Chapter 29: Chapter 29
“Me aka ɗaura Ahmad?” Ɗan lumshe kyawawan idanunsa yayi ya gagara amsawa
“Amma ce min kayi zaka je kuyi tambaya ai ba ce min kayi zaka aureta yau ba”
“Na sani Ammi” ya faɗa a hankali yana shafa forehead ɗinsa,
“I didnt plan it dis way, su uncle haruna suka ce a ɗaura kawai na faɗa miki whats going on ai Ammi shiyasa suka ce its better kawai a ɗaura, kuma..” katseshi tayi tun kafin ya kai ƙarshe
“Yaushe zaka dawo lagos?”
“Anjima in sha Allah”
“Kana dawowa dama ka same ni a gida immediately”
“Tohhh..” ji yayi ta katse wayar, ya sake sauƙe ajiyar zuciya a hankali, kafin ya buɗe motar ya sauƙa ya koma cikin gidan.
Zuwa ƙarfe 2:30 suka shirya komawa Lagos after much hospitality, sosai they were impressed with how sukayi treating ɗinsu, the genorosity and warmth sun tabbatar Na’ima yar babbar gida ce ba na arxiƙi kaɗai ba, sosai uncles ɗinsa ke ta yabonsu.
Ko da suka iso lagos lokacin ƙarfe 5:10, har lokacin bai sake kiran Na’ima a waya ba tunda ya kirata ɗazu bata amsa ba, direct gidansu ya wuce dan amsa kiran Ammi bayan sun rabu da Uncles ɗinsa da Nasir da shima zai je gida ya huta.
Yana shigowa Palourn Yasmeen da Rahama dake palour suka gaishe shi, ɗan murmushi ya musu ya amsa a gajarce kafin ya wuce sama, suka kalli juna Sannan suka sake kallon Saman, cause murmushin ne ya basu mamaki, hes not the kind of person that wastes smile, he is caring duk abinda suke so yana musu tun kafin ma Abba ya rasu amma affection ɗinshi is a quiet one, clearly something is different. Ba dai wacce tayi magana suka cigaba da kallon da suke yi.
A palourn sama ya iske Ammi wacce tana kallonsa ta miƙe ta wuce bedroom ɗinta, ɗan murmushi yayi kaɗan ya shafa gashinsa kafin yabi bayanta.
Ammi ta zauna a gefen bed kafin ta nuna masa kujera fuskarta ba yabo ba fallasa, ta ɗan tura ƙofar ɗakin kafin ya ƙaraso ya zauna a hankali yaƙi ya kalleta.
“Haka muka yi da kai?” Sai a lokacin ya kalleta yace
“Ammiii”
“Dont Ammi me anan pls, haka mukayi da kai?”
“Ammi da gaske na miki ba da wannan niyyar naje ba, after much tattaunawa ne suka ga hakan yafi dai dai, uncle haruna yace a ɗaura zaifi she’ll be more safe, Ammi kinsan yadda abubuwan suka kasance i told u”
“Shi harunan ne yace idan aka ɗaura yarinyar will be more safe koh? Tunda kaine zaka dinga gadinta?”
“Ammiii” ya faɗa a marairaice, ta wani hararesa tana cigaba
“Kana min abinda ka ga dama Ahmad, amma ba komai ni bazan hana ka zama da matarka ba tunda ƙiri ƙiri ka ƙi yar uwarka a kanta”
“Ammi it happened quickly ne…to kiyu haƙuri” kawai ya faɗa dan kawo ƙarshen maganar
“Ni kuma ina ruwana? Kai nake jiye ma ai, bayan na faɗa maka yadda mukayi da Salma akan yarinyar amma sam ka ce min kai ka san yarinyar ba haka take ba kai ka sani bayan ita fa take goyon yarinyar ai bazaka faɗa mata halin yarinyar ba”
“Hmm” kawai yace yana Shafa Kansa dan baya son ɗago maganar, kamar dai ba Salmar da lokacin da zata auri so called mijinta ba irin rashin kunyar da bata yi ma Ammi ba akan ta hanata amma wai har ta manta idan Ammi tana manta wasu abubuwan shi baya mantawa, ya kauda maganar muryarsa cike da lallashi yace
“Ammi albarkarki kawai muke nema a cikin aurennan kinji, ki mana addu’a idan ma akwai wani abinda ba alkhairi bane Allah ya kawar mana da shi albarkacin addu’arki sai komai ya tafi smoothly” ta ɗan ɓata rai tana kallonsa tace
“Toh me zan ce ma Salma kuma? Kawai sai in ce mata kayi aure kenan? Sai dai in ka amince zaka auri Suhaila itama tunda auren kake so kayi ta yi” ya ɗan haɗe rai yana gyara zamansa yace
“Ammi kiyi haƙuri amma ni ba auren Suhaila zanyi ba, Infact ni bazan iya zama da mata har 3 ba” wani harara ta masa tace
“Zaka iya zama da biyu sai uku ne bazaka iya ba?”
“Biyunma Allah ya gani da in ta ni ne da ɗaya zan zauna har ƙarshen rayuwa ta” sai kuma yayi ƙasa da murya ya dawo ƙasa kusa da ita ya zauna yace
“Ammi, pls dan Allah ki taimaka min, da gaske bazan iya zama da mata uku ba, am complete now i promise u, ko na aureta bazan iya musu adalci ba cause a yanzu ma ina tunanin yadda zanyi adalci tsakaninta da Amira” kallonshi kawai Ammi take yi kafin ta sauƙe ajiyar zuciya ita ta rasa ma ya zatayi da shi, but to be honest farincikinsa shine nata, duk da ta so ya auri Suhaila har cikin ranta ko dan ya sake jan yar uwarta a jiki, dan tun aurenta na farko da ta auri wanda ba musulmi ba sosai suka sami matsala da har salma ta yanke duk wata alaqa da ita dan dai kawai ta hanata auren tunda su biyu kaɗai suka rage ma juna sai dangin nesa nesa, amma sam Salma tace bata san zancen ba tace ita ta auri ɗan wata ƙasa tana mata baƙincikin itama ta auri bature bayan a gabanta take da zama kuma mijinnata shi yayi sponsoring karatun salmar a ƙasar wajen shiyasa shima yace bai yarda da auren ba, ko bayan aurenta na biyu ma ba wani sosai take neman Ammi ba sai dai in Ammi ce ta nemeta kuma zata iya ƙirga sau nawa ta zo 9ja, shiyasa da Suhaila ta dawo ƙasar gabaɗaya da mijinta she was very happy kuma ko da ta zo mata da buƙatar haɗa suhaila da Ahmad bata yi zuciya ba ta karɓi shawarar da tunanin hakan zai sa ta janyo ƙanwar tata jikinta sosai ta dinga nuna mata inda bata yi dai dai ba har ma da ita kanta Suhailar dan ta lura sosai Salma ta ɓata Suhaila atleast in a gida take aure zasu iya gyarata kar taje tayi aure inda zata sha wahala, but since things turns out this way ba yadda ta tsara ba dole ta haƙura ba yadda ta iya kar kuma Aje garin neman gira a rasa idanu.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tana kallonsa tace
“Allah ya sa haka shi yafi alkhairi, Allah ya baku zaman lafiya, Allah ya baka ikon yi musu adalci, ya sa ace gwamma da akayi ya muku albarka” murmushi kawai yake yana kallonta, kafin ya amsa da
“Amin Ammi thank you”
Dai dai lokacin Salma dake tsaye a bakin ƙofa tana jin conversation ɗin nasu dan ƙofar is slightly opened Ahmad bai tura da kyau ba ta sake jikin ƙofar zuciyarta na mata wani tsinannen zafi, bata jima sosai da zuwa gidan ba ta wuce su yasmeen a palour suna kallo suka ce mata Ammi na sama shine ta hauro, ganin ba kowa a palorn ta nufi ɗakin Ammin just to overhear wannan tashin Hankalin, Ahmad yayi aure kuma ba suhailarta ba kuma har Ammi na da bakin musu addu’ar zaman lafiya? Da sauri ta juya ta bar jikin ƙofar ta nufi ƙasa kamar zata tashi sama, a steps suka ci karo da yasmeen dake haurowa, da sauri yasmeen ta matsa mata gefe ta sauƙa kamar ana hankaɗa ta kafin yasmeen ɗin ta bita da ido sai kuma ta kalli sama, tohhh what happened hala? Wucewa saman tayi itama tana mamakin uban saurin da Salma keyi, itama Rahama da mamaki ta bi Salma da kallo dan ko amsa mata sai anjiman da take mata bata yi ba ta fice a gidan a fusace, itama dai saman ta kalla kafin ta tashi ta haura da gudu.
Dai dai lokacin Ammi ta fito palour daga ɗakinta a palourn ta gansu a tsaye tana kallonsu ta ƙarasa ta zauna kafin tace
“Ku kuma lafiya?” Kallon juna sukayi kafin su girgiza mata kai
“Babu komai..” yasmeen tace
“Mummy Salma ce naga ta sauƙa da sauri kamar zata tashi sama shine muka hauro mu ga ko dai lafiya?” Da mamaki Ammi ke kallonsu kafin tace
“Salma kuma?” Suka gyaɗa mata kai a tare, ɗan shiru tayi kafin tace
“Salma ta zo gidannnan ne? Kuma tun yaushe?” Dai dai lokacin shima Ahmad ya ƙaraso cikin palourn ya zauna yana kallonsu,
“Yaya Ahmad bai jima da zuwa ba tazo, kuma bata jima da Sauƙa ba da sauri kuma kamar ranta a ɓace”
Ammi ta kalli Ahmad shi dai ɗauke kansa yayi ya kwanta a kan doguwar kujera ya miƙe yana danna wayarsa
Ta miƙe ba tare da ta sake cewa komai ba ta wuce ɗakinta dan ɗauko wayarta ta kira salmar, sai dai duk kiran da ta dinga mata bata ɗagawa hakan yasa ta ɗan taɓe baki ta wuce toilet dan alwalar magriba.
Tunda Ammi ta wuce ɗakin su yasmeen suka zauna suna kallon Ahmad dake game a wayarsa harda tagumi, ya ɗan janye wayar yace
“Shi kuma kallon fa” murmushi sukayi a tare
“Babu yaya”
Ya miƙe zaune yana kallonsu sai kuma yayi murmushi ya shafa kansa yace
“I’m a happy man today, tell me duk abinda kuke so”
Da sauri suka tashi suka dawo gefensa kowa tana faɗan nata ya gyara zamansa yace
“Ku tura min acc ɗinku”
“Yaya ba kana da shi ba?” Yasmeen ta faɗa tana ta washe baki
“Toh ku barshi” da sauri suka shiga dariya da girgiza masa kai kowacce na danna wayarta da ƙoƙarin tura masa, ya miƙe ya nufi ƙofa dan an fara kiran sallar magrib.
Mummy Salma tuƙi kawai take amma zuciyarta wani irin zafi take mata, ta danna wani uban horn tana kallon motar da ke gabanta, mutumin dake take cikin da ke gefenta yace
“Ahh madam u wan fly?”
“Yes i want to fly to gidan uwarka tsinanne” daga haka ta ja glass ɗin motarta sama tana wani irin huci, tana kallonsa yana magana bata ma san me yake cewa ba ji take kamar tayi ta ashar a cikin traffic ɗin.
Ta lalubo wayarta daga jakarta ta nemo lambar Suwaiba ta danna mata kira tana ɗagawa ko amsa sallamarta bata yi ba tace
“Suwaiba kinje wajen malam?” Suwaiba daga ɗaya ɓangaren tace
“ke dai daɗina da ke gaggawa Salma, gobe nake shirin zuwa”
“To na canza shawara, Suwaiba gani nan tahowa yanzu mu tafi ogun” Suwaiba tace
“Wani irin ogun ana zaune ƙalau?”
“Wajen wancan mutumin zamu je, da ya min aikin auren mustapha, dan yafi guarantee, suwaiba komai ya kwaɓe min, gani zan zo gidanki yanzu mu tafi a motata”
“Ah ah dai ki bari da safe ko fa mun tafi yanzu cikin dare zamu isa, kuma sai mun jira safiya mu gansa ke ma kin sani ko yamma”
“Bazan iya komawa gida ba suwaiba idan bazaki je ba in tafi ni kaɗai amma yanzu zan ɗauki hanya kinji na rantse miki, na gwammace in yi jiran a can” suwaiba ta wani ja tsaki
“Gaskiya idan nace baki shiga rayuwata ba nayi ƙarya, nikam sai kin zo, idan kika so abu kamar ɗa ya so fita a cikin uwarsa ina jiranki toh”
Katse wayarta Mummy salma tayi tana driving da hannu ɗaya ta danna ma Daddy kira, sai da ya kusa katsewa ya ɗauka ta saisaita muryarta tayi ƙasa da shi suka gaisa kafin ta fara kuka har da sheshsheqa ƙasa ƙasa
“What happened?” Ya tambaya jin shehseƙar tata
“Wai suwaiba ce aka kirani yanzu wai tayi accident a hanyar abeokuta, kuma ni ce wacce mukayi waya ƙarshe da ita gashi they cant reach her other contact “
“Subhanallah, why not call her husband?”
“Ai sun rabu da mijin kasan, kuma gashi yar gudun hijira ce daga chad bata da kowa a nigeria sai shi ɗin ayya Allah am, kuma sunce accident ɗin yayi muni”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” kawai ya faɗa a hankali
“Shine na kiraka ko zan je in ga yadda abubuwan suka kasance” tana faɗa ta sake fashewa da kuka
Ɗan shiru yayi sai kuma yace “Allah ya tashi kafaɗunta no problem ill send u money now”
“Toh na gode Allah ya saka” daga haka ta katse wayar ta share hawayenta tass ta shiga kiran Suhaila har ya katse bata ɗaga ba sai ga suhailar ta kira back.
“Kina gida ne?” Mummy ta tambaya kai tsaye tana shan kwana da motarta,
“Ah ah mun fita da su philips”
“Da yaushe zaki dawo?”
“Sai gobe”
“Okay, nima nayi tafiya sai jibi zan dawo, make sure in rigaki dawowa gidannan we need to talk”
“Wani abin ya faru ne mummy?”
“Ni dai na faɗa miki”
“To nima sai jibin kawai zan dawo sai in dawo da safe”
“Idan Daddynki ya kira ki kije masa kina gidan Ammi”
“Toh” daga haka ta katse wayar tana mayarda hankalinta kan driving ɗin.
Na’ima na zaune a ɗakinta da daren ranar tana waya da Ahmad dan da alama gidan babu kowa sai ita kaɗai, muryarsa ƙasa ƙasa yace
“Wifeyyy”
“Uhm” tace tana kallon ring ɗin hannunta, dan bata wani ɗauki wifey da ya kirata da shi serious ba, dan names da yake kiranta da shi sunfi ɗari goma
“Are u leaving immediately after the exams goben?”
Ta marairaice tace “Ai mami ce tace haka, i wanted in bari sai jibi, kaga in na gama exams gobe sai inyi parking in yaso jibi sai in tafi”
“No its better ki tafi goben since Mami tace haka”
“Toh” tace a hankali.
“I’ll book u d flight” gyaɗa masa kai tayi kamar yana ganinta ta koma ta kwanta tana saurarar abinda yake ce mata next da murmushi a fuskarta.
Washegari tana dawowa daga last paper ɗinta wanda Ahmad ya sa aka rakata ta rubuta cause of Sadiq, dan shi da kanshi yaso ma ya kaita ta rubuta paper ɗin but dole ya haƙura dan akwai wani important deal da yake son closing a office.
Tana dawowa daga paper ta watsa ruwa ta canza kayanta kafin driver yayi dropping ɗinta a airport dan tun jiyan Ahmad ya tura mata ticket ɗinta via Email ɗinta, dama ta gama parking tun a jiyan, kuma ko da Dad ya dawo har palournsa taje sukayi sallama, though wasu maganganunnasa bata wani gane ba dan he kept on saying,
“ko miye mamanta zata faɗa mata a Abuja she should know that its for her own good and they want whats best for her” sosai jikinta yayi sanyi amma sai kawai ta masa godiya, shine ma yake faɗa mata mummy salma bata nan da tace masa zata je ta mata sallama he told her she travelled her friend met with an accident.
Basu jima ba jirginsu ya ɗaga zuwa abuja.
The same day ƙarfe 10 na dare salma ta shigo gidan a mugun gajiye, dan ta ƙosa ta dawo gida ta aiwatar da abinda ifagbemi yace ta yi, sosai suka ci wuya a ogun ita da Suwaiba with all the bad roads zuwa inda zasu sami mutumin and all, ita bata yi tunanin ma zasu dawo a yau ba sai gobe, but yadda abin ya tafi successfully kuma suka sami ganinshi da wuri ya sa suka juyo a yau, mutumin ya tabbatar mata Ahmad yayi aure, kuma ko da tace akwai step daughter ɗinta da take so ya gantalar da rayuwarta kar ta taɓa aure nan take ya duba yace mata ai yarinyar is already married, sai alokacin abin yayi clicking kanta wa Ahmad ya aura, kaɗan ya rage ta narka ashar a gaban mutumin jikinta har tsuma yake tace “a lalata auren, ya ɗaiɗaita rayuwar yarinyar sannan a saka ma Ahmad ƙaunar Suhaila ya saki Na’imar ya saki uwargidansa ya dawo suhaila ita kaɗai yake so kamar ransa” mutumin yace mata angama, shine fa ya haɗo ta da charms iri iri, har da waɗanda zata bawa Na’ima taci a abinci da abinsha, sannan ta saka mata under pillow ɗinta ta kwanta shikenan daga nan tana haɗuwa da Ahmad zai ji ya tsane ta baya son ganinta ko 1 minute ba zai ƙara da aurenta ba zai sake ta, sauran aikin kuma akan Suhaila zasu ƙarasa da kansu in ta shiga kuma sai a san yadda za’a fitar da Amira, cike da zumuɗi ta haura sama ta ajiye jakarta ta sauƙo taje ta ɗaura girki ko hutawa bata yi ba tana yi tana jin wani annashuwa da farinciki dan so take ta bata a abincin taci, itace bata gama girkin ba har kusan 11 na dare, duk da kaɗan ta dafa dan Na’imar tana ta zumuɗi, ta ɗauko bowl mai kyau ta ɗiba mata abin da ya sha haɗe haɗe iri iri, ta ɗauka ta haura sama tana murmushi ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Na’ima, jin babu amsa ta buɗe ta shiga ciki ganin babu Na’ima a ɗakin ta ƙarasa ciki tana kiran sunanta da murmushi, jin shiru ta fara kalle kalle kafin ta ajiye abincin a gefen bedside ta saka hannu a cikin rigarta ta ciro wani abu kamar ɗan ƙarami ta ɗaga pillow ɗin Na’imar har da zanin gadon ta ajiye saitin pillow kafin ta mayar da zanin gadon ta maida pillow ɗin tana wani murmushi ta ɗauki abincin tana cewa “ko kin toilet ne baby” jin shiru ta fito da abincin ta zauna a palourn sama ta ajiye abincin akan center table ta miƙe ta wuce ɗakin dad da bai ma san ta dawo ba shi.
Da mamaki ya dinga kallonta kafin yace “yaushe kika dawo?” Ta ƙaraso ciki tana murmushi tace “ba dole na dawo ba kasan instinct ɗin uwa, gashi na bar yarinya ita kaɗai a gida shiyasa na dawo ba daɗi ai kasan irin haka” yana kallonta yace
“Ya mai jiki” sai da ta ɗanyi shiru kafin ta tuna ƙaryar da ta masa na Suwaiba da sauri tace
“hmm ba’a cewa komai ai taji jiki tana can na baro ta wallahi sai ka gani hmm ɗan adam ba abakin komai yake ba”
“To da wa kika barta yanzu?”
“Umm ah ah ai mun dawo da ita nan lagos, kuma hospital ɗin sunce basa buƙatar patient relative sai dai in dinga zuwa ina ganinta
“Allah ya ƙara sauƙi” ya faɗa a hankali yana cigaba da kallon da yake yi
“Bari in je in ba Na’ima abinci bansan ko ta ci abinci ba baiwar Allah” kallon agogo yayi yaga 12 har ta gota yace
“Abinci by 12?”
“To ka sani ko yunwa take ji ai bata kwana da yunwa ba”
“As if she cant Cook?” Ya tamabaya iya kallonta
“Kuma hakane to bari in bari da safe sai in girka mata da kaina yanzu ma na shiga ai na samu tana toilet” ɗauke idanunsa yayi daga kanta a taƙaice yace
“Ta tafi Abuja, she’s done with her exams plus…..” ko jira ya ƙarasa bata yi ba tace
“Abuja kuma?wani irin Abuja?”
Ya gyara zamansa a kan gadon yace
“Eh ta je wajen mamarta ta zo ta miki sallama bakya nan, she had to go saboda a jiya aka …..”
Bata jira ya kai ƙarshe ba nan ba tace “amma tsakani da Allah ai wannan ba yi bane, ta yaya zata tafi Abuja bazata jira in dawo daga inda naje ta min sallama ba, saboda dai bata ɗauke ni uwa ba, duk abinda nake mata ba’a gani, in da ni uwarta ce ai bazata min komai ba amma babu komai…”
Kallonta kawai dad yake ganin yadda take ta jaraba tana haɗa zufa, abin ya bashi mamaki but bai ce komai ba
“Wallahi duk abinda ake min a gidannan ina shiru amma naga alama u guys a taking it for granted, idan ba ni ɗin bama wa ke riƙe ɗan wani a zamaninnan? Amma har zata wuce ta tafi bazata min sallama saboda ta raina ni bata ɗauke ni uwarta ba, an gama nuna mata bani da daraja a wajenta wallahi akwai hisabi tsakani na da ku akan yarinyarnan ranar ƙiyama” daga haka ta fashe da kuka ta nufi ƙofa ya bita da kallo kawai cike da mamaki.
Tana fitowa palourn ta hango Suhaila da ta dawo gidan a daren itama a zaune da kwanon abincin da ta ajiye a palourn a hannu ba bata san sanda ta haɗiye shegen kukan da take ba ta nufe ta da gudu.
“Suhaila!!” Mummy ta Kira sunanta tana ƙarasowa cikin palourn da sauri, suhaila ta ɗaga kanta tana kallonta da spoon ɗin abincin a bakinta wanda yanzu ne ta kai first spoon dama bakinta, ko haɗiyewa bata yi ba, kafin ta gama reacting har mummy ta iso gabanta ta ƙwace kwanon a gabanta ta dungurar akan center table ta kama fuskarta tace
“Buɗe bakin” ta faɗa tana ɗan bubbuga kumatun suhailar, da shegen mamaki Suhaila ke kallonta dan bata gane komai dake faruwa ba, bakinta cike da abinci tace
“Whats your problem?”
“I said open ur mouth ke dan ubanki” mummy ta faɗa tana yago tissue ta saka mata a dai dai bakinta, tofo abincin tayi reluctantly kan tissue ɗin tana ɓata rai.
“Whats wrong with u, daga ganin abinci sai ki kama ci a gidannan, ko ke kika dafa? Ko ni na baki abincin da zaki kama ki hau ci? Cokali nawa kika ci?”
Suhaila tayi rolling idanunta kafin tace “So? Ni ko ɗaya banci ba, to Miye ne idan naci? Whats the big deal ?Yunwa nake ji shiyasa naci, yanzu fa dawowata, to ma yaushe ya zama crime dan naci abinci mummy?”
“Kar ki sake taɓa abinda ba baki nayi ba a gidannan suhaila kinji na faɗa miki” tana faɗa tana zaro wani sabon tissue tace
“ buɗe bakin” kamr bazata buɗe ba ta buɗe bakin, tissue ta saka ta dinga goge mata baki kafin ta haɗa kan tissues ɗin ta miƙe ta ɗauki bowl ɗin abincin ma zata bar palourn, miƙewa itama Suhaila tayi tana ɗan jan siririn tsaki, “wallahi ure so extra sometimes, so dramatic” daga haka ta ɗauki wayarta ta nufi hanyar bedroom ɗinta, Mummy ta tsaya tana kallonta kafin tace “Suhaila, suhaila!” Amma ko juyowa batayi ba har ta kai bakin ƙofarta kafin ta tsaya ta juyo tana kallon mummy, mummy da har ranta ya fara ɓaci tace
“Ni nake miki magana kina wucewa ina dan baki da hankali”
“whatever..” kawai suhaila ta faɗa ta juya ta shige ɗakinta ta rufo ƙofarta, ajiyar zuciya mummy ta sauƙe ta juya ta nufi ƙasa da kwanon a hannunta tana jin wani irin relieve cause it was so close, what if bata fito ba da a minute later ? yo ya ta ƙare ma da Ahmad ɗin yanzu akan Suhaila bare kuma suhaila taci wannan abin ai sun shiga uku.
Sai da ta zubar da abincin a waste bin ta ɗauraye kwanon kafin ta koma sama amma har lokacin baƙin cikin yadda tayi asarar kuɗinta kawai take yi, gaskiya Na’ima ta cuce ta.



