⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 5: Chapter 5

Satin tafiyarta na kamawa. Gaba ɗaya ji tayi kamar ranakun gudu sukayi, Wai har ta shafe wata ɗaya a Nigeria!

Mamy ce ta taya ta packing, jikinta duk yayi sanyi. Sun mata shopping sosai da Big Daddy. Sun saya mata gifts kala-kala. Har mai hoto Mamy ta kira ya musu family picture. Ta ba Na’ima copy ɗaya da aka mata framing a cikin wani glass frame mai kyau .

“Zan ajiye a gefen gadona a New York” ta faɗa a hankali tana kallon Mamy dake haɗa mata kayanta

Ranar da zata tafi, da ƙyar suka rabu da Mamy wacce ta kasa ɓoye hawayenta. Na’ima ta rungumeta tana kuka.

“Mamy… I belong here… please, kice Daddy ya barni anan.”

Big Daddy ya ɗagota daga jikin Mamy yana share mata hawaye

“Look at me, Zaki dawo, kinji? Try and convince your Dad, I know zaki iya, Mamynki da ni zamu jiraki Kar kiyi kuka kinji.”

Ya rungume ta yana shafa kanta har sai da tayi shiru. Mamy ta juya da sauri ta koma mota, ba zata iya ganin take off ɗinsu ba. Na’ima ta bita da kallo, hawaye na gangarowa a idanunta. Big Daddy ne ya jira har suka tashi kafin ya koma mota. Har lokacin, Mamy kuka take. Bai iya ce mata komai ba, ya kuma gagara lallashinta dan shi yasan what she’s going through, yafi kowa sani, har suka iso gida, buɗe motar tayi ta wuce cikin gida ya bita da kallo sai kuma ya sauƙa ya bi bayanta….

Suna sauka a JFK, taji kamar ta dawo ne cikin ƙuntatacciyar rayuwarta, duk wani walwalarta ya ɓace kamar dai ta baro shi a jirgin Nigeria.

Dad ne ya zo ya ɗauketa da kansa a wata sabuwar Tesla. Duk da tayi kewarsa, bata nuna ba, Ta zauna a bayan motar kusa da shi, ta rufo ƙofar.

Sai da motar ta fara tafiya kafin ta gaishe shi, ya amsa ba yabo ba fallasa yana tambayarta how her flight was

“Alhamdulillah” ta faɗa a hankali tana maida idanunta kan taga

“Welcome back,” ya faɗa yana cigaba da duba jaridar hannunsa.

Ta gyaɗa kai kawai. Bata sake cewa komai ba har suka iso gida.

Duk da garin ya rage sanyi sosai, amma hoodie ce a saman kayan jikinta, Jakan goyonta kawai ta ɗauka daga motar, ta ɗaga masa hannu. Shi ma ya gyaɗa mata kai kawai.

Driver ne ya ƙarasa shigo da sauran luggages ɗinta cikin falon, yana sauri dan fita zasu yi da Dad dama sukayi branching to pick her up

Turus Na’ima ta tsaya a falon tana kallon wacce ke kwance kan kujera tana danna wayarta.
Tana sanye da high-waisted jeans da crop top. Babu ɗankwali akanta, sai expensive wig dake kannata. Kyakkyawa ce, fara tas, dan ta ma fi Na’ima haske kallo ɗaya tayi ma Na’ima ta mayar da kanta kan wayarta tana taunan gum.

Sai kuma ta miƙe, ta zura takalmanta ta wuce sama bata sake kallon Na’ima ba.

Dai-dai matakalan ƙarshe, ta juyo ta tambayi Andrew da ya shigo da luggage ɗin Na’ima na ƙarshe

“Andrew, where’s my Daddy?”

Andrew ya ɗan duƙa cike da girmamawa ya ce yana mota, amma suna shirin fita yanzu. Bata ce komai ba, ta juya ta wuce sama.

Na’ima ta sauƙe ajiyar zuciya. As if Daddy da Mummy ba su isa ba, yanzu kuma ga Suhaila? Wai yaushe ma ta dawo daga Cambridge ɗin? Jikinta ya ƙara yin sanyi.

Ta haura da luggages ɗinta ɗaya bayan ɗaya. Kafin ta rufe ƙofar ɗakinta ta kalli ɗakin Suhaila dake opposite nata jin kiɗan da ke tashi daga ciki.

Bayan tayi wanka ta shirya, sai da tayi magana da su Mamy da Big Daddy kafin ta fito zuwa ɗakin stepmom ɗinta. Tana sake kallon ɗakin Suhaila da har lokacin kiɗa ke tashi, girgiza kai kawai tayi, sannan ta ƙarasa tayi knocking ƙofar ɗakin Mummy.

Daga ciki ta ce

“Come in.”

Murɗa ƙofar tayi a hankali, ta tura ta shiga. Mummy da ke yi wa Suhaila head massage ta juyo tana kallonta.

“Shigo mana, me ya sa kika tsaya daga bakin ƙofa?”

Ƙarasowa tayi a hankali dan bata yi tsammanin Suhaila na nan ba, tayi zaton tana ɗakinta. Ta ƙarasa ta zauna a kan kujera tana kallon Mummy da ta cigaba da yi wa Suhaila head massage. Suhaila na zaune akan pillow mai taushi idanunta a lumshe, ita kuma Mummy na zaune bakin gado.

“How was your trip? Ya kika baro su Mamanki?”

Mummy ta faɗa ba tare da ta kalleta ba bayan Na’ima ta gaishe ta.

“Lafiya.” Kawai Na’ima ta amsa, tana miƙewa tace

“Mummy, let me find something to eat. I’m starving.”

Gyaɗa kai kawai Mummy tayi tana kallonta,

“Okay.”

Juyawa tayi ta fita, ta sauka ƙasa ta wuce kitchen. A can ta samu su Maryam suna shirya abincin dinner, dan oganniyar gidan ta dawo, basu isa su sake ba kuma sai ta koma makaranta.

abincin ma Kaɗan Na’ima taci,dan ji tayi gabaɗaya bata da appetite ɗin ma. Ta koma sama, Kusan karo suka ci da Suhaila, wadda ke ƙoƙarin sauƙa, Na’ima ta koma gefe da sauri tana faɗin

“Sorry, ban san kina tahowa ba.”

“Sorry for yourself. Ko kin makance ne da zaki ce baki ganni ba? You better behave yourself ni ba sa’arki bace.”

Wani kallon gefen ido Na’ima ta mata, bata ce komai ba. Ta raɓa ta zata wuce, Suhaila ta sa hannu ta finciko hular hoodie ɗin jikinta, ta dawo da ita baya tana mata wani kallo.

“What was that? Saboda raini ina miki magana zaki wuce?”

Hannu Na’ima ta saka, ta zare hannun Suhaila daga rigarta.

“Bani da lokacin faɗa dake yanzu, before kice ma Dad na miki abu da banyi ba.”

Daga haka ta wuce sama abinta, ta rufo ƙofarta.

Suhaila da ta bita da kallo, baki sake, ta juya fuu kamar zata tashi sama, ta nufi hanyar ɗakin Mummy.

Daga bakin ƙofa ta tsaya tana kallon Mummy tana huci.

“Duk abinda nayi ma yarinyar can ita taja! Mummy, I just can’t stay the same roof da ita. Na tsanetaaaa.”

Mummy da ke kallonta ta mata alama da ta shigo, ta kulle ƙofar. Ƙarasa shigowa tayi, ta rufe ƙofar tana jin ranta gabaɗaya na tafarfasa.

Mummy tana kallonta tace

“Why can’t you calm down ki yi abu kamar na masu hankali? Kina gidan ubanta, kina cewa kin tsaneta? Ko ance miki Daddy da kika ga yana biye miki baya son tasa ’yar ne?”

Tura baki tayi.
“Mummy, raini fa ta min.”

“Sannu babba. Two years fa kaɗai kika bata, amma sai wani ya ɗauka kin bata shekara goma tsabar yadda kike abubuwanki. Dan dai kin fita jiki ne kawai amma ai ba wani girmanta kika yi ba.”

Sake haɗe rai Suhaila tayi, bata ce komai ba.

Mummy tace

“Ki kwantar da hankalinki. Ta kusa ma ta bar gidan gabaɗaya for good. Ina ta ƙoƙarin convincing ubanta ya barta ta koma gun uwarta amma yaƙi, sai kace wani abu take tsinana masa. But na san abinda zanyi, Karki ɓata ranki a banza.”

“Better. Wallahi gwara ta san inda dare yayi mata, Dan ni bazan zauna da ita gida ɗaya ba.”

Daga haka ta fice daga ɗakin ko rufowa wa mummy ƙofar bata yi ba.

Kwana biyu Kenan da dawowanta daga Nigeria, Sosai take Kewan Mami, bare ma with the condition da gidan Ke ciki sai ya sake sa kwata-kwata ta tare a ɗakinta, ko abinci ta bar ci tare da su sai dai ta ci a ɗakinta, ba kasafai ma take saƙƙowa ba dan duk wani fitina Suhaila ta san yadda ake takaloshi, ita kuma bata son ta biye mata dan tasan ƙarshen abin ita Dad zai bama laifi, ba tun yau ta saba da halin Suhaila ba tunda Dad ya auri Mummy ta taho da Suhaila gidan basu taɓa shiri ba, bata san me ta tare mata ba but hakanan basa shiri, da idan ta tsokaneta tana retaliating not until lokacin da Dad ya mareta akan Suhaila tace ta mata rashin kunya, tun daga lokacin ta daina biye mata kwata-kwata, suhaila ta girme ta, ta bata 2 years amma ko kaɗan bata kama girman ba.

Wanda a ɓangaren suhaila ji take ta tsani Na’ima ba wai dan ta mata komai ba, kawai ji take she dont deserve all she have, she so much wish Na’ima bata da kyau cause apart from being Dad’s only daughter her serene beauty shi yake sake sa taji ta tsaneta, ita da she’s white ma bata da wannan kyan sai uban haske cause babanta is an american Mummy ce ʼyar Nigeria wanda tunda ta zo karatu ta haɗu da Simon Brookes a Makaranta, though ta san babu aure tsakaninta ita musulma da shi da yake christian hakan bai hana ta soyayya da shi ba, sosai suka sha soyayyansu irinta turawa, wanda daga baya da ƙyar Simon ya musulunta saboda yana son auren Salman (Mummy) kuma ta tabbatar masa bazata iya aurensa a Christian ba, har Nigeria ta kaisa aka ɗaura musu aure bayan ya musulunta, daga nan kuma suka koma newyork, ta daɗe kafin ta haifi Suhaila dan at first sam baya son haihuwa sai daga baya da ƙyar ya amince suka daina planning suka haifi suhaila, Simon za’a iya cewa musulmi ne irin waɗanda ake ce ma musulun musulun, dan Sallahr ma ba yinta yake ba sai ya ga dama, dama babu ilimin addini sam a tattare da shi, to ita kanta Mummyn ba isanta yayi ba bare ta ƙarar masa, haka dai suke rayuwarsu a bai bai, har Suhaila tayi 10 years lokacinne kuma sukayi divorcing juna, wanda a take yace ya bar ma musuluncin tunda dama ba don Allah ya shige ta ba, rabuwa dai ba na mutunci suka yi ba, sai da kotu ta musu iyaka da juna, kasancewar Mummy ƙwararriyar lawyer a lokacin bata bari an karɓe mata ʼyarta ba tayi anfani da duka connections da take da shi ganin ta karɓe ʼyarta, shima Simon ɗin bai wani damu ba cause yasan ko ba jima ko ba daɗe yarsa kam zata neme biological father ɗinta, Salma Family Lawyer ɗinsu Na’ima ce tun ma kafin ta rabu da Simon, bayan rabuwarta da Simon da abinda abinda bai fi 4 years ba kuma Alhaji Mustapha (Dad) suka rabu da Mariya (Mami) wanda a da suna shiri sosai da Salma, amma tun bayan incident ɗin da ya faru a ranan wanda ya janyo chaos ba ɗan kaɗan ba tayi switching sides, a lokacin Alhaji Auwal (big daddy) da sauran ʼyan uwan Mami ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba ganin halin da ʼyar uwarsu ta shiga as a result of shan giyan Dad, she was in a comer for weeks kafin ta san ma wake kanta, tana farfaɗowa suka maka Dad a court requesting for divorce na ƙanwarsu, duk yanda Dad ya so ya shawo kan matsalar using his money and power kasawa yayi, dan big Daddy sam bai bada chance ba shima, haka ya sake rura wutar rashin son juna da ke tsakaninsu tun kafin ma ya auri Mami, dole ya sake ta ba don ya so ba, ko da aka tashi batun custody na Na’ima, Salma ce tayi ruwa tayi tsaki tana kwantar ma Dad da hankalin cewa kar ya damu bazata taɓa bari a raba shi da yarsa ba kamar yadda bata bari an raba ta da tata yar ba, ai ɗa na kowa ne, kamar yadda tayi a na suhaila haka tayi uwa tayi makarɓiya ta samu custody ɗin Na’ima wa Dad, wanda babu yanda yan uwan Mami basu yi da ita ba amma taki testifying against Dad a court, suna ji suna gani aka karɓe Na’ima aka bashi a ranar ba ƙaramin Mamakin Salma Ammi tayi ba ganin yadda tayi bake-bake a kan lamarin……..

“I’m outside ur gate” message ɗin sadiq ne ya shigo wayarta, dakatawa tayi da scrolling ɗin da taje ta kafe wayar da idanunta, tunda ta dawo basu haɗu ba….

Wani saƙon nasa ne ya katse mata tunanin da ta tafi

“U gonna make me freeze out here, or?”

Ɗan murmushi tayi ta tashi da sauri ta ƙarasa wajen window ɗinta ta ɗan matsar da binds ɗin kaɗan tana leƙa shi, and there he was jingine jikin motarsa hannayensa tucked cikin aljihun jacket ɗinsa, ƙura masa idanunta tayi, kamar ya ji a jikinshi ya ɗaga kanshi saitin window ɗinta da sauri ta sake binds ɗin tana murmushi, mayafinta ta ɗauka ta nufi ƙofa kamar dai shine kaɗai escape ɗinta daga drama ɗin gidannan, tunda ta buɗe ƙofa ya juyo ya zuba mata idanu, a nitse take tafiyarta har ta ƙaraso inda motarsa take,

“Haka kace u were busy today..” ta faɗa tana kallonsa

Ɗan dariya yayi

“To ya kike zare min ido, da kika samu ma na ture all whats making me busy nazo?”

“Ni ban zare maka ido ba” a hankali tayi maganar tana jingina da motar

“Nigeria ɗinne ya saka kika ƙara kyau haka?”

“I guess” dariya suka yi tare, yana kallon yadda take wasa da gyalenta kafin ya mayarda idanunsa fuskarta, a hankali yace

“ive missed u Ni’ima”

Ɗan jim tayi kafin ta ɗan saci kallonsa taga ita yake kallo

“Um.. me ya kawo ka toh ma bayan ko kirana baka yi ba only a message asking how we landed?”

Yana cigaba da kallonta irin kallon da ta kasa gane masa yace

“Didnt want to disturb ur peace ne”

“Tun yaushe ka fara damuwa da wani peace”

Bai amsa ba banda ɗan murmushin da yayi

“Do u care to walk with me?, five blocks? Thats all”

“A sanyinnan?”

“Ai ba sanyi sosai kin dai saba da weather ɗin Ninja, kuma ma ke gashi har gloves kika saka a hannunki nifa?”

Ya faɗa yana ɗaga mata hannayensa like a helpless boy.

Ɗan dariya tayi

“Fine amma 5 blocks” ta faɗa tana juyawa ta kalli gidansu

“Deal”

A hankali suke tafiya side by side, shiru babu mai cewa komai

“I miss this moments and everything about u Ni’ima”

Ɗan dakatawa tayi da tafiyar tana kallonsa, sai da yayi two more steps ya fahimci bata biyosa, juyowa yayi yaganta a tsaye tana kallonsa kamar dai yau ta fara ganinsa..

“What?” Ya tambaya a hankali

“Babu ina so in koma gida ne, sanyi nake ji”

Ɗan shiru yayi yana kallonta, irin kallon da she can feel it under her skin kafin ya ɗage kafaɗa

“Okay…”

Ko kafin ya ƙaraso inda take ta juya da sauri ta fara tafiya, har ƙofar gida inda motarsa take ya rakota, yana kallonta yace

“U seem uncomfortable are u okay?”

“Babu komai ta faɗa tana masa murmushi”

“Tun da kince haka”

Ya faɗa yana buɗe motarsa, juyawa tayi har ta fara tafiya taji yace

“Wait… i forgot something”

Juyowa tayi tana kallonsa, bayan motan ya buɗe ya ɗan sunkuya, ita dai kallonsa kawai take kamar ta samu television, duk wani abu da take hasashe bata so ya zama gaskiya cause yau sadiq daban take gani ba sadiq ɗinta da ta saba da shi ba, tayi nisa a tunanin da take yi taji yayi snapping fingers ɗinsa a fuskarta da yasa ta ƙyafta idanunta tana kallonsa, kafin ta kalli hannunsa da ke ɗauke da bouquet na flowers, very beautiful one, ta zuba musu idanunta.

They were fresh, soft cream roses wanda aka yi mixing da delicate baby’s breath da lilac spray, an ɗaure da purple ribbon. understated and elegant.

Ta maida idanunta kanshi, fuskarta da alamar tambaya

“For you” ta faɗa yana kallonta da murmushi

Ƙara kallon bouquet ɗin tayi ta sake kallon fuskarsa,

“Na miye?”

Shafa bayan kanshi yayi nervously

“I dont know… na barka da dawowa? Or maybe i didnt text more, or i just missed u”

Kyafta idanunta tayi amma ta gagara ce masa komai, miƙa mata su yayi yana kallonta, a hankali ta saka hannu ta karɓa gently.

“Ni ka siya ma su?”

“Yes why?, ure just a girl and u need flowers dont make it wierd”

“Nagode” ta faɗa a hankali da murmushi a kan fuskarta, tana rungume da bouquet ɗin tana kallonsa

“Wow” ta jiyo muryar suhaila daga bayanta, juyawa tayi tana kallon Suhailar da ta ƙaraso wajen tana kallon flowers ɗin hannunta sanann ta kalli saɗiq da shima ya dakata yana kallon Suhailar,

Tana sanye da trench coat camel colour, sai designer boots dake ƙafafunta, da ɗan ƙaramin baƙin jaka a hannunta. Ɗauke idanunta tayi daga flowers ɗin ta kayar kan sadiq,

“Didnt know the city had grown so romantic”

“Suhaila” Na’ima ta faɗa tana kallonta

“ dont be shy bazaki introducing ɗina wajen saurayin naki bane?”

Shi dai sadiq kallonsu kawai yake yana karantar yanayin Na’imar, ajiyar xuciya ta sauƙe a hankali kafin ta dube shi ganin ita yake kallo yasa ta ce

“Ba saurayina bane…”

“Sadiq this is suhaila, yayata ce”

Ɗan kallon suhailar yayi sai dai baice komai ba, itama suhailar shi take kallo da wani makirin murmushi a kan fuskarta

“So sadiq are u around here?”

“Eh” kawai ya faɗa a taƙaice

“So kai da Na’ima is it something serious?”

“Suhaila…” Naima ta katse ta, ta juyo tana ma Na’imar wani kallo,

“miye? Ai ban taɓa ganin kin kawo wani gida ba, bare kuma Flower boys…” ta faɗa tana ɗan kallon sadiq

Wani kallo sadiq ke ma Suhaila da Naima ta gagara fassara, sai kuma ya cije lips ɗinsa kaɗan

“Kar ki fassara abinda kika gani, we only went for a walk”

“Au haba? To ba damuwa ai, carry on pls, ill just text my mummy that na ganku a street being all ROMANTIC”

Ta faɗi romantic ɗin tana kallon cikin idanunsa.

Zaro idanunta Na’ima tayi tana kallon Suhaila cike da mamaki, Suhaila tayi dariya tana kallonta,

“See u at home flower girl”

Daga haka tayi gaba abinta, duk suka bita da kallo har ta buɗe motan friend ɗinta da yazo ɗaukanta ya ja suka yi zooming off.

Ɗan kallonta yayi a hankali kafin ya sauƙe ajiyar zuciya

“That was…”

“Normal” ta katse sa da sauri

Shiru ya ɗanyi yana kallonta kafin yace

“She’s ur family?”

“Eh” ta faɗa a taƙaice

Gyaɗa kai yayi a hankali

“Okay see ya”

Ya faɗa yana zagawa ya shiga motarsa

Har ya bar layin tana tsaye, kafin ta juya jikinta a sanyaye ta koma cikin gida riƙe da bouquet ɗin flowers ɗin.

Lagos.

Ƙarfe 1:20 na dare, Zare jikinta Amira tayi a hankali daga nasa tana kallon kyakkyawar fuskarsa, ta gyara zamanta a kan gadon ta ƙurawa fuskarsa idanu ta kai hannu kamar zata shafa sai kuma ta fasa, a hankali without making motsinta obvious ta ƙarasa ta janyo wayarsa da ke gefen bedside, buɗe wayar tayi ta jingina da gadon ta hau bincike kamar akwai abinda ta ajiye a cikin wayar, ganin duk babu abinda take tunani ta ajiye wayar ta ɗauko ɗaya wayar shima ta hau bincikawa tun daga call logs ɗinsa wanda taga da Nasir suka yi wayar ƙarshe, har zuwa messages da photos ɗinsa, chats ɗinsa babu abinda bata bincikawa..

Da sauri ta sake wayar a kan gadon tana kallonsa, bata ma san yaushe ya farka ba at all ta fara kame kame, sauƙa yayi daga kan gadon, dogon wandon bacci ne kawai a jikinsa ta bishi da kallo har ya ƙaraso ya sa hannu ya ɗauki wayarsa daga gefenta yana kallonta kafin ya juya ya ajiye su a gaban mirror, har ya nufi hanyar toilet sai kuma ya dawo, yana kallonta ya nuna mata wayoyinsa da ya ajiye gaban mirror

“Amira”

Ɗan kallonsa tayi sai kuma ta juyar da kanta ta mayar gefe

“What exactly are u looking for? Me kike nema?”

“Nothing ai yanzu zan mayar maka da wayarka fa”

“Never again!! Kar ki sake”

Ya faɗa yana kallon cikin idanunta da ya sa tayi saurin gyaɗa masa kai ba tare da ta shirya yin hakan ba.

Juyawa yayi ya wuce banɗaki, bai jima ba ya fito ya koma ya kwanta

“Sleep or Dont”

Daga haka ya lumshe idanunsa yana tuno maganganun da sukayi da Amminsa ɗazu, which zuwa yanzu he dont think hell ignore..

Kwanciya itama tayi ɗan nesa da shi ta rufe idanunta amma sam baccin yaƙi zuwa, bata san meyasa zuciyarta take gagara sukuni ba haka kawai, ta yarda da shi ɗari bisa ɗari amma ji take gwara ta saka ido dan dai namiji ba’a shaidansa. Amma tasan yanzu ko da giyan wake bazata sake taba masa waya ba tunda har ya faɗa ɗin….

Jiya kunsha comments, was just seeing comments flying nace toh ko kufa ???? tnk u lovelies ❤️

Tana tsaye a kitchen tana slicing fruits, tana yi tana hamma, kayan bacci ne a jikinta riga da wando, Saif da ke shirye tsaff yana tsaye a kusa da ita a kitchen ɗin yana mata maganan da bata ma gane me yake cewa, dan Sam baccin bai isheta ba, its just 11:30 na safe fa amma zai wani tashe ta wai ta slicing masa fruits, duk masu aikin gidan miye anfaninsu da zaice bazata saka su ba? Ita takura ne sam bata so wallahi, shiyasa idan yayi tafiya take cin karanta ba babbaka haba ya fiye takura, tunowa da tafiye tafiyensa da kuma abinda ka iya faruwa a inda zaije da bata nan ya sa ta buɗe idanunta da kyau da sauri, ai ta gwammace takurarsa sau miliyan akan tafiye-tafiyensa da bata san su waye yake haɗuwa da su ba, kuma bata kusa bare ta saka masa idanu…

More than 30minutes kenan da ya sakata slicing masa fruits kamar wanda ya aiki bawa garinsu, miƙewa yayi, ya saka hannunsa ɗaya a aljihunsa yana tafiya a hankali ya nufi kitchen ɗin, tsaye yayi bakin ƙofa yana kallon Amira da ke bawa Saif kankana a baki duk ruwan kankanan ya ɓata masa gaban white shirt ɗinsa, girgiza kai kawai yayi

Ya ɗan yi gyaran murya duk suka juyo, Saif ya tafi wajensa da gudu, dakatar da shi yayi yana kallonsa da murmushi ganin yadda kayansa ya ɓaci

“Tell mary to change ur clothes”ya faɗa yana nuna masa hanyar ɗakin Mary, da gudu ya wuce sa ya tafi faɗa mata saƙon Papa..

Ya ƙaraso cikin kitchen ɗin yana kallonta da lazy eyez ɗinsa, kafin yayi magana ta rigasa,

“yanzu fa nake shirin kawo maka, Saif ne ya dinga ɓata min lokaci”

Murmushi kaɗan yayi kawai yana kallonta, ya karɓi plate ɗin hannunta ya ajiye yana bin yanda ta maida wajen kamar wacce ya sata girka abu, duk ta zubar da ruwa a wajen da bai san na miye ba, peels all over the sink, ya kalli blender da tayi plugging da socket da bai san me zata yi da shi ba.

“U know what ki barshi kawai zan ɗan fita ne, sai na dawo”

ƙura masa idanunta tayi kamar zata iya gano inda zashi daga fuskarsa

Ganin bata amsa ba ya juya ya nufi ƙofa tayi saurin shan gabansa

“To ina zaka je da sassafennan?

Kallonta ya tsaya yi da mamaki, ya bi gefenta zai wuce ta sake tarewa

“Ya zaka ce min zaka fita da sassafennan wai, bayan ka sa in maka abu, na sha wahala na maka ko sha bakayi ba kace zaka fita toh ina zaka je? Wacece take jiranka a wajen da ta fini muhimmanci”

Kallonta kawai yake yi cause wannan ya wuce insecurity ɗinta ya koma disrespect

In a very serious tone yace

“Bani hanya in wuce”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved