⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 41: Chapter 41

Ko da ya dawo gidan da yamma, sashen Na’ima straight ya wuce, fuskarsa a haɗe ya buɗe ƙofar palornta ya shigo, ya ɗan ƙare ma palourn kallo, yana nan yadda yake tun shekaran jiya baya jin ko tsinke ta ɗaga a palourn, ya nufi sama yana jin kansa na ɗan sara masa from rashin bacci da kuma damuwa da ya saka ma ransa daga jiya zuwa yau.

Ba tare da ya kalli ƙofar ɗakinta ba ya wuce nasa, yana buɗe ƙofar ya tsaya turus yana kallonta a kwance akan gadonsa tana bacci, ta lulluɓa da bargonsa in a very deep sleep, ya ɗan kalli agogon wayarsa yaga biyar saura, ji yayi baya so ya tashe ta ya ƙaraso cikin ɗakin a hankali ya mayarda ƙofar ya rufe ya ƙaraso bakin gadon ya tsaya da hannu ɗaya a aljihu yana kallon innocent face ɗinta da ko a bacci she looks too innocent and cute, ya juya ya ɗan kalli ƙofa, anan ta kwana ko da yaushe ta kwanta anan ɗin? Jin bashi da amsar tambayar ya sauƙe ajiyar zuciya a hankali yana cigaba da kallonta ji yake kamar kaso mai yawa na damuwarsa ya ragu kallonta kawai da yake yi a kwance a kan gadonsa, juyi tayi a hankali ta gyara kwanciyarta tare da juya masa baya ta cigaba da baccinta, sai a lokacin ya zauna a gefen bed ɗin yana kallon bayanta da rigar jikinta ya rufe mata bayanta sai wuyanta kawai yake iya gani da hannayenta da yake rigar guntun hannu take da shi, sai uban gashinta da ya baje akan pillows ya kai hannu ya taɓa gashin a hankali yana miƙar da coils ɗin gashin wanda yana sakewa suke komawa coils ɗinsu, ajiyar zuciya ya sauƙe ya miƙe ya wuce toilet.

Wanka yayi ya fito ɗaure da towel, ya wuce walk in closet ɗinsa ya shirya tsaf cikin wando three quatre baƙa da ta haske fair skin ɗinsa da armless shirt da ta kama body built figure ɗinsa ya kalli agogo shida har ta ɗan gota, hakan yasa ya ƙarasa ya hau gadon a hankali kamar mai gudun tashinta ya ɗaga duvet ɗin ya shiga ciki ya kwanta ta inda fuskarta yake, ya matso gefenta sosai yana ƙare ma fuskarta kallo, kafin ya kai hannu ya ɗan shafa fuskar yana mayar mata da gashin da ya ɗan sauƙa gefen fuskarta baya, ta ɗan yamutsa fuska amma bata buɗe idanunta ba da alama baccin ya mata nauyi sosai, ya kai hannu ya shafa hannunta inda ba rigar yana kallon face ɗinta ganin ta sake yamutsa fuska ya ɗan yi murmushi kaɗan, ya matso ya ɗaura bakinsa a goshinta ya sumbata, kafin ya janye bakinsa ya ɗan matsa baya kaɗan yana ƙare ma jikinta kallo, abinda yafi burgesa a jikinta ya zuba ma idanu kafin a hankali ya kai hannunsa ya ɗage rigar jikinta da take sakakkiya kuma bata kai mata har ƙasa ba, ya ɗage rigar sosai ya ɗaura hannunsa akan cikinta ya shafa a hankali, ta sauƙe ajiyar zuciya tana shirin juya masa baya, kawai ya sa hannu ya juyo da ita sosai ya ɗaura fuskarsa akan tata yayi kissing lips ɗinta a hankali, ai kamar an tsunguleta ne ta buɗe idanunta da har sun ɗanyi ja saboda bacci, ya janye bakinsa daga nata yana kallon fuskarta ganin irin kallon da take masa,

“Kin tashi?” Ya faɗa muryarsa ƙasa ƙasa yana ƙoƙarin rungumota jikinsa, ai da gudu ta tashi zaune tana zare idanunta akansa, ta ja baya da sauri daga kusa dashi still tana kallonsa, miƙewa yayi zaune shima yana kallonta yace.

“What happened?”

“Meyasa kawai ina bacci zaka kama taɓa min jiki?” Ta faɗa tana kallonsa dan ji tayi bata da buri yanzu kuma da ya wuce ta bar ɗakin, ta kalli ƙofa sannan ta sake kallonsa.

“Saboda ure my wife” ya faɗa yana ƙoƙarin matsowa inda take a gadon ai kamar ƙiftawar ido da bismillah ta dirƙa daga kan gadon ta tsaya tana kallonsa, shima da mamaki yake kallonta kafin yace

“Miye hakan?”

Ta haɗe rai taƙi tace masa komai, ya fara ƙoƙarin sauƙa a gadon, ganin haka ta nufi ƙofa a guje, da hanzari ya sauƙa gadon ya bita, kafin ta buɗe ƙofar ya mayar ya rufe ya riƙota ya juyo da ita ya jingina ta da ƙofa yace

“Na’ima!” Kawai sai ta fashe masa da wani irin kuka da ƙarfi ta fara bubbuga ƙafarta a ƙasa ji take kamar zata mutu idan bai sake ta ta fita a ɗakin ba, ya riƙo fuskarta da hannu biyu har idanunsa ya fara canza kala yace

“Na’ima, listen to me, tell me me yake damunki? Na miki wani abu ne dat ure punishing me dis way? Pls talk to me baby, i’m sorry idan na miki wani abin, look at me” runtse idanunta tayi tana cigaba da fizge fizge a jikinsa ita ya barta ta fita hawaye wasu na korar wasu a fuskarta tace

“Dan Allah dan Girman Allah ka barmin magana bana so, ka bar taɓani dan Allah” cikin kuka take faɗin haka, ya dinga kallonta kafin ya ja da baya kaɗan bayan ya sake ta yana kallonta yace

“Naji to na bar taɓa ki, lets talk”

Ko gama faɗa bai yi ba jin ya sake ta ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita da gudu, ya bita da kallo zuciyarsa na wani irin suya, this is not normal, something is definitely wrong with her, shi damuwarsa ta faɗa masa miye ne matsalar, me ya mata? Is it cause ya kwana a gidan Amira? Kishi take yi? But they were cool da safe bayan ya kwana a part ɗin Amira, koma miye ya faru daga baya ne. Ya koma bakin gado ya zauna ya dafe kansa a hankali kafin ya dunƙule hannunsa ya naushi isa

“Damn it”

Ko da ya fita sallar magrib bai dawo gidan ba sai da ya haɗa da isha, ya tsaya suka yi magana ba mai tsawo ba da security ɗin gate da few ma’aikata masu gyaran compound da flowers na gidan kafin ya wuce part ɗin Na’ima, ya daɗe a zaune a palourn ƙasa yana tunanin hawa saman ya same ta ga yunwa yana ji kuma gidan ma bai yi kama da ta girka komai ba, can ya miƙe ya wuce sama, ya buɗe ƙofar ɗakinta ya tsaya daga bakin ƙofa yana kallonta a zaune akan daddumar da tayi sallah ta zuba ma waje ɗaya ido tana ta kallo, tana jin buɗe ƙofarsa ta miƙe tsaye tana kallonsa kamar taga dodo, ya shigo ciki ya rufe ƙofar ya jingina da ƙofar ya harɗe hannunsa yana kallonta yace

“Baby i’m hungry” wani kalan mugun haushinsa taji take ji ta dinga kallonsa kafin kawai ta ɗauke kanta ta fara linke sallayarta tace

“I didnt cook”

“Ke me kika ci toh?” Ji take kamar tace masa bata sani ba amma ta share taƙi tace masa komai, ya dinga kallonta ganin ta ajiye tana ƙoƙarin wucewa toilet yace

“Na’ima” ta dakata a bakin ƙofar toilet ɗin ba tare da ta juyo ba, ya dinga kallon bayanta kafin yace

“Can we talk like adults for 5 minutes?” Ta juyo tana kallonsa taƙi tace masa komai

Tashi yayi daga jikin ƙofar Ya fara takowa cikin ɗakin, with each matsowa da yake yi ji take tana ƙara jin ranta na mata zafi, da sauri tace

“Kar ka matso kusa dani”

Cak ya tsaya a inda yake yana kallonta, to ko dai tana da aljanu ne? ya ɗan ɗaga both hands ɗinsa sama kaɗan yace

“ok” tayi shiru tana kallonsa a tsaye ɗan nesa kaɗan da ita ya sauƙe ajiyar zuciya yace

“Can u stop being childish ki faɗa min me aka miki? Why are u behaving like dis”

Ta watsa masa wani kallo tace “i should stop being childish?” Ya gyaɗa mata kai yace

“Eh” tayi shiru kawai tana ta kallonsa da expression ɗin da ya kasa reading. Kamar wacce aka ma wahayin maganar tana kallon idanunsa tace

“Ka sake ni mana, why dont u just divorce me” kallonta kawai yake da maɗaukakin mamaki, ahh lallai ba lafiya, duk da yadda kalmar sakinta da ta anbata hits him like knife daurewa yayi ya dinga kallonta in disbelieve, kafin yace mata

“Haba?” Ta gyaɗa masa kai hawaye na gangaro mata idanunta, ya gyaɗa kansa in pain yace

“Saboda me yasa to zan sake ki?”

“Saboda i dont love u anymore, ni bana sonka yanzu, ji nake na tsane…” bata san sanda yayi closing distance ɗin dake tsakaninsu ba, ita dai taji kawai ya fizgota yayi pinning ɗinta da ƙofar toilet ɗin da take kusa da shi yana kallon cikin idanunta dake ƙyallin hawaye yace

“Dont u dare” ya faɗa yana kallon idanunta, “u dont hate me kina jina? Cause ure mine, ure my Woman, do u hear me?”

Juya fuskarta tayi gefe ta fara ƙoƙarin karɓe jikinta muryarta kamar zata fashe da kuka tace

“let me go”

Sake matsowa yayi jikinta sosai yana sake pressing jikinsa against hers ya kama fuskarka ya ɗaura goshinsa a nata muryarsa dis time softer yace

“I’m never letting go, ke macen da na zaɓa ce, macen da nake so, u should calm urself down sanda kika shirya muyi magana sai muyi, idan bakya so in taɓaki i wont”

Hawayen idanunta ya gangaro kan kuncinta, duk zancennan da yake mata wallahi ko kaɗan ba burgeta yake ba, da ya san me take ji a jikinta yanzu haka da ya rabu da ita kawai.

“Dan Allah ka taimaka min ni ka bar ni in tafi, bazan iya zama a gidannan ba!” Matsawa baya yayi a hankali daga jikinta yana kallonta cause dis is serious, ya dake yace

“Okay zan barki ki tafi, but before then ina so ki faɗa min menene dalilin da ya sa kike son tafiyar?” Ya faɗa cike da azababben dauriya da dakiya dan shi kaɗai ya san me yake ji, ta runtse idanunta daga kallonsa tace

“Kawai ina so na tafi ne”

“Okay answer dis last question! Ni na miki wani abu?” Da sauri ta girgiza masa kai, yayi jim yace

“Amira ce ta miki wani abin? U can tell me”

Ta sake girgiza masa kai da sauri tace “ni bata min komai ba, da ta zo ma bata daɗe ba ta tafi and she was nice to me she did nothing wrong!” Kallonta kawai ya dinga yi kamar wata tv yace

“She came here?” Taƙi ta buɗe idanunta tace

“eh”

“When” durƙushewa tayi a wajen ta fashe da kuka taƙi ta amsa, ganin kukan da take yi kawai ya juya ya nufi ƙofa without saying anything again.

Nuwaira na zaune a kan kujera a office ɗin Alhaji Musa tana kaɗa ƙafafu, yayinda Daddyn Amira ke tsaye a kanta yana kallonta, kallon da ke cike da judgement da suspicion kafin cikin kumfar baki yace

“Magana nake miki wani irin ciki kike nufi na haihuwa ko na me?” Ta wani kalleshi kafin tace

“Idan ba na haihuwa ba Alhaji na miye? I’m pregnant with ur baby thats what i mean” yana mata wani banzan kallo yace

“And so? What has that got to do with me?” Nuwaira tayi murmushi ta miƙe tsaye tana kallon fuskarsa tace

“It has mana tunda cikinka ne, bazaka ganni anan ba idan ba cikinka bane”

“Shut ur mouth! Iskancinki kaina yau kika kawo? Ni zaki maƙala ma wani ciki? da uban yaushe na miki ciki?is it my name ure trying to drag into shame?”

Wani dariya Nuwaira tayi tace “da uban sanda kake cewa matarka kayi tafiya kake tarewa a gidan da ka saya mini dan ka dinga holewarka da ni, da uban sanda nake zuwa nan” ta nuna office ɗinsa da hannu, “ka sa a saka do not disturb at ur door, da uban sanda kake zuwa ɗaukata a makaranta ba tare da sanin yarka ba muje in biyaka kuɗin makaranta da ka kashe min, kaga alhaji ba tone tone na zo yi ba, kuma ba sunanka na ke ƙoƙarin shaming ba, sai dai in kai ne kayi compelling ɗina inyi hakan, idan kayi cooperating ba lallai kowa ma ya san da cikinnan ba!”

Kallonta ya dinga yi kafin yace “zancen banza zancen wofi, u better stop decieving urself, na sani kin sani im not the only man u open legs for, ko an ce miki i’m a fool ne?”

Nuwaira ta dinga kallonsa tana hura hanci sai kuma tayi wata dariya tace “sai kuma fa kayi, ciki dai naka ne, idan kuma kafi so muyi terere da ni da kai ure on ur own daga nan dama gidan Amira zani kaga idan naje sai in bata labari dallah dallah, and ni bana bada labari wallahi ba proove kai ka sani” babbar rigarsa ya sa ya goge fuskarsa yace

“Bari mana Nuwaira, wani irin Amira kuma? Tell me how much u want to abort it”

“Abort kace? Hehe, ai wlh ba wannan maganar bawan Allah aurena zaka yi muje mu raini ɗanmu” wani wawan tsaki ya ja yana binta da wani kallo yace

“Aurenki? U must be very very stupid” ya faɗa har yana in ina.

“Okay bazaka aureni ba kenan, lallai u dont know the fire ure playing with Alhaji, to na rantse maka da zatin Allah sai ka aure ni, wallahi wallahi bazan yi kaffara ba!” Tana kaiwa nan ta figi jakarta ta nufi ƙofa tana tafiyarta confidently akan heel ɗin ƙafafunta, ta fice masa a office ɗinsa ta barshi a tsaye a wajen banda zufa babu abinda yake gogewa da babbar riga dan zuwaira taji wannan maganar ya kaɗe har buzunsa.

Washegari Ahmad bai fita ko ina ba tun safe da ya fito zashi masallaci ya taɓa ƙofarta ya jishi a kulle da makulli da ya dawo sai bai sake bi ta kanta ba, dan kwana yayi yana saƙawa da warwarewa, Amira ta zo gidannan to do what exactly? And da yace ta zo she denied coming, it shouldnt be what he’s thinking dan wallahi he wont spare her.

Ƙarfe 10 na safe aka danna doorbell ɗin gidan, Na’ima dake gyaran gadonta ta kalli ƙofar ɗakinta kafin ta ɗauke kai ta cigaba da gyaran gadon, tun 8 da ya kawo mata abincin da ya siyo musu a waje bata sake jin ɗuriyarsa ba, jin an sake danna bell ya sa ta bar gyaran gadon ta ɗauki ɗankwalinta abayarta ta nufi ƙofa dan kanta ba hula sai doguwar rigar abaya ne kaɗai a jikinta, sai da ta ɗaura gyalen kamar scarve kafin ta buɗe key ɗin ƙofar ɗakinta ta sauƙo ƙasa cause ta san its definitely not him tunda shi zai iya buɗe ƙofar ai, tana sauƙowa ƙasa ta nufi ƙofa ta ɗan tsaya jin an sake dannawa ta ƙarasa ta buɗe ƙofar, ta tsaya shiru tana kallon Rahama dake tsaye ita kaɗai bakin ƙofa, Rahama ta mata murmushi itama sai ta mayar mata ta matsa daga jikin ƙofar tace

“come in” shigowa rahama tayi dan Ammi ce ta aiketa ta sa driver ya biyo da ita, haka kawai taji tana son zuwa gidan, ita da ba ma wani zuwa gidan take ba kamar yasmeen, Na’ima ta mayarda ƙofar ta rufe ta dawo cikin palourn tana kallon Rahama tace

“Welcome” itama rahama murmushi ta mata tace

“Ina wuni?” Na’ima ta zauna tace

“Lfy Alhamdulillah” Rahama ta ɗan gyara zama tana murmushi tace

“Yaya yana nan” ɗan kallon sama Na’ima tayi kafin ta buɗa mata hannu alamun bata sani ba.

Rahama tayi shiru tana kallonta, sai kuma Na’imar ta miƙe tace

“ba na kawo miki ruwa” Rahama ta gyaɗa mata kai kawai tana binta da kallo har ta wuce kitchen. Bata jima ba ta dawo ta ajiye mata tray ɗin a gabanta ta koma ta zauna, Rahama tayi murmushi ta kai hannu ta ɗau ruwa ta buɗe ta ɗan sha tana satan kallon Na’imar, gani tayi kamar ta ƙara mata kyau sosai ba kaɗan ba ko dan a biki bata nutsu ta kalleta da kyau ba.

Rahama ta miƙe bayan ta ajiye ruwan tace “toh zan tafi tunda yaya baya nan” ɗan shiru Na’ima tayi tana kallonta tace

“I’m not sure if he’s around or not he maybe around” Rahama ta dinga kallonta da mamaki, ta dai gagara cewa komai, Na’ima ta kalli sama sai kuma tace

“Pls wait for him” ƙaƙalo murmushi Rahama tayi tace

“Okay” ta koma ta zauna sai duk suka yi shiru, dan dukansu ba gwanin surutu bane, Rahama ta ɗauko wayarta tana latsawa, kusan 2 minutes Na’ima tayi breaking silence ɗin tana kallon Rahama tace

“Pls zan iya binki?” Da mamaki Rahama ta ɗago idanunta masu kama da na Ahmad sosai tace

“Ina? Gidan Ammi?” Na’ima ta gyaɗa mata kai, Rahama ta gyara zamanta tace

“Why?” Shiru tayi tana kallonta tace

“Pls, i dont want it here anymore” sake baki Rahama tayi tana kallonta sai kuma tace

“Sai ki dawo yaushe?”

“I’m not coming back, just take me with u pls i hate dis house i beg u” Rahama ta gagara rufe baki sai kallonta take, cause idanun Na’imar har ya ciko da hawaye, to me ya faru? Ko faɗa suka yi da yayan? Just 1 week ɗinne har zasu yu faɗa toh? Ta rasa me zata ce ma Na’ima, ita kuwa sai kallonta take tana jiran amsarta.

“To kin tambayi yayan ne?” Rahama ta faɗa tana kallonta, ta girgiza mata kai, Rahama tayi shiru confused sai can tace

“Faɗa kuka yi da yayan?” Na’ima ta girgiza mata kai da sauri, ganin har hawaye ya ciko sosai a idanun Na’imar Rahama tace

“Toh” dai dai lokacin suka ji footsteps ɗinsa yana sauƙowa stairs duk suka juya suna kallonsa yana sauƙowa a nutse fuskarsa fresh da alama bai jima da wanka ba, Na’ima ta miƙe da sauri ta tsaya tana kallonsa, da mamaki yake kallon Rahama yace

“Yaushe kika zo?” Ta masa murmushi tace

“Yanzu”

“Daga ina?”

“Gida” ta faɗa tana miƙewa itama tace

“Yanzu ma zan tafi” yace “okay” Rahama ta kalli Na’ima tace “bye” kallonta kawai Na’ima take yi ganij ta nufi ƙofa ta bi bayanta da sauri, rahama ta tsaya tana kallonta sai kuma ta kalli Ahmad da shi ma su yake kallo, rahama ta ɗan kalleshi tace

“Wai zata je wajen Ammi tace” kallon Na’ima Ahmad yayi, ya gagara ce mata komai, banda kallonta babu abinda yake yi, Rahama ta kalleta tace

“Kawai ki zauna watarana sai ya kawo ki anty Na’ima” ta girgiza mata kai tana kallonsa, yana kallon rahama yace

“Je ki abinki ke” ta ce “to yaya” tare da nufar ƙofa, fashewa da kuka Na’ima tayi dan kamar zuwan rahama ne ya sa taji gabaɗaya ta tsani gidan, so kawai take ta fita a gidan ko ina ne ma taje amma outside gidan, Rahama kam kanta ya gama kullewa, tana kallonsa ganin kallon da yake ma Na’ima ta gagara cewa komai, ya nufi ƙofa ya buɗe password ɗin yana kallon Rahama yace

“zo ki fita” rahama ta wuce ta fita a palourn tana kallon Na’ima da ta fasa kuka da ƙarfi, ya maida ƙofar ya kulle yana kallon Na’ima dake kuka tsakaninta da Allah yace

“Whats wrong with u?” Kamar ya ƙara mata ƙarfin kukanta ta haɗa kanta da jikin bango ta dinga kuka.

Tsaki kawai ya ja ya juya ya buɗe ƙofar palourn yana kallon Rahama da ke tsaye itama a bakin ƙofar ta gagara tafiya, ya ɗan harareta yace

“Kuje tare, i’ll be coming to the house later!” Rahama ta gyaɗa masa kai tana kallon Na’imar dake tsaye jikin ƙofa itama tace mata

“To muje” flat shoes ɗinta dake bakin ƙofar ta saka ta wuce shi ta sauƙo da sauri tana warware ɗaurin ɗankwalin kanta ta mayar da shi veil. Shi dai kallonta kawai yake, Rahama tace

“Sai kazo yaya” ya gyaɗa mata kai a hankali, ko sake kallonsa Na’ima bata yi ba tabi bayan Rahama zuwa knda driver ɗinsu yayi parking ya bisu da kallo kawai har suka shiga motar, ya jingina jikinsa da ƙofarta yana kallonsu har motar ta fita a gidan.

Har suka isa gidan Ammi ba wanda yace ma kowa ƙala ita da rahama, jingina kanta ma tayi da jikin ƙofa tayi shiru, itama rahama sai bata ce mata komai ba ta cigaba da chatting ɗinta, suna dab da isa gidan Ammi message ɗin Ahmad ya shigo wayarta

“Is she still crying?” Ɗaga kanta tayi ta kalli Na’imar kafin ta masa reply da

“Ah ah” ganin bai ce komai ba ta ɗan karkata wayarta tayi snapping Na’imar ta tura masa, da alama yana cikin dm ɗinta dan tana turowa ya gani sai dai bai ce komai ba, ta sake ce masa

“Me yake damunta yaya?”

“Nothing” kawai yace mata, ta tura masa sticker na kallonsa ta gefen ido amma sai taga ya sauƙa online ɗin hakan yasa ta taɓe baki ta cigaba da hira da friends ɗinta abinta.

Driver na parking, Rahama ce ta fara sauƙa bayan ta ɗauki ledan supermarket dake gefenta na aikan Ammi ta tsaya tana jiran Na’ima, itama ta sauƙo tana gyara mayafinta, sai da rahama taga ta fito kafin ta nufi cikin gidan, quietly Na’ima ke bin bayan Rahama a compound ɗin har suka iso ƙofar shiga palour.

Yasmeen ce ta buɗe musu ƙofa, ta ɗan tsaya da mamaki tana kallon Na’ima dake bayan Rahama fuskarta na nuna tambaya ƙarara, rahama ta harareta tace

“miye haka wai?kin tsaya mana a hanya kina kallonmu” matsawa tayi tana cigaba da kallon Na’ima ba tare da ta kula rahama ba tace

“Sannu da zuwa” Rahama ta kalli Na’ima tace

“Ki shiga” wuce su tayi ta shiga cikin palourn walking slowly dan sai yanzu ta fara tunanin me zata ce musu toh haka kawai ta taho gidan ko me zata ce? Yasmeen ta ɗage ma Rahama gira alamun tambaya amma rahama ko kulata bata yi ba ta shige ciki ta barta bakin ƙofa, yasmeen ta ɗan leƙa compound to ko tare suke da Yaya? Ganin ba kowa ta rufe ƙofar itama ta taho palour.

Tsaye tayi bayan kujera tana kallon Na’ima da rahama ta sa ta zauna, ta sake cewa

“Ina kwana” Na’ima ta ɗan ƙaƙalo murmushi tace

“Ina kwana” zagayowa tayi ta zauna a kujera opposite Na’ima da wayarta a hannunta, Rahama ta dubi Na’ima tace

“Bari inyi ma Ammi magana” gyaɗa mata kai kawai Na’ima tayi Rahama ta wuce sama, ita dai yasmeen na zaune tana danna wayarta tana ɗan satan kallon Na’imar dake ta wasa da yatsunta.

Ba’a ɗauki lokaci sosai ba Ammi ta sauƙo daga sama Rahama a biye da ita, har ta ƙaraso palourn ta samu waje ta zauna itama rahama ta zauna a hannun kujeran da Ammi ta zauna duk suna kallonta, ta ɗan zamo daga jikin kujeran cike da kunya tace

“Ina kwana” Ammi ta mata murmushi tace

“Ah ah tashi mana ki zauna Na’ima, ya gidan?” Komawa tayi ta zauna tace

“Fyn” Ammi tace

“Masha Allah” kafin ta kalli Yasmeen tace

“Kawo mata ruwa mana Yasmeen” yasmin tace

“Toh” tare da ajiye wayarta ta wuce kitchen, ita dai rahama na ta zaune a gefen kujera, Ammi ta miƙe tana kallon Na’ima tace

“feel at home ina zuwa kinji” Na’ima ta gyaɗa mata kai a hankali, Ammi ta ɗan dubi rahama amma bata ce mata kpmai ba ta wuce sama.

Rahama ta dawo kan kujera ta zauna tana kallon Na’ima tace

“ko kina jin yunwa?” Girgiza mata kai tayi, rahama tace

“Okay” dai dai sannan Yasmeen ta dawo ta ajiye tray ɗin a gabanta ta koma ta zauna itama tana kallon Rahama da ita kuma taƙi kallonta.

Ammi ta shiga ɗakinta ta zauna a gefen bed da wayarta a hannunta tana neman number Ahmad dan bata fahimci bayanin da Rahama ta mata ba at all, ringing ɗaya kamar mai jiran kiranta ya ɗaga, bayan ta amsa gaisuwarsa tace

“Ahmad ban gane bayanin da Rahama ta min ba” ɗan shiru yayi kafij yace

“I’ll explain idan Nazo Ammi, anjima in sha Allah zanzo, idan na zo ma zamu tafi tare da ita” Ammi tayi shiru tana saurarensa kafin tace

“Lafiya dai ko ina?”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved