Chapter 44: Chapter 44
“So yanzu ya kenan?” Amira ta sauƙe ajiyar zuciya
“Zan kira mummy ta kira a karya abin kawai, akwai other ways na fitar da ita a gidannan da yawa amma dis one is not helping me in anyway, ni shiyasa tun farko bana wani son zuwa wallahi”
Nuwaira ta koma ta kishingiɗa tana jan tsaki
“Dont start with that ur bullshit pls na wani baki son zuwa, ke dai kawai kinbi mamarki kunje inda ba’a wani iya aiki ba, kawai na zuba miki ido ne dama inga iya inda aikin zaije, yanzu wanke ƙafarki zakiyi mu koma wajen Baba shi yayi aiki akan Ahmad ɗin duk uban taurin kansa wlh bai isa ba”
Wani kallo kawai Amira ke mata, kafin itama ta ja tsaki,
“Ke ni wallahi ba gurin ko wani Malamin da zan sake zuwa, wanann ma ya isheni, ba abinda na so ya faru ba kenan kuma shima mutumin bai ce min Albi zai fita hayyacinsa saboda yarinyar ba da bazan yarda ayi ba, to kafin ayi aikinnan ma nuwa nafi gane kansa akan yanzu, yanzu banda shiru shiru da miskilanci babu abinda ya ƙaro, yayi ta haɗe rai dama can yaya lafiyar kura? Gaskiya ni ba haka nake so ba.”
“To tunda bazaki je ba shikenan kar ki sake cemin Ahmad ya miki kaza ko kaza, its soyayya dat will kee u Amira”
“Naji” Amira ta faɗa tana ƙoƙarin kwanciya akan kujera, Nuwaira ta tashi zaune da kyau tana kallon Amira tace
“Ami tashi ki zauna kiji, nima fa damuwata na kawo miki, nima ina cikin problem na rasa yadda zanyi da shi” Amira ta miƙe zaune tana kallonta tace
“Matsala kuma Nuwa” Nuwaira ta gyaɗa mata kai a hankali kafin ta janyo wayarta ta ɗanyi taɓe taɓe sai kuma ta ajiye wayar ta mayarda duka hankalinta akan Amira tace
“Amira ciki ne dani” kallonta kawai Amira take yi not so suprised kafin ta ɗage gira tace
“And?” Ganin Nuwaira nata kallonta tace “Na waye?”
“Hmm” kawai Nuwaira ta faɗa, Amira ta koma ta kwanta tana faɗin
“Kin saka na tashi zaune na zata wata magana mai muhimmanci ce to ciki nawa kika yi kika zubar Nuwaira whats special about wannan”
“Its special cause am keeping it” Amira ta ƙura mata idanu daga kwance da take tana kallonta with suprise kafin tace
“Zaki ajiye kuma Nuwa?”
“Yes” Amira ta tashi zaune tana kallonta tace
“Waye baban cikin?”
“Zan faɗa miki, amma yanzu kinsan he’s denying wai ba nasa bane, ni kuma aure nake so nayi kuma shi nake so na aura”
“Lallai ma kamar ya ba nasa ba, ai wlh dole ya karɓi ciki ya ma isa yace ba nasa ba ai tunda kika ce nasa ne to nasan ne, kuma girl if u feel kina son aurensa and keeping the baby am with u 100 percent, wallahi ki auresa, amma saurayine ko bazawari?”
“Da matarsa fa harda yarsa babba, amma do i care?”
Amira ta karɓe da “we dont” suka yi dariya tare, Nuwaira ta koma ta kishigiɗa tana shafa cikinta tace
“Idan ma blackmail bai isheshi ba yanzu zan kai sunansa wajen Baba, ke ko zaki amso min lambar malamin mummy in haɗa har da shi?amma kar kice mata ni ke nema”
“Baki da matsala zan karɓo miki ki ci ubansa, dama Allah Allah nake kiyi aure Nuwa”
“Aikuwa lokaci yayi in sha Allah Aminiyas” suka sake yin dariya kafin Nuwaira ta janyo wayarta ta tura ma daddyn Nuwaira voice ɗin da take recording, ta sake tura masa
“Ko in faɗa mata sunan?” Da emoji ɗin gwalo, tana tura masa ta ajiye wayar tare da miƙewa ta zare heels ɗinta tana nufar downstairs tace
“Bari inje inci uban Marynki ɗinnan dan uwatta bata ji ina kiranta bane?” Tana faɗa ta fice a palourn ta nufi ƙasa, ko minti ɗaya bata yi da sauƙa ba wayarta ta fara ringing Amira ta tashi zaune tare da kallon wayar taga
“Sugar Daddy” da love emoji, har kiran ya katse ya sake kira tana kallon wayar, haka ya dinga kira ba ƙaƙƙautawa hakan yasa ta fara tunanin ko shine uban cikin Nuwairaa?
Miƙewa tayi ta ɗauko wayar ta koma ta zauna tana Sliding call ɗin tayi picking ta kai wayar kunnenta tana gyara zamanta a kujera.
Muryarta cike da confidence tace “hello?” dan ba Yau ta Saba magana da Alhazan Nuwaira ba, Jin ƙarar yanke kiran immediately, yasa da mamaki ta ciro wayar daga kunnenta tana kallon screen ɗin, ta ƙurawa hoton Nuwaira dake kan screen ɗin idanu ta sha make up da attach tana zaune gaban mota da wata shirt blue, fingers ɗinta all 5 da ta ma kwalliyan black nails dogaye ta cika su da rings ta wani zaro harshe a selfie ɗin, kwata kwata kamar bata haɗa komai da musulmai ba , right above hoton kuma notifications ne na kiran da sugar daddy ɗin ya mammata har guda 4, swiping tayi zata buɗe lock ɗin wayar taga Nuwaira ta canza password ta ɗan tsaya jim kafin ta kalli hanyar stairs, dai dai lokacin Nuwaira ta hauro da plate na abinci a hannunta tana tauna wanda ke bakinta tace
“Ni wai miye Mary ke miki a gidannan? Ina saboda Saif ne kuma zuciyarki ta mutu kin barwa yan uwan ubansa shi, ta faɗa tana sake kai another spoon of rice bakinta ta ƙaraso ta zauna a kujera, sai a lokacin ta lura da wayarta da ke hannun Amira, ita dai Amira sai kallonta take, Nuwaira ta ajiye plate ɗin a gefen kujera tace
“Whats up?” Ta faɗa tana kallon Amira da abinci a bakinta da ta dakata da taunawa Zuciyarta na wani irin azababben bugawa, wani tsautsayi ne ya aiketa barin wayarta anan? Ta tabbata zai kikkirata, ta banu kar dai ya kira Amira ta ɗaga, miƙa mata wayarta Amira tayi tana faɗin
“Ana ta kiranki” Nuwaira ta saka hannu ta karɓa tana haɗiye abincin bakinta ba tare da ta gama taunawa ba tace
“wani tsinannen ke kirana, ni fa jaraba ce bana so” ta faɗa tana satar kallon Amira to see her rection amma sai taga komawa ma tayi ta kwanta tana faɗin
“Ki duba mana wani wai sugar daddy, ai har na ɗaga ya katse kiran hala shine wanda kike son auran ko wani ne daban?”
Nuwaira da ke ta danna wayarta ta share goshinta tace
“shi ne”
“to akan me ya kashe waya dan na ɗauka? ko bai san kina da Aminiya bane?”
“Shi kuwa yafi kowa sani, bai san ke bace da ba zai kashe ba ko da yake zai iya sani ma ya kashe kinsan yanzu haka ba kiran arziki ya min ba, ba na ce miki we’re not on the same page da shi ba akan cikin? Kullum cikin bura’uba muke da shi akan cikin, probably shiyasa da yaji muryarki ya kashe kinsan muryarki da tawa ba ɗaya ba na fiki babbar murya”
Amira ta ɗan yi dariya tace
“ai ni so nayi in ji dalilinsa na ƙin karɓar cikin bayan ya zage ya kwashi harka dan rainin sense” Nuwaira ta janyo jakarta ta mayarda wayar ciki bayan ta saka a silent ta janyo plate ɗin abincin ta cigaba da ci tana faɗin
“Ke ba fa shi da dalili, dalilinsa bai wuce baya so yayi ma matarsa kishiya ba kuma na faɗa miki yana da babbar ƴa kamar uwar da ƴar sun shanye sa ke kamar ma tsoron uwar yake, shiyasa ni kuma na rantse sai na auresa in ga ƙwal uwar daka, ke ni fa da ba ma shi na so aura ba mijin yar wallahi na so aura sai kinga yadda ya haɗu over amma guy ɗin bashi da mutunci ji yake kamar ya kashe ni tsabar tsanata shiyasa na canza akala na bi wanda zai fishsheni”
Amira ta dinga kallonta kafin tace
“kina da grudges da ʼyar ne baki bani labari ba? Me ta miki da kike ta son shiga rayuwarta toh” Nuwaira ta harareta tace
“Au wai ban faɗa miki yarinyar da muka haɗu a guess house ɗin Alhaji saminu ba ta kusa cire min gashin kai?” Amira na kallonta tace
“Itace?” Eh mana itace,
“To me ya kaita da aurenta?” Amira ta faɗa tana kallon Nuwaira, Nuwaira ta ja wani dogon tsaki,
“to matan aure nawa ke harkar wai aka ce miki, dan bakya yi doesnt mean wasu basa yi, kuma lokacin bata yi aure ba daga baya ne tayi auren bata jima da yin auren ba ma it was all over social media, i’ll send u video ɗinta da mijin ta insta”
“But girl it wasnt that deep ba kema kin yaga mata fuska ba da Nails har station fa Alhaji saminun ya kaiku?”
“Bura’uba! amma bakya kishi na Amira, wata ʼyar shegiya ta min duka in tashi ɗaukar mataki kice its not that deep?”
“Ta miki duka ko kuka ma juna?”
“To itama ta auri ubana a inda ta gansa tunda ba mijine da ni ba, amma na kusa nayi mijin wato ubanta, ke mu bar maganar nan ɓata min rai take”
ta faɗa tana ajiye plate ɗin da ta cinye abincin ciki tass ta zaro tissue ta shiga goge hannunta da bakinta. Amira na daga kwance tace
“Amma dai babannata ma kwarto ne, babban banza”
“Idan kika ce kwarto kin rage Amira yadda kika san maye, sai ma awajen harka zaki san asalin tantiri ne sai dai kinsan idan ta nan ɓangarenne babu wanda ya kaini tantiranci hajiya ” Amira ta ƙyalƙyale da dariya tace
“Shegiya muguwa” Nuwaira ma dariya tayi sosai tace
“Baki faɗa da gatse ba Wallahi Allah ni kaina har tsoron muguntata nake” Amira na dariya tace
“Wanda bai sanki ba bai more ba Nuwa, nto bani labari in details yadda nake baki malama dont go through corners”
Nuwaira ta taso ta dawo kujeran da Amira take tana faɗin “yanzu kuwa…”
Sadiq na zaune a gefen gadonsa yana kallon sunrays kamar dai kullum, tunda yayi sallah yake zaune a wajen, ji kawai yake rayuwar ma ta ishe shi, he hate everybody including himself, tunani kala ke crossing mind ɗinsa wanda rabinsa na Na’ima da Ahmad ne.
Turo ƙofar ɗakinnasa da akayi bai saka ya ko kalli ƙofar ba, har suka shigo cikin ɗakin, Senior doctor ɗin da ke gaba ya ɗan kalleta kafin ya ƙarasa cikin ɗakin, ya tsaya a gefen bed ɗin yace
“Mr Sadiq” ko kallonsa bai yi ba, ya ɗanyi murmushi kafin without minding rashin amsawar tasa yace
“your new doctor is here, she’ll be taking over ur case, say hi to Dr zahraah ibrahim”
jin ko bi ta kansu bai yi ba ya sa doctor Zahrah dake tsaye a bayan doctor tana kallonsa ta ɗan zagayo ta gabansa tana kallon face ɗinsa fuskarta ba yabo ba fallasa tace
“Good morning Sadiq” ɗaga idanunsa yayi da sauri ya kalleta jin accent ɗin da tayi anfani da shi wajen maganar, ya zuba mata idanu yana kallonta kamar yadda itama shi take kallo da manyan idanunta da suke nan farare ƙal babu ko ɗigon kwalli a cikinsu, bata da tsawo sosai amma kuma bata sahun gajeru sam infact zama a iya kiranta mai tsawo kawai dai ba can can ba, tana sanye da blouse cream colour sai tailored wando navy colour da tayi tucking blouse ɗin neatly a cikin wandon, a saman kayannata kuma fari ƙal ɗin doctors coat ne, ta ɗan naɗe sleeve ɗin da hakan ke nuna silver watch dake ɗaure a fari ƙal ɗin tsintsiyar hannunta, for once kamar wanda idanunsa suka masa gizo gani yayi kamar Na’ima ce a tsaye a kansa cause from their body to their height to their voice its almost all the same, sai dai wannan tafi Na’ima haske sosai amma a idanunsa babu wacce zata fi Na’ima kyau, ta kai hannunta ta gyara soft grey jersey veil dake naɗe a kanta da tayi pinning ɗinshi perfectly ya fito da asalin round fuskarta mai matuƙar kyau, ɗauke kansa yai ganin yadda take kallonsa da manyan idanunta haka kawai yaji bata masa ba cause she’s too confident he can see dat in her eyes, yadda ta ɗauki kanta with quite elegance yasa yaji he’s irritated at her haka kawai,
ya mayarda hankalinsa inda yake kallo ba tare da ya amsa gaisuwartata ba, wani guntun murmushi tayi da ya tsaya iya lips ɗinta ta kalli senior doctor ɗin shima murmushi ya mata kafin yace
“best of luck doctor” ta gyaɗa masa kai a hankali, yana faɗin haka ya nufi ƙofa ya fita, Zahraah ta bishi da kallo har ya janyo musu ƙofa kafin without saying anything to sadiq ta ƙarasa gaban kujera dake can gefe a ɗakin kusa da book shelf ta janyo kujerar har gabansa ta ajiye few feets kaɗai away from gadon da yake zaune ta zauna tana ajiye notebook ɗin hannunta akan cinyarta tana kallonsa da Nazarinsa tace
“So how’re u Sadiq” ku da bakwa wajen, dan ko kallonta bai yi ba kamar bai san da shi take magana ba, tayi shiru tana kallonsa, sai yanzu taga dalilin duka complaints ɗin da ake yi akansa tun zuwanta asibitin, a zuciyarta tayi wata murmushi, aikuwa inda taurin kai ne gidansa yazo duk taurin kansa ta fishi, taji da patients da suka fisa ma taurin kai basu girgizata ba duk da ƙananun shekarunta.
“Okay, baka son kayi min magana? To ni bari inyi maka, Sunana Dr zahraah Ibrahim, ni ce likitar da zata cigaba da kula da kai har Allah ya baka lafiya sadiq, i hope u’ll cooperate mu samu mu rabu da wuri, mind u its ur choice whether to speak or not, dan kaga i wont push but ull see me anan every morning har sai randa ka yanke shawarar kana so muyi magana, 1 thing i want from u is ur trust and i’ll get u out of here”
Tayi shiru tana kallonsa waiting for him to response, amma shiru dan ko kallonta ma baiyi ba, tayi shiru ta zuba masa idanu kawai tanaɗan clicking pen ɗinta a jikin note book ɗin amma har sannan bai ce mata komai ba bai kuma sake kallonta ba tun kallon farko da ya mata, kusan minti 5 ya wuce tana zaune tana kallonsa shi kuma yana kallon wani wajen daban, jin har sannan tana nan bata tafi ba ya ya ɗan ɗago idanunsa ya kalleta suka haɗa idanu ta ɗan masa murmushi kamar dai shirunnasa shi ya kawota dama ya ɗauke kansa yana mamakinta, ta wani zauna kamar stone tana kallonsa inda wasu ne da sun zama frustrated already sun ƙara gaba abinsu, idan taurin kai take ji zai nuna mata ya fi ta taurin kai he wants to see yadda zata sa shi yayi magana idan ana dole, itama kallonsa kawai take same tunani ke yawo a zuciyarta, seems like taurin kansa ya wuce yadda aka bata labari but zata nuna masa ta fishi taurin kai.
Half an hour ya zo ya wuce tana zaune yana zaune babu wanda ya sake cewa uffan, occasionally yake satan kallonta kuma a ko wanne sai sun haɗa idanu, agogon hannunta ta kalla ganin its almost an hour ta miƙe tsaye tana smoothening jikin coat ɗinta tace
“Alright Sadiq, enough for today sai na dawo gobe okay?” Bata jira amsarsa ba ta juya ta nufi ƙofa, sai a lokacin ya juya ya bita da kallo har ta fita ta ja masa ƙofar kafin ya sauƙe ajiyar zuciya ya hau saman gadon da kyau ya kwanta ya lumshe idanunsa deep in thought. Muryarsa ƙasa ƙasa yace “Na’ima…”
Kun jini shiru am so sorry ina asibiti yau, har yanzu ma am posting this for u all from there, jiki da jini sai a slow, but Alhamdulillah, i had to type for u guys even if its not much, cause the amount of love for this book is massive wallahi, messages from left, right and center akan posting, ban samu daman editing ba cause am not too comfortable so pls cope with me thank u all❤️
Kwana 5 suka zo suka wuce rolling kamar heavy clouds, jikin Na’ima Yayi sauƙi sosai duk da dama can bata da wata problem da jikinta sai da ganin Ahmad kaɗai, a kwanakinnan da take gidan Ammi ba ƙaramar shaƙuwa bace ta shiga tsakaninta da Rahama, Yasmeen har ma Ammi da take jinta har cikin ranta, ba’a ma maganan Saif dan shi dama tun can mutuminta ne, sosai ta sake jikinta a gidan bata da damuwar komai, kullum Ammi da kanta take bata magungunanta ta sha tayi wanka ta shafa mata na shafawa, duk Yadda Ahmad ya so janye jikinsa har sai taji sauƙi kasawa yayi, duk da haryanzu kullum yazo bata ko shiga harkarsa infact ko magana ya mata bata amsawa shima sai ya rage mata maganar baya forcing conversation sai dai kawai ya zauna yayi ta scrolling a wayarsa idan ya gaji ya tashi ya bar gidan. Yanzu kwata kwata ta bar wannan guje guje da ife ifen, wanda its a sign of recovery. Bayan Fadila ma har daddynta ya zo har gidan ya ga jikinta shima duk da basu yi wani magana mai tsawo da shi ba amma sosai lamarinsa ya tsaya ma Na’ima a rai dan ganin yadda he look pale and thin lokaci ɗaya kamar wacce ta daɗe bata gansa ba, ko da ta tambayeshi kuma ko he’s sick sai ce mata yayi he’s fyn but ita tasan he’s not, amma sai bata takura ba.
Tana zaune akan gado tana sorting kayanta da aka dawo musu da shi daga laundry, Saif kuma na kwance akan gadon yana bacci dan baya jin dadi bai jima da dawowa daga sch ba da guntun zazzabi hakan yasa ta shiryashi ta bashi magani tun sannan yake bacci, yasmeen da Rahama na ƙasa a kitchen suna girki tare da Fati, ajiye rigar hannunta tayi ta miƙe ta ƙarasa jikin window ganin yadda iskar hadari ke kaɗa thick labulayen ɗakin, ta ɗan matsar da labulayen tana kallon garin da ya haɗe da hadari, tuntuni dama hadarin ke ta haɗuwa amma har yanzu ruwa bai fara sauƙa ba sai iska da kuma lum da garin yayi alamun ruwa na daf da sauƙa, this is her favourite weather tana ƙaunar ruwan sama sosai, hakan sai ya tuna mata da Linda da yadda suke enjoying rainy seasons da ita back in newyork, ta ɗanyi murmushi kaɗan tana shirin sake labulen taga an buɗe gate ɗin gidan ya shigo da motarsa haka kawai taji ta gagara sake labulen ta zuba masa idanunta tana kallonsa har ya ƙarasa yayi parking a space ya buɗe ƙofar ya sauƙo, jingina jikinta tayi da wajen tana kallonsa ganin ya nufo cikin gidan walking majestically kamar ko yaushe, yanayin garin da iska da ake yasa taga ya ƙara mata haske da wani kyau sai dai kamar ya ɗan faɗa though not much, ta dinga kallonsa har ta bar ganinsa saboda isa da yayi ƙofar palour ya danna bell, sauƙe ajiyar zuciya tayi a hankali tana jin idanunta na ciko da ƙwalla marasa dalili, ita yanzu bata san abinda ke damunta ba, she wants to be staring at him from afar amma bata so taga ya mata magana sam haka kawai take jin haushi idan ya mata magana amma after that she wants to be seeing ya zo gidan ko da bazai kulata ba. Ta sake labulen tare da ƙarasawa ta ɗauki kayan da ta gama sorting ta tafi ta fara sakasu a wadrobe dan kayanta yanzu masu yawa ne a gidan kuma duk Ahmad ɗinne ya kawo mata su.
Har ta gama saka kayan tass a wadrobe bata sake jin motsinshi a gidan ba, ta zauna a gefen bed, tana son sauƙa taje wajensu rahama amma tasan tana sauƙa zasu haɗu da shi, ta ɗan yi tagumi shiru kafin cikin ranta to ko ya hauro ma yana wajen Ammi toh? Tunanin haka yasa ta gyara baƙin hular kanta ta miƙe ta nufi ƙofa, buɗe ƙofar tayi ta ɗan leƙo ganin ba kowa ta fito gabaki ɗaya ta janyo ƙofar a hankali kar ta tashi Saif, tana juyowa suka haɗa idanu da shi ya fito daga palourn Ammi, ta tsaya cak tana kallonsa shima ita yake kallo yana jiran ganin abinda zatayi, ganin ta tsaya bata gudu ba ya ɗanyi murmushi yace
“Zo ki wuce” girgiza masa kai tayi ba tare da ta ce komai ba ta juya ta koma cikin ɗakin da ta fito ta kullo ƙofa, ya tsaya yana kallon ƙofar sai kuma ya nufi ɗakin.
Tana shigowa ta tafi bakin gado ta zauna ta zuba ma Saif dake baccinsa idanu, jin buɗe ƙofa yasa ta ɗaga kanta da Sauri ta kalli ƙofar, suka haɗa idanu da shi yana tsaye daga bakin ƙofar, hakan yasa ta miƙe tsaye tana cigaba kallonsa, ya ƙaraso cikin ɗakin ya rufe door ɗin yana kallon dogon rigar jikinta mai guntun hannu wani mai taushi na zaman gida sai hula dake kanta yace
“Bakya jin sanyi ne? You’ll catch cold sitting like dat”
Ya faɗa ba tare da ya ƙaraso cikin ɗakin sosai ba dan he’s expecting her to crash out, ganin bata amsa ba sai komawa da tayi ta zauna a gefen bed amma ta haɗa rai yasa ya zare rigarsa ta sama dan daga wajen aiki yake ya bar iya ta cikin ya ƙaraso har gabanta ya ɗan durƙuso ya saka mata around shoulders ɗinta, duk da ya san ba wani sanyi take ji ba tunda har ta bar Ac ɗin ɗakin a kunne but kawai so yake ya samu dalilin zuwa kusa da ita, ta ɗaga idanunta ta kalleshi tana sake haɗe rai amma bata ce masa komai ba, ya miƙe a hankali yace
“I’m leaving” shiru ta masa tana kallonsa har ya nufi ƙofa, ya kai hannu da niyyar buɗe handle ɗin zai fita a ɗakin kamar daga sama yaji muryarta
“Gida zaka tafi?” Ya dakata da buɗe ƙofar ya juyo yana kallonta sai yaga ta sa hannunta biyu ta riƙe rigarsa dake kafaɗarta tana kallonsa, ya fasa buɗe ƙofar yana kallonta yace
“Eh”
“A ruwan?” Ta faɗa tana juyawa ta kalli window, yayi shiru yana kallonta dan duk maganar da take yi fuskarta ba yabo ba fallasa take yinsa. Ajiyar zuciya kaɗan ya sauƙe yace
“Its not heavy ai” ya faɗa yana cigaba da kallonta dan tunda aka fara wannan fitinan sai yau ne take masa maganar hankali cikin tsanaki, dis is more than a week.
“Okay bye” ta faɗa a hankali, ji yayi ya gagara juyawa ya tafi ya dinga kallonta kafin yace
“Ko zamu tafi tare” wani kallo ta masa kafin ta miƙe tare da cire rigar tasa ta ajiye akan gadon ta nufi toilet abinta, ya bita da kallo har ta shige toilet ɗin ta rufo ƙofar kafin ya sa hannu ya shafa kansa, ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe a hankali yana furta
“God have mercy,” cause he’s seriously missing her so much, ji yake kamar notikan kansa za su sussunce sosai yakw ƙoƙarin controlling kansa, Her walking past him yanzu didn’t help matters at all, it only made matters worse. Juyawa yayi ya buɗe ƙofar ya fita, ya nufi part ɗin Ammi don maganar Suhaila ta ɗauko masa Yayi excusing kansa ya fito.



