Chapter 3: Chapter 3
Girgiza Mata Kai Yayi ” Zan fad’a miki” ya fad’a Yana kallonta
“Let me guess, Ahmad? Umar? U look like Kamal”
d’an dariya Yayi da ya k’ara masa kyau ta tsaya tana kallonsa, a hankali yace
“Abubakar Sadiq, sadiq bulama”
“Thank you sadiq, for walking me home again”
“Welcome.” Ya fad’a, Tana kallonsa tace “later?” Shima a hankali yace “later Ni’ima”
لا اله إلا الله وحده لا شريك له ،له الملك و له الحمد وهو عل كلّ شيء قدير
Allah ya amsa mana addu’o’inmu yasa munyi ibada karɓaɓɓiya,Barkanmu da Shan Ruwa and Eid Mubarak in advance ❤️ ill not be posting until 3rd day of Sallah insha Allah, aci nama lafiya…..
Chapter 5: Echoes of Friendship and Summers Ahead
Tana kwance a kan gadonta, dan har tayi shirin kwanciya already, tunda suka rabu da Saɗiq ɗazu babu wani abin kirki da ta taɓuka. Sun dai tambayeta yadda fundraising ɗin ya kasance, ta basu labari a tsatstsaye ta wuce sama, tayi waya da Mamie, lokacin dinner ta sauƙa sukayi tare ta koma ɗakinta.
Wayarta da tayi ringing ne ya saka ta ɗan dubi wayar da ke kan gadon a gefenta. Ta ture laptop ɗin da take kallo, ta janyo wayar da mamaki, dan it’s something da bata saba da shi ba, wai a ƙira wayarta. Tana ta kallon lambobin har ya katse, sai gashi an sake kira. Yana dab da katsewa ta ɗaga, tayi shiru, jin shiru ba’ace komai ba yasa cike da mamaki ta cire wayar a kunnenta ta duba kafin ta mayar kunnenta.
“Hello…” Ta faɗa a hankali ganin bashi da niyyar magana.
“Hey Ni’ima,” ta jiyo muryarsa da nan take ta gane ta. Ita fa ta manta ta bashi lambarta ɗazu, kuma she wasn’t expecting zai ƙira da wuri haka.
“Saɗiq?” Ta tambaya tana murmushi.
“Don’t tell me baki yi saving digit ɗina ba.”
Ɗan dariya tayi amma bata ce komai ba. Shima shiru yayi kafin a hankali yace,
“Just called to check in.”
“Nagode sosai, it means a lot.”
“Mention not, alright good night.., Ni’ima.”
Sai da tayi ɗan jim kafin a hankali tace,
“Good night.”
Kwanakin da suka biyo baya are of their friendship da Saɗiq, sosai ta saba da shi. In some days idan aka tashi daga school zata same shi just outside St. Emery’s yana jiranta to walk her home. Weekends kuma ko da yaushe suna tare, either morning walks ko kuma afternoon at her house. Kullum suna waya kamar wanda ta shekara da saninsa.
Ranar Asabar tana ɗaki kamar ko yaushe, tana zaune a kan sallaya ta idar da sallar Isha’i kenan. Daga inda take zaune tana jiyo suna faɗansu da suka saba. Ajiyar zuciya ta sauƙe, ta miƙe ta zare hijab ɗin jikinta ta linke tare da darduman ta ajiye su ta zauna a kujeran gaban mudubi har sannan tana jinsu. Wayarta ta janyo a hankali, tayi dialing lambarsa. Katsewa yayi ya kirata, ta ɗauka muryarta a sanyaye ta gaishe shi.
“Are u alright?” Ya tambaya, muryarsa da alamun damuwa.
Girgiza masa kai tayi kamar tana gabansa, muryarta na rawa tace,
“Ah, ah.”
“Zan iya zuwa?” Ya tambaya.
“Yes pls,” ta faɗa da sauri, hawaye na sauƙa a idanunta.
“Okay,” kawai ya faɗa kafin ya katse wayar. Kifa kanta tayi a wurin, ta kama kuka.
Ƙarar wayarta ne ya dawo da ita hayyacinta. Ta janyo wayar tana jan hanci ta ɗaga.
“I’m outside.”
Gyaɗa kai tayi kamar yana kallonta ta katse wayar. Sai da ta wanke fuskarta a toilet wanda bai ɓoye kumburin idanunta ba kafin ta fito. A hankali, without making any sound da zai sa a san ta fita, ta sauƙa ƙasa kafin ta buɗe ƙofar a hankali ta fita da sauri. Yana tsaye jikin motarsa, ta hangoshi da rigar sanyi a jikinsa, hannayensa a aljihunsa. Har ta ƙaraso yana kallonta, ta tsaya ɗan nesa kaɗan tana kallonsa.
“U sneaked out didn’t u?” Ya faɗa yana buɗe mata gaban motar. Shiga tayi ta zauna ba tare da ta amsa tambayarsa ba. Ya zagaya ya shigo motar, cikin motar ɗumi sosai, jinginar da kansa yayi da kujera yana kallonta.
“Tell me,” ya faɗa yana kallonta.
“Ni bana son maganar,” ta faɗa tana jan hanci, saboda har lokacin danne kukan kawai take.
“Okay…” ya faɗa yana kallonta.
Juyawa tayi tana kallon window. Jin ya tada motar yasa ta juyo da sauri tana kallonsa. Bai kalleta ba sai driving da ya fara a hankali har suka bar street ɗin. Maida kanta tayi ta cigaba da kallon waje tana sauƙe ajiyar zuciya.
Bata san lokacin da suka ɗauka ba suna shawagi tsakanin layuka silently, babu mai cewa komai. Gyara zamanta tayi tana kallonsa, ganin sai wandering suke tsakanin streets. Katse shirun tayi, tayi clearing throat ɗinta tana kallonsa.
“Kaima ai ɗan Nigeria ne koh?” Ɗan kallonta yayi yana cigaba da driving ɗin ganin ta bar kukan gabaɗaya and she’s ready to talk now.
“Kin taɓa ganin wanda ba ɗan Nigeria ba yana Hausa?”
“Eh mana, ai akwai waɗanda koya kawai sukayi.”
Gyaɗa kai yayi kamar bazai ce komai ba sai kuma yace, “Kina da saƙon da za’a kai miki can ne?”
Dariya tayi tana gyara zamanta ta jinginar da kanta da kujeran tana kallonsa.
“Ai nima zanje during summer.”
“Da gaske?”
“Eh, har Dad ya barni ma, zanje in ga Mamie na.” Ɗan kallonta yayi. Dis is the first time yake sanin bata tare da mamanta, now komai makes sense shiyasa kullum take Sad.
“By then ai ure a big girl, lokacin kun gama high school sai kuma college.” Dariya tayi tana kallonsa.
“Wani gari a Nigeria?”
“Abuja,” ta faɗa tana murmushi.
“Sau biyu kaɗai fa na taɓa zuwa,” ta sake faɗa tana kallonsa.
“Ur Dad is not from Nigeria?”
Ɗan shiru tayi kafin a hankali tace,
“He’s from Nigeria also, amma ya ɗaɗe bai je ba.”
“Okay.” Ya faɗa yana parking a ƙofar gidansu ganin kamar shes now alright kuma dare yana ƙara yi. Wayarsa da tayi ringing sau karo na ba adadi yanzu ya ɗauka yana duba mai kirannasa, silencing wayar yayi ya ajiye ya juyo ya kalleta ganin kallonshi take, yasa yace,
“In kinje kenan yaushe zaki dawo?”
“Just three weeks maybe.” Gyaɗa kai yayi dai dai ana sake kiran wayarsa, ta kalli wayar sannan ta kalleshi. “Ka ɗauka mana” bai ce mata komai ba sai ma silencing kiran da ya sake yi.
Buɗe motar tayi ta fita ta tsaya a dai-dai window tana kallonsa.
“Good night, and tnk u for d ride.”
Yana kallonta har ta shige cikin gidan kafin ya ɗaga kiran da ake sake masa. Shiru yayi yana sauraron abinda ake faɗa.
“Sorry bana kusa da wayarne,” ya faɗa a hankali yana barin layin.
Final exams ɗinsu da ke ƙaratowa sosai ya sa ta mayarda hankalinta kan karatunta. Gabaɗaya tayi busy da karatu, zuwa yanzu sanyi ya fara raguwa, hunturu ya soma wucewa. Wanda a wannan lokacin shirye-shiryen zuwanta Nigeria ya kankama. Immediately after graduation ɗinsu wato walimar gama high school zata wuce Nigeria. Har ji take kamar ta janyo lokacin. Sun rage haɗuwa da Saɗiq sai dai suna waya yana sake kwantar mata da hankali akan exams da zasu fara soon. Shima aiki yasa hes not much available yanzu.
A haka suka fara exams ɗinsu na ƙarshe a matsayin ɗaliban St Emerys.
Ranar da suka rubuta paper ɗinsu na ƙarshe, tana miƙa paper ɗinta ta fito cike da murna. Linda da ta rigata fitowa tana kallonta da dariya tace,
“Ya kika ji Bio ɗinnan?”
“Worst dan Lit, kinsan manta enzyme chart nayi,” ta faɗa tana jingina da bango.
“To ni ƙwaƙwalwata ina ga narkewa tayi.” Ƙyalƙyakewa da dariya suka yi. Linda tana cin sandwich ɗin hannunta tace,
“We will pass, ni kaina ma nake tunani kekam nasan dama ull pass kamar yadda kika saba.” Duk da turanci suke maganganun da accent ɗinsu da bazaka ce ma Na’ima najin wani yare wai Hausa ba.
Ranar graduation ɗinsu sosai suka yi kyau cikin graduation gown ɗinsu. Na’ima ta gyara hular kanta tana ɗaukan enough selfies da zata tura ma Mamienta. Ɗaga kai tayi ta kalli Dad da ke zaune a row na uku cikin iyaye masu yawa da suka zo dan ʼyaʼyansu. Ga Mummy a gefensa tana danna wayarta. Murmushi ya mata ya ɗaga wayarsa yana ɗaukarta daga inda yake zaune. Itama murmushin kawai tayi tana gyara zamanta kusa da Linda. Sunayensu aka yi ta kira ana basu takardar kammala secondary tare da hotuna. Har aka kira sunanta cikin speaker ɗin,
“Na’ima Mustapha.”
Miƙewa tayi walking across the stage cike da nutsuwa da alfahari da kanta. Gurin ya ɗauki tafi kamar yadda aka yi ma sauran ɗalibai. Hannu biyu ta saka ta karɓi takardar shaidar kammala high school ɗinta a St Emerys. Idanunta na cikowa da hawaye ta kalli camera murmushi ɗauke a fuskarta, kafin ta sauƙo ta koma wajen zamanta.
Bayan an gama taro, sosai Linda ta rungumeta tana kuka, mascara da ta saka a idanunta na ɓata mata gefen idanu da hawaye.
“I’ll miss you, da duka stupid stupid poems ɗinki.” Dariya suka yi tare.
Na’ima ta ɗaga hannunta tana kallon Linda,
“Dont worry, I will see you in college, plus I’m going to Nigeria this summer, ill send u lots of poems daga can.”
Haka suka rabu suna kewar juna, suka dawo gida tare da su Dad. A wani gefe na zuciyarta, tana mamakin dalilin da ya hana Saɗiq zuwa, amma sai kawai ta kawar da tunanin ta maida hankali kan shirye-shiryen tafiyarta zuwa Nigeria da zata yi cikin sati mai zuwa.
A gidan ma sun yi murnar kammala makarantarta,duk da ba wai sun yi wani babban biki bane, bata damu ba, domin gabaɗaya hankalinta ya yi Nigeria wajen Maminta, wadda ta cika ta da hotunan graduation ta WhatsApp, ita kuma a ƙarƙashin ko wane hoto bata rasa abin cewa.
Washegari tana zaune a ɗakinta, tana sorting boxes ɗinta da jakunkunan tafiyarta. Duk ta wargaza komai a ɗakin, jakunkunan kyaututtuka da tayi wa Mami, Fauza, har da Aryan duk suna ajiye a gefe. Gyalen da ta ɗaura kamar ɗankwali ta sake gyarawa, ganin yana shirin suncewa, tana ci gaba da shirya kayanta daki-daki, kamar gobe ne tafiyar.
Ƙarar shigowar saƙo ya sa ta ajiye well ironed shirt dake hannunta, ta ƙarasa ta ɗauki wayarta a kan gado.
“Have u started parking already?” Ta ga saƙonsa a allon wayar, tura baki tayi kafin ta buɗe saƙon nasa.
“Ba ruwana da kai,” ta tura masa, tana ƙarasawa ta ci gaba da abinda take yi.
“I’m sorry Ni’ima, bana garinne, shiyasa. You know I would’ve never missed ur grad.”
“Hmm, kana ina?”
“Somewhere.” Ta yi murmushi ta bashi amsa.
Haka suka ci gaba da hira tana aikinta har ta gama tsaf, duk da ta san ba lallai ta gama ɗin ba kenan, domin zuwa ranar tafiyarta ta san zata sake samun abin da zata so ta tafi da shi. A haka har ranar tafiyarta yayi.
Kamar yadda aka tsara, jirgin ƙarfe 7:30 na dare zata bi daga JFK International Airport, New York, zuwa Murtala Muhammad International Airport, Lagos.
Tun ƙarfe 4:30 na yamma suka tafi filin jirgi, har yanzu akwai sanyi da ƙanƙara a garin, tana janye da akwatinta ta nufi check-in counter ɗin. Bayan sun yi sallama da su Dad, hannunta ɗaya riƙe da passport ɗinta da takardar tafiyarta.
“Ke kaɗai zakiyi tafiyar?” agent ɗin ta tambaya da fara’a a fuskarta.
Gyaɗa mata kai tayi.
Matar tayi murmushi, “You’ll be fine.”
Bayan duk wani bincike na tsaro ta samu guri ta zauna a kujerarta dake jikin window a cikin jirgin, tana ajiye journal ɗinta da hoodie ɗinta kusa da ita.
Tafiyar za ta ɗauki kimanin awanni 16 da layover guda ɗaya a Paris na awa ɗaya da rabi kafin a ci gaba da tafiyar; awa 7 ɗin farko zasu tsaya a Paris bayan sun ketare kogin Atlantic, sai kuma awa 6 da minti arba’in daga Paris zuwa Lagos, Nigeria.
Jirgin na tashi, ta jinginar da kanta tana kallon taga, tana kallon birnin New York yana ɓacewa a ƙarƙashin gajimare. Wata ma’aikaciyar jirgi ta kawo mata bargo da headphone, ta karɓa tana kallon matar dake gefenta wacce ke buɗe gum.
Ƙarfe tara aka kawo dinner, pasta ɗin da tasa aka kawo mata ma ba ta wani ci sosai ba, ta zuba ma map ɗin flight ɗin idanunta wanda yake nuna suna nufar tekun Atlantic.
Har tsakiyar dare kafin bacci ya ɗauke ta, ta haɗe gwuiwowinta ta jinginar da kanta a taga.
Ko da ta farka sama yayi jaa, dai-dai lokacin suka sauka a Paris. Sun ɗan huta, tayi amfani da wifi ɗin Airport ɗin ta tura ma su Dad da Mamie saƙo cewa sun sauka lafiya a Paris kafin ta tafi neman abin ci kafin jirginsu ya tashi.
Lokacin da suka iso Lagos ƙarfe 3:40pm agogon Nigeria, bata daɗe a Airport ɗin ba, domin tana da connecting domestic flight daga Lagos zuwa Abuja, wanda yake tafiyar awa ɗaya da rabi daga filin jirgin Murtala Muhammad.
Jirgin ƙarfe 7:00 zata bi zuwa Abuja, a wani café ta zauna cikin filin jirgin tana jiran lokaci.
Ta buɗe ruwan goran hanunta ta kurɓa tana jiran lokaci da tunanin in few hours zata ga Maminta.
Ƙarfe 7:00 dai-dai na dare jirginsu ya tashi daga Lagos zuwa Abuja, ƙarfe 8:35 suka sauka a Abuja. Ta ji jiki sosai, tayi miƙa tana sauka a jirgin cike da zumuɗin ganin Maminta.
Barka da Sallah, Allah ya maimaita mana, to all my amazing readers how body? ???? hope uve recovered from work overload da kuma meat overload????, kallonku nake dai ba wanda ya bani barka da Sallah, kun sha kyau abinku some tsabar kyau even the ram paused to admire ur beauty before becoming stew ????????
To now Sallah is over, so back to reading our story ????????
Welcome back and stay tuned lovelies ❤️❤️❤️
Chapter 6: A place called Home
Tana fitowa daga terminal ɗin wani ɗumi ne ya mamayeta, duk da dare ne amma kamar rana, haske ne darr ko ina a filin jirgin, ta juya ta kalli ko ina, kowa is busy with what hes doing, gyara gyalenta tayi tana bin ko ina da kallo kamar mai neman wani abu.
Sanye da Abaya navy blue color, kanta yane da babban mayafin abayan ta hango Maminta, a tsaye just outside the terminal, Kyakkyawar fuskarta ɗauke da murmushi, duk wani murna da ɗoki da yadda ta tsara yanda zatayi idan taga Mami sai duk suka yi evaporating.
Haɗa idon da sukayi ya sa Na’ima tahowa da sauri sai kuma ta sa gudu, shigewa jikin Mami tayi ta maƙalƙaleta ta fashe da kuka, Mami tasa hannu tana shafa kanta a hankali har sai da tayi shiru kafin ta ɗago ta daga jikinta tana ƙare mata kallo.
“Ke bakya girma ne?” Mami ta faɗa tana share mata hawayen fuskarta
Sake shigewa jikin Mami tayi ba tareda tayi magana sai ajiyar zuciyar kuka da take sauƙewa a jikin Mami.
“Okay zamu kwana anan ne?” Mami ta faɗa tana dariya, haka ya saka Na’ima saketa tana dariyar itama idanunta jiƙe da hawaye.
drivern Mami ne ya taya ta da luggage ɗinta har mota yana mata sannu da hanya, ita kam tana maƙale jikin Mami har suka iso Gidan Mami dake Maitama.
Tunda suka iso Mami ke ta ina zata saka ina zata ajiye da ita, varieties of Nigerian Food babu wanda bata tarar ba, bayan tayi wanka a ɗakinta da Mami ta kaita a sama ta shirya ta sauƙo tana jin wani farinciki marar misaltuwa despite the jetlag, sai da suka ci abinci tare da Mami da ta tabbatar ta ɗanɗana duk abinda aka girka dominta, sannan suka dawo babban palour ɗin gidan suka zauna, abinda Na’ima ta manta ne kaɗai bata faɗa ma Mami ba, duk da matuƙar gajiyar dake tattare da ita, amma kewan Mami overcomed it, ita dai binta kawai take da kallo tana murmishi.
Na’ima ta ɗago kanta daga fruit ɗin da take sha tana kallon Mami tace
“Mami banga Big Daddy ba”
“Sai yanzu zaki tambayeshi?” Mami ta faɗa tana harararta
Dariya tayi kamar ba ita ba tana zare fork ɗin da ta kai kankana bakinta
Mami tace ” yayi tafiya but he’ll be returning tomorrow insha Allah”
“Allah ya kaimu” ta faɗa tana ajiye bowl ɗin kan center table, hamma tayi da miƙa da yasa Mami ta kalleta
“Ure tired, u should rest” gyaɗa ma Mami kai tayi dan tana buƙatar hutun.
Har ɗakinta Mami ta rakata sai da ta wanke bakinta ta dawo sannan ta zo ta haura gadon tana kallon Mami dake zaune gefen gadon, Mami ta gyara mata duvet tana faɗin
“Fauza da aryan sai dai su ganki da safe kamar daga sama they’ll be so suprised”
Tana gyara kwanciyarta a kan lallausan zanin gadon tace
“wallahi kuwa, finally the’ll get to see me ido da ido not on video calls”
Kashe mata wuta Mami tayi bayan ta sata tayi Addu’a, ta ja mata ƙofarta.
Sai da ta fara duba twins ɗinta da sun jima da bacci a ɗakinsu, kafin ta wuce ɗakinta tana dialing number Big Daddy ganin missed calls ɗinsa da bata lura da su ba tun ɗazu.
Washegari ko da Mami ta zo tashinta da asuba ta tarar har ta tashi tana banɗaki, haka yasa ta koma ɗakinta dan yin sallah.
Tana zaune akan sallaya Na’iman tayi sallama a hankali ta shigo ɗakinnata da hijab a jikinta da tayi sallah, ta zauna saman kujera tana lumshe idanunta, Mami dake azkar a hankali ta kalleta, azkar ɗin itama ta fara yi tana lumshe idanunta har suka gama kafin ta taso ta kwanta akan daddumar Mamin ta kwantar da kanta a ƙafafunta
” Good Morning Ma,” shafa kanta tayi
“Morning sweetheart ya kika tashi?”
“Lfy Mami” ta faɗa tana lumshe idanunta, ganin bacci ne ya fara ƙoƙarin ɗaukanta a haka yasa Mami na cigaba da shafa kanta tace
“Na’ima tashi ki hau kan gado ki kwanta”
buɗe idanunta tayi kafin ta miƙe a hankali, zare hijab ɗin tayi ta haura gadon Mami ta kwanta, Mami ta bita da kallo tana jan chazbah ɗin hannunta, nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.
Ƙarfe 11:00 dai-dai na safe ta buɗe idanunta a hankali tana kallon 2 cute twins da ke kan gadon dabb da ita suna kallonta, Namijin da yafi wayo ya kalli twin sister ɗinsa dake kallon Na’iman kafin ya faɗa kan Na’iman kaman dama jira yake ta buɗe ido, ganin haka itama macen ta faɗa kansu suna ƙyalƙyala dariya,
“Wayyo, Aryan..,Fauza.., do u guys want to break my arm, baku ga kuna da nauyi ba”
Ta faɗa tana miƙewa zaune da su a jikinta
“Anty Na’ima from the video call” Aryan ya faɗa yana taɓa hancinta, dariya tayi itama ta taɓa nashi hancin “Aryan from the video call” itama ta faɗa tana kwaikwayonsa.
Ƙyalƙyakewa sukayi da dariya, ta dinga kallonsu ganin yadda ma suka fi girma a zahiri akan yadda take ganinsu on video calls, they look like sun fi 4 years ɗin ma da suke, alhalin ko 4 ɗinma basu ƙarasa cikawa ba, the last time da ta gansu they were 2.
Ganin Mami bata ɗakin yasa tace musu “ina Mami?” Ƙofa suka nuna mata a tare, tayi murmushi tana sauƙa a gadon
“To kuzo ku rakani in yi wanka sai muje wajenta”
Tana riƙe da hannun kowannensu har ɗakinta, zaunar da su akan gadonta tayi, ta kunna musu cocomelon a wayarta ta basu ta wuce toilet dan yin wanka, shes not yet done da unpacking saboda gajiyar da tayi jiya, da mamaki take kallon kayanta that are unpacked and well arranged a inda kowanne ya kamata ya zauna tayi murmushi ta ƙarasa ta shirya cikin jeans da t-shirt light blue, ta ɗaura hula a kanta kafin ta ƙarasa ta karɓe wayarta da suka nutsu suka bawa dukka hankalinsu.
Ganin zasu mata kuka ta ɗaga Fauza tana riƙe da hannun Aryan bayan ta soke wayar a aljihun wandonta, tace ” Muje Mami”
A kitchen suka tarar da ita da masu aikinta, tana shiryawa big daddy abinci.
Mami ta kallesu duka “kin tashi?kar dai su suka tashe ki?
Tana dariya ta ƙaraso tana sauƙe fauza a kan kujera a kitcen ɗin, suka gaisa da sabira kafin ta ƙaraso tayi hugging Mami kaɗan sannnan ta sake ta
“Me zan taya ki?” Ta faɗa tana ɗaukan crispy spring rolls da Mami ke soyawa ta kai bakinta.
Miƙa mata matsamin Mami tayi tana murmushi “zo to ki ƙarasa soya wannan bari inji ko big Daddy sun iso?”
Karɓa tayi ta cigaba, Mami ta dubi sabira dake wanke wanke tace
“Sabira in kin gama wanke-wanken ki taya ta ku shirya dining ɗin ill be right back”
daga haka ta fita a kitchen ɗin su Aryan suna biye da ita.
Sai da ta ƙarasa aikin da dama Mami ta kusa gamawa kafin ta shirya dining ɗin tsaf ta bar sabira da gyaran kitchen, ta wuce sama, a palourn sama ta iske Mami da su Aryan ta ƙaraso tana tura baki
“Har kin gama?”
“Eh” ta amsa tana ɗauko wayarta, message ɗin daddy tayi replying kafin ta kalli Mami dake kallonta.
“Ke baki da atampa a kayanki ne?”
“Ko ɗaya” ta faɗa tana dariya
Itama Mami dariya tayi kafin ta miƙe tana kallonta
“muje ki shirya, big Daddy na hanya dan har Musa ya ɗaukosa ma a Airport, he’s eager to meet his princess”
“To ba gashi na shirya ba ”
Mami ta harareta tana wucewa ɗakinta ba tare da tace mata komai ba
Miƙewa tayi tabi bayan Mami, akwati Mami ta janyo ta ajiye a kan gado ta buɗe tana kallon ciki, duka kayayyakin Na’iman ne da ta ɗinka mata, ta zaro wani less ɗinkin riga da skirt black colour ta ajiye mata da gyalenshi da takalmi
“Yi sauri ki shirya ban son shirme” Mami ta faɗa tana mayar da akwatin ta rufe.
Ɗaukan kayan tayi tana kallo, murmushi kwance a fuskarta, Mami ta juya ta fita ta koma falo, warware kayan tayi ta fara sakawa.
Ciff kayan ya mata kamar dai Mami ta gwada ta, ta tsaya tana kallon kanta a madubi riƙe da ɗankwalin da ta kasa ɗaurawa, juyawa tayi da niyyar fita sai ga Mami ta shigo, Mami ta ƙaraso tana kallon yadda kayan ya mata kyau sosai a ƙaramin jikinta.
Tana riƙe da ɗankwalin ta marairaice tana kallon Mami
“What do i even do with dis?”
Hararanta Mami tayi, ta ƙaraso ta karɓi ɗankwalin sannan ta zaunar da ita a kan dresser tana kallon coiled gashinta da ta kame shi, kwalli ta fara saka mata a idanunta wanda da ƙyar ma aka saka kwallin saboda yadda take ƙyafta idanunta, kafin ta ɗaura mata ɗankwalin ta buɗe drawer ta ɗauko simple gold ɗankunne ta saka mata harda siririn necklace.
Ta kalleta ta cikin madubin
“To ko ke fa?”



