind, kin manta ne koh?” Tayi tambayan tana kallonta
Da sauri ta gyaɗa Kai, ɗauke kansa yayi ya mayar kan wayarsa
” u better focus on important things like ur grade!”
“In sha Allah” ta faɗa tana sauƙe kanta ƙasa
Har suka ƙarasa breakfast ɗin ba wanda ya sake magana, Mummy ce ta fara barin table ɗin, ya ɗago ya dube ta yace
“Kina buƙatan wani abune?”
Girgiza masa kai tayi, ya miƙe shima
“Okay if u do let me know, study hard and stay out of trouble” ya faɗa yana barin table ɗin shima.
Jakarta ta ɗauka bayan ta ɗau packed lunch ɗinta ta saka a jakan, itama ta nufi ƙofar fita a gidan tana ɗaura jacket ɗinta saboda sanyi, sai da ta fita ta janyo ƙofar ta rufe kafin ta kalli street ɗin nasu, a hankali ta soma tafiya, ta kalli agogon hannunta she’s not late kamar dai ko yaushe.
Bus na tsayawa S.t Emery’s Academy, ta sauƙo tana kallon sauran students ɗin da duk Irin kayanta suke sanye da Shi , makarantan look like ƙaramin university than high school.
Yadda students suke wucewa kowa da ɗan uwan tafiyarsa wasu na dariya wasu na hira abinsu ta bi da kallo, kamar ko yaushe ita kaɗai take tafiyarta ba kuma dan rashin masu son kawance da ita ba, sai don ita ce bata taba sake wa har tayi kawayen.
“Nima”
ko bata juya ba tasan mai kiranta, dakatawa tayi har ta Iso ta, Linda, ita kaɗai ce ta nace mata take ƙoƙarin ganin kullum sun zama friends bata damu da shareta da Na’iman Ke yi sometimes ba, yarinyar wani Nigerian professor ne, akwai ta raha da barkwanci.
“U didn’t reply my text yesterday night”
“I was asleep”
“Uh-uh” Linda ta faɗa tana mata wani kallo da yasa tayi murmushi suna cigaba da jerawa tare har suka shiga class.
Ana fita lunch inda ta saba zama nan ta tafi ta zauna, ta ciro wani littafi da take karantawa ya ajiye saman table, box ɗin packed meal ɗinta ta ciro ta ajiye ta soma cin abincin tana kallon yadda sauran suke cin abincinsu in groups suna hira da dariya.
Rufe box ɗin tayi ta buɗe jakarta ta Ciro book da Pencil, sunkuyar da kanta tayi ta fara zane perfectly.
Fuskarsa bai fito sosai a zanen ba amma yanda zanen ya fita, da bridge ɗin, yanayin tsayuwarsa, a hankali ta zubawa zanen idanunta, mutumin rannan.
Ahmad Yarwa’s Residence
No. 10 Yewande Crescent, Ikoyi, Lagos, Nigeria.
Hasken fitowar rana ce ta haske dogayen bishiyun da suke zagaye da babban glass Mansion ɗin wanda hasken ranan ya ratsa har cikin babban living room ɗinnasa, a tsaye yake a gaban makeken glass ɗin Yana kallon waje hannunsa d’aya a cikin dark Gucci jogger pants dake jikinsa, Wanda yabi dogon figure d’inshi, tambarin Gucci dake jikin dogon wandonnasa ya k’ara wani modern flair to the look not as casual as he wanted to look, fitted balanciaga hoodie ne a jikinsa charcoal grey colour, taushin cotton d’in making him feel comfortable yet sophisticated.
K’afafunsa sanye cikin sandals na Hermes Izmir.
Faint knock d’in da akayi a bakin k’ofa sau biyu, ya sa Shi juyowa Yana barin jikin glass d’in ya zauna a gefen gado Yana bada izinin shigowa, da sallama ta shigo d’akin sanye cikin silk robe da yabi jikinta ya mata matuk’ar kyau, fuskarta d’auke da murmushi, d’ankwalin silk d’in a d’aure a kanta Yana bayyana gaban gashinta da Ke kwance gwanin sha’awa, idanunshi ya zuba mata har ta mayarda k’ofar ta rufe ta k’araso gefen gadon ta zauna dab da Shi.
“Good Morning albi”
ta fada tana Kai hannu ta Shafa fyn beard d’inshi, lazy hazel eyes d’inshi ya zuba mata
“Coffee’s ready”
ta fad’a tana mik’ewa ganin Irin kallon da yake binta da Shi, ta juya da niyyar fita ya sa hannu ya rik’o hannunta ya juyo da ita tare da zaunar da ita a tsakiyan k’afafunshi, Muryarsa cike da laziness yace
“Come here….”
ya fad’a yana d’aura fuskarsa a gefen wuyanta hannunshi d’aya na kan cikinta da Ke nan flat kamar bata taba haihuwa ba, d’ago kanshi tayi da hannu biyu ta tallafe fuskartasa tana marairaicewa, yadda tayi da fuskarta yasa Yayi dariya Yana mik’ewa tsaye tare da ita.
Hannunshi ya sa ya sark’e a cikin nata a hankali take biye da Shi har suka fito falon Shi da Ke saman, ya k’arasa kujera ya zauna itama zama tayi a gefensa wani Irin sonsa da k’aunarsa ña sake huda jininta, coffee d’in ya d’auka ya Kai baki ya kurb’a ya juyo ya kalleta ganin yadda ta kafe Shi da ido ya d’aga mata gira alamun “what?” da hannu ta masa alama da “I just love you so much”
murmushi Yayi ya cigaba da Shan coffee d’in, door bell d’in da aka danna ya sata kallon k’ofa sai kuma ta mik’e bai ce mata komai ba har ta fita, komawa Yayi ya kishingid’a ya lumshe idanunsa, bata jima ba ta dawo da package mai kyau a hannunta a ajiye a kan table ta dawo kujeran ta zauna tana danna wayarta
“Gardener d’innanne ya kawo plants d’in da kayi order for the backyard”
“Uhm”
sai kuma ya d’an zauna da kyau
” I want to make the garden even more beautiful, so that Ke da Saif zaku fi Jin dad’insa, kuma we can all relax there”
ya fad’a yana kallonta kanshi relaxed a kan kujeran.
Kallonshi kawai take yi babu ko kyaftawa
“did u know that ure the best husband ? and I love you so much”
ta fad’a tana matsowa ta kwantar da kanta a k’irjinshi
K’asa k’asa yace
“well, now I know, where’s saif?”
“Downstairs?”
“Woman u aren’t even sure”
ya fad’a yana mik’ewa tsaye, k’ofa ya nufa tabi Shi da kallo, ta yaya zata fasalta Ahmad a cikin rayuwarta? Mutum d’aya da take jin bazata tab’a iya had’a son Shi da kowa ba Kai hatta iyayenta, mutumin da bazata iya sharing d’insa da kowa ba, gwara mata mutuwarta akan hakan.
Tsaye Yayi a falon ganin bai ganshi ba ya sa shi k’arasawa wani dak’i da a gaban d’akin clearly aka rubuta SAIF’s kingdom, bud’e k’ofan Yayi without making a sound, a nan ya hangoshi lost a cikin abinda yake yi, babu abinda babu a d’akin, a gefe d’aya shelf ne a cike da books, ga kuma slide, sai wani babban digital screen ña drawing, prayer area d’inshi da small prayer mat a wajen harda wurin ajiye Qur’an d’inshi da sauran storybooks d’inshi, manyan toy cars d’inshi, chalk board mai kyau a gefe da “hero ” a rubuce a jiki da farin alli, Furnitures d’in cikin d’akin duk customized da sunansa “Saif AY” a jikinsu. Tiptoeing Yayi without making a single sound ya k’araso tare da saka hannuwashi ya d’aga Shi sama daga kan slide d’in da yake wasa akai. Sama Yayi da Shi Yana masa chakulkuli Wanda ya sa Shi kyalkyalewa da dariya kamar zai shid’e Yana wuntsula k’afafunsa shima dariyar yake yi kafin ya sauk’e sa a kan fyn bed d’insa
“Shh”
yace Yana d’aura yatsunsa akan lips d’in yaron da yake nan moist da yawun dake lips d’insa
“How’s my champion today huhn?”
Ya fad’a Yana gyara masa zaman clean white shirt d’insa,
“Papa put me down”
ya fad’a Yana wuntsula k’afafunsa da Ke sanye da snickers farare dai-dai da k’afafunsa, beige short d’in dake jikinsa da bai sauk’a Sosai ba yasa ana iya ganin kananun farare tass d’in k’afafunsa.
Sauk’esa Yayi Yana kallonsa ya tsaya a gabansa, Saif na kallon babannasa yace
“do I look like a big man papa?”
Amira da Ke tsaye daga bakin k’ofa tace
” u look like photocopy d’in babanka”
duk juya wa suka yi suna kallonta ta k’araso cikin d’akin.
“Sai dai ni da nake 4 years ban Kai haka kyau ba”
ya fad’a Yana gyara masa gashinsa. Dariya Amira tayi tana Kallonsu cike so da so k’auna mara surki
“Did you dress ur self” ya sake fad’a yana d’age giranshi Yana kallon saif d’in
” Nace ma Mary ta saka min shirt Irin wanda Papa ya sa a London shine ta saka min wanann”
ya fad’a yana nuna shirt d’in
“Uhm I see”
ya fad’a yana mik’ewa ya d’aga Shi ya d’aura Shi a kafad’anshi suka fice a d’akin, da ido ta bisu murmushinta ya gagara b’uya, a duk lokacin da Ahmad yake gida farincikinta kasa b’uya yake, shiyasa all his business trips suke matuk’ar damunta.
K’arfe uku da rabi dai-dai k’ararrawan tashi a school ya kad’a, Na’ima ce k’arshen fita a ajin goye da backpack d’inta da Ke cike da littafan da ba lallai ta karantasu Yau ba, sai da ta Fito harabar kafin ta Ciro wayarta da Ke cikin jakanta, out of habit ta duba kamar dai kullum babu wanda ya kirata sai Mummy da ta mata 1 missed call, kashe wayar tayi ta mayar jaka, ta d’an kalli parking lot d’in da Ke cike da tsadaddun private cars dan d’aukan yaran gata, William ta hango ya zo d’aukanta Yana tsaye Yana kallon harabar, tasan ita yake nema ko inda yake bata nufa ba sai ma canza hanyarta da tayi kamar ko Wace rana, she prefer trekking tunda ba wai wani nisa ne daga st Emery’s zuwa gidannasu ba, har yanzu garin sanyi k’alau kamar dai ba rana ba, a hankali ta cigaba da tafiyarta har ta fita daga makarantar gabad’aya ta kama hanyar gida, 2 streets away ta ja ta tsaya da mamaki tana kallonsa sai kuma ta cigaba da tafiya a hankali kamar bata gansa ba , Yana tsaye jikin wani brick wall a k’ofar wani gida Yana danna wayarsa, Yayi crossing legs d’insa, daga dukkan alamu daga gidan ya fito, Yana sanye da hoodie grey colour da farar shirt ta ciki, looking as simple and handsome as ever.
Har ta wuce Shi bai d’ago ba har sai da ta Kai k’arshen layin kafin ta d’ago ta sake kallonsa ganin kamar zai d’ago tayi saurin juyawa ta cigaba da tafiya gabanta ña fad’uwa
” is that his house?”
Ta tambayi kanta, murmushi kawai tayi tana jin nishad’i a lokaci d’aya har ta iso gida, wani zuciyar na mata fad’an meyasa bata masa magana ba, ko da ta Iso gidan ganin motar da William yaje d’auko ta da Shi a parking space alaman har ya dawo Kenan ya sata jan k’aramin tsaki ta k’arasa k’ofar falon ta bud’e ta shiga.
D’akinta ta wuce Kai tsaye, tana cilli da takalmanta ta jefa jakanta saman kujera ta k’arasa wajen Mirrow ta zare gyalen kanta coiled gashin kanta ya zubo kamar dama gyalen ya takura masa, cire blazer d’in tayi ta ajiye kan kujeran gaban dresser sannan ta zare socks d’inta shima ta ajiye a gurin ta wuce band’aki, wanka tayi da alwala ta Fito, sai da ta fara Sallah kafin sauri sauri ta shirya cikin farar shirt da wandon Jeans d’in da bai Kai k’waurinta ba ta d’auko oversized hoodie ta d’aura saboda sanyin garinnan is not for the weak, ta d’auko wasu socks masu kauri ta saka ma k’afafunta, Jin knocking a k’ofarta ya sa ta juya ta kalli k’ofan sai da ta k’arasa ta d’auke jakarta daga kan gadon ta Kai Shi ma’ajiyarsa ta tattare socks da takalman da ta watsar kafin ta bada izinin shigowa.
Mariam ce ta shigo d’aya daga masu aiki biyu ña gidan, sai da ta gaishe ta kafin ta tambayeta ko a kawo mata abinci nan sama, murmushi kawai tayi tana kallonta
” No Mariam Zan zo Yanzu, Dad Yana nan?”
” Ah ah sun fita tare da Mummy basu ma dad’e da fita ba”
Gyad’a mata Kai tayi “okay kije ina zuwa, kice ma Lilly ta min hot chocolate pls”
“Toh sai kin Fito” ta fad’a tana fita a d’akin ta rufo mata k’ofan, gurin jakar makarantarta ta k’arasa ta Ciro wayarta kafin ta sauk’o k’asa tana had’a steps d’in bibbiyu cike da kuzari kamar dai ba ita ba, a makeken falon ta tararda Mariam tana Kallo Lilly kuma na Kitchen tana had’a mata hot chocolate d’in da ta buk’ata, kujera ta ja a dining ta zauna ta d’aura k’afafunta duka biyu a kan kujeran ta tank’washe ta d’auki sandwich d’aya ta Kai baki tana maida hankalinta gabad’aya kan abinda Mariam take Kallo, har Lilly ta kawo mata hot chocolate d’in ta ajiye mata itama ta koma wajen Mariam suna kallon tare, sai da ta gama cin abinda zata ci ta mik’e ta wuce sama abinta duk suka bita da Kallo, ita haka take Sam bata da magana ko da yake basu sani ba ko tana da Shi ko bata da Shi, dan bata da abokin hira a gidan, sai dai a k’ananun shekarunta Zasu iya cewa bata da rawan Kai Irin na sa’aninta.
Ko da taje d’akinta, headphone ta d’auka ta saka a kunnenta tayi connecting da laptop d’inta ta cigaba da kallon da take yi, tana da assignments da yawa amma sai zuwa dare zata yi su.
Washegari ma bata yarda william ya ganta ba ta Fito abinta, har ta Iso inda ta ganshi jiya, tana ta kallon gidan sai dai Yau bata ganshi a wajen ba, d’an tsayawa tayi kamar mai jiran wani abu daga k’arshe ta juya ta cigaba da tafiya feeling a little bit Sad,haka ta wuni sukuku ba kamar jiya ba.
Har satin ya k’are weekend ya zagayo bata sake ganinsa ba, Ita ma kawai sai ta tattara saka ran ganinnasa ta watsar, Dad bai gaji da tura William d’auko ta ba duk da ya san ba binsa take ba, Yayi fad’an har ya gaji.
Kwana biyunnan kamar a kan k’aya haka ta dinga jinta a daddafe ta k’arasa weekend d’in, halin Dad da Mummy babu abinda ya canza, haka kuma boring life d’inta babu abinda ya canza.
Lagos, Nigeria.
K’arasawa tayi kan sofa ta zauna tana kumbura fuska, ita fa zuciyarta kawai bata aminta da duk wani wanda zai rab’esa ba gani take kamar zai rabata ne kawai da Shi.
Ahmad da Ke tsaye a tsakiyar d’akin ya zuba mata idanunsa, kwata kwata ya ma rasa me zai ce mata cause abinnata Yanzu ya fara wuce gona da iri.
Kallonshi tayi ganin har sannan kallonta yake yasa ta sake b’ata rai
“Albi, ni gaskiya bazan iya pretending ina kallo ko Wacce ta shigo min gida da sunan y’ar uwarka ce ba, u know I love you, ko ni kad’ai ban isheka ba?” Ta fad’a Tana mik’ewa ta k’araso gabansa tana k’ok’arin rik’e hannunsa.
Zare hannunsa da ta rik’e Yayi daga cikin nata Yana mata wani Irin kallo da yasa ta sha jinin jikinta ta sake tura masa baki ba tare da tace komai ba
Ba tare ya ce mata komai ba shima ya juya ya nufi k’ofa, da idanu ta bishi, ita fa gwara haka ta san zai sauk’o ne amma gaskiya bazata iya da wani tarkacen danginsa mata ba. Ta koma kan sofa ta janyo wayarta, whatsapp ta bud’e ta tura ma babbar k’awarta Nuwaira voice note na yadda sukayi dan dama ita ta bata shawaran Irin wulakancin da zata Musu Idan sun sake zuwa.
Tana Jin tada motarsa ta wurgar da wayar ta je bakin window tana kallonsa har ya fita a gidan, ranta ta sake Jin ya b’aci dan ta San ma ina za Shi, sake bind d’in tayi ta d’auko wayarta ta sauk’o k’asa, Jamila dake goge goge a falon k’asa ta tambaya Saif, tace mata
“ai tare suka fita da Sir”
Juyawa tayi ta koma sama ranta a mugun b’ace, d’anta zai d’auka ya Kai wajen mayunnan? d’anta? Mutanen da ba sonta suke ba? Kiransa ta shiga yi amma baiyi picking ba sai da ta Kira Shi sau hud’u sanin bazai d’auka ba ta wurgar da wayan cike da b’acin rai ta wuce bedroom d’inta.
Yau Sunday, wanda ya kasance Ranar fundraising na st Emery’s kamar yadda ake yi duk shekara.
iyaye, da malamansu harma da donors na makarantar duk sun hallara, event ne da ake yinshi dan samar ma makaranta kud’in shiga inda seniors wato d’alibai da Ke final grade d’insu suke gabatarwa, yanda aka yi decorating d’in makarantar Yau abin sha’awa ko wani d’alibi wato seniors d’in na k’ok’arin ganin abinshi aka fi saya. Na’ima na gefe guda cikin truck d’inta wanda a gabansa banner ne babba da aka rubuta “young minds big dreams” sai kuma wani banner daban da aka rubuta ” kasuwar makaranta akan taya ” wato “the crest cart, students market on wheels” kasancewar shagonnata kamar Mota.
Ko wanne senior an bashi damar tsara wani Abu da zai burge bak’insu na ranan, kama daga kasuwanci, tallace tallace, fashion shows Kai babu abinda babu. Wasu Kayan Zane ne da su da nasu banners d’in wasu kuma Sayar da lemuka ko abinci, kayayyakin fasaha na zamani babu Irin wanda babu.
Duk da Na’ima bata so zuwa ba, amma kasancewar Mummy ta riga tayi maganar ya saka ta Maida hankali kan nata project d’in cikin last weekdays. tasan babanta na cikin donors na makarantar kamar yadda ta san Yayi donating na d’aukan d’aukan nauyin sabon science lab da za’ayi amma bai fad’a mata ba kuma tasan bazai fad’a ba.
Babu abinda bata sayarwa a Shagon nata kama daga lemuka da popcorn, da tayi da kanta, tare da Yan team d’inta, kayayyakin kyauta har da riguna masu tambarin St Emery’s a jikinsu, Sosai ta ja hankali a wajen. Tana sanye da riga fara tass mai dogon hannu da jeans blue, ta nannade hannun rigan sai apron da ta d’aura navy color mai tambarin St Emery’s shima a jikinsa, kanta yane da bak’in gyale, gaba d’aya tayi busy da y’an team d’inta banda saye da sayarwa babu abinda sukeyi, layi Sosai suke da Shi a gabansu na masu siyan abubuwan da suke sayarwa wanda duk seniors d’in babu wanda ya kaisu busy da ciniki.
Gefenta ta kalla, ganin juliana sai aikin tallan arts d’inta take tare da nata team d’in sun cika wak’a, Kowa k’ok’arinsa a zo wajensa, murmushi tayi tana cigaba da sallamar wad’anda Ke window d’inta suna placing orders, kamar ance ta d’aga kanta ta hangosa, saurin tsugunawa tayi a cikin truck d’in
“Me ya kawosa?”
“Mira!” Josh ya kirata daga waje, tayi saurin d’agowa tana k’irk’iro murmushi
“Gaskiya layinnan Yayi yawa, anya bazaki kafa tarihi ba kuwa?”
Dariya tayi tana cigaba da sallaman mutanenta da taimakon kawayenta da Ke team d’inta tana kallon Josh da shima yake cikin nashi truck d’in. d’ago wa ta sakeyi a karo na ba adadi ta kalli inda yake cikin rashin sa’a sai suka had’a ido da sauri ta d’auke idanunta.
Bai zo inda suke ba sai dai kafin a tashi sun had’a ido yafi a k’irga, duk d’ago kan da zatayi sai taga ita yake kallo.
Har yamma kafin taro ya zo k’arshe inda shugabar makarantar ta rufe taro da bayani mai k’ayatarwa.
Sannan ta gayyaci seniors kan stage ta Yaba musu tare da basu kyaututtuka, inda Na’ima ta Samu kyautan “top earner of the Day”
Tana rik’e da plaque d’in ta sauk’o tana kallon yadda iyaye Ke d’aukar hotunan yaransu, kwata kwata dama bata saka ran ganin Mummy ba amma ta d’auka Dad zai zo, Gashi shima bai zo ba.
A jikin truck d’inta da sun riga sun sayar da komai ta ganshi a tsaye, ya nad’e hannunshi a k’irji Yana kallonta.
Har ta k’araso inda yake kafin tayi magana ya rigata
” me Zan Samu a abinda Kike sayarwa?”
d’an murmushi tayi tana k’arasawa dan kulle motar ” ka makara, an sayar da komai ka dawo wata shekara”
Yana tsaye har ta Fito da niyyar tafiya gida
” so nan ne makarantarku?”
” eh Kai me Kazo yi?”
Ta tambaya tana cire apron d’in Samar rigarta ta cusa Shi a jakarta ta zaro jacket ta d’aura tare da goya k’atuwar jakanta.
“Abokina happens to be one of the donors, Shi ya gayyace ni”
“Na gane!” Ta fad’a tana mai d’aga masa hannu alamun sai anjima, har ta soma tafiya ta ji ya biyota d’an murmushi tayi a hankali
“Walking home?” Ya tambaya Yana jerawa da ita cike da nutsuwa. Gyad’a mishi Kai tayi a hankali suka Jero suna tafiya a hankali.
Har k’ofar gidansu ya rakota, “thank you” tace tana rik’e hannun jakanta da Ke kafad’anta
” can I get ur number?” Ya fad’a sounding direct, like it was the most casual thing in the world
Sai da ta kyafta idanunta dan bata yi tsammanin tambayanba
“U don’t even know my name” ta fad’a tana kallonsa, jingina Yayi da poll d’in dake gefen sa Yana Kallonta
” not after yadda Kowa a shouting sunanki a makarantarku”
Bata san lokacin da tayi dariya ba tana kallonsa, wayarsa ya mik’a mata still looking at her, ta mik’a hannu ta karb’a tana saka masa lambar
” if u end up texting a stranger ni dai ba ruwana”
Murmushi kawai Yayi Yana kallonta bai ce komai ba, ta mik’a masa wayarsa ya karb’a Yana mik’ewa tsaye da kyau
” to Kai ai Baka fad’a min sunanka ba”



