Chapter 43: Chapter 43
“gulma ne yau ya tashe ki da sassafe kenan”
“Ina kwana Ammi!”
“Lafiya lau” Ammi ta faɗa tana sauƙa ƙasa, Yasmeen ta biyota a baya ƙasa ƙasa tace
“Surukarki ta miki breakfast”
“Ah ah surukarki dai Yasmeen” Ammi ta faɗa murmushi ta escaping lips ɗinta
“Dama fa zuwa zanyi sama wajenki sai ga ki kin sauƙo”
“To yayi kyau!” Ammi ta faɗa tana kallon Rahama da Na’ima da ke tsaye kusa da dining, Na’ima ta ajiye jar ɗin honey akan dining ɗin ko da wani zai so ya ƙara ta ƙaraso palourn ta ɗan tsaya bayan kujera tace
“Good morning Ammi” Ammi tayi murmushi tace
“Morning Na’ima kin tashi lafiya?”
“Lafiya Alhamdulillah” Rahama ta ƙaraso itama tace
“Ina kwana Ammi”
“Lfy lau rahama, ki ce har kun gama breakfast ɗin”
“Anty Na’ima ce tayi” ta faɗa tana kallon Na’ima da kunya duk ya isheta, Yasmeen tace
“Mu mukayi dukanmu” Rahama tace
“To wallahi Ammi yanzu sakkowarta ta samu mun gama”
“Okay! Wa ya jera a dining? No tell me wa ya jera ke kika jera Rahama?” Ko kulata Rahama bata yi ba ta kama hannun Ammi tace
“muje kici Ammi” har dining ta kaita ta ja mata kujera ta zauna, kafin Rahama ta ja wani kujera tana kallon Na’ima tace “anty Na’ima..” ƙarasowa tayi itama ta zauna, yasmeen kam dama ta rigata ma zama kafin Rahama ta zauna bayan tayi serving Ammi, suka soma cin abincin a nutse, Ammi ta ɗan kalli Na’ima dake ɗiban egg a plate, tun randa ta fara ganinta ta burgeta but today Sosai taji ta sake shiga ranta, more especially da bata da duhun kai ko ƙumbiya ƙumbiya irin na surukai, yadda su rahama suke abinsu haka take yi, kamar dai a gidansu take abinta. Kuma bata taɓa tunanin zata iya girki ba ma but ji yadda ta iya abinci mai daɗi sosai. Sunyi nisa a cin abincin Ammi na ta commenting on how delicious abincin is
aka danna bell, mai aiki dake goge goge a palour ta ƙarasa ta buɗe ƙofar, Ahmad ne ya shigo palourn sanye da ƙananun kaya da suka amshe shi ba kaɗan ba da alama bazashi office ba yau ma, kanshi sanye da face cap baƙa, tuni Na’ima tayi stiff da cokalin hannunta da take ƙoƙarin kaiwa bakinta kamar mai jiran ta gama tabbatar da shi ɗinne ya shigo dan ta bashi baya ne amma ƙamshin turarensa tuni ya tabbatar mata shi ne, tana riƙe da spoon ɗin ta juya ta kalli hanyar ƙofa, suna haɗa idanu ta sake spoon ɗin da sauri tare da miƙewa tsaye tana kallonsa, shima dakatawa yayi ba tare da ya ƙaraso sashen dining ɗin ba yana kallonta, Ammi tace “Naima?” Ai ko rufe baki Ammi bata yi ba ganin Ahmad na ƙoƙarin ƙarasowa wajen in a blink of an eye tayi sama da gudu, mayafinta har yana sulewa ya dawo kafaɗarta, duk suka bita da kallo shocked, kamar ya san dama abinda zatayi kenan, saurin bin bayanta yayi ya so ya rigata isa bakin stairs ya tare amma sai ta rigashi, da gudu ta shiga haura stairs ɗin shi kuwa yabi bayanta, Ammi da Rahama da yasmeen duk suka bisu da kallo dan duk sun miƙe ne sun tsaya suna kallon ikon Allah, Yasmeen ta zazzaro idanu amma ta gagara cewa komai.
Wani tsinannen bugawa xuciyarta keyi jin ya biyo ta burinta kawai ta shige ɗakinta ta kulle da makulli amma kash tana ɗaura hannu a handle ɗin da niyyar buɗewa ya iskota tare da riƙota jikinsa ƙamƙam yana faɗin
“Na’ima!”
“Leave me!, leave me alone!” Ta fashe da kuka tana zizzilewa tare da ƙoƙarin ɓanɓare hannunsa daga jikinta, “pls” ta faɗa tana fasa kuka da ƙarfi, muryarsa har rawa take yace
“Why are u doing this? Me na miki baby? Wallahi bansan me na miki ba, u love me remember?i know u do, why are u pushing me away?”
Girgiza masa kai ta shiga yi tana kuka ta shiga dukan ƙirjinsa da hannu bibbiyu dan ra rabu da ita burinta kawai ta bar ganinsa ta shiga ko ina ne ma in dai bazata ke ganinsa ba
“Bana sonka! Ni ka ƙyaleni leave me” ta faɗa da ƙarfi tana ƙoƙarin dambe da shi. Dai dai lokacin Ammi ta hauro saman Yasmeen da rahama na biye da ita dan duk efe efen da takeyi suna jiyota, jin kukan na ƙara ƙarfi ya sa Ammi haurowa ba shiri, ƙin sake ta yayi yana kallon yadda take struggling na ƙwace kanta a jikinsa idanunsa suka kaɗa suka yi ja, tuni kansa ya shiga wani irin sara masa, rahama tana kallonsu har idanunta ya ciko da hawaye tace
“Yaya dan Allah ka ƙyaleta please” but Ahmad couldnt let go, ya sa hannunsa a shoulder ɗinta hannunsa har trembling yake “come back to ur senses pls Na’ima” dakatawa tayi da dambe da take yi da shi ta tsaya tana kallon cikin idanunsa da suka kaɗa har kamr suna yalƙi, kamar wacce ke shirin dawowa hayyacinnata kamar yadda yace sai kuma ta fasa wani gigitaccen ihu wanda yayi daidai da haurowar Salma saman dan tun ɗazu take danna bell amma ba’a buɗe mata ba sai yanzu faty ta buɗe mata tana shigowa ta jiyo ihun hakan ya sa ta nufi saman da sauri itama da kumburarrun idanunta dan ko baccin kirki bata yi ba ganin bata da mafita ya sa ta taho wajen Ammi dan bazama ta fara faɗawa Daddy ba tunda ta faɗa masa Suhaila na gidan friend ɗinta da aka sallama daga asibiti.
da Sauri Ammi tace “Sake ta Ahmad” ta faɗa tana ƙarasowa ta saka hannu da ƙoƙarin cire hannunsa a jikin Na’ima, Tuni Na’ima ta ƙanƙame Ammi ta fashe da sabon kuka, Ahmad ya ɗan ja da baya yana jin kamar jiri ke neman ɗibarsa, Ammi ta rungume ta back tana shafa kanta tace
“Its okay!” Kallonsu kawai Salma take confused, Me Na’ima ke yi a gidan? Like whats happenening babu ma wanda ya kula da tsayuwarta a wajen.
Ɗagowa Na’ima tayi daga jikin Ammi muryarta har bata fita sosai tace “dan Allah ki ce masa ya tafi pls i dont want to see him pls…” sai kuma tayi baya luuu Ahmad yayi saurin matsowa amma kafin ya riƙota ammi ta rigasa, ta sume a jikin Ammi bata numfashi, sosai Ammi ta riƙota jikinta tana nanata
“innalilahi wa inna ilaihi raji’un”
Yasmeen da rahama kam kuka suka kama yi, Ammi ta kalli Ahmad tace
“kwantar da ita kan gadonta bari in kira Malam idris ya zo yanzu kawai yanzu subhanallahi” tana faɗa ta nufi hanyar bedroom ɗinta gabaɗaya hankalinta a tashe yake, Salma ta bi bayanta da Sauri jin ba’asin abinda ke faruwa.
ɗagata caɗak yayi bayan ya karɓeta a hannun Ammi nufi cikin ɗakin bayan yasmeen da ta tsuguna ta ɗauki mayafin Na’ima ta riƙe a hannunta ta buɗe masa ƙofa, ya kwantar da ita akan gado ya zauna a gefen bed ɗin bayan ya ajiye wayarta da ya kawo mata a gefen bed ɗin saboda yadda Mami da fadila har da big daddy suka kikkkirata shi kuma ya gagara picking calls ɗin, riƙe hannunta yayi ya kai hannun fuskarsa kawai ya lumshe idanunsa yayi shiru, only he knows what zuciyarsa is going through!, the pain! he cant explain it.
Su yasmeen duk suka tsaya cirko cirko a ɗakin suna kallon yayannasu. Ammi bata jima sosai ba ta dawo ɗakin Salma na biye da ita a baya, Ammi ta ɗan kalli Ahmad tace
“Malam na hanya yanzu!” Gyaɗa mata kai kawai yayi amma ya gagara tashi a wajen, itama Ammi matsowa tayi ta zauna a gefen bed ɗin, salma ta ɗan taɓe baki dan Ammi tace mata suma basu san me yake damun Na’imar ba haka kawai take misbehaving idan taga Ahmad a zuciyarta tace kaɗan ma suka gani.
Ɗakin shiru, like too Quiet, Sadiq na zaune akan gadonsa ya jingina bayansa da jikin cream wall dake cikin ɗakin, ya ƙurawa window dake ɗan moving a hankali, ɗakin sanyi ƙalau saboda Air condition dake kunne, hasken rana da ke ɗan shigowa kaɗan kaɗan daga jikin window ɗin yana haske ƙasan ɗakin da yake nan ƙal ƙal, kwata kwata wajen baiyi kama da asylum ba rather a hotel. Saboda private suit ne dake ɗauke da banɗakinsa a ciki harda bookshelf half filled da littatafai harda tv a ɗakin. Amma to sadiq Non of it really mattered, tunda yake ɗakin ko sau ɗaya bai taɓa kunna tv ba, ko kusa da book shelf ɗin bai taɓa zuwa ba, dan dole sometimes yake taɓa abincin da suke kawo masa ko herbal teas da suke kawo masa kullum kullum. Haryanzu akwai scar kaɗan na dukan da ahmad ya a goshinsa amma bayannan ya wawwarke sai abinda baza’a rasa ba.
Nurses ɗin lallaɓasa suke kamar yaro ƙarami wanda hakan ke sake soya masa ransa, kullum suka tsaya kansa da wannan hopeful smile ɗin nasu saying “good day Sadiq” ji yake kamar ya tashe ya kashe dukansu, haka zasu ajiye medications ɗinsa a bedside su ɓalla su basa, ko gardama baya yi da su yake karɓa ya saka a baki amma maimakon ya sha sai ya danne a ƙarƙashin harshensa ya sha ruwa, suna fita yake tofarwa a tissue ya yar a tsakar ɗakin.
Doctors da suke zuwa wajensa kullum tambayarsu baya wuce
“Whats ur name?
How’re u feeling today?”
Would u like to talk?”
Bai taɓa amsawa ko ɗaya a cikinsu ba,ko kallonsu ma baya yi, zuwa yanzu sun fara zama frustrated yau ma suna fita daga ɗakin ɗayan doctor ɗin ya kalli ɗayan yace
“Bana tunanin we can break through cause he doesnt wanna come back” shiru ɗayan yayi cause gaskiyar maganar kenan! Baya son dawowa dai dai, baya son treatment ɗin shiyasa baya basu haɗin kai tunda aka kawo shi bai taɓa cewa kowa ci kanka ba kwana 5 kenan he’s not violent kamar sauran mahaukata amma kuma he’s not responsive.
Nurse ɗin da ta kai masa Abinci ce ta haɗu da doctor musa a hallway da fari tass ɗin coat ɗinsa yana riƙe da shi a hannunsa ɗayan hannun da file, yana ganinta yace
“Fatima how was he today?”
Ta sauƙe ajiyar zuciya tace
“same, yanzu kam ma ya bar ko kallona” file ɗin sadiq ne dama a hannunsa ya ɗanyi shiru yana kallonta kafin ya buɗe file ɗin yana flipping da duba growing report na Sadiq, ko wani page iri ɗaya ne da na baya wato he’s non verbal, refusing therapy, eating little, babu aggression kuma babu progress. meaning babu improvement at all ya girgiza kanshi a hankali ya dube ta yace
“we’re wasting time gaskiya idan muka cigaba da d same method babu abinda zamu samu”
Matron dake bayan desk ta ɗago ta kalli Dr musa tace
“to ya zamuyi da shi kenan?”
Rufe file ɗin Dr musa yayi yace
“mu jira Dr Zarah ibrahim, ita kaɗai ce inaga zata iya handling case ɗinsa gaskiya”
Nurse Fatima tana kallonsa tace “the trauma specialist? Wanda bata jima da dawowa daga abroad ba?”
Firmly Dr musa yace “eh ita! Next week zata dawo until then a rabu dashi, no more forcing sessions, kawai a dinga monitoring ɗinsa a tabbatar he’s stable, He’s hers to handle”
Matron ɗin ta gyaɗa kai tace “okay Sir”
Ammi na zaune a gefen bed ɗinta tana ta kallon Salma dake zaune kan kujera tana share idanunta, ita kanta she’s shocked with abinda Salma ta gama faɗa mata game da Suhaila, tun bayan tafiyar Malam idris Hankalinta ke matuƙar tashe dan ya tabbatar da sihr ne a jikin yarinyar ba aljanu ba, amma sosai ya kwantar mata da hankali kafin tafiyarsa ya kuma tabbatar mata komai ya zo ƙarshe, kuma kamar yadda ya faɗa Allah subhanahu wa ta’ala ya faɗa cikin alƙur’ani mai girma
“Wa nuzzilu minal Qur’ani ma huwa shifa’un wa rahmatun lil mu’mineen…”
“Kuma Mun saukar daga cikin Alƙur’ani abin da yake magani da rahama ga muminai….” Tabbass alƙur’ani waraka ce, kuma babu wata matsala da ba’a bamu solution ɗinta a cikinta ba, saboda haka ya sa aka kawo masa bowl da ruwa yayi reciting suratul fatiha, ayatul ƙursiyyu da falaq da Nass, ƙarshen suratul baƙara wato amanarrasul da sauran ayatusshifa’a kamar suratul taubah aya ta 14, suratul yunus aya ta 57, suratul Nahl aya ta 69, suratul isra’i aya ta 82, suratul shu’ara aya ta 80, da kuma suratul fussilat aya ta 44 da sauran addu’o’i kamar “Allahumma rabbannas, adhhibil ba’asa, ishfi anta ash shafi, la shifa’a illa shifa’uka, shifa’an la yughadiru saqaman” Da dai sauran Addu’o’i ya bata ta sha aka kuma shafa mata, sannan yace a dinga mata haka ana bata tana sha tana kuma shafawa,kuma a nemi ganyen magarya da na kuka ko ɓaure ko Neem a tafasa su a haɗa da karanta ruqya a ciki, ta dinga wanka da shi da shan kaɗan kullum in sha Allah it will all come to pass, sannan ya sake jaddada musu su dinga karanta suratul baqara a gidan idan ma bazasu iya karantawa da baki ba su kunna shi, hadisi ne ingantacce wanda manzan Allah ke cewa
“Laa taj‘aluu buyootakum maqabir, inna ash shaytaana yanfiru minaal bayti allathee tuqra’u feehi Sooratul Baqarah” ma’ana
“Kada ku mai da gidajenku kamar ƙaburbura. Lallai shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Suratul-Baqarah a cikinsa.” Sosai hankalin Ammi ya ɗan kwanta duk da yace ba lallai ta warke farar ɗaya ba a cigaba da mata zai iya ɗaukarta 3 to 7 days ko fiye ma da haka depends on yanayin sihr ɗin Allahu a’alam, waraka a hannun Allah yake in sha Allah komai zai wuce, kuma idan Ahmad ɗin zai iya ya bata space har ta gama maganin in sha Allah da zarar ta gama shikenan kuma.
Hakan ne ma yasa bayan tafiyarsa har Ammi ta samu daman sauraren Salma only for her to tell her another tashin hankali. Ammi ta sauƙe ajiyar zuciya tana kallon Salma tace
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, kin gani ko Salma? Duk abinda nake faɗa miki bakya ji, kwanannan har gaba kika yi da ni kika bar ɗaga kirata kika bar zuwa gidannan duk akan suhaila, ko da yake ba yau kika fara wannan ba akan mahaifinta ma kinyi haka, gaba da ni ba sabon abu bane a wajenki tunda kinyi har da mijina wanda yake kamar matsayin uba a wajenki Salma shiyasa bai dame ni ba sam, akan Auren Ahmad da Na’ima babu irin ɓatancin da baki faɗamin akan yarinyarnan ba now u see ga yarki ta kiraki tayi akan kunnenki, ni na ma rasa me zance, kince baki san ƙasar da take ba ta ina zamu fara nemanta?”
Salma ta sauƙe ajiyar zuciya tace “Ni dan Allah anty Mami idan muna maganar da ta shafe mu ki bar sako Na’ima a ciki, na zo na same ki ne saboda bani da wanda zan faɗama, bazan fara faɗawa Daddynsu ba tunda tun farko na masa ƙaryar ga inda take”
“To miye anfanin ƙaryar da kika masa? Kenan ma da ɗaurin gindinki take kwana duk inda ta ga dama, sai dan ta bar ƙasar kuma sai ya miki zafi Salma? ke fa kika bata license ɗin yin duk abinda take yi, nan gidan da ta zo ta zauna da ta tashi tafiya ko sanin tafiyarta banyi ba saboda na hanata rawar gaban hantsi tana ganin kamar an saka mata idanu” Shiru Salma tayi tana kallon Ammi, baƙin ciki kamar zai kashe ta dan maganar ɓata mata rai kawai yake.
Ammi ta sauƙe ajiyar zuciya tana miƙewa tsaye tace
“zan yi ma Ahmad magana in ga ko akwai abinda zai iya yi a kai in sha Allah, Allah dai ya kyauta” daga haka ta fita a ɗakin ta bar Salma zaune tana binta da wani irin kallo har Ammi ta fita kafin ta ɗanyi ƙwafa ta miƙe ta nufi ƙofa itama.
Shiru Fadila tayi tana sauraron Nasir da ke faɗa mata halinda ake ciki, hankalinta yayi masifar tashi, dan duk kiran da suke ma Na’ima har yanzu ba na wanda ta ɗaga at first fadila da ta kira Ahmad yace mata ai Na’ima na bacci so sai ta ɗauka tsabar soyayya ce yasa bata da time ɗin picking calls ɗinsu, but Now Nasir is telling her something else, cike da damuwa tace
“Babe ban gane ba”
“Miyene baki gane ba a ciki? Ahmad told me imam ɗin yace sihr aka mata, wlh he’s very disturbed ni kaina hankali na ya tashi wa zai mata sihiri just 10 days da aure? Yanzu haka tana gidan Ammi ita Na’imar, she’s not fyn gaskiya”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un na shiga uku ni fadila” ta faɗa tana jijjiga inaaya da ke kafaɗarta, katse ta yayi dan yasan halinta da yadda take saka ma kanta damuwa too much yace
“Look baki shiga ukun komai ba, na riga na duba available flights for tomorrow morning kawai ku dawo gobe ba sai next week ɗin ba dama nayi kewarku da yawa” ya faɗa trying to make her calm down dan yasan yanzu haka in hankalinta yayi dubu to ya tashi duka
“Toh… Allah ya kaimu zanje in sanar ma Mami in sha Allah, duk kuma wanda yayi ma dis innocent girl wannan abin Allah ya isa wallahi on her behalf” ta faɗa tana kashe wayarta dan babu wanda zuciyarta ke raya mata face Amira.
Washegari Nasir da kansa yaje ɗaukosu daga Airport, bayan ya saka luggages ɗinsu a mota ya bata side hug ya karɓi inaaya daga hannunta ya ɗaurata a kafaɗarsa tare da riƙe hannun fadila da hannu ɗaya suka nufi mota, gabaɗaya ta ƙosa ta ganta a gidan Ammi ta ga yanayin jikin Na’imar, shi dai Nasir tuƙi kawai yake yana satan kallonta ganin yadda duk damuwa ya nuna a fuskarta dama yasan za’a rina.
Ɗan riƙo hannunta yayi yace “ko muje gida ki huta” ta wani kalleshi hakan yasa yayi dariya da bai shirya ba
“Calm down mana, ke she’s fyn fa its not like she’s sick or something, ita abinta da mijinta ne kaɗai”
Fadila tace “to ai ba lafiyan kenan, ba gwara to tayi da kowa ba akan mijinta kuma”
“Hakane” ya faɗa a hankali yana matsa hannunta dake cikin nasa bai sake cewa komai ba, ya maida hankalinsa akan tuƙi har suka iso gidan Ammi, Tana sauƙowa a motar da inaya a kafaɗarta ta nufi cikin gidan tana ɗan riƙe jikin tsadaddiyar abayar jikinta, ta ƙarasa bakin ƙofar ta danna bell ta tsaya tana jira a buɗe mata.
Na’ima da rahama na zaune kan carpet, Na’ima na taya ta cike wani form karatun alƙur’ani na tashi a hankali a speakers ɗin palourn, yasmeen kuma tana sama wajen Ammi, aka danna bell ɗin duk suka kalli ƙofa, Na’ima zata miƙe rahama ta rigata
“Bari na buɗe” gyaɗa mata kai Na’ima tayi ta cigaba da cike mata kafin ta dawo, kamar ance ta ɗaga kanta da biro a hannunta kawai ta kalli Fadila da ta tsaya daga bakin palourn tana kallonta, wani kalan zaro ido tayi ta cillar da biron tare da miƙewa da gudu ta nufo fadila, fadila ta rungume ta back dan tun a bakin ƙofa Rahama ta karɓi inaaya, maƙalƙaleta tayi tana murnar ganinta, fadila ma tana dariya tace
“Kai nayi kewarki da yawa Na’eematu” ta faɗa tana ɗagota daga jikinta tana kallonta ganin idanunta har ya ciko da hawaye, ta dinga kallonta, tana sanye da abaya black ta ɗaura scarve a kanta looking fresh kamar ko yaushe ita bata ga alamun rashin lafiyar komai a tattare da ita ba ko da yake she look a little pale amma its not much she still looks calm and very beautiful kamar kullum.
Rahama dai na tsaye gefe da inaaya tana dariya tana kallonsu, Na’ima tace
“Anty fadila shine baki kirani ba kince zaki zo wait yaushe ma kika dawo lagos?” Fadila ta harareta
“A ta wani waya zan kiranki? Wayar da baki ɗagawa? Duk kin ɗagawa mutane hankali ” Rahama ta karɓe da faɗin
“La ba laifinta bane fa anty fadila tunda yaya Ahmad ya kawo wayar Saif ya saka a ruwa mistakenly” ita dai Na’ima Shiru tayi tana kallonta,
Fadila tace “i hear u Rahama muje in gaida Ammi” Rahama tace “okay” tayi gaba Fadila ta bi bayanta hakan yasa Na’imar ma tabi bayansu itama.
Kallon Nuwaira kawai Mary keyi bayan ta buɗe mata ƙofar palourn da take ta dannawa ba ƙaƙƙautawa kafin tace
“Ina kwana Ma” ko kulata Nuwaira bata yi ba ta wuce ta ta shigo palourn ta wuce sama abinta ba tare da ta tsaya a palourn ba, Amira da ta fito daga ɗakinta kenan da niyyar sauƙa taji mai danna bell haka ganin Nuwaira ta ɗan ja tsaki
“Haba Nuwa wannan wani kalan danna bell ne kamar yaƙi”
“To wa ya sani ko yaƙinne?” Ta faɗa tana ƙarasawa cikin palourn saman ta zauna a kujera tana kallon Amira da itama ta ƙaraso tana faɗin
“Ai kuwa in yaƙi ne ba’a gidana ba”
“Sannu mai gida, tell person wey no get house abeg” Nuwaira ta faɗa tana ciro wayarta a jaka ta na tattaɓa screen ɗin da fingers, Amira tayi dariya
“Gidan miji ai nake magana ba gidan kai ba” Nuwaira ta bata wani side eye sai dai bata ce komai ba. Amira ta gyara zamanta tace
“Sai gaki yau a gidannan, rabonki da gidanna fa kin daɗe Nuwa” harararta Nuwaira tayi ta ajiye wayar a gefenta tana kallon Amira tace
“Saboda baƙin halin mijinki ba? Yanxu ma ji nayi bazan iya ba na zo na ganki tunda kwana 2 kin maƙale a gida kamar matar kulle, sai dai idan ya zo ya same ni a gidansa yayi abinda ya ga dama amma dole na zo naga ƙawata” tana gama faɗin haka ta hau ƙwallawa Mary kira da ƙatuwar muryarta
“Mary!!!!!, Mary!!!” Amira ta tsaya kawai tana kallonta kafin ta ɗanyi tagumi fuskarta na nuna damuwa tace
“Ai zaki tafi kafin ya zo bazai ma same ki ba, nikam gwara da kika zo Nuwa, ina cikin damuwa wallahi tallahi” Nuwaira ta dakata da kiran mary da takeyi tace
“Damuwar me? Ba kinyi yadda Mummy tace ba and kince the result is perfect” ta faɗa tana mayarda hankalinta duka kan Amira
“Which kind perfect? Ni da na san haka abinnan yake gaskiya bazanyi ba, ba na faɗa miki da muka je sunce bazai yiwu ayi ma Albi ba dan ko an masa bazai daɗe a jikinsa ba zai karye maybe kafin ma aikin ya fara ƙarfi zai karye shine yace sai dai ayi ma Na’imar ba” Nuwaira dake kallonta tace
“Uhum haka kika ce sai aka yi yaya ba hakan aka yi ba?”
“To Nuwaira anyi kuma ya kama Na’imar dan anan part ɗin nawa ma har rashin kunya ta masa ta ja masa tsaki, ni na san kwana biyu da sukayi a part ɗinta basu da kwanciyar hankali sam, shekaran jiya da sassafe naga ya fita maybe faɗa sukayi ohon masa, jiya kinga anan ya kwana amma wlh ko bi ta kaina bai yi ba kuma yau ma anan zai kwana amma Nuwaira ni na san ba zai wani kula ni ba, ko magana na masa a taƙaice yake amsawa, abubuwannan sun saka sa a damuwa ko bacci baya yi sosai, ni gaskiya ba haka nake so ba, duk abubuwannan memakon ya dinga jin haushin Na’ima ya san value ɗina amma inaa drifting ɗinmu kawai yake further away from each other” Nuwaira da ke kallonta tace



