⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 33: Chapter 33

“Ka gwada haɗa su ɗin Ahmad for peace to reign, idan akwai matsala sai ka raba su kaga bata ga kamar ita bata da muhimmanci ba ko wani abin, in the first place ba’a kyauta mata ba a barta taji da kishiyar da aka mata ba sai an ƙara mata da wani tension ɗin ba kaji” furzar da iska yayi a hankali daga bakinsa kafin yace

“Shikenan in sha Allah hakan za’a yi”

“Yauwa, jibi ai zasu zo jere koh?” Ya gyaɗa mata kai a hankali

“To sabon part za’a buɗe mata kenan” sake gyaɗa mata kai kawai yayi, kafin yace “za’a gyara sabon part ɗin gobe kafin jibin”
“to Allah ya maka albarka, ya sa hakan shine alkhairi” ƙasa ƙasa ya amsa da “Amin” miƙewa yayi ya ɗan leƙa fuskar Saif dake bacci a gadon Ammi ta bisu da kallo kafin tace

“kuka ya gama sha yayi bacci, rigimarsa ce yau kuma ta tashi ya dinga rashin mutumci”

Murmushi kawai yayi ya miƙe yana nufar ƙofa yace “Sai da Safe Ammi”

“Allah ya bamu alkhairi.”

“Masha Allah Amira, yanzu kika fara irin hankalin da nake so kiyi, yanzu ya ake ciki?”

“Mummy yau tun sassafe naga an buɗe other side ɗin ana renovating, kinga kenan ta masa maganar kuma yayi considering though ni bai ce min komai a kai ba”

“Rabu da shi ya ji da shi, yanzu dai kin tabbatar gidan za’a kawo ta ina?”

Miƙewa tayi daga saman gadonta ta ƙarasa jikin window ɗin ɗakinta na glass tana kallon other part na gidan da ake aikin renovating, shima part ɗin ƙato nw amma bai kai main nata da take ciki girma ba, shima sama da ƙasa ne lafiyayye

“Wallahi mummy nan za’a kawota yanzu haka ina kallonsu ma daga nan ana aiki, kinsan wai gobe za’a kawo kayanta!”

“Hmm okay, duk yadda nace miki kiyi Amira haka zakiyi, kinji yadda mukayi da malam ina?” Amira ta gyaɗa kai,

“to dan Allah kar kiyi mistake, Allah ya kawota” Amira tace “Amin” tana komawa ta zauna a saman bed, basu jima sosai ba suka gama wayar, mummy na kashewa ta kira Nuwaira, suna cikin magana da Nuwaira ya buɗe ƙofar ɗakinnata, kallon ƙofa tayi kafin ta ɗauke kanta ta kwanta a saman bed tana faɗin “will call u back babe ina zuwa” nuwaira tace “alright call soon” kallonshi ta dinga yi ta ƙasan idanunta ganin yana tsaye bakin ƙofa, sai kuma ta ga ya ja mata ƙofar ba tare da ya shigo ba ta miƙe zaune a kan gadon dan tun jiya bata leƙa ko wajen ɗakinta ba, tuno abinda Mummy tace mata ya sa ta haɗe rai ta sauƙa daga kan gadon ta nufi ƙofa dan jin dalilin shigowar tasa.

Yau ranar kamu, compound ɗin gidan ya sa decorations , strings na fairy lights ko ina, traditional drummers na ta fama, ga aunties da cousins, yan uwa da abokan arziƙi mata zallah sai rawa ake ana dariya, ciki kuwa har da su Rahama da Yasmeen da 2 of their other cousins da wasu daga yan uwa da suka taho daga lagos a jiya! Sun sha kyau sun gaji.

Na’ima na zaune akan wani low cushion seat, anyi drapping ɗinta da wani royal purple traditional kamu gown da aka ma golden embroidery cas da jikinta kamar amarya wanda ya haska ta ba ɗan kaɗan ba, an mata head mai shegen kyau da ya zauna a kanta ɗas, da manyan beads ɗinsa da ke wuyanta da hannunta, an mata kwalliya a heavy one ta fito a Amaryarta da yake event ɗin babu maza, tun da suka yi shoot da ita da shi na kamu before event ɗin ya fara shi da su Nasir suka ƙara gaba, Murmushi kawai take a hankali tana kallon yadda kowa ke nishaɗi cause of her amma ɗayan side na zuciyarta tsoro ne cike fal, more especially tunda Ahmad ya faɗa mata theyrr staying same house da Amira, ko da aka faɗawa su Mami ma basu wani ja ba aka je aka mata jerenta lafiyayye a part ɗinta da aka mugun gyara shi yayi shegen kyau kowa sai masha Allah kawai yake, Yusrah ƙanwar Fadila da ke cikin bridesmaid ɗinta dake zagaye da ita tana riƙe da ƙaramin fan for the bride kamar yadda Fadila tayi instructing ɗinta.

Top Abuja wedding media house su ke covering bikin daki daki, flashes everywhere hotuna ga videographers kala kala, drones na yawo yana capturing moments ɗin da kowa ke farinciki, ana rawa da waƙoƙi, a duk sanda sukayi zooming kyakkyawar fuskar Amarya its always a master peace dan yadda murmushinta da ke cike da kunya ke matuƙar kyau a hotuna da cinematic videos ɗin bikin kamar yadda shoot ɗinsu da Ahmad ya matuƙar ɗaukar hankali wajen yinsa dan ba ɗan ƙaramin kyau suka yi ba har ka gagara gane wanda ya fi wani kyau, social media kaf ya ɗauka from instagram to tiktok da sauran kafafen sada zumunta #hashtag AN2025, kowa ka kalla ba baya bane a dressing mai sunan dressing a wajen masu matuƙar tsada, make up ɗinsu mai matuƙar kyau masha Allah.

Duk wanda yake so sai dai ya je ya tsaya gaban babban wall da aka yi ma kyakkyawan decoration na flowers wanda instantly photographers zasu fara ɗaukarka hoto a wajen, ga banner da aka saka #Goldenunion#kamudeAN2025 wanda kowa ke so ya fito a cikin pics ɗin.

Yasmeen da Rahama sunyi pictures yafi thousand dan sosai suke enjoying bikin, pictures ɗin Na’ima kuwa sun tura ma Ahmad babu adadi, sosai dangin ango suka zuba bajinta wajen kamu suka zuba capacity iya capacity wajen fansar amaryarsu mai tsada.

Wajen negotiotions kowa dariya kawai yake saboda yadda aka dinga raha da nishaɗi yet very classy, the kamu sets Abuja agog, culture plus class, haka taro ya tashi Masha Allah sai son barka.

Washegari cousins and friends ɗinta suka shirya mata suprise bridal shower da bata san da shi ba a wani rooftop na wani lounge a Abuja da taimakon fadila, sosai shima ya ƙayatar kamar irin something out of pinterest ɗinnan, pink, da fari da rose gold ballons suna floating a sama wanda rubutun jiki ke glowing AN2025, wasu kuma Mrs Ahmad in capital letters, har sai da tayi hawaye, mayan event planners ne suka shirya musu shi suka yi styling komai gwanin sha’awa, ga wani three tier cake mai matuƙar kyau da initials ɗin ita da Ahmad a jiki su Yasmeen yau ma banda hotuna da videos babu abinda suka ishi Ahamd da shi ta whatsapp wanda suna turawa yake buɗewa ya kalla, tuni social media ta sake ɗaukar second event na bikin which is also a banger. #BridalblissAN2025

Washegarin Ranar aka yi Henna Night, setting ɗin ranan moroccon inspired setting ne, low couches, ga candles masu ƙamshi, da silk drapes all over, ga tray na sweets da dabino da danginsu, banda ƙamshi babu abinda ke tashi ta ko ina.

Na’ima da ta sha ado da jewelleries ta sha lalle haɗaɗɗen da wata ƙwararriyar mai lalle ta zo ta mata, ƙawaye na zagaye da ita ga masu lalle kaca kaca wadanda basu yi lalle ba nata yi, haka aka sake locking down social media da wannan event ɗin n ranar shima wanda a duk sanda Na’ima ta shirya for each event sai Mami tayi hawaye saboda irin kyau da take zubawa da haiba, tabarakallah masha Allah.

A daren ranar da za’a kaita Fahad ya zo har gidan ya bata kyautar diamond bracelate mai kyau da addu’ar zaman lafiya tare da kwanciyar hankali a aurenta da sabuwar rayuwar da zata shiga.

Washegari aka ɗauko Na’ima daga Abuja zuwa Lagos gidan mijinta Ahmad, after much koke koke da emotional moments tsakaninta da Ammi da su big Daddy kafin a nufi Airport dan tahowa lagos, this time not as a student, ba kuma a gidan fadila zata koma ba, but as a bride na Ahmad kuma wanda za’a kaita gidansa. sauƙarsu a Murtala muhammad Airport tuni ana jiransu da motoci jeri jeri, paparazzi da social media bloggers tuni sun gama watsa komai Na’ima cikin lafaya fara tass fuskarta a lulluɓe tuni ya baje ko ina, sai da aka fara kaita wajen Daddynta da ya saka mata albarka sosai, itama Mummy Salma ba’a barta a baya ba wajen tofa albarkacin bakinta kafin a ɗauki Na’ima straight to gidan Ammi, inda daga nan za’a yi dinner from there a miƙata gidanta kowa ya kama gabansa.

A duk cikin events ɗin da akayi the best of all shine dinner da ya tashi lagos da yayan cikinta, dan bikin was grand grand, classy dinner akayi na gani na faɗa a lagos with costomised invitations na A&N Lagos Soiree da a kayi delivering ɗinsu har gida for invited guests, sovieniers, kaca kaca ga security sosai.

Ahmad perfectly dressed in black tuxedo, da satin lapel, shirt ɗin cikin crisp white, bow tie ɗin wuyansa yayi knotting ɗinsa da kyau, looking regal, wanda presence ɗinsa kawai commands attension, amma har sannnan heart ɗinshi is restless, rabonshi da ganin Na’ima tun ranan kamu wanda tunda aka fara bikin shine ganinsa da farko da ita, rananr da ƙyar yayi bacci, and yanzu he cant help tunanin son ganinta a yau dressed for dinner ɗinsu, yana zaune a bayan mota waiting for fitowarta dan a mota ɗaya zasu tafi wajen event ɗin shi da ita, ko da ta fito haka kawai a jikinsa yaji presence ɗinta wanda hakan ya sa ya ɗaga kansa ya kalli window and thats how he froze, tana sanye cikin wani designer flowing gown champagne colour mai masifaffen kyau, wanda ya fito da natural innocence da kuma kyawunta a sarari, fuskarta ɗauke da kwalliya mai matuƙar kyau da ya bayyana kyawunta, ya lumshe idanunsa a hankali yana jin race na zuciyarsa kafin ya buɗe motar a hankali ya sauƙo, hankali duka friends da su yasmeen da suka yi kane kane a cikin ƙawayenta ya dawo kansa, fuskarsa a sake yake kallonta bayan ta ja ta tsaya da friends ɗinta a compound ɗin, ya tako a hankali with each of his step har ƙasan ranta take ji, tuni ƙawaye suna fara snaps ana awwning, ya ƙaraso har gabanta ya tsaya, ita kam kunya duk ya isheta, hannunsa ya miƙa mata, ta ɗan kalli friends ɗinta da ke ta washe baki kafin ta saka hannunta a cikin nasa, ai bridesmaids ɗinta banda awwning babu abinda suke yi, this is the second time yake taɓata after aurensu and it just felt as if duniyar revolves around su biyu kaɗai, da kanshi ya buɗe mata back seat ta shiga driver ya zaga ya buɗe masa shima ya shiga baya kafin shima ya shiga ya tada motar, convoy na su Nasir da bridesmaid suka jera zuwa wajen event ɗin.

Yadda ta zauna a gefe hannunta da ya sha lalle akan ƙafafunta yasa ya lalubo hannunnata ya riƙe a hannunsa, words sunyi failing ɗinshi dan ya kasa furta mata ko kalma ɗaya bayan amsa gaisuwarta, dukansu are lost a duniyar su.

Ko da suka iso wajen already su ƙaɗai ake jira hakan yasa entrance ɗinsu friends ɗinsa da kuma su Yusrah wato bridesmaid ya zama farko before nasu wanda yasa kowa narkewa cikin moment ɗin, masu video sai fama suke, tuni aka sake musu waƙar perfect na eid sheeran har suka zauna a mazauninsu, cause indeed theyre perfect for each other.

Sosai dinner yayi armashi Su yasmeen sunsha rawa har sai da suka gaji, wanda daga Ahmad har Na’ima babu wanda ya yarda yayi rawa a cikinsu dole aka rabu da ango da Amarya, har lokacin ya gagara saina satar kallonta, can yayi ƙasa da muryarsa ya raɗa mata a kunne “Baby pls ure too beautiful my God, lets just leave here and go home i need help” murmushi kawai tayi itakam kunya duk ta isheta, su dai audience sunga ango da amarya na ƙus ƙus abinsu, wedding cake ma da ya bata a baki da ƙyar ta amsa kafin itama ta daure ta basa.

Ko kafin a tashi biki ta riga ta bala’in gajiya kamr zata yi kuka, a can aka baro su yasmeen da sauran friends suna after party, gidan Ammi aka sake dawowa da ita wanda washegari za’a miƙa ta gidanta sai fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri’a ɗayyaba.

Tsabar gajiyar da tayi tun da suka baro wajen dinner kafin su iso gida tayi bacci, ta kwantar da kanta a jikin kujera ta lumshe idanunta, ganin baccinta take yi peacefully abinta ya ajiye waya ya zuba mata idanu kamar ya sami tv, she looks cute and innocent ko a cikin baccinta, ya jingina kansa da kujerar shima yana kallonta har sannan hannunta ɗaya na cikin nasa, bai yi ƙoƙarin tashinta ba dan da so samu ne from here su wuce gidansu straight but its not possible, ji yake kamar goben ma yayi nisa a kai masa ita.

Motar na tsayawa cikin harabar gidan Ammi followed by motar sauran friends ɗinta da basu tsaya for after party ɗin ba driver ɗin ya buɗe ya sauƙa a motar ya barsu su kaɗai, sai a lokacin ya kai ɗaya hannunsa thats free ya shafi gefen fuskarta, ta ɗan yamutsa fuska tana shirin gyara kwanciya, hannunsa ya ɗaura a fuskarta yana shafa kumatunta da thump ɗinsa a hankali hakan ya sa ta ɗan buɗe idanunta dake cike da bacci tana kallonsa

“Hey beautiful” ya faɗa ƙasa ƙasa, murmushi kawai ta masa tana ƙoƙarin sake lumshe idanunta, ya ɗanyi murmushi shima yana kallonta yace

“Ko mu tafi gidanmu kawai? Uhmm?” Sai a lokacin ta buɗe idanunta da kyau, ta dinga kallonsa kafin ta kalli inda suke ganin mota ce, ta juya ta kalli window ta ga ashe har sun iso gida, ta tashi zaune da sauri, ɗan dariya kaɗan yayi yana kallonta, itama kallonsa tayi kafin a hankali muryarta haryanxu da bacci tace

“Bansan mun iso ba, Goodnight!” Ta faɗa tana zare hannunta daga nasa ta kai hannun da niyyar buɗe ƙofar motar, Hannunta da ta kai ƙofar ya riƙo da sauri ta juyo tana kallonsa a shagwaɓe

“Not yet mana, not so fast saurin me kike?”

“Jira na fa suke mu shiga ciki” ta faɗa tana kallon friends ɗinta da ke wajen.

Matsowa kusa da ita yayi, voice ɗinsa na dropping, edge of hunger da ke cikin voice ɗinsa ya na saka heart ɗinta racing

“Let them wait! Nima ive been waiting ai” ya faɗa yana saka yatsu biyu gefen fuskarta ya shafa a hankali. The touch was enough ya sa ta lumshe idanunta, ganin yadda ta lumshe idanunta ya sa ya ɗaura lips ɗinsa a goshinta ya sumbata , Saurin buɗe idanunta tayi, ya janye bakinsa yana kallonta, idanunsa dark with desire, da hakan yasa ta ji she needs to leave motarnan yanzunnan.

Ya ɗaura hannunsa akan seat ɗin yana ɗan tapping a hankali, ganin abinda ya keyi ta kalleshi tace

“zan iya tafiya yanzu toh?” Kallonta yayi, ganin yadda idanunsa har sun ɗan canza ya sa ta ɗauke kanta a hankali, wani kallo yake mata da ya sa duk jikinta yin la’asar, ya sa hannunsa ya zagayo waist ɗinta ya janyota jikinsa sosai, a tsorace yanzu kam take kallonsa yana kallon cikin idanunta da tuni baccin ciki ya kama gabansa yace
“damn tradition lets just go home..cause this is torture!” Ita kam kallonsa kawai take dan wallahi bata gane inda ya dosa ba, amma duk da haka sai ta girgiza masa kai tana ƙoƙarin fita a jikinsa hannunsa ya saka ya ɗago fuskarta forcing her to look into his eyes, intensity ɗin da take gani a cikin idanunsa ya sa bata san sanda ta furta

“Ahmad..” da muryarta da ta kusa maƙalewa ma, ya lumshe idanunsa ya buɗe kafin ya jingina kansa da kujera har sannan tana jikinsa yana kallonta yace

“Say my name just like that!” Ya faɗa da wani lazy smile a kwance fuskrsa, dat looked dangerous to her.

Ganin yadda take ta kallonsa yace “ke kefa matata ce, do u know me hakan yake nufi?”

Ganin ta gagara amsawa ya miƙe zaune da ita a jikinsa

“It means any chance da na samu, i intend to remind u that ure my wife, and i’m ur husband, get used to it baby!” Yana gama faɗin haka before ta gama processing maganar ya ɗaura bakinsa a nata, the kiss was slow at first, he was gentle da ya sa ta lumshe idanunta bata san sanda ta sa hannu ta riƙe rigarsa ba tana gasping breath, hakan da tayi ya sa yayi loosing little self control da yake da shi yayi deepening kiss ɗin, hungrily ya koma kissing ɗinta da har ya sa sosai jikinta ke rawa, ya kai hannunsa bayan wuyanta holding her in place, tasting every bit of her mouth, gabaɗaya duk wani duniya outside nasu yayi dissappearing, numfashinta taji yana hitching ta sake riƙe rigarsa da ƙarfi hawayen da ya cika idanunta ya gangaro, duk yadda tayi ƙoƙarin pulling back he follows, yadda yake kissing ɗinta hungry yet tender all at once, riƙe head ɗinta yayi da hannu ɗaya, ɗayan hannun ya fara lalube jikinta sai a lokacin ta yi ƙarfin halin fizge jikinta daga nasa, da yake he was reluctant da abinda yake hakan ya sa har ta iya janye jikinta, wani irin ajiyar zuciya ya sauƙe a jere ya furta “ya Allah” can ƙasan maƙoshinsa kafin ya mayar da kansa jikin kujera ya runtse idanunsa, itama ajiyar zuciyar kawai take sauƙewa cause she’s breathless banda wani irin bugawa babu abinda zuciyarta keyi, ta ɗauke idanunta daga kansa tana kallon waje ganin ba kowa alamun duk sun shige sun barta ita kaɗai, bata san sanda ya taso daga jikin kujerar ba jinsa kawai tayi a jikinta ya ɗaura fuskarsa a gefen face ɗinta yana goga face ɗinnasa a nata a hankali yace a cikin kunnenta

“Idan kika ƙara 1 minute a nan, u arent going in i promise u, i wont let u, gida kawai zamu tafi damn the tradition”

“Ni ka bar cewa haka bana so”

“Why not?” Ya faɗa yana kissing curve na jaw ɗinta,
“I’m ur husband, i can say whatever”

“Dan Allah ka bari” ta faɗa muryarta ƙasa ƙasa

“Hmmm” kawai yace yana janyewa ya zauna da kyau, ya ɗan shafa kansa yayi murmushi yana kallon yadda ta daburce yace

“To jeki sai da safe” kallonshi tayi tace “ni bazan iya shiga ni kaɗai ba kuma sun tafi sun barni”
“Eh su ma sunsan ur husband needs u ne shiyasa suka tafi abinsu” ta ɓata rai tana kallon ƙafafunta,

“u know what, i love it when ure shy like dis, but dan Allah kar ki taho da shi gobe to my house” ɗauke kanta tayi tana hana kanta murmushi, ya lalubo wayarsa ya danna kiran Yasmeen, tana ɗagawa jin kiɗan wajen yasa yace

“a can zaku kwana ne?” Fita tayi daga wajen tana faɗin

“yanzu zamu dawo yaya”,

“20minutes! I’m waiting for u a gida” daga haka ya katse wayar ya mayar da kansa ya jinginar yana tunanin yadda gobensu zai kasance dan baya tunani akwai wani abu mai kama da ɗaga ƙafa a dictionary ɗinsa na gobe. Ita dai sai wasa kawai take da yatsunta dake kan gown ɗin jikinta, kusan 25 minutes sai ga su, suna isowa ganin motarsa a conpound suka zo suka ƙwanƙwasa, sai a lokacin ya kalleta itama kallonshi tayi kafin tace “Goodnight” ya lumshe mata idanunsa ya buɗe ƙasa ƙasa yace “Night beautiful” ta buɗe motar a hankali ta sauƙa, Yasmeen da Rahama suka kalli juna ganin wai ashe har yanzu amarya bata shiga gida ba, ba su dai ce komai ba, yasmeen ta zaga side ɗinsa ta ƙwanƙwasa ya sauƙe glass ɗin yana kallonta yace

“Uhmm?” Washe masa baki tayi tace

“yaya ango”

“Take her in, kun bar min mata a tsaye” bata san sanda tayi dariya ba tana kallon rahama da ke tsaye tare da Ita ta ɗaya side ɗin, tace

“oshey yaya, yanzu zamu shiga da ita in sha Allah” sai kuma ta ɗan sunkuya tayi ƙasa da murya tace

“yaya wallahi ur wife is so beautiful, tun a Abuja nake kallonta, ga wani accent mai shegen daɗi har son tana magana nake” murmushi ya mata yace

“Toh sai da safe” ta ɗan miƙe tsaye ganin ba biye mata zaiyi ba tace

“sai da safe” , ya gyaɗa mata kai daga haka ta zaga inda Rahama ke jiranta suka wuce cikin gidan da ita, binsu yayi da kallo kawai har suka shige ciki ya daina ganinsu kafin ya sauƙa a motar ya koma drivers seat dan a jiki driver ya bar key ɗin, he needs to go home now dan dare yayi sosai duk da ya san shi da bacci yau sai wani ikon Allahn.

Ringing ɗin wayarta shi ya tashe ta daga baccin da take yi, ta miƙe zaune tana jin kanta na sara mata dan kwanan nan kwata kwata damuwar sadiq baya barinta samun baccin kirki, cikin duhun ɗakin ta lalubo wayarta ganin Number ne ke kiranta ta ɗauka ta kai kunne tayi sallama, shirun da taji ba amsa ya sa ta sauƙe ajiyar zuciya dan she’s been expecting kiransa dama tuntuni.

Muryarsa taji da ke cracking, kamar kuka yake yace “Mama!” Ta sake sauƙe ajiyar zuciya idanunta na cikowa fa hawaye tace

“Sadiq, Sadiq ɗina, how’re u my boy?”

Ƙoƙarin magana yake amma ya gagara, tana iya juyo ajiyar zuciyar da yake sauƙewa a jere a jere alamun kuka yake yi, sosai zuciyarta ke mata wani irin zafi jin kukannasa, gagara daurewa yayi ya fashe mata da wani irin kuka jikinsa har rawa yake, ya matse wayar a kunnensa yana kuka sosai.

Rufe idanunta tayi ta buɗe tana karanto masa addu’o’i a zuciyarta kafin softly tace “Sadiq…Sadiq stop crying dan Allah kana ɗaga min hankali, calm down and listen to me kana ji na?” Daga kwance da yake a ƙasan carpet ɗin wani ɗaki ya haɗe kansa da ƙafafunsa ya gyaɗa mata kai a hankali yana cigaba da sauƙe ajiyar zuciya

“Let her go kaji, haka Allah ya ƙaddara sadiq ba rabonka bace, she was never meant for u, holding on will only destroy u kaji Sadiq”

“Nooo!” Ya faɗa da ƙarfi jikinsa na ɗaukar rawa kamar yadda muryarsa ke rawa sosai,

“Mama zan mutu ne idan na barta Mama, u dont understand do u? I cant breath without her Mama, she is my everything, mama everything. Mama bikinsu is all over social media me yasa zata min haka mama, bata san irin son da nake mata bane?Bai kai ni sonta ba kinji na rantse miki Mama, wallahi bai kai ni sonta ba” ya faɗa wasu waves na tears ɗin n wanke fuskarsa.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved