⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 42: Chapter 42

“Hopefully, Sai dai na zo ɗin Ammi”

“Shikenan, Allah ya kawo ka” daga haka ta katse wayan ta ajiye a gefen gado tana sake tunanin ce mata da rahama tayi wai kuka ta dinga yi zata biyo ta, kuma tana kallon idanunta ma yanzu taga alamar kuka, to ko baya binta a hankali ne take gudunsa?Gagara komawa ƙasan tayi ta zauna a ɗakinta kawai.

Ahmad bai zo gidan ba sai dare, lokacin Na’ima da Yasmeen da Rahama harda Saif da ya dawo daga sch suna ɗakin yasmeen suna kallo a laptop ɗinta, dan tuni ta sake jikinta a gidan kamar ba gidan surukai ba, dan ji tayi duk wani damuwa da ke damunta a wancan gidan babu shi yanzu, Saif kuwa dama yana ƙyalla ido ya ganta ya maƙale mata, sosai itama tayi kewarsa hakan yasa duk inda tayi yana biye da ita a gidan, da Rahama zata yi girkin dare ma kitchen ɗin Na’ima taje ta zauna a kujera da Saif a jikinta tana kallonta, Yasmeen kuma na zaune akan fridge tana ta basu labarin bikin ƙawarta dat she missed, kwata kwata ko kawo Ahmad bata yi a ranta ba ko sau ɗaya.

Tana zaune a kan gadon ta miƙe ƙafafunta Saif na kwance akan ƙafarta, Yasmeen kuma tana kwance ta kifa cikinta akan gadon tayi tagumi duk sun ƙura ma Animation movie da suke kallo idanu, yayinda Rahama ke ƙwance kan sofa tana waya da Aliyunta aka yi knocking kafin a turo ƙofar ɗakin, mai taya su aiki Fati ta tsaya daga bakin ƙofar cike da girmamawa tace

“Wai anty Na’ima ta zo inji Ammi” duk kallonta suka tsaya kafin Na’ima tace

“okay” Yasmeen tace

“tana zuwa” juyawa Fati tayi ta fita ta ja musu ƙofar, Yasmeen ta kalleta tace

“Ko yaya ne ya zo ɗaukarki?” Zuciyarta taji ta buga da ƙarfi tuno shi kawai da tayi ta dinga kallon Yasmeen amma ta gagara cewa komai, Rahama da ke waya itama hankalinta ya dawo kansu, Yasmeen tace

“Allah sarki yanzu tafiya zakiyi? Rahama gobe muje dan Allah” ita dai rahama kallonsu kawai take dan ta san a yadda suka taho da Na’imar she’s not sure idan she’ll want to go back to the house, Na’ima ta ɗaga kan Saif daga Ƙafarta ya tashi ya zauna a gadon yana kallonta, ta sauƙa a gadon ta ɗauki gyalen sabon abayan jikinta ba wanda ta zo da shi ba ta yafa a kanta ta nufi ƙofa, duk binta suka yi da kallo, dan gabaɗaya mood ɗinta ya canza kamar ba Na’imar da har mamakin yadda tayi saurin sabawa da su suke ba, Yasmeen ta miƙe ta sauƙa a gadon tabi bayanta, Saif ma sauƙa yayi yabi bayan Yasmeen, itakam rahama ta rakasu da idanu kafin ta gyara kwanciyarta ta cigaba da wayarta.

Tare suka shigo palourn Ammi su duka ukun, Ahmad da ke zaune kan kujera opposite Ammi ya ɗaga kansa ya kalle su, ai kamar an dasata a wajen haka ta dakata daga bakin ƙofa taƙi ta ƙaraso ganinsa a zaune a palourn, Ammi ta kalleta ganin ta tsaya cak taƙi ƙarasowa tace

“Ƙaraso mana Na’ima” girgiza mata kai tayi ifanunta har ya ciko da hawaye, Yasmeen ta tsaya tana kallon ikon Allah, ta kalli Na’imar sannan ta kallesa, Ammi ta ke ta kallon Na’imar itama ta ɗauke idanunta daga kan Na’imar ta mayar kan Yasmeen tace

“Me ya faru ke kuma who summoned u here?” a hankali tace

“babu”

“To a sauƙa lafiya, kama hannun Saif kuje sai anjima” gyaɗa kai tayi a hankali ta ƙarasa ta kama hannun Saif da ya sauƙa daga jikin babansa dan suna shigowa dama ya gansa ya tafi gunsa, suka nufi ƙofa, har Allah Allah take taje gun Rahama taji me yake faruwa.

Ammi ta kalli Na’ima ganin ta tsaya jikin ƙofa ta fara kuka, a zuciyarta tace “ikon Allah” kuma a iya maganar da sukayi da Ahmad there’s nothing wrong with her, its not even what she was thinking at first, Ammi ta miƙe ta taho bakin ƙofar tana kallonta tace

“Na’ima!” Share idanunta tayi tace

“Na’am”

“What happened?”

“Nothing” ta faɗa a hankali wasu hawayen na sake gangaro mata, Ammi ta ɗan kalleshi ganin su ya ƙurama idanu yana kallonsu, sai kawai ta kama hannun Na’imar ta shigo da ita har palourn, ta nuna mata kujera tace

“Zauna muyi magana” tana share ido ta zauna a ɗofane, Ammi dats confused tace

“Ya miki wani abune?” Ta girgiza kanta a hankali, Ammi tayi shiru kafin tace

“Toh what happened?”

“Nothing” Na’ima ta faɗa tana ƙin ɗago idanunta, shiru Ammi tayi duk jikinta yayi sanyi there’s definitely something amma to ya zatayi? Tunda Na’imar tace ba komai, ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya tace

“Ahmad kuje gida dare Nayi! Ke kuma kiyi haƙuri since kinƙi faɗa min damuwarki…” ko ƙarasawa batayi ba Na’ima ta fara girgiza mata kai tace

“Ni bazan bishi ba, i dont want to go with him” Ahmad ya sake baki yana kallonta, itama Ammi kallonta kawai take, ganin da gaske take har da kifa kanta da kujera tana kuka Ammi ta kalli Ahmad tace

“Toh kaje sai da safe tunda tace bazata ba, gobe sai ka zo ka ɗauke ta” kallon Ammi kawai yake amma ya gagara cewa komai can ya ɗan sauƙe ajiyar zuciya yace

“Ki bari mu tafi ɗin kawai Ammi, she’ll be fyn idan munje gida”

“Ni i wont be fyn, bazan bika ba, if u insist i’ll run away and u’ll never see me again” ta faɗa tana ɗago idanunta ta kalleshi kamar yadda shima tunda ta fara maganar yake kallonta.

Ammi tayi shiru tana kallonsu, ah lallai ba lafiya to ko dai yarinyar na da aljanu ne? Ganin sai kallonta Ahmad ke yi Ammi tayi breaking silence ɗin da faɗin

“Kaje kawai toh Ahmad sai da safe Allah ya bamu alkhairi! Ke kuma kin fi son nan ina?” Ta faɗa tana kallon Na’ima, gyaɗa mata kai tayi, Ammi tayi murmushi tace

“shikenan tashi ki tafi wajensu yasmin abinki” miƙewa tayi tana tafiya a hankali ta nufi ƙofa tana goge idanunta da bayan hannu, Ammi ta bita da kallo har ta fita kafin ta dawo da kallonta kansa tace

“Ko tana da aljanu ne?” Buɗa mata hannu yayi alamun bai sani ba, Ammi tayi shiru lost in tunani tace

“kuma fa wuni tayi tana walwala abinta, duk yadda aka yi tana da aljanu ne, zan kaita wajen malam idris gobe ya mata ruƙiyya, kasan Aljanu na hana yaya mata zaman aure sometimes, wata ba’a sanin tana da su ma sai tayi aure, if things escalate kuma zan kira mamanta inji ko akwai abinda yake damunta dama can, idanma magani za’a nema mata sai a nema mata cause dis is not normal kwana goma kaɗai da aure kuma haka ta faru” jinta kawai yake amma sam hankalinsa baya nan, can ya miƙe jiki a saɓule yace

“Sai da safe” Ammi ta dinga kallonsa ganin yadda jikinsa yayi sanyi, bata taɓa ganinsa haka ba ma itakam tunda yayi girma da wayo, a hankali tace

“Dont worry she’ll be fyn okay?” Gyaɗa mata kai kawai yayi ya nufi ƙofa walking slowly ya fita a palourn Ammi ta bisa da kallo.

Banda kiɗa babu abinda ke tashi a cikin babban club ɗin, Neon lights nata pulsing Red, Blue da violet accross babban dance flour ɗin, inda maza da mata ke ta tiƙa rawa, warin cigarette da all kind of alcohols ne kawai ke lingering a ko ina na club ɗin, dj na gefe yana basu sauti yana spinning fast paced track da ke gabansa, su kuwa sai sake haukacewa suke da rawa da ihu duk sanda sabon beat ya shiga, ko wani beat dirtier than wanda ya fita. floor ɗin wajen da ke nan na glass yana reflecting hasken wutar club ɗin yayinda mata da maza ke sheqa rawarsu abinsu, wasu na twekking a jikin wasu, it was chaos ba kaɗan ba amma a wajen Suhaila it was a beautiful chaos exactly irin wanda take so ne.

Tana sanye da wani guntun gown mai ƙyalli ƙyalli, sai glittering rigar yake under club lights ɗin, ya manne da jikinta, expensive gashin kanta a zube a bayanta hannunta ɗaya da ƙaramin cup na wine ta ta ɗaga ta kwankwaɗe ta cillar da cup ɗin tana zare jikinta daga saurayin da ya maƙale mata tun ɗazu tana masa twekking, ta kurɗa har tsakiyar crowd ɗin duka idanu suka dawo kanta, ta watsa gashinta baya tare da cije lower lip ɗinta tana haurawa stage inda wani chrome pole ke tsaye spotlight na haskasa, tuni aka shiga hailing ɗinta da alama pole dance is her thing.
duk aka shiga ihu ana shouting sunanta da waɗanda suka iya faɗa da waɗanda basu iya bama.

Wani irin nishaɗi take ji mixed da buguwa da tayi, tayi wrapping hannunta around pole ɗin tareda swinging jikinka effortlessly yadda zaka san ta saba, yadda take juya jikinta a jikin poll ɗinnan kana ganin kasan expert ce a harkar, yanda take bending tana ƙada jikinta, Maza na ihu da whistling, mata na mata tafi, wasu na video dan ba ƙaramar burgewa take ba, shi kuwa dj sai bata sauti yake dai dai da rawar da take yi, wasu har kuɗi suke watsowa saman stage ɗin ana ihu ana hailing ɗinta.

Sosai ta sha rawarta har Sai da waƙar ta ƙare kafin ta dirƙo daga saman stage ɗin, zufan da ta haɗa yana mannewa da jikinta, mutane kuwa suka dinga tafa mata, kafin dj ya sake musu sabon sauti wata ma ta hau ta shiga yin nata,

bangaje juna sukayi ita da wani dogon guy baƙi ƙirin,ƙaƙƙarfa yana sanye da Baƙar shirt da alama ɗan africa ne, kuma a yanayin jikinsa kamar na bouncers wani zabgege da shi, ta ɗan ja baya tana kallonsa cike da maye, ganin yana kallonta kawai ta matso gabansa ta ɗaga ƙafafunta ta saƙala hannunta a wuyarsa tana kallon idanunsa tare da cije lips ɗinta tace

“U want me?” Komai bai ce mata ba ya kama hannunta ya nufi ƙofa da ita, itama binsa kawai take tana tangaɗi da heels ɗinta da ta cire su bayan ta sauƙo a pole dance ɗin a hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ƙaramar jakarta ce ta da riƙeshi a kafaɗarta.

Cikin wata black mota tinted ya tura ta baya shima ya shigo bayan ya rufe motar yana kallonta, ta matso kusa tana ƙoƙarin hawa jikinsa tace “was just about to come home” tana faɗa ta ɗaura bakinta a nasa, shima karɓewa yayi urgently suka shiga kissing juna messy, hannunta na ƙoƙarin buɗe masa botur ɗin rigarsa, shima yana ƙoƙarin jan zip ɗin guntuwar rigarta a jikinsa, just as sun gama birkicewa kamar mahaukata a motar wayarta da ke jakar gefenta ta shiga ringing, ba ƙaƙƙautawa, ko kula wayar basu yi ba, amma mai kiran ya cigaba da kira shima ba ƙaƙƙautawa yasa dole ta tashi daga jikinsa tana danna ma koma waye mai kiranta zagi ta janyo jakar ta buɗe ta zazzage duk abin ciki a kan kujera kafin wayar ta faɗo ta ɗauka tana kallon mai kiranta, ganin Mummy ne ta ɗan ja tsaki kaɗan tare da ɗaka wayar ta saka a speaker.

Mummy salma tace

“Hello Suhaila”

“say what u want to say pls am in the middle of something” mummy ta haɗiye abinda take ji a ranta dan for the past week yanzu Suhaila ko ɗaukar wayarta bata yi kwata kwata yanzu da ta samu ta ɗauka ba zata iya mata faɗa ba kar taji haushi ta kashe, ta sauƙe murya tace

“Suhaila dan me yasa zan dinga kiranki bazaki dinga ɗauka ba, when are u coming back? Wani ƙasa kike ma tukunna?”

Suhaila ta ɗan ja tsaki cike da maye tace “ba ruwanki, tunda u didnt fulfil ur promise na auramin shi miye kuma kike kirana ki min, bayan kin gama min ƙarya, i hate u mummy!” Cikin tashin Hankali Salma tace

“Suhaila kin san kuwa me kike cewa?” Da ƙarfi Suhaila tace

“Na sani mana, cewa nayi i hate u mummy, kuma kar ki sake kirana dan ba dawowa zanyi ba baƙincikin Na’ima ya kashe ni”

Tana faɗa ta jefar da wayar a kujeran motar ba tare da ta kashe ba ta juya ta faɗa jikin mutumin suka cigaba da kissing juna, Mummy salma banda “Suhaila” babu abinda take kira amma ina ba amsa, ba ƙaramin tashi hankalinta yayi ba jikinta ya fara tsananin rawa jin abubuwan da ta koma ji daga cikin wayar, ta dinga nanata innalillahi wa inna ilaihi raji’una amma sam ta gagara kashe kiran tana jin duk badaƙalar da suke a motar da muryoyinsu duka duk tana ji.

Daddyn Na’ima na zaune a palournsa lost a cikin tunani, wani irin dogon tunani da kana ganinsa zaka ga tsananin damuwa a bayyane a fuskarsa, ya ƙurama waje ɗaya idanu yana ta kallo idanunsa sun kaɗa sunyi ja, tun jiya yake cikin wannan damuwar da ya gagara samun sauƙi a zuciyarsa, abubuwa masu tarin yawa kawai yake tunawa da yake jin zuciyarsa na daɗa karaya, he has been like dis tun dawowarsa daga asibiti jiya, abinda likita ya faɗa masa ya gagara mantawa, babu abinda yake tunani sai Na’imarsa, yayi tariyar rayuwarsa yayi replaying har ya gaji wanda tuno wasu abubuwan ji yake kamar zuciyarsa zatayi bindiga.

He wish zai iya mayarda hannun agogo baya ya gyara many bad decisions da yayi making, he wish zai iya dawo da lokacin da Yake auren Mami ya gyara abubuwa da yawa da ya ɓata a lokacin, he wish bai wargaza musu perfect family ɗinsu ba sun raini ʼyarsu cikin ƙauna da kulawa, he wish they can all forgive him, amma yanzu yasan its too late for him, hawayen da yake ta nemansu tun jiya suka silalo kan kuncinsa.

In kunga errors kumin haƙuri, i typed ɗis in a hurry, da zan biye ma jikina ma da bazan iya typing ɗin ba, amma bazan iya barinku kuna ta jira ba, so here u go❤️

Washegari da safe ita da kanta ta shirya Saif, dan tunda ta tashi da asuba tayi brush tayi Sallah taji bata son komawa bacci kamar dai yadda yasmeen ta koma abinta, dan tunda daren jiya Ammi ta canza mata bedroom hakan yasa Saif ya bita can, yasmeen ma ganin Rahama ta bawa banza ajiyarta a ɗakin kawai tabi bayansu tace acan zata kwana.

Har ta gama shirya Saif cikin kyakkyawar uniform ɗinsa da rahama ta kawo mata dan ta zo ɗaukarsa da safen taje ta shiryashi Na’ima tace she shouldnt worry so kawai sai ta koma ta kawo mata uniform ɗinsa da komai na gyaran jikinsa.

Tana shirya shi yana ta mata surutu itama kuma sai biye masa take har suka gama, yace “Mimi” kamar yadda yasmeen tace ya dinga faɗa not anty Na’ima, Na’ima dake brushing kansa tace

“Yes”

“Mimi, when are we going for polo again? Me u and papa? Its been long” ya faɗa yana kallonta harda karya wuya,

“Zamu je” kawai ta ce masa tana gyara masa necktie kafin ta ja kumatunsa kaɗan tace

“muje kaci abinci” kama hannunsa tayi ta nufi ƙofa, tana gyara yafin gyalen gown mai taushi na jikinta, irin egyptian gowns ɗinnnan masu mayafinsu cikin waɗanda Ammi ta bata jiya da dare, ɗayan hannunta riƙe da Bag ɗinsa suka sauƙo ƙasa, masu aiki biyu da ke gyaran gidan suka gaishe ta ta amsa tana kallon Saif da ya wuce kitchen da gudu yana faɗin

“Anty Rahama!” Itama kitchen ɗin ta shigo tana kallon Rahama da har ta haɗa masa lunch box ɗinsa,
Zaunar da shi rahama tayi kan ƙaramar chair dake kitchen ɗin purposely saboda shi da ƙaramar table tace

“Ci abinci ana jiranka Saif” gyaɗa mata kai ya yi, yai bismillah tare da fara cin abinci, rahama kuma ta koma tana gyara inda ta ɓata a kitchen ɗin, Na’ima ta ƙarasa ta buɗe fridge ta ɗau ruwa zata sha, rahama da ta gama abinda take ta jingina bayanta da sink tana kallonta tace

“Sa sassafennan zaki sha ruwan sanyi anty Na’ima”

“Babu kyau ?” Ta faɗa tana kallonta da goran a hannunta, rahama tayi dariya ganin how cute she looks, like morning face ɗinta is soo pretty, she looks simple and natural yet breathtaking.

“Naah ni ban sani ba amma ni idan na sha cold water da safe haka ƙullemin ciki zaiyi” Saida Na’ima ta kurɓi ruwan kafin tace

“Ke meyasa baki koma baccin ba”

“Hm ai ni bana bacci da safe wannan sai yasmeen, daganan har azahar kafin kiga ta taso, sanda muke sch da ƙyar take tashi ta shirya watarana sai sunyi faɗa da Ammi, ai next month zamu fara Uni zanga yadda zatayi, shegen bacci ne da ita kamar kasa” Na’ima tayi dariya ba dan ta san miye ma’anar kasa da ta faɗa ba, can dai tace

“Whats kasa” rahama tayi dariya tace

“Oops!” Tana cigaba da dariya tace

“kasa is a type of phython snake, ance it sleeps alot too”

“Oh” Na’ima ta faɗa tana buɗe fridge ta mayar da ruwan, lokacin Saif ya gama cin abinda zaici a abincin, Rahama ta kama hannunsa ta kaishi har compound inda Driver zai kaisa sch dan har 7:30 ya gota kafin ta dawo ciki ta samu Na’ima na wanke ƙaramin plate ɗin da Saif yaci abinci tace

“Laa da kin sani kin barsa na zo na wanke, yanzu ma breakfast zan ɗaura before Fati tayi na rana anjima, idan kuma Yasmeen taga dama sai tayi ita, bare ma nasan ba zata yi ba”

Na’ima na murmushi tace

“zata yi mana”

“Kai taɓ yasmeen ɗin? Baki san halin yasmeen ba kenan, she can be in the Kitchen for more than an hour without doing anything sai dai fati tayi tayi ita kuma tana cikata da surutu” Na’ima ta sake murmushi tace

“Me zaki dafa to yanzu?”

“Ammi zanje in tambaya yanzu, nasan ma yanzu zata sauƙo itama” Na’ima ta ɗan kalleta tace

“Ko inyi pancakes?” Rahama na kallonta tace

“Ke zakiyi?” Ta gyaɗa kai a hankali, rahama tace

“To ba sai na tambayo Ammi ba ma muyi kawai” Na’ima tace

“Tom”

Na’ima ta buɗe cupboard da tun jiya taga inda suke ajiye stuffs ɗinsu, ta ɗauko jar na flour, da sugar, ta ɗauko ƙwai, da milk da butter, sai wani ƙaramin bottle na vanilla essence da tun da ta gansa jiya taji tana son yin pancake ɗin, sai tin na cocoa powder da zatayi hot chocolate da shi.

Rahama dai kallonta kawai take can tace “let me watch closely its like naki daban da wanda na iya” dariya suka yi duka, Na’ima tace

“to ɗauko min bowl”. Rahama tace

“okay” ta buɗe drawer ta ɗauko mata bowl mai kyau ta miƙo mata, measuring flour tayi ta zuba a bowl ɗin, ta ɗan saka pinch na gishiri tayi whisking ɗinshi kafin ta fasa ƙwai ta zuba a ciki ta sake whisking tana kallon yadda mixture ɗin yake kauri and turning smoother. Sai sannan ta zuba milk slowly ta cigaba da mixing har sai da ya haɗe gabaɗaya turning into a creamy consistensy kafin finally ta ɗiga drops na vanilla essence ɗin. Already ƙamshinsa har ya fara cika kitchen ɗin.

Rahama dai ta naɗe hannu tana kallonta with admiration, Murmushi Na’ima tayi ta ɗan janyo mayafinta da ya sule rabin kwantaccen gashinta a waje, ta gyara mayafin kafin ta kunna stove ɗin, rahama ta miƙa mata nonstick pan da take ta riƙe da shi tun ɗazu, Na’ima ta karɓa ta ɗaura a wutan. Ta saka knob na butter ta jira shi ya narke tana sauraron Rahama da ke ta mata hira, ta fahimci Rahama halinsu ɗaya da yayanta at first zaka iya ɗauka bata da magana she’s nonchalant and the rest, but itama tana da magana sosai idan taga dama.

Ɗiban mixture ɗin tayi ta zuba a center na pan ɗin, Rahama ta zuba ma yadda abin ya bada perfect circle idanu ƙamshin vanilla da butter ne kawai ke tashi.

Na’ima ta saka spatula na hannunta tayi flipping ɗinshi, bayan kuwa ya gasu yayi golden brown abin gwanin sha’awa.

Yana gama gasuwa ta cire shi a wuta ta sake saka wani, haka ta dinga yi a tsanake har ta gama tass.

Ta kalli Rahama tace “ur turn ke kiyi scrambled egg sai inyi hot chocolate shikenan mun gama”

Rahama tayi dariya tace “easy work” tare da buɗe drawer ta ɗauko wani bowl ɗin ta zo ta fasa ƙwai a ciki da pinch na gishiri sai pepper ta kaɗa su kafin ta juye a frying pan dake kan wuta ta saka wooden spoon tana jujjuya shi tana kallon Na’ima da ta ɗauko pack na sassauge, ta ɗauko wani ɗan ƙaramin frying pan ta ajiye shi tana buɗe pack ɗin ta ciro sassauges ɗin tana jerawa akan pan ɗin har ta gama kafin ta kunna different stove ta ɗaura shi akan wutan.

Ta barsu suna grilling har sai da suka yi brown ƙamshinsu na tashi da ɗan hayaƙi kaɗan daga pan ɗin. daidai lokaicin yasmeen ya shigo kitchen ɗin da doguwar rigar bacci a jikinta ta tsaya daga bakin ƙofa tana kallonsu kafin ta ƙaraso tace

“Ina kwana anty Na’ima” Na’ima na jujjuya sussages ɗin tace

“ba mun gaisa da asuba ba”

“Haka!” Ta faɗa tana ƙarasawa ta leƙa abinda rahama ke juyawa a wuta kafin tace

“Oshey! ashe gwara da na tashi yanzu” rahama ta harareta tace “ai wallahi ban so kika tashi ba sai mun cinye” yasmeen ta ƙyalƙyale da dariya

“Sannu muguwa, to tun ɗazu ido na biyu” ta faɗa tana jan kujera ta zauna tana kallon Na’ima itama cike da burgewa.

Ita dai murmushi kawai takeyi tana kallonsu dan gasu dai yan biyu amma theyre pole apart kowa da halinsa a cikinsu kamar yadda kamanninsu ma ba ɗaya ba kowa da kamrta.

Sai da Rahama ta sauƙe ƙwan, itama ta sauƙe saussages ɗin kafin Na’ima ta ɗaura milk akan stove ɗin ta dinga zuba cocoa powder da sugar tana stiring har sai da ya narke ya haɗe into a smooth and rich hot chocolate. Ƙamshi ne kawai ke tashi a kitchen ɗin. Ta kalli Yasmeen tace “ur turn, ke sai ki tayamu jerawa a dining tunda mun gama dafawa” Rahama tace “aikuwa kin iya raba aiki” Yasmeen ta miƙe tana gyara hularta ta harari Rahama tace

“and so? Ai wannan dai ba komai bane” Duk sukayi dariya, Na’ima ta ƙarasa tana wanke hannunta a sink, sai da yasmeen ta fara kai golden pancakes ɗin da Na’ima tayi drizzling ɗinsa da honey ta jerasu gwanin sha’awa kafin ta dawo ta kai scambled egg ɗin da ke ta tiriri shima, saussages ɗin da jug na hot chocolate shine ƙarshe tana ajiye shi ta wuce sama, a stairs suka kusa cin karo da Ammi, Ammi na kallonta tace.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved