Chapter 39: Chapter 39
“Ni gaskiya Sadiq ɗinnan abinsa ya fara wuce gona da iri haukar tasa ma ai ba ta masu hankali bace, ta ya za’a yi ya cikaba da bibiyarki bayan ya san da aurenki ya dinga causing problem tsakaninki da mijinki a banza da hofi, ke kuma kamar wata wawuya fisabilillahi bayan kin san kin masa laifi u picked side ɗin ex ɗinki bayan duk abinda yayi its because of u yayi shi sannan ki dawo instead of u ki neme sa ki basa haƙuri shine kika je kika wani kwanta Na’ima?”
“Ai na je yanzu na basa haƙurin na samu baya nan”
Fadila da haushi duk ya cikata tace “to wallahi kar ki kuskura ki bari ya kwana yana fushi da ke, kar ki mayar da kanki wawuya kishiya ce da ke da take neman slight opportunity da zata ganku a rana dan ni har message ta min dogo ta zage ni tas tas akan ni ce munafuka da na haɗaki da mijinta ni dai ban kulata ba dan bani da lokacinta saboda haka kar ki sake ki bari ta san kun samu issue da mijinki after just 1 week da aurenku kina jina?” Gyaɗa kai tayi a hankali tace
“Eh”
“Yanzu yaushe zai koma ɗakin Amira”
“Yau” ta faɗa tana jan hanci,
“Kash! Ba dai komai ki samu ki basa haƙuri kafin ya koma can kar ya tafi can da fushinki dan Allah”
“Toh” ta faɗa a hankali
“Kuma ki bar kuka haka kar kanki yayi ciwo, this is officially ur first fight” ta faɗa tana ɗan dariya so that Na’imar ma zata ɗan sake ranta, Na’ima tayi ƙarfin halin ɗan yin murmushi tace
“Amma anty fadila fa yayi fushi sosai”
“Ke haka yake fa, Babe ya sha faɗa min wallahi cewa iya da zuciya sosai guy ɗin, ke baki ga Nasir kaɗai yake shiri da shi ba? Baya cika shiga harkar friends ɗinsu ma saboda abu kaɗan ke provoking ɗinsa to bare kuma ke da yake so da ya ɗauki matter ɗinki for head, shima Babe ɗin sun san halin juna ne kawai da shi, to shima sai su kwana biyu basa wani magana zuwanki gidana ne fa ya zozzo gidan namu amma baya zuwa wallahi, shiyasa da ya nuna interest ɗinsa a kanki nayi mamaki sosai ba kaɗan ba wallahi”
“Hmmm” kawai Na’ima ta iya cewa dan kuwa yanzu ai ta sake sanin halinsa, ashe shima yana da baƙin hali, sun jima suna waya da fadila tana kwantar mata da hankali kafin suyi sallama, sosai kuma taji hankalinta ya ɗan kwanta.
Har tayi isha’i bai shigo gidan ba, zuwa yanzu kam hankalinta ya soma tashi, sai a lokacin ta lura babu laptop ɗinsa dake ɗakinta da other stuffs ɗinsa, mamaki ya kusa kasheta does that means ba zai mata sallama ba shikenan ya koma part ɗin matarsa? Ai kamar hakan ya dawo mata da sabon kuka, ta tafi jikin window ɗinta ta tsaya tana kallon part ɗin Amira kafin ta koma gefen bed ta zauna a hankali. Ko yunwa kwata kwata bata ji ba bare ta nema ma kanta abinci, haka ta kwanta abinta, amma sam bacci yaƙi ya sace ta, har wajen ƙarfe 2 tana juye juye kafin da ƙyar bacci ya ɗauke ta around 2:30, shima kiran sallar farko ta buɗe idanunta da har sun mata nauyi, tana buɗe idanunta shine ya fara zuwa ranta dan dama da shi ta kwanta a ranta, ta sauƙa a gadon a hankali ta wuce toilet tayi fitsari ta fito sai ta gagara komawa ta kwanta ta tafi jikin window ɗinta tana kallon part ɗin Amira dan kam ta san in har yana gidan zuwa yanzu zai fita mosque, ilai kuwa bata jima da tsayuwa ba ya buɗe ƙofar part ɗin Amira ya fito yana sanye da jallabiya baƙa against his very fair skin, duk da duhun asuba hasken compound ɗin tarrrr yake kamar rana, ta zuba masa idanu har ya buɗe ƙaramar gate ya fita a gidan, ajiyar zuciya ta sauƙe a hankali ta juya ta koma cikin toilet ta ɗauro alwala itama.
Ƙarfe 6:10 ya shigo cikin gidan from masallaci, har ya nufi part ɗin Amira ya ɗan dakata ya kalli sashen Na’ima duk yadda ya so ya ɗauke kansa ya wuce sashen Amira kasawa yayi, ya haɗe rai ya nufi sashenta yana tafiya a nutse kamar babu abinda ke damunsa, Amira dake tsaye jikin nata window ta bishi da kallo, dan tun jiya what shes been witnessing a gidannan ita ta san wallahi definitely akwai abinda ya haɗosu da matar gwal ɗin nasa, cause akan idanunta suka fita dan ita dan yanzu ta mayarda wajen permanent wajen tsayuwarta a ɗakin, slight motsi taji zata yi maza ta leƙa, akan idanunta suka dawo seperately shi ya fara dawowa kamar ma a zuciye ya dawo ya wuce sashin Na’imar kafin Munafukincan Nasir shi kuma ya kawo ta after kusan more than 30minutes da dawowar shi Ahmad ɗin, from then kuma bata jima da shiga ba Ahmad ɗin ya fito a part ɗin ya nufo part ɗinta and hes been here tun lokacin har zuwa yanzu da ya tafi mosque bayan ya katse mata barcinta dan dole wai ta tashi tayi sallah, duk da jiyan ba wani shiga harkarta yayi ba, sama sama yake amsa mata maganarta but still she was happy, abinda ya bata mamaki shine rashin baccin da yayi dan a bedroom ɗinsa ma ta kwana infact a jikinsa but she can swear har tsakar dare da ta tashi ta je toilet idanunsa biyu, yanzu kuma ta ga ya nufi sashin Na’ima, to ko dai ba faɗa suka yi bane? Idan ba faɗa ba mai zai sa ya tattaro da wuri haka ya dawo sashinta ya bar matar so, ƙwafa tayi tana kallonsa a ranta ta riga ta san today is the end of it su gama abubuwansu wallahi yau shine ƙarshen tsinannen love story ɗinnasu.
Da mamaki ya ƙarasa cikin palourn nata ganin ƙofar babu lock an tura but ba’a rufe ba does that mean ƙofar part ɗinta a buɗe ta barshi ya kwana? Ya dinga kallon palourn ganin yana nan yadda ya barsa jiya ya wuce sama fuskarsa ba yabo ba fallasa, sai da ya ɗan tsaya jim a bakin ƙofarta kamar ya juya abinsa sai kuma ya tura ƙofar a hankali ya shigo ciki, a zaune a sallayar da tayi salla ya ganta ta rungume ƙafafunta ta ɗaura fuskarta akan ƙafafun, tun yana buɗe ƙofar taji shi ta ɗago idanunta daga ƙafafunta a hankali tana kallonsa, rungume hannunsa yayi a ƙirji yana kallonta bayan ya shigo har tsakiyar ɗakin fuskarsa ba yabo ba fallasa dama in dai ɗaure fuska ne a bar masa kayansa, ganin kallon da yake mata kawai ta fashe da kuka ta mayar da kanta ƙafarta tana kuka abinta shi dai yana tsaye yana kallonta ya ƙi kuma yace mata komai, jin yaƙi lallashinta ta miƙe a hankali ta fara naɗe darduman tana goge idanunta ta tafi ta ajiye ta cire hijab ɗinta tana linkewa tana kuka, ta zo zata wuce shi ta tafi kan gadonta ta ci gaba da kukanta, hannunta ya riƙo ya dawo da ita gabansa, ta ɗago idanunta tana kallonsa shima kallonta yake yace
“Me aka miki? Ko Saboda ke kaɗai kika fi kowa iya kuka?”
Rungumesa tayi ta sake fashewa da sabon kuka tana sheshshqa a hankali, ya lumshe idanunsa ya buɗe a hankali kafin ya kai hannunsa ya ɗaura a kanta yayi shiru, cikin kukan tace
“I’m sorry!”
“Hmm” kawai yace ta sake ƙanƙamesa kanta a ƙirjinsa tace “i’m sorry please if i hurt u unintentionally cause ill never do it intentionally, dan Allah kaji” ta ɗago kanta daga jikinsa tana sheshsheqa a hankali tana kallon fuskarsa tace
“Nasan i’m wrong, i should have stand with u, amma ni saboda kai nayi haka bana so kayi something ull regret, i want nothing but peace for ni da kai, i love you so much, pls forgive me, dont hate me for it” yatsunshi ya sa a bakinsa muryarsa ƙasa ƙasa yace
“Shhhhhh” ya faɗa yana ɗaura goshinsa a nata,
“i can never hate u” ya faɗa muryarsa ƙasa ƙasa ta gyaɗa masa kai a hankali, ya kama hannunta ya ja ta ya zaunar da ita a gefen bed ɗin shima ya zauna yana fuskantarta yace
“Muyi magana Na’ima” gyaɗa masa kai ta sake yi tana share idanunta cause she’s been longing suyi maganar.
“Jiya! U really did hurt me Na’ima, bazaki gane how much it hurts ba so forget it, da zan iya i wont be talking to u right now, but kin riga kiyi charming ɗina, i want relationship ɗinmu to be a straight one babu kwana kwana, if i wrong u in any way ki faɗa min i’ll apologise, same goes to me, so yanzu am telling u, what u did yesterday baki kyauta min ba Na’ima, i coulndt sleep yesterday thinking of how much uve cried for him”
girgiza masa kai tayi a hankali ya riƙo hannunta yana kallon henna ɗinta da ya fara fading hakan ya ƙara ma henna ɗin kyau yace
“Dont do that again i beg u”
“Na rantse bazan sake ba” ta faɗa hawaye na gangaro idanunta, ya kai hannu ya share mata idanunta yace
“Ya wuce, i’m sorry too”
Sake share idanunta tayi a hankali tace
“shine ka bar ni a can ka tafi abinka like i mean nothing to u, nima ai banyi baccin ba jiyan” kallonta kawai yake yadda take maganar kafin ya sauƙe ajiyar zuciya ya janyota jikinsa yana shafa kanta yace
“i’m so sorry, i wont do that again i promise, no matter how angry i’m”
Gyaɗa masa kai tayi a hankali tace
“thank you”
“Ure welcome, zakiyi baccin yanzu?” Ta ɗago kanta a jikinta ta gyaɗa masa kai a hankali alamar
“eh” sai kuma tace
“kai fa zaka yi?”
“Kece yar gata ai zaki iya bacci anytime, i’m resuming office today so i cant sleep like u” ya faɗa yana jan hancinta sai kuma ya miƙe a hankali yace
“u should sleep” gyaɗa masa kai tayi ta haura gadonta sosai tana kallonsa ji take kamar kar ya fita ya hauro gadon suyi bacci kawai, ya ɗan sunkuya ya sumbaci goshinta yace
“bye”.
“Bye” ta faɗa itama a hankali, daga haka ya nufi ƙofa ta bisa da kallo har ya ja mata ƙofar kafin ta kwanta a hankali a kan gadon ta lumshe idanunta tana sauƙe ajiyar zuciya dan da gaske tana jin baccin sosai.
Wajen ƙarfe takwas na safiya ta farka, zuciyarta sakayau ta nufi toilet ta gama abinda zatayi da wanka da komai ta fito, wadrobe ɗinta ta buɗe ta ɗauko wata simple shirt ta saka ta saka bomshort wando dai dai jikinta, gashinta da ta gyara tsaf ta kamasa as ponytail kafin ta saka facecap, ta ɗauko wayarta ta sauƙo ƙasa bayan ta maƙala headphone a kunnenta yunwa take ji sosai but since ita kaɗai ce she decides ba ta dafa noodle kawai taci before anjima, ta wuce kitchen tana danna wayarta replying chat ɗin fadila.
Tana cikin chopping albasa taji an danna door bell ɗin gidan, ta ɗan dakata tare da ɗan sauƙe headphone ɗin daga kunnenta taji still an sake danna dorrbell ɗin gidan, ta kalli agogon wayarta, to bai je office ɗin bane? Jin an sake dannawa ta ajiye wuƙar hannunta ta fito a kitchen ɗin ƙafarta sanye da takalmi mai taushi da take yawo da shi a gidan ta nufi ƙofa, dan ta san ba mai zuwa ƙofarta dai sai Mijinta, ta buɗe password ɗin ƙofar kafin ta janyo ƙofar ta buɗe, kallon kallo suka shiga yi ma juna, Amira ta dinga binta da kallo from head to toe, Na’ima dai na riƙe da ƙofa dan ko kaɗan bata kawo Amira bace ko misƙala zarratin, Amira ta ƙaƙalo murmushi tace
“Amarya ko na juya ne am not welcome?” Da sauri ta girgiza mata kai ta matsa daga jikin ƙofar tana faɗin
“Bismillah come in” Amira ta shigo ciki tana ƙare ma palourn kallo ita dai Na’ima har yanzu cikin zuciyarta da tsoro amma ta dake ta mayar da ƙofar ta rufe ba kirif ba amma yadda idan zata buɗe ba sai ta tsaya saka ko wani password ba, ta ƙaraso cikin palourn a hankali tana kallon Amira sai kuma tace
“i’m coming” ta wuce sama Amira ta bita da wani irin kallo baƙin ciki kamar zai kasheta, cigaba da kallon palourn kawai Amira keyi har Na’ima ta sauƙo da hijab a jikinta har ƙasa ta zauna a kujera opposite Amira ta rasa ma to me zata ce mata sai kawai tace
“Ina wuni” Amira ta gyara zamanta tace
“lafiya lau Amarya ya baƙunta?”
“Alhamdulillah” ta faɗa a hankali, Amira tace
“Masha Allah, ai naga bashi da niyyar haɗa mu yayi introducing ɗinmu to juna ne shine nace ni bari nazo mu san juna tunda yanzu an zama ɗaya koh?”
Na’ima ta ɗan saci kallonta a hankali tace
“hakane”
“Duk wani mijin ƙwarai ai idan yayi amarya haɗa su yake da uwargida ya faɗa ma kowa matsayinta amma kinga ai shi baiyi haka ba, kuma ai bazamu biye masa ba shiyasa ni na zo, dan in ce miki ure free to come to my side anytime kikeso nima zan dinga leƙowa ina ganin yadda kike ai shine abokiyar zaman ina jin koh?”
Ita dai Na’ima shiru tayi bata amsa ba, sai kuma ta miƙe tace
“bari na kawo miki ruwa”
“Thank you amarya” ta faɗa tana binta da idanu har ta wuce kitchen, tana shigewa kitchen ɗin Amira ta miƙe ta wuce sama tana riƙe doguwar rigar kimonon jikinta, dan wannan pretending ɗin da take yi ma baƙin ciki yake ƙara mata ji take kamar ta kashe Na’ima a nan yadda babu kowa ɗinnan daga ita sai ita, but idan ta tuna abinda ta shiryo mata sai taji gwara ta danne ranta ta samu ta aiwatar da abinda ta zo aiwatarwa ta kama gabanta, Daga nan kuma sai taga ƙarshen karuwanci da yawo da gajeren wando tana juya ɗuwawu.
Na’ima na fitowa da tray ɗin ruwa da lemo daga kitchen taga wayam ba kowa a palourn, ta ɗan tsaya jim kafin ta ƙaraso ta ajiye tray ɗin tana mamakin tafiya tayi toh ko me? Sam bata ma kawo ko sama ta haura ba tafi tunanin fita tayi abinta, ta ɗan kalli door ganin yana nan yadda ta ɗan tura sa ɗazu sai ta ƙarasa bakin ƙofar taga shoes ɗin Amira na nan a inda ta cire su, ta juyo ta dawo palourn tana jiran ganin ikon Allah ita kam, sai a lokacin ta kalli hanyar sama, sai kuma ta nufi saman walking slowly, tana shirin fara haura stairs ɗin sai ga Amira na sauƙowa daga saman fuskarta a haɗe kamar ba ita ta gama mata murmushi ba yanzunnan, Na’ima ta ja ta tsaya tana kallonta waiting for explanation ɗin abinda taje mata sama amma sam ko kallon sashin da take Amira bata yi ba ta sauƙo har palourn kawai ta nufi ƙofa, Na’ima was speechless har Amira ta buɗe ƙofa ta fita, to ko ba lafiyayya bace mamar saif ɗin? Kallon stairs tayi sai kawai ta nufi saman itama.
Haurawa tayi saman ba tare da tunanin komai a ranta ba, sai da ta bi ko’ina da kallo ganin ba ta ga wani canji ba everything seems normal and ordinary ta taɓe baki ta shige bedroom ɗinta. Kamar mai neman wani abu ta tsaya ta jingina bayanta a jikin ƙofa tare da ƙare ma ɗakin kallo, sai kuma ta lumshe idonta, after some seconds ta ja ƙafarta a hankali ta ƙarasa bakin gadonta ta hau ta kwanta.
Tunanin hawo mata saman da Amira ta yi kawai take like is that even normal? Ta sake tambayar kanta ko haka ake yi da ma kishiya ta shiga ko’ina da ta so a part ɗinka toh? Ko kuma ɗakunan ta kasa haƙuri ta hau gani don ta ga ta ajiye ta a ƙasa? But she didn’t even take long before ta dawo. Kuma reaction ɗinta after coming down shine ya fi tsaya mata a rai it wasnt friendly at all kamar sanda ta shigo, tabi ɗakinta da kallo, to me ta gani that pissed her off?
Juyi ta yi a kan gadon tare da miƙar da ƙafarta jin kamar wani abu na bin jinin jikinta da ba ta saba jin shi ba, slowly ta kai hannu ta ɗora a goshinta jin kanta ya fara yi mata ciwo, wani irin dull pain though its not much hakan ya sa ta tsayar da tunanin Amira da ta saka a ranta. Ta yi mintunan da ba ta san nawa bane a haka kafin ta tashi zaune ta ɗan yamutsa fuska.
“Whats happening to me?”
Ta faɗa a hankali can ƙasan maƙoshi kamar mai ciwon harshe, don ji ta yi ya yi mata nauyi kamar an ƙara mata girmansa, komai nata jin shi take wani iri kamar ba ita ba, duniyar ma kamar ba wadda ta saba rayuwa a cikinta ba haka take ji.
So take ta koma ƙasa ta ɗauko wayarta da ta bari a parlour amma ta kasa sarrafa ko da yatsanta ne, kwata kwata ma bata tunanin abincin da take da niyyar dafawa taci kafin zuwan Amira, ta bar onions half chopped da pot a kan wuta, Allah ma ya taimaketa bata kunna gas ɗinba tukun, a sanyaye ta ja jikinta ta kwantar da bayanta a jikin gado, sosai ciwon da kanta yake yi mata yake ƙaruwa, runtse idonta da hawaye ya cika kawai ta yi cikin rashin sanin abin yi, kwata kwata ji tayi bata jin daɗi kwata kwata ranta duk a dagule haka siddan.
Jikin Amira har rawa yake gurin kiran Mummy, garin sauri har kusan faɗuwa ta yi Allah ya taimake ta ta riƙe hannun kujera.
Har kiran ya katse Mummy ba ta ɗaga ba, cikin zaƙuwa ta ƙara kira tare da karkaɗa hannunta tana faɗin.
“Please Mummy ki ɗaga.”
Sai da kiran ya kusa katsewa ta ɗaga, muryar Amira na rawa saboda murna ta ce.
“Mummy!”
“Me ya faru? Kira da safennan ina bacci kin katse mini.”
“Mummy na je part ɗin nata na yi duk yadda kika ce.” Ta faɗa da farinciki sosai a muryarta. Da sauri Mummy ta ce.
“Really?, amma ya aka yi kika shiga har bedroom ɗinta? Ina fata dai ba ta gane komai ba?, i hope u did it wisely ba shirme kika yi ba Amira” Dariya Amira ta yi tare da gyara zamanta a kan kujera ta ce.
“Ta shiga kitchen wai za ta kawo mini ruwa kawai na haye na yi abin da zan yi na fito, amma ba mu kuma magana ba har na baro part ɗin, and bana jin za ta gane wani abu saboda yarinya ce sosai, kuma da ta yi tunanin wani abu na san da za ta tsayar da ni ta tuhume ni abin da na je na yi mata, kuma kinsan banzar bata san anything about kishiya ko abinda kishiya zata iya aikata ma mutum ba so i’m sure bazata kawo komai ranta ba.”
Ajiyar zuciya Mummy ta sauke ta ce.
“Good! Sai mu jira result, saura kuma ki yi abin da zai gane da saka hannunki a al’amarin, naki ido ne kawai duk ma abin da zai faru tsakaninsu, naki ido ne kawai idan ba nuna miki ya yi wani abu ya faru ba. Na san ki ba wani kan gado kika cika ba, u better be very careful”
Murmushi ta yi cikin zallar nishaɗin da take ji a cikin ranta ta ce.
“In sha Allah Mummy, thank you, har na fara jin na dawo nutsuwata cause Albina zai dawo nawa ni kaɗai, ba ki ji yadda na ji ba da na gan ta kamar na janyo ta na yi ta duka, ba ƙaramin danne zuciyata na yi ba na tsaya muna magana, mummy har da gajeren wando fa take yawo a gidan ita gata karuwar baturiya, shegiya mummuna”
Mummy tayi wata dariya dan itama cikin nishaɗi take jin kanta tace “gaskiya yarinyar bata da wani kyau, jikinta ne mai kyau hala shi ya ja hankalinsa shi kuma”
Amira ta ɓata rai tace “jikin ma bashi da wani kyau mummy, komai nata bashi da kyau, shi dai maye shi yasan me ya maƙale ma” ta faɗa tana haɗe rai dan tuno kyaun Na’ima da jikinta wani irin soya mata zuciya yake, she wish gaskiya ne mummuna ce Na’imar.
“Ki daina damuwa, don gidan ma gabaɗaya za ta bar miki soon, ni kaɗai na yi rayuwa a gidana, saboda haka wallahi ba wani jinina da zai rayu da wata a gidansa.”
“I love you mummy, wai ina daddy? I called him yeterday bai ɗauka ba kuma bai kira ni back ba”
“Ke rabu da wannan, shegen tsinannen tafiyar nan tasa ce wai ta taso baya ƙasar na kusa na hanasa wanann shegen tafiye tafiyen ya fara isata haka”
“Hm ai shikenan, bye mummy bari naje na ci abinci, ko karyawa fa banyi ba sai da na tabbatar na aiwatar da abinda ya kamata u should be proud of me mummy”
“Mtsw ai kanki kika taimaka ba ni ba” duk sukayi dariya, Daga haka ta katse wayar.
Wani irin wasai Amira take jin zuciyarta kamar an yi mata yasar dattin da ya tokare mata kofofin farin cikinta, rabon da ta ji ta cikin irin wannan nishaɗin har ta manta. Numbern Nuwaira ta lalubo ta yi dialing don ta labarta mata abin da yake faruwa.
Sai da aka yi sallar Zuhur sannan ta yunƙura ta sauko daga kan gadon da ƙyar, jikinta gabaɗaya ya yi mata wani irin sanyi kamar ba ta da laka, her body was very weak gashi cikinta babu abinci, a gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta kamar mai neman wani abu a jikin nata da ya canza mata shi lokaci ɗaya cause her body felt strange, walking slowly ta bar gaban mudubin ta ƙarasa toilet. Tsarki ta fara yi sannan ta yi alwalar da sai da ta koma baya 2 times saboda rikicewar da take, bayan ta idar ta koma bedroom ta shimfiɗa darduma, hijabinta da ya kai mata har ƙasa ta zura, sai da ta tabbatar ta tattara dukkan nutsuwarta sannan ta tayar da sallar.
Tana zaune a kan dardumar har aka kira la’asar, ta rasa me yake yi mata daɗi, me yake faruwa da ita, me ya kamata kuma ta yi, gabaɗaya ta rikice ba tare da ta san dalilin rikicewar ba.
Sallah da lazimin da ta yi ne ya sa ta ɗan fara samun nutsuwa, har ta yi la’asar, cikin rashin ƙwarin jiki ta sauka ƙasa don sama wa cikinta abin da za ta ci, don wata irin yunwa take ji kamar har kayan cikinta sun narke babu sauran abin da ya rage sai fata. Sai da ta fara sauka daga kan stairs ta ƙara tabbatarwa ba ƙaramar yunwa take ji ba, don ji ta yi kamar za ta hantsila, da bin bango ta ƙarasa saboda jirin da ta ji yana kwasar ta ita kaɗai, ita tunda take ma bata taɓa jin tana jin yunwa irin haka ba.
Bayan ta shiga kitchen ta tuna ashe ɗazu tana ƙoƙarin dafa noodles Amira ta shigo, ga albasar da ta fara yankawa nan a inda ta bar ta. Jiki a saɓule ta ƙarasa ta ɗora daga inda ta tsaya, ba ƙaramin dauriya take ba, don ji ta yi ba abin da take buƙata sai kwanciya, bayan ruwan da ta ɗora ya tafasa ta ɓare noodles ɗaya kaɗai ta zuba ta mayar da rufe, kamar wadda aka tsikara haka kawai ta juya ta fice daga kitchen ɗin da sauri ta koma parlour ta faɗa kan kujera ta kwanta ruf da ciki tana mayar da numfashi. Hango wayarta a gefen kujerar da ta zauna ɗazu ya sa ta tashi ta ɗauko, missed calls ɗin Ahmad ta gani har 4, sai na Mami ɗaya. Ba ta yi yunƙurin bin kowa a cikinsu ba ta koma ta kwanta bayan ta yi cilli da wayar kan kujera.



