Yana yin la’asar ya dawo gidan ba don ya gama aikinsa na rannnan ba sai don kiran da yake mata bata ɗauka, haka kawai yaji hankalinsa bai kwanta ba, ko da ya kira Amira ma gabaɗaya ji yake kamar yace mata ta kaiwa Na’ima wayar amma sanin hakan zai iya komawa fitina ya sa kawai yana la’asar ya taho gidan, direct part ɗin Na'eema ya wuce, yana buɗe ƙofar palour ya shigo ciki ya hango ta kwance cikin hijabin da ta yi sallah da ba ta cire ba a ƙasan carpet. ajiyar zuciya ya sauke a hankali ganin she’s fyn but bai san me yasa ba she’s been on his mind too much tun safe, tun kafin 10 am yake kiran ta, ganin har rana ta yi yamma ta fara ba ta ɗaga kiran ba ya ci gaba da kiranta, har message ya mata ta whatsapp amma ba ta hau online ba hakan ya sa yaji hankalinsa ya ƙi kwanciya, walking slowly yake nufar inda take, amma azababben ƙaurin da ya ji yana tashi a parlourn ya sa ya tsaya cak, wani choking scent na ƙonewar abu ya cika hancinsa, Lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarsa ta ba shi kitchen ne, da sauri ya nufi kitchen ɗin, sai da ya toshe hancinsa sannan ya iya shiga ya kashe gas ɗin, hayaƙi gabaɗaya ya turniƙe ko ina, ko ma mene ta ɗora ya san ya zama gawayi. Ƴar nutsuwar da ya fara samu ya nema ya rasa, sai da zuciyarsa ta buga da ya yi wani tunani akan Na'eema, saboda ganin tana kwance a parlourn amma ba ta zo ta sauke ko ma mene ba, and there’s no way za’a ce bata jin ƙaurin, don wannan ƙaurin ko baccin mutuwa take ya isa ya farkar da ita bare ma ita ba mai nauyin bacci bace at all. To ko bata da lafiya ne? In seconds ya fito daga kitchen ɗin ya ƙarasa inda take ya ɗan tsuguna yana taɓa jikinta jin ba zafi yace "Baby" kamar a tsakiyar kanta yayi maganar haka ta ji sa. Tana jin shigowarsa and all what happened bayan shigowar tasa, amma ta kasa ko da buɗe idonta ne, har yanzu da yake daf da ita take jin ƙamshinsa ya cika ta ba ta jin za ta ce komai, kaɗaici kawai ta ji ta fi buƙata fiye da komai a duniya, yanzu da yake tsugune a kanta kamar yana rura mata wuta a jiki haka ta ji. "Baby!" Ya sake kiran ta tare da kai hannusa ya janye nata da ta ɗora a kan fuskarta. A hankali ta buɗe ido ta sauke su a cikin nasa, Kyakkyawar fuskarsa ta bi da kallo kafin ta tashi zaune ganin yadda damuwa ta bayyana ƙarara a fuskartasa . Yasa hannu ya ɗaga hijab ɗinta ya tattaɓa wuyanta ya ce. "Ba ki da lafiya ne? Why arent u picking ur calls?" Kai ta girgiza masa a hankali ta ce. "Nothing." Ganin yadda yake bin ta da ido alamun bai yarda ba ta ce. "Bacci kawai na yi." “Bacci hun?” Ya faɗa yana ƙoƙarin janyota jikinsa da sauri ta janye jikinta tana yamutsa fuska amma ba ta ce komai ba. Jim yayi yana kallonta yace "Tell me what happened, ko tun abun jiya ne? Are u still angry?” So take ya tafi ya bar ta ya ƙyale ta, shi ya sa ta ɗan ƙaƙalo murmushi da iyakacinta lips ɗinta ta ce. "Wani abin jiya? Ni I’m fyn, kawai my mood is bad today ne." Kissing forehead ɗinta ya yi ya ce. "What happened to the mood lets fix it." "Hmm " kawai ta ce ta miƙe tana zare hannunta daga nasa da ya riƙe ta nufi hanyar kitchen leaving him a tsugune a wajen, ya bi ta da ido cike da tsananin mamaki, there’s definitely something she’s not telling him, ƙofa ya kalla lokaci ɗaya tunanin ko Amira ta zo ta mata wani abinne ya zo masa, ya miƙe tsaye ya bi bayanta Kitchen ɗin, ya tarar tana ƙoƙarin haɗa tea, rungume ta ya yi ta baya tare da ɗaura fuskarsa a gefen tata hannunsa a waist ɗinta ya ce. "Akwai abin da yake damun ki, tell hubby what it is?did anyone do anything just tell me anything" Kamar ta hankaɗe shi haka take ji, amma ta daure ta ce masa “babu komai”, tare da zare jikinta daga nasa ta ci gaba da abin da take. Kallonta kawai ya tsaya yi, kafin ya haɗe rai ya kama hannunta da take ta zuba madara a cup da shi ya juyo ta ita yana kallon idanunta yace “Ke tell me me aka miki?” Ta haɗe rai itama tace “Nace maka babu, what do u want me to tell u?” Tana faɗin haka ta zare hannunta ta fita a kitchen ɗin ta barsa a tsaye shocked and confused at the same time. Ko da ya fito palour bata nan ta wuce sama hakan ya sa kawai ya nufi ƙofa ya fita a part ɗinnata ya nufi part ɗin Amira. Daga yanayinsa Amira ta gane something is off definitely its a win for them aiki ya fara aiki kenan cause dama malam yace musu its going to start working immediately in dai har tayi shi yadda aka ce tayi shi, don tana hangen lokacin da ya shiga part ɗin Na'eeman, har da tsallenta na murna ta dinga yi tana ƙunshe dariya kwata kwata bata ji haushin zuwa can da yayi ba dan yau za ta ga ƙarshen soyayya da tattala matar gold. Kamar mai shan magani haka take kurɓar tea ɗin da ta dawo ta ƙarasa haɗawa bayan fitarsa a hankali a hankali, duk da yadda take jin bakinta babu daɗi na daɗewar da ta yi ba ta saka komai a cikinsa ba amma haka ta daure ta shanye duka wanda ta haɗa, ajiyar zuciya ta sauke ta zame daga kan kujera da take ta kwanta a kan carpet, nan take cikinta ya fara hautsinawa kamar za ta yi amai. Juyi kawai take har ta samu natsuwa, ganin har lokacin ba ta koma normal ba ta ɗauki cup ɗin ta kai kitchen ta ɗauraye, wata noodle ɗin ta sake dafawa ta ci a kitchen ɗin sannan ta koma sama. Kamar ba ita ba haka take jin ta, but wannan weakness ɗin yanzu kuma sai ta nemeta ta rasa ta ita kanta so take ta san mene problem ɗin da ya mayar da ita haka amma ta kasa ganowa, kawai sai tayi tunani maybe she woke up at the bad side of the bed ne, hijabin jikinta ta zare ta ajiye ta nufi toilet, tayi wanka ta haɗo da alwala ya fito ta shirya cikin wata riga mara nauyi da ta wuce gwiwarta da kaɗan, ta shafa turarukanta ta gyara gashinta sama-sama. Tsayawa ta yi tana kallon kanta a mirror kamar ɗazu, Ahmad ne ya faɗo mata a rai, ta ɗan ja tsaki da bata san dalilin jan tsakin ba tana jin yanayin da take ciki kamar ƙaruwa yake saboda tuno shi kawai da ta yi. Har ta yi sallar Magrib a ƙuntace take jin zuciyarta. Its like kamar an zagaye mata ita ne da ƙayoyin da tana tuna Ahmad sai su fara sukar ta. Sai da ya fara biyawa part ɗinta bayan ya dawo daga masallaci kafin ya koma na Amira, a ƙudundune ya tarar da ita a kan gado, yadda ta runtse ido jin shigowarsa ya sa ya yi zaton baccin gaske take cause of how she pretends to be asleep, Sunkuyowa yayi ya taɓa goshinta da wuyanta ya ji babu zafi alamun ba zazzaɓi a jikinta, ya zuba ma fuskarta idanu kafin yayi kissing lips ɗinta once ya gyara mata kwanciya cikin kulawa kamar Baby sannan ya miƙe ya fita. Da ido ta raka shi bayan ta sauƙe ajiyar zuciya a hankali, don taɓa tan da ya yi kamar yana danna mata garwashi a jiki haka ta ji ta kai hannu ta share bakinta tana jin hawaye na ciko idanunta da babu dalilinsu. Around 8:30 na daren yana zaune a bakin gado yana latsa waya Amira ta shigo ɗakin da sallama, sai bulbula ƙamshi take cikin kayan bacci riga da wando, ƙamshinta da ya ji ya cika ɗakin ya sa ya ɗaga kai ya kalle ta. Da murmushi ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi. "Sannu da hutawa Albi." Ta faɗa tana ɗora kanta a shoulder ɗinsa, Kai kawai ya iya jinjina mata kafin yace “Howre u?” Tana ƙara mannewa a jikinsa tare da saka hannu ta zagaye shi ta ce. "Im fyn, but i have 1 issue gaskiya dat i want me and u to talk about” kallonta yayi cause its so unlike Amira idan zata yi maganar ta yi kawai take yi abinta but today she’s asking him dat she wants to talk, yau mamaki kashi kashi kawai yake sha a gidan dan ko da ya dawo Amira har abinci tayi offering masa which zai iya ƙirga sau nawa yaci abinci a gidan tun aurensu he always eat out, shima abincin ya san ba ita ta girka ba “Albiii” “Ina jinki Amira” “akwai fa abin da ya kamata ka yi tun farkon auren nan amma ba ka yi ba." Kallon ta kawai ya yi bai ce komai ba. Hakan yasa ta cigaba "Ya kamata ka haɗa mu ka yi mana jawabai, dis is not how it should be, u didnt do ur part well, ure suppose to gather us and talk to us, make peace with both of us, hakan zai ƙara haɗa kanmu ya sa mu yi zaman lafiya, ba wai ka bar mu drifted apart ba its ur duty mu zauna lfy ba ka bar mu sakaka ba kace komai ba, ka ga zai saka mu ji kamar ka bar mu ne kowacce ta yi rayuwarta ita kaɗai, and ni na zauna na yi tunani na ga hakan its not the best thing to do, ko yaya ne tunda muna zaune tare gida ɗaya Ya kamata mu yi zumunci, zaman haka kamar masu gaba bai dace ba." “Bayan wanda kika je kuka yi?” Ya faɗa yana kallonta keenly dan so yake ya gano ko da gaske ta je ɗin, ko shine dalilin da yasa Na’ima ke behaving yadda takeyi, kallonsa kawai ta dinga yi kafin tace “Ni kuma naje ina?” Ya ɗauke kansa ba tare da ya ce mata komai ba kafin ba tare da ya kalleta ba yace “I thought u didnt accept her yet?” Tashi tayi ta zagayo ta zauna a ƙafarsa ta yi kissing lips ɗinsa lightly ta ce. "Ina son ka sosai ka sani, ina kuma son kwanciyar hankalinka, kuma tunda ka riga ka yi auren its better na zubar da komai na yi abin da zai faranta maka i love u more than i hate aurenka Albi." Kallonta kawai yake kafin ya Jinjina kai kawai still bai ce komai ba, “Idan kuma ba ka so muyi zumunci da matarka its not a big deal, do what suits u right, shawara kawai na ba da a matsayina na uwargida kuma babba a gidan after u, komai ka koya mata shi zata yi yanzu tunda ita yarinya ce” Komai bai ce mata ba, but deep down he feels once a rayuwarta she’s making sense, wayarsa dake hannunsa ya kalla sai kuma yayi dialing layin Na'eema, sai da ya yi mata 3 missed calls ba ta ɗaga ba, a na 4 ɗin ta ɗaga, cikin ƙasa da murya ya ce. "Har yanzu bacci kike?" Shiru ta yi masa, ya ɗan kalli Amira dake kallonsa da murmushi a fuskarta jin Na’imar ta masa shiru sai da ya ƙara maimaitawa sannan kamar mai ciwon haƙori ta ce. "Um'um." "Alright, can u come to part ɗin Maman Saif yanzu please ina son yin magana da ku." Ya faɗa cikin kulawa, Amira da ke kallonsa taji bazata iya cigaba da murmushin ba cause of how yake lallaɓa wata ƙaramar yarinya kamar wata uwarsa wai “can u come” ba ce mata zaiyi ta zo ba kawai, so what if tace she cant he wont have a say kenan? Like dis is not how yake mata magana at all wallahi tallahi, ta ɗauke kanta daga kansa tana gyara rigarta Na’ima bata ce komai ba ta kashe wayar, ya tsaya shiru with the phone in hand kafin kawai ya sauƙe Amira daga jikinsa ya miƙe ya nufi toilet Amira ta bishi da kallo. ta ja tsaki a ranta tare da danne zuciyarta ta ƙi amayar da haukan da yake cin ta a rai. Hankalin Ahmad da duk wani tunaninsa yana kan Na'eema, ba don Amira da ta zo ta naniƙe shin nan ba da da kansa zai je ya taho da ita, ya ƙara lallaɓa ta ya ji abin da yake damun ta, zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa da wannan sabon salon nata, ga shi ya ji jikinta babu alamun wani ciwo bare ya ce ko ba ta da lafiya ne. Ya kunna tap ya tara hannunsa a hankali ya cika ruwan ya watsa a fuskarsa, he cant wait for tomorrow ya gama yi ma Amira kwana 2 ɗinta ya koma part ɗin Na’ima zai fi iya fahimtar abinda ke damunta da kyau. Gyara kwanciyarta ta yi ta ajiye wayar a gefenta don babu inda za ta je, shi bai san ko muryarsa ba ta son ji ba ne zai wani kira ta, ko sunansa ba ta son ji bare kuma kallon shi har su yi wata magana kuma ma wai a part ɗin matarsa hmm. Kusan mintinsu ashirin da biyar a zaune a palourn waiting for her har ya fara tunanin tashi ya je part ɗin nata ta danna door bell, Amira tace “Bari na buɗe mata” ya gyaɗa mata kai kawai bai ce komai ba, Amira ta sauƙo ƙasa tana ma Mary alamar ta tafi ita zata buɗe da kanta ta wuce ta buɗe ƙofar tare da janyowa tana kallon Na’ima dake sanye da jilbab mai taushi Maroon colour har ƙasa, Amira bata ce mata komai ba banda tamke fuska da tayi ta matsa a jikin ƙofar, Na’ima ta tsaya a bakin ƙofar tana jin kamar ta juya tayi tafiyarta dan da ƙyar ta danne zuciyarta ta taso, guntun tsaki Amira tayi ta juya ta wuce sama abinta leaving Na’ima a bakin ƙofar, a hankali ta ƙarasa shigowa ciki ta tura ƙofar ta rufe ba duka ba ta zare takalmanta ta nufi cikin palourn, instead ta haura saman sai kawai ta samu kujera ta zauna a ƙasa, tana jin ranta na sake dagulewa. Amira ta koma ta zauna bayan ta dawo tana kallonsa tace “to matarka taƙi shigowa ina jin kai take so kaje ka ɗauko ta ba kishiya ba” ba tare da yace mata komai ba ya miƙe ya nufi ƙasan, a zaune ya same ta a kan kujera ita kaɗai tana ta wasa da gefen hijab ɗinta, ya ɗan kalli saman kafin ya ƙarasa sauƙowa a nutse ya nufo inda take, ta ɗaga idanunta ta kalle shi suka haɗa idanu ta ɗauke nata, zama yayi a gefenta ya ɗan riƙo hannunta yace “Pls tell me whats wrong baby” “Ni nace maka anything is wrong ne?ka tambaye ni nace nothing ion know me kake so in ce, or do u want me to lie?” Kallonta kawai yake cause This is not her words at all, ya matso kusa da ita ya saka hannu a kafaɗunta ya juyo da ita tana fuskantarsa, ya sa hannu ya ɗago fuskarta ganin hawaye har ya gangaro kumatunta ya rasa kuma me zai ce mata, ya sa hannu yana share hawayen dai dai lokacin Amira ta soma sauƙowa daga sama tana kallonsa, sake Na’imar yayi ya ɗan matsa kaɗan daga kusa da ita yana kallon Amira da ta ƙaraso ta zauna a kujera opposite them tayi tagumi tana kallonsu kafin tace “Na ji shiru ne nace to ko a ƙasa zamu yi maganar shiyasa kawai nima na sauƙo” ɗan shafa kansa yayi a hankali ya lumshe idanunsa ya buɗe dan shima ji yayi ya rasa abinda ke masa daɗi gabaɗaya, Na’ima ta matsa can jikin hannun kujera bata sake kallonsu duka ba, ya ɗanyi gyaran murya ya fara magana a nutse sosai choosing his words to make sure its suits the both of them, words about unity and peace amd what he wanted for the three of them, tun da ya fara magana Na’ima ke jin kamar ta kama da wuta dan takaici, ita dai Amira na ta lura da ita, zuciyarta fess take sauraronsa har ya kai aya. Amira ta gyaɗa kai jin yayi shiru kafin cike da kinibibi itama ta hau ƙara nata advice ɗin na yadda zasu zauna lafiya a gidan, shi dai Ahmad sai satan kallon Na’ima yake da ta sunkuyar da kanta lost in her own world, Amira ta kalleta tace “Do u have anything to say, sister?” Ko ɗago kanta batayi ba bare ta kallesu, sai duk suma suka yi shiru suna kallonta, “Na’ima” Ahmad ya faɗa yana kallonta, miƙewa tayi tsaye ta ɗan ja ƙaramar tsaki ta nufi ƙofa da dama bata kulle kirif ba bare ta jira masu gidan su buɗe mata ta fice a palourn, Da ido Ahmad ya bita in disbelief, like “what the hell?” Amira ta taɓe baki tare da riƙe haɓa tace “toh fah” gani tayi ya miƙe ya nufi ƙofar shima ta miƙe da sauri ta biyo bayansa amma tuni har ya fice ya bi bayan Na’imar, ta tsaya a bakin ƙofarta tana kallon ikon Allah, jin kamar footsteps Na’ima ta dakata da tafiyar da take ta juyo ta kalleshi ganin shi ɗinne kuma wurinta yake zuwa ya sa ta kwasa da gudu ta nufi part ɗinta dan kwata kwata bata son ya mata ko wace magana, ta shige ta rufe ta nufi sama da gudu tana shiga ɗakinta ta datse da key. Tsaye yayi a compound ɗin cak, he has never been dis confused a rayuwarsa. Ya kai kusan 1 minute a tsaye a compound ɗin yana kallon hanyar part ɗinta with his chest heavy kafin kawai ya juya ba tare da ya ƙarasa part ɗinnata ba ya koma sashen Amira, Queitly ya wuce Amira da har lokacin ke tsaye a bakin ƙofarta ya ƙarasa cikin palour, ta taɓe baki tare da rufe ƙofar ta biyo shi cikin palourn tana faɗin “Lafiya dai koh? Whats the meaning of what she just did?” Ko kulata baiyi ba ya wuce sama, dan shi kaɗai ya san me yake ji a ransa a lokacin, he cant even think straight, idan ma wasa take its really getting to him fiye da yadda take tunani. Amira ta bishi da ido ganin ya wuce sama abinsa, ba haka tayi expecting yayi reacting ba, ta sanshi iya da zuciya and yarinyar nan hissed at them, like tsaki fa ta masa yana magana fa, amma ji ya dawo sumi sumi ya wuce sama sai ma ita da yake ba ma attitude kamar itace ta masa tsakin. Binsa saman tayi da niyyar maƙale masa har sai ya manta da wani ɓacin ran Na’ima ya zama babu kowa a duniyarsa sai ita kaɗai amma sai taji ƙofar ɗakinsa a datse da makulli, ya kulle kansa a ciki, ta dinga kallon ƙofar kafin ta sake murɗa handle ɗin tace “Albi” ko kulata baiyi ba, ta sake jijjiga ƙofar “Ya wacce ta maka abu daban wacce kake hukuntawa daban? Ni ka buɗe min ƙofar” miƙewa yayi ba tare da ya kalli ƙofar ba ya wuce toilet. Kusan mintinta ashirin a tsaye a bakin ƙofar tana masa maganganu dan ita fa darennan so take taji daɗinsa kamar yadda ta ji na jiya haka kawai wata banza bazata ɓata mata ba. Ganin ya ƙi buɗewa kuma ta san ba buɗewar zaiyi ba ta juya fuuuu ta nufi ɗakinta da ta san haka ne zai faru da bata kawo shawaran kiran Na’ima ba, dama ita so take taga ko aikin ya fara aiki kamar yadda aka ce immediately zai fara kuma taga zahiri amma bata san it will cost her rashin kwana tare da shi ba, so tayi idan Na’ima ta zo tayi rashin kirkin da zata yi ita kuma sai ta rungume abinta ta kwantar masa da hankali. Na’ima na jingine da jikin ƙofarta bayan ta rufe ta saka hannunta a tafin fuskarta amma sam kukan ma ta kasa yi, ita yanzu kawai komai nasa ne bata ƙauna amma bayannan she’s fyn, ta cire hannunta a fuskarta ta ƙarasa cikin ɗakin ta zare hijab ɗinta ta linke ta ajiye ta haura gado ta kwanta ta duƙunƙune jikinta ba tare da ta rufa da duvet ba. Jin zuciyarta sai tafasa kawai take ita kaɗai yasa ta miƙe zaune kawai ta fashe da kuka tayi iya yinta ta gaji kafin ta rarrafa ta ɗauko wayarta dake can dungun gado inda ta kwanta ɗazu kafin ya kirata yace taje, ta zauna tana kallon wayar ta buɗe wayar da niyyar kiran fadila, Ganin Numbersa da tayi saving da hubby, taji zuciyarta ta sake dagulewa ta ja wani dogon tsaki da bata ma san ta iya sa ba ta goge lambar a wayarta kafin ta cillar da wayar ta sauƙa ƙasa ta kwanta a carpet banda juye juye babu abinda take yi, sai kuma ta tashi zaune ta jingina bayanta da gado ta zuba ma ƙofa idanu, duk da rashin son ganinsa da take yi she still expects him to come knock ƙofarta ko da bazata buɗe ba, wani waje nesa a zuciyarta is craving for him amma wannan tunanin kaɗai da tayi sai taji kamar zata mutu dan ƙirjinta zafi ya dinga mata, ta haɗe kanta da gwuiwa ta fashe da kuka, gidanma gabaɗaya ji tayi ya ishe ta, bata sonsa kuma kamar a kurkuku take haka ta fara jinta all of a sudden. Bai buɗe ƙofarsa ba sai da asuba ya sauƙa ya wuce mosque, ko da ya dawo bai ko kalli part ɗin Na’ima ba ya wuce na Amira, ya buɗe ɗakin Amira ya ganta tana ta bacci akan gadonta, ya ƙarasa ya tsaya a kanta fuskarsa ba yabo ba fallasa ya ɗan bubbuga jikin gadon, ko motsi batayi ba ya sake bubbugawa da ƙarfi tare da faɗin “Amira!” Ta buɗe idanunta ta ɗan kalleshi sai kuma ta ja tsaki ƙasa ƙasa ta ja pillow ta juya masa baya ta rungume pillow ɗin. “Ki tashi kiyi sallah madam” kamar zararriya ta miƙe zaune da pillown akan ƙafarta tana kallonsa a mugun fusace tace “Ina ruwanka da sallah ta? Tunda ba kai nake ma sallar ba, ba dai ni ka walaƙanta jiya ba saboda wata yar mahaukaciya?” Wani irin Kallo ya watsa mata ba tare da yace mata komai ba, but d look alone tells she’s hitting the right spot, ba tada burin da ya wuce tayi provoking ɗinsa yau shima ya ji irin zafin da taji jiya. “Saboda wata banza ta zo ta gama haukarta shine ni zaka wulaƙanta ka hanani haƙƙina, da ka sani buɗe ƙofar kayi ta tafi wajenta kawai kuka kwana banga anfaninka a ƙofarnan ba jiya gaskiya” tana kaiwa nan ta sauƙa ta wuce toilet ta banko ƙofar toilet ɗin kamar ana yaƙi, da idanu ya bita zuciyarsa na masa wata kalan suya, bai taɓa jin Amira ta fita masa a rai irin na yau ba idan zai biye ma zuciyarsa abinda zai ma Amira its something da bai taɓa yi ba, sai kawai ya juya ya bar ɗakin ya wuce nasa, Haka ya shirya zuwa office half distracted, ko da yaje office ɗinma he couldnt pay attention Allah Allah yake ya dawo gida cause dole Na’ima ta faɗa masa abinda aka mata take behaving irin haka. Da abin ya kwana a ransa amma ya gagara nemo bakin zaren, Signing documents ɗin gabansa kawai yake amma fuskarsa a haɗe dan shi kaɗai ya san abinda yake ji a ransa.