Chapter 49: Chapter 49
“Yeah! I need to go to the office tomorrow, dat reminds me, kina so kije kiga office ɗina?” Gyaɗa masa kai tayi a hankali tace
“Company ɗinka ne ko u work for someone” yayi dariya kaɗan yace
“Inda i work for someone i wont be at home today, its Abbu’s company so yeah its ours, not just this he have many companies har a ƙasarsu ethiopia” cire kanta tayi a rigarsa ta tashi zaune tana kallonsa tace
“I said it” yayi dariya yana kallonta yace “u said what?”
“Ure not a Nigerian” dariya yayi yana kallonta yace
“Well maybe..!”
“Kasan many times na so na tambayi rahama sai na fasa” yana kallonta daga kwance da yake yace
“Me yasa baki tambaye ta ba ?”
“Haka kawai”
“Hm okay” ya faɗa yana ɗaura hannunsa a thighs ɗinta ya maida kansa ya cigaba da kallo, ta yi shiru tana kallonsa, can kuma tayi tagumi tana kallonsa, juyowa yayi ya sake kallonta kafin yace
“Why are u looking at me like dat” tayi dariya tare da sauƙa a kujerar ta tsaya a gabansa tace
“Wani abu na tuna” ya gyara kwanciyarsa tare da juyowa gabaɗaya ya kwanta akan side ɗaya yana kallonta yace
“Me kike tuna?” Matsawa baya tayi kaɗan tace
“How grumpy u use to behave da” ya shafa kansa yana dariya kafin yace
“Ni? To so kike kawai in ta dariya ni kaɗai kamar dai bansan me nake ba?” Harararsa kaɗan tayi tace bari in tuna maka yadda kake yi, haka kace min a airport with a serious face kamar zaka mare ni
“Ure in public, try to act like one” ta faɗa tana haɗe rai tana kallonshi mimicking yadda yayi, ya tuntsire da dariya yana girgiza kansa yace
“Ke thats not how i speak pls”
“wlh haka kake yi, rananda aka ci sa’a kayi magana kenan, a bikin anty fadila dat i bump into u, i wanted to say sorry amma kallon da ka min like say u wan slap me ya sa na fasa i was like whats wrong with dis one” dariyar da yake yi yau bata taɓa ganinshi iya dariya haka ba, itama dariya ta fara yi
Yace “ wa ya koya miki pidgin english yarinyar nan” sake kwashewa dariya tayi she looks soo happy tace
“Do u remeber ranan da ka ɗauko ni from sch? Kawai fa unlocking mota kayi ka wani tsaya i was so confused ranan, kar na shiga ka min jaraba” yana dariya yace
“Ni ne jarababbe? How on earth xaki ga mutun yayi parking in front of u, ya buɗe lock ɗin mota, kuma bai tafi ba kice wai baki san shiga aka ce kiyi ba” kallonsa kawai take kafin tace
“Hmm a bar maganar, sai kuma da na shiga kace wai dis is lagos kar na sake bari wayata ta mutu ko me kace ne ni na ma manta but dai it was very commanding with glasses a idanunka na gado kullum da glasses a idanunka fa lokacin” janyo hannunta yayi ya dawo da ita jikinsa yana dariya yace
“Ure crazy! But kinsan me? all that while i wanted seeing u, da ƙyar nake hana kaina miki magana”
“When?” Ta faɗa tana kallonsa, ya gyara mata zama a jikinsa yace
“Okay kinga a bikin fadila i stared at u too much that na haddace ki, ban so zuwa dinner ba i went cause i knew ull be there, but lokacin i dont know if it was love but my heart was soft for u, a wajen dinner da kika zo wajen motata and check ur self a jikin mirror ɗina i coulnd forget ur face throughout the night..” ta buɗa idanunta tana kallonshi tace
“Dama kana ciki?” Ya gyaɗa mata kai a hankali ya cigaba yana ɗan shafa cikinta yace
“Da na haɗu da ke a Airport kika bugeni by mistake, i was so suprised, i didnt know how to react shiyasa nace miki haka, but lokacin i find u wierd gaki shiru shiru very nice girl ashe kin iya surutu sosai” ya faɗa yana kama lips ɗinta da fingers ɗinsa.
“Then sai na haɗu dake a asibiti, then a gidan Nasir ko da na tambayeki sch ɗinki i knew everything about u then, then ƙofar school ɗinku that ride i hold it close to my heart duk da baki ce min komai ba banda tnk u” tana murmushi tace
“Then u started bringing my champ, ranan kace in ajiye maka ɗanka idan bazan shigo motarka ba” dariya yake sosai yanzu ma yace
“Saif was an excuse to be with u, sometimes ni zan ce masa in kira mata anty Na’ima and he’ll be like yes, kawia so that in saurari hirarku and ur voice” bata san sanda ta ƙyalƙale da dariya ba tace
“Wasa kake!” Ya shafa kansa yace
“Am serious” ta langaɓar da kanta a hankali tana kallonsa ta ɗanyi cute pout idanunta na cikowa da hawaye tace
“I love you” ya shafa fuskarta ya mata murmushi yace
“The day da na kaiku polo ke da Saif, dat day i made my mind ure going to be my wife” share idanunta tayi a hankali tace
“Ni kuma a ranan na fara jin sonka a raina” ya zuba mata idanunsa kawai yana kallonta yana cigaba da shafa fuskarta tare de saka thumps ɗinsa yana share hawayen gefen idanunta
“Ranan na fara jin sha’awar kasancewarka mijina, but a lokacin na san kafi ƙarfina, na ƙaryata kaina na sa a raina ure doing all tht for ur son”
Janyota jikinsa yayi ya rungume ta a hankali a jikinsa yace
“Kinsan which days are my worst? Days ɗin da u didnt want to see me, Na’ima ban san ta yaya nayi surviving days ɗinnan ba i dont really know, dont ever do that again” gyaɗa masa kai kawai tayi tana sake maƙalƙakesa.
Har sun ɗanyi shiru sai can kuma yana shafa bayanta yace
“Yaushe zaki bani babies as beautiful as u, yaushe zaki bawa Saif siblings” ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya tace
“Duk randa Allah ya bamu” ya gyaɗa kansa a hankali, muryarsa ƙasa ƙasa yace
“I love kids alot, amma Allah ɗaya ya bani Saif, i love him alot, ina roƙon Allah ya bani plenty from u, i cant wait to hold a little version of me and u, a piece of me and u, our own mixture of love”
“In sha Allah” ta faɗa a hankali tana jin sonsa fiye da misali a zuciyarta.
Da dare yana dawowa daga isha’ yace ta zo su je for a walk, sosai taji daɗin walk ɗin saboda yadda suke tafiya hand in hand a serene evnironment ɗin, ko ina haske tar, at a point ta tsaya ta ɗaga kanta ta kalleshi tace
“A selfie?” Murmushi ya mata ya miƙa mata wayarsa dan ta bar tata a gidan Ammi, yau ta musu hoto a wayarsa yafi ɗari goma, yanzuma ita ta musu hotunan kafin shima ya karɓa ya musu tare saboda tsawonta, dey look so cute together, tana kallonsa tace
“Dan Allah idan mun koma gobe ka ɗauko min Saif ni bazan iya zama ni kaɗai ba” gyaɗa mata kai kawai yayi yana riƙe hannunta, kafin ma su dawo gida har ta saka masa hoton a wallpaper ɗinsa, ya zauna a kujera yana kallonta tana zare gyalen kanta yace
“Baby gobe zaki saloon ɗin?” Sama ta nufa da gyalen a hannunta tana gyaɗa masa kai tace
“Ai dama da yau zamu je da su rahama ka sato ni” ya miƙe ya bi bayanta yana faɗin
“To muje in ƙarasa abinda yasa na sato ki dama” da gudu ta haura stairs ɗin tayi ya bi bayanta shima.
Washegari da wuri suka bar gidan, dan idan yayi dropping ɗinta home he’s going to the office briefly for a quick meeting, kuma Ammi tace yaje ya karɓo magungunan Na’ima ya kawo ta cigaba da anfani da shi, sai da ya buɗe mata part ɗinta ta shiga kafin ya wuce office, Urgent meeting yake da shi amma Yana isa office ɗin ya tuna ya bar the exact file da yazo office ɗin dominsa a gida, ɗan tsayawa yayi for a moment trying to recall inda yake kafin kawai ya juya da makullin motarsa a hannunsa yana amsa gaisuwar ma’aikata ya koma elevator ya sauƙo ya fito a babban company ɗin ya nufi private parking space ɗinsa na wajen ya buɗe motarsa ya shiga ya bar company ɗin, he need to fetch it real quick ya dawo.
A waje yayi parking bayan ya iso gidan ba tare da ya ƙarasa gate ba ya sauƙo ya ƙarasa da ƙafa ya ƙwanƙwasa gate ɗin, ɗaya daga masu gadi ya buɗe inda suke leƙa waje ganin Ahmad ne yayi saurin buɗe masa ƙaramar ƙofa yana faɗin
“Welcome sir” gyaɗa masa kai kawai yayi ya shigo ya nufi part ɗin Amira, sau ɗaya ya danna bell mary dake goge goge a palour ta buɗe masa ƙofa ta koma gefe tana gaishe shi, itama small nod kawai ya bata ya wuce sama abinsa, ɗakinsa ya wuce ya dinga bubbuɗe drawers yana duba file ɗin amma bai gani ba, ya duba shelves har side tables amma bai gani ba, ɗan zama yayi yana tunanin inda ya saka sai a lokacin ya tuna ya bawa Amira to keep dem ya sauƙe ajiyar zuciya tare da miƙewa ya nufi ɗakin Amira, tun kafin ya ƙaraso ƙofar yake jin kukanta kasancewar bata rufe ƙofar kirif ba, he didnt have any intention na eavesdropping amma maganar da tayi ne ya fizgi hankalinsa ya sa ya dakata da kai hannu da yayi zai tura ƙofar yana sauraren abinda take faɗa
“Mummy wannan malamin naki kawai is useless, mummy wallahi bai jima da dawowa da Na’ima ba nace miki, duk abinda kika saka nayi a kanta ya tafi a banza da hofi kenan” shiru tayi tana cigaba da kukanta, da alama sauraren mamarta takeyi a wayar kafin ta sake fashewa da sabon kuka tace
“To miye anfanin aikin in dai zai karye da wuri haka mummy, miye anfanin wannan asirin tunda Albi bai tsane ta ba?” For a moment he coulndnt comprehend abinda take faɗa ya kai hannunsa tare da taɓa ƙofar ɗakin. Instantly yaji Amira tayi shiru daga cikin ɗakin, kafin yaji footsteps ɗinta towards ƙofar da alama ta kashe kiranne, ƙarasa tura ƙofar yayi suka kusa cin karo a ƙofar da ita, ta ja baya da sauri tana kallonsa bayan zuciyarta ta buga da ƙarfi ganin shine a bakin ƙofar, tayi freezing a inda take tana kallonsa, kallonta shima yayi with his face blank kafin ya mata murmushi yana kallon fuskarta yace
“What happened to ur face, have u been crying?” Share idanunta tayi tana kallonsa ta ɗan haɗe rai kaɗan ganin bai ji komai ba ta juya ta koma cikin ɗakin tana faɗin
“Ko mutuwa ma nayi ai Albi ynzu babu ruwanka kai, rabonka da gidannan how many days now” ƙarasowa cikin ɗakin yayi yana bin ɗakin da kallo yace
“2” ta zauna a gefen bed tana kallonsa ganin ya jingina da mirrow shima yana kallonta kafin ya kalli wayarta dake gefen bed, Amira ta tace
“2 days? Ina kaje to a 2 days ɗin?” Kallonta kawai yake kafin ya ɗauke kansa yana faɗin
“I dont think u should ask me that tunda ba kwananki bane 2 days ɗin, ba wannan ya kawo ni ba yanzu ina file ɗin da na baki weeks back ki ajiye?”
“Wani file?” Shiru yayi yana kallonta hakan yasa tace
“Au, iya cikin drawer ɗin can” ta faɗa tana nuna masa drawer ɗin da yake kusa da shi, sai da ya kalli drawer ɗin kafin ya tafi can dan ɗauka, tana kallonsa tace
“Kai da matarka ne kuke tare for 2 days ɗin kenan” ya dakata ya juyo ya kalleta kafin yace
“Yes, kuma tunda kwananta ne it shoulndnt concern u much koh?” Ƙuri ta masa tana kallonsa, kwana biyu da yayi baya nan ta kirashi yafi a ƙirga amma yaƙi ɗaukar waya shiyasa ɗazu yana dawowa ta leƙa only for her ta ganshi da Na’ima kuma har part ɗinta ya kaita wanda ke nuni da ta dawo kenan, to ita kam wallhi bata ga anfanin wannan tsinannen aikin da Malam ɗin ya musu ba, ta miƙe fuuuu ta fice a ɗakin ya bita da kallo kawai kafin ya daure ya ƙarasa ya buɗe drawer ɗin, maganganun da yaji tana yi da mamarta na dawo masa tiryan tiryan sai kuma zancen Na’ima na rannan cewa Amira taje part ɗinta and from there ne komai ya fara taɓarɓarewa, connecting dots ɗin kawai yake yi har ya zaro file da ke ajiye neatly a cikin drawer ɗin a cikin wani folder mai kyau kamar dai yadda ya bata.
Yana zaro file ɗin idanunsa ya sauƙa akan pills na magunguna da ke ƙarƙashin file ɗin, ya zuba musu idanunsa yana kallonsu trying to figure out su kuma na miye? Cause Amira wasnt sick, bata masa complain ɗin anything ba recently kuma in har bata da lafiya to ta dinga damunsa kenan akwai ta da rakin ciwo.
Ajiye folder ɗin yayi a gefe ya ɗauko sackets ɗin ya jujjuyasu a hannunsa kafin ya duba lebel ɗinsu ɗaya bayan ɗaya, ganin bai fahimta ba ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya ɗauki very clear hotonsu duka dan shi bai taɓa ganinsu a gidanba kafin ya maida su ya ajiye a inda ya gansu ya ɗauki file ɗin ya nufi ƙofa, a dai dai ƙofa suka sake cin karo da shi tana shirin shigowa ɗakin da sauri, ya ɗan matsa baya yana kallonta ta kalleshi sannan ta kalli ɗakin.
Raɓata yayi zai wuce muryarsa ba yabo ba fallasa yace
“Sai na dawo” ta ɗan bishi da kallo kafin tace
“Allah ya dawo da kai lfy ” tana mayarda idanunta hannunsa ganin file, yana wucewa ta juya da sauri ta ƙarasa ɗakinta, drawer ɗin ta buɗe da sauri ta kalli magungunan kafin ta kwashe su da hanzari zuciyarta na bugawa, kar fa ya riga ma ya gani? Amma ta san halinsa da ya gani da yanzu bazai kula ta ba bare har ya ce mata sai ya dawo, buɗe wadrobe ɗinta tayi ta sake musu mazauni a wajen tana sauƙe ajiyar zuciya a hankali.
Ko da ya shiga motarsa sai da ya jinginar da kansa da kujera for like 10 minutes idanunsa a lumshe kafin ya buɗe su ya tada motar ya fara driving da hannu ɗaya, ɗaya hannun kuma yana danna wayarsa, forwarding hotunan yayi to wani friend ɗinshi Dr Sameer ta whatsapp with caption. “Whats this for?” Kafin ya ajiye wayar a gefe ya cigaba da driving, yana isowa office wayar kawai ya ɗauka da file ɗin ya nufi cikin building ɗin, ya wuce sama to his office bai ƙarasa office ɗinsa ba ya tsaya a desk ɗin sakatariyarsa ya miƙa mata ta karɓa da ladabi yana kallonta yace
“Make 3 copies kiyi attching da report ɗin and send it to Mr idris immediately”
Ta gyaɗa masa kai da sauri tace “okay Sir” dai dai wayar da ke hannunsa tayi ƙarar shigowar message, ya kalli wayar ganin Sameer ya sauƙe ajiyar zuciya tare da buɗe saƙon, he knew abinda zai gani kenan but bai san meyasa it hits him more than yadda yayi tunanin it would ba.
Mayarda wayar kawai yayi aljihunsa ya nufi hanyar barin office ɗin, sakatariyar ta bishi da ido dan saura few minutes to meeting ɗin nasu gashi he’s leaving again.
Yana fitowa ya shiga motarsa ya tada zuciyarsa na masa wani irin ɗaci ya nufi gidan Ammi straight.
The drive to gidan Ammi was silent, juya steering kawai yake yi amma shi kaɗai yasan abinda ya ke ji a ƙirjinsa, ko da ace ya tsaya back ya san ba abinda zai fahimta a meeting ɗin kwata kwata, yana yin parking ya fito ya nufi cikin gidan.
Ba kowa a palourn gidan ya wuce sama har ɗakin Ammi, yayi knocking once tare da tura ƙofar a hankali, Ammi dake kwance a kan gado tana bacci ta buɗe idanunta jin knock ɗin a zatonta ma su rahama ne kafin taga an buɗe ƙofar, ta dinga kallon Ahmad dake tsaye daga bakin ƙofa, tashi zaune tayi tana kallonsa dan bata jima da komawa baccin safen ba kanta ma ke ciwo, ƙarasowa ciki yayi a hankali ya zauna a kujera ya dafe kansa a hankali, Ammi na kallonsa tace
“Are you alright” kallonta kawai yayi amma bai ce mata komai ba, ta sauƙe ƙafafunta daga kan gadon ta taso ta taho inda yake tana kallonsa tace
“Ahmad” muryarsa kusan a shaqe yace
“Na’am?”
“Ina Na’ima?” Girgiza mata kai kawai yayi a hankali yace
“Lfynta ƙalau tana gida” ta dafa kafaɗarsa fuskarta na nuna damuwa tace
“To me ya faru” kallonta yayi kafin a hankali yace
“I’m fyn”
“Kai da Amira ne?” Gyaɗa mata kai yayi a hankali, Ammi ta samu waje ta zauna tana kallonsa tace
“Wai me kuma ya faru?” Ta faɗa cike da gajiya da lamarin Amira, gagara faɗa mata na asirin yayi a hankali yace
“Amira contraceptives da abortion pills take sha to not carry my baby, idan ma cikin ya shiga she aborts it”
“Subhanallah, wa ya ce maka haka Ahmad? Wani irin aborting kuma? Wani irin contraceptives akan wani dalili?” Buɗa mata hannu kawai yayi alamun bai sani ba, Ammi tayi shiru tana kallonsa kafin ta sake tambayarsa yadda aka yi ya sani, faɗa mata yayi duka Ammi ta sauƙe ajiyar zuciya tace
“Innalillahi wa inna ilahi raji’un” ta faɗa tana kallonsa da alama abin ya bata mamaki sosai itama, gabaɗaya ma ji tayi ciwon kan nata ya ƙaru tace
“Ko zaka same ta ka yi magana da ita kaji dalilinta na yin hakan?” Girgiza mata kai kawai yayi a hankali yace
“Ah ah Ammi am not asking her anything, Ammi tare da ita muka je muka ga likita a dubai ko akwai any issue da ya sa 4 years kenan har yanzu bamu sake conceiving ba bayan Saif, Saif yanxu shekararsa 5, ashe ni ta mayar mahaukaci she knows dalilin hakan” Ammi dai ta rasa me zata ce masa kallonsa kawai take har yanzu mamaki yaƙi barinta, wani ajiyar zuciya kawai ya sauƙe ya miƙe a hankali yace
“I came to get stuffs ɗin Na’ima da kika ce in zo in karɓa, and tace in kai mata Saif” gyaɗa masa kai Ammi tayi tana kallonsa kafin tace
“Kayi haƙuri kaji? Kar ka yanke ko wani hukunci cikin fushi kaji” ya gyaɗa mata kai a hankali yace
“In sha Allah” daga haka juya ya fita a ɗakin, miƙewa tayi itama ta biyo sa dan basa magungunan Na’ima da turarukan wutanta da other stuffs da ta haɗa mata dama zata koma da su idan ta tashi komawa, shikam Ahmad ɗakinsu Rahama ya wuce, yayi knocking ƙofar twice, Yasmeen ce ta buɗe ƙofar idanunta cike da bacci, ganinsa a tsaye a bakin ƙofar fuskarsa ba yabo ba fallasa hannunsa ɗaya a cikin aljihunsa tace
“Ina kwana yaya”
“Shirya Saif ki kawo min shi downstairs”
“Bacci yake yaya”
“Ki tashe shi” gyaɗa masa kai tayi a hankali, ya juya ya sauƙa ƙasa, juyawa itama tayi ta koma ɗakin tana mamakin me ya ɓata masa rai dan she can clearly differentiate ɓacin ransa da kuma normal grumpiness ɗinsa.
Suna zaune a palour,Ammi na sake tausansa Yasmeen ta sauƙo tare da Saif da tun zazaɓin da yayi 2 days har yau bai koma school ba, yana ganin Ahmad ya sake hannun yasmeen ya taho wajensa, ya shafa kan yaron ganin har ya ɗan rame yace
“How’re u feeling” kwantar da kansa yayi a ƙafarsa yace
“fyn” Ahmad ya ɗan kalli Ammi ganin duk ta shiga damuwa yace
“Kar ki damu, its fyn Allah, am okay and i wont do anything reckless dont worry” ta gyaɗa masa kai itama a hankali tace
“To shikenan Allah ya kyauta, ita kuma Allah ya shiryeta” kallonshi kawai yasmeen take har ya miƙe tare da Saif a jikinsa, dama ta san akwai a inda aka taɓa shi, kuma tunda taji ana Allah ya shirya ta san Amira ce, a zuciyarta ta ja guntun tsaki tana bin bayansa da bags ɗin kayan da Ammi tace ta kai masa mota.
Sai da ta saka a back seat ɗin motar kafin ta zago tace
“Yaya Amma dai ba anty Amira zaka kaima Saif ba” girgiza mata kai yayi yace
“Na’ima” tana kallonsa cike da son jin damuwarsa amma ta san ko ta tambaya ba faɗa mata zai yi ba tace
“Okay” tare da miƙa masa wayar Na’ima da dama ta ɗauko ganinsa, ya karɓa ya saka a aljihunsa ya juya ya buɗe motar ya saka Saif ya rufe sai a lokacin tace
“Yaya wani abin na damunka ne” shiru kawai yayi yana kallonta can yace
“Me kika gani?” Ta girgiza masa kai tace “nothing” bai sake ce mata komai ba ya zaga mazaunin driver ya shiga ya tada motar, sai a sannan ya kuma kallonta yace
“Ki shiga gida” ta juya a hankali ta wuce cikin gida shi kuma ya ja motar suka bar gidan, yana tuƙi jifa jifa yana kallon Saif da ke kallon window ji yake kamar he failed him, kamar bai zaɓa masa uwa ta gari ba, uwar da zata zama garkuwarsa kamar yadda Ammi ta zama tasa, uwar da zata saka shi a hanyar daidai, amma Amira ita kanta tana buƙatar mai saka ta a hanyar dai dai bare har ta saka wani. Ya ɗan shafa kansa a hankali yana cigaba da driving ɗin.
Suna isowa gidan ya sauƙa ya sauƙo da Saif sannan ya buɗe backseat ya ɗauko jakakkunan guda 2 har bakin ƙofarta ya kaisu Saif na biye da shi ya ajiye tare da danna doorbell, ya shafa kan Saif yace
“Wait for Mimi to open” gyaɗa mishi kai yaron yayi yana kallonsa, Ahmad ya juya ya nufi motarsa ya buɗe ya shiga drivers seat ya zauna yana kallon part ɗin na’iman waiting for her to open for Saif, Na’ima na buɗe ƙofar ta dinga kallon Saif da mamaki kafin tace
“Champ” ƙarasowa yayi ya rungume ƙafafunta yace
“Mimi” ta kalli compound ɗin kafin ta ɗan sunkuyo tace
“Kai da waye? Ina papa?”
“Ya tafi” ya faɗa yana nuna mata inda motarsa yake, sai a lokacin Ahmad ya tada motar ya nufi gate, tabi motar da kallo, meyasa ya bar Saif a bakin ƙofa bai jira ta buɗe ba, ko sauri yake ne? Bata kawo komai ranta ba tace ma Saif ya shiga ciki ya wuce ciki ita kuma ta shigo da jakankunan ta ajiye su a palour ta kulle ƙofarta ta dawo ta tsuguna tana buɗe jakankunan tana kallon Saif tace
“Shi yaje ya ɗauko ka?” Ya gyaɗa mata kai yace
“Yes” ya faɗa yana miƙa mata wayarta da Ahmad ya bashi a hannunsa a bakin ƙofar, barin jakar tayi ta karɓi wayar tana masa murmushi tace
“Tnk u” ta ajiye wayar a gefe ta buɗe jakankunan taga magungunanta ne, sai kuma abubuwa na mata da baza’a rasa ba, da kuma kayan girki a kitchen da tasan ba lallai tana da su ba yanzu, Na’ima tayi murmushi tana jin ƙaunar Ammi da godiya a zuciyarta da Allah ya hadata da surika ta gari kuma mai kaunarta kamar Ammi, kafin ta tattara duka kayan ta kai kitchen ta shirya su a inda zata shirya dan tun da ta shigo gidan take aikin gyara duk da ba dattin komai a gidan, sai da ta gama saka komai a inda ya dace kafin ta dawo palourn tana kallon Saif da sosai taji daɗin kawo sa da Ahmad yayi da wuri ko ba komai bazata ji kaɗaici ba at all more especially da dare da Ahmad zai kwana a part ɗin Amira tace
“ in dafa mana noodles?” Juyowa yayi ya kalleta tare da Gyaɗa mata kafin ya maida kanshi ya cigaba da kallon youtubekids da ta kunna masa a tv
Tace “okay” tare da juyawa ta koma kitchen ɗin dan ɗaura musu noodles ɗin.



