Chapter 46: Chapter 46
Club ɗin was alive ana ta casu duk da dare ne sosai a lokacin, amma banda kiɗa babu abinda ke tashi suna ta rawa suna mannuwa da juna, Suhaila da ƙawarta sai dariya suke suna rawa Suhaila na wining jikinta a jikin ƙawarta clara ita kuma ta sa hannu a waist ɗinta suna yi tare, Guy ɗin da suka zo tare ne ya janyo ta daga jikin clara ya dawo da ita jikinsa, tuni ta saƙalo hannunta a wuyansa suka cigaba da rawa tana juya jikinta a nasa, kayan jikinta su da babu duk uwar babansu ɗaya, suna cikin rawar suka fara kissing juna, duk hankali ya dawo kansu aka shiga hailing ɗinsu tunda a tsakiyar dance floor ɗin suke, kamar mayu haka suke kisisng juna a wajen masu video nayi ko a jikinsu, kamar ance ta buɗe idanunta da ke lumshe suka haɗa idanu da Ahmad dake zauna a edge na Vip lounge na club ɗin yana kallonta across the dance floor, duk da yawan strangers da ke wajen idanunta a nasa suka shige straight, hasken club lights na haska mata fuskarsa da kyau tana gani, tuni dariyar fuskarta ta ɓace ta zaro idanunta tana furta “yaya Ahmad” wani bugawa da ƙarfi zuciyarta tayi ta fara ƙoƙarin zare jikinta daga na guy ɗin da ke ta lalube mata jiki, janye jikinta tayi da ƙarfi daga jikin mutumin tana kallon Ahmad idanunta a waje da tsoro, duk kiɗan dake tashi a club ɗin ta daina jinsa yadda ya kamata, giyan da tasha ma ji tayi she’s not tipsy anymore, Ahmad wasnt smiling at all infact gani tayi ma kamar he’s not even blinking, his jaw tight, idanunsa burning da bala’i da masifa da takaici da baƙin ciki.
Ƙafafunta taji sunyi freezing a wajen ta gagara ture guy ɗin da ya sake ƙwaƙumeta amma still tana kallon Ahmad da ya miƙe ya nufo wajen a fusace, yadda yake wuce crowd ɗin with kind of precence ɗinsa dake saka su matsa masa yana wucewa ba tare da yace musu komai ba yasa gabanta tsananta bugawa, hankaɗe mutumin dake jikinta tayi da ƙarfin gaske ta juya da nufi fita a wajen da gudu kafin ma ya kamata, dan har lokacin mutane basu ma lura da abinda ke faruwa ba, amma ina ya riga ya iso inda take, ganin zata gudu ya riƙo hannunta a fusace tare da juyo da ita ya ɗauke fuskarta da wani shahararren dirty slap da ya sa hankalin kowa ya dawo kansu immediately, before she could recover ya sake ɗaura mata wani da har sai da ta kusa faɗuwa, tayi baya tana dafe kuncinta, kowa a dance floor ɗin yayi freezing for a second hankali ya dawo kansu ana faɗin “yoooo” tuni aka kashe music, ƙawarta clara tace
“What the hell” wani kallo da Ahmad ya mata ya sa ta ja gefe bata sake magana ba tana kallon ikon Allah, yana kallon Suhaila da ta fara kuka cike da ɗacin rai yace
“Ure a disgrace Suhaila, wannan kika baro gida ki zo kiyi dan ubanki?”
Ya faɗa yana nuna cikin club ɗin, mutumin da ke rawa tare da ita yayi stepping forward amma wani deadly kallon da Ahmad ya masa ya sa ya dakata a wajen yana kallonsu ganin sai kuka kawai suhailar take farar fuskarta tayi jajir amma bata ko ce masa komai ba sai ma jajjan kayanta da take yi tana rufe jikinta, cikeda takaici Ahmad ya cire rigarsa ta sama ya sa mata a jikinta over her shoulders dan kayan da ke jikinta are too exposed yana jin tsantsan takaicin kasancewarta jininsa kafin ya kama hannunta ya nufi ƙofa da ita,
“Leave me” ta faɗa yana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga nasa da ya ma wani shegen riƙo dan tsoron tafiya tare da shi take yi, gani take kamar dukanta zaiyi, ko kulata baiyi ba ya fara dragging ɗinta ya nufi fita a cikin wajen da ita ba tare da ya sake ce wa kowa komai ba, masu son suyi intervening ma ganin how furious he’s sai duk suka rabu da su tunda sun fahimci family issue ne, tsoro ne a cike a ranta as tana bin bayansa yana dragging ɗinta across dance floor ɗin suka fita a wajen ba tare da ya damu da duk kallon da aka bisu da shi ba, har suka fito waje kafin ya sake hannunta yana kallonta cike da takaicin wai she’s his cousin, he feels disgusted at the thought of that, mascara ɗin idanunta duk ya damalmale da hawaye tace
“Yaya Ahmad pleas…”
“Shut up” ya faɗa yana bata wani kalan deadly stir, his voice iced. Hakan ya sa tayi tsit, yayi gaba zuwa mota jikinta har rawa yake ta bi bayansa, tana cigaba da kuka.
ita da mamarta ce ta ganta haka wallahi ko a jikinta but Yaya Ahmad of all people? She wont forgive mamanta for sending him to get her.
Basu bar ƙasar ba sai wahsegari da dare bayan ya tisa ta ta ɗauko passport ɗinta and d rest kuma har lokacin kwata kwata bai bata fuskar bashi hakuri ko wata doguwar magana ba, itama she’s too ashamed to even look at him, tayi kuka har ta gaji.
A jirginma ita ke zaune jikin window idanunta a kumbure saboda kuka amma ko kallon sashin da take baiyi ba, da ta gwada yi masa magana ma trying to see if tana da chance ɗin pleading tuni ya danna divider dake tsakanin seats ɗinsu yayi shutting nata out ta bar ma ganinshi kwata kwata.
Duk awannin da suka ɗauka a jirgi babu abinda ya sake haɗasa da ita har suka yi landing a Nigeria kusan ƙarfe 11:50 na dare, driver dake jiransu yayi picking ɗinsu daga Airport, bai kai ta gidan Ammi ba ko wajen mamarta salma ba sai ya wuce da ita gidansa with the intention sai gobe zai kaita wajen Ammi idan ya so Mamarta ta ɗauke ta a gidan Ammi.
Ko da suka iso gidansa kusan ƙarfe 12:30 Amira tuni tayi bacci, ɗakin da suhaila zata kwana a downstairs ɗin kawai ya nuna mata yayi wucewarsa sama.
Washegari da safe Ahmad na kitchen yana haɗa ma kansa cup of coffee fuskarsa a ɗaure tamau dan har yanzu tension ɗin jiya bai sake sa ba gashi Amira ko tashi ma daga bacci bata yi ba shi kuma da wuri yake son fita dan sai ya fara dropping Suhaila a gidan Ammi sannan yayi magana da Ammi ya ga Na’ima before going to the office, gashi yau su Mamin Na’ima zasu zo daga Abuja so he’ll leave office early today, yana cikin haɗa coffee ɗin Suhaila ta shigo kitchen ɗin, ganinsa a tsaye a kitchen ɗin ta tsaya daga bakin ƙofa tace
“Ina kwana” ko kallonta baiyi ba bare ta saka ran zai amsa, ta cigaba da tsayuwa a wajen tana kallonsa dan har idanunta sun ciko da sabbin hawaye, Amira da tashinta kenan ta sauƙo ƙasa cikin kayan bacci dan bata ma san Ahmad ya dawo a jiyan ba, ta tsaya a palour tana kallon ƙofar kitchen ɗin wondering wacce ke tsaye a wajen da gown baƙa gata fara ƙal bata ganin fuskarta dan ita yarinyar kitchen ɗin take kallo, hakan ya sa ta nufo kitchen ɗin, tsaye tayi bayan Suhaila tana kallon Ahmad dat didnt send both of them da mamaki, yana juya ta spoon a cup ɗin gabansa, kafin ta saka hannu ta juyo da suhaila dake hawaye, kallonta Amira ta dinga yi, Suhaila ta ƙwace shoulder ɗinta tana ma Amira wani kallo, tuni Amira ta haɗe rai tamau ganin wacce ke wajen ta ƙarasa cikin kitchen ɗin tana kallon Ahmad tace
“What is going on here?” Ko amsa ta baiyi ba ya cigaba da stirring coffee ɗinsa.
“Me take yi da sassafennan a gidannan?” Suhaila dake binta da wani kallo ta taɓe baki tace
“Saboda anan na kwana” Amira ta kalli Ahmad sannan ta kalli suhaila
“Anan kika kwana saboda gidan na ubanki ne?” Suhaila ta dinga harararta amma tayi shiru tana satan kallon Ahmad dan tsoron tankawa take yi ta ƙara ma kanta laifi idan ba haka ba ai wallahi Amira bata isa ta zageta ta ƙyale ta ba. Ɗaukan cup ɗin coffee ɗin yayi ya nufi ƙofa ya fice a kitchen ɗin dan already ransa a ɓace yake baya son sabon ɓacin rai, ya wuce sama da cup ɗin ya barsu duka a tsaye a wajen Amira ta juya da nufin binsa saman sai a lokacin Suhaila ta yi magana
“Da kika ce gidan ubana ne da na kwana, to ba gidan ubana bane kuma kema ba gidan ubanki bane da kike kwana, kuma mai gidan shi ya tafi ya ɗauko ni daga wata uwa duniya ya kawo ni cikin gidansa yace in kwana har kin isa ma kice min gidan ubana ne?” Ko ƙarasawa batayi ba Amira ta juyo ta ɗauke ta da Mari, suhaila ta dafe fuskarta cike da bala’i tace
“Bura’uba!” Ta kai hannu da niyyar cakumo Amira, Ahmad da ya ke sauƙowa ƙasan bayan ya ajiye cup ɗin a sama da niyyar yace ma Suhaila taje ta shirya su tafi ya daka mata tsawa
“Dont u dare!” Dakatawa Suhaila tayi ba tare da ta taɓa Amira ba tana kallonsa har ya ƙaraso wajen yana mata wani kallo yace
“Matata zaki buga dan ubanki” fashewa tayi da kuka tana faɗin
“Mari na fa tayi yaya Ahmad!” Amira dake tsaye gefe tana jijjiga ƙafa tana jin wani shegen daɗi na defending ɗinta da Ahmad yayi tace
“Na mareki, ko zaki rama ne?har ni zaki faɗa ma banza, jaka, albino”
“Shut the hell up Amira!” Ya faɗa yana kallon Amira ransa a ɓace, duk shiru suka yi suna kallonsa ya nuna Amira yace
“U think dis is how wives behaves?, obsessed, jealous?paranoid? Kina tarnishing image ɗinki together with mine, u must be very much out of ur mind, and mind u am not urs to control, idan kika sake ɗaga filthy hannunki kika taɓa any of my relative da ya zo gidannan Amira ba ma taɓawa ba kika kallesu anyhow thats when i’ll show u my actually colour ki kiyaye ni, i’ll not tolerate it anymore”
kallonshi kawai Amira take yi shocked dan tunda take da shi ma bai taɓa mata magana haka ba, he has never called her out bluntly irin haka.
“Ke kuma wuce ki je ki ɗauko hijab ɗinki ki wuce mu tafi, stupid fool, ko ance miki u can just come in dictating foolishness ɗinki anan?” Kallonshi Suhaila tayi ta gagara cewa komai ta juya fuu ta nufi ɗakin da ta kwana ta ɗauko gyalenta da wayarta ta zo ta nufi ƙofa, shima bai sake kallon Amira ba ya nufi ƙofar, Amira ta bisu da kallo shocked to death.
Wanda na muku da farko har ya fi wannan yawa amma duka ya goge, e pain me no be small sef ???? amma ai shiknan ????Happy Sunday guys ❤️
Har suka iso gidan Ammi bai sake ce mata komai ba itama haka dan bata ma ga fuskar ce masa koman ba, yana parking a space ya sauƙa ya wuce cikin gidan leaving her behind a motar hakan ya sa ta sauƙa itama ta bi bayansa, har lokacin cika take tana batsewa na rashin rama marinta da tayi, duk da yadda zuciyarta ke cike da fargaban haɗuwa da Ammi na abinda ta aikata dan tasan Ammi wont take it likely with her dan har tafi shakkar Ammi akan mummynta amma marin da Amira ta mata ba ƙaramin tsaya mata yayi ba, wallahi ba dan yadda taga ransa ya ɓaci ba babu abinda zai hanata ramawa.
Suna shigowa palourn ya haura sama, ita dai suhaila ta tsaya a palourn da babu kowa tana tunanin haurawa, kafin a hankali ta haura itama, a palourn Ammi ta same shi seated tare da Ammi ta tsaya daga bakin ƙofa tana kallon Ammi kafin ta ɗan ɓata rai tace
“Ina kwana Ammi” ba tare da Ammi ta kalleta ba a taƙaice tace
“Lfy” dan ba yanzu ne zata zazzageta ba sai salma ta zo kuma ta riga ta kirata tazo gidan, so take ta gama da case ɗin Suhaila su tafi kafin ma su Mami su iso Lagos.
Ganin Suhaila na ta tsaye still a wajen ya sake tamke fuska ya kalli Ammi yace
“I’ll be back before su iso” Ammi ta gyaɗa masa kai kawai tana faɗin
“To Sai ka dawo” har ya miƙe sai kuma yace
“Ina su rahama?” Ammi ta kalleshi tace
“Suna Garden dukansu, Saif ɗin ma bai je school ba yau”
“Okay” kawai yace tare da juyawa ya nufi ƙofa, Suhaila ta matsa masa a hanya ya wuce ya fita a palourn, yana fita Ammi ma ta miƙe ta wuce bedroom ɗinta ba tare da ta sake kula suhailar ba, ganin ta gaji da tsayuwa a wajen ya sa itama ta juya ta fita da niyyar zuwa Garden ɗin.
Yana fitowa compound ya wuce wajen motarsa ba tare da ya je Garden ɗin ba kamar yadda Ammi tace duk suna can, ya jingina jikinsa da motarsa tare da ciro wayarsa ya tura ma Na’ima text
“Come to the car, im waiting”
Na’ima dake zaune a kan wani persian rug mai kyau da faɗi ga throw pilows a zagaye da rug ɗin, ta tanƙwashe ƙafafunta tana kallon Yasmeen dake yi ma rahama calaba a dogon gashinta mai santsin gaske suna hira ta kalli wayarta da ke gefe a ajiye jin ƙarar shigowar saƙo, ganin wanda yayi saƙon yasa ta kife wayar kawai ba tare da ta tashi ba tana cigaba da kallonsu tana dariyar dramarsu dan Rahama tace ta gaji da kitson ta bar mata kanta tunda gobe duk zasu je saloon su wanke kan amma yasmeen insisted zata kunce mata shi a goben, ita dai Na’ima dariya kawai take dan rahama have a valid point ita bata ma taɓa kitsa kanta ba kuma bata jin zata taɓa, tana sanye da silky dogon siga sakakke sai scarve da ta ɗaura ta ɗan ja shi baya ta dawo da ends ɗin ɗan kwalin ta gaban ƙirjinta hannunta ɗaya riƙe da cup na juice, Saif kuma na kwance rub da ciki shima a kan rug ɗin yana kallo a ipad ɗinsa.
Jin ƙaran message again ya sa ta ɗauko pillow ta ɗaura a ciyarta tare da ɗaukar wayar ta buɗe, ganin wai cewa yayi ta same shi a mota ta kalli agogo its just 9 na safe fa, ta ɗan yi jim ba tare da ta amsa masa ba sai kuma ta miƙe tana kallon su Rahama tace.
“Let me get something ina zuwa” suka gyaɗa mata kai suna cigaba da hira, Saif ya tashi zaune yana kallonta har ta saka flat shoes ɗinta ta juyo ta kalleshi tace
“ko zaka rakani” girgiza mata kai yayi
“No go and come back Mimi” ta masa murmushi tace
“Okay champ” daga haka ta nufi hanyar fita a garden ɗin da wayarta kaɗai a hannunta, tana fitowa compound ta hangosa, shima ya ɗago kansa suka haɗa idanu ta ɗan tsaya tana kallonsa kafin ta shiga tahowa, sosai rigar jikinta ya manta kyau dukta its plain but its screaming elegant and classy, ta ƙaraso har inda yake tana kallonshi ta langaɓar da kai tace
“Good morning” ɗan sake fuskarsa yayi kaɗan yace
“Good morning ya kike?” Ta ɗan dawo ta gefensa tace
“I’m fyn whats with d frowning?” Ya ɗan shafa kanshi yace
“Am i?”
“Eh mana” kallonta kawai yake yi ya rasa me zai ce mata, ya ɗan cije lower lip ɗinsa kaɗan ya juyo duka yana fuskantarta yace
“U saw my first message” tana kallonsa ta gyaɗa masa kai
“I did”
“And?” Ya faɗa yana shafa girarsa da finger ɗinsa, tayi murmushi tace
“Ba fa igonring nayi ba da na gani kana ji ba” yace
“Uhm”
“da na gani ban zata cewa zakayi kana jira na ba i just thought its a normal message, cause i didnt know ure coming to this house early, afterall jiya fa kawai ka dawo daga tafiyar, so kuma muna hira da su rahama shiyasa i wanted to reply later but da ka sake second one ɗin shine na duba”
“And u came running”
“No sir i came walking” murmushi yayi yana kallonta itama tayi murmushi tare da jingina kanta da motar tana kallonsa da shaƙar mayen ƙamshin turarensa da ke mata wani azababben daɗi ji take kamar ta rungumesa tayi ta shaqa, ya ɗan shafa fuskarta yace
“Muje ki raka ni office” kallon hanyar garden tayi kafin ta kalli hanyar cikin gida tayi dariya kaɗan set ɗin jerarrun teeths ɗinta na bayyana tace
“Ah ah tnk u, sai in ce ma Ammi naje ina?”
“Sai ki ce mata kin bi mijinki” ya faɗa yana riƙo hannunta cikin nasa, jin tayi shiru sai murmushi kawai da take yasa yace
“Sauri nake zanje office ne yanzu, Ƙarfe nawa su Mami zasu zo?”
“3” ta faɗa tana ɗan kallon hannunta da yake murzawa kafin ta dawo da idanunta kansa,
“Okay” ya faɗa yana janyo hannunta ya dawo da ita gabansa tsakanin ƙafafunsa shi kuma yana jikin motar, Na’ima ta marairaice fuska tana ɗan juyawa ta kalli compound ɗin ganin ba kowa at all a compound ɗin kuma masu gadi na can gefe sosai so they can only see motarsa not them ya sa ta tura baki zata fita a jikinsa ya sa hannu ya zagayo waist ɗinta ya dawo da ita jikinsa muryarsa ƙasa ƙasa yace
“U smell nice” murmushi kawai tayi bata ce masa komai ba tana sunkuyar da kanta.
“Baby” ta ɗaga idanunta ta kalleshi yace
“Something is very much wrong with me today” ɗan haɗe girarta tayi alamun tambaya tace
“Miye?”
“Matso kiji” kallon ɗan space ɗin dake tsakaninsu tayi da bashi da maraba da babu tunda ma a jikinsa take gabaɗaya tace
“Ta ina zan matso?” Ya ɗan yi murmushi yace
“I want to tell u in ur ear”
“Ohkay..” ta faɗa tana matsowa jikinsa sosai ya ɗan sunkuya da kansa gefen fuskarta ya faɗa mata a kunne, ɗago kanta tayi ta kalleshi suka haɗa idanu ya kashe mata idanu ta wani girgiza masa kai tare da faɗin
“Taɓ”
“Please” ya faɗa a marairaice da hakan sai da ya sa ta kalleshi cause its so unlike him and that makes him sound so cute.
“To da yaushe?”
“Anjima i’ll tell u ta chat”
“Hmm” kawai tace tana kallonsa, ya sunkuyo yayi kissing goshinta yace
“Good girl, i love you” shiru tayi bata ce komai ba, yana kallonta yace
“Kiss me too” wani kallo ta masa ta fara ƙoƙari fita a jikinsa ya riƙo ta da sauri yace
“Anan fa zaki min” ya faɗa yana nuna kumatunsa, ganin tayi shiru yace
“Kinji” juyawa tayi ta kalli compound ɗin again kafin ta saka hannunta a wuyansa ta ɗan ɗaga ƙafarta tayi kissing kumatunsa single peck, ya lumshe idanunsa ya buɗe yace
“And here too” murmushi tayi ta sake masa a ɗaya kumatun, ya sake lumshe idanunsa, kafin ya buɗe ta ɗaura lips ɗinta a nata tayi kissing fyn lips ɗinsa just once kafin ta janye da sauri, ta na ƙoƙarin zillewa ta gudu, ya riƙo hannunta da hanzari yana dariya yace
“Ke kin ma isa” dariya ya farayi itama ganin ya sake dawo da ita jikinsa, ta marairaice tace
“Wai ka fasa zuwa office ɗinne?” Kallon agogon hannunsa yayi da sauri kafin ya cikata, ta sa dariya tana kallonsa, shafa kansa kawai yayi yana murmushi kafin ya zaga mazaunin driver itama ta bishi tana kallonsa har ya buɗe sleek motar ya juyo ya kalleta yace
“Bye” ta ɗaga masa hannu tace
“Bye, drive safe” shiru yayi yana kallonta, he cant believe itace, kamar ba itace few days da suka wuce bata son ko ganinsa ba, tabbass ko wani tsanani yana tare da sauƙi, ya ɗan yi shiru bayan ya shiga motar yana kallonta kafin yace
“I love you” murmushi ta masa a hankali tace
“Me too” kallonta kawai yake da idanunsa da ke sa tana jinta somehow, ta ɗaga masa hannu tace
“Bye” sai a lokacin ya tada motar bayan ya sake ce mata bye, ta matsa gefe tana kallonsa har ya ɗage glass ɗin duka kafin ya ja motar ya nufi gate, ta rungume wayarta a hannunta da murmushi a fuskarta har motarsa ya bar gidan kafin ta juya da nufin komawa Garden, a tsaye taga Suhaila a bakin ƙofar palour, she have no idea how long she has been there, to yaushe ma ta zo gidan in the first place, kallon da Suhaila ke mata across babban compound ɗin kaɗai yasa jikinta ya bata ta jima a tsaye a wajen amma sai bata sake kallon Sashin da Suhailar take ba kawai ta nufi Garden ɗin tana tafiya a hankali, Suhaila ta bita da idanu har ta bar ganinta zuciyarta na mata wani ƙonannen zafi, look how Ahmad yake biye ma yarinyarnan being all clingy and touchy da ita, kamar ba shi ne yake frowning all day ba, wai what did Na’ima posess ne da best mens ke mutuwa a sonta, duk haɗuwar sadiq haka ya susuce a sonta, yanzu kuma Ahmad? Ta ya ma akayi har ta janyo ra’ayinsa so much haka? Ta sunkuya a bakin ƙofar tana jin zuciyarta na zafi sosai kawai ta fashe da kuka.
Na’ima na daf da shiga garden ɗin wayarta ya fara ringing ganin Ammi ke kiranta ta dakata tare da ɗagawa ta kai kunneta tare da amsa sallamar Ammi, Ammi tace
“Mamana ina su Rahaman?”
“Duk muna tare da su Ammi”
“To ku shigo gida, yanzu mukayi waya da Maminki tace by 3 zasu iso”
“Eh haka tace min nima” ta faɗa tana ƙarasawa cikin Garden ɗin, Ammi tace
“Okay, ki ce ma Rahama da yasmeen ku zo yanzu”
“Toh Ammi” daga haka Ammi ta katse wayan, Na’ima ta ƙarasa ciki tace
“Ammi na kira” da hanzari Rahama ta miƙe tana faɗin
“shikenan ma, wannan kitso dama ya isheni abinda ma duk warwarewa zaiyi zuwa dare” dariya kawai Na’ima tayi ta ƙarasa ta ɗauke ipad ɗin Saif tana faɗin
“Up” ɗan mirginawa yayi kaɗan kafin ya tashi zaune, ta kama hannunsa ta miƙar da shi ta ɗauko takalmansa ta saka masa ta kama hannunsa suka nufi hanyar fita a garden ɗin, Yasmeen ce ta naɗe rug ɗin rahama ta tayata tattaro pillows ɗin suka fito duk suka nufi cikin gida.
Daga wajen Ammi duk kitchen suka wuce har da Ammi dan yi ma su Mami girki, har Ammi zata aika a kira Suhaila ganin bata cikinsu amma sai ta fasa ta haɗa kan yan matanta da fati suka shiga kitchen suka soma girke girke.
Sai 2 sannan Salma ta zo gidan hakan ya sa Ammi ta barsu a kitchen suna ƙarasa girkin da sun kusa gamawa ita kuma ta ja Salma palournta na sama, sai a lokacin tukun ta sa aka kira mata Suhaila da ta shige ɗaki tuntuni ta kwanta kamar wata mara lafiya.
Tana shigowa ɗakin fuska a haɗe Ammi ma ta haɗe nata firmly tace
“Zauna” Suhaila ta zauna tana kallon Mummynta da itama ita take kallo, dan Ammi bata ma ce mata ya dawo da Suhailar ba, Ammi bata wasting any time ba bafore ta fara ma Suhaila faɗa muryarta very sharp and commanding tace
“Suhaila ashe baki da hankali? Do you know the disgrace you have caused this family?” Suhaila tayi shiru kawai bata ce komai ba sai aukin tura baki da take, Mummy dai ba bakin magana shiru kawai tayi tana kallon Suhaila, Ammi ta cigaba



