⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 45: Chapter 45

“Kawai so nake ka dawo da ita da kanka Ahmad ai hannun mutum baya ruɓewa ya yanke ya yar” ya ɗago kansa ya kalli Ammi kafin ya sauƙe ajiyar zuciya a hankali cike da takaicin halin Suhaila yace

“amma kinga yarinyarnan koh she’s destorying rayuwarta, ko da yake she’s to be blamed…” yayi shiru ba tare da ya ƙarasa ba yana jin zuciyarsa gabaɗaya ta lalace akan abinda Ammi ta faɗa masa akan Suhaila

“Ni dai ko ma miye ne she’s ur cousin Ahmad, saboda Allah kawai zakayi kaji” ajiyar zuciya ya sauƙe feeling defeated dan Allah na gani bai yi niyyar saka bakinsa cikin lamarin ba, but ba abinda Ammi zata ce yayi ya gagara yi yana kallon Ammi yace

“Shikenan, i’ll bring her back in sha Allah, Allah kuma ya kyauta” ta ɗan masa murmushi tace

“Amin ya rabb, Allah ya maka albarka ya baka masu maka kaima” ya amsa da “Amin”, kafin ya miƙe a hankali yana ɗaukar wayarsa da ke gefen kujera

“Ba na ƙarasa gida Ammi”

“Bazaka jira a ɗauke ruwa ba?

“Zan jira downstairs”

“To ka gaida Amira, kunyi magana da Na’ima?” Gyaɗa mata kai kawai yayi ya nufi ƙofa ta bishi da idanu har ya fice a palourn.

Buɗe ƙofar ɗakinta ya sake yi ganin bata ciki sai saif dake bacci still ya sa ya janyo ƙofar ya nufi ƙasa dan sosai yanzu ake zuga ruwan sama, ya tsaya a palour yana adjusting wristwatch ɗinsa kafin ya nufi kitchen ɗin da ya tabbatar duk suna can, tsayuwa yayi a bakin kitchen ɗin yana kallonsu dan ba duka suka rufe ƙofar ba, Rahama da yasmeen na gefe ɗaya na kitchen ɗin sun basa baya Suna aikinsu, Fati na gefe itama tana wanke vegetables a bakin sink, a tsakiyar kitchen island ɗin kuma Na’ima ce a tsaye itama ta bawa ƙofar baya ta jingina jikinta da island ɗin tana folding dish towel dake hannunta innocently.

For a moment he just stood there da hannunsa ɗaya a aljihu yana kallonta, gashin kanta ya kwanta lub a bayan wuyanta ta ƙarƙashin hular kanta, ya bi jikinta da kallo kafin ya sauƙe ajiyar zuciya a hankali dai dai lokacin ta juyo tana duba abinda ke cikin pan ba tare da ta lura da shi ba kamar yadda dukansu sauran basu lura da shi ba, turo ƙofar yayi da kyau ya shigo cikin kitchen ɗin yana clearing throat ɗinsa duk suka juyo lokaci ɗaya, da Mamaki Rahama da Yasmeen ke kallonsa cause kitchen ɗin gidan dai ba wajen zuwansa bane tun kafin yayi aure ma kafin ya shiga sau ɗaya yayi aika sau goma, duk fuskarsu a washe suka gaishe sa ya amsa idanunsa akan Na’ima dake juya plantain ba tare da ta kalleshi ba sai ma haɗe ranta da tayi kaɗan tana rage gas ɗin kamar bata san ya shigo kitchen ɗin ba, Ya ƙarasa gaban counter ɗin da take ba tare da yace mata komai ba ya ja kujeran jikin wajen mai kamar dining a haɗe ya zauna, hakan yasa Yasmeen ta kalli Rahama, wayarta kawai rahama ta ɗauka ta nufi ƙofa abinta, yasmeen ta bita da wani kallo, ji wani gulma miye na fita maimakon su tsaya su cigaba da aikinsu tanan su ga ya zasu kaya sai ta kama ta fita yadda dole itama sai ta fita kenan, wallahi rahama tana bata takaici, dole itama ta nufi ƙofa tana jin kamar ta tsaya amma bata isa ba tunda fati ma tuni ta fice ace ita kaɗai zata tsaya ai ya zama gulma ya tsaida ta, ta ƙasan ido Na’ima tabi yasmeen da kallo tana gama ficewa a kitchen ɗin ta janyo towel ta goge hannunta tare da barin bakin gas ɗin ta nufi ƙofa itama, miƙewa yayi ya sha gabanta dan har ta zagayo ta nufi ƙofar fita, ta ɗaga idanunta suka haɗa ido ta sake haɗe rai tana kallonsa

“Where are u running to?” Ya faɗa yana kallonta,

“daga cewa mu tafi gida tare ɗazu shine kika shige toilet, yanzu kuma ina zaki shige?”

Ko amsa masa bata yi ba ta nufi ƙofar fita kitchen ɗin ta baya ya bita da kallon mamaki, a wannan uban ruwan zata fita compound? Hakan yasa yace

“Na’ima wait!” Amma ina har ta buɗe ƙofar, ƙarar sauƙar ruwa a waje ya ƙara sauti a kitchen ɗin wani iska sosai ya shiga shigowa kitchen ɗin, ganin da gaske fita zatayi ya sa ya nufo ta muryarsa cike da lallashi yace

“To tsaya kiji, am leaving dont go in dat rain” ta tsaya a bakin ƙofar riƙe da ƙofar tana kallonsa, hannunsa ya miƙa mata alamun ta zo ta maƙe masa kafaɗa, ya tsaya jim yana kallonta sai ya ga ta ɗanyi murmushi kafin ta sake ƙofar ta fita outside kitchen ɗin bai san sanda ya biyota wajen ba yayi saurin riƙo hannunta kafin ma ta ƙarasa babban compound ɗin ta baya, already har ruwan ya fara soaking through shirt ɗinsa, ta tsaya tana kallonsa ruwan da ake yana jiƙa hularta yana shiga har gashinta yana gangarawa fuskarta,

“Look at u, zakiyi zazzaɓi fa” ya faɗa shima ruwan da ya jiƙa gashinsa na bin gefen fuskarsa, ta tura baki tana ƙoƙarin ƙwace hannunta hakan yasa ya tura ƙofar kitchen ɗin ya rufe da ɗaya hannunsa, ita kuma ya jinginata da bango ya ɗaura goshinsa a nata a nata breath ɗinsa na fita a hankali saboda yadda sanyin ruwan ya gama kame rigarsa a jikinsa dukansu ɗigan ruwa kawai suke tare suka sauƙe ajiyar zuciya muryarsa ƙasa ƙasa yace

“Zaki jiƙe fa” ta ɗan tura shi kaɗan tana faɗin

“Ni ka ƙyale ni” kamar wanda ta tura takadda haka ta ture shi daga jikinta tsabar yadda jikinsa ya gama mutuwa shi kaɗai ya san me yake ji, ta wuce shi tana shiga ruwan sosai, ya jingina da bangon wajen ya lumshe idanunsa ya buɗe yana kallonta kafin ya tashi daga bangon ya nufeta, tana ganin haka ta tattare dogon rigarta da ya gama jiƙewa jagwab ya manne da jikinta da niyyar fecewa ta zagaya ta front door, da hanzari ya riƙota sosai jikinsa, ya saka hannu ya zagayo a waist ɗinta yana kallon cikin idanunta kamar dama jiran moment ɗin yake itama shi take kallo ta rasa me take ji haushi ko ƙaunarsa, ya kai ɗayan hannunsa ya shafa fuskarta a hankali, lumshe idanunta tayi ta buɗe su a hankali tana kallonsa ya sake jinginata da wall ɗin wajen ya sunkuyo ya ɗaura fuskarsa a gefen tata duk suka lumshe idanunsu suka yi shiru, kafin a cikin kunnenta a hankali yace

“Zanyi tafiya” ɗago idanunta tayi ta kalleshi shima ya ɗago yana kallon face ɗinta da jikinta dats drenched da ruwa, muryarta a hankali tace

“Ina?”

“Somewhere” ya faɗa yana ɗaura goshinsa a goshinta ya kai lips ɗinsa yayi kissing karan hancinta lightly, buɗe bakinta tayi da niyyar sake tambayarsa yayi leaning in ya haɗe bakinsa da nata, it wasnt rushed, it was deep but very desperate kamar bai taɓa kissing ɗinta ba a rayuwarsa, hannunsa har rawa yake wajen tallafo fuskarta, ganin bata hanasa ba ya sake birkicewa, wani irin mixed emotions yake ji yana cika ƙirjinsa, ruwan na soaking ɗinsu har face ɗinsu, mixing the warmth of their breaths.

Na’ima bata yi responding ba at all at first har sai da taji ƙarfinta na shirin ƙarewa, like all of a sudden she felt weak, zuciyarta na bugawa da ƙarfin gaske, its like she’s fighting hard to be in this moment, ganin tana shirin sulewa ya sa ta riƙo rigarsa da ta gama jiƙewa sharkaff da ruwa suna sauƙe ajiyar zuciya tare.

Ko da yayi pulling back gagara ɗauke kansa yayi daga jikinta, ya ɗaura kansa a wuyanta ya gagara ce mata komai, duk yadda ta so ta rungumesa back kasawa tayi banda ajiyar zuciya babu abinda take sauƙewa a hankali, hawayenta da ya haɗe da ruwan na gangarawa kan kumatunta, sun kusan 3 minutes a haka kafin ya ɗago daga jikinta yana kallon fuskarta yace

“Lets go home” kamar dama tuntuni abinda take jira kenan ta fara kuka, ya sake rungumota jikinsa yana shafa gashinta da ya jiƙe sharkaff shima da ruwa yaba ɗiga dan tuni hular ta kama gabanta, cikeda lallashi muryarsa ƙasa ƙasa tace

“I’m sorry, u can stay all u want, i love you so much Na’ima”

“Ta yaya zan koma to bayan ka jiƙa min kayana” ta faɗa a shagwaɓe har sannan tana jikinsa tana kuka, Shiru ya ɗanyi yana shafa kanta kafin yace

“My bad, kiyi haƙuri toh, in kira rahama ta kawo miki hijab?”

Gyaɗa masa kai tayi a hankali, ya saketa yana taɓa aljihunsa jin ba wayarsa yace

“Yana kitchen wayar” kallon juna sukayi kafin yace

“muje sai in kirata”, ta gyaɗa masa kai ya riƙo hannunta suka nufi bakin ƙofar kitchen ɗin feeling like kar moment ɗin ya taɓa wucewa, har ya kai hannu zai buɗe ƙofar a hankali sai kuma ya tsaya ya juyo ya kalleta

“What if sun dawo” bata san sanda tayi dariya ba ya tsaya kawai yana kallonta tana cigaba da dariyar tace

“Then u tell them me mukeyi a waje” ya ɗan harareta kaɗan

“That u dragged me outside and kissed me?” Ta wani buɗa ido tana kallonsa kafin tayi wata dariya tana matse ruwan hularta tace

“I kissed u or u kissed me?” Kallonta kawai yake, like she’s fyn to ai yanzu meyasa bata son komawa gidansu yace

“Baby ko mu tafi gida kawai? I have my keys with me” ya faɗa yana lalubo key ɗin motarsa dake aljihunsa, ta wani ɗan harareshi kafin ta fara ƙoƙarin wucesa ta shiga kitchen ɗin, da gudu ta ƙarasa cikin kitchen ɗin bayan ta buɗe jin ƙaurin da ke tashi ta ƙarasa bakin gas ɗin a sittin ta sa hannu ta kashe gas ɗin tare da toshe bakinta tana kallon sa daga inda yake tsaye bakin ƙofa shima drenched da ruwa irin kallon look what uve done, ganin plantain ɗin da ta bari kan wuta ya gama babbakewa tass sun koma baƙi ƙirin a cikin pan ɗin gwanin tausayi, dai dai lokacin Rahama ta buɗe ƙofar kitchen ɗin ta shigo ai da sauri ya mayar da ƙofar bayan ya rufe kawai ya zaga ya nufi motarsa a ruwan yana lalubo keys ɗinsa dan yasin da Rahama da gansa a haka gwara ya tafi a ruwan.

Rahama ta tsaya tana kallon Na’ima da ke ta fifita Hayaƙi da hannu duk da ma extractor hood dake saman cooker ɗin ya zuƙe hayaƙin sosai da ba haka ba, rahama ta ƙaraso kitchen ɗin ta leƙa pan ɗin tana kallon plantain ɗin kafin ta kalli Na’ima tana gumtse dariya tace

“Ina yayan?” Buɗa mata hannu tayi alamun bata sani ba tana marairaice fuska, Rahama ta bi gashinta da jikinta da ke jiƙe da kallo kafin tace

“Love birds” cike da tsokana, Na’ima ta ɗan harareta cike da kunya tana sauƙe pan ɗin daga kan gas, Rahama tace

“In ɗauko miki hijab?” Da sauri ta gyaɗa mata kai, Rahama ta gyaɗa mata kai tare da juyawa ta nufi ƙofa fuskarta ɗauke da murmushi, dan she’s happy Na’ima is getting better, kuma Allah ya so ma itace tazo da yasmeen ne ai sai tafi jin kunya.

Da daddaren ranar tana kwance a gadonta amma ba bacci take ba, Saif kuma na ɗakin Ammi yace acan zai kwana, yasmeen da rahama na ɗakinsu probably ma sunyi bacci amma ita tana ta kwance idanunta biyu ba tare da ta san abinda ya hana ta baccin ba, kamar wadda aka ma dole ta miƙe zaune ta janyo wayarta a hankali ta zuba ma wayar idanu, sai kuma a hankali ta buɗe lock ɗin ta shiga messages ɗin da ya tura mata tun ɗazu da batayi replying ba kuma zaiga blue ticks alamar ta buɗe, ta zuba ma lambarsa thats not saved a wayarta idanu kafin a hankali ta shiga tayi saving da Yaya Ahmad, ta sake dawowa tana karanta messages ɗin, the first one is of him telling her ya wuce gida wanda tun da ta dawo ɗaki tayi wanka ta canza kayanta daga jiƙaƙƙu na ɗazu taga wannan message ɗin amma bata amsa ba, sai ɗazu ya sake mata wani cewa he’s cold from ruwan da suka shiga.
ta dinga contemplating kamar mai yaƙi da zuciyarta kafin ta tura masa

“How’re u, ya jikin?” Ganin baya online taji kamar ta goge message ɗin gabaki ɗaya, amma sai bata goge ba, sai kawai ta kirashi normal call, har ya katse bai ɗauka ba haka kawai zuciyarta ta raya mata yana tare da Amira ne a lokacin tayi shiru tana kallon wayar kafin kawai ta tafi ta goge message ɗinta ta kashe wayar ta kwanta ta rufe idanunta trying to force herself to sleep amma inaa taji ta gagara, ta kai hannu ta share idanunta a hankali tana hana kanta kuka amma a banza, ta tashi ta zauna ta haɗa kanta da guiwa ta kama kuka,

ƙarfe 2:30 wayarta ta fara ringing, ta share idonta ta kalli wayar ganin shi ke kira ta ɗauke kanta har wayar ya katse, tayi shiru tana jiran ya sake kira taga bai kira ba ta juya ta zuba ma wayar idanu kafin ta janyo wayar kusan a fusace ta buɗe whatsapp taga ya sending mata question mark kaɗai da ya ga tayi deleting message ɗin, sai taji abin ya ƙara ɓata mata rai, message ta fara masa typing cikeda rigima itama ta tura masa question mark, gani tayi ya gani immediately hakan yasa ta gane yana dm ɗinta tayi ta jira yayi reply amma baiyi ba kusan 2 minutes kafin ta tura masa sticker dat shows she’s waiting for his reply amma nan ma ya buɗe bai ce mata komai ba, haɗe girarta tayi tana jin haushin rashin reply ɗin nasa bayan yana buɗewa ya karanta ta sake tura masa

“Good luck with ur happy life, dont worry i wont disturb u again in sha Allah” tana turawa kuwa taga ya sake gani amma yaƙi yace mata komai ta dinga kallon message ɗin da mamaki wato ya kalla bai kula ta ba, haɗe rai tayi ta sake tura masa

“Thank you” nan ma tana turawa ya sake gani amma bai ce komai ba, kamar zata fashe ta tura baki kafin ta bi ta goge messages ɗinta duka. Ganin har sannan bai ce mata ci kanki ba ta gagara haƙuri dan har ta ajiye wayar ta kwanta tana dana sanin fara masa magana ta sake miƙewa zaune ta janyo wayar ta tura masa

“Are u ignoring me?wow, okay” shima tsaf ya karanta amma bai amsa ba, da mamaki ta dinga kallon wayar kafin muryarta ƙasa ƙasa to herself tace

“magani na” ta faɗa tana dangwarar da wayar duk ranta a dagule ta koma ta kwanta, hawaye har sun sake ciko idanunta.

Yana idar da Sallar dare da yake yi ya kalli gadon dan dama abinda ya tashi yi kenan yaga missed call ɗinta and a deleted message shine ya kirata da bata ɗaga ba kuma he assumed tayi bacci ne so sai bai sake kira ba ya shiga chat ɗinta da ta tura masa ta goge ya sending mata question mark and ba tare da ya fita a chat ɗin ba ya miƙe ya wuce ya ɗauro alwala ya zo ya tada sallah, message notifications da yake ta ji tun yana sallah yasa ya miƙe ya ƙarasa gefen bed ɗinsa ya ɗauki wayar ya zuba ma messages ɗin da duk ta gogesu idanu sai na ƙarshen ne kaɗai bata goge ba baisan sanda murmushi ya kuɓuce masa ba ya zauna gefen bed yana share goshinsa still murmushi ya ƙi barin fuskarsa ya danna mata kira immediately, yana fara ringing yaga tayi rejecting abin sai ma ya bashi dariya, ya shiga whatsapp ɗinta ya tura mata

“What did u delete baby girl?” Ta dinga kallon message ɗin, wato ma what did she delete bayan ya gama karantawa duka,
daga kwance da take ta masa reply

“Babu komai dont stress urself, ka cigaba kawai da enjoying life ɗinka without me”
Ahmad yayi wani dariya shi kaɗai, pls he miss dis girl way too much amma sai yaƙi ya amsa da gangan yana ta dariya wanda ya san shaqa zata sake yi ai kuwa bai gama assuming ta sake mai message

“Kasan me just forget i said that” ganin bai amsa ba ta tura masa stickers har uku duk na kallonsa da hakan ya sake saka shi dariya amma still bai amsa ba

“Meyasa zaka dinga buɗe min message kuma bazaka kulani ba”

yana buɗewa taga ya fara mata reply, few seconds later reply ɗinsa ya shigo wayarta

“Because you’re too cute when you’re angry. I don’t want to spoil it.”

Shiru tayi tana kallon message ɗin nasa, ta hana kanta murmushi tana shirin tura masa sabon message ya rigata

“Sallah nake, baby. Not ignoring you. I can never ignore you.”

Rufe fuskarta tayi a Pillow cike da jin kunya amma murmushi ya ƙi barin fuskarta, kafin ta ɗago fuskar jin ya sake turo mata message

“Drama queen, now tell me abinda kika ce kika goge?”

“Kawaai kar ka damu” ta masa reply tana murmushi,

“Ah ah tell me”

“Cewa nayi ya cold ɗin ya sake ka?”

“Ah ah ba duka ba i’m still sneazing” ɗan shiru tayi kafin tace

“Sorry” ya amsa mata da

“Tnks”

“Nima bari inyi sallahn” ta tura masa tana tashi zaune a gadon,

“In kira ki?”

“Ah ah i want to pray now”

“Okay baby, i love you, je kiyi sallah, as soon as na dawo daga tafiyar da zanyi gobe we’re going back home kinji”

shiru tayi bata amsa ba tana zaune gefen bed ɗin shiru, ganin bata amsa ba ya shiga kiranta voice call ta dinga kallon wayar kafin ta ɗaga, cikin very calm muryarsa yace

“U still dont want to come back?” Ya faɗa yana atishawa a hankali dan sosai sanyin ruwan da suka shiga ya dameshi da ƙyar ma yayi bacci,

“Sorry” ta faɗa a hankali jin sai atishawa yake a jejjere, tissue ɗin dake gefen bed ɗinsa ya sa zari ɗaya ya share tip na hancinsa da har yayi ja abinka da fari saboda tsabar attishawan da yake tayi tun da suka shiga ruwan yace

“Tnk u” kafin ya sake maimaita tambayar, ta Girgiza masa kai a hankali kamar yana ganinta tace

“Ni bana son Gidan” ya ɗanyi shiru yace

“Why?”

“Ance sihr ne kuma it might still be in the house ni gaskiya bazan koma ba, Mami da big daddy idan sunzo jibi i’ll follow them to Abuja”

“Amma ai an cire komai na gidan an canza baby, an sake gyara gidan ma, even if there’s sihr it wont be in the house anymore, ko in sake sa a yi sauƙar alƙur’ani a gidan”

“Ko kasa anyi ma ni bana son gidan”

“Idan na canza miki new house zaki yarda idan na dawo daga tafiya mu tafi gidanmu” muryarta ƙasa ƙasa tace

“Eh” ya lumshe idanunsa ya buɗe a hankali yace

“So be it, idan na dawo zamu koma gidanmu Allah ya miki albarka”

“Amin, kaima Allah ya maka albarka” murmushi yayi yace

“I missed u so much” bata amsa wannan ba tace

“Bari nayi sallahn”

“Ok” kawai ya faɗa ta katse kiran ta ajiye tare da miƙewa ta wuce toilet.

Wahsegari har ya gama shiryawa na tafiyar da zaiyi london dawowa da Suhaila dan tuni ya sa aka bincika masa inda take, kuma wanda ya sa ɗin bai sha wahala ba ya gano inda take through snapchat posts ɗinta and other social media handles, da kuma friends ɗin da ta yiyyi videos da su a lokacin, har address ɗin inda take a london yana da shi da irin mutanen da take yawo da su a garin.

Amira na kallonshi har ya gama abinda zaiyi kafin tace

“Tafiya zakayi?” Ba tare da ya kalleta ba yace “yes”

“And where exactly zaka je? Abuja? Tunda naga alamar matar taka kamar bata gidannan kuma bani da muhimmamnci a faɗa min ƙanwata bata nan, saboda kar ma in gane yasa kake zuwa can kake kwana ranar kwananta” ba tare da ya amsa wannan maganar ba straight yace mata

“London zani” Amira ta dinga kallonsa kafin tace

“Business trip?” Ya gyaɗa mata kai kawai

“Hmm” kawai tace tana zama a gefen bed ɗinsa.

Da ya tashi tafiya har bakin mota ta rakosa tana kallonsa ita sam bata yarda da tafiyar ba, ko Abuja zashi gidan iyayen Na’ima? Ta dinga kallonsa har ya shiga mota suka bar gidan kafin ta ɗaga masa hannu ta koma cikin gida ta rufe ƙofarta ta haura sama tare da shigewa ɗakinta ta ɗauko wayarta ta dawo parlour ta kira Nuwaira.

Wayar na connecting tace

“hello Nuwa” shiru tayi tana sauraran Nuwaira dake magana daga ɗaya ɓangaren kafin tayi saurin katse ta,

“Dan Allah nikam ba maganar ciki na kira ki min ba, Albi fa kamar ya saki yarinyarcan” ta faɗa tana murmushi

“Dan ya rasulallah?” Nuwaira ta faɗa da hanzari,

“Wallahi!” Suka tuntsire da dariya, nuwaira na dariya tace

“Sai da ke ƙawata yanzu shi ya faɗa miki ya sake ta?”
Amira na dariya tace

“Ah ah idan ma ya sake ta ai kinsan bazai faɗa min ba, ni ce na haɗa 1 plus 1 ɗina na gane da kaina, wai ashe bata gidannan tuntuni ni ban sani ba, sai kwana 2 da suka wuce na lura, in faɗa miki duka kayanta ma anzo an kwashe Albi ya zuba sababbi kar kar kar, komai na gidanma ya canza, gidan ma gabaɗaya ya canza masa fasali ke zanyi iya rantsuwa ma kuma bazanyi kaffara ba ya sake ta, maybe dan kar ya dinga tunata ne yayi haka, ke ko aikin baba ya kamashi ne shima?” Nuwaira ta fashe da dariya,

“To ance miki Baba wasa ne, yanzu dai kin dawo ke kaɗai abinki ƙawata, hehe yanzu ina Ahmad ɗin?” Sai a lokacin ta sauƙe ajiyar zuciya tace

“Abinda yasa na kiraki kenan yanzu, Yace min wai zai tafi london business trip, sha ni dai ban yarda ba, wa ya sani ma ko sulhu zai je nema da ita a Abuja”

Nuwaira tace “ki cigaba da yi ma kanki fatan tsiya, kar ki tsarkake ranki ki barshi a london ɗin zashi tunda can yace miki zashi”

“Allah ko nuwa” nuwaira ta ja tsaki tace

“bansani ba, kika sani ma ko ƙasar ce ta masa zafi zai je ya sha iska yayi jinyar zuciya shine ya fake da business trip” suka sake yin dariya tare

“Kuma fa hakane ƙawata.”

“Ah toh…” Nuwaira ta faɗa tana canza akalar hirar zuwa tata matsalar.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved